Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a wajenta. Ita kuwa tace ai ba haka ake yi ba. Nadiya ma kam tace kwarai tayi gaskiya, don kuwa ba taren Allah da Annabi bace ba kenan, ta son abin duniya ce. Madam ce ta hanata tafiya lokacin data leka dakinta da niyar yi mata sallama, "ki zauna wajen Halima kawai, saboda goben da safe ina so a hada abin kari mai kyau, za a kai gidan Hajja Umma!" Ita bata ma ji labarin Hajja Umma din zata je wajen bikin ba. Duk da bata santa ba, amma tasan labarinta a bakin mutane sosai. Tace, "to shikenan. Me kike tunanin za a dafa mata ne?" Ta yi jim tana tunani kafin ta daga kafada, "just cook something fancy! (Kawai ki dafa wani abu mai dadi da kuma tsada), a hada da wuri dai kafin karfe tara. Mu kuma ki dafa mana wani abin mara nauyi saboda ban taho da cook dina ba, already har na fara gajiya da abincin restaurants din garin nan! Sam basu iya abinci to my liking ba!" Nadiya dai tayi dan murmushi ta amsa mata da 'to' ta juya ta koma dakin Anty Lima. Ita kadai ta shiga kicin din, ta bar Anty Lima a daki tana waya da wanda zata aura bayan sun gama sallar isha'i kenan. Kasancewar dare ne kuma sun yi yan ciye-ciye, sai ta musu jollop din macaroni, ta kuma hada musu shayin chamomile. Suna gama ci Madam ta musu sai da safe ta wuce daki, itama Nadiyar kayan da suka yi amfani dasu ta wanke kawai ta koma daki tayi shirin barci. Anty Lima ta bata aron kayan barci ta sanya. Ta zauna akan stool din madubi da earpiece jone a kunnenta suna waya da Aramide. Labari take bata irin fadan da iyayen Mijin nata suka mishi akan irin abinda yake mata, sun kuma yi yarjejeniya dashi akan cewa duk ranar daya kara daga hannu ya tabata da sunan duka to a bakacin aurensu, kuma babu su babu shi, yace ya amince. Nadiya ta tayata murna da kuma addu'ar Allah Yasa karshen abin kenan. Daga nan suka jima suna kara tattaunawa game da yadda zasu kara fadada wajen kasuwancinsu da kuma abubuwan da suke ganin zasu kara jawo musu kwastomomi. Lokacin da suka gama wayar tuni Anty Lima ta jima da yin barci. Ta kwanta a gefen katifar tare da yin addu'ar kwanciya barci ta kwanta. Babu jimawa barci ya kwasheta. *** Tun sallar Asubahi da tayi bata koma barci ba. Ta dora karamar hijabi a saman kayan barcin jikinta ta fada kicin. Duk wani abu da za a bukata akwai a ciki, komi a shirye tsaf kamar dama can da mutane a cikinshi ba wai zuwa suke yi su tafi ba. Babu bata lokaci ta hau aiki. Alkubus tayi niyar yi, don haka ta yi kwabin ta ajiye. Kafin ya tashi ta ciro tantakwashi da naman kasa a cikin firiza ta hau tafasawa. A gefe guda kuma ta hau kwabin special Banana bread dinta. Kwararren kwas tayi akan shi ta online a kasar Indiya wanda ya dauketa kusan watanni biyu, bata taba yi ba amma yana daya daga cikin menu din da suka tattauna jiya da Aramide akan zasu kara shi a shagonsu. Zuwa karfe takwas na safe ta gama cin karfin aikin sai abinda ba a rasa ba. Da yake abincin da dan yawa tayi, sai ta samu warmers masu kyau ta zubawa Hajja Umma nata, sauran kuma ta shirya musu akan dinning table. Madam Zarah ta fito daga dakinta misalin karfe takwas da mintuna arba'in. Bathrobe ce kawai a jikinta sai tawul data nada a kanta, daga ganinta daga wanka ta fita. Ta samu Nadiya a kicin tana kokarin dura kunun gyada a cikin flask. Taga tuni har ta kammala komi sai wanke-wanke dake jiranta. Tace, "thank God Nadiya, barci ya daukeni na manta in tasheki ashe har kin kammala komi." Nadiya tayi murmushi, ta juya tana fuskantarta, "Nda watu ya (Barka da safiya Mama)" Tayi murmushi, "Kin tashi lafiya Nadiya, ya