Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
isa. Ta tsaya a cikin tashar tana kalle-kalle don kuwa ba tasan ina zata nufa ba daga nan. Ga AbdulHadi yana ta tsala mata kuka, gajiya da yunwa su duka sun lullubesu. Yan canjin daya rage mata ba wasu masu kauri bane. Ta matsa wajen wata mata dake sayar da abinci. Da alama ma ranar abincin kwantai ya mata don kuwa tashar ba wasu mutane bane da yawa. Ta bada aka sanya mata dafadukan shinkafa, ta kara da kunun gyada ta matsa gefe ta zauna tana ci hannu baka hannu kwarya, don kuwa tun karin safe da tayi babu abinda ya kara shiga cikinta, tana yi tana mikawa AbdulHadi shima yana ci. Da suka gama ta lallabashi yayi barci, ta samu waje tayi alwala sannan ta shiga biyan bashin sallolinta. Data kula da wannan mata mai abinci dai rumfa take da ita a kusa da tashar, kuma anan take kwana, sai ta matsa ta sameta da hawayenta a ido ta roki data taimaka mata ta kwana a wajenta. Ta mata karyar ai ganin gida taje, kuma sai ta yanke shawarar ta koma gida kafin adadin data dauka ya cika, kuma abin bata taba zuwa ko'ina ita kadai ba tare da maigidanta ba, shine dare yayi mata kuma tana tsoron yin tafiyar dare ko kuma kwanan tasha ita kadai. Matar ta tausaya mata kwarai, don haka ta mata. alfarmar ta kwana din. Kafin safiyar ta gama yankewa kanta shawarar daukar hakuri ta koma gidan Auwal tunda bata da wani zabi wanda yafi wannan. Gari yana wayewa kuwa ta yiwa matar nan sallama da godiya, ta shiga mota suka dumfari Kaduna. Inna Deluwa sai ganinta tayi da tsakiyar rana kamar wadda aka jefo. Tayi salati ta sanar da Ubangiji. Ta kamata ta rungume cikin murna. Daga ita har Auwalun sun shiga cikin tashin hankali da damuwa kwarai da gaske. Don kuwa duk iskancin da yake yi, yana sonta kawai giyar mata da kudice take kwasarshi tana sa wa yana mata wulakanci. Tafiyarta kuma ita ta kara tabbatar mishi da hakan. Shi yasa hankalinshi ya dagu yayi sama, gashi lokacin waya bata zagaya ko'ina ba, to ko da wayar ma wa suka sani da zasu tuntuba? Shi yasa suka mayar da hankali wajen addu'a kawai. Kafin a sanar dashi dawowar tata yaje har sunyi wanka, Inna Deluwa ta hada miyar kuka da tuwon dawa da Juwairah din ta sameta tana tukawa ta kai mata ta ci tayi nak, sun kwanta ita da Abdul din sun hau barcin gajiya. Sai gashi ragajab-ragajab kamar wani amale yana ta baza uwar babbar riga ko daga ina yake? Ganin suna barci sai yayi turus daga bakin kofa yana zabga fara'a yana tambayar Inna Deluwa da yaushe suka dawo? Ta amsa mishi ciki-ciki don kuwa har lokacin cikin fushi dashi take. Zuwa dare ta sake hadasu ta musu sasanci da kara tausar Juwairah din. Ta amince da cewa zata riki da, amma fa ya daina mata gorin dangi. Ya amsa da saurinshi yace ya daina. Da haka dai suka tattara suka koma gidansu, ta rike Hannafi da AbdulHadi ta rika kamar dukansu ita ta haifesu. Shima kuma Auwalun yayi mugun sanyi ya shiga taitayinshi, sai tattalinta yake yi. Cikin lokaci kankani sai gata da wani cikin. Ya kuma nuna matukar farincikinshi da jin haka. Ashe ba tare da sanin kowa ba, ya hadu da