tafiyarshi ko?"
Madam tace, "sai ku san juna ta dalilin haka ai. Ki shirya da wuri, wajen karfe takwas zasu zo su daukeki."
Ta katse wayar ba tare data bari Nadiya ta sake cewa wani abu ba.
Ta ajiye wayar yaraf! akan cinyarta jiki a matukar sanyaye. Gabadaya wadannan abubuwa dake faruwa ta kasa fahimtarsu. Ta rasa ta yaya zata fahimcesu. Ya za ayi ita dake kokarin nesanta kanta da abu kuma a dinga kokarin kusantata dashi? Yanzu da zancen aure yake lilo a tsakaninsu, gani take kamar idan ta rabu dashi hakan zai iya zama gaskiya.
Don haka kafin ta kwanta, ta riga ta gama yankewa kanta shawarar abinda zai faru kawai.
Asubahin farko, ta gangara akwatunta ta fito. Ta bugawa Dada kofa, ta bude ta fito da tasbaha a hannunta alamun lazumi take yi.
Ta kalleta da mamaki, tace, "Nadiya, sammako kika bugo kuma? Nayi tunanin zaki bari garin ya gama wayewa?"
Tace, "ai Dada saboda yanayin hanya shi yasa, gwara in fita da wuri din zai fi."
Dada ta yi mata fatan alkhairi sosai. Maigadin gidan ya fita ya samo mata abin hawa ta loda kayanta a kai ta hau, sai tasha.
Sai dai zuwan nasu tashar sai suka tarar da jira. Dole ta shiga mota ta zauna bayan ta biya kudi, aka hau jiran fasinjoji.
Suna nan zaune har bakwai ta kusa rufawa, gabadaya ta fara kagara da zaman jira.
Sai taji wayarta tana kara. Data duba ta ga lamba ce babu suna sai ta mayar ta cikin jaka ta ajiye. Bata cika kin daga sabuwar lamba ba, amma dai wannan lambar ji tayi hankalinta bai kwanta da ita ba, don haka ta ki dagawa.
Aka yi ta kira tana kin dagawa har sai da aka ajiye mata missed calls kusan guda hudu, daga karshe dai ta daga cikin nuna alamun gajiyawa.
Ta kara wayar a kunne, tace, "wai waye ne?"
Shi kuma mai kiran ya tareta da tambayar, "Nadiya kina ina ne?!"
Sai da taji zuciyarta na canza bugawa, amma ta danne zuciyartata. Duk da ta fahimci mai tambayar kuma sai ta mayar mishi da wata tambayar, "waye ne wai?"
Daga can ya fara bata amsar tambayar tata, "kina ina...?"
Kafin ya karasa kuma sai taji yace, "got you!"
Kafin kuma ta ankare kawai taga mutum a tsakiyar kanta.
Ya tsaya ta gefen da take yana kallonta ta cikin bakin gilashi daya rufe fuskarshi da shi, wai ya hau yi mata alamun ta fita daga motar.
Ta kuwa danna mishi harara ta juya kanta gefe guda. Wannan bakar masifa har ina! Ta gudu din ma bata tsira ba sai an dauki hanya an biyota har tasha sai kace wadda tayi sata? Tafiya ko? To ba zata hau motar ba sai taga yadda za ayi da ita.
Ganin ba fitar zata yi ba sai ya koma ga direba, bata san me suke cewa ba, bayan yan mintuna sai taga ana fitar mata da akwatu daga mota. Ta juya tana kallonsu cike da mamakin wannan karfin hali. Da taga dai da gaske fitar da kaya suke yi, sai ta tashi ta fita daga motar, tana tambayar direba lafiya kuma?
Direba ya kalleta, yace, "yata, kiyi hakuri kin ji? Komi na rayuwa fa hakuri ake yi da shi kinji? Ki daure ki taushi zuciyarki ki bi mijinki. Don bai shirya da wuri ba sai kawai ki ce zaki tafi ki bi motar haya? Dama ana haka ne? Yanzu dai tunda gashi ya shirya din, kuma kinga motar ma har yanzu ko rabin cika bata yi ba, ki daure ki bishi din. Allah Ya kiyaye muku hanya!"
