a basu."
Maryam tace, "wallahi sauran abincin kenan dama na ki ne ya rage, sai na Abba. An zuba musu tun dazu sun cinye!"
Taga yanayinsu dai su duka taga babu alamun sun koshi, ita kanta Nadiyar yunwar take ji saboda ko da rana bata tsaya ta ci abincin ba sosai.
Don haka ta bada aka sayo musu shayi da biredi suka kara da shi.
Tayi tunanin idan Abba ya dawo su Basira din sun gaisa, tafiya zata yi kamar yadda ta saba. Sai taga da yazo ma Basirar bata je ta gaisheshi ba. Yaran ma bata bari sun fita wajenshi ba. Sai tasan ba lafiya ba.
Wannan shine karo na kusan barkatai da Basira din tayi yaji ta je gidansu, a wannan tsakankanin kuma mijinta ya saketa har sau biyu.
Ta tambayeta, 'yau kuma lafiya?'
Ta bude baki tace, "yaji na yi!"
Nadiya ta kama baki, tace, "yanzu yaji kuma saboda Allah da Annabi? Me ya faru ne?"
Tace, "menene ma bai faru ba? Aure idan mata tana ciyar da kanta da 'ya'yanta ai babu shi, don ban ga abin yi ba a gidan da miji ba zai fita ya nema ya kawo min ba. Sai dai idan ni na samu in ciyar damu. Sakina ma zai yi wallahi, Mali zan tafi neman kudi!"
Nadiya ta dafe baki cikin mamaki, Mama kuwa ta hau sallalami da salati. Tace, "ke yar nan! Yaran kuma kiyi yaya da su?"
Tace, "yo in barsu wajen ubansu mana tunda ba dasu naje gidan ba! Yau ma don nasan idan yaga yaran ba lallai ya biyoni ba, ai da wallahi a can zan baro su. Amma yanzu daya bani takardata, kayan dakina zan sayar inyi tafiyata sai in kai mishi yaranshi!"
Mama ta sanya musu baki, tace, "a'ah fa Basira! Ita rayuwa da kike gani fa yar a bi ta a hankali ce. Shi kuwa zaman aure dama ai ya gaji haka. Musamman ga mutum marar tsayayyen aikin yi. Dole fa sai matarshi tana hakuri, itama kuma idan da hali ta dinga taimaka mishi. Sai kiga watarana hakurin yayi mata rana!"
Ta tabe baki, tace, "ai wallahi in dai da cuta a ciki fa ba zan yi wannan hakurin ba! Zaluncin ai yayi yawa!"
Nadiya kallonsu kawai take yi, Mama tana ta kokarin tausar Basira ita kuwa tayi biris da ita.
Tasan halin Basira sarai, bata da hakuri, kuma akwai kafiyar kai idan ta yankewa kanta abu.
Ta numfasa tace, "ke ma fa Basira kina da naki kason laifin a ciki! Waye yace miki mijine kadai yake hakuri da mace ita ba zata yi da shi ba? Kin san halin mijinki sarai, ai yana da kokarin yi. Kuma lokacin da yayi miki hidima ai yayi, me yasa baki taba korafi ba sai yanzu? Ashe ke ba zaki iya zama ki rufawa mijinki asiri ba a lokacin da ba shi? Shikenan ke kullum kina tafe akan hanya yau kinyi yaji gobe kin kaso aure? Yanzu kuma kice wai kasar ma zaki bari kwata-kwata ki tafi neman kudi? Saboda rashin wadatar zuciya da rashin godiyar Allah irin naki? Sau nawa ana baki jari iye? Ina ce ko wancan watan da ya wuce Yaya AbdulHadi dubu saba'in ya tura miki ki ja jari, me kika yi da ita ne cikin abinda bai gaza wata biyu ba?!"
Budar bakinta sai cewa tayi, "yo wai kema kina ta wani tada jijiyar wuya kina fada. Me kika sani ne a cikin rayuwar auren da abinda ke cikinta? Gaskiya ki daina yi min irin wannan katsalandan din! Ki bari idan kinyi auren kin hadu da miji irin nawa kin fahimci ko me kenan. Yauwa!"
