daga shagon.
Abaya ce a jikinta ruwan zuma da aka yiwa adon furanni ruwan madara. Tayi nadin gyalen a fuskarta inda ya fitar mata da fuskarta tayi round, kumatunta da lebunanta da suke a cike suka mayar da ita kamar wata Balarabiyar kasar Oman.
Ya kara gyara zamanshi yana kallonta, yadda take tafiya a nutse, hannunta daya dafe da wayarta a kunne tana kyalkyala dariya. Komi na Nadiya ya mishi. Bai san ta yaya, ko a wane lokaci Nadiyar tayi mishi irin wannan kamu na kazar kuku ba.
Ya bude murfin motar ganin tana kokarin wuceshi. Kawai ganin mutum tayi a gabanta sai kace wanda ya dira daga sama.
Tayi baya da sauri hannu dafe da kirjinta saboda yanda ya tsoratata. Da ta fahimci ko waye yayi mata wannan aika-aikar, sai ta ja fuska kawai tayi kokarin bi t gefenshi ta wuce, shi kuma yayi saurin sake shan gabanta. Ta sake juyawa ta daya bangaren, nan ma ya sake binta.
Sai ta cewa Rabi'ah da suke waya da ita, "zan sake kiranki Rabi'ah!"
Ta kashe wayar, shi kuma ta bi shi da wani irin kallo cike da kufula, tace, "lafiya?"
Ya langabar da kai gefe daya, "don Miji ya zo gaishe da Matarshi dama hakan ya taba zama laifi ne da za a ke tambayarshi lafiya?"
Ta ga idan tace ma zata tsaya bashi amsa rai kawai zai bata mata a banza, sai ta kankance idanu tace mishi, "ba ni hanya in wuce to!"
Yayi wani irin murmushi, "ko kuma ki shige mota mu tafi ko?!"
Ta ma rasa me zata ce mishi. Wannan abu na Habibun Hajiya Ummah nema yake yi ya wuce misali. Ta rasa ta ina zata bullo mishi kuma. Mutum a dinga yakiceka amma kana bin mutane sai kace wani guntun cingam?
Tace, "Malam ka bani hanya in wuce wallahi ko in tara maka jama'a a wajen nan!"
Yace, "kafin mu kai ga hakan ma zaki shige mota mu tafi..."
Ta daga baki zata mishi musu, ya hade fuska, "I am not asking Nadiya. Ki wuce muje kawai kafin in miki abinda ke zai tara miki jama'a anan wajen!"
Akwai wani abu can cikin idanunshi data hanga dake nuna mata cewa da gasken gaske yake, ba kamar ita dake cika baki ba da ban tsoro, shi kam idan ta kai ga hakan, zai aikata abinda yace din ba tare da bata lokaci ba.
Ta daga kafa ta nufi wajen motar tashi as if in a trance, kamar wadda wani maganadisu yake ja. Yayi murmushi cike da samun nasara, ya wuce ya bude mata gaban motar da kanshi ta shiga, ya mayar ya rufe.
Ya zagaya ya shiga, ba tare da bata lokaci ba ya ja motar suka dauki hanya.
Tuki yake yi cike da kwarewa da natsuwa a tattare dashi. Ta kurawa waje daya idanu tana kallo tun bayan shigarta motar. Shima kuma da yake tunda ya fara tukin bai sake nemanta da wani zancen ba sai abin yafi yi mata sauki.
Ya kaita har kofar gidansu yayi fakin. Ta bude motar ta fita abinta babu ko godi bare na gode. Tana jin lokacin da shima ya bude bangaren da yake ya fita, ya kira sunanta da wata irin murya mai sanyi da taushi data sanya ta dakata da tafiyar da take yi ta juya tana kallonshi ba tare da zuciyarta da gangar jikinta sun gama aminta da hakan ba.
Yace mata, "Gobe zan wuce Umarah, ba zan samu ko addu'ar Allah kiyaye bane a wajenki Nadiya?"
