ita yana mata wasu abubuwa yasa tayi baya tana kare jikinta da sai lokacin ta fahimci ashe babu kaya a jiki.
Ya kai hannu yana kokarin kamota, ta fashe da kuka tun karfinta. Ita ta ma rasa ta yadda aka yi har ya bude dakin nata ya shiga.
Tace, "kasan Allah ka tashi ka fita ka kyaleni. Haba wannan wane irin abu ne haka? Ba za a bar mutum ya huta bane?"
Kallonta yake yi kasa-kasa, "Nadiya dama akwai hutu a cikin rayuwar aure ne?"
Tace, "ban sani ba! Ni dai wallahi ko ka fitar min anan, ko ni in fita. Amma wallahi ba zan iya ba!"
Ganin yadda ta hakikance tana kuka bilhakki, yasa ya dauki kayanta ya mika mata, yace, "to naji, shikenan. Yi hakuri ki daina kukan."
Ta amsa cikin sauri ta sanya, ta tsaya tana kallonshi cikin alamun rashin yarda.
Ya kwanta tare da tapping din kusa da shi, yace, "taho ki kwanta kin ji? I promise babu abinda zan miki. For now."
Duk da haka dai kasa yarda dashi tayi din. Shi kuwa ganin haka sai ya juya mata baya yayi kwanciyarshi.
Ita kam sai da ta jima sosai a hakan, ta tabbatar da yayi barcin sannan ta silala kamar barauniya ta kwanta. Gunaguni take yi kasa-kasa, duk bata san lamo yayi mata ba sai da Asubahi tayi yaje yayi sallah ya dawo. Yayi ram da ita yana neman sake maimaita yar gidan jiya. Ta hau magiya da rokon ya daga mata kafa, yace, "a'ah, ba kin ce na dameki da kwarzaba da bita zaizai ba? Ai baki ga komi ba ma Nadiya, don kuwa ko farawa ma ban yi ba."
Tace, "to kayi hakuri ka bari in gama warkewa tukun. Wallahi bana jin dadi ko kadan."
Yace mata, "muna da magunguna ai a gidan."
Bai kuma kara barin ta furta wani abu ba sai daya karasa gudanar da abinda ya kudurta sannan.
32.
Cikin yan kwanakin amarcinsu suke ci ka-in da na-in, ko kuwa tace Habibu amarcinshi yake ci babu kakkautawa. Don kuwa tana ganin kwarzaba da bita-zai-zai din da yace mata zata gani, sai daya zamana har bata son girkinta ya juyo kanta ko kadan. Idan kuwa ta ganshi har wani faduwar gaba take ji tana ziyartarta.
Babu yadda baya yi da ita akan ta saki jiki, amma wannan din ya gagareta.
Wannan sabon kusancin da suka yi yasa ta kara fahimtar ainihin wanene Habibu Abdullahi Makama, Babangidan Hajiya Ummah.
Bawa ne ga duk abinda yake so da kauna, mai fahimta ga abinda baya ma kauna. Yana da kyautatawa da son kyauta ba kuma don a gani a yaba ba. Ga matanshi da Iyalanshi, mutum ne mai taka-tsantsan da gudun bacin ransu. Mutum ne mai saka alkhairi da alkhairi, sharri ma a wajen Habibu da alkhairin yake maidashi. Bakin kokarinshi yana yi don ganin ya kyautata musu, yana musu uziri a duk al'amuransu, haka yana da fahimta. Lokuta da dama idan suna tare da Nadiya ya kan maida kanshi kamar wani karamin yaro ne ko matashi, baya da girman kai kuma baya cikin mutane masu amfani da ikon dake kansu don su hanawa matansu motsin kirki. Abu daya da Nadiya ta fahimta a tare da shi shine wannan abu daya da bata so, zai iya hakuri akan komi ma, zai kuma yi uziri da fahimta, amma fa yau yace mata zo gyara shimfida tace a'a, anan ne kam take ganin rashin uziri da fahimta. Don kuwa baya mata wannan hakurin.