aiki?" Tace, "Klewa slai (lafiya lau). Sau tari ko waya suke yi da Madam din basu cika hausa ba sai Kanuri ko Turanci. Shi yasa itama idan ta je can din take kokarin juya harshenta. Ta nuna mata inda ta ware abincin Hajja Umma din a cikin wani kwandon zuba abinci mai kyau, tace, "ga shi an hada komi. Wannan kunun kawai zan zuba shikenan!" Ta matsa tana daga kwanukan tana gyada kai cike da gamsuwa, "good, good! Yayi sosai. Bari in kimtsa yanzu-yanzu sai in kai mata!" Nadiya ta bita da kallo cike da mamaki lokacin data fita daga kicin din. Iyaka saninta ita dai Hajja Umma da Madam din basa ga maciji a tsakaninsu. Amma yanzu shine Madam din da kanta ce zata je kai mata abinci da kanta ba aike ba? Ta jinjina kai a ranta tana fadin 'lallai in da ranka ka sha kallo!' Cikin yan mintuna Madam din har ta fito cikin wata doguwar rigar Bubu ta shadda data sha dinkin surfani na yan Senegal. Bata daura dankwali ba sai gyale data dora a saman kanta daya fitar da sassalkan bakin gashinta da yayi kwance luf. Idan ka ganta a lokacin sai ka rantse Yayar Nadiya ce ba mahaifiyarta ba, saboda iya daukar gayu da kuma yanda yarintarta take fita kullum. Nadiya ta tayata daukar kayan zuwa wajen motarta. Ta shiga gidan gaba ta tashi motar tana fadawa Nadiya kada su jirata saboda ba anan zata yi karin ba. Amma ta zubawa security dinta abincin, kuma su zauna a gidan har ta dawo saboda masu planning da decorations zasu je, tunda anan gidanta za ayi kamu da misalin karfe biyar na yamma. Nadiya ta amsa da 'to' Ta koma tayi duk yadda tace, kafin ta wuce daki. Anty Lima tana bandaki da alama wanka take yi. Ta dauki waya ta kira Aysha ta fada mata idan da yadda za ayi ta kai mata akwatinta ko kuma kayan da zata sanya saboda kayan Anty Lima sun yi mata yawa. Aysha tace tunda ga direban gidansu nan yaje kai wasu bakin Mamansu gidan Dada din, bari ta bishi sai ta kai mata kayan, ta mata godiya ta katse wayar. Suna waya ita da su Maryam Anty Lima ta fito daga wanka. Ta zauna tana ta shafe-shafen mayuka da turaruka sai kace wadda zata canza fata, Nadiya dai tana ta binta da kallon mamaki. Ita sam wadannan shafe-shafen bata ganin amfaninsu. Anty Lima ta kalleta lokacin data ajiye wayar akan katifa, tace, "Kanna (sister) sannunki da aiki, na jiyoki a kicin kina ta aiki wallahi barci da gajiya ne suka hanani tashi in tayaki." Nadiya ta girgiza kai, "kai haba, babu komi wallahi. Wannan aikin a wajena kam ai ba komi bane, kada ki damu!" Tayi dariya, tace, "kaji fa professionals. Bari inyi sauri dai inje in ci delicacy dinnan da zafinshi kafin ya huce, kin san yafi dadi!" Tayi yar dariya kawai ta shige bandaki don ta watsa ruwa. Allah Ya taimaketa kafin ta fito daga wankan har Aysha ta kai mata kayanta. Ta bude akwatin ta ciro riga da siket na wani material mai taushi. Da yake bashi da dankwali sai ta dora hular turban akanta. Ta fita falo ta samu Anty Lima da Aysha suna hira. Ta zuba abincin da zata iya ci a plate, ta zuba kunun gyadar da yawa a cikin kofi ta kara madara da zuma a ciki, ta koma wajen su Aysha suka cigaba da hirar da ita. Anan ne take jin cewa a ranar Safiya zata zo, don sunyi waya ma da Aysha tace mata suna hanya don a Kaduna ma suka kwana. Anan kuma take jin ashe Madam hanyar bude wani babban Arena ne take yi a Kaduna mai dauke da manyan shaguna, kuma Hajja Umma tana da manyan Realtors a hannu da zasu iya taimaka mata. Ga kuma bugu da kari kanin mijinta Marigayi shine Controller Janar na Najeriya. Da yake tana samun matsala wani lokaci wajen shigo da kayanta daga kasashen ketare, shima tana bukatarshi a gefenta