taki tashi.
Ta zauna a gefen gado tana ta sharbar kuka cike da takaici da bacin ran wannan rayuwa. Yau ga abinda tafi tsana da kyama a cikin rayuwar gidansu, wato daukar kwanan wata a kaiwa wata, ya faru da ita kiri-kiri tana gani, amma bata da halin tankawa. Shin dama haka mata suke ji ne?
35.
Yana dawowa sallar Asubahi kai tsaye dakinta ya wuce. Cikin sa'a ya samu ta bude dakin amma tana kwance tana barci. Da kamar ya tadata saboda yasan bata yi sallah ba, sai kuma yayi tunanin watakila ko tana fashi tunda yana kirge da kwanakinta dama. A yadda kuma ya san ta da rashin wasa da sallah, yasan mawuyacine ta makara da gan-gan. Don haka ya juya ya tafi nashi bangaren don shima ya kara dan runtsawa. Daren jiya kwana yayi yana saka da warwara ta inda yakamata ya bullowa wannan al'amari. Don ya kula maimakon abin ya fara yin kasa sai ma kara hawa da hau-hawa yake yi.
Sai wajajen karfe goma ya baro sashenshi ya fito. A farfajiyar gidan ya ci karo da motoci da escorts suna jiranshi saboda fita zasu yi da karfe goma din. Sai yace musu su dan dakata, ya shiga bangaren Hajiya Ummah ya gaisheta kamar yadda ya saba. Ta amsa mishi kamar kullum, kamar dai babu abinda ya faru daren jiya. Yayi mata sallama tana ta mishi fatan alkhairi.
Ya samu Nadiyar a zaune akan abin sallah tana lazumi. Kasancewar ta riga ta saba da gudanar da sallar walaha a dai-dai wannan lokaci a duk ranakun duniya, shi yasa koda bata sallah to sau tari ta kan nemi waje mai kyau tayi lazumi ko karatun Al Qur'ani mai Girma
Ta shafa addu'ar data gama yi, sai ta juya daga zaune din da take tana fuskantarshi. Murya a shake cike da rashin sukuni har zuwa lokacin a tattare da ita ta gaisheshi. Gabadaya sai ta kara bashi tausayi, ya taka da sassarfarshi ya karasa gareta, gabadayanta ya jata zuwa cikin jikinshi ya rungume a tsanake.
A haka din yake furta mata kalmomin, "tayi hakuri ta yafeshi, hakan ba zai sake faruwa ba yayi mata alkawari!"
Tayi kokari ta janye daga jikinshi a hankali tana ja da baya tare da girgiza mishi kai. Ya kyaleta din, amma duk da haka sai daya kama hannuwanta ya rike.
Tace, "kayi hakuri Abban Ammar. Amma ba zan iya yarda da kai ba a wannan gabar!"
Zuciyarshi ta karye, amma duk da haka sai ya dake. Yace mata, "kada ki ce haka Nadiya. Please have a little faith in me, ko yaya yake. Nasan cewa ban baki dalilai masu karfin da zasu sanya ki yarda da ni a take ba, amma don Allah wannan karon, ina rokon ki yarda da ni. Ki bani dama in gyara komi. Nasan ni nayi saken da har muka zo kan wannan gabar, amma zan gyara Nadiya. I promise!"
Hawaye suka shiga zarya akan fuskarta, tace, "ta yaya? Ta yaya zaka gyara iye? Tun ran gini tun ran Zane. Tun a farkon fari daya kamata ka yiwa tufkar hanci, baka yi ba. A yanzu da aka kawo kan wannan gabar kuma bana tunanin zaka iya yin wani katabus. Don Allah kaje kawai, wallahi a yanzu haka ganinka munana raina yake yi. Amma kaje na yafe maka hakkina da kuka shiga, ko babu komi ba zan so ka tashi a gaban Ubangiji ba a matsayin mutum marar tsayar da adalci a tsakanin iyalinshi!"