Tace, "idan kaje don Allah ka roka min Allah Ya yaye min wannan kidagar auren da aka kakaba min, ya koma kan mai so!"
Maimakon abin ya bata mishi rai kamar yadda taso, sai ma hakan ya bashi dariya. Yayi dan murmushi yace, "zan dai yi addu'ar Allah Ya baki ikon fito da wannan son nawa dake makale a cikin zuciyarki kina kokarin boyewa. Ya kuma kakaba miki son nawa ya zamana idan zan yi tafiya irin haka ba zaki taba iya jurewa ba!"
Tayi wani irin murmushi na bacin rai, tace, "son ka kuma? You wish!" Ta wuce gida abinta.
Shi kuwa har da komawa ya jingina da motarshi yana kara kallonta har ta shige gidan. Yayi ajiyar zuciya a hankali yana furzo da wani numfashin daga bakinshi.
Yara biyu matasa ya samu ya bude musu booth din motarshi yace su kwashi kayan su shigarwa Nadiya da su. Ya sallamesu kafin ya ja motarshi yayi gaba kafin ma su gama shigewa gidan don yasan kadan daga aikin Nadiya ne ta sanya su yo kwana da kayan nan.
Tuki yake yi wannan karon cike da tunani da sake-sake har ya karasa gida. A ranshi tunani yake ko ya Hajiya Umma zata ce idan taji cewa saboda Nadiya kadai ya daga tafiyar daya kamata ace yayi ta a yau? Da yanzu ya gama shan ruwa a Makkah. Amma idan ya tuna Nadiya, da yadda suka rabu da ita, sai ya tsinci kanshi da yin murmushi. Shi yasan ba zai taba damuwa ba idan ya kara daga tafiyar tashi ta yan kwanaki, batawa Nadiya rai da ganin tsiwar nan tata ma kadai sun isheshi debe kewa.
Tana ganin yara suna ajiye katan-katan din Maltina da madara peak ta ruwa da tarkacen kayan shayi har da su crates din kwai, duk kuma wai inji Habib, ta zabura tace musu su wuce su mayar mishi da kayanshi. AbdulBaqi yace mata ai tuni daya riga ya tafi. Ta rufe ido ta fara zazzaga musu masifar me yasa to suka amso kayan tun a farko? Tace musu tana bukata ne? Suka yi tsuru-tsuru a tsaye suka kasa gaba ko baya. Mama data ga haka tace musu su ajiye kayan anan. Ta dauki dari biyar ta basu, su kuwa suka ce mata ai tuni daya sallamesu suka wuce.
Ta kalli Nadiya da take jefawa kayan harara kamar su ne suka aikata mata laifin. Tace mata "sai ki dauke kayan ki kai daki ko?"
Ta wani turo baki gaba. Da kamar ba zata dauka din ba, sai kuma ta kira Amina suka fara jidar kayan suna kaiwa dakin.
Mama ta kalli yanda take ta guna-guni da bata fuska, tace, "Allah Ya kyauta miki Nadiya wallahi. Zan so in ga wannan zaman aure naki!"
Amarya dake aikin dama kokon da za a sha ruwa da shi tayi dariya, tace, "Mama ki kyale diyar nan taki da zurfin ciki, tana son kayanta ne kuma tana kaiwa kasuwa. Muna nan dake tsit zaki ji ta idan aka yi auren, ko motsinta ba zaki dinga ji ba. Watakila ma sai kin dinga nemanta da kanki ma sannan!"
Nadiya dake jinsu tayi caraf tace, "tab! Allah Ya tsareni wallahi!"
Mama da Amarya kam me zasu mata idan ba dariya ba?
Da aka nunawa Abba kayan da aka kai mata kuwa cewa yayi a kaisu dakinshi, haka aka sake jidarsu aka kai mishi. Ya dauki Maltinar nan da madara da ruwan gora ya kai kuryar daki ya ajiye, kwai yace matan su raba kowa ta dinga soyawa ita da 'ya'yanta idan an sha ruwa. Kayan shayin kuma yace a ba Nadiya ta dinga hada shayi tunda dama ma'abociyar shan shayin ce.