yayinda kuma yaki bata hadin kai. Shine take so ta biyo ta bangaren Hajja Umma din. Ta tabe baki a ranta tana jin babu dadi, dama a ranta sai da tace wannan mutuncin da Madam take yiwa Hajja Umma ba na Allah da Annabi bane, wani abu take bukata. Ita kam sai take ganin bata san inda Madam zata kai son kudi da duniya ba, daidai gwargwado tana da kudinta da rufin asiri, haka ma mijinta, amma ita sam bata gani, kullum cikin neman kari take. Maimakon tayi kokari ta gyara zumuncinsu da Hajja Umma daya tabarbare, su koma tsintsiya madaurinki daya kamar dai yadda yakamata su kasance, amma ita ta kudi da duniya take. Ta san hakan dama ce sosai da zata iya kusantasu da Hajja Umma din, tunda ba cika shiga cikin al'amuransu tayi ba. Ta dauki shekaru da dama bata ji ance taje Maiduguri ba, haka ma bata ji ance wani yaje inda take ba. Maimakon Madam tayi amfani da hakan ta kusantota jikinsu, a'ah, sai dai ta kusanta kanta da ita saboda wani dalili nata na daban. Ta girgiza kai a ranta tana addu'ar Allah Ya kawo karshen wannan takaddama tasu. Sun yanke shawarar kawai su yada zango anan gidan Madam din har Aysha da kuma Safiya da zata zo, saboda gidan Dada ma baki za a kai sosai. Amma tunda Madam ba baki zata ajiye anan ba, nan din zai fi musu dadin zama. 14. Karfe biyu na rana suna zaune a farfajiyar gidan akan kujeru da lemuka a gabansu da fruits suna ci suna hirarsu, suna kuma kallon masu gyara da suke ta kaiwa da kawowa suna hada wajen. Aka bude gate wata galleliyar lafiyayyar Benz munch ta gangaro ta shiga gidan. Suka tsaya da hirar da suke yi duka suka juya suna kallon motar da kuma wadda take kokarin fitowa daga bayan motar. Ta zuro kafarta daya waje dake saye cikin wani hadadden sneakers na kamfanin Ryka, da bakin wandon jeans. Safiya ta fito daga cikin motar bayan wasu yan mintuna, hannu daya rataye da yar madaidaiciyar jakar hannu, dayan kuma rike da wayarta dake makale da earpiece a kunnenta tana waya. Wandon jeans din jikinta irin crazy dinnan ne, an tsattsagashi daga tsakiya. Sai dai maimakon ya nuna fatar jikinta, sai aka done kofofin ta yadda dai akwai tsagar amma kuma bata nuna fata. Da yake skinny ne sai ya bi ya lafe mata a jiki gabadaya. Rigar bubu din data sanya data tsaya mata a tsakiyar cinya ma ba wani abu na azo a gani ta boye a jikin nata ba. Ta sha kitsonta kalba kuwa ta attach, ta zubo mata har baya. Sai ta dora siririn gyale a saman kanta. A shekaru na goma sha tara kacal a duniya, tauraruwar Safiya tana matukar haskawa. Irin yan gatan yaran nan ne na masu kudi da suka tashi cikin gata da dadin rayuwa, iyayenta sun tsaye mata, bata san Fadi-tashin rayuwa ba kamar yadda sauran wasu mutanen suke fama. Wannan yasa ta tashi a matukar sangarce. Kasancewar ta fi Nadiya garin jiki da kiba, ko a yanzu zata iya kamo Nadiyar a tsayi da fadin jiki. Don ba kowa bane zai yarda da cewa Nadiya ta bata shekarun data bata ba. Ta taka cikin kasaita da nuna isa, cikin gidan take niyar shigewa ba tare data kalli inda su Nadiya suke ba, direban daya tukata kuma yana binta da akwatunanta a baya. Nadiya kasa daga baki ma tayi ta mata magana tayi, ta manta rabon data sanyata a cikin idanunta. Sai Anty Lima ce ta daga baki ta kwala mata kira, sannan ta waiga ta kalli inda suke. Ta tafi da sassarfa cike da murnarta suka rungume juna ita da Anty Limar cikin murna. Nadiya tana zaune tana kallonsu fuska dauke da dan murmushi. A ranta tana jin babu dadi da kuma tunanin ta yadda aka yi suka rasa shakuwar yan'uwantaka a tsakaninta da Safiya din. Ta tashi tsaye tana kokarin rungumar Safiya din lokacin da