Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba, da kika ga haka ba sai ki bata hakuri ba? Shukurah dai ta girmeki, anan gidan kuma matsayin babba take a wajenki. Dole ki bata girmanta yadda yakamata. Saboda haka nan gaba, kada ki kuskura inji abu makamancin hakan ya faru a tsakaninku. Kina ji na ko?" Hawayen nata suka karasa dirowa kan kumatunta. Abu goma da ashirin ya mata rubdugu. Dannewa dai tayi ta gyada mata kai. Ta wuce ta fita daga wajen nasu jiki a sanyaye ko karyawa bata yi ba. Wannan tsagwaron rashin adalci har ina? Ga gaskiya kiri-kiri amma a danne don kawai ba a son mutum? Haka ta koma sashenta tana ta wannan mitar a ranta. Sai da yunwa ta isheta ne sannan ta hada custard ta sha. Da dare da kamar ba zata koma sashen na Ummah ba saboda har zuwa lokacin abinda ya faru dazun bata mata rai yake yi idan ta tuna. Ta dai daure ba don ranta ya so ba, ta tafi. Tana kallon Shukurah akan dinning da ta sha kwalliya kamar zata je wajen gasar kyau, ita ala dole ga mai girki a ranar, ta ki gaisheta. Saboda dai ta mata magana ne ai har take binta da sharri ko? To babu kari. Nan gaba sai ta ga da abinda kuma zata kakaba mata wani abin. Ta zuba abinci ta zauna tana ci, da wayarta a hannu tana chatting. Data gama sai ta koma falo ta zauna tana kallo don ta rage dare. Ta shafa kan Ammar da yake faman yin assignment. Daga karshe ma sai ta buge da taya shi tunda taga yana kakarewa a wani wajen. A haka gogan ya shiga ya samesu. Kai tsaye shima dinning din ya wuce ya zauna. Bata san ya aka yi ba, bayan wani dogon lokaci da ta kai kallonta wajen da yake, sai ta tsinci Shukurah kusan zaune akan cinyarshi. Tana ta wani kissa da abubuwa. Tayi saurin dauke kanta ta mayar gefe daya, tana kokarin dauke hankalin Ammar daga kallonsu don bata ga tsari a abin nasu ba. Zuwa can kuma sai Shukurah din ta taso, ta wuceta tana wani taku dai-daya. Da taje dai-dai inda take sai ta juya tana ce mishi, "baby ina jiranka fa!" Ta karasa fita, takalmin kafarta yana 'kwaras-kwaras!' akan tiles din falon. Ta kalli gogan ta ga ko waiwayenta bai yi ba, sai kawai ta girgiza kai abinta. Ta cigaba da taya Ammar da zanen gida da motoci da yake yi, don kuwa abin na Shukurah bai wani dadata da kasa ba. Da ya gama cin abincin fita yayi daga sashen. Ita kam tana nan har sai da Ummah ta sauko kasa, ta gama cin abincinta ba tare da wata magana ta hadasu da ita ba bayan gaisuwar da ta mata. Ammar da zai yi barci ta rakashi dakinshi da kanta, anan saman yake kusa da na Hajiya Ummah. Ta taimaka mishi ya wanke baki tare da canza kayan barci, ta mishi addu'ar kwanciya barci kafin ta sauka kasa. Ta yiwa Ummah sai da safe, ta koma sashenta itama tayi shirin barci. Har karfe sha daya ta gota, lokacin shima ya gama tura wasu takardu can Kasar Indiya game da wani project da yake yi akan siyasa da kuma tsarkin muhalli, yana kokarin kwanciya sai ga kiran Ummah ya shiga wayarshi. Wai tambayarshi take yi 'me ya hanashi zuwa dakin Shukurah?' Yayi jim na wani lokaci mai dan tsayi. Ba ya so maganganu irin haka na ratsawa a tsakaninsu, shi