da Inna ta zo ta haɗa ta da wani mutum da suke turo masa da kaya yake sayarwa anan wani ƙauye Luran dake gaba da su, kayan za su dinga sauka a gurin Inna, shi kuma zai dinga zuwa yana ɗauka, idan ya sayar ya kawo mata kuɗin, a ciki ita ma sai ta dinga ɗaukar nata percentage ɗin. Da da wani mutumi suke haka, yanzu kuma ya rasu, shi ne Innar Ma'u ta cewa ƙaninta kawai su dinga ba wa Inna, ta san za ta riƙe musu amana, kuma hakan zai taimaka mata matuƙa da samun ɗan na kashewa. Ba ƙaramin farinciki Inna ta yi da jin wannan labarin ba, ta ƙara tabbatarwa idan aka ce mutum masoyinka ne mai son cigaban ka har abada hakan take, ta dinga yi wa Innar Ma'u godiya har da hawayen farinciki. Bayan kwana biyu da zuwan Innar Ma'u aka turo kayan.
*One Year later*
Alhamdulillah rayuwa ta sauyawa su Inna, don harkar turo kaya nan ba ƙaramin taimakon su ta yi ba, don a yanzu sun fi ƙarfin ci da sha da wasu buƙatun. Ƙalubale da ƙuncin rayuwa sun ci karanci a gare su, duk da ba su daina fuskantar tsangwama da tsana daga mutane ba, amma hakan ba ya damun su, sun toshe kunnuwansu tare da miƙa komai ga Ubangiji. A'isha ta ƙara girma da zama ƴanmata, kasancewar tana da garin jiki da diri Masha Allah. Har wannan lokacin ta kasa mantawa da Umar a cikin ranta, musamman idan ta kalli zobensa dake sanye a ɗan'yatsanta wanda ya ba ta. Yanzu tana J.S.S 3, suna daf da zana jarabawar junior WAEC. Har wannan lokacin Inna ba ta ba ta labarin asalinsu ba, ita ma ba ta kuma tambayar ta ba, amma kullum da son jin hakan take kwana take tashi.
Yau da yamma Inna tana yanke mata farce ta ce. "Insha Allahu wani watan dai za mu je asibiti a duba idon nan naki." Cikin farinciki A'isha ta ce. "Allah ya kai mu." Inna ta ce. "Amin, don ma kuɗin ya ƙi taruwa ai da tuni mun je, kullum da rashin ganin nan naki nake kwana nake tashi, abun yana damuna sosai, sai dai babu yadda muka iya da ikon Allah, haka ya so da mu." A'isha ta ce. "Ni fa Inna har na saba da rashin ganin yanzu, gani nake ma kamar idon ba zai buɗe ba." Cikin tausayawa Inna ta ce. "Zai buɗe da yardar Allah, ai ba a cire rai da rahamar Ubangiji."
"Allah ya sa Innata, ni ma ina so ya buɗe ko don na ƙara ganin ki a rayuwata, na ga ya kika koma yanzu."
Murmushi Inna ta yi ta ce. "Yadda kika san ni haka nake, ba abun da na ƙara sai tsufa." Ita ma murmushin ta yi, cikin ranta tana addu'ar Allah ya amsa addu'arsu idonta ya buɗe.
Cikin dare suna cikin bacci A'isha ta ji ana lalubar ta cikin wata irin siga da ta kasance baƙon al'amari a gare ta, a firgici ta farka jin ana ƙoƙarin danne ta tare da ƙwala kiran sunan Inna.........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
_By_
_Zeey Kumurya_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*2️⃣1️⃣*
Kamar an saka iska an janye mutumin haka A'isha ta ji ya tashi daga jikinta cikin sauri, kuka ta fashe da shi tana ƙara kiran sunan Inna.
"A'isha! A'isha! Lafiya? Me ya faru?"
Inna ta tambaya a gigice bayan ta farka tana laluben fitila.
