ce wadda aka fi samunta a dattijai maza wadanda suka haura shekaru arba'in a duniya, kuma ta fi yin kamari ga irin masu yawan aure-aure dinnan ko yawan neman mata. Bayan matsalar fitsari ma suna tunanin kodarshi ta dan tabu amma ba da yawa ba, akwai kuma yiwuwar yana fama da matsalar low sperm count. Don haka zuwa gobe zasu kara yin wasu gwaje-gwaje don su tabbatar da zarginsu.
Zasu dorashi akan magunguna, zuwa nan da sati biyu idan basu gamsu da aikin magungunan ba to sai sun kai ga yi mishi aiki gaskiya.
Tayi shiru tana sauraren bayanin da yake yi mata har gama, ta mishi godiya tare da tashi tsaye. Sai data tsaya ta fara biyan duk wani abu da aka biyosu ta sayi magungunan da duk abinda za a bukata kafin ta koma dakin da aka kwantar da shi.
Ta zauna anan tare da matan tana kara yi musu maimaicin bayanin da likita yayi mata har zuwa lokacin daya farfado. Suka dukufa a kanshi suna tambayarshi ya jiki?
Sai zuwa yamma sannan Babangida yaje da kanshi ya dauketa bayan ya shiga har dakin da aka kwantar da Abban ya gaidashi ya mishi ya jiki. Shima sai daya sake ganawa da likitan da case din Abban yake hannunshi. Likita daya fahimci ko surukin wanene yake kulawa nan da nan ya kara shiga cikin hankalinshi, kulawa sama da kasa ya sake daukowa ya dora akan Abba.
Suka rabu dashi akan cewa daga yanzu komi na kulawar Abba din yana hannun Habibun, don haka duk wani abu daya taso ya fara sanar dashi. Sannan koda aikin ne ya taso, to shi zai dauki dawainiyar aikin.
Yana komawa dakin ta tashi ta fara gyara lullubin jikinta don tasan karshen zancen. Mama ce da Lantana a wajen lokacin da yaje, ya duka yana yi musu sallama tare da sanya hannu a babbar rigarshi ya ciro sabin kudi wrapper na dari biyar ya mikawa Nadiya data karasa wajenshi, yace a ba Mama an siyawa Baba magani.
Ta mikawa Mama kudin wadda ta sanya hannu biyu ta amsa tana musu godiya tare da fatan Allah maidasu gida lafiya.
Suna bada baya Lantana ta kaiwa kudin nan damka tana lalasu a hannu baki har kunne, cewa take, "kai! Auren 'ya mace mai dadi idan aka dace! Don Allah kiga irin wannan abin alheri da Malam yake gani iri-iri daga aurar da mace daya kadai!"
Mama ta kalleta cike da takaicinta amma bata ce mata komi ba. Ta raba kudin nan gida biyu ta soke a zaninta, ta mikawa Mama daya rabin tana ce mata, "gwanda ki boye wadannan kafin sauran su zo su ga ni su sanya miki wawa. Allah na tuba kuma me za a siyawa Malam yanzu? Duk wani abu da za a bukata sun kawo sun ajiye mana fa!"
Tsabar haushi Mama kasa ce mata komi tayi, ta cigaba da jan carbinta tana lazumi abinta, ta bar Lantana na cigaba da santinta da zubawa Nadiya da mijinta Habibu godiya.
****
Cikin satin suna ta kaiwa da kawowa wajen duba jikin Abban wanda aka sallamo daga asibiti bayan kwana uku. Yara ana ta shiga da fita kullum kaje gidan kusan a cike yake da yaya da jikoki yan dubiya.
Bayan kwanaki sha hudu suka sake komawa, likita yace dole sai sunyi mishi tiyata saboda abun ya riga ya taba mafitsararshi ga kuma koda da take kokarin tabuwa.
Aka sanya ranar aiki, aka yi cikin ikon Allah aka yi lafiya aka gama.
Sai dai likita yace akwai yiwuwar ba lallai ya sake haihuwa ba. Kai auratayya din ma gaskiya zai iya daukar lokaci mai dan tsayi kafin ya iya.