Barira, mahaifiyarsu Jamila. Lokacin itace ma Vice Principal a FGGC Munjibir, kuma haifaffiyar garin Kano ce a unguwar Galadanchi. Ya je raka wani Ubangidanshi ganin diyarshi da take karatu a makarantar suka hadu da ita, jininsu ya hadu da ita. Kuma cikin dan kankanin lokaci zancen aure ya shiga tsakaninsu. Ya gundura mata karyar ai bashi da aure sun rabu da matarshi. Aka yi aure ta tare abinta kasancewar kuma zawara ce, ta taba aure amma bata taba haihuwa ba sai abin yaje musu da rashin hayaniya. Shikenan duk karshen sati yana tafe kan hanyar Kano, ya cewa Juwairah din ai wani aiki ne na musamman yake kaishi gidan Gwamnatin Kano, ita kuma ta hau kai ta zauna daram. Kusan a tattare suka haihu su biyun, ita Juwairah ta haifi 'ya mace, Barira kuma ta haifi danta namiji. 9. Diyar da Juwairah ta haifa bata dade ba ta koma sakamakon matsananciyar rashin lafiyar data yi. Suka yi jimami na dan lokaci suka hakura suka maidawa Allah lamarinshi. Rayuwa ta cigaba da tafiya a haka. Auwalu kuma ya cigaba da aure-aurenshi. Juwairah tun tana jin haushi da tashin hankalinta har ta gaji ta hakurewa kanta. Tunda abin dadin matan basu cika zama ba. Abin takaicin shine da yawancinsu suke maida mishi 'ya'yanshi da zarar sun rabu. Don ma tun bayan Saminu bai kara kai mata da ba sai dai wajen Inna Deluwa yake kaiwa. Don kuwa a lokacin daya zaunar da ita yake bata labarin yana da wata matar a Kano har suna da 'ya'ya biyu da ita, akwai wasu yaran biyu a hannun Inna din. Itama kuma da wata diyar wadda ta sake haifa tana shayarwa. Cikin ikon Allah kuma sai taji kwata-kwata hankalinta bai tashi ba sam. Ta tabe mishi baki tace to 'Allah raya!' Ta tashi ta bar mishi wajen. Shi kanshi sai da yayi mamakin hakan. A cikin wannan kwaramniya kwatsam sai Allah Ya hadashi da Fatima Zahra. Sun je can Maidugurin lokacin ana ruguntsumin siyasa kuwa. Tun bayan da karayar arziki ta samu Lamin, gabadaya komi ya cukurkude ya rikice, abubuwa duk sun tsaya musu cak. Lokacin Hauwau tayi aurenta, Allah Ya hadata da wani mutum magidanci ya nuna yana da sha'awar aurenta kuma yayi alkawarin tsaye mata tayi karatu har ta gama. Babu bata lokaci kuwa aka daura aure ta tare a gidanta. Anan Maidugurin suke da zama saboda mijin nata Lakcara ne yana koyarwa a Jami'ar Maiduguri. Yasir shi kuma cikin ikon Allah ya samu scholarship a Bangladesh ya tafi. Ita kuma Zarah ta samu ta gama karatun sakandaren da kyar babu zancen cigaba da wani don kuwa a lokacin ta abincin ci ma ake yi karewa. Fatima Zahra wata irin yarinyace mai tsananin son abun duniya. Tana da son hutu da watayawa, kuma zata yi duk abinda zai kai mata yan kudade komi kankantarsu kuwa. Tana kuma da kutse-kutse da tura kanta wajen masu hannu da shuni. Duk da dai yawanci su masu mu'amala da ita kyawunta ne yake dibarsu suke so suyi kawance da ita. Kawancen ne ma ya hadata da wata diyar wani hamshakin mai kudi, wanda yake na hannun damar Gwamnan da ya ci takara a wancan lokacin. Kuma so take yi ta samu dama, ta rokeshi akan ya taimaka ya hadata da wani Kaninshi dake zaune a Kano kuma babban