Daga fari ma da cewa tayi su Mama su raba ita da Amarya, sai da Mama din ta rufe idanu ta manna mata shirme sannan ta amshi kayan.
Washegari tana shago, ta dan bude datar wayarta tana duba halin da duniya ke ciki kafin su fara aiki.
A WhatsApp dinta ta kula wata sabuwar lamba ta tura mata sako. Ta bude cike da mamakin ko wanene? Sai ta ci karo da hoton mutumin nata, yana sauka daga jirgi. Yayi shigar wata bakar jallabiya wadda ta haska shi, gashin kanshi da sajenshi sun kwanta luf-luf gwanin sha'awa, ya dora farar hula a kanshi. A kasan hoton ya rubuta 'mun sauka lafiya. Nasan dai kina nan kina ta tunanina!'
Ta saki wani irin dogon tsaki har sai da Aramide ta juya ta kalleta tana tambayar lafiya? Ta girgiza kai.
Ta rasa abinda mutumin nan ke ji da yake da wannan confidence din. Ta fita daga WhatsApp din ma gabadaya. Tayi tunanin tayi blocking din lambar tashi ma gabadaya, sai kuma ta fasa daga baya.
Sai ta koma ta cikin messages ta zauna da kyau tana karanta dogon sakon da Abdullahi ya tura mata dazu da safe.
Sai jiya da dare sannan ta samu kwarin gwiwar kiranshi a waya ta sanar dashi abinda ake ciki tare da bashi hakuri. Saboda bata so yaji maganar a wani waje na daban. Ko babu komi sun yi alaka ta mutunci da shi, za kuma taso su rabu akan hakan.
Ya kuma saurareta da kunnuwan rahama, ya kuma nuna mata ya fahimta, ya kuma yarda da hukuncin Allah don haka ba shi data cewa. Hakan da yayi duk sai ya kara sanyaya mata gwiwa, har suka yi sallama dashi hakuri take bashi.
Shine ya sake tura mata sakon cewa kada ta damu kanta saboda shi dai tsakaninshi da Allah ya hakura da ita, ba don baya sonta ba sai don zai fi son ya tayata yiwa iyayenta biyayya. Shima har da kara yi mata nasiha da wa'azin muhimmancin yiwa iyaye biyayya da kuma biyayyar aure. Daga karshe yace mata ta tura mishi da account number dinta yana so ya bada gudummawarshi ta biki.
Tayi murmushi ranta cike da jindadin hakan. Ta tura mishi da sakon ta gode dai kwarai da gaske da fahimtar da yayi mata, amma yayi hakuri ta gode da addu'arshi ma a hakan kawai.
Ta kashe wayar tare da janyo Aramide ta zaunar da ita. Itama sai a lokacin take bata labarin auren da zata yi.
Don kuwa zuwa lokacin ta fara sakewa da lamarin gabadaya.
Aramide ta rungumota cikin murna, tace, "kai kawata! Amma na tayaki murna sosai da sosai wallahi! Amma shine baki fada min tun a lokacin ba?"
Ta dafe kumatunta tana kara jingina da kujerar da take kai. Tace, "to me kike so in ce Ara? Har ga Allah auren nan fin karfina aka yi. Kin sanni sarai bani da akidar wai dole sai auren soyayya zanyi, amma ko babu soyayyar dai at least ace an samu fahimtar juna da gamayyar hali. Amma wadannan dinma bamu dasu ni da shi. Kada kuma ayi zancen irin rigingimu da nake hangowa zasu iya faruwa anan gaba ta dalilin auren nan wallahi. Bana son abinda zai iya dawowa daga baya ya karasa bata dan guntun zumuncin dake tsakaninmu da Hajiya Ummah, dama ba wani mai kwari bane."