Suna komawa gida bayan an sallamesu ya tara matan duka, ya yi musu bayanin abinda likita yace. Ya fada musu su dukansu ya basu zabin duk wadda taga zata rabu dashi ko kuma zata cutu saboda haka ta fada mishi, gwara kawai ya sallameta akan ya dinga shiga hakkinta. Suka yi shiru su duka suna kallonshi, Mama dai tashi tayi ta fita ma daga dakin abinta ta cigaba da ayyukanta da take yi. Yaya AbdulHadi ya sake siya mata firjin babba ta hada da dayan da take da shi, don haka abubuwan sanyi da take yi ana saida mata yanzu ta kara yawansu. Don kuwa yanzu har daga gidajen biki da suna aikawa ake ana yi a kai musu.
Suma sauran duk sai suka tashi suka fita alamun dai babu mai niyar rabuwar. Duk da haka sai ya kara tsayar da amarya, yace mata ita ce karama a cikinsu, wadda ko haihuwar fari bata yi ba. Ba zai iya cigaba da zama da ita ba bayan shi babu tabbacin zai iya ma tsinana mata wani abun nan gaba. Don haka tayi hakuri amma ya sauwake mata igiyarshi dake kanta biyu. Ta kuma yi hakuri ta yafe mishi idan ya taba yi mata wani laifi.
Daga Mama har Nadiya babu wanda yaji dadin wannan hukunci daya yanke, sai dai su dukansu sun san cewa hukuncin daya yanke shine dai-dai. Sai kawai suka yi mata fatan Allah Yasa hakan ya zame mata alkhairi kawai. Zumunci kam ai sun riga sun daura shi da yardar Allah, za kuma su ci gaba da yi koda bata gidan.
Ta je ta kwashe kayanta tayi sallama da mutanen gidan.
Su kuma matan suka rukufa a kan maigida ana ta aikin jinya. Wannan zaman jinyar da yayi duk shi ya kara tsayar da duk wani samu nashi, ragamar kulawa da gida ta koma hannun Mama da Nadiya. Don ma su Anty Jamilah da sauran Yayunsu suna nasu iyaka bakin kokarin.
Tuni su Salame aka dawo cikin hayyaci don sun gane dai babu fa wani Sarki sai Allah. Ranar nan Nadiya taje gidan duba Abban sai ta tsinto Salame a kofar dakin Mama tana tayata zuba kunun tsamiya da zobo a cikin jarkoki suna jerawa a firjin ita da su Maryam. Lantana din kuma tana bakin kofar kicin tana aikin taya Mama din dahuwar abinci.
Ta kama baki cikin mamakin wannan abu, a ranta tace, 'lallai dai wato in da ranka zaka sha kallo har ka gaji! Dama wannan rana zata zo?!'
✷✷✷✷
Watanni uku ne bayan hakan, suka nabba'a a falon Ummah su dukansu family din a ranar wata Juma'ah da dare a cikin watan Afrilu, inda ake fadin sakamakon zaben da aka gama gabatarwa a ranar Alhamis, jiya kenan. Kasancewar an daga zaben da kusan watanni biyu sakamakon wani canji da Gwamnati tayi na tsare-tsaren zaben, amma da tuni an yi an gama ma.
Tana zaune da rindimemen cikinta Tubarkallah, wani lokacin har rinjayarta yake yi idan zata tashi. Hannunta damke cikin na Babangida, bakinta dauke da Bismillah. Ji take yi kamar ta fada cikin Talabijin din ta dubo rahotannin da kanta.
A gefe daya Ummah ce da Shukurah da Mami da itama taje cikin satin da kuma babban danta Ma'aruf, wannan shekarar ya hada degree dinshi akan Social Work, a University of Washington Zarqa (Zarqa shine babban gari na biyu a cikin Kasar Jordan). Farida da Yayanta Fu'ad suna tare da mahaifinsu da bai samu damar zuwa ba saboda karatun yaran da kuma wajen aikinshi da ba a jima da yi mishi karin matsayi ba.
