Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels NADIYA! WRITTEN BY JEEDDAH LAWALS Sadaukarwar wannan littafi na duk wasu 'ya'ya ne da suka yi hakuri suka jure wa duk wani yanayi da hali da rayuwa da iyayensu ya jefasu ciki. Suka mikawa Allah lamuransu kuma suke cigaba da girmama iyayensu, suke kuma yi musu uziri da kokarin fahimtarsu. Allah Ya jikan Iyayenmu, Ya gafarta musu kura-kuransu, Ya kuma yi musu kyakkyawan tukuici da gidan Aljannar Firdaus. Ameen! Tukuicin littafin NADIYA! Na ki ne, yar'uwata jinin jikina, Anty Zee. Allah Ya bar min ke, Ya kuma raya zuriya ameen. 'Bismillahir-Rahmaanir-Raheem!' Kaduna, Unguwar Sarki. Misalin karfe sha daya da rabine na dare, Nadiya na lafe a jikin bangon dan karamin dakinta, jikinta a dunkule a waje daya kamar kullin kaya, ta nade kafafunta yayinda ta sanya hannu ta zagaye gwiwoyinta dasu ta nutsa kanta a tsakankanin cinyoyinta. Kanta masifar buga mata yake yi kamar ana kada mata ganga. Ita kadai tasan yanayin da gabadayanta take a ciki, ciwon kan yaje mata da wani irin zazzafan zafi a cikin kirjinta daya sanya taji kamar ana mata suya ne a kirjin. Idanunta da suka kwashe tsayin mintuna suna digar hawaye, babu abinda suke mata face zafi da zugi, kada ma kuma ayi maganar yadda dakin ya dauki wani matsanancin zafi saboda yanayin garin gashi kuma babu wuta. Macece ita mai matukar dauriya, ba kananun abubuwa bane suke sanyata zubar da hawaye ba, amma a yawancin lokuta, lokaci dai kamar wannan, dauriyarta gazawa take yi. Allah kadai yasan iya lokacin data dauka a haka kafin sautukan dake fita daga dakin dake kusa da nata babu kakkautawa kamar an jona da lasifika, su dan sarara, sannan ta saki wata irin ajiyar zuciya. Ta dago kanta da fuskarta da tayi dashe-dashe da hawaye da zufa da majina, ta jinginar da kanta a jikin bango. Tana jin yadda suke sauke ajiyar zuciya, haka itama take sauke nata daya bayan daya. Har zuwa lokacin da suka gama abinda suke yi har ya tayar da ita daga daddadan barcin daya kwasheta. Waye yace wai jin sautin mu'amalar aure da mutane suke yi yana tasar da sha'awa? Ita kam zata so ganin ko wanene don ta fada mishi wannan kanzon kuregene. Don ita a bangarenta babu abinda hakan yake haifar mata sai sanyata tsanar abin da aure da ma mazan baki daya. To ma menene abin jin dadi ga diyar da zata ji mahaifinta da matarshi, going at it kamar wasu sex addict?!. Dan siririn tsaki ta saki tare da mikewa, tasan cewa ita da barci a daren ranar yau kuma shikenan sai na washegari idan Allah Ya kaimu. Ta dauki yar siririyar tocilan dinta ta haska, haske ya mamaye dakin. Dankwali ta dauka ta yafa a kanta, ta mike tsaye akan kafafunta da suka yi mata nauyi kwarai, ta daga labulen dakinta ta fita tsakar gida. Gidan da unguwar, dama duniyar gabadaya, sun dauki shiru a dai-dai wannan lokaci, ba kamar hayaniya da cunkuson jama'a da suka saba dauka ba. Ta shiga bandaki tare da kimtsa kanta. Duk da cewa bata yin sallah, hakan bai hanata yin alwala ba ta fita ta koma dakinta. Ta shimfida tafkeken abin sallah tare da daukar doguwar hijabi ta sanya a jikinta, zama tayi ta gyara murya, ta fara rero karatun al-qur'ani mai girma cikin tausassa kuma nutsattsiyar muryarta a cikin