suka gama murnar ganin juna ita da Anty Lima. Jinta take yi banbarakwai, kamar wata sabuwar halitta. Ita kuwa Sophie ko a jikinta, ta rungumeta tana tsallen murna, "Kanna! Kitawu nasaraye (Yaya! Na yi kewarki!)" Tayi murmushi cike da jindadi tana maimaita mata itama hakan. Bayan sun gama murnar ganin juna, suka tayata shiga da kayanta ciki. Dakinta daban wanda dama a ciki ta saba sauka, kusa da na Madam. Tayi wanka ta ci abinci, suka sake fita wajen masu shirye-shiryen suna kallonsu. Sai wajen karfe takwas na dare ma sannan aka fara gudanar da taron bikin. Zuwa lokacin duk sun shirya cikin ankon bikin da za ayi a ranar, jar lafaya ce suka sha mai taushi. Sophie duk ita tayi musu kwalliya da yake ta iya sosai. Nadiya kam bata bari an fente mata fuska ba, ta dai ce a mata kwalliyar sama-sama. Su dukansu sun fito sharr abinsu kamar ka daukesu ka gudu. Wajen event din ya tsaru iya tsaruwa. Su Madam ana can a teburin iyaye, sai feleke ake da iyayi. Idan kaga irin kwalliyar da taci da adon data dauka sai kayi zaton ko ita ce uwar amaryar ko ma amaryar gabadaya. Amarya kuma ita da angonta suna kan teburi a zaune, angon yayi shigar wata galleliyar shadda ruwan madara da babbar rigar ta sha surfani tun daga sama har kasa, da hularshi baka ta Dara. Amarya kuma tayi shigar lafaya itama ruwan madara, kitson da aka yi mata ya sauko a gefen fuskarta, hannu da kafa ta sha lallenta mai kyau. Kallo daya zaka mata kasan cewa ka ga yar asalin bare-bari. Sunyi kyau ita da angon nata kamar ka daukesu ka gudu. Suna can a teburin da suka kebance kansu ita da Anty Lima da Safiya da kuma Aisha. Nadiya bata yi wata kwalliya ba ta azo a gani. Ta nannade kitson da aka yi mata a cikin tafkeken ribbon ta kulle, duk da rashin fitar da gashin da tayi idan ka kalli gargasa da gashin daya kwanta a goshinta zaka san cewa tana da gashi. Zaune tayi tana kallon Safiya data dame cikin kalar tata kwalliyar, kitson data yi duk ya barbazu, wani ya watsu a gefen fuskarta, wani kuma ya sauka a bayan wuyanta ya gangaro zuwa saman kirjinta. Selfie kawai take watsawa kanta a wayarta. Nadiya ta girgiza kai ta mayar da kanta ga su Anty Lima da suke hira. Ko awa daya cikakkiya ba ayi ba da fara sha'anin taji har ta fara kosawa da zaman wajen. Dama can ita ba ma'abociyar halartar irin wadannan al'amuran bane. Zuwa lokacin ita kadai ta rage a teburin nasu, tunda aka kira yan'uwan amarya filin rawa don su taka duk suka tashi suka barta da sauran daidaikun mutane da basu shiga filin rawar ba. Ta dauke idanunta daga kan Madam da Safiya da suka dage tun karfinsu suna zabga rawa kai kace wasu shakikai ne. Don Safiya ma har kama kafadar Madam din take yi tana wani girgiza da kanainayewa kamar wata macijiya, ita kuwa Madam baki ya ki rufuwa, sai like take mata da kudi. Tayi kwafa a sanyaye bayan da suka hada ido da Madam ta daga mata hannu kafin ta juya ta cigaba da kwasar rawarta, ta dauki kofin da suka tsiyaya lemu a ciki ta kai baki ta kurba. To me zata ce? Fadan da yafi karfinka ai dole ka maidashi wasa. Zuwa can taji wayarta tana vibrating a cikin karamar pouch data rike a hannunta. Ta zaro wayar ta duba, ganin Rabi'ah ce mai kiran yasa ta tashi ta bar wajen, musamman data ga ta ajiye mata missed calls har uku tasan kiran gaggawa ne. Can waje ta fita saboda har a farfajiyar gidan ana jiyo sautin kidan da yake tashi. Layin babu kowa sai motoci da suka yi jere suka kewaye wajen iri-iri. Ta matsa gefen wata farar Sedan ta dannawa Rabi'ah kira. Tana fara shiga ta daga. Tun ma kafin su gaisa ta fara watsa mata tambayar idan za ayi velvet cake da