tafi ga hanya nan!"
Ya juya ya fita fuu! cikin fushi. Ta bishi da kallo, ita ba abun tayi fushi ba ko tayi dariya. Ban da abinshi, yaushe ma ta samu damar yin maganar arziki da Shukurah balle har ta zugata wai akan ta dinga guje mishi?
Ita tunda take da shi ma bata taba sanin irin wannan rayuwar suke yi da Shukurah din ba sai yanzu. Don haka sai taji ranta duk babu dadi. A ranta ma dai tasan hakan ba dai-dai bane, ba kuma haka yakamata ta bullo mishi ba. Don haka ta tashi ta gyara jikinta ta fita ta sameshi a falo a zaune yana latse-latsen channels da remote, har lokacin cikin fushi yake kwarai.
Ta karasa a hankali kusa da shi, fuskarta na nuna nadamar hakan data aikata mishi. Ta duka ta dafa gwiwarshi tare da tausasa muryarta, tace, "kayi hakuri Abban Ammar, nayi nadamar abinda na aikata maka. Don Allah ka yafe min, idan kuma zancen tafiya ne in shaa Allah na cireta daga raina tunda baka so!"
Ya dan kalleta, da gaske fuskarta ta nuna nadamar hakan, ya kuma hangi alamun da gaske take yi, zata iya hakura da tafiya wajen bikin duk da yadda take matukar son zuwa. Sai yaji ta bashi tausayi, ya kamota ya zaunar da ita cikin jikinshi yana mata magana a hankali.
"Zan fi so ko abu kike so ko nayi miki wani laifi na daban Nadiya, ki zaunar da ni ki fada min. Ko ban amince ba ko na amshi laifina a take ba, I promise idan kika yi hakuri kika dan bani lokaci kankani, zan iya canza shawara. Amma bana so, Koda wasa ki sake yi mun hakan, bana so ko kadan kinji baby?"
Yadda ya kira babyn ne cike da kulawa da so, sai taji jikinta yayi sanyi. Ta kwantar da kanta a kirjinshi tana gyada kai a hankali. Ta dauki hannunsu daya sarke da nashi, ta mannawa bayan hannunshi sumba a tausashe, "kayi hakuri!" ta furta hakan a cikin karamar murya.
Ta samu dai ya yarda ta bi bayan Mami din, da sharadin da an kai amarya to washegari ta dawo gida, bai kara mata ko kwana daya ba. Tayi sauri tace taji ta yarda ta amince.
Daren ranar dai ita da barci suka yi hannun riga, don kuwa cewa yayi sai ta fanshe mishi kwanakin da zata tafi ta barshi shi kadai yana yawo a garin Kaduna sai kace wani gwauro.
Washegari su Ammar suka tasheta daga barcin wajen karfe goma sha daya. Ta bude musu kofa shi da Farida suka shiga, su suke fada mata cewa Mami ce tace su je su tayata hira, ita ta tafi unguwa.
Lokacin kari ya wuce, kuma ba yunwa take ji ba. Tasan ko ta fita ma ba lallai ta iya cin wani abu ba. Don haka ta barsu a falo suna wasansu, ita kuma ta shiga kicin ta fara tunanin abinda zata hada da sauri ta karya.
Ta hada wapple da yayi taushi tubus, ta yi topping da whipped cream da inabi ta zauna tana ci bayan ta hada shayi ta zabga mishi lemun tsami. Don gani take idan bata ci wani abu mai lemun tsami ba tashin zuciya zata cigaba da yi.
Su Farida suna gefe ita da Ammar suna cin wanda ta zuba musu.
Sai ga knocking anyi, ta bada iznin a shiga. Sai ga Bishola, ma'aikaciyar gidan. Tana ganinta ta sha jininta, ila kuwa tana gama gaisheta, sai ce mata tayi, "Ummah ce tace a kira Ammar!"
Yaron ya kalleta da sauri yace, "to ai Ummah ce da kanta tace mu taho nan. Kuma ranar nan ma da kika ce tace inje, tace ba ita bace!"