Ara ta dafa kafadarta, "ke wallahi kada ki wani sanyawa ranki damuwa, wannan fa ba komi bane. Don soyayya da fahimtar juna zasu biyo baya jazaman ne, kin ganki kuwa Nadiya? Wane namiji ne zai ce wai ba zai so ki ba? Ai karya ne. Zancen zumuncin su Madam kuwa ki barsu a yadda kika gansu kawai. Idan ma ta dawo ta cabe musu daga baya dai babu hannunki a ciki, shi tsuntsun da yaja ruwa dama ai shi ruwa kan doka. Ki cigaba da addu'a kawai. Wa ya sani kuma ta dalilinki zumuncin ya kara karfafa?!"
Nadiya ta ajiye gwauron numfashi, "I doubt. Amma don addu'a kam ina yi sosai!"
Tace, "yauwa, sai ki kara zage dantse abinki. Yanzu dai da me-da me ake shirya mana na bikin?"
Tace, "babu abinda za ayi, aure kawai za a daura shikenan. Hakan kuma ni yafi min dadi."
Ta dan turo baki alamun ba haka ta so ba, "to Allah Yasa hakan shi yafi alkhairi. Amma dai ai naso ace bikinki na cashe sosai da sosai!"
Ita kuwa ta tabe baki, tace, "ai bikin da ake so da doki shi ake cashewa!"
Ara tayi dariya tace, "lokaci ne ai. Lokacin da zaki yi naki casun saboda murnar auren wa zai sani?!"
Ta wuce ta cigaba da ayyukanta Nadiya na binta da kallo tana girgiza kai.
*
Sannu a hankali sai gashi azumi har an yi na goma sha daya kamar da wasa.
Ta fito zata tafi shago da misalin karfe biyu na rana. Kasancewar daren jiya an kwana ana yin ruwa yasa garin yayi luf-luf, ni'ima ta samu.
A kofar dakin Mama ta ci karo da Amarya da Mama din suna gyaran gero da barzar kwakwa. A gefe guda kuma su Fatima ne da Amina da Maryam, wata na bare dabino, wata na gyaran ganyayyaki da Nadiya ta rasa ko na menene, wata kuma na aikin daka mazarkwaila gata nan kifi-kifi, tana zubawa a cikin wani kwano.
Nadiya tayi turus tana kallonsu, "yau kuma aikin me ake yi ne haka?"
Amarya tace, "ai wannan aiki naki ne ke kadai, ki je ki dawo zaki sha mamaki!"
Tayi dariya, tace, "ni dai in tukudi ne zaku yi to a sanya kwakwa da dabino sosai a ciki fa, na fi son shi a haka!"
Mama tayi yar dariya, tace, "ai in dai tukudi ne har sai kin gaji da ci Nadiya, don kuwa wannan duk naki ne."
Tana shirin bata amsa sai ga AbdulBaqi yayi sallama ya shiga hannu riki-riki da leda, Amarya ta amsa ta bude tana ciro faifayen cukui da wasu karin ganyayyaki da itace. Nadiya ta kama baki, tace, "yanzu wannan tarkacen duk a cikin tukudi?"
Amarya tace, "wannan ai ba ma duka bane. Kin san mu da yake sana'ar gidanmu ce yin wannan tukudin musamman na matan aure da masu shayarwa da kuma amare, to duk nasan abubuwan da ake sanyawa. Ai gyaraki zamu yi da kyau amarya, sai kin amsa sunan naki na amarya da babbar murya!"
Ita sai lokacin ma ta fahimci ashe tukudin amare ne suke kokarin yi. Ta tabe baki ta musu sallama ta wuce.
Ta bar Lantana dake gefe daya tana bare gyada tana turo baki, "aikin banza aikin wofi! Allah sa uwar mai hada kayan mata ma za a ba mutum ya hadiya, aikin banza ne. Ita matar cushe ai bata daraja!"
Nadiya dai ta kada kai ta fita daga gidan abinta. Yadda bata tankata ba haka su ma babu wanda yace mata uffan.