Ta juya da sauri ta shige cikin closet dinta tana kokarin rufewa, ya bi bayanta da sauri shima tare da rungumota ta baya.
Yace, "ina so ki san cewa duk duniya Nadiya, ba ni da wanda ya kai Ummah. Saboda a duk duniya, babu wani mutum mai karamci dana sani irin nata. Ta so ni, tana kuma so na fiye da yadda ni kaina nake son kan nawa Nadiya. Abinda zai sanya inyi musu da ita ba karami bane Nadiya, amma a kanki nayi, ina kuma kan yi. Saboda so da biyayyar da nake mata ba zasu sanya ni take miki hakki ba. Wanda nayi a baya ma ban ji dadinshi ba, kuma ina neman afuwarki akan hakan. Kuma abinda kike zargi bai faru ba, ban je ga wata ba a daren jiya, ban kuma dauki kwananki na kaiwa wata ba. Ba kuma zan taba yin hakan ba...!"
Ya juyo da ita suna fuskantar juna shi da ita, yayi kasa da muryarshi yana kallon yadda idanunta duk suka yi luhu-luhu.
Yace, "kiyi mun alfarma daya don Allah, kada ki kullaci Ummah a wannan abin. Don Allah ki tayani sonta da girmamata da yi mata biyayya. Na shaku da ita fiye da yadda na shaku da mahaifiyar data haifeni, zan kuma iya ce miki duk duniya babu wanda yasan halinta kamar ni din nan. Mugunta ba a jininta yake ba, all these abubuwan da take yi I promise you zata daina cikin dan kankanin lokaci. Idan kuma ta tashi son ki Nadiya, na tabbatar miki sai ta so ki fiye da ni dinnan a karan kaina!"
Anan sai ya sosa mata inda ya jima yana yi mata kaikayi, sai ta kalleshi a tsakiyar idanu tace mishi, "Abban Ammar duk kusancinku da ita da shakuwarku, ba zai taba kamo na wanda kake dashi da mahaifiyarka ba. Saboda wannan bond din Allah ne kadai yake sanyashi a tsakanin uwa da da kadai, shi kadai kuma yasan adadinshi. To ko ita din, ba huruminta bane ta sanyaka taka shari'ah da hakkin addini ba. Idan ma kuma tayi hakan, kana da damar taka kafa ka take umarninta, kuma ko a wajen Allah baka da laifi!"
Ya dan lumshe idanu yana dan girgiza kai, "I know, na sani Nadiya. Kiyi hakuri don Allah!"
Ta girgiza kai, "baka yi mun laifin komi ba ni, kawai ina tunasar da kai abinda na tabbata mantawa kayi. Iyayenmu wasu muhimman figures ne a cikin rayuwarmu da babu wani abu da zamu iya musanyasu dasu. A zance na gaskiya kuma kana shakulatin-bangaro da al'amarin Mahaifiyarka. Don Allah, don Allah Abban Ammar, ka daina hakan. Wallahi you've no idea yadda abinnan yake sanyani a cikin damuwa da tunanin me hakan zai zama makomarka? Ba lallai sai ka guji daya a cikinsu bane dayar zata san lallai kana sonta da girmamata ba, you can love and respect them both, a lokaci guda. Don Allah do this for us..."
Ta karashe maganar kwalla tana taruwa a cikin idanunta. Kallonta kawai yake tunda take magana ba tare daya iya cewa komi ba. Tsakaninta da Allah magana take saboda ta damu da shi, da halin da duniyarshi da lahirarshi take ciki. Yaji wani irin abu a tattare da ita irin wanda bai taba ji ba. Girmanta da so da kaunarta suka ninku a cikin ranshi ninkin-ba-ninkin, har ya rasa ina zai kai su.
Tunda yake a rayuwarshi, bayan Mami, baya tunanin akwai wani daya taba nuna damuwarshi akan halin da yake ciki da mahaifiyarshi. A kalaman Nadiya a yanzu kuma, sai ya dinga tsintar traces din maganganunsu shi da Mami din idan tana yi mishi nata zancen da nasiha cikin hikima irin tata da ribata.