Cikin rawar murya da na jiki A'isha ta ce. "Wa...wani ne ya shigo mana Inna." Haske ɗakin Inna ta shiga yi cikin matuƙar tashin hankali, tabbas cikin bacci ta ji kamar mutum ya taka ƙafarta, har tana shirin tashi ta yi wa A'isha faɗa, a zatonta ita ce ta tashi fitsari. Babu kowa a ɗakin, alamun wanda ya shigo ɗin ya yi nasarar tserewa. Ganin yadda A'isha take kuka da rawar jiki wanda ke nuna ba ƙaramar firgita ta yi ba, Inna ta tashi ta ƙarasa kan gadon ta rungume ta. Ƙanƙame Inna ta yi tare da sakin ajiyar zuciya. A ruɗe Inna take haska jikinta tare da faɗin. "Me aka yi miki? Ta yaya kika san wani ya shigo?" Cikin ƙunar rai ta ce. "Ji na yi ana tattaɓa ni tare da ƙoƙarin hawa kaina."
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un."
Inna ta ambata cikin bugawar zuci, wani irin juyawa ta ji kanta ya mata, lokaci ɗaya jiri na neman kwasar ta. Kamar wadda ƙwai ya fashewa a jikinta ta zauna a kan gadon tana jin kamar jini ya daina dawo a jikinta, har lokacin A'isha tana jikinta tana cigaba da kuka. Sunayen Allah da duk addu'ar da ta zo bakinta take karantawa, har ta fara dawowa cikin nutsuwar ta. Cikin sauke numfarfashi ta ce. "Wai me muka yi wa mutane ne? Me ya sa kullum cikin ƙoƙarin saka mu a ƙuncin rayuwa da son cutar da mu ake? Waye wannan ya zo yake ƙoƙarin ɓata miki rayuwa?" Sai ta fashe da kuka, wanda ya ƙara tsinka zuciyar A'isha, ta ƙanƙame ta sosai tare da tsananta kukanta. Ganin kuka ba shi ne mafita ba Inna ta rarrashi kanta ta miƙe ta fara haɗa musu kayansu da abubuwa masu amfani a gare su, ta kai maƙura kuma, abubuwan da ake musu a garin nan ya ishe ta, ko garin gwal ne yau za ta bar shi, ba don dare ba ne da ko awa ba za ta ƙara a cikinsa ba. Ana yin Sallar Asuba ta fito da komai nasu tsakar gida ta kulle ɗakin tana jiran gari ya fara haske su tafi. A'isha da take jin ta tamkar mai cuta ta kama hannun ta, cikin muryar da ta ci kuka ta ƙoshi ta ce. "Don Allah Inna mu koma gurin danginmu, kar mu kuma zuwa inda ba mu alaƙa da su a wulaƙanta mu." Hawaye mai zafi ne ya zubo daga idon Inna, cikin raunin murya mai tattare da ɗimbin damuwa ta ce. "Duk abin da kika ga ya koro ɓera daga rami ya faɗa wuta, to ya fi wutar zafi, ban taɓa tunanin rayuwa za ta zo mini a haka ba, ban taɓa tunanin zan bar rayuwa a cikin ƴan'uwana da dangina ba, amma wani dalili mai ƙarfi ya sa na aikata hakan." Zuciyar A'isha ta sauke, cike da kwaɗayin son jin labarin asalinsu ta ce. "Mene ne dalilin?"
"Ke ce."
"Ni kuma Inna? Me ya faru da ni? Ta tabbata gaskiya ne Baba Malam ba shi ne mahaifina ba?"
Cikin kuka Inna ta ce. "Gaskiya ne, ba shi ba ne."