yasa tun farko bai tsaya yin wani dogon jayayya da ita ba a game da hukuncin data zartar a tsakaninshi da Nadiya. Yana da alkunya da girmamawa ga duk wani wanda zai mu'amalanta. Personal zance irin wannan ba da kowa yake yi ba. Dalili kenan da yasa bai taba daga baki ya kai mata karar Shukurah ba, wadda ta maida kwanciyar aure da shi wani kasuwanci na musamman. Ba ta ba shi hakkinshi har sai ta san da akwai wani abu da zata samu a gareshi ko wata bukatarta ta kanta da zata biya sannan. Wai a hakanma kuma ba koda yaushe ba, ba kuma zama za tayi ta tarairayeshi ba kamar yadda yake so. Sai dai kawai ta mishi kim, ya gama kidanshi da rawarshi ya kara gaba. A hakanma sa'a ce ya ci idan bata ce mishi ta gaji ba ta tashi ta barshi. Duk wannan abu, bai taba daga baki koda sau daya ya furtawa Hajiya Ummah ko wani na kusa da shi ba. Saboda a ganinshi zance irin haka yayi tsauri da nauyi a tsakaninshi da Ummah din. Amma sai yaga kuma ita tana nuna hakan ba komi bane a wajenta. Duk da hakan, sai ya daga baki yace, "Ummah ita me ya hanata zuwa?" Tace, "ka rufe min baki anan, bana son wata doguwar magana. Iyalinka ce ai, ita in bata zo inda kake ba kai sai ka je gareta ai. Ko baka san mata yan lallashi bane? Tana ganin yadda kayi mata kishiya dama ai dole ta ja baya da kai, kai ne zaka yi kokari har ka ja ta a jikinka!" Yana so ya tambayeta, 'to ita kuma Nadiya ba Iyalina bace kenan da kike umartata da in gujeta?!' amma sai ya kame bakinshi. Yace mata, "kiyi hakuri Ummah. Zan tafi yanzu in shaa Allah." Tace, "yauwa!" tare da kashe wayar abinta. Yayi jim zaune a gefen gado cikin zuzzurfan tunani. Bai manta abinda Shukurah din ta mishi ba kwanaki, shi yasa shima yayi niyar shareta. Tunda dai dama ba wani abu yake mata ba, haka itama ba wani abin kirkin take tsinana mishi ba. Shi kanshi yayi mamakin tarairayar data dinga mishi dazu, sai da yayi tsam da ranshi sannan ya fahimci saboda ganin idon Nadiya ne take yin hakan. To ina amfanin abinda ba don yaji dadi aka yi ba sai don a kuntatawa wani? Har ga Allah Ya so ace Ummah bata shiga cikin zancen ba. Don kuwa ya sha alwashin shi da Shukurah dai, sai dai idan ita ta je gareshi. Amma ba dai ya kai kanshi gareta ba. Da kyar ya iya tashi ya wuce bangaren nata. Wannan fita da yayi karaf a idon Nadiya kamar an ce ta daga kanta. Da yake tagar kicin dinta tana fuskantar bangaren Shukurah din da na Hajiya Ummah. Tana kallo ya bude kofar dakin ya shige. Tayi kwafa rai na suya. To! Ashe dai da gasken gudunta yake yi? Shi kuwa Asubahin fari ya bar wajen. Bayan mita da yada kananun maganganu babu abinda ya tsinta a wajen Shukurah din. Ita ala dole ya ci zalinta tunda ya mata kishiya. Daga baya kuma ta koma nuna mishi tasan dai baya kwana tare da amarya har yanzu, idan ya yarda tafiyar tasu ta dore to zai iya duk abinda ya ga dama da ita. Wato dai har yanzu tana kan bakanta. Ya kalleta a wulakance, yace, "me kike yi min ne wai? Me kuma kike bani wanda ba sai kin wulakanta ni ba? In dai don wannan ne, ki rike kayanki. Ki kwadashi kiyi duk abinda kika ga zaki iya