tace ka aikata mata rashin adalci."
Yace, "ni kuma Ummah? Me nayi mata ne bayan ba na ma garin?"
Tace, "cewa tayi ka dinkawa Amaryarka kayan sallah ka kai mata? Bayan kuma ita haka ka tafi ka barta zikal!"
Ya hade fuska kamar yana gabanta, "ita tace miki haka ne? To ki tambayeta kiji, da zan tafi nawa na bata na siyayyar kayan kamun azumi da kuma na sallah? Me take nufi da ni ne wai? Ko kuwa ba ita bace ta fada min iyaka adadin abinda take so ba, na kuma dauka na bata babu musu?"
Ummah tace, "duk da haka, gata nan tana korafin ita ai baka taba dinko kaya ka kai mata ba sai dai ka bata kace ta saya. Yanzu kuma ka dauki na wata daban, ka kai telan da yake mata dinki ya dinka mata. Anya ka so tsayar da zancen gaskiya anan Habibu?"
Ya shafa goshinshi da yaji yana shirin daukar zafi, yace, "Ummah, ni ban ma san ko wane tela ne yayi aikin ba. Sannan Shukurah ita da bakinta tace in daina yi mata dinki in dinga bata kudin. Saboda sau nawa ne zan kawo mata kayan tace kalarsu bata mata ba, watarana tace bata son design din, watarana ma haka zata ce kwata-kwata ba su take so ba. To ya zan yi mata ne? Ni Allan-musuru ne da zan san abinda ke cikin ranta? Ko kuwa a kanta zan kare ina bin kanta tana wulakantani? Wahayi aka min da ita ne?"
Ummah da taga ranshi yana neman baci sai ta jefawa Shukurah harara da tayi zaune tana sauraron hirar da suke yi. Tace mishi, "to naji, ta bangarenta dai bata kyauta ba kam. Amma duk da haka ka dinga kokarin daidaita adalci. Tunda dai kaga nauyi ne mai girma yake kokarin hawa kanka. Sannan daga yau na kashe zancen wai a ba mata kudi ta sayi tufafin sallah, ka sayo duk abinda kaga yayi maka ka bata. Idan bata amsa ba kuma zata gamu da ni ne."
Ta karasa fadin hakan tana kallon Shukurah don ta fahimci gargadinta. Sai ta dauke kai.
Shikuwa yace, "to shikenan Ummah."
Har zata kashe wayar sai kuma ta dakata, tace, "da ba munyi da kai ba za a yiwa Nadiya komai ba tunda nan zata zo ta tarar da lefenta?"
Yace, "ai Ummah nima Mami ce ta kirani dazu tace ta bada dinkin da za a kaiwa Nadiya din tayi kwalliyar sallah dashi. Nayi tunanin ma ko kunyi maganar ai."
Tace, "ita Sumayyah din?"
Yace, "ehh."
Ta jinjina kai, "ok. Ai shikenan. Goben kake tafe dai ko?"
Yace, "in shaa Allah Ummah."
Tace, "to Allah Ya kawo mana ku lafiya. Allah tsare mana ku."
Yayi murmushi cikin jindadin addu'arta, "ameen ameen Ummah na!"
Suka yi sallama.
Ummah ta juya tana kallon Shukurah dake tabe baki, tace, "to ke kin dai ji da kunnenki ko? To wallahi idan zaki shiga taitayinki ki shiga Shukurah. Ina kula dake ai, tunda zancen auren Babangida ya tashi kika tsangwami kanki, kina neman ki tadawa mijinki hankali kema kuma ki hana kanki sukuni. An fada miki dama haka ake yi ne? Ko kuwa kin taba jin an ce ana yiwa namiji haka a zauna lafiya? To wallahi ki kula, don kinga yana binki a hankali yana miki yadda kike so, ba wai tsoronki yake ji bane. Lallabine yake miki, duk kuma ranar da ya gaji ke zaki kwan a ruwa!"
Shukurah ta zumburo baki, "to kuma Ummah sai a yiwa mutum rashin adalci amma ya kasa furtawa haka ake yi?"