Wallahi tsabar mamaki sai ta ma kasa daga baki tayi magana, sai cira idanu data dinga yi a tsakaninsu.
Ta kalleshi, rannan nata idan yayi dubu a bace, tace, "wai wacece matarka?"
Yayi wani murmushin tura haushi, "ga ki nan a tsaye kina kallona!"
Ta jinjina kai kamar wata tsohuwar kadangaruwa tana kwafa, ta juya ta kalli yaron mota dake kokarin daukar kayanta, tace mishi, "Malam ajiye min kayana!"
Babu musu ya ajiyesu ya tsaya yana raba kallo tsakanin ita da Habibu din.
Ta kama akwatinta taja, ta kalli Habib, tace, "kaje ka nemi inda matarka take amma ba Nadiya ba. Tafiya kuma ba zan yi da kai din ba, ka kama hanyarka ka tafi salin alin!"
Ya daga kafada, "ke dai zaki zo mu tafi salin alin saboda kinga lokaci yana kara ja. Don haka tun kafin dare yayi mana, ki zo mu tafi kafin in ciccibeki daga ke har kayan naki wallahi!"
Wata irin dariya ta kwace mata mai cike da takaici da bacin rai. Bata ma iya ce mishi komi ba kawai ta juya zata tafi. Motar ma ta fasa hawa. Gwanda ta tafi wani wajen, kai ta gwammace ta tafi a kafa akan ta bi bayan mutumin nan su tafi tare.
Kamar wani wanda yake jira, ya tattare hannun rigarshi tsakaninshi da Allah har da dan dukawa wai zai dauketa. Taga dai tsakaninshi da Allah daukar nata zai yi a tsakiyar tasha, ga mutane sun zubo musu ido suna kallo.
Sai tayi saurin dakatar dashi, tace, "tsaya, tsaya! Zan tafi da kafafuna!"
Yayi murmushin samun nasara, ya kama akwatinta har da karamar jakar hannunta don ma kada tayi yunkurin tserewa ta barshi da kayan sanyawa. A yadda ya fara karantarta yasan zata aikata fiye da haka ma.
Ya nuna mata hanya, "yauwa, muje!"
Haka ya sanyata a gaba kamar wata diyarshi, suka tafi. Direba yana tambayar kudin motarta fa data biya? Ya juya ya kalli wata tsohuwa dake cikin motar yace a biya mata kudin mota dasu.
Haka suka bar tashar nan tsohuwa na ta kwarara musu addu'ar Allah kiyaye, Allah Ya tsare. Shi kuwa direba ya dage yana karawa Nadiya nasihar a kara hakuri, zaman aure dan hakuri ne. Ji take kamar daga Habibu din har direban ta kamasu tayi ta hade musu kawuna.
Suna fita daga tashar suka samu lafiyayyar bakar Jaguar tana jiransu. Da kanshi ya bude booth ya sanya kayanta a ciki.
Ya dawo har lokacin jakarta tana hannunshi, ya bude mata gidan baya. Taja tsaki, ta harareshi, ta murguda bakin, taga shi dai ko a jikinshi wai an tsikari kakkausa. Sai ta kara jan wani tsakin ta shiga. Ya maida kofar ya rufe, ya zagaya daya gefen shima ya shiga ya zauna.
Sai da yaga direba ya tashi mota sun dauki hanya, ya kuma tabbatar ya dantse kofofi, sannan ne ya mika mata jakarta da wayarta take ta faman ruri.
Ta warci jakar kamar fada, shi kuwa yayi wata irin siririyar dariya data kara bata mata rai.
Ta ciro wayar ta ga Anty Lima ce take kiran nata. Tayi-tayi ta daga kiran wayar taki motsawa. Abin tun faduwar da tayi take bata matsala, wani lokaci sai screen din yaki dannuwa. Tunanin idan ta koma gida ta hade yan canjin hannunta ta canza waya take yi.