Shukurah! Ba na so!" Sai ta fashe mishi da kuka. Shi kuwa ya juya mata baya ya kyaleta tayi ta gama. 31. Zuwan su Amarya ganin daki washegari shi ya dauke mata damuwa da ta kwana da ita. Don kuwa barci gagararta yayi a daren daya gabata. Ta kwana tana tunani da tambayar kanta, wai shin menene matsalar? Kuma ta ina za ta tattago wannan al'amari? Suka mata yini guda ita da sauran yaran gidan da suka je. Amarya sai binta take da kallo tana murmushi, ce mata take yi tana karawa, 'ai lallai wannan amarci ya karbeta!' Nadiya dai dariya kawai take binta da ita. Sai zuwa can yamma suka shirya tafiya, da suka je yiwa Hajiya Ummah bankwana, haka ta musu sha tara ta arziki, ta kuma hadasu da direba tace ya mayarsu gida. Amarya ta ja Nadiya gefe tana kara mata nasihar lallai ta kama Surukarta hannu bi-biyu, ta mata biyayya ta girmamata. Tunda tana sonta, itama ta kaunaceta don Allah. Nadiya ta yi shiru ita dai tana jinta, don kuwa bata tunanin shawarar da zata cigaba da bata kenan idan taji abinda ke faruwa a gidan. A haka dai direba ya ja su suka tafi tana daga musu hannu. Da dare suka hadu da mutumin nata a wajen cin abinci, kasa ko daga ido ta kalleshi tayi a lokacin saboda tsabar yadda yake bata haushi. Ita kanta bata san tana da irin wannan kishin ba sai a yanzu. A da gani take yi ita Allah bai dora mata wannan abun ba, a da, gani take yi koda Allah zai sa ta shiga yanayi kamar wannan to ba zata taba damuwa ba. A yanzu kuma sai ga shi labari ya sha bambam. Kishin Habibun take ji yana nanikarta har a cikin kokon kanta, ta kasa daga ido ta kalleshi daga shi har Shukurah din saboda dukansu haushinsu ma take ji. Ta gaisheshi a kaikaice, da ya zauna a kujerar kusa da ita kuma sai ta juya mishi baya. Ta dinga tura abincin ma da kyar saboda ji tayi cikinta ma ya cushe gabadaya. Ai tana gamawa ta musu sai da safe ta tsere sashenta. Abin daren jiya bata samu barci da yawa ba, tana kwanciya cikin ikon Allah sai barcin yayi awon gaba da ita. Shi yasa sanda ya bi sahunta ya buga mata kofar falo bata ji ba, waya kuma da yake a silent ta sanyata ko da ya kira bata ji ba. Washegari shima tunda farar safiya ya bar gidan don haka basu hadu ba. Ita dadin hakan ma ta ji. Don kuwa duk da bata ga shigarshi bangaren Shukurah ba jiya, amma zuciya da sake-sake haka suka dinga auna mata ai a can dinma ya kwana. Yau ma haka ta tashi rai a cunkushe. Taje ta gaida Hajiya Ummah wadda itama ta sameta tana shiri da alama dai fita zata yi. Shayi kadai ta iya hadawa mai dan kauri ta sha, ta wuce dakinta. Kasancewar ranar Public Holiday ce, Ammar bai je makaranta ba. Sai Ummah ta fita da shi. Gida ya rage daga ita sai Shukurah kadai. Wajajen karfe sha daya ta shiga kicin da niyar dora abinci saboda yunwar data fara nanikarta. Ta samu shinkafarta ta barza, ta dora rigana ta hau aikin dambun shinkafa. Nan da nan gidan ya kacame da kamshi mai dadi. Kafin ta gama kuma sai ta dora farfesun kaji. Aikin da dan yawa tayi saboda yau ta kudurta har Ummah za ta kaiwa abincin. Ta ga abinda zata ce mata kafin kuma daga nan taga ko idan za ta