Ta jefa mata harara, "zo ki fada min rashin adalcin da aka miki a wannan zance inji don Allah! Yanzu tunda Babangida ya bar kasar nan, sau nawa kika kirashi a waya?"
Tayi shiru tana hararar waje daya. Ummah kuma ta tabe baki, tace, "ke dai kika sani ai. Kada ta kara kwabe miki wallahi don kin bar hakarki tayi ruwa da gangan kuma kizo ki ce zaki sanya min ciwon kai Shukurah." Ta tashi ta barta anan.
Itama tashi tayi ta fita daga sashen Ummah din ta koma nata tana sake-sake a ranta.
✯✯✯
Ranar sallah yan gida duk an zuba ido ana jiran a ga Nadiya ta fita da tsofin kaya zata je idi. Don Lantana tun da uwar safiya ta tashi ta ci kwalliya cikin sabin kayanta, ta je kofar dakin Salame ta nemi waje ta zauna. Fadi take tana karawa, "yau dai sai taga karyar masu karya!"
Sai ga Nadiya din ta fito ta ci kwalliyarta abinta tana ta bada kamshi. Salame da itama take ta saurin tayi tata kwalliyar ta fito sai ta koma tana lekenta ta taga. Musamman da su Maryam suma suka fito cikin shigarsu mai kyau wadda Mama ce tayi musu dinkin, suka tsaya a kofar dakinta suna kashe selfie abinsu. Da suka gama kuma suka dauki hanya suka tafi masallaci abinsu. Sai Lantana taja jiki ta koma daki kamar kazar da kwai ya fashewa a jiki.
Ranta fal bakinciki da takaici a cikinshi ya mata katutu.
Ana jimawa kuma sai ga Mama ta fito cikin rantsattsan leshinta da Yaya AbdulHadi ya dinka mata. Ta dinga kaiwa da kawowa a tsakar gida ita da amarya wadda ita ce da girki ranar, hankalinta kwance babu abinda ya dameta. Sai suka bar su Salame da makalewa a daki suna lekensu, reshe ya juye da mujiya.
Don kuwa da so suka yi ranar su gallazawa Nadiya su tura mata haushi da takaici. Sai suka ga kuma lamarin bai je musu yadda suka so ba.
Ita kuwa Nadiya har ga Allah ma tuni data manta da abinda ya faru game da dinkin sallah da ba ayi mata ba. Kwalliyarta tayi tsakaninta da Allah ba don ta turawa kowa haushi ba.
Da suka taso daga Masallacin, suka biya ta shago ta dauki abubuwan motsa baki, saboda tasan ranar ba zasu rasa baki masu zuwa yawon sallah ba. Tasan kuma dasu zasu bude baki a gidan ranar tunda abincin da za a dafa ma sai a ranar aka kai gida, tasan ba a kai ga saukewa ba yanzu. Suka sake tarar abin hawa suka wuce gida.
Ta mikawa mai Napep din daya daukosu kudinshi, ta biyo bayan su Maryam da suka rigata fita tana mai gyara zaman gyalen dake jikinta.
Kamar an ce daga kanki, tayi kyakkyawan gani da wanda ya zame mata tauraro a halin yanzu.
Yana tsaye ta can bayan gidansu a jikin motarshi, shi kuma da waya a hannunshi yana kokarin kiranta sai suka hada ido.
Duniya da abinda ke cikinta suka dauke mata a wannan lokacin. Tsakanin ita da shi bata san wa ya fara takawa zuwa ga dan uwanshi ba, sun dai tsinci kansu a kofar gidansu Nadiya dinne a tsaye, sunyi carko-carko kamar wasu tsofin zakaru.
Kamshin nan nashi ya lullubeta yayi mata kawanya, akwai wani abu a can karkashin ranta dake kokarin janta zuwa gareshi, wanda ta rasa ko menene.