Ya gyada kai a hankali, yace, "Allah Yayi miki albarka Nadiya, nagode da wannan tunatarwa taki. In Allah Ya yarda kuma, zan yi aiki da ita. Ina kuma fatan abinda ya faru a jiya shima ya wuce a wajenki?"
Tace, "ni ai na fada maka babu laifin da kayi mun."
Yace, yana matsawa jikinta sosai, "to idan hakane, dan bani lebbanki kadan mana inji ya suka kwana?"
Tayi baya da sauri tana kawar da kanta gefe daya, "kayi hakuri don Allah. Amma ba zan iya aikatawa wata abinda nasan idan ni ka min ba zan ji dadi ba!"
Sai ya saketa shima, ya ja da baya yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Barin nata shi zai fi a daidai wannan lokaci. Don kuwa shi kanshi yasan idan har ya sumbaceta din a yanzu, to fa ba zai iya barinta ba don wasa.
Yace, "shikenan Nadiya, na hakura. Bari inje. A sanyamu cikin addu'a please!"
A fili tace, "in shaa Allahu!"
A ranta kuma cewa take, 'addu'a ai kullum cikin yin ta nake, sai dai idan ban daga hannuna sama da sunan yin addu'ar ba!'
Ta bishi da kallo har ya fita daga dakin, kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali.
Ta sanya takalmi a kafarta kasancewar bata cire hijabin jikinta ba. Bangaren Hajiya Ummah taje ta gaisheta, cike da girmamawa da mutuntawa kamar yadda ta saba a kullum. Bata bari fuskarta ta nuna wani abu na daban ba, har ma ta hada da tambayarta ko tana bukatar ayi mata wani abu ne?
Ita gabadaya ma sai taji kunyar yarinyar ta rufeta. Tana so ta daga baki ta bata hakurin rashin kyautawar da ta yi mata jiya, tunda ita a karan kanta tasan ba dai-dai ta aikata ba, amma girman kai ya hanata cewa komi. Sai kawai ta ce mata bata bukatar komi, ta tashi ta haye sama.
Nadiya ta hau dinning ta zuba soyayyar doya da kwai da sauce din hanta, ta hada shayi ta sanya ciyawar shayin Victoria ta strawberry. Ta zauna ta ci abinda zata iya a nutse, ta kwashe kayan duka ta kai kicin inda masu aiki ke faman wanke-wanke da kokarin fara shirin dora abincin rana.
Don ta samu ta rage yawan tunane-tunane da take yi sai ta hau sama, ta shiga dakin Ammar ta shareshi ta gyara tare da fitar da kayan dattinshi ta ba masu wanki da guda. Ta sake dawowa falo nan ma ta kara gyarawa duka na sama da kasan, sannan ta wuce sashenta ta kwanta domin samun barcin da bai gama isarta ba.
***
Madam Zarah ta shiga gidanta a yammacin ranar Lahdi afujajan da ita. Hannu daya rike da jaka, dayan kuma ya sangalo gyalenta. Kitson attachment da aka mata ya sauka har gadon bayanta. Pencil skirt ne aka yi mata na kamfala da riga half bubu, amma duk da hakan bai hanata shiga falon ba a sukwane cikin sauri kamar wadda ake bibiya.
Sai kuma ta dan ja tayi turus ganin mijinta Alhaji Shehu da waya a hannunshi yana dannawa. Watanni fiye da uku kenan baya cikin Najeriyar gabadaya, ita dashi sai a waya kawai suke haduwa. Bai kuma sanar da ita zuwan nashi ba duk da cewa sunyi magana dashi a daren jiya.
Ta karasa wajenshi ta dan duka ta sumbaceshi a gefen kumatu kafin ta zauna kusa dashi.
"Yallabai, what a surprise! Ai ban san da dawowarka ba yau, da ban fita ba sam!"