cigaba da kai mata. Da ta sauke dambun ta zuba cikin mazubai masu kyau guda biyu, sai ta bar farfesun under low heat don ya karasa dahuwa. Kunun ayar data hada kuma ta sanya a cikin firjin don ya kara sanyi kafin ta tashi sha. Ta wuce dakinta ta fara watsa ruwa kafin ta dauro alwala ta je tayi sallar Azzuhur. Tana tahiyar karshe taji alamun an bude kofa an shiga dakin tare da maidawa aka rufe. Kafin ta fara mamakin ko wanene kamshinshi ya bayyanashi. Ta sallame sallar ta zauna tayi tasbihai da ladubban da take gudanarwa a duk sallar da ta yi. Ta mike tsaye tana nade abin sallar hannunta tana kallonshi yana zaune ta gefen gadonta yana latsa wayarshi. Tayi tsaye bayan nan tana kallonshi ba tare data cire doguwar hijabin jikinta ba. Don kuwa bayan wankan da tayi bata maida wasu kayan kirki jikinta ba. Karamar rigar shan iska ce a jikinta da bata gama rufe mata cinyoyinta ba, sai ta dora zani a kai. Ganin ita kadai ce a sashen nata ba wani yake je mata ba. Ya bita da kallo tun daga sama har kasa yana lura da yadda take kaucewa hada ido da shi. Yace, "wai ni wannan shan mur din da ake mun na menene? Na lura tun jiya kina wani jin haushina da kin yi mun magana. Akwai abinda na miki da ban sani ba ne?" Ta dan tabe baki tana kallon can gefe daya, "ni kuwa me kayi mun? Yaushe ma muka hadu da kai da har za kayi mun abinda raina ba zai so ba?!" Yayi murmushi yana kallonta kamar abinda tace din dadada mishi rai yake yi, yace, "to idan haka ne, zo nan ki zauna kiji wani abu." Ya fadi hakan yana daddabar kusa da shi alamun nan za ta zauna. Tayi tsaye cak tana kallonshi ta ki motsawa, maimakon ta je din sai tace mishi, "abinci nake son ci idan hakan babu damuwa." Ba shi take kallo ba, shi yasa bata ma san lokacin daya tashi daga inda yake ba har ya karasa gabanta. Sai data ganshi gab da ita sannan tayi kokarin juyawa, ya kama gefen hijabin nata ya rike gam, ya hanata matsawa ko nan da can. Yace, "to wai me yasa ne idan zaki yi magana ba za ki kalleni ba Nadiya? Kuma na tambayeki kin ce wai ba kya fushi da ni? A haka kike so in yarda dake?" Kokarin ya sake mata hijabi take yi, "to tunda nace babu wani abu ka kyaleni mana! Nace maka yunwa nake ji!" Ji tayi kawai ya zame mata hijabin ya yar, ta daga hannu a sukwane ta kare kirjinta tana kokarin durkusawa kasa. Ya sanya hannu ya jata cikin jikinshi ya rukunkume. Kanshi a cikin gashinta yake ce mata, "know what? Nima yunwar nake ji Nadiya, amma daga ni har ke yau ba zamu bar dakin wannan ba har sai kin fada min abinda na miki sannan!" Ganin babu Sarki sai Allah yasa ta sauko daga tsinin data hau ba shiri, ta hau magiya da kankan da kai. "Na rantse da Allah babu abinda ka min. Ka wa girman Allah ka kyaleni, don Allah. Yau fa ranar girkin Anty Shukurah ne ko ka manta?!" Ya kai hannu bayan wuyanta yana shafawa zuwa gadon bayanta, wasu abubuwa suka fara mata yawo a jiki da jijiyoyi. Jikin nata gabadaya sai ya dauki wata irin rawa kamar wadda lantarki take ja. Idanunshi a rufe, tunaninshi da kwalwarshi ba lokaci daya suke tafiya ba, shi yasa ma ya fara rasa