Shi yasa ma wani lokacin sauran kawaicin nashi baya burgeta.
Haka tsananin biyayyar da yake yiwa Ummah wani lokacin har tsoro take bawa Nadiya, saboda baya taba iya ce mata a'ah a duk wani umarni da zata bashi. Haka yana matukar kambama abubuwanta da yin taka tsantsan wajen gudun bacin ranta. Tana lura da yadda yake ta boye-boye da kokarin kada abinda ke tsakaninsu ya bayyana a wajen Ummah din. Saboda da aka kwana biyu ma sai ya zamana baya shiga bangarenta ranar girkinta sai can cikin dare ko kuma tunda Asubahi. Sai dai a ranta tasan da kyar idan Ummah bata gama ramfoshi ba a yadda dai idanunta suke a kansu a kodayaushe kamar wata mikiya.
Tun karon farko daya fita daga dakin Shukurah ya koma nata, ya sameta da rana a bangarenta da zancen ta bashi abincin rana. Ta kalli plate kwaya daya tal da ta yi roasted macaroni don ta ci, tace mishi bata dafa da shi ba.
Ya dauke plate din tana kallonshi ya tadashi a gabanta, ya gama ya kora da ruwa ya tashi tana kallonta, yace, "banda ma rashin kara irin naki, ranar girkin naki ma sai na dinga rokonki da barar kiyi mun abinci kenan? Idan kin ga dama ma gobe kada ki sa girkin da ni!" ya fita ya barta anan.
Tun daga nan ita kuma ta kan zauna ta tsara girki mai rai da lafiya ta ajiye mishi ranar girkinta da rana.
Daya dauko hanyar ranar girkin Shukurah ya je da rana yace wai ta bashi abinci, sai tayi saurin taka mishi burki tun kafin hakan ya kai ga kara janyo mata bakin jini a wajen Ummahn da Shukurah. Don kuwa ta kula hatta da abincin ranar da yake ci a bangarenta su dukansu ba son hakan suke yi ba.
Wani hali nashi dake kara burgeta shine yadda baya da halayyar korafin wata a wajen wata. Duk yadda Shukurah zata bata mishi rai, koda wasa bai taba yiwa Nadiya korafin hakan a wajenta ba. Hasalima kullum kokarin boye wata baraka ko matsala dake faruwa a tsakaninsu da Shukurah din yake yi. Hakan ita kuma sai yake kwantar mata da hankali, tunda tasan ba zai taba kai maganarta wajen abokiyar zamanta ba.
A haka kuma sai ta fahimci wani abu, zama a matsayin matar Habibu abu ne mai dadi da kuma wahala a lokaci daya.
Dadi saboda duk macen data samu miji kamar Habibu dai, to ta huta. Mutum ne mai saukin kai da tarin alkhairori, haka kuma yana matukar kokari wajen sauke nauyin iyalinshi daya rataya a kanshi.
Wuyarshi kuma shine ba kowace mace bace zata iya hakurin barin wadannan halaye nashi ya dinga rabasu a tsakaninshi da wata ba. A bangarensu kam, har Ummah ta shiga ciki. Tunda kuwa babu abinda yake zartarwa ba tare da hukuncinta ba. A gefen Nadiya kuma, ta kula Ummah din duk wani kokari nata, to shine na ganin bai kyautatawa Nadiya ba. Wadannan abubuwa dama wasu, suka sa dole sai data kara koyawa ranta hakuri da kawaici da kawar da kai akan wasu al'amuran. Saboda tasan idan tace akan komi sai tayi magana, ba lallai hakan ya haifar musu da da mai ido ba.
Ta cinye wata guda a hakan, tana so taje gida ta gaidasu amma fir hakan ya ki ya yiwu. Duk lokacin da tace tana so taje gida sai yace mata ta dan dakata, ba zai kara yi mata maganar ba kuma sai ta sake mishi. Daga baya ta gano umarnin Hajiya Ummah yake jira, don kuwa ta taba tsintar hirar tasu bisa kuskure inda taji Ummah din na mitar, 'ita Nadiya din me zata je yi ne a gidan nasu yanzu? Me ake yi? Ita fa bata son yawace-yawace marasa kan gado!'