darakta domin harkar fim take so ta fara. Daga farko so tayi Lamin ya hadata da mutanen da shi ya sani tunda har lokacin suna dan yin hulda da wasu manyan mutanen. Shi kuwa yayi tsalle ya dire yace ba a gidanshi ba, ya kuma fada ya kara nanata mata, matukar ta shiga harkar film to haihata-haihata shi da ita, sun rabu kenan. Ita kuwa wata kawarsu ce ta tsole mata idanu. Tana tsakiyar karatun sakandare ta ajiye ta tafi harkar film. Kuma cikin ikon Allah da yake taje da kafar dama, sai gashi cikin abinda bai gaza shekara guda ba har tayi suna tayi arziki. Don taji ance ma har motar tukawa ke gareta. Yadda kuma abokanta suke zugata da kara nuna mata baiwar kyan da Allah Ya mata, suna fada mata Fadilar da ko rabin kyanta bata yi ba ta samu wannan daukaka ina ga ita? Sai kanta yake kara huruwa suna kara mata karfin gwiwa. Wannan dalili yasa ta nemi yin kawance da Karimah ta kuma samu damar shiga jikinta da iyayenta. A cewarta, ko basu yi mata hanyar shiga film ba, zasu mata hanyar haduwa da wani babban wanda shi zai iya yi mata hanyar. Nan da nan kuwa dai gashi ta riga ta zama kamar yar gida, ya zamana duk wasu shirye-shiryen abubuwa da ake yi na walimar da mahaifin Karimah ya hadawa sabon Gwamna da ita ake yi. Don hatta ranar da Gwamna da iyalanshi suka tare a gidan Gwamnati da ita aka je. Anan kuma suka hadu da Auwalu wanda shi kuma Gwamnan abokin Ubangidanshi ne na kut-da-kut. Duk wani namiji dake cikin gidan wannan a lokacin Zahra ta tafi da imaninshi. Kuma kowa a shirye yake da tace zata aureshi a daura musu aure. Cikin ikon Allah sai hankalinta yafi karkata ga Auwalu. Don kuwa akwai shi da iya tsara zance, ga kuma naci da rashin zuciya in dai akan macen da yake so ne. Ga shi ya rufe ido ya dinga mata barin kudi ba ji ba gani. Duk wulakancin data dinga mishi ko a jikinshi bai dinga nunawa ba, sai ma salo da dabaru na sace zuciya daya dinga je mata dasu iri-iri. Har dai ya tashi komawa Kaduna bata bashi wata gamsasshiyar amsa ba amma bai karaya ba. Don kuwa ko wata guda cikakke bai yi ba ya sake koma mata tafiya ta musamman Anan suka daidaita da ita. Ya galla mata karyar matarshi daya da danshi daya amma sun rabu da matar shi kuma dan yana wajen mahaifiyarshi. Ya kuma nuna mata yana da irin makudan kudaden nan, don yana ma gab da shiga siyasa. Jin haka sai tayi caraf tace ta amince. Nan da nan sai ga magana tayi karfi, abin mamakin har aka yi aka gama abokan ango ne ke ta kaiwa da kawowa babu danginshi ko daya. Amma barin kudin da suke musu yasa babu wanda yayi gigin cewa ba haka ba. Allah kadai yasan iyaka adadin kudin da Auwalu ya kashewa Zarah. Zai iya cewa tunda yake bai taba kashewa mace rabin abinda ya kashe mata ba, har Juwairah din kuwa. To amma da yake so ya rufe mishi ido, ko a jikinshi. Ta bangaren iyayenta ma kuma da dangi sun yi iyaka bakin kokarinsu sun mata duk abinda ya dace. Ranar daurin aure kwatsam sai ga dirar Ummulkhairi diyar marigayi Alhaji Kachalla gidan. Wasu jibga-jibgan motoci kosassu kamar ana ciyar dasu suka yi mata rakiya, sai ga bodyguards na take mata baya. Kai