suratul-Aal_Imran. A hankali take rera karatun cikin karamar murya mai rauni, ta yadda ita kanta ba duka kalmomin ke shiga cikin kunnenta ba sai daidaiku, har ta gama ta shiga suratun-nisa'i itama ta gama, sannan ta ninke kafafunta ta daga hannuwanta sama, ta fara jerowa Allah kirari da kyawawan sunayenSa dari ba daya, kafin ta fara karanto mishi bukatunta na rayuwa daki-daki, daya bayan daya, cikin kaskantar da kai. Ta shafa wasu hawaye na cika mata idanu tayi kokarin mayar dasu, sai taji jikinta da zuciyarta sunyi sanyi a take, kuma taji kamar an dauke mata wasu gingima-gingiman kaya a kanta. Filo ta ja ta ajiye kawai ta dora kanta a kai ta dauki carbi ta fara ja. Ba ita ta samu barci ba sai gab da asubahi. Bata tashi sanin inda kanta yake ba sai da wani irin azababben kukan yaro ya tasheta kamar wanda ake cakawa wani tsini a jiki, tayi firgigit ta tashi zaune tana sakin ajiyar zuciya tare da karanto addu'o'i a fili. Sai a lokacin idanunta suka sauka akan karamin agogon dake dakin taga karfe bakwai da rabi, ta zabura da sauri ta tashi tana laluben zaninta na wanka da kuma kayan wankanta ta fita tsakar gida. Kananun yaran gidan dake zuwa makaranta har sun shirya cikin shirinsu na tafiya, yayinda wadanda ba a kai ga kaisu ba suna zaune a kofar dakin nata daga su sai dan feto da fuska dambare da kwantsa da busasshen koko da saleba. Bata bi ta kan kowa ba ta fada bandakin tsakar gida, duk cikin gidan, da dakunan dake cikinshi, dakin da take cikine kadai bashi da mahadin bandaki, kaca-kaca ta sameshi, sai data bata wasu kyawawan mintuna biyar wajen gyarashi sannan ta fara wanka a gaggauce. A sukwane ta fita ta fada dakinta ta fara shiri. Cikin yan mintuna kalilan ta fito cikin wata rigar buba ta jan material mai zanen furanni, ta dauki karamin yellow din gyale ta yana a kanta. Bakar jaka ta dauka ta watsa duk wasu abubuwan da zata bukata, ta zari bakin flat din takalmi ta zura a kafarta ta fita. Ta jawo dakin ta rufe da key shima ta sanya a cikin jaka. Dakin Mama ta shiga, ita kadai ta samu akan doguwar kujera, ta duka ta gaidata a tsaitsaye ta sanar da ita fita zata yi, Mama ta kalleta a nutse, tace, "yau ma ba zaki karya ba zaki fita Nadiya, anya?".. Dan murmushi tayi, "ai babu matsala Mama, zan samu abinci idan naje can". Mama ta yada kai, "to shikenan sai kin dawo, Allah Ya kiyaye Ya kuma tsare, ki kula da titi!". Ta girgiza kai tana dan murmushi ta juya ta fita da sauri. Tuni Abba ya fita duk da cewa dakinshi a bude ta sameshi hakan ya tabbatar mata da cewa ba nisa yayi ba, amma hakan ma ya mata dadi tunda dai babu wanda zai tursasasu ganin fuskokin juna a yanzu. Da yake gidansu ba a can cikin lungu yake ba, ba tayi tafiya mai nisa ba ta fita bakin titi. Kai tsaye napep ta tara ta shige. Karfe takwas da wasu yan mintuna tana kofar shagonsu dake cikin Unguwar Rimi. Babban shagone mai girma sosai, suna sana'ar cake da kayan makulashe irin su ice cream, doughnuts, special bread dinsu na banana da zuma da kuma yoghurt. Lokacin da taje ma'aikatan da suke musu aiki har sun jima da zuwa sun yi goge-goge wajen ya fito tsaf yana ta sheki, wasu kuma suna can kicin dinsu masu hada dough na doughnuts nayi masu baking din cake da cupcakes