Taga wani irin yawo ne a cikin zuwa ganin danginka? Tunda ga Shukurah nan ita ba zaman gidan take yi ba, babu ruwanta ma ita fita sai ta gama shirinta sannan take sanar da ita. Akwai lokuta da dama ma sai dai kawai ta fadawa Ummah din zata fita, Nadiya bata tunanin tana fadawa Habibun, amma da wasa bata taba jin Ummah tayi mata fadan yawo ba. Sai ita? Akan wane dalili? Me tayi mata? Don haka ta bar maganar fita ta hakura.
Iyaka tunani ita dai tayi akan ta gano menene wai ta yiwa Hajiya Ummah haka? Amma ta kasa gano dalili. Don haka sai ta kudirci wata aniya a ranta, ita zata kyautata, ba zata gaji ba kuma har sai ta ga abinda ya turewa buzu nadi. Hajiya Ummah za tayi ta shareta da kokarin hanata rabar jikinta, amma ba zata bata wannan damar ba.
Kullum idan tayi abincin rana to sai ta sanya da Hajiya Ummah ta kai mata nata, bata taba tsayawa ta ga ta ci ko bata ci ba, ita dai aikinta ta hada girki mai kyau mai cike da ganyayyaki na karin lafiya, hadin abinci kuma ya zamana irin wadannan tsofi zasu ji dadinshi ne sosai.
Haka kuma idan taje sashen nata ta kan yi mata gyare-gyare da goge-gogen falo da falon sama duk da cewa akwai masu yi, kuma itama Ummah din tana hanata amma bata bari ba.
Yau ba ita ke da girki ba. Zaman kadaici ya fara isarta da takurata, kwarai take bukatar fita ko yaya ne ko don ta samu ta ga gari. Bata saba zama a gida har haka ba, musamman wajen da idan ba kai kaso ganin mutane ba zaka iya share sati ma ko fi baka ga wani yaje inda kake ba.
Ta fito cikin doguwar rigar atamfa anyi mata freestyle, ta yafa dan karami gyale a kanta. Sashen Hajiya Ummah ta wuce kai tsaye, so take yi ta ji ko tana da wani abu da take bukatar ayi mata. Ta kudiri niyar idan ta samu Habibun zata tambayeshi izinin ya barta da yamma ta dan zaga koda cikin unguwar ne kawai ko gidajen makotansu ko ta dan warware daga yanayin kadaici da take ji yana ratsata.
Ta samu Hajiya Ummah din da Lailah a kicin, da alamu tsarin wani abu ne suke yi don ga takarda nan da biro a gabansu suna yin list.
Ta duka ta gaidata, ta amsa hankalinta gabadaya akan lissafin da take yi, itama Lailah ta gaisheta ta amsa. Sau tari anan wajen Lailah din take zuwa su sha hira abinsu, saboda ta kula yarinyar bata da rawar kai. Abinda ya kaita gidan shi kawai take yi, ba kamar sauran yan aikin gidan ba data kula kusan dukansu hadiman Shukurah ne. Duk wani motsi nata suna kula dashi ta kuma san suna kai mata rahoto, don haka take taka tsantsan a gabansu.
Ta tsaya bata tafi ba tana tsintar maganganun da suke yi jifa-jifa, daga karshe dai ta fahimci cewa Ummah din baki ne zata yi daga Riyadh, Saudi Arabia. Ita kuma Lailah za tayi musu girki ne na tararsu.
Sai ta matsa kusa da ita, tace, "aikuwa Ummah na iya Arabian girki sosai, idan babu damuwa ki bari inyi ko kuma in taya Lailah muyi tare."
Ta kalleta a nutse tace, "kin tabbata?"
