komi ya zamana a kammale kuma a tsare."
Sai suka yi sallama da ita akan haka din. Zuwan da tayi cikin dar da taraddadin me zata tarar? Sai ta koma gida cikin farinciki da sukunin zuciya kwarai da gaske.
Madam da ta tashi zuwa ganin jikoki kuwa abin ba a magana. Aka dinga sauke kayan jinjirai na sa wa da na wasa yadda kasan za a bude shago, don wasu kayanma sai sun girma sannan za su fara sanyasu. Yini guda tayi anan, kafin ta tafi da cewar ba zata dawo taron suna ba saboda washegari Abuja zata je.
Haka suka cigaba da yin jegonsu mai dadi suna karbar yan barka. Ranar suna aka yi hidima kwarai da gaske. Abinci dai a ranar an ciyar da masu azumi bila adadin, a masallatai da gidajen marayu. Kyautuka da sadaka iri-iri haka Habibu da Hajiya Ummah suka dinga yi.
Aka yi hidimar suna aka gama lafiya, aka tafi aka bar maijego da Abulkhairi da Khairiyya, -yadda suke kiran yaran- suna karbar jego mai suna jego a wajen Mami da Ummah. Ga Mama itama da take a gefe, hadin tukudi mai kyau ta bada Amarya ta yo mata, da tsumi jarka-jarka haka aka kai mata da sauran abubuwa.
Mami kuwa gyara take mata na ainihin Bare-bari din kamar wata sabuwar amarya. Don haka kafin zagayowar ranar arba'in dinsu, ita da yaran sun yi wani irin kubul-kubul dasu yadda kasan rainon yis. Duk inda ta baza a gidannan kamshi kawai yake tashi, jikin nan ya kara budewa ma shaa Allah komi ya zauna daram.
Shukurah dai ta lallaba a wannan dan zaman sun daidaita da Ubangidan, wai masu iya magana suka ce a rashin uwa akan yi uwar daki. Kuma in dama ta ki sai a koma hagu. Amma fa duk da haka, idan yaga gilmawar Nadiya a gidan nan sai ya dinga binta da kallo yana hadiyar yawu kamar wani tsohon maye. Don kuwa Nadiya din ce tayi wani irin canzawa ta ban mamaki.
51.
Gab da sallah sai ga Safiya ta je, hutun karshen semester suka samu. Don lokacin da aka yi haihuwar suna tsaka da jarabawa. Nadiya ta ji dadin zuwanta sosai da sosai, musamman da tun bayan auren nata babu wata maganar kirki data kara hadasu da ita. Ita dai bata taba neman Nadiya ba, ita kuma idan ta nemeta din bata samu. Sai ta hakura da neman nata.
A dan zaman da tayi da Nadiya sai take bata hakuri akan abinda ya faru kafin aurenta, ta fada mata cewa kunyar abinda tayi ne a lokacin ya hanata kiran Nadiya kwata-kwata, saboda bata san me zata ce mata ba. Ita kuwa Nadiya tace mata ita dama can bata taba riketa a cikin ranta ba, kuma in dai akan wannan zancen ne, to don Allah ta ma daina bata hakuri.
A wannan lokaci suka zauna suka yi hira irin ta yan'uwantaka a karo na farko a rayuwarsu. Nadiya ta fahimci ashe kallon da take yiwa Safiya a da ba haka bane, kwarai akwai sangarta da rashin sanin girman na gaba a tattare da ita wanda hakan ya biyo bayan rashin tsawatarwa ne daga Madam. Amma kuma tana da saukin kai da wayon zama da mutane. Don haka a dan wannan zaman da suka yi, Nadiya tayi kokarin nuna mata sakacin tarbiyantar da ita da Madam tayi, da kuma kokarin gyara mata a duk inda taga ta kuskure.
Da yake tace tana nan har a rantsar da Habib kafin ta wuce Maiduguri, sai kawai aka gyara mata daki anan wajen Nadiya ta zauna.