tsaye kuma gidan bikin ta yiwa dirar mikiya babu wanda ta nema a cikin dangi. Nan da nan sai murna ta hadu gida biyu, aka taru ana ta murna ana mata sannu da zuwa da nan-nan da ita kamar a dauketa a goya a baya. Ta yini guda cur cikin dangi ana ta hira da ita da raha gwanin dadi. Zuwa yamma ta tashi tafiya don tace ba zata kwana a nan ba, an riga anyi mata masauki a masarautar Borno, kuma idan gari ya waye ba zata biyo ba daga can zata wuce. Ta yiwa yan uwa kyauta ta kudade masu yawa, suna ta mamaki da godiya baki ya kasa rufuwa, amma aka rasa wanda zai tambayeta inda ta samu wadannan kudade. Tana da aure ko bata? Wani hali take ciki? Duk babu wanda ya mata wannan tambayar. Sai da zata tafi dinne ta bukaci ganin Lamin. Duk a zaton mutane kyautar bajinta shima zata mishi kamar yadda ta musu. Suka shiga uwar daka suka rufe. Shiru-shiru suka jima a ciki, me suka ce, me suka tattauna? Allah kadai ya sani. Zuwa can bayan lokaci mai tsayi ta fito, tayi waje kai tsaye ta shige mota aka ja suka tafi. Sai ga Lamin ya fito daga daki yana ta zabga zufa kamar wanda aka watsawa ruwa, idanu sun rine sunyi jawur sai kace wanda yayi kuka. Mutane suka dinga binshi da tambayar lafiya? Amma babu amsa. A haka dai aka lallaba washegari aka tafi kai amarya dakinta. Kalilan daga cikin danginta sune masu yin rakiyar. In ka debe Hauwau sai wata Yayar Babarta, Iya Lantu sai kuwa kanwar Lamin din Harira, sai maza guda biyu. Suka je suka dawo da daddadan labarin diyarsu tayi goshi. Don kuwa irin gidan da aka kaita da kayan alatun da aka zuba mata, ko diyar wani hamshakin mai kudin sai haka. Ana ta wannan murna da yiwa juna san barka, watarana Lamin ya fita kawai sai ganinshi aka yi ya fadi, barin jiki ya shanye. Aka kwasa hankali tashe aka yi asibiti dashi. Bayan dogon bincike dai likita ya tabbatar da cewa damuwa ce tayi mishi yawa, jininshi ya hau da yawa. Kuma babu abinda zasu iya yi akai sai dai kawai a rubuta magungunan da za a dinga bashi, sai kuma yayi kokari ya rage yawan damuwa. Haka aka kwasheshi aka koma gida aka hau jinya. Amarya mutanen Kaduna, tana can tana ta shan amarcinta bama ta san kalar wainar da suke toyawa ba. Soyayya ake zubawa kamar ba gobe, yadda kasan su hadiye juna ita da Auwalu tsabar so. Yace mata yana aiki a Kano, don haka kwana biyu yake yi anan ya tafi wajen aikinshi yayi kwana biyu. Bata kuma taba tambayar wani aiki bane yake yi wanda har ranar karshen sati sai yaje. Ita dai tunda ya ajiye mata duk abinda take bukata shikenan. Ga talbijin dinta da bidiyo, ya sayo mata kaset-kaset sai wanda ta zaba, kwana take yi ta yini kallo babu abinda ya dameta. Abinda dai yake ci mata tuwo a kwarya shine yadda har ta tasar ma cinye wata daya a gidan babu wani dangi nashi data ga ya taka kafa yaje inda suke. Shi kuwa dama tunda auren ya gabato, ya sanarwa da Inna Deluwa da Juwairah zai yi aure. Juwairah ta yada kai gefe guda tace 'Allah bada zaman lafiya!' don kuwa ita abin ya riga ya zame mata jiki yanzu. Inna Deluwa ce ta dinga kallonshi kamar wani wanda ya samu matsalar kwalwa, musamman da ya