Tayi tsaye a bakin titi tana jiran abin hawa. Sai kuma ta fito da wayarta daga jaka ta shiga WhatsApp. Kara dubawa take yi wai taga ko cingam din nata ya tura mata hotonshi daya saba tura mata a kowace rana.
Yawanci idan sun fita sallar la'asar a can yake tura mata, nan kuma din a Nigeria wajajen karfe biyu kenan lokacin da take tafiya wajen aiki. Sai ya tura mata hotonshi hade da maganganu na tsokana da neman magana, wasu lokutan kuma ya kan tura mata wani hadisi ko aya data dauki hankalinshi ne idan yana wajen tafsir.
Ko wanne ne dai daga ciki, bata taba tura mishi da amsa ba. Sai dai kuma a hankali, cikin rashin saninta balle yarjewarta, har ta fara sabawa da sakonnin nashi.
Lokuta da dama ta kan samu kanta da dariya ko murmusawa idan ya tura mata wasu hotunan da zai yatsine fuska, ko ya mata gwalo, ko ya kanne ido.
Gani take a girmanshi, da yadda ake fadinshi, kamar ba zai yi irin wadannan halaye ba. Amma sai ga shi yana yi mata hakan. Girman kan data fara ta'allakashi dashi sai ya fara wankewa daga ranta. Saboda wane mai girman kai ne zai iya yin abinda Habibun yake yi? Ta fara tunanin watakila duka fahimtar data mishi a baya, akasari ne na dan Adam kawai da kuma 'bad first impression'
Yau dai babu abinda ya aika mata. Haka ta je shago, bini-bini sai ta daga waya ta duba. Aka sha ruwa nan ma bata ji daga gareshi ba. Ranta sai yaki yayi mata dadi, abin ya fara damunta. Ta fara tunanin anya lafiya kuwa?
Tana shan tukudin da aka dama mata, wanda ya hadu fiye ma da yadda tayi tunani, don kuwa ya sha kayan hadi, ya kuma hadu da nono mai kyau wajen damun. Ta bude chats dinsu tana bibiyar sakonninshi, ta samu kanta da murmusawa kawai. Wani abu mai kama da kewa ya fara ratsata. Kawai sai ta kashe wayar da sauri tayi jifa da ita gefe daya.
Ita abin ma nema yake ya fara bata tsoro. Ta yaya tun kafin aje ko'ina Habibu zai sanyata zubar da makaman yakinta ne?
Hakan kuma ba shi ya hanata jan wayarta da sauri ba ta daga bayan kamar mintuna ashirin. Ta duba sakon da aka tura mata, ta ga shi dinne dai da take jira.
Shigar larabawa yayi yau, har da su lullubin nan da manyansu ke yi. Fadar kuma irin kyawun da yayi ma bata baki ne. Ta samu kanta da zama tana karewa hoton kallo na fiye da mintuna goma. Kafin kuma ta fita daga cikin gallery dinta da taga ya tura mata wani sakon ta kasar hoton.
'Nasan ke ma kina kewata Nadiya! Ina jin hakan har a cikin raina da ruhina da gangar jikina.'
Kuma da yaga bata mayar da amsa ba na yan mintuna, sai ya kara tura mata da,
'kiyi ta kauce-kaucenki dai. Kwanaki ashirin da tara ne suka rage. Na miki alkawarin sai bakinki ya furta min hakan a cikin kunnuwana!"
Ta saki wani wata yar dariya kawai tana girgiza kai, kwana ashirin da tara yace ko? Sun zuba ita dashi kuwa!
Ta kashe wayar tayi kwanciyarta.
24
Wajen karfe goma na safe ta tashi tana nade abin sallar data hau tana yin lazumi da yake kwana biyu ta tashi da fashin sallah ne.
Maryam dake zaune akan kujera tana kallonta, tace, "Wallahi Anty kin ji dadi abinki ke kam. Kinga azumi rabi amma har kin sauke Al-Qur'ani Mai Girma kin juya. Dama ni ce ke!"