Wata daya kacal daya wuce, idan wani yace mata wai zata kalli fuskar Habibu taji kewarshi ko dadin ganinshi, wallahi sai tace mishi bashi da lafiya. Amma sai gata din, bakinta ba ma zai iya furta irin yadda taji dadin ganinshi ba. Ta kasa dauke idanu a kanshi da yake kallonta yana sakin wani tausassan murmushi.
Yace, "ba kallona zaki tsaya kina yi ba haka kawai Nadiya, idan kinyi kewata ne just tell me. Kin dai san ba zan iya karanta abinda ke cikin ranki a halin yanzu ba!"
Sai ta kawar da kanta gefe daya, tana dan gyara fuskarta don kada ya fara karantar irin abubuwan da zuciyarta ke fitarwa. Abin ma nema yake ya daure mata kai. Yaushe ne tayi sake har Habibun ya yiwa ranta wannan kamun kazar kukun? Har yaushe suka yi sabon da zata ke jin shi kamar wani tsohon masoyi da tayi shekara da shekaru bata gani ba?
Tayi kwafa cikin kokarin boye abinda ke cikin ranta, "wani kewa kuma ana zaman lafiya?"
Ya sake yin dan murmushi a hankali yana takawa zuwa inda motarshi take, itama tana binshi a baya.
"Ko baki fada da bakinki ba ai idanunki sun gama tona miki asiri Nadiya! Shi yasa ma ban fada miki zan zo yanzu ba kenan. Saboda ina son ganin abinda kike kokarin boye min ne da idanuna."
Ta dakata da tafiyar da take yi, suka koma suna fuskantar juna, "ban dai san me kake son cewa ba, amma ni dai nasan babu wani sirri dana boye a cikin raina!"
Bai bata amsa ba sai dan murmushi kawai da yayi, ya dauko kallo ya kare mata tun daga tafin kafarta har tsakiyar kanta. A gefe guda kuma ita satar kallonshi take yi, sai lokacin ta fahimci ashe ma ankon shadda suka yi ita dashi.
Yace, "wai ni amaryar nan tawa kullum wani kara fresh kike yi abinki, wai don Allah menene sirrin?"
Dariya sosai ta saki tana kallonshi a kaikaice. Ta dai fahimci tsokanarta kawai yake ji da neman magana. Don haka ta biye mishi.
Suka jima dashi anan suna hira kafin yayi mata sallama ya tafi. Saboda daga Masallaci nan ya zarce kai tsaye bai koma gida ba.
Itama ta wuce gida, data tarar an sauke abinci ma zuwa lokacin ta zauna ta ci kayanta.
Washegari gidansu ya cika da iyalan gidan yan yawon sallah. Su Basira da Zainab da Habiba duk sun je da yaransu, haka Anty Aisha matar Yaya Saminu. Ita Haulatu sai zuwa biki sannan zata zo.
Suka yiwa Nadiya caa da zancen me yasa bata fitar musu da anko ba? Ita dai nata bada uzirin su yi hakuri an ce babu taron da za ayi ne shi yasa.
Washegari ta fara zuwa gidan mai gyaran jikin da Anty Hauwa ta samar mata. Can ake mata turaren jiki dana gashi, a kuma yi dilka da halawa. Kullum nan take zuwa yini guda ana wannan aiki. Ita kanta duk korafin da take yi nan da nan sai gashi ta fara yin wani irin 'fresh' kamar yadda Habibun nata yace. Ta fara kilewa tana kara yin bul da ita. Kamshi kuwa duk inda ta ratsa sai ka ji shi, har sai ta bace ta barka kana shakarshi.
Bikin saura kwana uku, su Anty Hauwa da Anty Lima da wasu kannen Dada da yan'uwansu suka dira a Kaduna. Gida guda Madam ta ware musu inda nan ne itama zata yi nata taron bikin.
Sai ga Anty Lima ta dira da akwatu guda shake da kaya wai na fitar biki.
Ta kama baki tana kallon kayan cikin mamaki, tace, "wannan fa daga ina?"
Tace, "daga ina kuwa idan ba daga Angonki ba? Tun cikin azumi ya kirani yace in mishi estimating din abinda zai isa ayi miki dinkin kayan fitar biki, har da kudin kwalliya da na gyaran jiki. Na mishi calculations ya turo min kudina cas. Anty Hauwa ce tace kada a fada miki, don shi dinma cewa yayi kada a fadawa kowa."