Nadiya bata fahimci inda zancen nashi ya nufa ba, kawai sai ta kallesu tace musu, "ku je tunda ita ta aiko!"
Suka tashi simi-simi suka bi bayan Bishola.
Ta bisu da kallo a ranta tana wani tunani. Wannan wai wace irin rayuwa ce suke yi a gidan nan ne?
Taji wani irin bacin rai ya dabaibayeta, taga yau idan ta shanye wannan maganar kila zuciyarta ta buga, ta fadi ta mutu a banza babu wanda za a yiwa asara a gidan.
Kawai sai ta sabi gyale a kafada, ta wuce sashen Hajiya Ummah buguzum-buguzum kamar wata kububuwa.
Yaran suna falo suna kallo, ta haye sama da sauri ganin Ummah din bata nan kasa.
Ta ci nasarar samunta a falon kasa tana kallon labaran safiya a tashar Farin Wata.
Ta duka a gabanta tana kwasar gaisuwa, kafin ta kai ga gama amsawa Nadiya ta rushe da kuka.
Sai ta bita da kallon mamaki, murya a dan daburce ta fara tambayarta, "subhanallahi, Nadiya! Me ya faru ne? Me aka yi?"
Ta bude baki tana magana, amma yadda shessheka da kuka suka ciyota, ba a ma fahimtar abinda take cewa.
Ganin haka sai Ummah ta kamo hannunta da kanta, ta zaunar da ita akan kujera kusa da ita, tana shafa bayanta a hankali cikin lallashi da kulawa da suka ba Nadiya mamaki.
Ita har ga Allah bata ma san takamaiman kukan me take yi ba ko musabbabinshi ba. Amma bata yi tsammani samun wannan kulawar daga gareta ba. Tayi tunanin kyararta zata yi ko tace ta tashi ta bata waje bata da lokacin wannan shirmen.
Ummah sai data ga ta nutsu, ta daina kukan, sannan tace mata a tausashe, "yanzu kiyi min bayanin abinda kike cewa yanzu. Menene akan zancen Ammar da rashin son kusancinku da menene? Na kasa fahimtar abinda kike fada sam!"
Sai ta sadda kanta kasa a kunyace, a ranta tana fadin dama tayi hakuri ta taushi zuciyarta bata zo da zancen ba. Me zata ce mata yanzu? Ta dai tari aradu da ka, ta fara magana kanta a kasa.
"Ummah, nasan cewa I'm not your favorite person a gidannan, wanda ban san dalilin hakan ba amma idan ma nayi miki wani laifine da ban sani ba, ko wani nawa ne yayi miki hakan, don Allah a madadina da nasu su duka ina rokonki da kiyi hakuri. Amma sai in ga hanani kusanci da kike yi da Ammar kamar ba mafita bace mai kyau, tunda ko babu komi naga yana son zuwa wajena, kuma nima ina son yaron. Sannan bana tunanin ina kokarin canza mishi halinshi ne ko dabi'a."
Ummah tayi shiru tana saurarenta a nutse. A ranta cewa take ranar da Sumayyah take ji mata tsoro gata nan ta zo! Tunda har an fara zuwa ana confronting dinta, ai ana gab da fara fadi-in-fada ita da suruka.
Amma abinda bata gane ba kuma take son ganewa, shine;
"... me ke faruwa da Ammar ne da kike cewa ina son shiga tsakaninku? Ban fahimceki ba?"
Nadiya ta kasa kallonta, sai ta gyara zama ta fada mata yadda duk lokacin da Ammar yaje bangarenta take aika Bisola ta ce yaje tana nemanshi?
Ummah zaune tayi sandardar a zaune cikin mamaki, don kuwa ita dai bata ma taba jin wannan zancen ba sai a ranar.
Don haka ta kalli Nadiya tace mata, "dan bani minti daya!"
