kaf a tarihin Jahar Kaduna ba a taba ganin jajirtaccen Gwamna ba kamar shi.
Mutane da dama sun so ya sake neman kujerar Shugaban Kasa, amma yace a'ah, wanda yayi ma a baya Allah Ya sanya albarka. Yanzu kam yana son karkata hankalinshi ga iyalinshi ne kawai.
Nadiya a halin yanzu marikiyar Masters ce, tana aiki da wata Private University anan Kaduna din inda take koyar da Home Management. 'Ya'yanta shida, Yan biyu yanzu shekarunsu sha daya, Juwairah yar kimanin shekaru takwas da yan watanni, bayan ita akwai wasu yan biyun duka maza, Hassan da Hussaini, shekarunsu biyar. Sai Fatima (Maamah) itace autarta shekarunta uku.
Shukurah kuma Yayanta uku, Muhsin, Mus'ab da kuma Ruqayyatu. Ita Shukurah din yanzu tana aikine da hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa.
Kawunansu a hade yake sosai, haka ma yayansu sun taso cikin kauna da girmama juna da kuma iyayensu, don kuwa a lokuta da dama ma baka iya bambance dan wannan dakin da na wancan.
Shekaru uku da suka wuce su Mami suka dawo Najeriya da zama gabadaya ita da iyalanta. A kuma cikin shekarar ne aka yi auren Safiya da Fu'ad, dama can Nadiya ta jima tana zargin akwai wani abu a tsakanin yaran, don haka bata yi mamakin jin zancen ba. Suka sha biki sosai da sosai kamar babu gobe, Safiya ta tare a gidanta dake nan Kaduna. Ba a gina mata asibitinta na kashin kanta ba bayan ta kammala karatunta, amma kuma tana aiki da wani babban asibitin kudi anan Kaduna din, sannan kuma tana zuwa asibitin Gwamnati lokaci zuwa lokaci. Diyarta daya a halin yanzu.
Alhaji Habib yanzu babban dan kasuwa ne, wanda yake safarar jewellies, kayan ado na maza da mata har ma da furnitures daga sassa na duniya daban-daban. Shagunanshi suna da manyan rassa a jahohi daban-daban a cikin Najeriya, nan Kaduna, da Maiduguri, Abuja, Kano har ma da Lagos.
Ita kanta Nadiya tana da babban wajen cin abinci mallakinta, wanda yayi shura ya kuma yi fice a cikin Kaduna kwarai da gaske. Don kuwa wajene wanda yake tafiya da zamani sosai da sosai, haka ba a abincin nan kasarmu Najeriya kadai suka tsaya ba, suna lekawa har kasashen ketare suna yin irin girke-girkensu.
Haka kuma, ita din yanzu tana rike da gidauniya har guda biyu ta tallafawa mata da marayu tata ta kashin kanta.
Aikin Hajji ya kwashi iyalan nashi suka je gabaki dayansu banda yan kananun, su a wajen Ummah aka barosu.
Ranar da suka dawo, a gidan Hajiya Ummah suka yi masauki gabaki dayansu. Aka yi musu tarba mai kyau, abinci iri-iri, babu irin wanda ba a dafa ba.
Suka hau kan babban dinning table wanda ya daukesu gabadayansu tsaf, har da sauran kujeru ma. Kowa ya zuba abinda yake son ci, babu abinda ke tashi a wajen sai tashin sautin muryoyinsu kawai suna ta hira cike da nishadi da kauna irin ta yan'uwantaka.
Nadiya ta harari Khairiyya wadda ta dauke sauran soyayyen kifi guda daya daya rage akan farantin Mus'ab, ta kuma kaishi baki ta taune tana gaggaba mishi dariya.
Tace, "wai don Allah me yasa kin cika tsokana ne Khairiyya? Ba na hanaki cin kayan kannenki ba?"
Ta turo baki tana cewa cike da shagwaba, "To Mommy na ga ya zauna yin tsentseni ne, yanzu wannan sai kiga har mu tashi daga nan bai gama cin abincin ba. Ni kuma ina so in ci ne."
Tace, "to amma ai ba haka ake yi ba ko? Sai ki tambayeshi kiji idan ba ci zai yi ba kafin ki dauka. So kike yi ya miki bore ke kuma kice zaki nuna seniority ki ci zalinshi ko?"