Ga sauran amintattun mutanensu duk suna warwatse a zaune a falon suna zaman jiran jin sakamakon in a bated breath.
Duk da cewa daga yadda ake fadin irin nasarorin da suka samu a wurare da dama, suna da tabbacin suna da jagorancin tafiyar, amma duk da haka basu sakankance ba.
Har zuwa lokacin da mai gabatarwar yace, "sai kuma gari na karshe wato nan cikin Katsina City, an samu kuri'a dubu arba'in ga jam'iyyar BOP, kuri'u dubu hamsin da biyu ga jam'iyyar CPA, da kuma kuri'u dubu tamanin da dari hudu da takwas ga jam'iyyar New Hope Party..."
Ya dakata da maganar na dan lokaci, Nadiya ta ja numfashi sama, "....Da wannan muke cewa Jam'iyyar New Hope Party ita ce ta lashe zaben wannan karon a jahar Katsina da rinjaye ga sauran jam'iyu da kuri'u har dubu goma sha biyu. Don haka muke cewa congratulations to our new Governor, Alhaji Habib Abdullahi Makam tare da shi da mataimakinshi Malam. Abubakar Khamis. Allah Ya baku ikon sauke wannan nauyi da ya rataya a kanku, Allah Ya tayaku riko!"
Falon gabaday sai ya dauki Kabbara da shewar murna da farinciki, aka shiga yiwa juna barka.
Ta rungumoshi cike da tsananin farinciki da murna, tace, "Congratulations Habibi!"
Murmushi yake sosai lokacin daya rungumeta shima, yace mata, "I know we will make it dama, Alhamdulillah!"
Ya duka ya tafi yayi sujjada anan wajen, ita da su Ummah duk sai suka rufa mishi baya. Suka kai goshinsu kasa suna yiwa Allah godiya da wannan nasara da suka samu.
Falo ya rincabe da murna da farinciki, wannan ya rungume wannan, wancan ya rungumi wancan, sai ga su ita da Shukurah sun rungume juna cikin rashin sani. Suka yi kokarin janyewa, Nadiya tayi karfin halin rike hannunta tana kallonta fuska cike da farinciki. Tace, "ina tayamu murna Anty Shukurah, Allah Ya bamu ikon taya mijinmu sauke nauyi da hakkin daya hau kanshi."
Sai tayi dan murmushi, tace mata, "ameen ameen Nadiya!"
Zuwa lokacin kam duk wani abu dake ranta ta saukeshi. Sai dai ta kasa sakin jiki da Nadiya ko kadan, sai ita din take kokarin shiga jikinta tunda dai ta kula ta sauko. Ko babu komi, tana son kwanciyar hankalin mijinsu. Bata son abinda zai raba mishi hankali ko kadan, shi yasa take kauna da kwadayin su hade kansu da ita. Bata kuma son abinda zai taba tarbiyar yaransu, tana so ne su tashi su dukansu cikin farinciki da kaunar juna, wanda hakan ba zai taba samuwa ba matukar suka tashi suka ga iyayensu kansu a rarrabe.
Ita din ai victim ce na irin tsarin wannan gidaje, ga gidansu nan kowa wanda suka fita ciki daya ta sani da kuma uwashi. Musamman kannensu dake tasowa a yanzu, zaka yi mamaki idan kaga karamin yaro na nunawa dan wani dakin yan ubanci tsantsa. Babu kuma yadda za ayi dasu tunda tushen matsalar daga iyayensu yake.
Mutane suka fara yi musu sallama suna tafiya tare da kara tayasu murna.
Zuwa karfe goma sha daya duk an watse sai su ne kadai a falon suna cigaba da maida yadda aka yi.
Ya dubi yadda ta kwanta tayi lamo a kusa dashi, ya kalleta cike da kulawa, "baby lafiya?"
Ta girgiza kai a hankali tana dan yin hamma, "babu komi, barci kawai nake ji."
Sai ya tashi tare da kama hannunta, yace, "to muje mu kwanta. Ai kin ma yi kokari yau. Ke da kike kwantawa tun karfe tara."