Ta dinga daga kayan tana dubawa baki a dage, "wannan kayan ai sunyi yawa wai a fitar biki kawai gaskiya! Duk ya zanyi da wadannan ne kam?"
Anty Lima tace, "sai ki mishi kwalliyar da sauran idan kinje gidanshi. Don na fahimci dai mijin nan naki dan kwalliya ne sosai da son kyale-kyale. Shi yasa nima na kawo miki gudummawata ta musamman..."
Ta janyo wata jaka ta bude ta fara zarowa Nadiya wasu shegun night wears da underwears. Kallo daya ta musu ta kauda kai, ita kunya ma kayan suka bata.
Tace, "ki rasa abinda zaki bani yanzu sai wadannan yan iskan abubuwan? Kin dai san ba zan taba sanyasu ba ko?"
Anty Lima ta maida kayan inda suke tare da sanyasu a cikin akwatun kayan data kai mata.
Tace, "ke kika sani ai, ko ki sanya ko kada ki sanya duk ya rage naki. Ni dai ai nayi mai wuyar. Amma dai in fada miki gaskiya, yadda jikin nan naki yake daukar gyara yana kyalli da shekinnan, wallahi gwara kiyi amfani da damar nan. Ki dinga shiga ta raina sa'a!"
Tayi dariya, "Allah Ya kyauta miki wallahi Anty Lima. Kuma sai aka ce dole sai nayi shigar rashin kirki sannan ne ba za a raina ni ba?"
Tace, "ahaf! Zauna anan dai kina mamaki. Zaki fahimci tsarin abin nan ba da jimawa ba. Tashi mu tafi gidan gyaran nan kinji? Don nima gaskiya yau dai sai an dan shafa min dilkar nan na dan yi haske!"
Ta kyalkyale da dariya, "wato abin ma har da sharri kenan?!"
Ta hade kan kayan ta rufe akwatu ta ajiye, ta zari hijabinta suka fita.
27.
Madam taje da tawagarta mota guda, daya kuma tana binsu a baya shake da tarkacen souvenirs na biki. An bugo jakunkuna da mugs na shan shayi da abin turaren wuta. Kowanne dauke da sunan Nadiya din da Habibu ana tayasu murnar aure da fatan kasancewa karkashin inuwa daya har karshen rayuwarsu.
Basu kuma jima da zuwan ba sai ga masu hada waje suma sun karasa. Aka hau gyaran waje babu kakkautawa, nan da nan sai ga wajen taro mai kyau an hada.
Mai kwalliya taje har gida ta yiwa Nadiya kwalliya, aka shiryata cikin lafaya mai kyau ruwan zaiba, suka fita cikin yan'uwa da abokan arziki ana gaisawa. Duk yadda bata so a sanya kida ba, sai da Madam ta sha casunta ita da abokanta aka yi ta liken kudi kamar ba gobe. Sai can wajen karfe tara na dare kafin suka koma gida.
Can ma gidan cike yake da yan biki. Su Anty Haulatu da su Anty Jamilah duk sun je da iyalansu. Da suka zauna zaman hira duk ba su suka nemi makwanci ba sai wajen karfe daya na dare.
Washegari Juma'ah ranar daurin aure. Tunda Asubahi Abba ya tura aka kira Nadiya din, taje yayi mata nasiha daidai gwargwado, ya kara mata da gargadin kada ta kuskura tace zata taba taka kafarta cikin gidanshi da sunan yaji ma balle ayi zancen kaso aure. Daga nan kuma ya mata addu'ar samun zaman lafiya, yace taje ya sallameta.
Ta lallaba ta tashi da kyar, ta fita daga dakin cikin mutuwa da sanyin jiki. Haka ta wayi gari ranar gabadayanta jinta take kamar wata wadda aka yiwa mutuwa. Duk ta bi ta rasa duk wani kuzari nata.