suna yi, ta bisu daya bayan daya ta gaidasu ta kuma duba yanayin aikinsu da gyara musu wasu abubuwa da suka kauce kafin ta shiga dan karamin dakin da take canza kaya da kuma hutawa idan bukatar hakan ta taso. Karfe tara suke bude wajen aikin, kasancewarta manager din wajen yasa bata cika shiga cikin tsarin ayyukan shagon ba, ta dai tsaya a supervising din abubuwan da suke yi da kuma masu yi. Sabon tsarin da suka bude cikin watan na herbal tea ne ma yasa take hadawa da bada odarshi da kanta saboda har lokacin basu kai ga samun kwararre a wannan fannin ba. Apron kawai ta daura a saman kayanta mai dauke da tambarin wajen aikin nasu, 'Diamond-Ara cakes and snacks'. Ta rataye jakarta a jikin hanger kafin ta fita daga dakin ta rufe ta sanya key din a jikin aljihun apron din jikinta. Shagon da yake babbane, zagaye yake da kujeru da tables masu kyau da quality, akwai wajaje da aka yi na musamman saboda VIP. Sai suka zagaye wajajen da gilasai, a waje daya idan ka shiga zaka samu leather seats green a zagaye da wajen, tv din kallo da aka hada games kala-kala saboda masu zuwa da yara wajen. Ta bi ko'ina tana dubawa da gyara wajen sai data tabbatar da cewa komi yayi yadda take so sannan ta tafi bayan kanta inda take yini. Kanta din ta Gilashi ce saboda anan suke showcasing duk abubuwan da suke yi. Nan da nan ma'aikata suka fara fito da abubuwan da suka gama, aka jera a kanta din saboda masu saya su ci anan, yayinda wasu suke daga can store suna wrapping wasu a cikin takarda su sanya a cikin jaka saboda masu yin order. Karfe tara suka bude shagon, kafin kace me kuwa wajen ya cika da mutane, yan aiki sai faman kaiwa da kawowa suke yi saboda kula da mutane. Su hudu ne a bayan kanta, masu kula da su cakes biyu, ita da wata Sakeenah suna zuba shayi a kananun kettle su mikawa Amaka ta dora akan karamin tray da kofunan tangaran ta dauka ta kaiwa tarin kwastomomi da suke zaune a jerin kujerun dake cikin falon zasu karya, ko kuma ta zuba a cikin dan dogon thermo-plastic kofi a sanya a wata rectangular jaka mai dauke da tambarin wajen aikin nasu a hada da bread slice ko duka ko kuma cupcake ko doughnut ko kuma duka, a kaiwa masu tafiya kasuwa ko ofis dashi. Kasancewar wajen da suke a gefen wata babbar ma'aikata yake wadda take da ma'aikata fiye da dubu biyu, ga manyan Makarantu na Firamare da Sakandare da kuma wata Institute ta koyon Kwamfuta, a bayansu kuma akwai babbar Coci da babban masallacin Juma'a, shi yasa a koda yaushe shagonsu baya rasa kwastomomi. Basu samu kansu ba sai wajen karfe sha daya saura kafin mutanen suka daga. Masu gyaran wajen suka je suka sake gyarawa, masu aiki kuma suka koma kicin aka cigaba da wasu batch din na kaya. Kafin su gama ta cire apron din ta makala a jikin hanger ta fita. Nan opposite dinsu wata babbar Rsstaurant ce ta Arabian Cuisine, sun riga sun saba da mai Rssaturant din sosai, Fatima, da kuma ma'aikatan wajen. Tana shiga suka fara gaisawa dasu, bata bata lokaci ba tayi odar abinda zata ci aka sanya mata a take away ta biya ta koma shagonsu. Dakin hutunsu ta shige ta zauna, ta tsiyaya shayi ta zauna ta karya a nutse kafin ta sake fita wajen aiki. Wannan karon decorating din cake da aka yi oda na Birthdays da