Babu musu ta mike, suka yiwa su Ummah sai da safe. Shukurah itama ta bi bayansu tana cewa itama kwanciyar zata je tayi.
Suna zuwa sashenshi wanka tayi, ta yi shirin kwanciya ta kwanta. Babu jimawa shima yaje ya bi bayanta ya kwanta.
Cikinta yayi wani irin girma mai ban mamaki, gashi har ta shiga cikin watan haihuwarta, duk scanning din da ake yi mata tace kada su duba mata gender ko wani abu. Tunda dai abinda ke cikin yana lafiya, idan ya fito sun gani da idonsu. Don haka yanzu bata iya aikata mishi komi. Duk da cewa yana mata matukar kara da kawaici, haka zasu kwanta da shi su tashi baya taba neman komai a wajenta duk kuwa da cewa tana ganin yadda haka din yake damunshi. Ta kuma yi suggesting ko ya dinga kai kwanan nata wajen Shukurah a lokacin da yaga ba zai iya jurewa ba? Yayi kici-kici da fuska a lokacin yace mata kada ta sake mishi wannan zancen baya so. Don haka bata kara tada mishi zancen ba.
Yadda taji yana shigewa jikinta da shafarta yasa taji ta fara shan jininta.
Yace, "celebrating nake yi Nadiya kada ki hanani, ai nayi kokari ko? Yakamata ace har award din Sarkin hakuri da dagawa matarshi kafa kika bani."
Ta dai san bata da bakin hanashi, don haka ta kyaleshi ya dinga juyata son ranshi. Har zuwa lokacin daya samu abinda yake so din, ya ja ta cikin jikinshi ya rungume tsamtsan kamar ya tsaga kirjinshi ya maidata ciki.
50.
An sanya ranar handing over wato ranar da za a rantsar dasu kwanaki arba'in masu zuwa. Ana sanya ran azumi nan da kwanaki uku, don haka a kiyasce dai bayan sallar azumi da sati daya kenan.
Duk cikin satin basu samu zama ba, suna ta karbar baki iri-iri yan taya murna da kuma shirye-shiryen karbar mulki da Habibu yake yi, don haka ba yawan zaman gidan ba ma yake yi.
Mami tana nan anan zata yi azumi, tace sai an shiga gidan Gwamnati da ita sanna zata juya ta tafi, saboda hutu ta dauka a wajen aikinta mai tsayi. Sessions da take yi da patients dinta kuma yawanci suna yi through Google Meet, don haka bata da matsala.
Suna ta shirye-shiryensu da tsara yadda suke ganin zasu tafiyar da mulkinsu, ita Nadiya ba ta wannan take yi ba. Don kuwa cikin kwanakin duk a tsaitsaye take, ita kanta tasan bata jin dadi amma kuma ta ma rasa me ke damunta. Shi yasa ma bata fadawa kowa ba kawai ta daure tana cigaba da al'amuranta.
Sun kai azumi na takwas, ta tashi cikin dare zata yi fitsari. Ita kadai ce a sashen nata saboda Habibu yana wajen Shukurah.
Tayi fitsarin ta koma ta kwanta, sai kuma barci ya gagareta. Zuwa can kuma sai wani fitsarin ya taho. Tun safiyar ranar dama ta tashi tana zubar da wani ruwa mai kala kadan-kadan. Ganin bata jin ciwon komi kuma EDD dinta sai nan da sati daya ma zai cika, sai bata kawo komi a ranta ba.
Wasa-wasa sai gashi ta fara zaryar zuwa bandaki. Tun tana yin fitsarin har abu yazo ya gagara, sai dai kawai ta tsuguna ta tashi. Tafi-tafiya ma sai tafiyar ta fara gagararta. Nan dai tasan abin ba na wasa bane. Sai ta lalubo waya ta kira Babangida, amma wayar tashi a kashe. Ta manta idan zai kwanta barci wayarshi a flight mode yake sanyata, ta sake kiran ta Mami itama din dai a kashe. Ta cije lebe, a ranta tace bari kawai ta lallaba ta tafi sashen nasu da kanta. Cikin ikon Allah kuma duk ba wani ciwo ne take ji na azo a gani ba, wani barci ma yake janta, don haka sai kawai ta koma ta kwanta.