Ta gyada kai da sauri tana dan murmushi, "sosai ma. Ai ina yawan yin girke-girkensu. Saboda kafin in bar wajen aikina ma ai da muna tunanin gabatar da daya daga cikin abincinsu da yayi shura ne a wajen, kuma nima shi nafi iyawa."
Ummah ta kalli Lailah, ta juya tana kara kallon takardar gabanta cikin dogon tunani, sai kuma ta gyada kai, tace, "to tunda hakane, sai ku hadu din kuyi saboda dama Lailah tace bata kware ba a harkar girke-girkensu. Bakine zamu yi masu muhimmanci Nadiya, kada ki dauki aikin da ba zaki iya ba fa!"
Tace, "in shaa Allah Ummah zan iya, babu matsala!"
Ta gyada kai, "ok. Tunda hakane, ga Lailah nan ki rubuta abubuwan da zaki bukata duka, a duba wadanda muke da su anan, wadanda babu sai ta fita ta sayo. Gobe zasu zo, don haka a tanadi komi yau. Kin gane?"
Tace, "to Ummah!"
Ta fita ta basu waje, ita kuma ta nemi waje ta zauna suka hau sabon list. Yinin ranar hankalinta sai ya karkata gun irin abincin da zata yi, duk suka hada komi a ranar kamar yadda Ummah din tace. Bata koma sashenta ba sai can bayan isha'i, hakan sai ya yaye mata kadaicin data jima tana yawo dashi a ranta.
Washegari kuwa tunda safe taje suka hau dafe-dafe. Ba su suka gama komi ba sai can wajen karfe uku na yamma, ta koma sashenta domin tayi wanka. Tana jin lokacin da bakin Hajiya Ummah din suka karasa, amma bata yi gigin zuwa ba sai ta zauna a sashenta. Gudun ruwansu take so ta gani.
Zuwa can wajen karfe biyar da rabi sai ga Lailah taje tace mata Ummah ce tace taje su gaisa da bakinta. Dama a shiryenta take tsaf cikin wani maroon din swiss lace, ta yafa gyalenta ta zura takalmi ta bi bayan Lailah.
Bakin na Hajiya Ummah mata biyu ne manya, zasu iya yin sa'annin Hajiya Ummah din, sai wata matashiya da zata iya girmar Nadiya da yan shekaru.
Ta duka ta gaishesu cikin dan larabcin data iya, tunda babu laifi ta iya gaishe-gaishen Larabci. Ga mamakinta Hajiya Ummah ce take tadata a inda ta karkare, sai taji ita larabcin take yi sosai kamar dama can yarenta ne.
Take ce mata sun ci abincin nan sosai sun kuma yaba, saboda daya a cikinsu ma cewa tayi wai yafi wanda suke ci a can dadi. Shine tace bari ta kira wadda ta musu girkin su ganta. Tayi kasa da kanta tana dan murmushi cikin jin dadin hakan. Ko babu komi Ummah ta bata mutuncin daya dace da ita, ayi acknowledging abinda kayi na bajinta ba tare da boye-boye ba ai abin dadine. Ba kamar yadda Madam ta taba yi mata ba.
Ta zauna anan har bayan isha'i kafin aka raka bakin Hajiya Ummah bangaren baki suka kwanta.
Kwanansu biyu a gidan, Nadiya kuma bata gajiya wajen dawainiyarsu ba ta bangaren abinci da abubuwan sha dana motsa baki. Hakan kadai sai daya kara kankaro mata mutunci sosai a wajen Habibu, bata san ta bangaren Hajiya Ummah ba dai.
Da bakin zasu tafi suka yiwa Nadiya kyauta ta musamman, kudi suka bata masu yawa, daloli na kasar America. Wadanda idan aka canzasu ba kananun kudi bane. Koda ta nunawa Hajiya Ummah sai tace ai nata ne. Me zata mata da su? Ta sake yin godiya sosai, amma data tashi sai ta raba kudin biyu ta ba Lailah. Tunda itama tana tayata a wasu abubuwan a kokarinta na son ganin itama hannunta ya fada a girkin.