Ammar ya katseta, yace, "Mommy da ma kin daina shiga tsakanin wadannan yaran wallahi. Yanzun nan zasu baki kunya a bainar jama'a. Kin gama tare mishi fada yanzu, yanzu kuma zaki gansu sun hade kawuna suna shan hannu da dariya abinsu."
Shukurah tace, "ai ni dama tuni na gama fita daga cikin harkokin yarannan da kike ganina. Ni ai tun ranar nan da suka gama yace min zani a kasuwa ita da shi, nace to anyi babu kari. Shi yasa bana taba ce musu komi idan suna abinsu."
Wajen suka dauki dariya sosai da sosai.
Ummah kallonsu take yi, a cikin ranta wani irin farincikine irin wanda bata taba jinshi a rayuwarta sai in tana cikin wannan zuriya.
Ba ita ta haifi Habib ba, don haka 'ya'yanshi ba jikokinta bane na jini. To amma kuma so da kauna da shakuwa dake tsakaninta da su, sun ma fi na wadanda suka hada jini din. Komi yaran suka dauko, kaji sun ce granny, granny. Duk da cewa itama Yakumbo din suna sonta akwai kuma shakuwa a tsakaninsu sosai, to amma fa bata kamo kafar shakuwarsu da Ummah ba ko kadan.
Sai zuwa dare sannan ya hada kan matanshi suka wuce gida. Su kadai suka tafi, don Ummah tace a bar mata yaran su zauna tare da ita har su koma hutu. Saboda tana so ne ma a cikin satin su je su kaiwa Yakumbo ziyara a Makarfi koda ta yini daya ne ko kwana.
*
Bayan an kwana biyu, sun gama hutawa da kuma karbar baki yan sannu da zuwa, ta fita a yammacin ranar Alhamis zuwa gidansu.
Ruwa aka gama yi babu jimawa, garin yayi luf gwanin sha'awa. Ta fita a cikin silver Jaguar F-Pace sport car dinta, sabuwar mota ce wadda bata jima da siya ba.
Allah Ya buwaye mata, sai gashi ta wayi gari rayuwarta tayi kyawun data fi karfin abubuwa da dama a cikin rayuwa. A halin yanzu ita da kanta bata san iya adadin kadara da kudade data mallaka ba, wanda kuma duka cikin buwaya ta Ubangiji nata ne, mallakinta, ba tare da wani ya taimaka mata da asin kwabo ba.
Ita take tuka kanta a hankali, cikin jin dadi da ni'imar da ruwan sama din ta saukar mata. Gidansu ta yiwa tsinke, bikin Amina da Fatima ke tunkarosu a cikin wannan watan. Ita Maryam an jima da yin aurenta, ta samu miji a cikin yan'uwan Mama, a yanzu haka tana can Kano da zama ita da yayanta.
Ta yi horn a bakin gate din gidan, yaran gidan suka dinga rige-rigen bude mata kofa. Ta danna hancin motarta farfajiyar gidan ta shiga, ta kashe motar tare da fita a hankali tana gyara gyalen data rataya a kanta.
Ta tsaya a jikin motarta tana karewa gidan kallo, shine dai gidan da suka tashi, aka kuma rainesu a ciki. Wanda a shekarun baya kadan suka sayi sauran gidaje dake makwabtaka dasu, aka sake rushe tsohon aka yi sabon gini na zamani. Lantana tuni ta jima da barin gidan itama. Saboda bayan wasu yan lokuta, tace ita ba zata iya wannan rayuwar ba, ta nemi saki shi kuma ya sallameta.
Aka warewa matan dakunansu, shima Abban haka aka ware mishi nashi bangaren daban, ta yadda zai dinga cin karenshi babu babbaka ba tare da wani ya jiyo shi ba balle yasan wainar da yake toyawa. Irin rayuwar da taso ace ta rayu a cikinta kenan, irin wannan tsarin tayi burin ace shine a gidan a lokacin da take nan.