Can taji kamar an mintsineta, ta fara jin ciwo a mararta da kwankwasonta sama-sama, nan ta sake tashi ta nufi bandaki. Kafin ta karasa sai jin wani abu ya fashe tayi, sai ga ruwa yana bin kafafunta.
Bata san lokacin data durkushe a inda take ba saboda wani gigitaccen ciwo daya riketa a take. Ta dafe baya tana murkususu har dai ta samu ciwon ya lafa.
Ta sake lalubo wayarta a sukwane tana bin jerin contacts dinta har idanunta dake wani dishi-dishi suka dira akan sunan Shukurah, ta danna mata kira cikin fatan Allah Yasa ta daga.
Sai data kusa katsewa sannan ta daga muryarta cike da gagin barci, tace mata, "don Allah don Annabi Anty Shukurah ki kira min Mami ta zo, bayana zai cire!"
Tayi jifa da wayar tana sakin wani kakkarfan salati bayan da taji wani ciwon ya sake turnuketa.
Shukurah ta zabura ta tashi sakamakon jin wannan ihun da tayi, a ranta tace babu lafiya.
Ita kadai ce a sashen nata, don kuwa tun dawowarta har yau basu daidaita da shi ba, fushi yake yi sosai tun karfinshi. Itama kuma data gaji da ban hakurin sai ta koma ta zuba mishi idanu kawai, Allah Ya gani ai tayi iyaka bakin kokarinta, hakan kuma ba shi zai sa ta zubar da ajinta ba don tana so ya sauka daga dokin zuciya daya hau ba.
Ta dauki zane ta dora akan doguwar rigar barcinta ta fita da sauri taje ta bugawa su Ummah kofa.
Sai ga Mami da Ummah da Shukurah din bangarenta a sukwane. Da kyar ta iya tashi a duke taje ta bude musu kofar. Lokaci daya tayi wani wujiga-wujiga da ita. Mami tayi saurin tarota tana kamata, ta dubi Shukurah da jikinta ya dauki rawa ganin halin da Nadiya take ciki.
Tace mata, "kiyi sauri ki je ki bugawa Babangida kofa, ya dauko mota ya zo mu tafi asibiti."
Ta juya babu musu ta fita da sauri.
Nadiya ta kama hannun Mami ta rike kamar zata karyata, "ki taimaka min Mami, kuguna zai karye!"
Mami tace mata, "daure Nadiya, in shaa Allahu babu abinda zai sameki kinji?"
Tayi kokarin daga kai, amma abin ma sai ya gagara.
Tace mata, "wani abu zai fito..." ta tafi ta sake dukewa a wajen.
Mami ta zabura ta jata daki a sukwane, tana gyara mata kwanciya ta duba sai ga kan da. Ai nan da nan sai ta hau aiki.
Kafin dawowar Shukurah da Babangida daya rigata zuwa saboda saurin daya dauka har da hadawa da gudu-gudu, yar yarinyar ta fado tana ta tsala kukanta.
Anty ta dagata sama tana hailala, uwar sai ta koma kasan tiles ta yada kai tana salati tana karawa a matukar galabaice.
Ummah tana falo tana kaiwa-da-kawowa bakinta dauke da salati itama da sallallami, sai jin kukan da tayi. Shima da yaji kukan sai ya nemi danna kai cikin dakin a sukwane, tayi gaggawar dakatar dashi. Tace yayi hakuri ya bari a gama kintsasu tukun. Haka ya ja tunga shima ya tsaya anan, amma gabadaya ilahirin jikinshi bari yake yi. Kukan yarinyar jin shi yake har cikin kwanyarshi, so yake yi kawai ya sanyasu a cikin idanunshi.
Mami ta yankewa diyar cibi, ta nadeta a cikin shawl mai taushi bayan ta gogeta tas da man zaitun. Shiru-shiru uwa bata biyo baya ba.
Nadiyar na kwance ita dai gata nan, don kuwa maimakon ciwo yayi kasa ma sai wani sabo daya taso. Kafin ma Mami tace mata bari ta tadata tsaye ta jijjiga ko tayi kasa, sai ga sabuwar nakuda ta taso.