Anniversaries ta fara yi wadanda aka riga aka yi baking. Lokacin da aka kira sallar azzuhur masu sallah sun je sun yi, suka fara amsar wasu Customaers din wanda yawanci meat pie da sansanyan kunun ayan da suke yi ya kaisu. Haka ranar suka yini busy kuma cikin ayyuka kamar dai yadda suka saba a kowace rana. Karfe biyar na yamma kamar kowace rana suka rufe shagon. Babu wanda ya tafi a cikinsu sai da aka kimtsa ko'ina. Tana bayan kanta tana lissafin da suka yi a ranar da shigar da komi cikin littafin da suke yi, daya bayan daya ma'aikatan na mata sallama har suka tafi aka barta ita kadai. Bayan ta gama lissafin ta bi komi nasu daki-daki tayi sorting komi saboda ayyukan washegari, ta duba abubuwan da suka fara yin kasa a shagon tare da daukar list don washegari ta bada a sayo, ko kuma ta shiga kasuwar da kanta idan ta samu sarari tunda washegari zai kama public holiday, watakila cunkuson shagon nasu zai ragu. Sai data tabbatar da komi ya kimtsu, ta kulle ko'ina ta kuma kashe duk wasu electronics kafin ta kulle shagon, sannan ta fita da leda mai dauke da kadan daga sauran kayan da basu samu sun sayar ba a ranar. A karamar farfajiyar wajen da take cin motocin da basu fi biyar ba, ta samu maigadin wajen yana sauraren radio. Nan ta mishi sai da safe ta shiga restaurant din su Fatima inda ta sameta cike da kwastomomi da yan aiki ana ta hada-hada kamar a lokacin garin ya waye. Ita kanta Fatimar sai a tsaitsaye suka gaisa, ta bata cupcakes da doughnuts wadanda zata kaiwa yaranta, ita kuma tayi odar soyayyar shinkafa mai kwakwa da gasasshiyar kaza aka sanya mata a leda, ta musu sai da safe ta bar gidan cin abincin. Mai napep ta tara ya kaita har kofar gida. A matukar gajiye take kwarai, kanta sarawa yake yi har wani jiri take gani. A haka tana daga kafarta da kyar ta shiga cikin gidansu. Tun daga bakin kofa ta fara jiyo hayaniyar yara da sautin hirar matan gidan tana tashi kamar a cikin gidan biki. Babu wanda zai yi tunanin wai magriba tana gabatowa a hakan balle ayi maganar hakura da hirar hakanan a nemi mafakar yin ibada. A soron gidan ta ci karo da su Fatima da sauran yaran gidan, kowa da kalar abinda yake yi, babu wanda ya daga kai ya kalleta ko ya nuna alamun yi mata sannu da zuwa, don haka itama bata bi ta kan kowa ba ta fada cikin gidan. Lantana da Salame, matan mahaifinta, suna zaune daga bakin madafi, hayaki da kauri sun turnike gidan gabadaya amma kowa aikin gabanta take yi, suna hira da shewa kamar wasu kananan yara. Tayi sallama a nutse ta wuce ta gabansu ba tare data kara kallon inda suke ba, kamar yadda suma babu wadda ta amsa daga cikinsu ko kuma ta kalleta. Tana basu baya, Lantana ta juya ta kalli Salame tana tabe baki tare da shunata da baki, "yan bariki an dawo daga yawon ta zubar!". Salame tayi wata yar dariya, "jibeta ko kunya bata ji bayan kowa yasan abinda taje tayi, sai a wani shigowa mutane gida ana hura hanci sai kace bamu san abinda ke wakana ba...!". Juyawa tayi tana kallonsu da idanunta da suka fara canza launi, "me kuke cewa?!", ta jefa musu tambayar cikin rawar murya saboda tsananin fusata da bacin rai da suka dirar mata anan take. Lantana tayi tsamo-tsamo tana raba idanu, sai ta hau kame-kame tana nade