Ta tashi ta dauki waya ta kira chief security ta gidan, suka yi maganarsu kasa-kasa wadda Nadiya bata jin abinda suke cewa. Amma dai ta sha jinin jikinta da cewa akwai matsala. Gabanta ya hau faduwa, a ranta cewa take dama dai bata hau dokin zuciya ta biye mata ba ta zo wa Ummah da wannan zancen.
Shukurah tana zaune gaban madubi, shafe-shafe ta gama, tayi kwalliyarta sosai cikin wata jar abaya. Wani taro ne ta hada na manyan mata yan siyasa, don su taru su karawa juna sani akan hanyoyi da dabarun samun nasarar kamfen da iya tafiyar da mulki. Don har matar Gwamna mai ci sai data gayyata.
Aka buga kofar dakinta sau biyu, ta bada izini, aka shiga.
Yar aikin ta karasa gabanta, ta duka tana mata rada a kunne. Kai kawai ta gyada mata alamun ta gamsu, ta daga gaban drawer dinta ta ciro kudi a cikin envelope ta mika mata. Ta amsa da rawar jikinta tana mata godiya, ta bude kofar dakin ta fita cikin murna. Sai tayi turus ganin Mrs. Atiku, Chief Security dinsu. Ita ce mai kula da duka securities da yan aikin gidan. Wadda bata wasa da aikinta ko kadan, bata kuma taba bada kofar da za ayi wasa da aiki tana gani. Karya da zamba da munafunci suna cikin manyan abubuwan da bata aminta dasu.
Don haka tunda Bisola taci karo da ita, tasan cewa tata ta zo karshe! Tun ma kafin ta mata magana ta fara hawaye da neman gafara, ta duka kasa takardar kudin da aka bata itama tana faduwa. Ta duka, ta duba taga kudin dake ciki shake, ta dan gyada kai tana kallonta cikin nuna alamun ba sani ba sabo, tace, "kije wajen Shu'aibu, zai baki takardar sallamarki da kudin da kika ci na wannan watan. We no longer require your service!" Ta tsallaketa ta wuce ta barta anan tana kukan nadama.
Dakin Shukurah ta wuce da take jiyo abinda ke faruwa. Duk da cewa jikinta yayi sanyi da jin abinda ke faruwa, amma wani sashe na zuciyarta yana kara karfafarta da cewa kada ta karaya. Don haka koda Mrs. Atiku ta sanar da ita cewa Hajiya Ummah tana son ganinta, da confidence dinta ta tashi ta bi bayanta. Tana fada da karawa a cikin ranta, ita din ai ta gama cin dubu sai ceto, don haka babu abinda hakan zai zame mata. A wajen Ummah da Habibu, ita din ai ta zama duwawu, ko ana so ko ba a so dolene a zauna da ita.
45.
Suka nabba'a a gaban Ummah ita da Shukurah, kai a kasa suna sauraren irin fadan da Ummah din take zubawa sosai da sosai cike da bacin rai. Saboda abin bai mata dadi ba sam.
Ta cewa Shukurah, "akan me zaki aikata haka iye? Har ki dinga amfani da sunana a cikin gidannan kina aikata abinda bai dace ba? To daga yau, kada in sake jin abu makamancin hakan ya faru anan gidan. Ammar da ne a gareku ku duka, ban ga dalilin da zai sanya daya ta dinga hana daya mu'amala dashi ba, a kiyaye. Sannan daga yau, idan na kara jin wai an hada baki da yan aiki ana yin abinda bai kamata ba, to mutum zai gamu da bacin raina kwarai!"
Shukurah ta kyabe baki cike da wani sobaranci da sokanci, tace, "Ummah kina ganin yadda dai ta janye yaron wannan jikinta duk ta kanainayeshi, shi dama Ubanshi tuni ya gama zama mijin tace a kanta. Sai a zuba mata ido kenan tana juya mutane?"