zaren tunaninshi gabadaya. Wasu abubuwan yi yake, amma shi kanshi ya fara rasa sanin abinda yake aikatawa din. Sunbatarta yake, shafata yake, komi ma yi mata yake, amma duk da haka ji yake yi it's not enough. Cikin hakan yake ce mata, "kin manta cewa ku dukanku da zarar an gama karin safe shikenan kun gama fita daga girki? Yanzu kuwa lokacin Azzuhur ya shiga Nadiya, lokacinki ne. Don haka ki barni in fanshe takaicin kwanakin da na rasa na amarcina!" Maganar tashi ta so ta bata haushi ma, ta bude baki tace, "to ni na hanaka cin amarcin? Ko kuma ni ce na sabbaba maka hakan?" Sai ya dakata, ya kalleta da kyau da murmushi akan fatar bakinshi, "ai dama nace hakan yana damunki amma kika ce ba haka ba. Ana son mutum amma ana kaiwa kasuwa! Nadiya wannan hali naki sai ke. Amma dai a hakan kike burgeni." Ya juyata ta fuskanci gado, kafin ta ankare sai ta tsinceta tsamo-tsamo akan gadon shi kuma ya bi ta yayi mata rumfa. Abubuwan nashi neman wuce gona da iri suke, tuni sai ta hau magiya da neman hanyar tsira. Fadi take tana karawa, "don Allah don Annabi ka taimaka min kayi hakuri ka kyaleni. Wallahi Tallahi yunwa nake ji!" Yace, "ai mai rabani da ke yau Nadiya, sai ikon Allah. Ko kin yi zaton jiya ban ga irin hararar da kika dinga auna min bane? Kuma nasan duk cikin jin haushin rashin kwana a dakinki ne, don haka yau dai sai na wanke kaina a wajenki tas!" Sai hawaye shar! sharr!! Suka hau zarya a fuskarta, tace, "ka rufa min asiri, don Allah kayi hakuri. Wallahi ni ban harareka ba, in ma na harareka din cikin rashin sanine, don Allah kayi hakuri Abban Ammar!" Tana ta magiyarta da neman hanyar guduwa shi tuni ya gama yin nisa a al'amuranshi. Yace, "kin ji ma Abban Ammar kike ce min kai tsaye, ba Angon Nadiya ba! Ai wallahi yau dai sai na amsa sunan nan!" Daga wannan magana bai kara bata damar yin wata maganar ba, ya kara zafafa al'amuran nashi a gareta. Da ta samu ya saki bakinta daya damka da nashi cikin yanayi na fitar hayyaci, sai ta bare baki ta hau kwala mishi ihu. Da taga abin ba kanta sai ta fara hadawa da bugu. Abin dai nashi yaki raguwa sai ma kara kaimi da yake. Idanunta suka gama raina fata, ta saki wani irin kuka mai cike da tashin hankali da wata azaba ta musamman da taji tana ratsata. Sai ga ta ta hau kiran su Madam da Mama, a je a ceceta Habibu zai kasheta. Shi ai bai ma san kalar wainar da take toyawa ba. Ta yi Ala-wadai da yarda da maganganun Anty Lima da tayi, da take ce mata wai ai idan budurwa ta jima bata yi aure ba fatar budircinta na budewa ne ta yadda ba zata ji zafi ba sosai a first night dinta. Ashe duk kanzon kuregene? Ita kuma ta hau kan magana ta zauna daram, a ganinta bulis zata ci. Ashe Habibu shi zai kwashi bagas! Gashi nan yanzu yana bambance mata tsakanin aya da tsakuwa. Lokacin da yaji shi da kanshi yana neman wuce makadi da rawa, ya dakata, saboda tausayawa irin halin da yaga ta shiga ne na galabaita. Ya lumshe idanu wani irin murmushi mai tattare da sanyi da salamar jiki data zuciya daya dade bai samu a tattare da shi ba kwance akan fuskarshi. A haka barci ya