Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"Ina katin da kika siyo? bani_bani in saka da sauri, yau da sa'a na tashi, abun da na shirya a cikin ƴan mintuna har na samu nasara an wuce gurin." Haulatu ta karb'i wayar Uwa ta fara saka mata katin ta ce. "Me kika shirya?" Uwa ta ce. "Lambar mahaifiyar Umar na je samuwa a gurin Sarki, kuma wallahi cikin ruwan sanyi na samu, ban yi tunanin hakan ba ma." Haulatu ta ce. "Me zaki yi da Numbern ta ke kuwa? bayan kin ce ba ta da kirki." Uwa ta zauna ta ce. "Ke dai kira mun Lambar farko a gurin kira, ita ce tatan, zaki ga abun da zan yi da ita." Babu musu Haulatu ta yi dialling numbern, cikin sa'a bugu ɗaya ta shiga ta fara ringing, saka wayar ta yi a hands-free ta miƙawa Uwa, sai da ta kusan katsewa sannan aka ɗauka. Cikin kwantar da murya Uwa ta ce. "Assalamu alaikum, Ranki ya daɗe barka da yamma, dafatan an wuni Lafiya?" Cikin izza irinta Mom ta ce. "Yawwa, wake magana?" Uwa ta yi murmushi mai sauti ta ce. "Uwa ce matar Sarkin Kumurya abokin mijinki." Ɗan jim Mom ta yi tana tunani, lokaci ɗaya ta haɗe rai cikin ƙyama ta ce. "To ya aka yi?" Uwa ta ce. "Uhm dama akan yaronki ne Uwar na kira in faɗa miki wani muhimmin abu." Tsaki Mom ta yi wani irin takaici na cika mata zuciya, Umar ya ja mata yau tana waya da matar ƙauye. Cikin ƙagauta ta ce. "Ina jin ki." Uwa ta gyara zama ta ce. "Hajiya ba gulma ba ko wani abun, amincin dake tsakanin mijina da naki ne ya saka zan faɗa miki wannan abu....." Cikin hasala Mom ta ce. "Malama ki faɗi abun da zaki faɗa da'Allah cikin sauri, dan ina da abun yi." Ta ƙara jan tsaki cikin takaicin kanta da ta tsaya ma tana sauraren wannan yar ƙauyen, har za ta katse wayar ta tsinkayi muryar Uwa tana cewa. "Hajiya wata mata ce a cikin garin nan irin zuwau ɗin nan ba ƴar asalin garin ba ta lashe kurwar Umar tun zuwansa garin nan, da yake mayya ce ita, in tak'aice miki zance kullum yana gidanta gurin makauniyar ƴarta yana faman yin wahala da su, shine cinsu, shansu, suturarsu da komai nasu. Ta yi masa siddabaru irin nasu na mayu ta mallake shi ta cusa masa son ƴarta, kuma yarinyar ma fa makauniya ce, ba......" Cikin tsananin kad'uwa Mom ta ce. "What? Wanne Umar ɗin? Ba dai Faruq ɗina ba ko?" Uwa ta ce. "Shi mana, ko ba da matar Alh. Aliyu Kaduna nake magana ba?" Mom ta ma rasa me za ta ce saboda tsabar firgici, Son ɗinta ne Mayya ta kama shi ya tare a gindinta? Wato shi yasa ya ƙi barin garin? Tsabar ya raina mata hankali shine ya ce mata shukar da suka yi ce ta lalace sai da aka sake wata? ashe wata sabuwar shukar da zai tozarta ta ya bak'anta mata rai ya dasa? To kuwa wallahi zai san ita ce ta haife shi ba shi ya haife ta ba. Katse Wayarta ta yi ba tare da cigaba da sauraren soki burutsun zancen da Uwa ta cigaba da yi mata ba. Jiki a sanyaye Haulatu ta dubi Uwa ta ce. "Na shiga uku, haka dama matar nan take? Ji yanda take magana fa kamar irin da bayin nan nata take yi." Uwa ta ce. "Ai tafi ma haka, amma ni ko ajikina, yanzu plan ɗinmu na farko zai yi aiki sai mu tafi na biyu, dan na san a yau sai ta raba Umar da waccan makauniyar Yarinyar, ai ina sane na kunna ta, na san hankalinta