Runtse ido A'isha ta yi cikin tsananin tashin hankali, duk da zuciyarta ta daɗe da ba ta tabbacin hakan, amma da Innan ta ƙara tabbatar mata sai damuwar ta akan hakan ta ninku, domin kodayaushe cikin fatan Inna ta ƙarya mata hakan take yi. Cikin magana da ƙyar ta ce. "Waye mahaifina to? Don Allah ki sanar mini kar zuciyata ta fashe." Janyo ta Inna ta yi ta rungume tare da faɗin. "Akwai lokacin da nake jira kafin na sanar miki da labarin komai, ki ƙara haƙuri. Ki kuma sani rayuwa cike take da tarin ƙalubale, duk halin ƙuncin da kake ciki wani yana cikin fiye da naka, a kullum ina faɗa miki ki karɓi rayuwa a duk yadda ta zo miki, duk abin da kika ga ya same ki rubutacce ne daga Ubangiji tun fil azil, ki kasance mai gode wa Allah a duk halin da kika tsinci kanki a ciki. Duk wannan abubuwan da suke faruwa za su wuce su zama tarihi watarana da yardar Allah, dukkan tsanani yana tare da sauƙi, mu ci gaba da addu'a kawai." Ɗaga mata kai ta yi tare da ƙara damƙe hannunta a cikin nata, cikin sanyin murya ta ce. "Ke ce komai na rayuwata Inna, kin sha wahala sosai a kaina, Allah ya biya ki da gidan Aljannah, ina son ki fiye da kowa da komai a duniyar nan." Murmushi Inna ta yi mai haɗe da hawaye ta ce. "Babu wahalar da nake sha a kanki, ki daina faɗar haka." Jan majina Aisha ta yi ta ce. "Wataƙila da ke kaɗai kika zo garin nan babu ni ba za ana yi miki cin fuska kamar wanda ake yi miki yanzu ba."
"Hmmmm" Kawai Inna ta ce tare da sauke numfashi.
"Tashi mu tafi, na ga garin ya fara haske."
"Wai ina za mu je?"
"Kano gurin Innar Ma'u, idan muka sauka a tasha zan nemi waya na biya kuɗi a kira mini ita tunda muna da lambarta."
Nunfasawa A'isha ta yi ta ce. "Amma Inna sai nake ganin kamar in muka je za mu ɗora musu nauyi ne." Inna ta ce. "Ba zaman dindindin za mu yi a gurinsu ba, gidan aiki zan nema ko wanke-wanke da shara da wankau ne na dinga yi ana biya na, ko a washegarin ranar da muka je na samu gidan aikin sai mu tafi." Ajiyar zuciya A'isha ta sauke ta ce. "Allah ya sa a dace." Inna tana miƙewa ta ce. "Amin."
Sai da suka daɗe a tasha kafin mota ta cika su ɗauki hanya, kallon ƙarshe Inna ta yi wa garin KUMURYA cikin wani irin yanayi, ranar da ta zo garin ce ta faɗo mata a rai. A'isha ta rasa me ya sa ta ji zuciyarta wani iri, ta daɗe tana fata da addu'ar Allah ya kawo ranar barin su garin, amma kuma ga ranar ta zo ta kasa yin farinciki. Sai ma faɗuwa da ta ji gabanta yana yi. Kwantar da kanta ta yi a jikin Inna tare da lumshe idonta. Cikin kulawa da ƙauna Inna ta ɗora hannunta a bayanta ta ƙara shigar da ita cikin jikinta. Ƙarfe goma da mintuna na safe suka sauka a garin Kano a tashar KANO LINE. Sai a lokacin Inna ta tuna ko sunan Unguwar su Innar Ma'u ba ta sani ba, direban da ya tuƙo su ta roƙa ya ba ta aron wayarsa ta kira ta. Bayan ya ba ta, ta saka lambar ta kira aka ce akashe. Ƙara kira ta yi still nan ma switch up. Jiki a sanyaye ta miƙa masa wayar tare da yi masa godiya ta kama hannun A'isha suka fara tafiya.
"To yanzu Inna ina za mu je?"
"Ban sani ba ni ma, amma mu fita daga cikin tashar nan, kamar yadda direban ya ce anjima mu samu wata wayar mu ƙara kira ko za a yi sa'a ta kunna wayar. Yanzu kasuwar da ake siyar da wayoyi kawai zan ce ɗan sahu ya kai mu, tunda da kuɗaɗe a jikina gara na siyi ƙaramar waya kawai, kar na rasa mai ba ni aron ta kiran."