Ta saki tsaki.
Nadiya tayi wani dan murmushi dake nuna bacin ran da kalamanta suka haddasa mata.
Tace, "kwarai kuwa, ban yi aure ba Basira, ban kuma san me ke cikin rayuwar auren ba don haka Allah Ya baki hakuri da katsalandan din da na miki. Sai dai ita duniya ai ta fi bagaruwa jima, kuma ni nasan wallahi da ni ce a yanayin da kike ciki, ba zan tattara in kashe aurena ba wai in tafi duniya neman kudi. Su yaran nawa su yi yaya kenan? Tunda haka ne kuma, ki tanadi wajen zaman yin idda kin dai san Abba ba zai barki ki zauna mishi a gida ba!"
Yana daya daga cikin dokokin Abban nasu, mace in dai ya aurar da ita, to daga ranar ta bar gidanshi har abada. Shi da ita sai dai zuwa gaisuwa da yini, amma kwana ma shi bai amince ba saboda yace hidima ce suke kai mishi.
Don haka da ya fuskanci ma wai yaji kika yi ko auren ya mutu, yake rufe ido ya zabga miki rashin kirki, komi dare kuwa sai kin bar mishi gida, babu sassauci.
Sai idanun Basira kuma suka raina fata, tayi narai-narai da ido.
Tace, "yanzu ya zanyi to? Gashi Innata itama tana gida fa, yanzu idan na kwasa na tafi can abubuwan sai suyi musu yawa!"
Nadiya ta tabe baki tace, "shi yasa ai masu iya magana dama su kan ce wai a dinga sara ana duban bakin gatari!"
Ta juya tayi kwanciyarta ta kyale Basirar anan tana maida yadda aka yi.
Washegari tunda farar safiya sai ga Abbansu ya dira a kofar dakin Maman.
Dama Nadiya tasan dole sai ya san da zuwanta, tunda ko ita ta buya bata je inda yake ba ko 'yay'anta, dolene matan gidan zasu bashi labari.
Ya kankance idanu yana kallon Basira din data tsuguna tana gaida shi. Ko amsa gaisuwar bai yi ba ya hau watsa mata tambayar, 'me take yi a gidan?'
Ta karkace kai zata hau kora mishi bayani, yayi gaggawar dakatar da ita, yace, "kinga, ba dogon bayani nake nema ba, ga mijinki can ya doko min sammako ya zo nemanki da 'ya'yanshi, don haka ki kwashesu ku tafi salin alin. In ya so idan kun koma gidan sai kuyi duk wadda zaku yi dai, amma ba anan gidan ba. Kin sanni sarai, kin san bana daukar wannan rashin hankalin da hauka! Idan ma auren kika kashe daga karshe, kada ki kuskura in ga ko mai kama dake ne a kofar gidana. Don wallahi sai na sanya katako na sassake miki su, kin dai ji na fada miki!"
Ya juya fuu! ya wuce yana mai kara maimaita mata lallai nan da yan mintuna ta bar gidan.
Basira ta dora hannu aka zata kurma ihu, Nadiya tayi gaggawar dafe mata baki data hango su Salame suna lekensu ta kofar dakinta ita da Lantana.
Samu suka yi ita da Mama suka tausheta akan tayi hakuri ta bi mijinta tun kafin Abba ya tata mata rashin kirkin da yake ikirari.
Nadiya tace mata, "idan ma rashin sana'a ne matsalarki, kinga wajen aikinmu muna neman masu wanke-wanke da goge-goge, idan kina so sai a baki, tunda albashin babu laifi yana da dan kauri!"
Nan da nan kuwa sai ta hau zubda fara'a, tace, "Yo Anty Nadiya da tun wuri kika yi min wannan bayanin ai da bamu kai ga haka ba. Aiki ni ko wane irine in dai za a biyani ai wallahi ina so!"