Mami tayi salati ta kara da hailala, sai ta sanya murya tana kiran Ummah. Dama ita kanta kara ce ta hanata shiga, sai kawai suka danna kai ciki ita da Babangida, Shukurah dai ta kasa shiga. In banda rawa babu abinda jikinta yake yi. Dama haka haihuwar take, take nemanta ruwa a jallo? Gaskiya da sake.
Suka shiga suka samu wani sunkucecen dan har ya ma fi yarinyar girma. Cikin ikon Allah kuma sai ga mabiya din ta fado.
Ummah ta karbi yarinyar ta rike, Babangidan ya rabe ta bayanta yana lekenta, kyakkyawar diya da ita Ma shaa Allah, babu abinda ta bari na uwarta, tana ta tsotson baki alamun tana neman tsotsa. Ummah na tsokanar 'daga gani wannan acici ce!' amma hankalinshi yana ga Nadiya da Mami da take kokarin gyara dayan yaron.
Ta gyareshi tsaf ta mika mishi shi, ya amsheshi cikin rawar hannu. Sai daya lalubi kujera ya zauna.
Mami ta taimakawa Nadiya ta tashi suka wuce bayi. Ta zaunar da ita akan stool yayinda take kokarin hada mata ruwan wanka saboda jiri.
Sai lokacin Shukurah ta shiga dakin. Sai ta lalubo kayan goge-goge ta shiga gyaran dakin.
Ita ta gyare wajen tsaf ta goge ko'ina, Mami kuma na can tana gasa Nadiya da tawul mai zafi. Don tace mata wanka zata mata mai suna wanka.
Kafin kiran Asubahi Maijegon da yan biyunta sun fito tsaf da su an gyaresu.
Ranar Ummah da kanta ta shiga kicin ta tukawa Nadiya tuwon dawa da miyar kuka, tana da kominta a ajiye dama, miyar ma dumamata kawai tayi tunda tana da ita a cikin firjin a ajiye. Ta zuba yajin daddawa wanda Nadiyar bata rabo dashi a cikin yan kwanakin da man shanu. Ta kuma hada mata kunun gyada mai kauri sosai.
Tana zaune a gefen gado Ummah ta shiga kwanon. Ji take kamar ta kwato shi saboda yunwar data ke ji.
Ta daure dai har ta kai mata kafin ta amsa. Ta gyara zama tana ci hannu baka hannu kwarya.
Shukurah da Mami na zaune suna kallonta cikin dan murmushi.
Ummah ta wuce sashenta don yin sallah, shima Habib din ya tafi masallaci.
Ta gama cin abincin tsaf, ta wanke hannunta, ta gyara kwanciya yaran na gefenta. Ta lumshe idanu sai barci mai dadi ya kwasheta.
Shukurah itama ta lallaba ta koma nata bangaren don ta huta kafin wayewar gari. Mami kuwa nan ta gyara zama akan sofa tayi kwanciyarta tana lazumi.
Zuwa wayewar gari su Mama sai jin labarin haihuwar kawai suka yi.
Duk da cewa Mami ita ta karbi haihuwar, amma ba bangarenta bane. Don haka sai da likita taje har gida ta dubata ita da jarirai, ta tabbatar musu da cewa lafiyarta lau babu wata matsala.
Mama taje gidan ita da su Maryam da Salame, suna falo tare da sauran yan'uwan su Mami da iyalan Uncle Hashim da suka je.
Ta fito daga wanka da misalin karfe sha daya na safe. Mami ta sake yiwa yaran wanka, yan barka sun gama ganinsu suna kwance cikin baby net dinsu suna barci.
Ta zura doguwar riga marar nauyi. Jin jikinta take yi shafal, kamar in aka hureta zata iya faduwa. Kai ita gabadayanta ma jinta take yi kamar wadda aka canza.
Ta fito ta sameshi zaune a gefen gadon ya kurawa yaran idanu yana kallo, Ammar a gefenshi yana tambayarshi, "Daddy wadannan duk kannena ne?" Yana dariya ya amsa mishi da, "ehh! Duk naka ne."