Cikin gamsuwa A'isha ta ce. "Ya fi kam." Wani mutumi Inna ta tambaya inda za su bi su samu motar zuwa kasuwar sayar da waya ya ce musu su tsallaka titi za su samu. Godiya ta masa tare da ƙara damƙe hannun A'isha ganin titin babba ne, sun hau kan titin kenan aka ba wa b'arin da suke hannu, kasancewar ba ta saba da ganin motoci na gudu akan titi haka ba duk sai ta ruɗe, ta rasa gaba za ta yi ko baya, sai ta tsaya cak ta kasa ɗaga ƙafafunta, ga horn ɗin da ake musu duk ya ƙara ruɗar da ita.
Duk yadda ya so ya taka burki kafin ya ƙarasa inda suke amma abun ya ci tura, saboda tazarar dake tsakaninsu babu yawa. Jin sun tsaya A'isha ta buɗe baki za ta yi magana amma bugar ta da Motar ta yi tare da cilli da ita gefe ya hana ta maganar. Cikin matuƙar tashin hankali dattijon ya taka burki tare da buɗe Mota ya fito a ruɗe yana kiran "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Duk wani mai abun hawa dake gurin tsayawa ya yi tare da fitowa hankali a tashe, Inna dake kwance ba ta motsi saboda taka gefen kanta ta tayar Motar ta yi aka fara janyewa, ganin jinin dake zuba ya ƙara tayar da hankalin wanda ya buge su. Ba tare da ɓata lokaci ba aka zuba su a cikin Motar mutumin, wani ɗan karota ya shiga front seat, suka tafi zuwa asibiti police da aka kira su a lokacin na biye a bayan su.
Wani babban Private Hospital dake kusa suka je, cikin gaggawa aka karɓi su A'isha aka yi emergency room da su. Ƙarshen tashin hankali mutumin nan ya shiga, don gani yake kamar gazawar shi ce accident ɗin da ya faru, ya kasa zaune ya ƙasa tsaye sai kaiwa da komowa yake cikin ransa yana kiran sunan Allah, tare da addu'ar Ubangiji ya tashi ƙafaɗun su.
Bayan wani lokaci wani likita ya fito daga ɗakin da su Inna suke, da sauri mutumin ya nufe shi tare da faɗin. "Doctor yaya? Suna raye dai dukan su ko?" Daga yanayin fuskar Likitan ya san da matsala, hakan ya ƙara tsananta bugun zuciyarsa. Cikin son kwantar masa da hankali likitan ya ce. "Yarinyar babu abin da ya same ta, buguwa kawai kanta ya yi, mun yi mata duk abin da ya dace, yanzu ta samu bacci sakamakon allurar da muka mata." Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin. "Alhamdulillah, ita kuma matar fa?" Cikin damuwa Doctor ya ce. "Sai haƙuri Alhaji, ita Ubangiji ya karɓi abarsa.".........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
_*Zeey Kumurya*_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*2️⃣2️⃣*
Tamkar saukar aradu a ka haka kalaman likitan suka daki zuciyarsa, yadda ya ƙura wa likitan ido za ka yi zaton suman tsaye ya yi, bakinsa dake rawa alamar yana son ya yi magana amma ta ƙi fita shi zai ba ka tabbacin bai suman ba. Ganin halin da yake ciki Likitan ya kama shi ya zaunar da shi a ɗaya daga cikin kujerun dake reception ɗin.
"Take it easy Alhaji, komai muƙaddari ne daga Ubangiji."
Likitan ya faɗa cikin rarrashi.
Numfashi ya sauke cikin sanyin murya kamar wanda ya ci kuka ya ƙoshi ya ce. "Doctor, please ku ƙara duba ta, wataƙila dogon suma ta yi za ta farfaɗo." Girgiza kai likitan ya yi ya ce. "Ba a mutuwa a dawo ai, sai da muka tabbatar ta mutu sannan muka fito don mu sanar maka, ka yi haƙuri tare da yi mata addu'ar ganawa da Ubangijinta lafiya, Allah ya sa mu dace." Ya ƙarashe maganar tare da barin wajen. A raunane ya ce. "Allah ya ji ƙan ki, ya gafarta miki." Ya daɗe yana juya abun a cikin ransa, tamkar mafarki haka yake kallon al'amarin, bai taɓa tunanin cikin ƙaddarorin rayuwarsa akwai sanadin ran wani ba. Cikin mutuwar jiki tamkar wanda aka yiwa mugun duka ya lalubo tsadaddiyar wayarsa ya latsa tare da karawa a kunne.