Tayi dan murmushi, "to Maryam in banda abinki ai zage dantse ne yake kawo hakan. Ke ma idan kinyi kokari sosai, sai kiga kin ma zo kin wuceni."
Tayi yar dariya tace, "Anty kenan!"
Mama ta shigo dakin a daidai wannan lokacin. Tace, "yauwa Nadiya, ga abu can na ajiye miki a firjin zaki gani cikin gallons na ruwa, ki tabbata kullum kin sha kofi biyu safe da dare."
Ta yamutsa fuska jin hakan. Ita fa abubuwan da ake bata dinnan sun fara ci mata tuwo a kwarya. Mama da Amarya sun dage tun karfinsu gyarata suke so suyi, su basu san cewa shi gyaran sai ana dokin miji da aure ba sannan ake yin shi ba? Ko kuwa fada musu aka yi cewa zaman auren take muradin yi da mijin ne da zasu dameta da wannan gyare-gyaren? Idan kuma kace ba zaka sha ba Mama ta hau fada.
Yanzu ma Mama tana ganin yadda take tabe fuska da mele baki tace mata, "saura kuma in ga baki sha ba ko kuma ba kya sha kamar yadda nace kiga abinda zai faru!"
Ita sai abin ma yaso bata dariya. Ta girgiza kai kawai, Allah sarki Mama. Tana ta kokarin tayi mata abinda mahaifiyarta ma wadda ta haifeta ta kasa yi mata shi.
Tunda zancen auren nan ya motsa sau biyu ta kirata. Na farko shine lokacin data kira ta tayata murna dinnan har ta bita da fada da gori. Na biyun kuma sake kiranta tayi da gargadi da fadan ta fa kama kanta ta kuma mike tsaye tun karfinta. Tayi kokari ta tsaya tsayin daka domin ganin ta zama ta farko a wajen mijin da zata aura.
Ta koma lallashinta da tausarta, akan ta kwantar da hankalinta, ta dangwali arziki ta sha romonshi tunda har yazo har inda take ba tare data nemeshi ba.
Nadiya dai bin ta ta dinga yi da 'to' kawai har suka kammala wayar. Shikenan ta kashe bayan nan tana mai kara jaddada mata lallai fa ta nacewa Habib, kiran safe daban, na rana da dare daban. Haka kuma kada ta sanyaya wajen aika mishi da sakonni da kalamai na kauna. Abinda ya hadasu kenan. Babu zance ko tambayar ya tsarinta yake? Me take tanada ta kuma shiryawa rayuwar auren da take kokarin sanyawa kafa?
*
Ranar bayan an sha ruwa, Hajiya Ummah tana dakinta wanda aka tanadeshi musamman saboda shan iska. Waya suke yi da Madam wadda take fada mata irin nasarori da maganganu masu dadi da suke samu a wajen mutanen da take tunkara da zancen Habib.
Don a halin yanzu ma haka ta samu nasarar zama da Jagoran jam'iyyar da ita Hajiya Ummah take ganin da ita zasu yi tafiyar, ya kuma tabbatar mata da cewa lallai Habibun shi zasu tsayar a matsayin dan takara.
Ta kuma kara da shaida mata da cewa a yanzu haka, ta tashi mutane bila adadin, suna shiga kauyuka suna bada tallafi iri-iri, duk da sunan shi Habib din. Juma'ar da zata yi kyawu tun daga Laraba ake ganeta, tana kuma ganin cewa lallai sun gama samun nasara a wannan tafiya.
Hajiya Ummah tayi murmushi cike da jindadi, "shi yasa dama tun farko banyi kokonto akanki ba Zahra'u. Nasan lallai-lallai sai kin kai hakarmu ya cimma ruwa."