Nadiya tace, "tun farko idan baki manta ba ai na miki zancen aikin lokacin kina cikin ganiyar jin dadin arzikin mijinki, kika ce min ke mijinki ya tsaye miki don haka baki bukata ko?"
Sai ta hau nade tabarmar kunya da bori, ta hau dariyar jin kunya, tace, "dadina da ke Anty Nadiya ba dai riko ba! Ni dai don Allah ki min kokarin aikinnan kinji? Kuma don Allah kiyi hakuri akan maganganun dana fada miki jiya, raina ne ya baci da yawa."
Nadiya tace, "ni kuwa me yasa zan yi fushi don kin fada min gaskiya? Ai gaskiya ce, ni da ba sanin rayuwar aure nayi ba meye nawa na baki shawarar yadda zaki zauna da mijinki?!"
Da haka dai ta musu sallama ta bi Mijin nata bayan Mama ta bata kayan masarufi dangin su sabulai na wanki da wanka da su omo da kayan su maggi da su daddawa, har da dora mata da dubu biyu. Haka tayi ta musu godiya ta tafi.
*****
Kamar yadda tayi alkawari kuwa, a satin daya biyo baya Basirar ta fara zuwa shagonsu. Aka bata aikin goge-goge da wanke-wanke, biya kuma mai kauri ake mata wanda Nadiya take da tabbacin zai iya rufa musu asiri a rayuwar takatsantsan.
Sati biyu da yin haka suka je Kano gidan Anty Jamilah ita da Maryam. Mijin Anty Jamilah din aka yiwa aikin koda a asibitin Murtala dake nan Kano din suka je dubashi.
Da suka je din kuma sai suka tarar ana yiwa kanwar abokiyar zaman Anty Jamilah din biki, don haka suka shiga ciki aka yi ta fafatawa da su.
Daga zuwa wajen dinner da dare, Yayan amarya ya tafi ya saukesu ita da su Rabi'ah da abokan amaryar guda biyu da aka yi musu masauki anan gidan Anty Jamilah din, sai bawan Allah Ya mannewa Nadiya.
Tun a wajen dinner din ta kula da yadda yake ta bibiyarta da kallo da magana, duk kuma yadda tayi kokarin yakiceshi wannan bawan Allah ya ki amincewa.
Sai daya samo lambar wayarta a wajen Rabi'ah, haka ko shigarsu cikin gidan ya dameta da nacin kira da tura sako, shi fa tsakaninshi da Allah sonta yake yi. Duk kuma yadda taso ta fahimtar dashi akan cewa ita dai ba wannan ne a gabanta ba, ya ki saurarenta.
Haka washegari da safe yaje gidan ya kasa ya tsare, shi fa ala dole sai taje sunyi magana. Bata yi niyyar zuwan ba kuwa sai da Anty Jamilah taje ta furtomata sannan.
Ta dauki hijabi ta dora akan doguwar rigar material dake jikinta, ta tafi ta sameshi a falon farko.
Yana ganinta ya jimke hannu alamun gaisuwa, yace, "ranki ya dade! Barka da fitowa... Takawarki lafiya Hajiya Nadiya. Ina godiya da wannan karamci da aka min na bani damar ganin wannan kyakkyawar fuska taki a wannan hantsi mai albarka!"
Duk kinta sai da tayi dan murmushi. Ta fahimci mutum ne shi mai barkwanci da ban dariya. Ko a maganganunshi zaka fahimci hakan.
Ta zauna a kujerar dake fuskantarshi tace, "wannan kirari duk ni kadai dai?"
Yace, "ai kin cancanci fiye da hakan ne ma. Idan kina so in nuna miki kuma to mu fara."
Tayi gaggawar girgiza kai, "a'ah, hakan ma nagode... Ina kwana?"
Yace, "lafiya lau. Da fatan dai kin tashi lafiya? Allah dai Yasa su Rabiah sun bar kin ke kinyi barci da kyau. Don idan ba haka ba lallai fa zan shiga har gida in zanata!"
Yar dariya kawai tayi da jin haka.
Ya gyara zama yana kallonta a nutse, duk da haka fuskarshi a sake take babu daurewa.