kuma whipped cream icing ya za ayi? Kuma me da me ya kamata a sanya? Tayi yar dariya tana tarar numfashinta, "haba Hajiya dan dakata mu gaisa mana tukuna! Saurin me kike yi?" Tace, "wayyo Anty Nadiya Sorry, wallahi mantawa nayi. Kin ga second batch ne fa nake yi na cake din saboda na farkon bai yi ba yadda ake so, kuma nayi pre heating din oven dina already." Nadiya tace, "to yanzu dai mu fara gaisawa tukun. Kin dai san bana son irin wannan wayar ko?" Cike da saduda tace, "na sani Anty. To Assalamu alaikum, ina yini?" Tayi dariya tare da amsawa. Tambayarta tayi abubuwan data sanya a cikin cake din, kafin ta mata karin bayani da gyara a inda ta kuskure. Hirar tasu bata yi tsayi ba suka yi sallama saboda Anty Lima data dinga danna mata kira. Ta katse kiran Rabi'ah tare da amsa na Anty Lima dake kan kira a lokacin. Tambayarta tayi ko tana ina? Tace mata waje ta tafi amsa kiran waya amma ga ta nan dawowa. Ta juya cikin takun sassarfa zata koma wajen bikin. Hankalinta yana kan kokarin mayar da wayarta cikin jaka lokacin data taka kafarta cikin gate din gidan. Daidai lokacin shi kuma ya kawo kai zai fita, suka yi karo. Kasancewar shi ya dan duka kansa kasa saboda kofar jikin gate din ba tsayi ne da ita ba, suka hada goshi ji kake garamm! Gabadaya sai da taji duniyar tana juya mata saboda buguwar da kanta yayi. Bata san lokacin da wayar hannunta ta fadi ba, ita kuma tayi taga-taga tana shirin faduwa saboda wanda suka yi karon dashi da karfinshi ya fito. Da ba don shi ba kuma da sai ta kai kasa din. Yayi azamar sanya hannu ya rikota, bakinshi da nata na furta 'Hasbunallahu wa ni'imal wakil' a lokaci guda. Ta samu ta tsaya akan kafafunta, hannu dafe da goshi, ta daga idanu tana kallon mutumin da niyar watsa mishi tambayar baya kallon gabanshi ne? Shi kuma bakinshi yana furta, 'sorry!' a lokaci guda. Duk sai suka tsaya suna kallon juna cike da mamaki. Maganar da tayi niyar yi ta makale mata a makoshi. Shi kuwa gira ya daga, cike da wannan izza da rainon wayau da bata manta ba. Yace, "such a small word huh? Ke idan kina tafiya baki duba gabanki ne ko me? Ko kina da matsalar idanu ne?" Ta bata rai tana hadiyar wani yawu na takaici, wayarta ta duka ta dauka ba tare data dubata ba. Ta daga kai tana kallonshi fuska a cune, "ina ga dai naka idanun ne suke bukatar a tambayi ko suna aiki ko basa yi. Saboda in case baka gani, kai ka kawo min karo ba tare da ka duba inda kake zuwa ba. Kamar yadda kayi mun a wancan lokacin!" Ta ratsa shi ta shige gidan rai a bace, bata cika son yin tsiwa ba saboda tasan bata da kyau idan ta fara. Taimakon da Allah Yayi mishi daya a wajen biki suke, inda bata son ja wa kanta attention. Amma da ba don haka ba da sai ta wankeshi tass ko ta huce takaicin daya kara kunsa mata a karo na biyu. Babu ma kamar data duba wayar hannunta taga tayi raga-raga, gashi bata sanya mata screen guard ba. Ji tayi kamar tayi me! Ta dai cije ta karasa wajen su Anty Lima inda suke zazzaune suna ta dambe da naman kaji da lemuka da aka shirya bayan fitarta. Ta zauna tana harare-harare ita kadai. Saboda bacin rai ko kallon naman bata yi ba duk da yadda kamshin naman yake kai mata. An cigaba da gudanar da shagalin biki har zuwa wajen karfe goma sha biyu na dare. Duk da haka basu samu sukunin tafiya makwanci ba sai wajen karfe daya na dare. Saboda sai da suka taimaka aka rage tarkacen dake wajen duk da wadanda suka shirya event din su suka yi aikin, amma Madam tace su sa musu hannu don a samu a gama da wuri. Don haka a matukar gajiye suka kwanta. Da kyar ta iya tashi tayi sallar asubahi. Ta koma ta