Koda ta koma daki, kasa biyewa hirar da suka sake jonawa tayi, ta shige can dakin Mama tayi lamo a kan gado. Ko abinci sai da Mama din taje ta kai mata shi da kanta, sannan ta samu ta iya tsakurar kadan.
Da gari ya washe kuma, Anty Lima ta matsa mata tayi wanka, aka yi mata kwalliya madaidaiciya. Ta samu leshi fari mai kyau cikin kayan fitar bikinta ta sanya, ta fita tsakar gida aka hau hotuna da ita haka nan ba don ranta ya so ba.
Duk wannan abin da ake yi su Salame suna lafe a cikin dakunansu sun ki fitowa ko nan da can, kiran duniya babu wanda ba a yi musu ba akan su je a dauki hoto dasu amma suka ki fita. Sai Lantana ce ma daga baya da taji mutane suna maida magana, ta lallaba ta fito tana dariyar yake.
Zuwa lokacin da ake gab da daura aure, ta sake yin wata kwalliyar cikin atamfa holland abinta. Da bakin Madam yan Maiduguri suka je gidan nasu, aka hadu dasu aka cigaba da gudanar da hidimar biki.
A ranar ta Juma'ah bayan an fito daga sallar juma'ah a babban masallacin unguwarsu, aka daura auren na Nadiya Auwal Iko da Habibullahi Abdullahi Makama. Akan sadaki naira miliyan daya, lakadan ba ajalan ba.
Mata suka dauki guda da shewa, yara suka hau tafi da murna lokacin da sakon daura auren ya riskesu.
Tana can cikin zugar su Anty Lima da su Aramide da suke ta mata tsiya, ita kuwa gabadaya ta rasa sukunin biye musu ma kwata-kwata.
Aka shiga sanarwar ango zai shigo gida a gaisa da mutane. Nan ya shigo har cikin falon Mama cikin zugar abokanshi, ya sha shadda fara tas tana ta sheki. Suka kwashi gaisuwa tare da godiya suka juya suka tafi.
Tana jinsu har suka gama gaisawar, zuciyarta na aikin bugawa a gaggauce. Rabon data sanyashi a cikin idanunta tun ranar sallah da yaje. Da bikin ma ya kara matsowa sosai, sai wayar da suke yi ta ragu.
Tana dai jin su Anty Lima na gulmar irin kyawun da angon nata yayi, bata iya ce musu komai ba.
Aka cigaba da hada-hada da hidima a gidan. Anty Hauwa da Amarya su suke ta shige da ficen hada mata kayayyakin da masu kai amarya zasu wuce mata da su.
Ana yin sallar la'asar, taji ance wai a fara shirya amarya ga motocin daukar amarya nan sun taho. Sai idanunta duk suka raina fata, hawayen da tun safiyar ranar suke son zubo mata tana makalesu, suka hau kwarara. Jin abin da take yi kamar a mafarki, sai a yanzu ta fara yarda da lallai gidansu zata bari.
Anty Hauwa ta ja ta bayi, ta hada mata wani irin ruwa tayi wanka dashi mai tsananin kamshi da sanya fata laushi. Data fito kuma ta tareta da turare kala-kala, tayi na tsuguni, aka yi na jiki, aka yi na gashi, aka yi na kaya. Abu fa sai gata ta zama kamar wata gidan kamshi. Duk inda ta motsa sai kamshi ya watsu.
Wani swiss lace aka sanya mata riga da skirt, rigar ta sha adon stones da net, idan ka gani sai kayi tunanin ko inji ne yayi dinkin ba mutum ba.
Gashin nan nata da ya sha gyara yana ta kamshi, aka sakar mata shi ya sauka har baya, saboda ta hana a fiddo wani ya zuba a gaban goshinta. Aka kai bakar Alkyabba aka dora mata.
Da aka kaita gaban Mama tayi mata nasiha, kawai sai ta dora kanta akan cinyar Mama din ta fashe da kuka sosai. Baiwar Allah itama Mama din sai ta kasa cewa komi, ta dora hannunta a gadon bayan Nadiya din tana shafawa a tausashe, daya hannun kuma tana share mata hawayen.