Ummah tace mata, "shi da ya zama mijin tace din ai shi ya so hakan, kema kuma da kin zage dantse tun farko da kin zama matar mijin tace din. Da kuwa da kike ganinshi ai shi yana wajen duk mai sonshi ne da kyautata mishi and lets face this Shukurah, yaron nan ba jan shi kike yi a jiki ba, hasalima idan yazo wajen da kike baki bari ya rabeki. To zai zauna yayi ta biye miki ne?!"
Kawai Shukurah sai ta dargwaje da kuka, ta tashi tsaye tana sakin maganganu cike da rashin da'a da kirki. Ai dama ita tun ba yau ba tasan cewa Ummah din tafi son Nadiya a cikin gidan. Yanzu har ta kai a dinga mata gorin haihuwa da yi mata shune akan d'a? Kenan ita duk kokarin da take yi a gidan ba a ganinta da mutunci? To ta gama zaman gidan, zata tafi inda ake ganinta da mutunci ake girmamata.
Ummah ta kama baki cike da mamaki tana kallonta, tace, "Shukurah! Wane irin zance ne kike yi haka? Me kuma ya kawo wadannan maganganun? Ashe ban isa kiyi kuskure a gidannan in tsawatar miki ba?"
Tace, "wace tsawatarwar? Wannan ai son kai ne kawai! Idan ma fadan ne kiyi mun daga ni sai ke mana, sai ki hadamu da wasu banzaye can sanadin su dinga raina ni?!"
Ummah ta daga murya cikin bacin rai, tace, "Shukurah ni zamu zauna muna sa-in-sa dake a gidannan?"
Sai ta daga hannu sama kamar mai surrender, "kinga, gidan ma zan bar miki ni. Sai ki kama wannan akwajalar da kike neman kamawa, kiga idan zata iya yi miki rabin abinda nake miki!"
Ta juya ta fita fuuu! Tana sakin wasu maganganu marasa dadin ji.
Jikin Nadiya yayi wani irin sanyi a wajen, ta kasa motsa ko dan yatsanta ne. Da tasan abinda zai je yazo kenan, da bata dauko maganar wannan ba.
Tace, "Ummah don Allah kiyi hakuri. Wallahi da nasan haka zata faru, da na hakura na bar zancen."
Sai taga Ummah din tayi dan murmushi, tace mata a tausashe, "kada ki damu Nadiya. Ki kuma daina bani hakuri akan laifin da baki aikata min ba. Akan gaskiyarki kike, ina so daga yau kuma idan abu irin haka ya faru ki dinga sanar dani ko Maigidanki, saboda wannan zancen bai kamata ayi shiru ba kinji?"
Sai ta gyada kai a hankali, "to Ummah!"
Tana kokarin tashi din ne taji Ummah ta mata magana, tace, "ya ki zo nan Nadiya!"
Ta gurgusa, ta matsa kusa da Ummah din inda take nuna gefen kujerar da take zaune, amma ta kasa zama akan kujerar. Sai kawai ta zauna a kasan kafafunta. Ita kuma sai ta kama hannuwanta ta rike tana kallonta da idanu masu cike da kauna irinta Iyaye.
Tace, "zauna muyi magana dake sosai Nadiya, akwai misunderstandings da dama da nake so mu warware yau!"
A lokacin ta zaunar da Nadiya ta bata labarin ko wacece Hajiya Ummah. Duk wani fadi-tashin rayuwa da suka shiga bayan abinda ya faru da su, da kuma irin burika da ta sha akan duk wani iyalin Alhaji Laminu.
Tace mata, "amma a yanzu duk na ajiye wadannan abubuwan, na nemawa zuciyata maslaha. Ina kuma baki hakuri akan abubuwan da duk na aikata miki bayan shigowarki gidannan, har a yadda muka gudanar da neman aurenki ba tare da mun baki zabi ba. Ki yafe min kinji?"
Nadiya sai ta hau share hawaye, tana jin wata irin salama da sanyi na shigarta a duka sassan jikinta.