Wai hakan kuma sai ya bakanta ran Shukurah, har sai da taso tayar da rigima. Wai akan wane dalili aka zabi Nadiya? Ita yanzu kenan nema ake a mayarta saniyar ware? Ana so a nuna mata karfin yan'uwantaka kenan?
Ta yiwa Habibun korafin haka lokacin suna kan dinning da dare suna cin abinci. Tun tana maganganunta bai tankata ba har dai ya kai ga ajiye cokalin da yake tsakurar abinci dashi tana kallonta. Wasa-wasa girkin Nadiya ya fara shagwabar da shi, ya sanyashi fara raina duk wani abu da zai kai cikin bakinshi matukar ba ita ta girka ba.
Ya ambaci sunanta a kausashe kafin yace, "yanzu me kike so ayi akai kenan?"
Ta tabe baki, "oho! Ni ai ina fada maka ne don kasan matakin da zaka dauka ko? A matsayina na babba kuma wadda tazo ta tarar a gidannan, ai ya cancanci ace duk wani abu da zai faru a gidannan ni ce zan fara sani. Kuma koda ma bakin ne zasu zo, ai kamata yayi ace ni ce ke da masaukinsu. Lailah wannan da kake gani shahararriyar chef ce, matar tsohon shugaban kasa ma daya sauka ita take mata girki kafin ta dawo nan gidan. Don haka ban ga abinda za a gwada mata ba a fannin girki na kowace kasa ma balle kasashen larabawa. Amma don daurewa karya wani gu, shine za ayi mun danwaken zagaye wai ace Lailah bata iya girki ba?"
Ya gyara zama da kyau yana kallonta, "ke me yasa ba zaki tsaya da kanki kiyi girkin ba sai dai ki sanya wata? Kin fara fahimtar bambancin naku tun yanzu?"
Ta tsaya tana kallonshi, "ok! Yanzu goyon bayanta ma kake yi kenan? Ina maka korafi amma kana fada min wai bambancin dake tsakanina da ita? Kaga tun anan ma ka gama nuna min kaima kalar naka rashin adalcin ko?"
Dai-dai lokacin Hajiya Ummah ta karaso wajen da Ammar yana binta a baya. Ya daga baki zai bata amsa sai ga zuwan Ummah din, sai yace mata, "yauwa, ki tambayi Ummah sai ta fada miki dalili ko?"
Ummah tace, "dalilin me?"
Daya fada mata abinda ke faruwa, Ummah baki ta tabe, ta harari Shukurah da itama take turo baki saboda tasan fada ne zata sha a wajenta. Tunda ita ta fara yiwa korafin amma tace mata ta bar maganar.
Tace, "wai ke a wajenki magana bata mutuwa ne Shukurah? Ba a isa ace miki ki bar magana ba ki bari? Sai kije kiyi tayi ai, ni dai ko fitar ni daga cikin wannan maganar!"
Ta tashi ma ta bar musu teburin gabadaya.
Amma duk da haka dai maganar bata mutu ba a wajen Shukurah.
33.
Sai da tayi kwana hamsin a gidan sannan Ummah ta yarda taje ganin gida. Ranar dai murna a wajen Nadiya kamar tayi me, shi gogan daya bata albishir sai gefe ya koma yana kallonta yana sakin murmushin yadda take ta shigi da ficin laluben kayan da zata sanya. Tayi kewarsu Mama fiye da misali, su kansu yaran gidan tun bayan da aka kaita sau biyu kadai suka koma. Tasan kuma babu mamaki Mama ce zata hanasu zuwa saboda kada ace sun cika zarya.
Tayi shirinta tsaf, Habibun da kanshi ya kaita gidan nasu tare da Ammar data bukaci a bata shi ya mata rakiya tunda babu makaranta ranar.
Gida ya kacame da iface-ifacen murnar ganin Nadiya. Fadar irin murnar da Mama tayi ma ba karama bace, duk inda Nadiya din ta juya idanunta na kanta tana dan murmushi cike da jindadin yadda alamun hutu da jindadi suka bayyana a jikinta.