Da za a fita da ita har dakinsu Salame da Lantana aka shiga da ita son suyi bankwana, Salame dai cewa take, "ayi hakuri, zaman aure dan hakuri ne."
Lantana kuma na aikin amsawa da "kwarai kuwa. Hakane kam!"
A haka su Anty Jamilah suka ja ta aka fita da ita zuwa inda motoci suke jiransu.
Ba wasu mutane aka dauka da yawa ba, daga Anty Jamilah din, sai Anty Hauwa da Maryam da Anty Lima da Amarya. Da suka tsaya gidan Madam itama ta mata nasihar da zata musu, sai abokiyarta daya ta bi bayansu.
*
Gidansu Habibun gidane ba kamar sauran gidaje da suka sani ba, haka ba irin gidan da Nadiya tayi tunanin tararwa bane.
Kanta a kasa yake tunda aka fara tafiya, jifa-jifa hawaye kan diga daga cikin idanunta tasa hannu ta share.
Daga bakin mutanen cikin motar take jin irin hirar da suke game da haduwa da tsaruwar gidan.
Masu jan motar suka kaita har kofar sashen da Nadiya din zata zauna, acan suka samu Rashida a tsaye tana jiransu. Ita tayi musu jagoranci har zuwa ciki.
Suka shiga ta wani lafiyayyen falo, ya sha leather seats jajaye, suka ratsa ta wani karamin corridor suka karasa dakin Nadiya din.
Dakin madaidaicine, gado ne sambal dan kasar Italy ya sha lullubi da zanin gado mai taushi, aka kama hannunta aka zaunar da ita a gefen gadon.
Su Anty Lima sune masu karade gida don ganin me ya kunsa? Kuma kowannensu ya yaba, ya kuma gamsu da abinda ya gani. Don kuwa tsayawa fadar irin daula da aka narkar a wannan waje ma bata baki ne. Aka shigar musu da abinci a cikin kuloli da lemuka.
Da suka gama zagaye da yan gyare-gyaren da zasu yi, Rashida ta musu jagoranci har wajen Hajiya Ummah. Ta musu tara ta girmamawa, ta bisu daya bayan daya ta runguma, fara'a fal fuskarta da nuna jindadi. Da ta yiwa Nadiya nasiha game da hakuri da rayuwar aure, sai ta bisu da godiya da ban gajiya. Ta kuma bi yan kawo amarya da dubu ashirin-ashirin, kafin tace a kaita sashen Uwargida don tayi mata maraba. Haka suka tafi ransu fal farinciki da jindadin wannan mutunci da karamci na Hajiya Ummah.
Zuwanau sashen Shukurah kuma sai ya sage musu gwiwoyi. Sun samesu su uku ne kadai a falon. Suka yi sallama aka amsa, sauran gaisuwa kuma data biyo baya babu wanda ya taga musu. Su Anty Jamilah suka karaci maganganunsu suka gama, in bango yayi magana to sun tanka. Don Uwargida ma ana cikin bada amanar ta shuri takalminta tayi cikin daki abinta. Suma da suka ga haka sai suka lallaba suka juya.
A dakin Nadiya Anty Jamilah ce take kara yiwa Nadiya fada da wa'azantarwa, zaman aure dan hakuri ne musamman gida na kishiya, wanda kuma za a zauna tare da suruka. Tace tasan dai ba zata samu wata matsala daga Hajiya Ummah ba, itama kishiyar tata tayi kokari ta fahimceta, ta bata girma da hakkinta, don ta taimakawa mijinta kwatanta adalci a tsakaninsu.
Miji kuma tsakaninta dashi yi, na yi. Bari, na bari. Matukar hakan bai sabawa addini ba. Ta girmamashi, ta girmama mahaifiyarshi. Ta kaunacesu tsakaninta da Allah, ta kuma kiyaye hakkinshi dake kanta.
Da suka gama nasihar, lokacin har an fara kiran Magriba, suka mata sallama zasu tafi.