Yayi dan murmushi, "afuwan my dear, tafiyar ce nima ta zo min kai tsaye shi yasa kika ganni yanzu din. Wannan sabon kamfanin da nake fada miki zan bude na energy drink aka samu wasu yan matsaloli, shi yasa na taho domin mu samu muyi tackling din matsalar da wuri."
Tace, "da gaskiyarka kam. Kana bukatar wani abu ne? Ban yini a gida ba don haka ko abinci ban samu damar yi ba. Amma zan iya sama maka wani abun da gaggawa."
Tun wani lokaci data kama mijin nata da yar aikinsu dumu-dumu akan gadon barcinshi, ta manna mishi hauka mai lasisi har da dauko wuka da cewa zata yanke mishi mazantakar tashi taga da abinda zai ke bin mata. Ya dai samu da kyar ta shawo kanta da bata hakuri kan cewa tsautsayine, bata kara daukar yar aiki ba.
Sai data sanya gardawa suka yiwa yar aikin data kasance wata Bakaniya lilis kafin ta sallameta. Ta gwammace gwara ta dinga yin girki da kanta, yan aiki kuma sai dai a kullum suje suyi mata ayyukan da za ayi mata su tafi, amma babu masu kwana.
Duk a dabararta na kada mijinta ya kyalla ido ya kara ganin wata a cikinsu ne. To in ma banda hayyata da jaraba irin ta namiji, mutum me mata kamar Madam Zarah me zai nema a wajen matan banza?
Yadda take kulawa da kanta da lafiyarta, duk watan duniya akwai ranaku na musamman da take warewa na zuwa spa kawai, ga gyara cikinta da wajenta da bata gajiya dashi. Shi yasa har kullum idan ka ganta sai kayi zaton bata kai adadin shekarun da take dasu ba. Musamman idan mijin nata yana gari, har soke harkokinta take yi gabadaya ta kasance a tare dashi. Duk dai don kada yaji kewar wani abu balle har ya kai ga kissima fita ya nema a wajen wata.
Bata san cewa namiji ba in dai mai halin bunsuru ne, mace ko uwar gyara da kayan mata za ta hadiya, su ko a jikinsu.
Don kuwa fitar nan da yake yi kasashen ketare babu abinda yake yi sai sheke ayarshi da matan banza yadda yake so.
Ya girgiza mata kai yace, "noo... Ban jima da sauka ba ai. Kuma na ci abinci a jirgi. Dinner kuma ki shirya sai mu fita mu ci a waje ko? Amma me ke faruwa ne? Naga alamun kamar kin shigo cikin damuwa."
Tayi ajiyar numfashi mai nauyi, "ka bari kawai Darling. Ina wannan arena da nake fada maka zan gina a Kaduna? Ina ta cin karo da matsaloli ne wallahi, ina tunanin kamar akwai wata a kasa, amma kuma ban san ta ina zan duba lamarin ba. A halin yanzu kuma ma ni Investors nake nema saboda budget din dana dauko babba ne. But I don't know who to trust."
Yayi shiru yana tunani, yace mata, "me zai hana ki barni inyi investing? Kinga hakan sai ya saukaka mana damar gabatar da sabon drink dinmu idan ya shiga kasuwa. Tunda akwai wajen events da kwallo a can, sai kiga mutane sun san shi nan da nan."
Ta saki murmushi cike da jindadi, "dadina da kai Yallabai, ba dai iya warware matsala ba cikin dan kankanin lokaci. Wannan shawarar taka na ji dadinta sosai da sosai fa! Bari inyi sauri in watsa ruwa, zan fito maka da duk tsarukanmu da muke yi, sai muyi maganar over dinner, yayi?"
Ya gyada kai, "of course!"
Ta duka ta kara sumbatarshi a kunci kafin ta wuce dakinta, wannan karon da kuzarinta.
Ya maida kallonshi ga wayarshi daya ajiye bayan shigarta falon, chat din da suke yi da yarinyar daya baro a kasar London ya bude yana kallon watsattsun hotunan data tura mishi yana sakin murmushi.