Tace, "ni dama can ban taba rikeki ba Ummah. Kuma a yau nima, a madadina da duka zuriyar Laminu, don Allah ina neman yafiyarki Ummah. Ki yafe mishi ko Allah Yasa ya samu sassaucin kwanciyar kabari!"
Tayi murmushi wanda ya fito tun daga can karkashin zuciyarta, "na dade da yafe mishi Nadiya. Allah Ya yafe mana baki daya. Allah Yayi muku albarka ku kuma tare da duk zuriyarku bakidaya!"
Nadiya ta amsa da ameen bakin nan nata har kunne saboda tsabar farinciki da jindadi.
Ta mike kafa anan kusa da Ummah, hira suka sha sosai irin wadda basu taba yi ba. Hira irin ta iyaye da yan'uwa, ba ta suruka da suruka ba.
Ba tasan lokacin da barci ya kwasheta ba anan tsakiyar falon. Sai da Ummah ta tasheta tace ta koma daki ta kwanta. Barcin ya gama cin karfinta, ko fahimtar abinda Ummah din ke cewa bata yi. Ta dai koma kan sofa ta mike kafa sadidan ta cigaba da barcinta.
Ranar ko zarafin tashi ta dafa abincin rana bata samu ba. Dole sai a wanda aka yi anan bangaren Ummah ta daukar musu ita da Babangidan ta wuce sashenta dashi. Shi kanshi dai ranar ya ji dadin halin sukuni da farinciki data yini dashi.
*
Washegari suka dauki hanya ita da Mami da kuma Farida. Hanya suka dauka dodar a cikin motar da Babangida din ya bada a kaisu, Rav4 dinshi ja. Ya hadasu da amintaccen direbanshi, Mr. Hassan Bayareben kasar Ilorin, an cika musu bayan mota da akwatu guda da Ummah din ta bada a kaiwa amarya, da kuma tarkacen tsaraba da za a kaiwa yan uwa.
Nadiya kuma ta cika musu mota da kayan tabe-tabe, motsi kadan ta ciro lemun Teem ta bincire hancin, bata ajiyewa sai ta ga babu komi sai robar.
Farida barcinta take sha cikin kwanciyar hankali, tafiya suke yi a cikin mota kamar dai ba ma a cikin mota suke ba, babu bumps na titi, basa ko jin kwarzaben kan hanya da titi sabida sun samu kosasshiyar mota.
Mami ke kallonta tana dan murmushi ganin halin da take ciki, tace, "ba zaki daure ki ci wani abu ba Nadiya? Ga nama nan Babangida ya hadomu dashi kala-kala, ga kuma snacks da ke kika yi da kanki, amma ki ki duka ki buge da shan lemu?"
Ta dan turo baki, "ba na jin yunwar ne wallahi Mami. Ni tunanin cin nama ma yanzu tayar min da zuciya yake yi wallahi. Wannan lemun ne kadai nake jin dadinshi."
Mami ta yada kai gefe guda, tace, "ai shikenan. Idan kinji kina son wani abu dai ki fada da wuri, sai mu tsaya a duba ko a hanya ne."
Tace, "to."
Suna tafe Mami tana janta da hira cikin hikima ta manya da kwarewa irin ta likitoci therapists da suka kware a harkar bin kwakkwafin magana da zance.
Mr. Hassan ya dage yana gudanar da aikinshi cikin kwarewa da iyawa, a gefe guda kuma he's very alert ga duk abinda ke faruwa akan hanyar. Saboda bayan lasisin tuki da yake dashi, Dan sanda ne na farin kaya da aka yi musu training na musamman. Ba yaren hausa yake ji ba sosai, hakan ya ba Nadiya damar sakin jiki suna magana ita da Mami.
Abun nan daya dake damunta ta kasa gane mishi shine take yiwa Mami korafi akai. Don bayan ita bata san wa zata fuskanta da zance makamancin wannan ba.
Sai Mami din ta mata murmushi, tace mata, "kin cika tsoro ne Nadiya, shi yasa!"
Ta kalleta da mamaki, tace, "tsoron me kuma Mami?"