Zaman nata ya yiwa Nadiya dadi sosai, don kuwa duk da cewa ga Ummah da Mami suna tsaye a kanta babu gajiyawa, amma akwai wani abun da dole sai shakikinka zai yi maka shi ko kuma ya sani.
*****
Aka yi sallah lami-lafiya lau, sati ya zagayo aka yi bikin rantsar da su. Ranar da za ayi rantsuwar suka yi ankon wani dandatsetsen swiss lace ita da Shukurah din, daga Nadiya din har Babangida basu san da shi ba, don kawai ita Shukurah tace ya bata kudin kayan fitar ranar rantsuwa, ya dauka ya bata babu musu. Itama Nadiya sai ya dauki adadin abinda ya ba Shukurah ya bata, yace ta sayi abinda zata dinka din. Da ce mishi tayi ma ya bari, tunda ita dai kayan lefenta ma bata gama sanya ko rabi ba, ga na fitar suna ma bata sanya wasu ba. Tace mishi a ciki ma ba zata rasa na sanyawa ba, sai yace to ta rike kudin shi dai ya fita hakkinta.
To kuma sai ga kayan a dinkensu inji Shukurah, ta musu anko. Duk da cewa zaman nasu har zuwa lokacin kadaran-kadahan ne, in ka gansu ba zaka ce sunyi irin wannan kusancin na a zo a gani ba, amma kuma suna zaune lafiya. Sannan babu jan magana da jan fada, akwai kuma girmama juna cikin zaman nasu yanzu. Musamman bayan haihuwar Nadiya din, Shukurah tana kokarin leka Nadiya din a duk safiya bayan da Ummah ta hanata fitowa, a cewarta tayi zamanta a bangarenta ta huta. Abinci ma sai dai a dafa a kai mata ko kuma ita ta dafa. To Shukurah din kan shiga wajenta su gaisa, watarana ma har ta dauki yaran ta musu wasa ko ta tafi bangarenta ko na Hajiya Ummah da su. Aka ce wai mai da wawa, kusan da wannan zan iya cewa ta shawo kan Babangida din. Gashi a yanzu shi kanshi Ammar din ya sake da ita.
Haka suka yi shigar wannan leshi ruwan sararin samaniya da adon kananun fulawoyi masu kalar giwaiduwar kwai da kuma brown. Gyale da takalma kadai suka bambanta su, Nadiya ta sanya gyale brown, da takalmi da jaka ta LV suma brown ne. Shukurah kuma sai ta sanya ruwan Gwaiduwar kwan.
Suka tsaya a bayan maigidansu lokacin da ake rantsar dashi, su Khairiyya suna hannun su Mami da ke zaune a can kasan step suna kallo, aka yi handing over da komi, yan jarida da masu video suna aikin dauka.
Daga nan kai tsaye gidan Gwamnati aka wuce da su, inda suka hada yar kwarya-kwaryar liyafa ga abokansu na kusa da kuma yan'uwa da abokan arziki. Aka ci aka sha mai kyau, aka basu souvenirs din jakunkuna madaidaita masu dauke da hoton Habibu da mataimakinshi, da lemuka da snacks a ciki da memo da biro, kyauta daga Madam.
Duk suna zaune akan kujeru da aka zagaye wajen da su, tattausan kidan wakar 'Mad Over You' ta Runtown take tashi a wajen. Mami ta tashi ta wuce filin rawar a hankali ta fara takawa ita kadai, sai mutane suka fara dan murmushi da yar dariya ana kallonta. Zuwa can kuma sai Madam ta bi bayanta, ta fara manna mata sabin yan dari biyu a goshi suna dariya. A hankali wajen sai ya cike da yan rawa, aka fara liki da casu kamar ba gobe.
Shukurah itama dai ta mike daga baya ita da abokanta biyu, take tambayar Nadiya din ba zata shiga bane? Tace mata inaa, su je dai suyi tayi. Don haka ta tashi ta barta ita da Aramide da Anty Lima da itama taje wajen taron.
Suna ta hirarsu ta abokan da suka jima basu hadu ba, yan rawar suka fara dawowa suna zaunawa su ma. Sai ga shi an bar Safiya ita kadai a filin rawa.