Madam ta saki wata yar dariya, "ai Ummah ba yabon kai ba, amma ni nasan duk wani buri da zan sanya a gaba, to hakika sai na cimma nasara a cikinshi. Don haka ki kwantar da hankalinki, in Allah Ya yarda nan da dan kankanin lokaci, Kaduna sai ta zama tamu. Idan kika rike hannuna kuwa, na miki alkawarin har Nigeria ma baki daya sai na sanya ta durkusa a gabanki!"
Murmushi take saki sosai, jin maganar da Madam din take yi. "Hakika da babu abinda zai kai hakan faranta min rai Zahra'u. Allah Yayi mana jagoranci dai."
Madam tace, "ameen." Kafin kuma ta dan dakata.
Sai kuma ta nisa, tace, "to Ummah ina zancenmu kuma ya kwana?"
Tace, "Zahra'u baki da matsala game da wannan ko kadan. Kamar yadda na fada miki tun ba yau ba, bana magana biyu. Idan nace zan yi, to zan yi din babu mai canza min shawara. Fili naki ne, babu kuma wanda zai hanaki shi da yardar Allah. Nan da dan kankanin lokaci za a damka miki takardunshi da komi a hannu!"
Madam tayi tsallen murna, "nagode sosai Ummah, Allah Ya kara Girma da daukaka. Ai ni tuni na gama hada komi ta bangarena, go ahead kawai nake jira daga gareku muje mu fara gini."
Murnar da take ciki ta hanata sauraren maganganun da Hajiya Ummah take mata. Itama data fahimci hakan sai kawai ta mata sallama ta kashe wayar.
Suna gama wayar Madam ta tashi ta hau tikar rawa a dakinta cikin murna da farinciki.
Kamun kafar data samu a wajen Hajiya Ummah yasa ta bi wasu shaguna dake kusa da filinta inda take so tayi gini, ta siya domin ta kara fadada wajen. Duk wani abu da zata yi, tuni ta riga ta gama tattarawa, an fitar mata da tsarin wajen, an tanadi kamfanonin da zasu kai mata kayan aiki da kuma wadanda zasu yi aikin. Kai tsaye rana daya sai aka je mata da labarin ai wannan waje data saya ba a wajen ainihin mai wajen bane, don haka zance ya tashi. Don kuwa mai waje yace ba zai sayar da waje ba. Aka mayar mata da kudinta.
Ta nuna musu zata iya kaisu kara akan wannan maganar tunda ta riga ta gama sayen waje, kuskuren data yi a yarjejeniyar sayen wajen bata sanya idan an yi abu kamar wannan ba zata iya shigar da kara ba. Saboda bata taba sanin irin haka din zai faru ba
Da taga dai babu Sarki sai Allah sai ta koma bin kafa wajen Hajiya Ummah. Wadda cikin dan kankanin lokaci ta samo mai wajen, Alhaji Tijjani, da kuma sanyawar bakinta ne yace zai sayar da wajen amma sai yayi shawara. A hakan ma kuma sai da Madam ta kara mishi da wani gida flat da take dashi a Kinkinau bayan ainihin kudin data sayi shagunan dasu.
An fi sati biyu da yin hakan har yau kuma babu wani cikakken bayani data ji daga garesu. Amma maganar da suka yi da Hajiya Ummah sai ta karfafa mata gwiwa sosai da sosai.
Ta ci wa wannan waje da zata bude buri fiye da tunanin mai tunani. Akwai kuma mutane da dama da suma suke jiran budewar wannan waje. Saboda bayan shaguna da wajen wasanni da zata bude, akwai wani bangare na daban da zasu bude wanda wannan waje, na musamman ne. Na manyan kusoshin Gwamnati ne da suka ci suka tada kai da nera. Ba zata bari wani abu yazo ya gittawa wannan buri nata data kwashe shekara da shekaru tana ayyanawa ba.
*
Ita kuwa Hajiya Ummah suna kashe waya, wata wayar ta dauko daga cikin drawer ta kunna. Kai tsaye ta shiga cikin jerin contacts dinta, ta dannawa wata lamba kira.
Tana shiga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 36