Ganin wayar ba daguwa zata yi ba, da takaici ya cikata sai kawai ta kasheta ta jefa cikin jaka.
17.
Tunda suka dauki hanya bata iya ce mishi komi ba, kanta a gefe daya don ma kada yayi gigin tunanin janta da hira.
Hakan bai dameshi ba ko kadan, haka yayi ta yunkurin janta da hirar kuwa ta hanyar watsa mata tambayoyi daban-daban, amma duka tayi biris dashi. Don kanshi ya hakura ya hau kiraye-kiraye da dage-dagen waya.
Basu sarara da tafiya ba sai da suka shiga Damaturu, ya yiwa direba magana akan su tsaya a gidan abinci.
Suka tsaya a wata restaurant mai kyau, ya bude kofar ya fita kafin ya kalleta yace, "ki fito muje mu nemi abin karyawa ko?"
Ta kalleshi a kaikaice tace, "nagode!"
Shi kuwa bai kara ce mata komi ba suka fita shi da direban suka shiga gidan abincin.
Ta kwantar da kanta a jikin kujera tana binsu da kallo har suka shige. Yunwar take ji sosai, cikinta sai kugi yake, amma saboda tsabar taurin rai ta kasa tashi ta bi bayansu. Sai ma rufe idanu da tayi wani wahalallen barci yayi awon gaba da ita.
Bata san lokacin da suka dauka a ciki ba, sai da taji an bude motar an shigo sannan ta dan farka. Data duba lokaci sai taga sun dauki kusan mintuna talatin.
Ta gyara zama a hankali tana kara gyara zamanta.
Yana zama direba ya tashi mota suka kara daukar hanya. Ya mika mata leda madaidaiciya, ganin bata amsa ba yasa ya dora mata ita akan cinyarta.
Tayi biris da ita na dan lokaci. Kamshin dake fita daga ledar yana shiga hancinta yasa yunwar dake nanikarta ta kara tasowa, don dama daren jiya ba wani abin kirki ta ci ba.
Ta daga ledar tana zaro kayan ciki a hankali kamar wata mai tsoron dagawar, ta fara zaro samosa, meatpie, danginsu spring rolls da lemuka guda biyu na exotic, har da karin tarkacen cakuletin dairy milk da alewar bounty. Ta tabe baki kamar ba wani abin arziki ya mata ba.
Ta fara cin kayan a hankali tana korawa da lemu, kafin kace me ta kusa cinye komi. Sauran da suka rage ta dukunkune su a cikin leda, ta kara kwantar da kanta a jikin kujera ta koma wani barcin.
Wannan kam yayi nisa sosai. Jifa-jifa dai ta kan farka ta duba inda suke da kuma lokaci kafin ta koma, bata tashi daga barcin sosai ba sai da suka shiga Kano. Nan ma sai da suka tsaya ne a wani masallaci na matafiya sannan.
Su duka suka fita, su suka wuce bangaren maza, ita kuma ta wuce na mata.
Daga nan suka sake daukar hanya. Tafiya lumi-lumi gwanin dadi, sai gashi ana kiraye-kirayen la'asar suka shiga cikin Kaduna.
Babu wata kwakkwarar magana data hadasu har a lokacin.
Ya juya ya kalleta yana ce mata, "a ina zamu ajiyeki?"
Tace mishi, "idan mun je Kawo kawai ku ajiyeni, zan karasa da kaina!"
Ya sake kallonta fuska a dan gintse, "tambayarki nake inda zamu ajiyeki."
Ta turo baki kamar zata ce wani abu, sai kuma ta canza shawara. Ta fada mishi unguwar da zasu sauketa.
Da taimakon kwatancen da take yiwa direban sai gasu har a kofar gidansu.
Yana yin parking, ta bude murfin motar ta fita kamar wadda ake mintsina a cikin motar.
Direba ya fita ya bude booth ya fitar mata da kayanta. Sai ga yaran gidan sun fito aka hau murnar ganinta da kuma fadan wanda zai daukar mata kaya.
Bai fita daga motar ba, sai gilashin motar na bangarenshi daya bude, ya dan zura kanshi waje yana mata magana, "baki ji ba!"