karkace kai ya hau bata labarin ai ba a gida daya zai hadasu da Juwairah ba. Saboda ita din yarinya ce, wadda ta tashi a gidan hutu bai kamata ya dauketa ya kaita gaban kishiya ba da hayaniyar yara. Inna Deluwa tace, "wallahi kai dai anyi mutumin banza Auwalu! Har kana da bakin dagawa kacewa Juwairah wai ba zaka hadata da kishiya ba saboda yarinya ce kuma gidan hutu ta tashi? To ahir dinka wallahi! Aure ba zan hanaka ba, kaje kayi tayi matsalarka ce, 'ya'yane kayi ta tarawa kowa da uwarshi, daga baya kai abin zai dawo yana ciwa tuwo a kwarya. Amma wai raba kan mata wannan shine ban yarda dashi ba sam! Ka kawota nan kamar yadda ka kawo wadanda suka fita. Wannan ita ce magana!" Ta tashi ta barshi anan. Amma duk da haka bai ji maganarta ba, sai yayi kunnen uwar shegu da ita ya cigaba da bidirinshi. Wannan dalili yasa koda aka kawo amarya da yace su je su ga daki basu je ba. Dama Inna din a shake take dashi. Bata taba sanin yana da wata matar ba a Kano sai a wannan dan takin kafin aurenshi da Zahra din. Rana daya sai mata ta musu sallama a gida da yaranta biyu mace da namiji, don namijin ma da alama ya haura shekara goma macen kuma zata yi takwas. Ta amshesu da hannu bibiyu, ta basu wajen zama ta kai musu ruwa suka sha. Bayan sun gama hutawa sai take tambayarsu ko daga ina? Budar bakin mata sai ce mata tayi ai matar Auwalu ce. Tace 'wace mata kuma yar nan?' Ta sake ce mata, 'matar Auwalu dai dake zaune a Kano?!' Inna tayi salati da salallami, taji kamar ta dora hannu aka ta dinga kwala ihu. Sai suka hau kallon-kallo ita da mata da yara, Inna ta rasa abin cewa. Don kuwa iyaka rikicewa tayi. Tana cikin wannan yanayi sai ga Juwairah ta shiga gidan hannu rike da kwanukan abinci data dafa zata kaiwa Inna din. Inna tace, "yauwa diyar nan, zo kiji min wani lamari! Wai matar Auwalu ce tazo daga Kano!" Ga mamakinta sai taga Juwairah din ko dar bata yi ba. Ta zauna a gefenta tace, "to! Kwarai kuwa ya taba fada min cewa yayi aure a Kano matar har ta haihu. Lallai shekara kwana ga mai yawan rai! Kinga yara sun girma tubarkallah!!" Inna tace, "yanzu kin san da hakan shine baki taba fada min ba?" Ita kuma mata kallonsu take yi cike da mamaki, ta kasa boyewa dai ta daga baki ta tambayesu, "wai ko kanwar Auwalu ce wannan?" Juwairah sai tayi dan murmushi kawai, bata yi mamaki ba da Auwalun bai sanar da ita yana da mata ba sam. A halayen Auwalu ai kalilan ne bata sani ba. Inna ta kada baki tace, "kanwar ina? Matarshi dai. Ai ita ce matarshi ta lalle!" Ta dinga kallonta da mamaki zane akan fuskarta. Don kuwa ko ba a fada ba to ta girmi Juwairah din nesa ba kusa ba. Tana nan sai ga Auwalun ya shigo bararam-bararam, karin hula a gefen kunne. Kafafunshi furtutu kamar wanda aka tono daga rami. Yana ganin wadda ke zaune a tsakar gidan sai yayi turus, ya hau share zufa. Ita kuwa wani murmushin takaici tayi, ta kalli Inna tace, "dama Inna ba wani abu bane ya kawoni face in zo in nuna miki yan jikokinki ki gansu. Tunda shi Uban nasu yaki sadasu da ku balle ku san juna!" Inna ta hau gyada kai, "kwarai kuwa yar nan, kinyi