ba ƙaramin tashi zai yi ba." Haulatu ta ce. "To amma idan mun ci nasara kina ganin wannan uwar tasa zata bari a yi auranmu da Umar kuwa?" Uwa ta ce. "Ki saka a ranki tamkar an yi gama, auranki da Umar ba, ni kaɗai na san ta inda zan ɓullowa al'amarin." Murmurshi Haulatu ta saki cikin jin daɗi, a ranta na hango ranar da za'a ce an aura mata aure da Uwar, wayyo daɗi, ta auri ɗan birni ɗan gayu kyakkyawa ɗan masu kuɗi, ranar ta san sai farinciki ya kusa hallaka ta. Umar ne zaune akan kujera ƴar tsugunno yana kallon A'isha dake zaune akan tabarma, sanye take cikin atamfa mai kyau ɗinkin doguwar riga, ɗinkin ya yi dass a jikinta kasancewar yanzu ta ƙara murjewa sanadiyyar cima mai kyau da kuma kwanciyar hankali da suka samu. Atamfar da Innar Ma'u ta ɗinka musu ce Sallar da ta wuce, Inna ta yi mata d'auri duk da ba wani na gayu ba ne amma ya yi mata kyau, fuskarta ta sha powder da Umar ya siya mata, ɗan ƙaramin lips ɗinta sai k'yalli yake na white lipstick. Kallon ta yake yi cikin wani irin yanayi ko ƙifta idonsa ba ya yi, zuciyarsa na bugawa a hankali a hankali, wani irin son A'isha da tausayinta na ƙara mamaye ko'ina a cikin zuciya da gangar jikinsa, har mamakin kansa yake yi yanda a cikin 5 months ya faɗa cikin irin wannan zazzafar soyayyar akan ƴar ƙanƙanuwar yarinyar da ko autarsu ta girme ta, ko a mafarki bai taɓa tunanin hakan zai kasance da shi ba. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, cikin kulawa ganin yanayin A'isha ya ce. "Me ya faru kika yi shiru Humairah? And yanayinki ya nuna mun kamar akwai abun da yake damunki, tell me what happened?" Idanun A'isha akan fuskarsa kamar mai ganin sa cikin sanyin murya ta ce. "Ban san me yake damuna ba nima, kawai ina jin jikina babu daɗi ne." Umar ya ce. "Ko ba ki da lafiya ne?" Girgiza masa kai ta yi ta ce. "Lafiyata ƙalau, kawai gabana ne yake ta fad'uwa." Umar ya ce. "Subhanallahi, ki dinga maimaita innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, ko kina ambatar sunan Allah, za ki ji sauƙin abun." Ta ce. "Toh, Insha Allahu." Numfashi Umar ya sauke dan shi ma haka kawai ya ji jikinsa da zuciyarsa wani iri, bai kuma san dalili ba. Kamar A'isha za ta yi kuka ta ce. "Ni fa Yaya Umar a rayuwata so nake kawai in gan ka, in ga ya kake, amma na san daƙyar idan hakan za ta faru." Hannunta Umar ya kama ya ce. "Watarana za ki ganni Insha Allahu Humairah, a cikin watan nan nake so mu tafi Kano a duba miki idonki a yi miki magani, ki daina damuwa Insha Allahu zaki warke ki cigaba da gani kamar kowa." A'isha ta ce. "Allah ya yarda." Murmurshi Umar ya yi ya ɗauko key ɗinsa ya gogawa A'isha a gefen wuyanta, ɗan zabura ta yi ta sosa wurin tana ɓata fuska, kan ƙafarta Umar ya kai key ɗin ya ƙara goga mata, da sauri ta janye ƙafar a tunaninta wani k'waron ne yake bin jikinta. Murmurshi Umar ya yi mai sauti ganin yadda ta zama uncomfortable a gurin sai juye_juyen kai take yi. Turo baki ta yi ta ce. "Kai kake saka mun wani abun a jikina ko?" Umar ya ce. "Ba ni ba ne, Ni wayata ma nake kallo." Ta ce. "Na san kai ne, ai ba yau ka saba mun haka ba." Uwar ya ce. "Ba fa ni ba ne." Shiru ta yi alamar ta yi