Yi tayi kamar ba zata juya din ba, sai kuma ta juya tana kallonshi, fuskar nan idan ka ganta kamar wadda tayi tuntube da kashi.
Wata jaka yake mika mata irin gift bag dinnan ruwan hoda, tayi tsaye kawai tana kallonshi babu alamun zata matsa ma balle ta amsa. Sai ya yafici Fatima, ita kuwa ta ruga da gudunta taje har da dukawa tana gaida shi. Ya mika mata jakar yace mata, "rikewa Antynki wannan ko?!"
Ta kuwa sanya hannu biyu ta amsa, kafin ma Nadiya tace mata wani abu har ta falla cikin gidan da gudu.
Shi kuwa ya kalleta, ya sakar mata murmushi, ya rufe gilashin mota direba ya ja suka yi gaba.
Tayi tsaye a kofar gidan tana bin motar da kallo har ta wuce. Mamakin wannan al'amari take yi, karfin halin mutumin ai har ya wuce misali.
Ita abin gabadaya ya fara daure mata kai. Wannan shisshigi da ake mata ya fara shigar mata hanci da kudundune fa. Tayi kwafa ta wuce cikin gidan itama, a ranta tana fadin zata taka mishi birki matukar ya kara hada hanya da ita.
Tana shiga gidan ta kula da canjin da aka samu. Ita gabadaya ta ma manta da zancen amaryar Abbansu zata tare, sai da ta ci karo da bakuwar fuska a zaune akan dan dandamalin dakin Mama da farantim shinkafa a gabanta tana aikin tsinta.
Su Salame da Lantana kuma suna kofar dakin Salame din wanda yake fuskantar na Mama, sun baza tabarma akai suna ta zubda ruwan habaici.
Data musu sallama sai taga sun watsa mata kallon banza, suka kara da harara da tsaki. Don haka ta dauke kanta daga garesu, ta karasa kofar dakin Mama da take a tsaye, kai tsaye ta rungumeta cike da kewa da jindadin ganinta.
Bayan sun gama gaishe-gaishensu, amarya ta juya tana mata sannu da hanya.
Ta kare mata kallo cike da mamaki. Da ake cewa amaryar ta Babansu yarinya ce, bata yarda ba sai data ganta da idanunta sannan.
Yarinya ce danya shataf, da kyar idan ta haura sha takwas. Amma wai a hakan ma aurenta ne na biyu.
Ta amsa mata a nutse, kafin ta karasa cikin dakin.
Ta shige can cikin dakin Mama ta watsa ruwa don bata tunanin zata iya shiga na tsakar gida. Data fito ta sanya doguwar riga ta jan material marar nauyi, tayi sallah.
Kafin ta gama har Maryam ta kai mata danwake, da alama shi suka yi a gidan da rana. An yanka mishi albasa da tumatiri da latas, ta zauna ta ci sosai da sosai ta kora da ruwan sanyi.
Ta jona wayarta a caji, kafin ta fita wajensu Mama da suka koma kofar kicin yanzu ita da amarya. Amarya na jajjagen kayan miya a turmi, Mama kuma tana kokarin dora tukunya akan wuta.
Nan ta zauna suna hirarrakinsu tana tayasu da wani aikin har aka yi Magriba.
Ta fahimci amaryar ta Abban nasu babu laifi tana da hankalinta, kuma bata da rawar kai. Gashi tana girmama Mama sosai, don hatta da ita kanta Nadiya din bata kiran sunanta kai tsaye, sai dai tace Antyn yara. A ranta take tunanin wata kila ita za ayi zaman mutumci da ita.
Har ta gama shirin kwanciyarta, sunyi waya da su Dada da Anty Lima har da Anty Hauwa. Data kira Madam bata dauka ba sai ta tura mata sakon cewa ta isa gida lafiya, itama Safiya sai data kirata suka gaisa.
Idanunta suka sauka akan jakar da aka bata dazu, wadda ta dorata akan TV stand, bata kuma kara bi ta kanta ba sai a lokacin.