kyan kai! Kin kyauta sosai wallahi, Allah Ya shi albarka!" Ta kama hannun yaran tana kokarin jan su da hira. A gefe guda kuma aka dinga kallon-kallo tsakanin Auwalu da Juwairah da Barira dake ta watsa mishi wani kaskantaccen kallo. Zuwa can kuma ganin ya coge a bakin kofa yana ta muzurai ya kasa cewa komi yasa ta tashi tsaye ta kama hannun yara, ta cewa Inna, "to Inna zamu koma. Dama zuwa muka yi mu ga gida, ku ganmu mu ganku muma. Amma in Allah Ya yarda zamu dinga zagayowa ana gaisawa." Inna ta rasa abin dauka ta basu, sai yan abubuwan tabawa da ba a rasa tsofi dasu ta basu. Suka yi sallama ta kama hannun yaranta suka wuce. Da suka je gaban Auwalu, ta watsa mishi wani mummunan kallo taja tsaki ta zagayeshi ta wuce. Kamar wanda aka dankare a tsaye, har suka fita ya kasa yin wani motsin kirki. Inna ta kalleshi tana girgiza kai, tace, "ban san me kake so ka zama ba Auwalu, amma wannan dai ba hali bane na kwarai wallahi. Allah Ya shiryeka Ya dawo da kai kan hanya." Ta tashi ta shige uwar daka. Juwairah ma kuwa bata ce mishi komi ba ta tashi ta hau yan ayyuka a tsakar gidan don ma kada ya nemeta da wata magana. Ya gaji da tsayuwarshi ya lallaba ya fita. Washegari asubahin fari ya yiwa Kano tsinke. Sai dai duk yadda yaso ya shawo kan Barira ta riga tayi fushi sosai. Ta ma ki bashi fuskar yin magana. A takaice dai ba a yi sati ba sai daya rubuta mata takardar saki. 'Ya'ya kuma tace ba zata bashi ba ya kai mata su gidanshi. Daya so nuna mata jan ido sai ta mishi duniyanci itama, ta nuna mishi akan wannan maganar zasu iya zuwa har kotun koli don kuwa ba zata yarda ba. Idan kuma ya matsa to wallahi zata iya sanyawa a batar mata dashi. A haka dai suka yi sasanci, da cewar zai dinga aika musu duk abinda zai iya duk karshen wata. Ya koma ya sanar dasu Inna wannan labari. Duk da basu ji dadin hakan ba, sai suka yi addu'ar Allah Yasa hakan shi yafi alkhairi. To kuma sai gashi ko wata ba a rufa da yin wannan zance ba ya kara babbako wani zancen auren a Maiduguri. Kuma yake zancen ba zai hadasu gida daya da Juwairah ba. Abin daya konawa Inna rai kenan. 10. Sai ta wayar Auwalu suka samu daga can Maidugurin aka kira Zahra aka sanar da ita halin da ake ciki, hankalinta yayi kololuwar tashi, babu bata lokaci ta tafi Maiduguri. Lokacin watansu daya da yan satika da yin auren. Halin data sameshi ya matukar tayar mata da hankali kwarai. Yana nan a kwance sai dai a kwantar a tayar, baya 'Uhm' baya 'uhm uhm!' sai dai ya bi mutane da kallo. Gabadayan Iyalinshi babu mai nutsuwa a tattare da shi. A sati biyun da tayi anan babu wani canji da aka samu na azo a gani. Takurawar da Auwalu yayi akan ta koma gida da kuma yadda Dada Iyani itama take mata korafin ta koma dakinta hakanan, yasa ta hakura ta tafi din ba don ranta ya so ba. Ta koma suka cigaba da gudanar da soyayyarsu ita da Auwalu, lokaci zuwa lokaci kuma tana kiran gida su gaisa ta kuma ji yadda jikin Lamin yake. Ana nan sai ta fara laulaye-laulayen ciki. Hankalin Auwalu kacokam sai ya koma kanta kamar a kanta aka fara mishi haihuwa. Kulawa da dadi na duniya