Ta karasa gefen gadon ta zauna itama tana kallonsu cike da murmushi, ya bita da kallo har ta zauna.
Kallonta yake yi da wani kallo da bai taba yi mata shi ba, da so da kauna da wata tsantsar girmamawa da mutuntawa irin wanda bai taba jinsu a ranshi ba akan kowa bayan Ummanshi.
Ya riga ya gama nuna mata irin godiyarshi tun da Asubahi din kafin ya tafi sallah, lokacin data fito wanka su kuma su Ummah sun fita don yin sahur, Mami na bayi tana wanke yaran, ya tattagota cikin jikinshi ya rungume yana rada mata irin farinciki da jindadin dake ranshi a lokacin, da dimbin godiya da alkawarurruka iri-iri na nuna mata so da kauna irin wadanda ba za su kwatantu ba ita da yayanta har su gama rayuwarsu a doron duniya. Amma ji yake kamar duk wadannan basu isa ba. Kamar bai ma nuna mata komi a cikin irin farincikin dake ranshi ba.
Ta maida hankalinta ga Ammar dake watsa mata nata kalar tambayoyin, ta biye mishi tana amsawa a nutse, wani tayi dariya. Yana saurarensu yana murmushi a tausashe shi kuma. A haka Shukurah ta shiga dakin ta samesu. Taji wani abu ya dan taba mata zuciya, ga su nan dai idan ka gansu ka ga the perfect family. Masu son junansu da kulawa da juna sosai, ita kuma tayi saken da bata kasance a cikinsu ba. Ta ji jikinta yayi sanyi kwarai, tana son ta gyara kuskurenta amma ta rasa ta yaya? Shi kuma Habibu ya ki bata damar yin hakan.
Ta kalli Nadiya a sanyaye tace mata, "Ummah ce tace a tambayeki idan da abinda kike son ci ki fada sai a dafa miki."
Tayi dan murmushi tana girgiza kai, "a'ah, ba ni da zabi gaskiya. Duk abinda aka dafa zan ci. Nagode."
Ta gyada kai, ta juya ta fita.
Shi kuma ya gyara zamanshi yana kallonta a nutse. Yace, "kinga har zuwa yanzu bamu yi maganar abinda kike ganin ya dace a sanyawa yaran nan ba."
Ta girgiza kai kanta a kasa, "ai ni duk abinda ka sanya musu ba ni da zabi. Allah Ya raya su."
Ya jinjina kai, "to ameen ameen Maman biyu!"
Ta jefa mishi hararar wasa, ya yi murmushi.
Yayi Bismillah ya dauki babbar yayi mata duk abinda Uba ya kamata yayi, kafin ya dauki namijin shima ya maimaita mishi.
Ya dora mata su duka akan cinyoyinta, "to ga Abdur-Rahman da Ummulkhairi!"
Ta kankamesu a jikinta tana dan murmushi, a ranta take addu'ar Allah Ya bata ikon kulawa da tarbiyantar dasu bisa tsari da tarbiya na addinin musulunci.
Ummah da taji anyi mata takwara kamar ta dauki Nadiya ta goya a bayanta saboda murna.
Wannan haihuwa taje musu da sauyi mai matukar dadi a rayuwarsu. Don kuwa a ranar da Hajiya Hadiza taje ganin yaran lokacin kwana hudu da yin haihuwar kenan, sai ga shi Ummah ce da kanta tayi mata jagora zuwa bangaren Nadiya. Ta dauki yaran ta mika mata su, ana ta raha da tsokanar juna da hira su biyun kamar wasu tsofin aminai. Haka da zata tafi ma sai da Ummah din ta rakata har waje, tana kuma kara maimaita mata lallai fa ta zo wajen rantsarwa. Ita kuma tana dariya take ce mata, "ai ko bata zo ba, ita Ummah din ta wadatar!"
Ummah itama tayi dariya sosai, tace, "ke dai Hajiya ki zo, saboda zuwan naki shi zai sa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 36