36.
Cikin yan kwanakin kewa duk ta bi ta dabaibayeta a cikin gidan nan kamar dai ita kadai take rayuwa. Habibun ya fita zagayen kamfen dinshi a Kauyukan dake kusa dasu fiye da kwanaki hudu kenan, Alhamdulillah kuma suna ganin nasara. Social media da su gidajen radio duk sun karade da zancenshi, duk inda ya sanya kafa kuma ya shiga jama'a ne ta kowane bangare ke dako da bibiyarshi suna nuna mishi kauna.
Ita da take a gida ba fita ba take yi, tana ta binshi da addu'o'in data saba yi a kowace rana.
Ranar Juma'ah bayan an fito Masallaci, ta shiga sashen Hajiya Ummah da kanta ta kamo hannun Ammar ta wuce bangarenta dashi. Gurasa tayi da rana, ta kuma fahimci daga Ammar din har Babanshi suna son ta sosai. Don haka ne in dai tayi, to ko bata ajiyewa Baban nashi ba shi sai ta ajiye mishi.
Suka zauna ita dashi suna ci a kwano daya, tana tambayarshi game da rayuwar karatunshi da mu'amalarshi da sauran yara cikin hikima da dabara. A ta haka ta tsinci zancen akwai wani yaro daya takura mishi a makarantar saboda ya fishi kokari, yana hanashi sukuni ta hanyar muzguna mishi tare da fara janye mishi abokanshi. Ranar nan har littafinshi ya yaga mishi.
A ranta ta yanke shawarar zata tuntubi mahaifin nashi game da zancen, in ta kama ma ita zata iya bin kanun zancen domin ta yiwa tufkar hanci tunda wuri kafin lokaci ya kure. Cases irin haka a hankali suke juyawa su koma bullying, sai kaga yaro mai kokari ya dawo dakiki saboda rashin samun sukuni a makaranta da kuma takurarwar abokai. Wanda hakan kan iya affecting dinshi emotionally, sai kaga yaro ya kasa yin abokai, ya zama socially inept.
Suna cikin yin hirar wannan sai ga mai aiki taje kiran Ammar din inji Hajiya Ummah. Nadiya ta dan bata fuska cikin rashin jin dadin hakan, shima Ammar din ga dukkan alamu bai ji dadin kiran ba. Amma bai yi musu ba ya tashi ya bi bayan mai aikin.
Ta bisu da kallo cike da taraddadi. Ba tun yau ba ta fahimci kokari ake yi a janye yaron daga jikinta, a hanasu mu'amala.
Yanzu haka kiri-kiri hirar da suke zama su yi da bitar karatu da suke yi an soketa saboda da sun zauna ne, zaka ga yar aiki a saman kansu, 'Hajiya tace lokacin kwanciya barcin Ammar yayi' ko 'Hajiya tace Ammar yaje tana son ganinshi'
Ita dai ta kasa fahimta dalili da manufar yin hakan. Idan Ummah ta rabata da Ammar ribar me zata ci ne? Saboda me?
Wadannan tunane-tunane da take yi sai taji ranta ya fara baci. Al'amarin nasu ya fara kaita bango kuma. Tun zuwanta gidan bata ga wani abu marar kyau ko na assha da tayi ba, amma kuma duk da hakan kullum yadda ake treating dinta kenan. Kamar wata wadda ta aikata wani gagarumin laifi.
Zuciyarta take tambayarta, to haka zata cigaba da zama ne? Ana takata duk yadda ake so, alhalin babu wani takamaiman dalili?
Abu daya Nadiya ta rike akida a cikin ranta, shine, hukunci kowane irine zata iya dauka matukar tana da laifi a cikinshi. Tana kuma yiwa mutum uziri idan taga yana hukuntata din.
A inda kuma tasan bata da kuskure kuma taga ana hukuntata, nan ne fa bata iya dauka. Don kuwa ko sama da kasa zata hade, ba zata dauki laifin wani ta kakaba a kanta ba. Ko ta karbi hukunci akan abinda bata aikata ba.