fushi. A hankali ya ce. "Sorry Dear na daina." A'isha ta ce. "Ai na san baka daina ba, kullum sai ka tsokane ni ka tsorata ni, ranar nan har kuka ka saka ni dan ka ga bana gani." Cikin shigar rarrashi ya ce. "Na ce fa ki yi hak'uri na daina daga yau." A shagwab'e ta ce. "Ba zan hak'ura ba ni dai, kuma ba ruwana da kai." Umar ya marairaice ya ce. "Please... Ni ne fa, dan Allah ki yi hak'uri." A'isha ta ce. "Tom shikenan na hak'ura." Ya ce. "Yawwa Darling, kawo hannunki ki ga wani abu. Ba ta ce komai ba ta miƙa masa hannun damanta. A hankali ya zare wani ring ɗin azurfa mai kyau dake ƙaramin finger ɗinsa ya zira mata a babban ɗan'yatsanta yana kallon cikin idonta. Zare hannunta ta yi daga cikin nasa a hankali ta shiga murza zoben da ya saka mata da murmurshi ɗauke akan fuskarta. Umar ya ce. "Wow ba ki ga yanda ya yi miki kyau ba." Ta ce. "Ka bar mun ne?" Ya ce. "Eh mana, dan ma sauran sun miki yawa ne da duka na hannuna zan baki." Ta ce. "Saboda me? Kai baka so ne?" Ya ce. "Zuciyata ce kawai ta bani umarnin in bar miki su." A'isha ta ce. "Na gode, amma na ji ya ɗan mun yawa fa, ba zai faɗi ba." Umar ya ce. "Ba zai faɗi ba, ai ba sosai ya yi miki yawan......" Vibrate ɗin da wayarsa ta fara ne ya katse masa maganarsa. Zaro wayar ya yi daga aljihun gaban rigar sa ya duba, Mom ce take kiran sa, haka kawai ya ji gabansa ya yanke ya faɗi. Jiki a sanyaye ya ɗaga kiran ya kara a kunnensa tare yin sallama. Cikin kaushin murya ba tare da ta amsa masa sallamar ba ta ce. "Sannu Faruq." Cikin ladabi ya ce. "Me ya faru Mom?" Dan jin yanda ta yi magana ya san ba ba ƙalau ba. Cikin tsantsar ɓacin rai ta ce. "Ban sani ba, na kuma gode da abun da ka yi, ka kyauta mun ka kyautawa kanka, amma ba lefinka ba ne, laifin mai ɗaure maka k'ugu kake abun da ka ga dama ne. To bari ka ji, wannan karon komai zai faru sai dai ya faru, ka shirya gobe da safe za'a zo a ɗauke ka, ka gama zaman nan ƙauyen nan, kai da garin kuma har abada ." Cikin damuwa Umar ya ce. "Mom Please listen to me, na faɗa miki fa shukar da muka yi ce aka samu matsala amma...." A fusace ta ce. "Shukar Ubanka? ka tsaya dai kana shuka abun da ka san baza ka taɓa girba ba, ka je ka tare a jikin matar da ba'a san asalinsu ba kana kashe musu uban kuɗi ko? to tatsar ta isa haka, ta samu iya rabonta, kai kuma zaka zo ka same ni ne har inda nake, wallahi sai na nuna maka ɓacin raina irin wanda ba ka taɓa gani ba." Dafe kai Umar ya yi ya ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Mom wa ya faɗa miki wannan maganar?" Mom ta ce. "Ban sani ba, ashe shi yasa sai inji mahaifinka yana ta cewa ya tura maka kuɗi, in rasa uban me kake yi da kuɗin ashe ga inda suke tafiya, Khausar ma kullum cikin yi mun complain ɗin irin wulaqancin da kake yi mata take, ashe shi ma da dalili." Sosai hankalin Umar ya tashi da jin Mom ta samu labarin yana tarayya da su A'isha, domin bai san hukuncin da za ta ɗauka akan hakan ba. K'wafa Mom ta yi ta ce. "Wallahi, wallahi, wallahi Faruq na yi rantsuwa sau uku idan ba ka baro garin nan a gobe ba sai dai ka nemi wata Uwar ba ni ba, kuma ko da wasa bayan ka dawo ka cigaba da mu'amala da faƙiran mutanen