tabarmar kunya da bori, dama can yar kanzagin Salame ce. Bata samun kwarin gwiwar yin komi sai Salamen tana kusa da ita, kuma duk rashin kunyarta bata iya yi a gaban idon mutum. Salame ta watsa mata wani irin kallo kamar taga kayan banza, "yo! Ai ba gulmar mutum aka yi ba, kuma gaskiyarmu muke fada balle ace, ehe!". Ta gyara tsayuwarta, "shi yasa ai nake tambaya, me kuka ce?!". Ta wani kyabe baki, "ke bari kiji in fada miki, ba fa tsoronki muke ji ba ko kuwa don kinga ana miki shiru ne? To na fadi na kara, nace daga yawon ta zubar kike! Sai a fita waje a gama lalata, a dawo mana tsakar gida ana wani hurawa mutane hanci, to mun san komi!!". Dama ba tun yau ba tasan da kalar kazafin da suke jifanta dashi, taji a bakin mutane da dama. Maimakon ta nuna bacin ranta irin yadda Salame taso tayi, sai tayi kokari ta danne zuciyarta, ta kama kugu tana jefawa Salame din wani kazamtaccen kallo, tace, "da ke nake zuwa yawon tambadar hala?!". Ta wani zabura kamar wadda aka jonawa bakin wuta a jiki, "ba dai ni ba sai dai uwarki don abu ta kazarki! (ta dankara wani irin zagi). Ke har kina da bakin cewa wani yana yawon karuwanci bayan karuwanci da dadiro a kugunku ya kare ke da matsiyaciyar uwaki??". Kalmar ta matukar tabata, a zafafe ta daga baki zata mayar mata da amsa dai-dai da ita, ta jiyo muryar Mama a bayanta, "Nadia me yake faruwa ne?". Ta juya da sauri tana kallon Mamar jikinta har rawa yake yi saboda masifar bacin rai, tace, "nima ban sani ba Mama. Wai kawai daga shigowata ban san hawa ba ban san sauka ba suka hau jifana da zagi da munanan kalamai." Mama tace, "to kuma banda abinki Nadia don sun zageki sai me? Yau suka farane? Bai kamata kina biye musu ba don haka maza zo ki wuce daki, kinji ma har an fara kiran sallah." Duk cikin gidan, ita kadai ce take fada mata magana ta bi a take ba tare da tantama ko neman karin bayani ba. Yanzun ma bata iya kara cewa komi ba sai wani kallo data watsa musu, ta juya ta wuce ciki abinta. Dakinta ta bude ta shiga, tasan maganar bata kare ba, Abbansu yana dawowa zata dawo sabuwa kal. Tana jiyo Salame tana yiwa Mama ihun, "dama ai dole kice ta daina biye mana tunda ga mahaukata kamar ki!,' Mama dai bata tanka musu ba ta juya ta wuce dakinta. Lokacin data fita bandaki don kimtsa jikinta tunda ta samu tsarki, har lokacin su Lantana abinda ya faru suke maimaitawa. Salame ta daga murya yadda zata jiyota sosai tana fadin wasu maganganu marasa dadi, bata ce musu komi ba sai kwafa da tayi ta shige bandakin kawai. Ranta ya kara baci data samu bandakin kaca-kaca kamar anyi shekara da shekaru ba a wanke shi ba. Ta gama sallar isha'i, tana zaune akan abin sallar tana lazumi, ta ji alamun karar mashin din Abban nasu. Yaran gidan duk suka dauki shewar barka da zuwa suna mishi, kasancewar babu wuta yasa hayaniyar tasu ta karade gidan. Gabanta ya fara bugawa sama-sama saboda tasan rigimar da Mama ta samu ta kashe da kyar ce zata dawo sabuwa dal. Ila kuwa, tana jin karar lokacin daya bude dakinshi ya shiga. Tana nan zaune tana saurarenshi har ya shiga bandakinshi domin watsa ruwa, tasan hayaniyar yara ce ta hanata jin motsin wankan da yake yi, amma da ace dare ya tsala ko kuma asubahi ce da sai ta ji. Tana dai jiyo