Kyakkyawar farar mace ce doguwa ƴar dumaduma zaune a wani rantsatstsen parlour tana kallon SUNNA TV, kyawawan idanunta sanye cikin farin glass ɗin da ya ƙara haska ƙawatuwar fuskarta. Wayarta dake gefenta ce ta fara vibration, a hankali ta kai hannunta da ya sha jan lalle ta ɗauki wayar. Ganin sunan mai gidanta na yawo a kan screen ɗin wayar ya sa mamaki bayyana a kan fuskarta, saboda sanin da ta yi idan ya fita ba ya amsa kira ko shi ya yi kiran a irin wannan lokacin, sai da wani babban dalilin. Numfashi ta sauke tare da ɗaga kiran ganin yana ƙoƙarin katsewa ta kara a kunne tare da yin sallama cikin kamilalliyar murya mai tattare da nutsuwa.
"DR."
Ya ambata cikin matuƙar raunin murya.
Gabanta ne ya yanke ya faɗi, don daga jin muryarsa kamar ta wanda ya tashi daga bacci ko ya ci kuka ya ƙoshi ta san ba ƙalau.
"Na'am Nurul ƙarbi, lafiya na ji muryar haka?" Ta tambaya a hanzarce. Numfashi ya sauke ya ce.
"Babu lafiya Dr, ina asibiti yanzu haka. A ruɗe ta ce. "Subhanallahi, mai ya faru?"
"Ki zo kawai, maganar ba za ta yiyu a waya ba."
Ƙara shiga cikin rikici ta yi, cikin ƙarfin hali ta ce. "Okay gani nan zuwa yanzu, wanne asibitin ne?"
Faɗa mata ya yi sannan ya katse kiran.
Mintuna ƙalilan suka ƙarasa asibitin saboda gudun da ta ce driver ya yi. Cikin sassarfa ta ƙarasa emergency ward ɗin. Hango mai gidan nata zaune cikin ƙoshin lafiya ya sa ta sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi. Kasancewar kansa yana ƙasa ya sunkuya ya sa bai san da isowar ta ba, sai da ta zauna a kusa da shi sassanyan ƙamshinta ya bugi hancinsa sannan ya ankare ya ɗago kansa. Ganin yanayin mijin nata ya sa damuwar ta ƙaruwa. Hannunsa ta kama a raunane ta ce. "Me yake faruwa Abbansu? Ka saka ni a zullumi da faɗuwar gaba, duk da na gan ka lafiya ƙalau amma zuciyata ba ta daina bugawa ba."
"Accident muka samu, na kaɗe wasu mata har ɗaya daga cikinsu ta rasu.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'jiun, garin yaya haka ta faru Abbansu?"
Tsautsayi ne kawai Dr." Ya ba ta amsa cikin karaya. Dafe kanta ta yi cikin tsantsar tashin hankali, lokaci ɗaya ƙwalla ta ciko a cikin idanunta. A sanyaye ta ce. "Yanzu mene abin yi? Ina gawar da ɗayar marar lafiyar?"
"Duk suna ciki, da jira nake yarinyar ta farfaɗo sai a tambaye ta daga inda suke a kai gawar can, na kira Khalifa da Alhaji Abubakar duk na sanar musu, na san yanzu haka suna hanya insha Allahu." Gyaɗa kai ta yi ta ce. "Amma mu fara karɓar gawar mu kai can gida, idan muka jira sai yarinyar ta farfaɗo za a ɗauki time, tunda ba mu san tsawon lokacin da za ta ɗauka ba."
"Haka za a yi."
Cikin sauke numfashi mai tattare da damuwa ta ce. "Mu je mu ga yanayin jikin yarinyar." Bai ce komai ba ya miƙe ya nufi ɗakin da ya ga an shiga da A'isha.