Anty Lima tace, "kai, Allah Ya shirya mana Sofia, wai dama yarinyar nan har yanzu bata daina wannan shirmen ba?!"
Nadiya ta kalleta kasa-kasa, "kaji fa dan wuta yi da konanne, ke baki yin rawar ne a wajen biki? Naga dai daga ke har ita din za ni ce ta tarda muje mu?"
Ta kyalkyale da dariya kuwa, tace, "ke ki kyaleta tayi kinji? Lokacine. Mu ba gashi mun girma mun daina ba?"
Tace, "babu wani girma wallahi, shiriya dai!"
Suna wannan tattaunawar sai ga Fu'ad ya shiga filin rawar ya fara yi mata mannin yan dari biyar shi kuma. Nan fa kallo ya koma sama, don kuwa shima rawar ya biyeta suka fara anan. Nadiya sai baki kawai ta sake tana kallonsu kamar wasu mahaukata. Musamman da taga wai iyaye da yan uwa na musu shewa da tafi. Ta girgiza kai cike da takaicin wannan al'amari, a ranta take cewa ko yaushe Madam da Safiya din zasu gane Annabi ya faku?
Sai ga Safiya din tazo ta zauna dabas akan kujera tana goge zufa, ta dauki gorar ruwa mai sanyi ta kafa a baki ta shanye. Ana canza waka wai Fu'ad ya hau daga mata hannu taje, zata mike Nadiya ta zabga mata harara, tace, "na rantse da Allah kina komawa wajen rawar wannan sai na tadeki kin fadi akan wannan dan iskan 6 inches din takalmin naki!"
Ta kuwa koma ta zauna amma tana kyalkyala mata dariya, "wallahi ke dai Adda har yanzu baki gama wayewa ba sai an kwana biyu kila!"
Ta tabe baki, tace, "aikuwa in dai wannan dabi'ar kike kira wayewa to wallahi kina da sauran samun sanayya akan wayewar mutane. Ke yanzu ina wayewa ga diya mace, musulma, ta tashi ta dinga tika rawa a gaban iyayenta da yan'uwa da mazan da ba muharramanta ba, ana kallonta. Ina kika baro addininmu da al'adarmu Safiya? Ni dai kullum ina fada miki wallahi ki dinga kiyayar kanki, don kin iya rawa ba a hanaki ba, kiyi kayanki ke daya mana..."
Anty Lima ta katseta ta hanyar cewa, "... ko ta jira idan tayi aure ta dinga yiwa mijinta ba! Kinsan fa mazajenmu like that chic-thing. Twerking da...."
Nadiya ta katseta, "...to kara turata don Allah ni ina kokarin yi mata nasiha da fada."
Anty Lima ta daga hannu sama tana yar dariyar tsokana, ta tashi ta bar wajen ta koma wajen Mami bayan ta karbi Khairiyya dake hannun Hajiya Hadiza.
Nadiya ta maida kallonta ga Safiya, "ni dai ina kara miki fada da jan kunne Safiya, ki rage wadannan abubuwan. Don kina zaune a kasar waje kina ganin babu mafadi a gabanki, hakan bai baki damar dagewa ki dinga cin karenki babu babbaka ba. Kiji tsoron Allah wallahi. Wannan raye-rayen naki ni bana ganin fa'idarsu wallahi. Maza da dama kuma basu cika ganin mace mai wannan raye-rayen da mutunci ba sam!"
Tayi kasa da kanta jiki a sanyaye, "in shaa Allah Adda zan daina. Ai na Tiktok da Insta din ma duk na daina fa, na goge duk accounts dina wallahi."
Tayi dan murmushi "hakan yayi. Allah Yasa to Safiya. Allah kawo miji nagari mu sha biki!"
Ta tabe baki, "tab! Ai ni da aure ba yanzu ba tukun. Sai na gama karatuna na zama cikakkiyar likita, an bude min asibitina sannan."
Nadiya tayi dan murmushi kawai.