Saboda idan ta zauna ta duba baya da kyau, sai taga cewa raini mai yawa daya shiga tsakaninta da matan mahaifinta ba komi bane ya assasa hakan ba face mu'amalarsu da take ji da duk wani sirri daya kamata ace nasu ne su kadai, wadanda bai kamata wani kunne yaji ba face su. Shi yasa ta rainasu, bata sonsu, bata girmamasu, shi kanshi Abban nasu sai da rainin ya so shiga tsakaninsu ai.
Bata son kannenta na baya su dandana irin wannan rayuwar data dandana a baya, shi yasa ta bada shawarar ayi haka din. Musamman da bayan yan shekaru da yawan shan magunguna da yake sha, ya samu lafiyarshi garas duk da cewa dai har lokacin babu tabbacin zai sake iya haihuwa.
Bayan wannan kuma haka suka samu shago babba aka zuba mishi yadika da shaddodi na maza inda ya fara gudanar da sana'arshi, duk sunyi hakan ne saboda zaman hakanan din bashi da dadi musamman ga mutum mai iyali irinshi.
Ta nisa a nutse, kafin ta taka a hankali akan takalminta mai matsakaicin tsayi na Chanel da mahadin jakarta data sanya kan wayoyinta da sauran abubuwan da zata bukata a ciki.
Ta shiga bangaren Salame da a halin yanzu da ita da Mama suke amsa sunan Hajiyoyi. Ita da su Yaya AbdulHadi da su Anty Jamilah suka biya musu aikin Hajji a wata shekara, suka je su duka suka sauke farali.
Ta zauna akan daya daga cikin kujerun falon, suka gaisa da ita cikin girmama juna. Haka diyan Salame din da kuma na Lantana data bari a gidan bayan tafiyarta, suka dabaibaye Nadiya din suna gaidata, ta dinga amsawa da fara'arta tana tanbayarsu game da karatunsu. Su dukansu sun girma Tubarkallah, hankali ya ratsasu, haka kuma kowannensu karatunshi yayi nisa na Arabi da boko wadanda su yayun nasu suka tsaye musu.
Ta zauna a cikinsu tana sauraren matsalolinsu da korafinsu daya bayan daya, Salame na daga gefe tana musu dariya idan sun ce wani abun. Bayan dogon lokaci dai ta mata sallama ta wuce wajen Mama.
Ta sameta zaune a kan kafet, Aminatu tana yi mata tsifar kai. Su duka suka daga kai suna amsa sallamar da tayi. Sai kuma fara'a ta fadada akan fuskar Mama.
Tace, "Lale marhabun da Hajiyoyi. Har kun fara fitowa ne?"
Ta lalubi kujera ta zauna tana kallonta, "ai Anty Jamilah da Anty Haulatu ne suka tasoni wallahi ba shiri. Zancen abubuwan biki dana hidima suke so muyi da ke wai don su fara shiri da wuri. Kin sansu ba dai son bidiri ba da casu in dai akan bikine"
Mama tace, "ki fada musu to su ma daina wahalar da kansu, don kuwa babu wani shagalin biki da za ayi. Haka Abbanku ya fada ko a dazu da safe da zai fita."
Amina ta zumburo baki, sai tayi dan murmushi tana kallonta. "ke kyale Abba kinji? Ba da gaske yake ba fa. Bikin autarmu guda wai ace babu shagali? Ai wannan sam ba sai yiwu ba."
Sai lokacin suka gaisa da Mama din. Ta kuma fara jero mata ire-iren abubuwan da suke sa ran yi da bikin, aka kira Salame taje don ayi maganar da ita. Tace, "ni ina ruwana da shiga harkar yara? Duk abinda kuka tattauna da yan'uwan naki mu namu ai Allah sanya alkhairi ne. Amma don Allah dai kada ku sanya shashanci da kide-kide a ciki."
Ta tashi ta fita bayan ta fadi haka. Don haka ita da Mama suka tsara abinda za su tsara.
Sai can gab da Magriba ta tashi zata tafi. Ta cewa Mama, "a gaida Abba idan ya dawo. na so ace yana nan da mun gaisa."
Mama tace mata, "zai ji in shaa Allah. Ranar nan ai yace Maigidan naki har shago yaje ya gaisheshi, ya kai mishi jallabiya da sallaya tsarabarshi ta Makkah."