Yace, "Malama Nadiya, kamar dai yadda kika sani, Sunana Abdullahi Aminu. Sannan ni likita ne, ina aiki a Aminu Kano Teaching Hospital. Shekaruna talatin da hudu yanzu a duniya, ba kuma zan boye miki ba, nayi aure amma mun rabu da matar. A zance na gaskiya kuma, da na ajiye auren ne a gefe, babu ranar sake wani, amma a yanzu dai har ga Allah na ganki ne, ina sonki, kuma in shaa Allah ina son hakan ya kaimu ga aure!"
Ta jinjina kai tana kare mishi kallo a hankali. Yanayin jikinshi dogo ne, bashi da kiba, yana da tsayinshi dai dai misali. Ba zaka kirashi baki ba, haka ma ba zaka kirashi fari ba. Sannan duba da shekarunshi daya fada mata, idan ba sani kayi ba sai kace shekarun nashi basu haura talatin ba.
Tayi tsai da ranta tana kara tunani. Zata iya cewa wannan shine karo na farko a shekaru fiye da biyu da wani namiji ya nuna sha'awar aurenta kai tsaye. Ta sha samun samari da magidanta da ke zuwa wajenta, wadanda tun kafin lokaci ya ja ma take fahimtar ba aure ya kaisu ba. Soyayya da holewa kawai suka je yi, ita kuwa ta zubar dasu a take ba tare da bata lokaci ba.
Taga shi auren kamar yadda suke fadi dace ne. Kuma zaman gida da take yi, ba zabar hakan tayi ba, ba kuma don tana jin dadinshi bane. Menene ma amfanin cigaba da zaman gidan da a kowace dakika nuna maka ake yi ba fa wajen zamanka bane na dindindin? Kuma ba a gajiya da goranta maka rashin aure kamar kai ka janyowa kanka?
Watakila idan ta nutsu, zata iya samun abinda take so a wajen Abdullahi din.
Tana daya daga cikin mutanen da suka yarda ba wai lallai dole sai anyi soyayya ba ake yin aure. Ta fi yarda da cewa kawai dai fahimtar juna ta fi taka rawa a wannan bangaren.
Don haka ta nisa ta kalleshi, tace mishi, "to Malam Abdullahi, naji duka kalamanka kuma na gamsu. Amma kayi hakuri ka bani wasu yan lokuta domin in tattauna da manyana, saboda kada in yanke hukunci ni kadai."
Ya gyada kai, "ehh, kwarai hakane, da gaskiyarki kam! To yanzu zuwa yaushe zan baki kenan? Yau ko gobe?"
Ta saki yar dariya a tausashe, tace, "a'ah Malam, me kake ci na baka na zuba ne haka? Ka dai bani yan kwanaki dai!"
Ya langwabar da kai gefe daya, "to ni dai ina rokon alfarmar a daure a tunana lamarin nan nawa da wuri. Saboda so nake as soon as possible inyi caraf dake, kafin inji ana min guda a tsakar kaina wani yayi awon gaba dake!"
Ta yi murmushi kawai tana girgiza kai.
Sun jima sosai suna hira da shi anan har sai da aka kira Azzuhur kafin suka rabu da shi.
Ko a yinin haka suka yini suna waya, motsi kadan ya kirata, a zauna ayi ta hira abin har ya fara gimsarta.
Da dare ta samu Anty Jamilah da zancen, ta tambayeta ko me take gani ya kamata tayi a shawarce?
Tace mata, "Abdul fa yana da hali na gari, gaskiya mawuyaci ne ki samu wani ya fada miki akasin haka. Sannan ko a yanayin mu'amala da mutane, mutum ne mai tausayi da tausasawa. Idan kina ganin hankalinki ya kwanta da shi, to ki bashi dama ki ga inda hakan zai kaiku. Amma dai kam babu wani mutum da nake ganin zai dace da ke kamar shi din!"
Hankalin nata bai kwanta dashi duka ba, amma a hankali a hankali watakila hankalin nata zai kwanta dashi dari bisa dari.