Ta so ta kyaleta tayi ta zama anan, amma curiosity ya hanata. Ta tashi ta dauki jakar, ta koma ta zauna tare da fara zaro abubuwan dake ciki.
Ta zaro idanu cikin tsananin kaduwa da mamaki, zuciyarta na duka ganin gyallelen kwalin wayar Samsung a ciki. Ta hau kwale kwalin wayar har ta ci karo da ita, taga da gaske dai wayar ce ba wasa ko tsokana ba. A bayan kwalin an lika karamar post it card an rubuta, 'fansar wayar da na lalata miki. Fatan za ki karba' a turance.
Ta kama baki cike da mamaki, kafin kuma ta janyo sauran abinda ke ciki. Kwalayen turaruka ne masu kyau kusan kala hudu, da Borneo Oud, Oud Violet, Nishane, Amouage, Thomas de Monaco Raw Gold. Su kuma a jiki an rubuta 'to a fellow perfume lover'
Ta tabe baki kamar yana gabanta. Ta rasa ta yadda aka yi cikin dan kankanin lokaci har ya fahimci tana da son kamshi. Da alama dai yana da kula, 'da kuma sa ido ba!' Wani sashe na zuciyarta ya ayyana mata hakan.
Ta zauna na tsayin lokaci anan tana tunanin abinda ya kamata da sake-sake. Daga karshe dai ta janyo wayarta ta dannawa Anty Lima da yake karfe goma bata kai ga yi ba.
Tace mata ita dai gaskiya zata mayar mishi da kayanshi don bata ga dalilin da zai sa yayi mata wannan kyautar ba.
Anty Lima tace, "to wai sai me don ya baki kyautar waya da turare? Kin rokeshi ne kika ce ya baki?"
Tace, "wa? Allah Ya tsareni!"
Tace, "to kin gani? Shi yayi radin kanshi ya baki, don haka ki amsa da hannu bibiyu. Ina ruwanki da shi da kayan daya baki? Idan kin tashi ki ware min turare guda don nasan zasu hadu sosai, na ji turarukan da yake amfani dasu masu kyau ne kuma suna da kamshi."
Tayi yard dariya, "Allah Yaa kyauta miki wallahi! Sai ki bari sai nayi tunani na tabbatar zan rike din sannan. Sai da safe, barci nake ji!"
Suka yi sallama ta kashe wayar.
Kwanciyarta tayi ta ajiye kayan a gefe.
Da asuba tayi mamaki da taji Abbansu ya fito ya bi daki-daki wai yana tashinsu sallar Asubahi.
Abin ya bata mamaki matuka, ta kame baki cike da tsananin mamaki. Mama da ta sallame sallah ta kalleta ganin yadda tayi hangangam da baki tana bin wannan lamari da kallo, tace, "Nadiya ki tashi kiyi sallarki kada lokaci ya kure kinji!"
Haka ta lallabata ta tashi tayi alwala tayi sallah.
Gari yana yin haske ta je ta gaishe da Abbansu.
Ta fito daga dakin nashi ta tsinci Salame tayi kerere a kofar dakin amarya, ita kuma amaryar ta ci kwalliyarta da wani mini skirt dinta da yar yaloluwar riga zata shiga dakin Abban nasu.
Tana ganin Nadiya sai ta hau fara'a, "a'ah! Antynsu kin tashi kenan? Ina kwana, ya gajiyar tafiya?"
Gaisuwar tata sai ta bata kunya, tace mata, "Gajiya fa Alhamdulillah. Ina kwana?"
Salame ta ja wani dogon tsaki, dai dai lokacin Lantana ta fito daga nata dakin da riga da zane daban-daban, fuskar nan tata dagaje-dagaje da alama dai ita ko sallar da aka tashesu bata kai ga yi ba.
Laminde tace, "oh ni Yaya! Jiya kinji tashin hankalin da naji kuwa?!"
Nadiya ta kalli Laminde din cike da mamakin abinda tace, a tunaninta ko rashin lafiya ta kwana da ita.