daukeshi mai nauyi. Ita kanta tana ta jan shessheka da auna mishi harara barcin yayi awon gaba da ita bata ankara ba. Kiran sallar la'asar ya katse mishi barcin, ya tashi da sauri yana duba agogo. Allah Ya taimakeshi ranar baya da wani abu mai muhimmanci da yammacin, da lallai ya makara. Ya juya yana kallon yadda ta kanannade a cikin bargo ta rufa gabadayanta, fuskarta ce kadai a waje. Barci take a nutse tana sakin ajiyar zuciya akai-akai. Ga sawun hawaye nan a fuskarta da suka bushe. Yayi murmushi a tausashe yana girgiza kai, tunano irin rigimar daya san za su kwasa idan ta tashi. Ya lallaba ya shiga bayi cikin taka-tsantsan din kada ya tasheta. A gurguje yayi abinda zai yi ya fita. Lema-lema da sanyin ruwa da ta dinga ji a fuskarta ya sanya ta fara bude idanunta a hankali da suka yi mata nauyi. Suka yi face-to-face da shi, ya duka a kasan gadon yana kallonta. Wata irin kwalla ta ciko mata ido a take, ta mele baki da fuska tana shirin fara kuka, yayi saurin tashi tsaye yana kokarin boye dariyar data ciwo shi. Yace mata, "Masallaci zan je. Ga ruwa can a bayi na hada miki kiyi sauri ki yi wanka kafin ya huce." Ya bar dakin cikin sauri kafin ta kai ga mayar mishi da amsa. Sai data jima tana kara jinjina abinda ya faru a cikin ranta kafin ta tashi a hankali, ta lallaba da kyar ta shiga bandakin. Ta fito tayi sallah ta gama. Yunwa take ji matuka har wani jiri-jiri take gani. Ta samu riga doguwa marar nauyi ta sanya. Ta fita falon tana jin jikinta babu karfi ko kadan. Tafiyar kanta sai take nema ta zame mata wani aiki na daban. Sai ta sameshi already a falon, ya zuba dambun nan cike da faranti da farfesun kazar nan a gabanshi yana ta aikin durawa a ciki babu kakkautawa. Haushinshi kifi da kifi ya lullubeta. Ji tayi kamar ta kwace kwanon hannunshi ta hanashi cin abincin. Ta dai daurewa ranta bata aikata hakan ba, ta wuce kicin itama. Yace mata, "zo nan mu ci wannan da na zuba mana? Idan mun cinye sai ki karo." Tayi kunnen uwar shegu dashi. Anan cikin kicin din ta zauna ta ci kayanta don tsakaninta da Allah ko ganinshi ma bata son yi. Tana cikin cin abincin ya shiga da empty plates, ya ajiyesu a cikin sink. Ya daga firjin ya tsiyaya kunun aya ya kafa kai yana sha har da wani lumshe idanu. Harara kawai take jefa mishi, karaf suka hada ido da shi lokacin daya juya. Yayi murmushi yana ajiye kofin hannunshi, "wato harara ta ma kike yi ko? Lallai ma ashe ban gama goge rainin da kika yi mun ba har yanzu. Da alama ina da sauran aiki kenan." Ganin yana nufarta gadan-gadan sai ta mike tsaye sukwane tana shirin tserewa. Shi kuwa me zai yi in ba dariya ba? Yace, "farar kura! Ga tsoro ga ban tsoro. Dawo ki ci abincinki babu abinda zan miki. Lokacin da zan damkeki a hannuna Allah na tuba ai you wouldn't even see it coming. Besides, ke din ai amaryace da bata laifi. Don kin harareni ai ba wani abu bane!" Ta koma ta zauna din a darare, amma ta kasa sakin jiki ta ci abincin yadda ya kamata. Saboda ya sanyata a gaba yayi kikam, sai taji duk ta takura. Ta kalleshi a kaikaice tace mishi, "ni fa gaskiya ban cika