Shi yasa zaman gidansu ya wahalar da ita kwarai. Saboda a can, da gangan ake tsokanarta kuma daga baya azo a lakana mata laifin da ba nata ba. Ita kuma ga rashin iya daukar laifin da ba nata ba, ga rashin iya bada hakuri shima a laifin da bata aikata ba.
Ganin tunanikan nata suna neman jefata cikin wani yanayin na daban sai kawai ta dauki waya ta kira su Mama.
Abba ya dawo daga aikin Hajji lafiya. Gida ya cika dankam da mutane yan sannu da zuwa, kwana biyu da dawowar tashi amma har yanzu gidan da sauran yan sannu da zuwa basu tafi ba. Maryam ta hadasu da shi ta sake yi mishi sannu da zuwa, kafin ta kirata ta vedio call ta hadata da kowa da kowa dake gidan suka gaisa suka kuma ga juna.
Lallai da ake cewa lokaci babu abinda ya bari. A yan watannin baya har alwashi take sha iri-iri, akan cewa idan har ta samu damar barin gidan wannan, da ba don su Mama ba da sai ta shekare bata waiwayesu ba. Sai gashi a yau, babu abinda take so kamar ta bude idanu ta tsinci kanta a tsakiyar gidansu da dandazon yara da matan gidan.
Da zasu yi sallama ta cewa Maryam ta samu su ware rana ita da yaran gidan su je suyi mata yini kafin ta fara zuwa makaranta. Sun rubuta jamb cikin ikon Allah ta cinye. Yanzu Post utme zata yi sai kuma jiran admission.
Ta mata alkawarin in shaa Allah za tayi hakan, sai suka yi sallama daga nan.
Ta karashe yinin ranar cikin kiraye-kirayen waya da gaisawa da yan'uwa, da Anty Lima suka yi waya ta karshe. Ta ajiye wayar kan center table a nutse, ta koma ta zauna tana bin wayar da kallo.
Rabon da suyi waya da Maigidan yau kwana biyu kenan. Ta kira shi har sau biyu, amma tarin uzirirrika sun hanashi iya daga wayar. Balle ya samu damar dawo mata da kiran. Don haka itama sai bata sanyawa ranta lallai-lallai sai ya daga wayar ba, ta koma gefe abinta. Shawara take yi da canki-cankar ko ta sake kiranshi ne? Daga karshe dai ta tashi taje tayi sallar la'asar.
Ta karashe yinin ranar akan abin sallah tana karatun Al Qur'ani da yin lazumi. Kasancewar karshen sa'ar ranar Juma'ah lokacine mai tsananin falala, Nadiya bata bari ya kufce mata ba tare da tayi addu'o'i ba.
Cikin kwanaki biyun da suka biyo baya ta fara fahimtar kamar Hajiya Ummah bata jin dadin jikinta.
Ta fara lura da rashin cin abinci da take yi yanzu, sannan ta rage yawan yin zirga-zirga kamar yadda ta saba. Yanwancin lokuta zaka sameta ne a kwance ko a shingide, ga shi cikin dan lokacin har ta fara rama a fuskarta. Ubangidan ya dawo ranar Asabar da yamma a gurguje, ya sake juyawa ranar Lahdi tunda safe, don haka Nadiya bata tunanin ya kula da halin da Ummah din take ciki.
Ita kuma bata son shisshigi da tura kanta inda ba a yinta, ko don gudun kada a gwasaleta. Don haka ta rasa confidence din tambayar Ummah din ko bata da lafiya? Amma ta damu kwarai da gaske a cikin ranta.
Ranar Litinin ta tashi da azumi a bakinta kamar yadda ta saba. Ya jima da fada mata matsayarshi akan azuminta na nafila, yace ba zai hanata samun lada ba da neman yardar Allah. Amma dai bai amince mata da yin azumi ba ranar da take dashi, don kuwa bai yi mata alkawarin zai kauda kanshi daga gareta ba. Amma duk da cewa ranar girkinta ne, sai ta tashi da azuminta tunda dai ai baya gari.