nan ban yafe maka ba." Tana gama faɗin haka ta katse wayar. Sunan Allah kawai Umar yake maimaitawa a fili cikin tsantsar damuwa. A rud'e A'isha ta ce masa. "Yaya Umar me ya faru? Wa ya kira ka a waya? Me aka ce maka?" Duban ta Umar ya yi da idanunsa da suka fara sauya kala saboda jin kalaman Mahaifiyarsa masu tsauri a gare sa, cikin sanyin murya mai cike da damuwa ya ce. "Babu komai Humairah, zan je gida in dawo, tashi mu je in raka ki ɗaki, idan Mama ta tashi ki ce mata na wuce." Kamar za ta yi kuka ta ce. "Ko mutuwa aka yi muku?" Girgiza kai kawai ya yi dan ko magana ba ya son yi, kama hannunta ya yi ya kai ta ƙofar ɗakin, sai ta kasa shiga ta tsaya kawai cikin yanayin damuwa. Shi ma kasa tafiyar ya yi ya tsaya yana kallon ta, yana jin kamar ba zai iya rayuwa ba idan babu ita. A hankali ya juya ya fice daga cikin gidan, dan kallon ta ma ba ƙaramin ƙara karyar masa da zuciya yake ba. Jin ya fice A'isha ta ja ƙafarta daƙyar wadda ta ji ta yi mata nauyi ba tare da san dalili ba ta shige ɗakin, wasu hawaye masu ɗumi suka kwaranyo daga cikin idonta ba tare da ta shirya musu ba. Daƙyar Umar ya iya kai kansa gidan Sarki saboda sarawar da kansa yake masa, yana zuwa ya buɗe ɗakin da yake ya faɗa kan katifa ya kwanta ruf da ciki. Wani irin zafi zuciyarsa take masa, bai shirya barin A'isha yanzu ba, be shirya yin nesa da ita ba, be shirya tafiya ya bar su a cikin wannan garin da ba'a k'aunar su ba, be shirya tafiya ya bar ta a cikin makanta ba, ya gama tsarawa a cikin watan nan zai ɗauke ta ya kai ta gidan k'anwar mahaifinsa ita da Inna su zauna kafin a gama zirga-zirgar zuwa asibiti ganin likita, dan ya san ita kaɗai ce zata yi masa wannan taimakon cikin ruwan sanyi. Amma Mom ta wargatsa komai, domin ba shi da zaɓi face ya bi umarninta ya koma gida a gobe. Wunin yau gaba-d'aya cikin damuwa ya yi shi, gaba-d'aya jinsa yake wani iri kamar mai cuta, Sallah ce kawai take fitar da shi waje. A ɓangaren A'isha ma haka ne, dan ita kuka ta sakawa Inna na babu gaira babu dalili, rarrashin duniya Inna ta yi mata amma ta ƙi yin shiru, ta kuma ƙi cin abinci, gashi ta ƙi faɗa mata abun da yake damun ta. Abun da ya ƙara tayarwa da A'isha hankali ganin yamma ta yi lokacin zuwan Umar ya yi amma bai zo ba, Inna ma ta yi mamakin hakan, amma sai ta ɗauka wani uzurin ne ya tare shi. Daren yau Umar bai rintsa ba, kwana ya yi yana tunanin mafita, bai taɓa tunanin ƙaddara makamanciyar wannan za ta riske shi ba a cikin rayuwarsa, abun da yake ƙara tayar masa hankali furucin Mom na ƙarshe, da ta ce ko bayan ya koma gida ya cigaba da mu'amala da su A'isha ba ta yafe masa ba. Tambayar kansa ya dinga yi wa ya faɗawa Mom wannan zancen? Shi dai ya san ba ta mu'amala da kowa a garin nan, kuma mahaifinsa ma haka balle ya ce ko shi ya samu labarin ya faɗa mata, ya san Sarki kuma ba zai taɓa faɗa masa ba. Koma waye bai yi masa adalci ba, domin kuwa ya saka ana ƙoƙarin yi masa katangar ƙarfe da farinciki a cikin rayuwarsa, dan matuƙar ya rabu da A'isha to tabbas ya san tausayin ta da k'aunar ta dake cike fal a cikin zuciyarsa ba zai bar shi ya cigaba da jin daɗi da walwala kamar kowa ba a cikin rayuwarsa, matuƙar ba cigaba da kasancewa da ita ya yi ba har ƙarshen rayuwarsa..........