Bata san lokacin da Fu'ad ya fito daga filin rawar ba, sai juyawa tayi ta ganshi ya ja kujera a kusa da Safiya din ya zauna yana janta da hira. Ta bisu da kallo tana dan murmushin ganin yadda ya dauki gabadaya hankalinshi ya maida gareta. Duk wani motsi da zata yi to akan idanunshi suke, baya ko kifta ido haka yake kallonta tana mishi magana cikin jan aji da kwainane.
Ta kara murmusawa, a ranta take cewa, to bari mu ga yadda zata kaya dai!
Zuwa bayan isha'i an gama taro, sunyi sallama da mutane, aka tafi aka barsu su kadai da tarin ma'aikatan dake shake a gidan.
Ummah ta samo mata wata yar dattijuwa, Baba Adama, daga cikin danginsu dake nan zaune a Kaduna, wadda zata dinga tayata kulawa da yaranta har zuwa lokacin da zasu gagije.
Kowacce daga cikinsu tana da dakinta babba, falo mai dauke da bedrooms biyu kuma dukansu manya ne kuma well furnished. Duk da cewa dakunan daya yana kallon daya ne, sai daya ba Shukurah zabi ta fara zaba.
Shi na shi yana gefe da su kadan, kusa da dakunan yara.
Kasancewar bangaren baki a can waje yake kuma akwai doguwar tafiya kafin a karasa, sai kawai ta nunawa Baba Adama daya dakin dake bangarenta tace ta zauna. Ammar yana wajen Ummah. Suna hutun makaranta ne a lokacin, kuma tace tana so su je Maiduguri da shi a cikin satin. Don haka sai idan ta dawo sannan za a mayar dashi wajensu. Duk da cewa dai Ummah na nuna take-taken ita zata rikeshi a hannunta.
Suna shiga daki wanka kawai suka yi, ta kwantar da su cikin crib dinsu bayan ta shiryasu. Itama ta fara nata shirin na kwanciya.
Washegari da safe wajen karfe goma ya bukaci ganinsu a falonshi. Ta riga tayi wankanta ta shirya, yaran ma ta shiryasu tsaf. Sai ta goya Abulkhairi, Khairiyya kuma ta rungumeta ta wuce falon nashi cikin shigar doguwar riga ta atamfar Holland mai ruwan ganye. Ta cake daurin dankwalin nan sassalkan gashinta ya fito wanda ta kame da band a keyarta. Daga ita har yaran kamshi kawai suke zubawa mai taushi.
Ta sameshi shi kadai a falon da takardu a gabanshi yana dubawa, ta duka ta gaidashi ya amsa mata a nutse yana binta da wani irin kallo kasa-kasa. Musamman data kwantar da Khairiyya a gefenshi ta kuma duka tana shirin sauke Abulkhairi. Sai ya saki ajiyar zuciya, ya ture takardun gefe yana shirin damkota, tayi sauri ta zille tayi gefe tana sakar mishi wata irin dariya a tausashe. Ya lumshe idanu yana jingina kanshi da kujera, "ni kike tsokana ko Baby? Zaki yi bayani ne duk ranar dana kamaki a hannuna!"
Tayi murmushi ta ajiye mishi Abul akan cinyarshi, kamshin turarenta na kara kai mishi karo.
Sallamar Shukurah ce ta sanya ta matsa daga gefenshi, ta koma kujerar kusa da shi ta zauna.
Ta kalleta tana dan murmushi, "Anty Shukurah Ina kwana?"
Ta zauna a kusa da ita, "lafiya lau Maman biyu, ya gajiya?"
Ta amsa mata da, "gajiya ta bi lafiya ai."
Ta matsa ta dauki Khairiyya kafin ta kalli Habibun itama tana gaidashi, "Honey barka da safiya!"
Ya amsa mata a hankali.