Ta samu Amarya bata nan taje duba kaninta da bashi da lafiya. Ta bi su Salame da Lantana har dakunansu ta gaidasu. Sai taga alamun duk sunyi sanyi a jikinsu, ko kuwa don ta kwana biyu bata ji duriyarsu bane yasa? Ta koma dakin Mama ta bude jakar tsaraba da tayo musu a hanya, tarkacen su sabulan wanka ne dana wanki, yara kuma alewowi da biskits da cakuleti. Haka duk ta bi ta raba musu, har su Salame dinma sai da aka kaiwa sabulai.
Ranar ta yini a gaban Mama tana ta tattalinta, duk abinda ta kai hannu ta dauko na ci, ta mikawa Nadiya. Ita kam ranar ranta wasai.
Tana nan har dare da Abba ya dawo. Taje suka gaisa tare da yi mishi sallama, saboda yana ta shirye-shiryen tafiyarshi aikin Hajji wanda za a fara kwasar mahajjata nan ba da jimawa ba.
Suka gaisa dashi yana tambayarta mai gidanta da iyayenshi, ta amsa mishi suna nan lafiya lau. Ya kara da yi mata nasihar zaman lafiya da bin miji sau da kafa, kafin ta yi sallama da yan gidan baki daya suka tafi saboda direban da aka aika ya dauketa ya karasa. Ta koma gidan Hajiya Ummah rayuwa ta cigaba da tafiya a haka.
*
Watanni suka shiga suka shude. Nadiya ta kasa gama fahimtar wata irin rayuwar aure take yi. Ta kasa gano kan matsalar dake tsakaninta da Ummah wadda take kamar Uwa ce ga mijinta. Balle tasan irin takun da zata yi da ita.
Hajiya Ummah baudaddiyar macece mai wani irin baudadden hali da daga ita sai Allahn daya halicceta suka san iyakarshi. Abu daya data gama fahimta da ita shine cewa tana da riko, kuma fushinta baya da iyaka ko kadan. Idan mutum ya kuskura tayi fushi da shi, to akwai matsala.
Habibu ya fara fita zuwa yawon kamfen dinshi, zaben da ake sa mishi rai nan da abinda bai gaza shekara ba. Wannan dalili yasa gabadayanshi yayi wahalar gani, ko ta waya bai cika samuwa ba. Saboda tafiye-tafiyen nashi wani lokacin har kwana suke sanyawa yayi ko fi, ko kuma idan ya fita tun safe sau tari sai cikin dare yake komawa.
Ta gefen Hajiya Ummah da Shukurah su ma suna tayashi nasu kalar kamfen din. Ita kanta Shukurah din tana yawan fita kamfen din ko ma ta bi bayanshi a matsayinta na matarshi. Da rana daya basu taba sanya Nadiya a cikin sabgar su ba, itama da taga haka sai ta koma gefe tana kallonsu. Bata taba musu magana ba, kuma bata taba nuna musu sha'awar tana son zuwan ba. Tana jin Shukurah watarana tana waya tana fadawa wanda suke wayar mutanen data tanada wadanda zata yi aiki da su idan ta shiga ofishinta na Matar Gwamna. Tana ta daga murya da hayagaga da sakin habaici duk don Nadiya ta ji ta ne wadda a lokacin tana falon a zaune tana chatting da Anty Lima wadda bikinta yake ta matsowa. Tayi banza ta kyaleta ta nuna kamar bata ji abinda take cewa ba. Harkar siyasar Habibu ta kula idan ma tace zata sanya abun a ranta, ita za a dinga bari da bacin rai.
Akan wannan maganar har sai da Madam ta kirata wata rana cike da bacin rai, take tambayarta 'wai me yasa bata taba ganinta a kafar yada labarai ko daya ba game da siyasar Habibu? Me yasa har yanzu babu wanda ya santa a matsayin matar Habibu?'
Nadiya tace mata, "to Mommy tunda ba a gayyaceni ba ba sai in kama kaina ba kada in sayowa kaina cin mutunci da kaina?"