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣5️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..........Washegari daƙyar Umar ya iya fita Masallaci da asuba, saboda wani irin sanyi da yake ji yana ratsa ƙasusuwan jikinsa, ga wata irin kasala da ta lullub'e shi. Bayan ya dawo ya shiga haɗa kayansa cikin ƙarfin hali, ganin abun yake tamkar a mafarki wai yau zai tafi ya bar A'isha. Bayan ya gama haɗa komai nasa ya yi wanka ya shirya cikin manyan kaya. Ƙarfe Bakwai da mintuna Mom ta kira sa, jiki a sanyaye ya ɗaga kiran. Ba tare da ta bi ta kan gaishe tan da yake yi ba ta ce. "Ina fatan ka gama shiryawa? Dan tun asuba driver ya taho ɗaukar ka." Cikin sanyin murya mai cike da damuwa ya ce. "Na gama." Mom ta ce. "Better, ka san kuma me zaka faɗawa Mahaifinka idan ya ga ka dawo dan ban sanar masa zaka dawo yau ba." Umar ya ce. "Zan kira shi yanzu in faɗa masa, ba zai ji daɗi ba idan ya ga kawai na dawo kuma ban sanar masa ba." Mom ta ce. "Kai ka sani kuma, saura ka yi kuskuren ambatar sunana a cikin zancen dawowar taka." Umar ya ce. "Na san me zan ce masa." Taɓe baki Mom ta yi ta kashe wayarta. Numfashi Umar ya ja ya fesar, Numbern Abbansa ya kira ya sanar masa zai dawo gida yau. Cikin mamaki Abba ya ce. "Yau yau ɗin nan kuma Faruƙ?" Umar ya ce. "Eh." Abba ya ce. "Wanne irin abu ne haka kamar yaƙi? Tafiya lokaci ɗaya, kuma sai a yau ɗin zaka sanar mun?" Umar ya ce. "Tun jiya nake ta ƙoƙarin kiran ka ya ƙi lafiya babu network, sai text na yiwa Mom na faɗa mata, ina jin mantawa ta yi ba ta sanar maka ba." Abba ya ce. "To ai shikenan, Allah ya kawo ka lafiya, bari na sanarwa Ado driver ya zo ya ɗauko ka." Umar ya ce. "Ai Mom ta faɗa masa ma har ya taho." Abba ya ce. "Alright, Allah ya kawo ku lafiya, amma Are You ok Faruƙ?" Umar ya ce. "Lafiya ƙalau Abba, me ka ji?" Abba ya ce. "Muryarka na ji kamar ta wanda ba shi da lafiya, ko wani abun ne ya faru?" Umar ya ce. "Babu komai Abba, yanzu na tashi daga bacci ne." Abba ya ce. "Okay, to Sai kun ƙaraso, Allah ya tsare hanya, kar ka manta da addu'a." Umar ya ce. "Insha Allah Abba, na gode." Daga haka suka yi sallama ya katse wayar. Miƙewa ya yi yana jin yanda kansa da ƙirjinsa suka yi masa nauyi saboda damuwa ya fice daga ɗakin ya nufi cikin gidan Sarki. Da mamaki Sarki yake duban Umar bayan ya faɗa masa yau zai tafi, yana jinjina kai ya ce. "Ikon Allah, kuma Umar sai yau ɗin da zaka tafin zaka sanar mun?" Ɗan murmushi ya yi bai ce komai ba. "Sarki ya ce lafiya dai ko wannan tafiya haka kamar wahayi?" Umar ya ce. "Lafiya ƙalau, dama ka san already na gama abun da ya kawo ni garin nan, zama na yi kawai saboda ban gaji da garin ba." Cikin murmushi Sarki ya ce. "Yanzu kuma ka gaji kenan?" Umar ya ce. "A'a, na kusa komawa karatu ne, to ina son zan ɗan yi wasu shirye_shirye kafin na tafi." Sarki ya ce. "To ai shikenan, Allah ya taimaka, amma za mu yi kewar ka sosai." Murmusawa kawai ya yi bai ce komai ba. Sarki ya ce. "Bari na saka a haɗa maka tsaraba, duk da ma dai a ƙurarren lokacin ka faɗi tafiyar, da ko tun jiya ne ka