Salame ta dannawa Amarya harara, "jiya ke kika ga tashin hankali ko ni! Wallahi ban taba ganin rashin mutunci ba irin na jiya. Kawai aka hanani barci don tsabar jaraba da kwarzaba da rashin tunani! Kai baka ganin gidanka gidane na yara, kuma dakina da inda kake bango-da-bango amma ba zaka yi tunanin hakan ba? Wannan ai shiga hakkine da rashin sanin darajar dan Adam!"
Sai lokacin ta fahimci abinda ke faruwa a wajen, dariya ce ke kokarin kufce mata, ta sanya hannu tana rufe baki don kar ta fito.
Ita kuwa amarya bata nuna ta fahimci abinda suke nufi ba, sai ta bisu daya bayan daya ta gaishesu, ta juya ta fada dakin Mai gida ta barsu anan ba tare da ta jira sun amsa ba.
Suka bita da harara kamar idanunsu zasu fadi. Lantana tayi kwafa tace, "yar iska kawai! Da alama dai wannan karon tsohuwar karuwa aka kawo mana!"
Salame tace, "bar ni da ita, in takamarta iskanci, ni ai na fita iyawa! Wallahi sai na gasa mata gyada a tafin hannunta!"
Nadiya da har lokacin take wajen tana kallonsu da murmushi akan fuskarta, ta kyalkyale da dariya har da tafa hannuwa, suka hau binta da kallo kamar wadda ta samu tabuwa.
Tace musu "ai shi yasa masu iya karin magana suke cewa wai a dinga sara ana duba bakin gatari. Kuma dai sannu bata hani na zuwa sai dai fa a dade ba a je din ba!"
Suka zaburo mata a lokaci guda, "me kike nufi?!"
Ta haskesu da wani murmushin tura haushi, "abinda nake nufi kenan!"
Ta shige ta barsu anan suna ta sakin maganganu sai kace wadanda ke shirin tada bori.
Da ta nunawa Mama wayar da Habibu ya bata da kuma abubuwan da suka wanzu a Maiduguri. Itama dai shawarar da Anty Lima ta bata ta maimaita mata, tace ta amsa tayi amfani da su tunda dai shi ya bata kyauta ba roka tayi ba. Kuma dai babu mai mayar da hannun kyauta baya sai shaidan. Don haka ta amsa kawai.
Maryam da take jinsu kuwa tayi tsalle ta dafe tsohuwar wayar Nadiya din, tace, "dama ina ta jiran ranar da zaki yi sabuwar waya ki bani wannan, sai in ba Amina ta wa."
Da yake ta hannun nata karama ce.
Nadiya tayi murmushi, tace "to shikenan. Bari idan na dauke kayan cikinta sai a bada a canza screen din, sai a canza."
Suna karyawa suka fito da kayan wanki jibgi guda, ranar haka suka yini suna aikin wanki ba kama hannun yaro. Da suka gama suka shiga dakin Mama shima suka gyara har da canza zaman kayan dakin.
Zuwa yamma ta dauke duk abubuwan da take bukata daga tsohuwar wayarta zuwa sabuwar, ta bada a kai tsohuwar wajen gyara.
Ta kira Aramide tana tambayarta game da wajen aiki, ta bata tabbacin an je an share komi an gyara, don haka idan sun je gobe aiki za a hau yi kawai babu bata lokaci. Tace itama satin sama zata dawo saboda wajen aiki. Suka yi sallama akan hakan.
18.
Kwana da kwanaki suna ta wucewa a hankali. Nadiya ta koma ta cigaba da gudanar da ayyukanta kamar da. Tuni ta manta da abin wani Habib da kurar data kwasoshi. Musamman da tun barinta da shi na karshe bata kara gani ko jin labarinshi ba.
Wata ya shige a haka, sai gashi har an fara zancen shigowar azumi nan da wata daya.
Zaman gidan nasu sai ya rikide ya koma wani yanayi na daban. Yadda su Salame suka so shine idan amarya ta zo, su yi kokari su janyeta ta koma cikinsu, su dinga muzgunawa Mama. Sai abin ya juye ya koma kansu.