Hadasu yayi ya sake musu nasiha da wa'azi na sabuwar rayuwa da suka shiga, da kuma nuna musu girman irin nauyin da ya hau kansu, ya kuma hada da rokon yana fata zasu bashi hadin kai su tayashi ya sauke wannan nauyi. Duk suka amsa da 'in shaa Allahu'
Daga nan ya dawo kan yadda zamantakewarsu zata kasance. Zasu cigaba da yin kwanaki bi-biyu kamar da, ga masu aiki nan da masu girki a gidan, su samu lokaci su zauna da su saboda su sanar da su irin cimar da suke so a dinga yi. Bai hana yan aiki yin abinci ba, amma yana rokon alfarmar duk wadda yake a wajenta ta dinga yi mishi girkin dare da hannunta, zasu iya? Duk suka ce babu matsala in shaa Allah.
Ya gyada kai, "ok! Nadiya yaushe kike yin arba'in?"
Ta kalleshi bakinta na son yace ya taimaka ya bari tayi kwanaki sittin, amma tasan ba zai karbi maganar da hannu biyu ba musamman da yake ga Shukurah nan, sai ta langwabe kai gefe guda, tace, "nan da kwanaki uku masu zuwa."
Yace, "It's settled then, nan da kwanaki ukun idan kunyi canjin girki sai dokar ta fara. Akwai mai tambaya ko karin bayani?"
Suka yi shiru suna kallonshi.
Ganin haka sai ya gangara kan ainihin zancen daya sanya ya tattarasu, wato wa zata rike mukamin First Lady a cikinsu? Shi yana tunanin idan zasu iya, su yi running din ofishin su biyu. Tunda dai babu wata doka ta Constitution da tace dole sai mutum daya ko kuma ga wani na daban da zai iya rike kujerar. Amma me suke gani?
Nadiya ta gyara zama tace, "ni dai ina ganin kawai gwanda mutum daya yayi wannan din, saboda gudun samun matsala da abinda ya danganci haka. Bugu da kari kuma gaskiya ni bana ma ra'ayin hakan gaskiya. For the time being ina so in samu lokacin kula da yarana da kuma tunanin abinda zan yi da rayuwata."
So take yi in da hali, ta samu ta cigaba da Masters dinta ko da ta online ne. Bata gama yanke shawarar abinda zata yi ba har yanzu saboda so take yi sai ta fara mishi maganar taji yanda ya karbi zancen sannan.
Shukurah kuma cewa tayi, "ni dinma zan so ace mun rike din tare gaskiya. Amma duk abinda kuka yanke, bani da matsala ni."
Yayi shiru yana tunani kafin ya nisa, yace, "to shikenan. Shukurah zata kula da abinda ya shafi ofishin First Lady, amma title din First Lady ku dukanku zaku amsa regardless of ga wadda take rike da ofis da sauransu. Kema Nadiya akwai kungiyoyi da dama da suke yi min zancen suna so su gayyaceki tun bayan wannan shirin da kuka gabatar kwanaki. Don haka zamu zauna mu fitar da wani program kawai, ta yadda koda sau daya ne a wata za a gabatar da wani shiri na daban domin wayarwa da mata kai akan abubuwa mabanbanta, in yaso ke sai ki dinga jagorantar shirin. Ina tunanin hakan ma ai wani aikin ne na daban ko?"
Ta gyada kai cikin yin na'am da hakan. Da haka dai suka kare zaman bayan ya hadasu da Aides dinsu, suka gabatar musu da ma'aikatan gidan da duk abubuwan da suke yi.
Har tour dinsu aka yi a cikin gidan, haka kuma an hadasu da wasu matan guda biyu wadanda zasu dinga taimaka musu game da harkokin gidan Gwamnati da siyasa for the time being, kafin kansu ya gama wayewa.
*
Kwanaki uku kenan, ta gama shirinta cikin kayan barci marassa nauyi, saman rigar net ne yayinda kasanta kuma silk ne, sai dan wandonta na 3-quarter shima silk.
Tayi addu'a ta tofe jikinta da na yaran, ta gyara gado ta kwanta abinta.
Barci ya sureta mai dadi sosai, sai jinta tayi cikin jikin mutum. Ta juya a hankali tana fuskantarshi ta cikin hasken bedside lamp guda daya data bari a kunne mai taushin haske saboda yaran.