Tayi dan murmushi a tausashe, don kuwa Koda wasa bai fada mata hakan ba. Yanzun ma kuma saurin komawar da take yi kenan, saboda ranar girkinta ne. Ga Ogan sam bai jurar ya koma gida ya tarar ba ta nan. Lokuta da dama ya sha mata korafin hakan da nuna yadda baya jin dadi, don haka take kokarin kiyayewa. Ta musu sallama da cewa idan sun gama maganarsu da yayun nata, zata kira Mama ta sanar da ita yadda ake ciki.
Ta shiga motarta, su Sa'idu suka bude mata gate zata fita. Tana kokarin tayar da ita taji alamun shigar sako cikin wayarta, sai ta dakata tare da ciro wayar daga jakarta. Kamar yadda tayi zato, Habibin nata ne.
'Ban taba sanin cewa ni din mai tsananin sa'a bane, sai da kika shigo cikin rayuwata. A lokacin da ni kaina ban taba sanin cewa ina tsananin bukatarki a kusa da ni ko gefena ba. Ki ka haskaka min rayuwata fiye da hasken tauraro da duk wani abu mai sheki a duniyar nan. Ki ka dusashe hasken duk wata 'ya mace da take a cikin rayuwata idan ba ke daya dinnan ba tal! I love you baby. Rayuwata da ta iyalina bata taba daidaituwa idan ba kya kusa da mu. Shi yasa a duk lokacin da zan shigo gidana, nake samunshi duhu dindim matukar ba kya nan ... Where are you my sunshine? You are the peace and happiness I have been longing for in my life... Come back to me my baby....!"
Da wasu irin kalamai masu nauyi da suka sanya ta kafa kai a jikin sitiyarin motarta tana sakin wani irin murmushi mai cike da tsananin shauki da soyayyar Maigidan nata.
Koda wasa, kuma a kowane yanayi yake ciki a tare da ita, bai taba bude baki ya ce mata ko wani ba, she's his favorite a cikin matan nashi ba. Amma ita ta sani. Koda bakinshi bai furta ba kuma, gangar jikinshi da zuciyarshi suna fada mata. Ita ce haskenshi kamar yadda shima ya ke hasken rayuwarta da duniyarta baki daya.
Haka itama bata taba yin amfani da wannan 'weakness' din nashi ba domin ta kuntatawa abokiyar zamanta. Sai ma kokarin boye shi da take yi, domin su samu mijinsu ya tashi a gaban UbangijinShi a cikin sahun masu kyautatawa ga iyalansu. Tunda kuma baya taba kokarin nuna musu bambancinsu a fili, a kullum addu'arta bai wuce ya kasance miji mai saisaita adalci a wajen Iyalanshi ba har abada.
Ta maida wayar jaka bayan ta tura mishi amsa a layi guda daya kacal... 'ina nan zuwa gareka, Maigidana Abin alfaharina!'
Ta yi ribas, ta fita daga gidan nasu ta tunkari nata, wanda take fatan ta mutu a cikinshi, ta kuma tashi a matsayin matar Maigidan har a gobe kiyama. Zuciya cike da doki da shaukin sanyashi a cikin idanunta.
Karshe.
❥❥✿✯❥❥
To the girls who dream of meeting a prince but end up falling for the misunderstood villain!
Alhamdulillah! Ma shaa Allah La Quwwata illa Billah!
Wannan labari kirkirarre ne, ba ayi duba da rayuwar wani/wata wajen rubutashi ba. Idan hali ko yanayi ko tsari yazo daya da naka/ki, to arashi ne kawai.
Ina matukar godiya kwarai da gaske ga duk mambobin group din HADAKAR FIKRA 2024, wadanda adadinsu ba zai fadu ba. Your love, comments, da karfafawar gwiwarku ne ya kawomu wannan karshe mai kyau. Da fatan labarin Nadiya ya fadakar tare kuma da nishadantar da ku. Allah Ya bamu ikon amfanar darasin dake tattare da wannan littafi, kurakuran ciki kuma Allah Ya yafe mana bakidaya ameen. Nagode, nagode, Allah Ya bar kauna. Ma'assalam. Sai mun sake haduwa da ku in shaa Allah.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 36