Madam din cike da mamaki take tambayarta, "yanzu ita Hajiya Ummah din ce bata taba sanyaki cikin harkokin siyasarsu ba?"
Nadiya tace, "basu taba ba Mommy. Don haka kema da kin kyalesu, kada ki musu magana don Allah!"
Madam sai ta hau fada, tace, "ashe ma ke baki da hankali Nadiya? A tunaninki wai duk don saboda wa nake wannan hakilon ne? Ba don ke bane?! Kuma sai a zo ace wai an wareki a harkar wannan? To ni duk bautar da nake yi a yaya take kenan? Ai wallahi ba zata sabu ba! Idan aka hau mulkin wannan a haka ai ban ga abinda auren naku zai tsinana min ba!" Ta kashe wayar tana cigaba da fadanta.
Bata san ko ya suka kwashe da Hajiya Ummah ba, ta dai ga Madam bata kara yi mata zancen ba, don haka itama sai ta watsar da maganar.
Ranar wata Laraba tunda safe sai ga kiran Rashida, take fada mata tana nan hanya yau. Nadiya tayi murnar jin hakan sosai, saboda wasa-wasa tayi kewar Rashida kwarai da gaske.
Ta taba yiwa Habibu maganar sau daya watarana da taga yana cikin nishadi, take ce mishi tana son zuwa ta ga Rashida, yakamata dai ranar da yake free ya kaita ita da Ammar su gansu. Yayi shiru kamar bai ji ta ba, daga karshe ya basar da zancen. Fahimtar da tayi cewa baya son zancen yasa sai bata sake yi mishi ba itama.
Duk da cewa ranar ba girkinta bane, sai ta shiga kicin a bangaren Hajiya Ummah da kanta ita da Lailah suka yi girki ranar.
Rashida din bata karasa gidan ba sai bayan la'asar, da taje kuma sai Nadiya taga ashe ba ita kadai bace. Tare suke da wata dattijuwar mata, wadda ko ba a fada ba kasan cewa mahaifiyarsu ce. Saboda kamarta da Habibu har ta baci.
A falon Hajiya Ummah taje ta samesu, ta zube har kasa tana gaishe da ita cike da girmamawa. Girmanta da nauyinta suka kamata a take, ta rasa wace irin tarba zata mata? Nan da nan sai ta hau fito da kayan abinci daga kicin da lemuka tana shiryawa akan dinning.
Jikinta sai yayi sanyi lakwas ganin irin tarbar da Hajiya Ummah tayi mata. Ta sauko daga kan bene tana takunta daya bisa daya, ta nemi kujera ta zauna a hakimce, Rashida na gaisheta tana amsawa da kyar. Hajiya Hadiza, wadda Nadiya taji Rashida na kira da Yakumbo, ita ta dinga gaishe da Hajiya Ummah. Ita dinma cike da wata irin ginshira ta dinga amsawa, babu ya hanya ko ya bayan rabuwa ko tayi kokarin jan ta da hira, sai kiraye-kirayen de waya data hau yi. Zuwa can kuma sai ta kalli Nadiya tana tambayarta wai an kaiwa baki ruwa? Ita data coge a kusa da teburin cin abinci tana kallon wannan abin mamaki sai lokacin ta iya motsawar kirki. Ta matsa tana yiwa Yakumbo tayin abincin da ta gama shirya musu.
Tayi murmushinta mai cike da kamala da rashin jin haushin abinda Hajiya Ummah din tayi mata, ta cewa Nadiya, "Alhamdulillah, a koshe muke wallahi. Rasuwa aka yi cikin family dinmu muka zo gaisuwa, shine nace Rashida ta rakoni in ga matar Habibu. Har anyi biki an gama bamu samu mun leko ba."
A ranta taji babu dadi sosai da wannan abu dake faruwa, amma sai bata nuna hakan a fuskarta ba. Ta dauko lemuka da snacks ta kai mata, ta koma kusa da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 36