A kwance suka tarar da ita an saka mata drip a hannunta. Cikin tsananin tausayawa Dr ta ƙarasa ta shafa fuskarta tare da yi mata addu'ar samun lafiya.
"Ko ya yarinyar nan za ta ji idan ta samu labarin mutuwar matar can? Wataƙila ma mahaifiyarta ce."
Abba ya faɗa a raunane. Kallon shi Ummi ta yi ta ce. "Haƙuri za ta yi, haka Ubangiji ya ƙaddaro." Girgiza kai Abba ya yi ya ce. "Haka ne, Allah ya sa mu dace."
"Amin, mu ƙarasa mu ga gawar matar mu yi wa likitocin maganar tafiya da ita."
Gyaɗa kai Abba ya yi ya ce. "Ya kamata a samu mai zama tare da yarinyar, bai dace mu bar ta ita kaɗai ba, matsalar babu komai a tare da su wanda za mu samu information na inda suke ko numbern wani nasu, don ko waya ba a gani ba a tare da su." Numfashi Ummi ta sauke ta ce. "Zan zauna da ita, har zuwa lokacin da za ta samu lafiya." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Na gode sosai DR da wannan karamcin naki, Allah ya saka da Alkhairi." Tana miƙewa ta ce. "Babu godiya tsakani na da kai Mijina, ko da wanda ban sani ba ne zan iya yin jinyar shi idan ba shi da me yi masa, balle wannan da alhakin hakan yake kanmu, duk abin da ya shafe ka ai ya shafe mu." Cikin jin daɗi ya ce. "Ubangiji ya yi miki albarka, ya biya ki da gidan aljanna." Idanunta a kan A'isha ta amsa da "Amin."
Cikin awa ɗaya aka ba su gawar Inna da kanta ke ta zubar da jini, har lokacin A'isha ba ta farka ba.
Haɗaɗɗen Bedroom ne wanda ya tara komai na da ake buƙata ga kowane bedroom. Duk da girmansa bai hana munsharin lukutar matar dake bacci a kan luntsumemen gadon dake cikinsa cika shi ba. Da ƙarfi wata farar budurwa dake sanye da ƙananun kaya ta turo ƙofar ɗakin ta shigo ba tare da sallama ko neman izni ba.
"Mumy! Mumy!"
Shi ne abin take furtawa cikin yanayin razana, ganin ba ta ko motsa ba ta hau kan gadon tare da jijjiga ta tana cigaba da kiran sunanta. Hakan ya sa matar motsawa tare da Buɗe idonta a firgice. A tsawa ce ta ce. "Baby ba ki da hankali ne kike mini irin wannan tashin?" Shagwaɓe fuska ta yi ta ce. "Abu fa na zo na faɗa miki."
"Mene ne?" Ta faɗa cikin hamma.
"Abba ne na ga sun shigo da mutum shi da Ya Khalifa a lulluɓe, alamun dai gawa ce, kuma kamar accident aka yi sai zubar da jini tak..."
"What?" Ta faɗa cikin ƙaraji tare da tashi zaune.
"Ina kika ga sun yi?"
"Part ɗin Abba suka shiga."
A ruɗe ta hantsilo daga kan gadon bayan ta damƙi ɗankwalinta ta fice daga ɗakin cikin sauri tamkar magen da ta hangi ɓera.