kwanta kenan, a ranta tana raya yadda zata kai har karfe goma ko sha daya ma bata tashi ba, sai ga Madam ta kwankwasa musu kofar dakin. Ta tashi zaune tana kallon Madam din wadda har lokacin kayan barcine a jikinta, daga alamun fuskarta kuma ko sallar asubahin ma bata kai ga sallata ba. Ta amsa gaisuwar da suke mata a tsaitsaye, da alama sauri take yi. Nadiya take kallo, "Nadiya ya za ayi ne? Jiya mantawa nayi fa in fada miki yau ma za a kaiwa Hajja Umma abin kari. Ina ga ai za a samu a hada ko?" Jikinta a matukar gajiye yake, bata kuma tunanin zata iya aikin da Madam din ta bukata. Sai dai sanin halin Madam din, tasan ba tambayarta take yi ba, umarni ne kawai take bata, yasa ta daga baki tace, "to me za a dafa ne?" Tace, "kawai ki dafa duk abinda ya dace da abinda dattijuwa zata ji dadinshi. Amma ki sake yin kunun gyada saboda taji dadin na jiya sosai." Nadiya ta amsa da 'to!' Ita kuma ta juya ta tafi. Ta tashi da kyar ta nufi kicin din, Anty Lima ta bi bayanta zata tayata aikin. Duk da yadda taso ta koma ta kwanta, ki tayi. Don haka suka shiga tare. Tuwon shinkafa ta malmala da miyar agushi ta yi kunun gyadar. Ta hada komi ta zuba a mazubai masu kyau ta ajiye. Sai ta kara yi musu couscous da sauce din kifi don tasan ba lallai Madam da Safiya su ci tuwo da safe ba. Bata ma iya tsayawa karyawa ba saboda tsabar barci da take ji, ayaba kawai ta iya ci da tuffa, suka koma suka kwanta. Bata san lokacin da Madam ta bar gidan ba. Sai can wajen Azzuhur da suka tashi, suke jin tana can gidan Hajiya Umma, yau har da Safiya suka tafi. Kasancewar shagalin ranar na yamma ne, da suka yi sallah suka ci abinci, sai ta dauki sauran tuwon da suka yi suka tafi gidan Dada. Acan suka shirya tare da su Aysha, suka tafi can wani wajen tarar baki na musamman inda a can ne za ayi Mothers Eve. Suka fita daga motar Anty Lima ita da Aysha da Anty Lima din da wata cousin dinsu diyar kanwar mahaifiyar Anty Lima din, Zainab. Wata tsanwar atamfa suka shiga, Nadiya an mata dinkin gown wadda ta bi jikinta sosai ta lafe. Duk da cewa ba wani matseta tayi na azo a gani ba, amma yanayin yadda ta fitar mata da surarta yasa data tashi sanya gyale, sai ta samu mai yalwar fadi kuma mai duhu ta yafa. Su Anty Lima ma sun fito gwanin kyau cikin nasu ankon. Ita skirt tayi straight, an tsaga mata shi daga baya. Nadiya har maganar yadda sharabarta take a waje ta mata, amma tace mata hakan ba wani abu bane, ai ta ma yi shigar mutunci. Ta sanya rigarta half gown wadda shape dinta ya fita da kyau, ta kuma yi mata matukar kyau. Ita da kanta ta kashewa Nadiya daurin kallabi mai kyau. Suka jera suka shiga wajen cikin taku na daukar hankali. Gab da zasu shiga wajen da ake event din suka ci karo dashi cikin zugar matasan samarin danginsu, diyan yan uwansu Madam. Ta duba iya dubawa, ita dai ta kasa gano ta ina suka hada iri da wannan dan wulakancin mutumi. Ta kasa daurewa dai sai data daga baki ta tambayi Anty Lima. Ta saci kallon samarin da duk suka bisu da kallo sai kace sun ga wani danyen nama. Anty Lima tace, "wai wancan? Nima gaskiya ban wayeshi ba. Amma cikin su AbdulHalim nake ganinshi. Watakila ko abokinsu ne tunda ba cikin zugar angwaye yake ba." Zainab dake sauraronsu tunda suka fara maganar tayi caraf ta amshe zancen. Tace, "wai wancan haddaden gayen? Ance fa babban dan Hajiya Umma ne. Bata taba zuwa nan dashi ba sai wannan karon shi yasa duk ba a san shi ba!" Suka kalleta da mamaki, Anty Lima tace, "kai jama'a! Dama Hajiya Umma tana da babban da kamar wannan? Ashe matar ba ta yau bace!" Nadiya tayi dan murmushi.

Chapter 9 of 36