Ta kai hannunta ta kamo nashi dake yawo a jikinta, ta dan turo baki cikin yanayin alamun ban tausayi, "kai Abban Ammar, abin ma ai da tausayi!"
Bai dakata da abinda yake yi ba, sai ma kara zafafa sumbata iri-iri da yake manna mata a duk inda bakinshi ya kai a jikinta.
Yace, "ni ai dama na dade da sanin ba ki tausaya min Nadiya ko kadan. Shikenan daga kinyi 'ya'ya sai ki manta da ni, kika shareni kwata-kwata, kika wancakalar da lamurana. Yanzu kuma kina fada min wai da tausayi? Tausayin me zan ji, bayan ma nine abin tausayin?"
Ta dan janye jikinta daga nashi tana kallonshi, "ni dai don Allah kayi hakuri ka bari mu kara kwana biyu tukun. Ka ga fa su Abul basu gama yin kwari ba."
Ya kama baki yana kallonta cikin mamaki, "lallai ma, kin kuwa ma san abinda bakinki yake furtawa? Ina ganinki ko sati uku baki cika da haihuwa ba kika fara sallah. Nayi hakurin, na kara hakurin akan wanda nayi, yanzu kuma kike wai bani wani labari na daban?!"
Ya rarumota ya hade da jikinshi, "na rantse da Allah na gama hakurin, yau dai, da yardar Allah sai mun samo wasu yan biyun!"
Da yake itama maganar tata bata gama kaiwa zuci ba, don kuwa itama tayi kewar mijinta. Jan baki ne kawai da tsokana, sai ta biye mishi. Suka raya wannan dare cikin tsananin kauna da soyayya mai sanyaya rai. Yayi sa'a har ya gama cin angon nashi yaran basu motsa ba.
52.
His Excellency (Dr.) Alhaji Habib Abdullahi Makama. Magidanci dan kimanin shekaru arba'in da takwas. Yana daya daga cikin Gwamnoni wadanda suke da karancin shekaru akan karagar mulki a wannan lokacin.
Ya fara aikinshi da gasken-gaske ba da wasa ba, Yayi sa'a kuma ya dauki amintattun mutane a matsayin wadanda zasu tayashi rikon mulkin, don haka komi yana tafiya cikin dadin rai. Dan abinda ba a rasa ba bai wuce sukar makiya da yan adawarsu da suke binsu suna bata musu suna da kokarin nunawa Talakawa da mutane babu aikin da suke yi. To da yake dai idanu ko da ba mudu ba amma sun san kima, talakawan suna ji kuma suna gani a aikace irin aikin da Gwamnatin tashi take musu babu dare babu rana, sai sukar tasu take faduwa a banza.
Cikin watanni takwas kacal da yayi da karbar aiki, an ga canji irin wanda aka jima ba a gani ba a cikin garin Kaduna da Kauyuka.
Ya tsayawa makarantu na Gwamnati da asibitoci da kuma ma'aikatanshi, babu jinkirin yin albashi, asibitocin Gwamnati an cikasu da magunguna na kyauta. Kuma duk wanda aka kama da kokarin satar kayan Gwamnati babu bata lokaci ake cireshi daga kan mukaminshi. Wannan ya matukar sayo mishi mutunci da kima a wajen mutane kwarai da gaske.
Haka suma matan nashi suna matukar kokarinsu wajen ganin sun sauke nasu hakkin dake kansu.
Duk da cewa Nadiya bata fita ko'ina, tana gida tana kula da yaranta. Hakan bai hanata tashi tsaye wajen ganin cewa tayi nata kokarin ba. Ta dukufa wajen ganin cewa ta inganta rayuwar kauyuka.