Don haka data koma daki ta kirashi ta sanar dashi abinda ta yanke. Irin murnar da yayi ba kadan bace, har hakan ya bata mamaki.
Tace, "sai dai wani hanzari ba gudu ba!"
Yace, "me fa?"
Tace, "to ina sa ran cigaba da karatuna saboda yanzu haka admission nake tsammani daga ABU Zaria daga nan zuwa ko wani lokaci. Ina fata hakan ba zai zama matsala ba?"
Yayi saurin cewa, "ko kadan! In shaa Allah hakan ba zai zama matsala ba!"
Tace, "to nagode!"
Haka suka kusan raba dare suna hira. Sai data gaji tace mishi kanta yana ciwo sannan ya mata sai da safe.
Washegari suka koma Kaduna. Kwanakin da suka biyo baya kuwa soyayya ake sha ita da Abdullahi din ba ta kadan ba. Ko kuwa ita a bangarenta hira zata ce? Gata nan dai. Ita dai duk wani dokin masoyi da kewa da shauki da ake ji na masoya, bata jin ko kadan a tattare da Abdullahin.
Sai dai har zuwa lokacin tana ba kanta uzirin zata so shi a hankali. Tunda dai shi ta tsayar a matsayin wanda zata aura.
19.
Ranar Alhamis basu bude shago da wuri ba saboda sun zauna meeting akan yadda yakamata su gudanar da tsarin azumi da ake sa ranshi kwanaki uku masu zuwa ko biyu.
Su duka sun fi ta'allaka akan a cigaba da tsare-tsaren da aka saba yi kamar dai sauran azumummuka da suka wuce. Wanda zasu dinga bude shagon da yamma, ana yin kayan ciye-ciye saboda masu son motsa baki bayan shan ruwa.
Sai kuma aka kara shawarar a dinga gashin kaza da kuma yin tatattun lemuka na kayan marmari don a dinga hadawa dashi. Da wannan shawarar duk suka yi amanna, aka ware mutane biyu da zasu dinga kula da wajen da dare din saboda daga Nadiyar har Aramide kowa kafin a sha ruwa yake tafiya gida, meeting din ya tashi.
Kasancewar ranar Aramide bata je wajen aikinta ba, sai duk suka hadu har ita aka cigaba da sallamar kwastomomi da gudanar da ayyuka kamar yadda aka saba.
Wajajen karfe hudu da rabi ne, Nadiya tana cikin decorating din wani 4 steps cake taji daya daga cikin ma'aikatan wajen tana nemanta.
Ta juya tana kallonta cike da alamun tambaya, sai tace mata, "wani yaro ne yazo yana nemanki!"
Tace, "ni kuma?" cike da mamaki.
Tace, "ehh! Kwatancen da yayi dai kamar na ki ne, kuma ya ambaci sunanki!"
Tace, "to shikenan!"
Dama saura kadan ta kammala abinda take yi, don haka tace mata taje tace mishi ya dan jirata.
Ta kammala touching din da take yi, tayi packaging din shi nan da nan, ta bada a kira masu kaiwa su kai, ita kuma ta fita wajen da ake jiranta.
A bangaren VIP aka ajiyeshi, can kuma aka nuna mata data tambayi wanda yake nemanta. Ta wuce can cike da mamakin wane yarone wanda zai je yana nemanta a dai dai wannan lokacin.
Zaune yake akan daya daga cikin kujerun dake wajen, da remote control na game dake wajen yana bugawa.
Yaron ne kuwa kamar yadda aka ce, bata tunanin shekarunshi zasu haura bakwai. Yana saye da wasu kyawawan cotton din sweat pants na yara na Nike ruwan toka, da farar vest. Ta kalleshi kamar ta sanshi, amma kuma ta kasa tunano a inda ta san shi din.
Ta matsa ta zauna a kusa dashi, shi kuma daya ganta sai ya ajiye abin wasan nashi ya juya yana kallonta da murmushi, "Anty Ina kwana?"