Mami ta gyara zama sosai tana kallonta, tace, "watakila kema baki san da hakan ba, amma a can karkashin zuciyarki tsorone yake hanaki sakewa da maigidanki. Amma kada ki damu, hakan yana yawan faruwa a cikin mata da dama. Akwai mata da yawa da zaki ga yawan yarda da suka yi da mazajensu, ita ce take hobbasawa kuma ta dadada musu rayuwar aure. Ta bangarenki zata iya yiwuwa akwai wani abu tare da Babangida da kila ke a karan kanki baki dauki hakan wata hujja ba, amma kuma unconsciously zuciyarki ta dauki hakan a matsayin wani abu na kare kanta. Kila kina tsoron idan kin sakar mishi jiki watarana zai rabu dake ne, watakila zuciyarki na rada miki ai baya sonki dari-bisa-dari, silly excuses dai iri-iri wadanda basu da kai ma balle kafafu. Abune dake faruwa damu psychologically. Ke da kanki zaki zauna ki nutsu, ki tambayi zuciyarki me kike tsoro? Ki lalubo amsar da kanki. Idan ta magancewa ce ke kadai, sai ki maganceta. Ko ku zauna ke da shi, talk about duk wani insecurity dake addabarki. Idan kinyi hakan, zaki samu mafita in shaa Allah. Sannan kofata a bude take kullum, ko da ace bana nan, zaki iya tuntubata a kodayaushe Nadiya. I'll be glad to help!"
Nadiya tayi shiru tana saurarenta sosai da sosai. Akwai kamshin gaskiya sosai a cikin kalaman Mami. Ta mata godiya, sai kuma ta yada kai kan kujera ta hau barci.
Barci tayi sosai a cikin motar nan har tayi mamakin hakan, don ita ba ma'abociyar yin barcin mota bace. Ga shi tafiyar tasu tayi sauri sosai wannan karon.
Sun shiga Maiduguri wasu masallatan ana kiran sallar la'asar. Kai tsaye gidan da aka sauki Hajiya Ummah wancan lolacin aka wuce da su. Suka samu dafifin yan uwa ana jiransu.
Tarba suka samu sosai da karramawa. Suka yi wanka suka yi sallah, Anty Lima tana ta mata shakiyancin wai me take ci ne ta canza kala da kamanni, ko dai canza musu ita aka yi ne? Tayi banza ta kyaleta tayi ta gama abinta, don gajiyar da tayi da zazzabin dake kadata ma kadai sun isheta. Da kyar ta iya zama ta kira Habibun ta sanar dashi sun sauka lafiya, ta kira Ummah da su Mama suma suka gaisa. Ta kashe wayar ta lalubi gado ta zube har da su rufa.
Anty Lima ta shiga ta sameta cikin wannan halin. Sai ta ajiye kwanukan abinci data kai mata, ta yi kanta da sauri tana tambayarta lafiya? Jin yadda jikinta ya dauki zafi yasa ta fita da sauri ta kira Mami. Tana dubata tace ba wani abu bane, gajiyar tafiya ce kawai. Aka samo paracetamol da ibuprofen ta bata tace ta sha amma ta dan fara cin wani abu.
Ga abinci nan varieties Anty Lima ta shigar mata da su, musamman dashishi da taushen gyada da ya ji naman kaji zako-zako da man shanu da tasan tana cin shi sosai, amma ta kasa ci. Hasalima cewa tayi warin man shanu yana so ya sanyata amai.
Ta janye kwanon daga gabanta tana danne dariyar dake ciyota, tace, "ai ce min zaki yi kawai junior Habibu ne yake tambayarki, har kike nema ki tayar min da hankali!"
Ta watsa mata idanu cikin harara, "a'ah, abinda ya fi junior mantawa kika yi! Ni gajiyar tafiya ce kawai ta sanyani hakan ba wani abu ba!"
Anty Lima tace, "haba yarinya, ai wallahi kici gaba da denying, amma ni tuni na gama harbo jirginki. Baki ga irin murmushi da kallon da Mami take ta yi miki bane ba wai sanda tana dubaki?"