Yadda ta shiga parlour'n Abba a hargitse ya sa su ɗaga kai dukan su a tare suka kalle ta. Idanunta a kan Abba ta ce. "Alhaji! Waye ya rasu? Gawar waye wannan?" A sanyaye Abba ya ce. "Accident muka samu na kaɗe wasu mata za su tsallaka titi, a ciki ɗaya ta rasu." Ajiyar zuciya ta sauke tare da yatsina fuska ta ce. "Amma saboda Allah maimakon ka nemi ƴan'uwansu ku kai gawar can gurinsu shi ne za ka kawo ta gidan nan? Nan ɗin ma ba ɗakin mai gadi ko guest room ko BQ ba sai cikin part ɗinka a falonka? Saboda kawai ka faɗar mini da gaba ka sa hankalina ya tashi, tunda ka fi kowa sanin ɗana yana wata ƙasar kuma ya ce a cikin satin nan zai dawo, ai sai na yi tunanin ko shi ne ya taho suka yi accident a hanya. Gaskiya ba ka kyauta mini ba." Baki suka saki suna kallon ta cikin tsananin mamakin maganganunta. A tausasashe Abba ya ce. "Saratu gawa ce fa a gabanki amma kike wannan maganar mara kan gado, duk mai guntun imani a zuciyarsa idan ya ga gawa sai ya risina ko yaya ne."
"Gawar ta Uba na ce?" Ta faɗa kanta tsaye.
"Amma ai ta ɗan'uwanki musulmi ce ko?" Abba ya faɗa cikin ɓacin ran da yake ƙoƙarin dannewa. Ɓata fuska ta yi sosai ta ce. "Ka tofar da yawon bakinka don ni talaka ba ɗan'uwana ba ne, kar ƙara dangata ni da su."
"Ce miki aka yi talakawa ne? Idan ma su ne su ba mutane ba ne?"
"Sai an faɗa mini zan sani, tunda ka ce za su tsallaka titi da ƙafafunsu ai talakawa ne, tunda ba su da arziƙin hawa mota." Abba bai kuma magana ba saboda tsantsar ɓacin rai da takaicin halin matar tasa. Khalifa dake sauraren su ya miƙe ba tare da ya yi magana ba ya fice daga parlour'n, da wata muguwar harara ta raka shi sannan ta juya ita ma ta fice. Ƙwafa Abba ya yi cikin tsananin takaicin mugun halin Saratu.
Ummi tana Sallar Azhar A'isha ta farka. Da farko tunaninta guduwa ya yi ta kasa tuna komai da abin da ya faru da su, sai bayan wasu mintuna komai ya dinga dawo mata tiryan-tiryan cikin ƙwanyarta, kamar wadda aka tsikara da allura ta tashi zaune ta fara laluben gefenta, jin hannun hagunta kamar wanda aka ɗaure mata shi da wani abun ya sa ta fara kiran sunan Inna a tsorace....✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
_*Zeey Kumurya*_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*2️⃣3️⃣*
Da sausauri Ummi da ta yi sallama ta miƙe ta ƙarasa bakin gadon, cikin tausayawa ta ce. "Kin tashi? Sannu, bari na kira Doctor." Shiru A'isha ta yi gabanta na faɗuwa jin muryar wata ba ta Innarta ba." Cikin kuka ta ce. "Ina ne nan nake? Ina Innata?" Hannunta Ummi ta kama cikin rarrashi ta ce. "Ki kwantar da hankalin ki, asibiti ne nan, kun yi accident ne Mota ta buge ku." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Ina Inna?" Yadda ta yi maganar cikin nuna damuwa da zumuɗin son ganin Innar sai ya karyar da zuciyar Ummi, a raunane ta ce. "Tana bacci, an mata allurar bacci ne."
"Ki kai ni na gan ta."
"Ki bari na kira Doctor ya duba ki ya tabbatar babu sauran matsala sai mu je, kin ji?" Gyaɗa mata kai ta yi ba don zuciyarta ta so ba. Mayar da ita Ummi ta yi ta kwantar sannan ta fita. A hankali ta lumshe idonta tana jin yadda ƙamshin asibitin ke hautsina mata ciki, ga sarawa da kanta ke mata. Gurin da aka saka mata drip ta dinga tattaɓatawa har ta gane ƙarin ruwa ne. Ba jimawa Ummi suka dawo tare da doctor ya dudduba jikin nata tare da yi mata tambayoyi. Bayan ya fita ta juyar da kanta inda ta ji maganar Ummi, ta ce. "Zan yi fitsari." Ummi ta ce. "Ki yi haƙuri ruwan da aka saka miki ya ƙare a cire sai ki yi." Ba ta ce komai ba ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 20