Ta murmusa itama sosai, Allah Yayi ta da son yara ita dai, tace, "lafiya lau boy. An ce kai ne kake nemana?"
Ya gyada mata kai, "Daddy ne ya kawoni nan yace in zauna a wajenki zai je ya dawo!"
Ta dan juya kanta cike da mamaki, tace, "Daddynka kuma? wanene shi?"
Yace, "Habib Abdullahi Makama?!" cikin sigar tambaya.
Jin sunanshi kadai ma sai daya sanya taji bugun zuciyarta ya canza. A duka kwanakin da suka wuce tun bayan daya ajiyeta a kofar gidansu ya wuce, karya take yi tace babu wata rana da zata fito ta koma ga mahaliccinta bata tunano wannan mutumin ba. Abin har ya kusa zame mata jiki, yin tunaninshi a lokacin da taje yin kwanciya barci. Da kuma yawan tunanoshi a cikin yini, randomly zata ji kawai ya fado mata a rai. Ko kuma ta tsinci kanta da tunanin ko me yake yi a daidai wannan lokacin? Wasu dararen kuwa har da mafarkinshi da tunanin wannan daddadan kamshin nashi, wanda ta samu ta lalubo turaren da yake amfani dashi cikin wadanda ya bata, itama ta mayar dashi nata turaren.
Yaudarar kanta take yi, da take cewa wai tuni ta manta da sha'aninshi da kurar data kwasoshi. Ita tasan karya take yiwa kanta.
Duk kuma yadda taso abinda ke tukarta a zuciya kada ya bayyana, sai daya bayyana din. Ta rasa fara'ar kirkirowa tayi ko da ta yake ce kuwa, haka bugun zuciyarta ya ki saisaituwa duk yadda taso ta saisaita shi din kuwa.
Ta daure dai da kyar tace, "ok, kwarai na ganeshi. Yana ina yanzu?"
Ya dan daga kafada, "ban sani ba nima. Kawai dai yace in zauna a wajenki zai dawo ya daukeni. Kuma bai ce ga lokaci ba."
Ita abin ma sai ya girmame mata, mamaki ya hanata motsi. To ita kuma a su wa? Da zai dauko danshi ya kai mata? Sai lokacin ta tunashi a matsayin yaron data gani tare dashi lokacin da suka ci karo a Makarfi. Ashe har d'a ma gareshi amma yake tata rashin kirki haka sai kace na wanda bashi da responsibility na Iyali. Koda yake ai dama Anty Lima tace yana da Mata, mutum kuwa mai mata ai ba zai rasa d'a ba ko ma 'ya'ya idan ba wani ikon Allah ba.
Tayi dan murmushi don kada yaron yaga kamar ba ta so zamanshi anan ba, tace, "to shikenan. Zaka iya zama anan kai kadai har zuwa lokacin da zan kammala abinda nake yi?"
Ya gyada mata kai.
Don haka ta barshi anan ya cigaba da wasanshi, amma sai data dauki kayan tabe-tabe ta kai mishi ya ci da lemu. Haka duk bayan yan lokuta zata leka ta inda yake ta ganoshi da abinda yake yi.
Data sake komawa a wani lokaci sai ta sameshi yana gyangyadi, don haka ta kama shi taje ta kwantar dashi a dakin hutunsu, ta koma ta cigaba da ayyukanta.
Da rana ta mishi take away din jollop din shinkafa aka kai mishi ya ci.
Yinin nan guda na ranar anan yayi shi. Yaron yana da wayo, kuma yana da saurin shiga rai. A hirarrakin da suka yi da shi taji cewa shi kadai ne a wajen mahaifin nashi. Kuma bata tunanin ma Mahaifiyarshi tana gidan saboda koda wasa baya ambatarta, sai dai Babanshi din, da Granny da tasan bata wuce Hajiya Umma, da Anty. Wannan kuma bata san ko wacece ba. Sai wajajen karfe hudu na yamma sannan security din wajen yaje yace Ammar yaje inji Babanshi.