Dan tsaki ta ja, "kin ji da shi dai ko menene. Idan akwai nono ko yoghurt a dama min fura ko tukudi ni dai."
Tayi saluting dinta, "an gama ranki ya dade! Ai fura da tukudi yau sai kin gaji da su!"
Ta fita da sauri sai ga ta dawo babu jimawa, hannu rike da tasa an dama fura ta sha nono mai kyau. Ta gyara zama da kyau ta sha, ta kora da maganin kafin ta koma ta kwanta.
Cikin dan kankanin lokaci zazzabin ya sauka, sai gata ta tashi an cigaba da bidiri da ita.
Da dare suka wuce gidan Anty Hauwa ita da amarya tunda a can take ita da abokanta, suka bar Mami a can.
Wata sabuwar tarar suka samu a can gidan Anty Hauwa. Ita dai suna zuwa da kyar ta iya shiryawa a tsaitsaye, ta bi lafiyar gado ta kwanta ko karfe tara bata gama rufawa ba.
Ta tashi da Asubahi ta tarar da missed calls din Babangidan bila adadin. Don haka ta kirashi suka gaisa. Fadi mata yake yana karawa, shi already gidan ya gama mishi fadi da bata nan, anya ba dawowa zata yi ba ko kuma shi ya biyo ta ba? Ta dinga mishi dariya tana cewa 'ashe da ya zama bita zai-zai?!'
Yace, "ai baki ga bita zai-zai ba sai kin dawo na hanaki zuwa ko nan da can na shekara sannan zaki tabbatar!"
Tayi dariya sosai har ta gode Allah.
Anty Lima tana zaune tana saurarenta tana ta sakin murmushi abinta, har suka yi sallama da shi. Ta kalleta kasa-kasa cike da alamun tsokana, tace, "su yar ware ana cewa ba a so, ba za ayi ba, yau kuma ga ki kece kike i love you I miss you?! Lallai in da ranka ka sha kallo!"
Tayi dan murmushi kawai, tace, "oho miki dai. Ni ki daina tuno min lokacin kan ta waye don Allah!"
Anty Lima kuwa me zata yi ba dariya ba?
A washegarin ranar aka fara gudanar da shagulgulan bikin Anty Lima wanda ya matukar kayatar ya kuma burge.
Sai dai tunda aka fara bikin Nadiya ba zata ce ga takamaiman abinda ke faruwa ba, don kuwa cikin barci take sosai da sosai. Yanzu bata da lokacin komi sai barci, koda yaushe za ka sameta to barci take yi, abin har ya fara damunta kuma. Don kuwa tunda ake events na bikin sau daya taje wajen sisters evening, ta dawo da ciwon kai sosai da sosai har sai daya haddasa mata zazzabi. Don haka Anty Hauwa tace mata ta hakura da zuwa kawai, ta dinga zama a gida tunda ga dangi nan suna ta shiga da fita abinsu, idan taji barci kuma ta gyara kwanciya ta kwanta abinta.
Ga abinci har yanzu bata iya cin komi, sai fura da kankana kullum da lemu mai tsami. Amma biredi wannan in dai zata hadiya sai ta tanadi lemun tsami a kusa da ita. Wannan da kuma rashin ganin bakonta na wannan watan ya sanya ta fara tunanin anya?
A haka dai ta lallaba aka cinye satin nan guda tas ana ta biki kamar ba za a kare ba. Washegarin ranar da aka daura aure, suka dauki amarya aka kaita Garin Kano. A can iyayen mijinta ke zaune, amma harkokinshi sun ma fi karfi a California. Don haka akwai yiwuwar can zata bishi da zama.
Sun kaita gidanta dake can Hotoro G.R.A. Gidanta hadadde ma shaa Allah, ya sha duk wani abu da ake bukatar samu a gida.
Suka wayi gari ita da yan'uwansu anan ana ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 36