babu wanda bai jiyar da ita ba. Kai gabadaya ma sai daya kwashe fiye da wata daya bai je wajen aikin nashi a Kano ba. Tsakaninshi da Juwairah da 'ya'yan dake gabanta sai dai ya leka a tsaitsaye ya bata abinda ya sawwaka na cefane ita da Inna Deluwa, ya kara gaba. Ita kam tuni ta dawo daga rakiyarshi, tun tana fadan abinda yake kai musu na cefane din baya isarsu, har dai tayi hakuri ta sallama. Allah Ya taimaketa tana sana'o'inta iri-iri, ba a zaune take ba. Don haka ko da wani abu da ake bukata ita take yiwa kanta. Don kuwa ko su Saminu da AbdulHadi da kaninsu Tanimu dan wata Bafulatana daya aura ta kai mishi dan bayan sun rabu, ya daukesu ya kai almajirci can Jama'are bai kuma kara bi ta kansu ba sai in sun je gidan ya gansu, ita take dawainiya dasu. Duk sanda za a kira a nemi wani abu, mawuyaci ne ya dauka ya bada sai ita ce mai badawa. Daga karshe ma ta roki Malamin nasu daya sanyasu a makarantar boko, kuma ita take musu bukatun makarantar tunda ta gwamnati ce. Bata ma tunanin yasan da zancen suna makarantar, idan kuwa ya sani to bai taba fada mata ba. Ita fa gabadaya komi nashi ya fita a kanta sam. Kawai dai tana zaune dashi ne don bata da wani zabi wanda yafi haka. A kwana a tashi, Zahra ta fara warwarewa daga laulayin da take yi. Jikinta yayi kyau yayi luwai hankalinta a kwance yake, bata da wata matsala sai ta rashin lafiyar mahaifinta da kullum jikinshi ke kara hautsinewa. Da take ta samu Auwalun ya bata jacen wayar salular hannunshi. Wani lokaci da suka je taron nadin sarautar wani hakimi da aka yi a Zaria, aka ba manya-manyan na hannun damar Gwamna kyautar salulolin a kwalinsu, ciki har da Auwalun. Ta samu da wayo da kissa ya bata tsohuwar tashi ya hada mata sabon layi, don haka kusan kullum akan waya take tana gaisawa da yan'uwa. Cikin ikon Allah cikinta ya shiga watanshi na shida, aka aika musu da mummunan sakon rasuwar Alhaji Lamin a wata safiyar ranar Talata. Tashin hankali wanda ba a sa mishi rana! Suka kwasa gabadaya har Auwalun suka tafi Maiduguri. Rasuwar tashi ta girgiza iyalinshi da ma al'umma da dama, duk da cewa ya dade yana jinya amma dai babu wanda yake bashi rasuwa. To dama rayuwa da mutuwa duk suna hannun Allah ai, idan kuma Yaso kaje gareShi, ko da ciwo ko babu sai kaje. Aka yi zaman makoki aka watse, aka bar Iyani da zaman takaba. Itama Zahra satinta uku ta koma. Duk da cewa taso ta yi zamanta anan har ta haihu don ta dinga debewa Iyani kewa, amma Auwalu ya nuna sam bai yarda da wannan zancen ba. Don haka ta tattara ba don rai yaso ba ta tafi. Zancen rabon gado kuwa babu shi, don kuwa babu wani abu daya bari sai ma bashi da kudaden mutane dake kanshi. Don haka ne ma aka yanke shawarar a sayar da gidan da suke ciki tunda yana da girma sosai, sai a samu madaidaici a saya, in yaso sauran kudaden sai ayi biyan bashin dasu. Zahra ta koma Kaduna da niyar su sake sabunta kauna da soyayyar da aka jima ana cin bashinta. Sai dai abin sai yaje mata ba a yadda tayi tsammani ba. Don kuwa a bakin mutanen unguwa ta dinga jin wai Auwalunta aure zai kara, kuma

Chapter 6 of 36