Ta samu leda babba ta zuba mishi cima iri-iri na makulashe ta damka mishi a hannunshi.
Tayi tunanin ta barshi ya tafi shi kadai kamar yadda yazo, sai kuma tayi tsoron yanayi da ake ciki da kuma abinda kan iya zuwa ya zo idan aka samu matsala ta dalilin haka. Don haka ta kama hannunshi suka fita farfajiyar wajen inda security ya nuna musu wata farar Elantra, a gefenta kuma bakar Highlander ce.
Kafin ta karasa wajen motar, ya fito daga bayan Elantra din.
So tayi ta buga mishi warning din kada ya sake kai mata dan shi wajen aikinta, kai ko inda take ma kada ya sake tunkara. Don bata ga alakar da zata hadasu dashi ba. Sai kuma yayi mata wani irin kwarjini a ranar.
Farar shadda ce ya sha ta sha surfani baki, ya dora bakar hular Dara a kanshi, kafarshi ta sha takalmi sai ciki shima baki.
Kasancewarshi mutum mai dan gwabin jiki, da kuma kalar jikinshi da ta kasance mai dan duhu, sai shigar ta matukar haskashi, ta kuma fitar mishi da kamala da cikar haibarshi.
Ta kasa ko hada ido dashi balle ta samu bakin iya gaida shi. Shi kuwa hankalinshi yana ga dan shi, ya kama hannunshi yana tambayarshi 'ya yake?' da kuma 'ya ji dadin zamanshi anan?'
Shi kuwa yana ta amsa mishi da 'ehh!'
Ya juya yana kallonta a nutse, cikin tausassar murya yake ce mata, "nagode da kulawa da kika yi da shi Nadiya. It means a lot!"
Ta kasa cewa komi sai, "uhm!!"
Tana so ma ta daga baki ko yaya ne tace mishi wannan ya zama karo na karshe da zai mata haka, amma ta kasa. Shi kuwa yayi tsaye yana kallonta, ba tare da yace mata uffan ba.
Sai kuma ta juya da sassarfa ta koma cikin shagon babu ko waiwaye.
Tana lekensu ta cikin taga, tana kallo har suka fita daga wajen, bakar motar nan tana take musu baya. Ta saki ajiyar zuciya a hankali tare da sauke numfashi, tuhumar kanta take yi, anya ba nema take ta wuce makadi da rawa ba kuwa?
Zuciya cike da sake-sake ta gama ayyukan ranar ta wuce gida.
Washegari Juma'ah ta tashi da farinciki akan sakon samun gurbin karatun Masters data yi a jami'ar Ahmadu Bello Zaria. Wanda suka tura mata shi ta email dinta a ranar da safe.
Ranta fari tas, tuni ita har ta gama tsara yadda karatun nata zai tafi da kuma aikinta da take yi. Tunda saboda shagon ne ma yasa ta yanke shawarar tsayawa a kusa da gida, amma da ba don haka ba so tayi ta cilla can Kudancin Nigeria ma abinta.
Ta so su hadu da Abba ta sanar dashi da wuri tunda ana gama sallah zasu fara darasi, don cikin azumi ma zata je tayi registration. Sai bata samu haduwa dashi ba saboda ya fita.
Don haka ta bari sai da dare sai taje ita da Mama, ita ta mishi maganar karatun. Sai ta bar Mama ta mishi zancen Abdullahi da shima yake so a bada rana da lokaci magabatanshi su je. Saboda shima so yake yi da zarar anyi sallah a tado zancen biki gadan-gadan.
Sam ranar bata yi mata tsayi ba. Sai taga nan da nan kafin tace me har lokacin rufewa yayi, ta dauki hanyar komawa gida.
Haka kawai taji gabanta yana faduwa, wani irin abu ya danne mata kirji, gabadaya ta nemi sukuni da jindadi ta rasa. Yadda kasan wadda aka fadawa sakon mutuwa.
Cikin tsananin mutuwar jiki ta shiga dakin. Ga mamakinta sai ta tarar da gidan ra-rai, yadda kasan babu wani rai da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 36