son ina cin abinci ba ana kallona. Ai sai ka sa in shake!" Bai ce mata komi ba, taga yayi hanyar fita kamar tafiyar zai yi. Kafin ta sakankance ta ji ta a cikin jikinshi ya rungumota ta baya. Ya lalubi kunnenta yana rada mata, "madallah da ke Nadiya. You've made my day! Allah Yayi miki albarka, Allah Yasa munyi dacen samun yan biyu..." da wasu zantukan da suka yiwa kunnuwan nata nauyin ji. Ita dai tayi turus a zaune tana sauraronshi har ya gama fadin abinda zai fada, ya juya ya fita yana fada mata wajen tafsir da ake yi na yammaci a Masallacin dake makale da gidansu zai je. Ita dai bata samu sakewa ba sai data ji da gaske din ya fita, sannan ta saki ajiyar zuciya. Ta zauna ta ci abincin sosai da sosai. Data gama ta hade kwanukan ta wankesu duka. Sauran dambun da suka rage kuma ta barshi a cikin kular tunda dama ba wani na azo a gani ne tayi ba, wanda za ta ci da wanda zata kaiwa Ummah kawai ne. To kuma ga shi Habibun nata ya bi ta kanshi. Sauran yammacin ranar a kwance tayi shi tana jinyar jikinta. Don kuwa sai a lokacin ma take gane kalar ta'asar da Habibun yayi mata ashe ba karama bace. Ko motsin kirki tayi sai taji a jikinta. Sai can wajen Magriba sannan taji dawowar Ummah. Amma bata shiga bangaren nata ba sai da aka yi sallar isha'i. Data shiga tayi mata barka da zuwa, sai ta ja Ammar gefe suka zauna tana tayashi yin assignment kamar yanda ta saba. Ta kula yaron yana da rauni sosai ta bangaren lissafi, haka kuma fannin addini ma yana da mas'aloli da dama. Ganin kuma babu wani tsayayye dake bibiyar lamuran makarantar tashi yasa ita ta azawa kanta wannan nauyin. Tana taimaka mishi da spelling, da kira'a, har ma da haddar abubuwan da ake yi musu a duka Islamiya da makarantar boko. Da suka gama suka cigaba da kallon Fina-finan yara da ake nunawa a tashar Mbc 3. Kasancewar cikinta a cike yake tun bayan dambun da ta ci, bata ma tunkari teburin cin abincin ba. Tana nan Shukurah itama ta shiga falon, ta zauna a dan nesa dasu kusa da Hajiya Ummah. Magana take mata kasa-kasa duk don kada Nadiya din taji me suke cewa, ta tabe baki a kaikaice ta kara dauke kanta daga garesu don kuwa itama ba son jin abinda suke cewa take yi ba. Kamar ba zata gaisheta ba, daga karshe dai ta daga baki da kyar ta gaidata din, itama ta amsa a fuzge kamar wadda aka takurawa. Tasan ganin idon Ummah ne yasa ma ta amsa. Wajajen karfe tara ta musu sai da safe ta koma bangarenta. Sauran farfesun data rage ta cinye da kunun aya. Ta shiga bayi ta watsa ruwa kafin tayi shirin barci cikin pyjamas masu dan nauyi pink masu digon fari a jiki. Hadari ne a garin sosai ta san ba dadewa ruwa zai sauka. Sai da taje ta kulle sashenta kafin ta kwanta saboda kada Habibu ya mamayeta irin na dazu. Ila kuwa tana kwanciya ba jimawa, aka tsage da ruwa kamar da bakin kwarya. Ta kara shigewa cikin bargo barci mai dadi yayi awon gaba da ita. Kamar cikin mafarki kuma ta dinga jin wani abu na faruwa da jikinta. Ta fara bude idanu cike da magagin barci, tana kokarin fahimtar me ke faruwa. Fahimtar da tayi mutum ne kwance kusa da

Chapter 20 of 36