Ita da Shukurah su kan zauna su zabi kananun kauyuka, a duba matsalar da tafi addabarsu, abin amfanin gona ne? Ko kuwa matsalar ruwa ce? Ko kuma matsalar rashin kyawun hanya ne? Sai ayi compiling din binciken, a turashi ofishin Mai Girma Gwamna daga ofishin First Lady. Inda shi kuma zai dora alhakin bincike da kwangilar yin aikin a hannun Kwamishinoninshi domin a gabatar da aikin. Haka kuma baya yin kasa a gwiwa, ya kan tashi wani kai tsaye domin yaje yaga aikin da aka yi. Idan kuma damar hakan ta samu sai ya taka yaje da kanshi.
An gina rijiyoyi bila adadin a kauyuka da dama ta dalilin haka. An gina masallatai da makarantu na Arabi da boko a Kauyukan da suke da karancin wadannan, haka kuma an samarwa manoma da dama taki da iri na noma sosai. Ciki da wajen Kaduna idan ka zagaya zaka ji kalamai na yabo da sanya albarka ta wannan Gwamnati daga mutane tana tashi kawai.
Yaranta suna ta girma da wayo tubarkallah. Idan ka gansu baka taba cewa wai watanninsu tara yanzu. Rarrafe suke yi zuwa ko'ina, don Abul da yake ya fi Khairiyya kazar-kazar da rashin gwabin jiki har ya fara tsayuwa yana kokarin takawa.
Baba Adama ta tafi gida tun bayan da suka cika watanni hudu. Ita da Maigidan nata suka yi mata sha-tara ta arziki lokacin da zata tafi.
Ummah kuwa da gaske dai ta kwace musu Ammar. Ta hanasu rikonshi kiri-kiri, tace tunda ga yan biyu nan a gabansu, kuma da wasu masu zuwa nan gaba ma da Allah kadai Yasan iyakarsu sai su bar mata shi a wajenta tunda ita babu kowa a gabanta, ta samu mai tayata debe kewa.
A halin yanzu Ammar din yana wajen su Nadiya din, Ummah din ta tafi Umarah tun watan daya wuce.
Gida ake gina mata mai suna gida a can Shagari Low cost. Tace dama can ai estate din Makama mallakin Habib ce, don haka ita zata koma nata mallakin itama.
Yace mata, "Ummah ko dai munyi miki wani laifi ne? Barin estate dinnan kai tsaye sai kace ana korarki? Naga dai zamanmu lafiya lau ko? Idan kuma ginin cikin estate dinne bai miki ba to ki fadi irin wanda kike so sai a rushe wancan a gina miki shi din. Amma don Allah kiyi hakuri kada kiyi nisa da mu. Gidan wallahi fadi zai min sosai idan baki nan!"
Tayi dan murmushi mai kayatarwa, a babban falonshi suke da yake shakatawa tare da Iyalinshi a cikin gidan Gwamnatin.
Ranar wata Asabar ce taje gidan da hantsi domin tayi musu sallama saboda washegari jirginta zai daga kasar Jordan. Taje ta gano Mami wadda ta samu minor accident a hanyarta ta zuwa aiki ta samu gocewar kashi a hannu, daga can ne kuma zata wuce Saudiya yin Umarah. Bata fadi ranar dawowa ba saboda tace sai sun ganta kawai.
Tace mishi, "laifin me kuma Babangida? Kada ma ka sanyawa ranta wannan abin, don kuwa ba haka bane. Kawai dai naga lokaci yayi daya kamata in barku hakanan, in koma cikin 'yan uwa nima. Ka Girma yanzu, ka zama abinda mu da kai muka jima muna fata. Bayan hakkin iyalanka dake kanka, ga na Jihar Kaduna gabadayanta, ba zan kara maka wani nauyin ba. Ka cigaba da jagorantar da rayuwarka data iyalanka da Jaharka yadda kake yi, in shaa Allah Allah zai dafa maka!"
Yadda kasan wani karamin yaro haka ya koma a lokacin, yana tuno yadda tun tashinshi bai taba rabuwa da Ummah ba sai ta sanadin lalura. Son samu daga shi har ita su zamana a waje guda kamar yadda ya tashi a gabanta, ace koda mutuwa ce tazo ta dauki dayansu a gaban dayan.
Yadda duk damuwa da rashin jindadi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 36