Anty Jamila tace mata, "na cewa Yaya AbdulHadi ya amshi sadakinki ya ajiye miki, bayan biki zan mishi magana sai ya turo miki su ko kuma a duba wani abu a saya da su."
Ta gyada kai tana sharar hawaye. Bata yi mamakin jin hakan ba. Don duk yanmatan gidan da za a aurar a gidansu to Abbansu idan ya amshi sadaki baya badawa, idan kuma an mishi magana yace hidimar biki yayi dasu. Don haka daga baya sai Yayunsu maza suke amsa da kansu, in yaso daga baya sai a ba amaryar tayi abinda zata yi da su.
Haka tana ji tana gani su Anty Lima suka tafi. Ta zauna tsuru ita kadai anan. Kadaici da tunane-tunane suka dameta. Daga karshe dai ta mike a hankali ta shiga bayi.
Bata tsaya duba abubuwan ciki ba da yabawa yadda aka tsara wajen, aka wadatashi da duk wasu abubuwan da za a bukata a bayi. Kawai tayi alwala ta fita.
Kofar da taji ana cewa nan wardrobe take ta bude, sai ta tarar da walk-in closet. Nan kam tsayawa tayi baki a bude kawai tana karewa komi kallo. Duk wata sutura, babu wadda babu. Sashen komi kuma daban. Sashen atamfofi da lesuka gasu nan, shaddodi gasu nan, ga jakunkuna da takalma suma ba su kirguwa. Ga mirror da itama aka shake samanta da kayan shafa da turaruka, a kusa da ita kuma wani dogon show glass ne da aka shakeshi da humrori da turarukan wuta da mayukan shafa hadin hannu, tasan wannan aikin su Anty Hauwa ne.
Ta samo hijabi mai tsayi ta sanya, ta fuskanci alkibla ta tayar da sallah. Koda ta gama bata tashi ba, ta cigaba da zama akan abin sallar tana lazumi har aka kira isha'i, ta yi. Ta daga hannunta sama tana addu'a, duk akan Allah Ya jibanci lamuranta game da wannan sabuwar rayuwa data shiga.
Bayan lokaci mai tsayi ta tashi tana nade abin sallar da hijabin jikinta, sai taji an yi knocking, kafin aka turo kofar dakin aka shigo. Ta juya a hankali tana kallon angon nata dake saye da doguwar farar jallabiya, shi kuma ya karasa shiga cikin dakin tare da maida kofar ya rufe.
Kallonta yake, in appreciation. Kayan sun matukar yi mata kyau fiye da tunani, haka sun fitar mata da kirarta kwarai da gaske. Musamman da yake babu kallabi a kanta sai gashinta da yayi baya ya kwanta, hakan sai ya kara kayatata a gareshi sosai.
Ya tsaya a gabanta yana cigaba da kallonta, ita kuma haka kawai ta tsinci kanta da rawar jiki da sagewar gwiwa. Yasa hannu ya karbe hijabin hannunta ya ajiye a gefe.
Yayi murmushi ganin yanda tayi wani tsuru-tsuru tana muzurai kamar wadda aka kama ta yiwa sarki karya.
Yace, "Tubarkallah Amarya. Ma shaa Allah. You look so breathtaking wallahi Nadiya! Anya zan iya jumurin bari wani ya kalle min ke kuwa, ba zan kulleki a dakina inyi ta kallonki ni kadai ba?!"
Ta rasa kalar amsar da zata bashi, kawai sai ta buge da gaidashi, tace, "ina yini?"
Yayi dariya sosai, ba zato kuma sai tsintar kanta tayi cikin jikinshi. Kanta saman kirjinshi tana iya jiyo bugun da zuciyarshi take yi, yace, "lafiya lau Love. Ya bakunta?"
Ita ai tuni bakinta ya gama macewa, abubuwan da kusancin da suka yi suke haddasa mata a jikinta suna da yawa. Bugun da zuciyarta yake yi shi kanshi sai daya jiyo shi. Yayi dan murmushi, "to, tun kafin a kai ga zuwa ko'ina har na kashe bakin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 36