sanar mun ai da an san abun yi." Umar ya ce. "An goge Allah ya saka da Alkhairi, bari na shiga ciki na yi musu sallama." Sarki ya ce. "To sai ka fito." Yana fita suka ci karo da Ɗan_juma ya fito daga cikin gida, wani irin kallon banza Ɗan'juma ya dinga bin sa da shi, shi kuwa tun kallon farko da ya yi masa bai ƙara kallon inda yake ba ya shige ciki. Sashen Uwa ya fara shiga, tana zaune a falo tana zuba abin kayarwa zata ci Umar ya yi sallama. Cikin mamaki ta ɗago tana kallon sa tare amsa masa sallamar. Barin abun da take yi ta yi cikin faɗaɗa fara'a ta ce. "Áaa Umaru kai ne a gidan namu? Bismillah zauna akan kujera mana, ka tsaya a bakin ƙofa kamar wani baƙo. Bai ce komai ba ya zauna a ƙasa saman tabarma ya gaishe ta. Ta amsa kamar bakinta zai tsage biyu saboda fara'a ta murnar zuwan Uwar. Haulatu tana ɗaki tana shirin makaranta kamar a mafarki ta ji Uwa na ambatar sunan Umar, cikin sauri ta ƙarasa shirinta ta fito. Zuwa lokacin Uwa ta gama cika shi da surutunta da ba fahimta yake ba. Ido a waje Haulatu ta ce. "Ina kwana Umar." D'agowa ya yi ya kalle ta sau ɗaya tare da amsa mata ba yabo ba fallasa. Uwa ta dube ta, ta ce. "Had'o masa abun kari mana, kya tsaya kina kallon sa kuma." Haulatu ta yi murmurshi sannan ta ce. "Toh." Uwa ta tashi tana gyara ɗaurin zanin jikinta, gaba-d'aya ta rud'e sai wani irin murmushi take yi, shi dai kallo kawai yake bin ta da shi. Furewater ta kawo masa guda biyu ta ajiye a gabansa tare da faɗin. "Ka sha ruwa ɗana kafin ta kawo abincin." A hankali ya ce. "Alhamdulillah na gode." Uwa ta ɓata fuska ta ce. "Haba Umar kamar ba gida ba? Nan fa gidanku ne wata alkunya kuma zaka yi? kai da mai iya kawo wani ne ma ka ɗibi abu ka ba shi a gidan nan." Cikin mamakin yanda ya ga tana rawar jiki a kansa ya ce. "Na ƙoshi ne Mama shi yasa." Dai-dai nan Haulatu ta fito da kayan karin da aka ce ta haɗowa Umar a hannunta. Cigaba da magana Umar ya yi ya ce. "Dama yau zan koma gida ne shine na shigo in muku sallama." Haulatu dake tsaye ba ta san lokacin da ta saki kayan hannunta suka zube a ƙasa ba, saurin miƙewa Umar ya yi tare da ja baya yana yatsina fuska. Cikin ɗaga murya Uwa ta ce. "Tafiya kuma Umar? Kana nufin gida zaka koma?" Ya ce. "Eh Insha Allahu." Bai jira cewar su ba ya tsallake kunun gyaɗar da ya mamale a ƙasa da k'osai ya fice daga ɗakin. Haulatu da ta yi mutuwar tsaye cikin damuwa ta ce. "Na shiga uku, Uwa kina ji fa wai tafiya zai yi, to a ina zan ƙara ganin sa balle har a yi maganar Aurenmu?" Cikin karaya Uwa ta ce. "Na rasa ma bakin magana Haulatu, wannan shine ga bikin zuwa amma babu zanin d'aurawa." Zama Haulatu ta yi dab'as a ƙasa, ba ta sani ba ashe ta miƙe ƙafarta akan kunun gyaɗan dake zuba uban tiriri, da sauri ta janye ƙafarta tare da sakin ƙarar azaba, a rud'e Uwa ta yi kanta tana tambayar ta abun da ya faru. Inna ce zaune a gaban A'isha tana kallon ta cikin takaici da kufula ta ce mata. "Wallahi A'isha zan saɓar miki, dan iskanci tunda kika tashi yau kike mun kukan banza, na tambaye ki me yake damunki kin ce ba komai, yanzu kuma na kawo miki abinci tun ɗazu kin ƙi ci." Aisha ta goge idonta ta ce. "Ki yi

Chapter 10 of 20