Don kuwa ita dai amarya ba ta tasu take yi ba, ta kama Mama da 'ya'yanta ta rike kam da hannu biyu. Babu abinda ya dameta, yadda kowa yake kiranta Mama itama abinda take kiranta da shi kenan. Haka zata zage ranar girkin Mama ta tayata kamar ita ke girkin, ita kuma Mama ranar girkin amaryar sai su Maryam da Amina su tayata. Itama Nadiya idan tana nan ta kan tayata din.
Nan da nan kuma sai suka saba sosai, ya zamana dakin Mama nan ne wajen zamanta. Hakan kuma sai ya zama abin gulma da maida magana a wajen su Lantana. Su ce Mama ta asirceta, su ce ta mallaketa, su ce ta maidata baiwa. Zance dai kashi-kashi. Ita kuwa Mama da yake dama can ba kulasu take yi ba, sai tayi kunnen uwar shegu da su. Itama amaryar da Allah Yayi ta marar son rigima, sai take kyalesu bata shiga harkarsu.
Har yaran gida suka sa wai su dinga yiwa amarya rashin kunya, ko kuma Idan ta aikesu su ki zuwa. Shi din ma da ba don Nadiya ta taka musu burki ba da sai abin ya fi haka.
Ranar juma'a ta taso daga shago da dare dai-dai lokacin data saba dawowa. Tayi sallama ta shiga gidan, da yake girkin amarya ne ranar bata tsaya ta sayi abinci ba. Tunda tana da tabbacin kwanon abincinta yana nan.
Su Salame dama ba a zancensu, tuni ta fita ta harkarsu akan abinci dai. Saboda su dai farko ba kasafai suka cika tsayawa su dafa abinci mai dadi ba. Na biyu kuma abincinsu suna saukeshi a tukunya, da shi da babu duk daya ne. Idan kana kusa da su kayi wuf ka mika kwano su zuba maka, idan ka zauna jira kuwa sai su ce maka ai ya kare yara sun cinye. Ta sha biye musu akan hakan su yi ta fada, su mata gori su zageta tas, shima Abbansu idan ya dawo ya sameta yayi ta zagin har ya dinga hadawa da zagin 'katuwar banza da ita ta zaune mishi a gida yana ciyar da ita a banza! Idan ta ji haushi ta bar mishi gidan mana ko ta dinga ci da kanta!'
Da taga abin ya kai ga haka sai ta yiwa kanta fada. Tunda dai Allah Yasa tana da rufin asirinta dai-dai gwargwado. Shagon da take zuwa shi ya taimaka mata take sauke nauyin al'amuranta da dama. Sai ta kara da lissafin abinci a ciki. Idan ba girkin Mama ba dama ba abincin su ke ci ya ishesu ba. Don haka ta kyale musu kayansu.
A dakin Mama ta ci karo da Basira ta je gidan, da 'ya'yanta uku. Ta zauna suka gaisa da ita tana tambayarta ya kwana biyu, saboda sun jima basu gaisa ba. Gwara Zainab suna yawan yin waya da ita tunda da waya a hannunta, ita kuwa Basira da yake bata da wayar a hannunta sai idan ta samu aro sannan ne take kiransu. Shima kiran sau tari bai wuce ta ce Nadiyar ta tura mata kudi ba ko kaya.
Ta kunce ledar sauran doughnuts da suka yi da cupcakes, ta bada biyu aka ba amarya, su Fatima ma ta basu biyun su raba, ta ba yaran Basira dai-daya sauran kuma ta barwa su Maryam.
Tayi sallah, ta zauna aka zubo mata abinci zata ci. Daga Basira har yaran suka zuba mata idanu yuu! Suna kallo kai kace sauran yunwa ne. Sai kawai ta mika musu kwanon, suka karba suka hau ci hannu-baka-hannu-kwarya. Kafin kace me! sun tada faranti guda. Suka tsaya suna lasar hannu da kwano.
Ta kallesu da tausayi zane akan fuskarta. Tace, "ko baku ci abinci bane? Maryam je ki tambayi Anty amarya ko da sauran abinci
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 36