Tayi sallama bangaren Ummah din da misalin karfe goma da rabi na safe, falon babu kowa sai TV da take ta aiki.
Tayi kokarin hayawa sama don su gaisa da Ummah, sai ta ganta tana kokarin saukowa.
A hankali take tako steps din tana sauka kamar marar laka. Daga yanayin tafiyar tata kadai ma zaka san cewa lallai bata da cikakkiyar lafiya. A kullum tafiyarta cike take da isa da takama mai dauke da wata irin haiba. Hajiya Ummah bata tafiyar salo-salo, kodayaushe zaka ji tana tafiya ne cike da sassarfa, mai dauke da nutsuwa da kuma alamun karfi. Amma yau duk babu wadannan a tattare da ita.
Data sauko, Nadiya ta tareta a tsakiyar falo tana gaisheta, ta amsa mata cikin yar karamar murya. Sai ta tsinci muryarta na tashi a cikin falon, tana furta, "Ummah ko ba kya jin dadi ne?"
Ba tare data gama tauna hakan a cikin ranta ba.
Tace mata, "lafiya lau" kawai, ta wuce kan dinning.
Ita kuma ta koma kan kujera ta zauna tana jan tasbahar hannunta cikin yin zikiri tana ambaton Allah. Lokaci zuwa lokaci kuma tana satar kallon Ummah data hada shayi baki ta sha. Ta ture kofin ta tashi, taje ta wuce Nadiya zata sake hawa sama.
Sai ga Hajiya Shukurah ta fado falon kamar wadda aka jefo. Ta ci kwalliya cikin doguwar riga ta leshi, don kyau kam tayi shi har ta gaji. Gashin nan an tamkeshi a keya da yake babu laifi tana da yalwar sumar kai, an daura kallabi a samanshi yadda ya fito da kyau. Dan gyalen nan ta yafo shi a kafadarta yadda kasan wata budurwace. Ita dai tasan ko Maryam ba zata yafa wannan dan gyalen ba.
Ganin Ummah tana kokarin hawa sama yasa ta karasa da dan saurinta tana kiranta, "Ummah! Ummah!!"
Sai ta juya tana kallonta a nutse. Ta ja tunga a gabanta kafin tace, "Ummah ina bukatar wasu kudine yanzu-yanzu, saboda abubuwan da muka saya jiya na kayan masarufi basu isa ba don haka dole yau sai mun kara sayen wasu."
Ta daga baki da kyar tace, "ki yiwa Zakari magana Shukurah."
Shukurah tace, "ok! Sannan jiya na fara miki maganar wata women leader da nake zargin fa kamar tana cin duga-duginmu ne. Ina bincike a kanta ne don in tabbatar, amma akwai yiwuwar tare take da kungiyar adawa, don naji daga bakin mutane da dama suna cewa bata aikin komai sai na zaginmu da yi mana batanci. Ina so ne idan har hakan ta faru, ki barta a hannuna. Don kuwa wallahi sai na sanyata yin dana sanin abinda tayi mana!"
Magana take ta zubawa, hankalinta ko bai kai ga yadda Ummah din take layi bane daga tsaye? Idanunta na budewa da kyar suna kara komawa su rufe. Nadiya tayi wuf ta tashi da sauri, nufinta ta karasa wajen ta fadawa Shukurah tayi hakuri da zancen wannan tukun, sai Ummah din ta samu zama ta huta.
Tana karasawa wajen, Ummah tana silalewa zata fadi, Nadiya tayi azamar tareta, suka tafi su duka suka fadi a kasan tiles din wajen. Allah Ya taimaka duk basu yi wata buguwa ba, amma dai da alamun Ummah ko dai ta suma, ko kuma tana kan hanya.
Tayi gaggawar tallabota tana kallon Shukurah
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 36