hayaniyar su Salame da Lantana suna kara maida yadda aka yi. Yana kuma fitowa daga wanka suka hau kora mishi bayani, babu ko duba da cewa bai gama hutawa ba balle a kai ga maganar cin abinci. Yayi shiru yana saurarensu har suka dire aya, tana jiyo sautin muryarshi cike da fushi lokacin da ya ba Salame umarnin taje ta kirata. Ko cikakken minti daya ba ayi ba kuwa sai gata ta banko kofar dakinta babu ko sallama, tayi mata kerere a daga bakin kofar tana watsa mata wani kallo na rainin hankali, "kije ana nemanki!" Ta furta hakan cike da gatsali wanda ya kara sanyayar da gwiwar Nadiya din. Amma tayi ta maza ta matse don ma kada ta gama gano abinda ke cikin ranta. Sai dai fa ayi duk abinda za ayi a gidan don kuwa she wouldn't go down without a fight! Nadiya ce fa!! Ta tashi tsaye tana watsawa Salamen kwatankwacin irin kallon da take mata, ta gefenta ta ratsa ta wuce ba tare da ta tankata ba. Tana ji ta biyo bayanta tana fadin maganganu marasa dadin ji da daukar alwashi iri-iri. Tayi kunnen uwar shegu da ita, can a kasan ranta tana furta addu'a iri-iri, tana kara maimaitawa, wai Allah Yasa ta yiwa Abban nasu kwarjini ya ki yi mata ta'asar da tasan an shirya mata. Tayi sallama a dakin a nutse, ta durkusa a gabanshi tana mishi sannu da zuwa, yayinda yake zaune akan kujera mai cin mutum biyu, Lantana a gefenshi tun kayan data sanya da safe data tashi barci sune a jikinta bata canza ba, itama Salamen kuwa duk zani ce ta tarda muje mu. Warin hayaki kawai suke yi duk sun cika dakin da hamami. Da kyar ya amsa gaisuwar yana jefa mata wani irin wulakantaccen kallo, "me matana suka miki da zaki far musu da rashin kunya da maganganun banza dana wofi? Wai ke ba nayi miki shamaki da su bane?" Ta daga kai tana kallon mutumin da ke amsa sunan mahaifi a wajenta. Amma mahaifi ko kuwa dai _sperm donor?!_ Don kuwa dai ba haka mahaifa suke ba. Ba haka iyaye suke treating 'ya'yan da suka haifa ba. Da ba don tana da tabbaci ba daga Mama wadda tace mata lallai shi din mahaifinta ne, kuma tasan Mama bata karya ko da wasa, to wallahi da cewa zata yi ba shi bane ya haifeta. Kila ma har wasu daga cikin iyalan gidan. Tace, "Baba ina fa dawowa daga wajen aiki kawai suka tareni da maganganu da zagi, har suna kiran mahaifiyata da karuwa" Budar bakinshi sai yace, "to dama mecece idan ba karuwar ba?!" Sai tayi duf kamar an dauke ruwan sama. Yayinda shi kuma ya rufe idanu ya fara zabga mata ruwan fada, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba. Zagi kuwa ta uwa ta uba, kai kace sa'arshi ce ita din ba wai diyar shi ba. Duk yadda taso ta daurewa ranta ta danne kukan da yake cinta, gazawa tayi, dauriyarta ta kare, murya cike da rishin kuka take cewa, "ai dama ba so na kake yi ba, kafi girmama matanka akan 'ya'yanka. Shi yasa ba zaka taba iya tsayawa ka kwatanta adalci ba. Idan ka so adalci ai kamata yayi ka fara tambayata abinda ya faru ne, ba wai ka hau min fada ba haka kawai!" Aikuwa nan ya kara harzuka, ya fara fadin wasu irin maganganu marassa jin dadi, har da cewa shi wallahi da haihuwar diya irinta gwara ma babu, "mutuniyar banza mutuniyar wofi! Ni zaki zauna ina fada kina fada saboda kin maidani sa'anki? Yar iska kawai, banza, bari ki gani...!" Ya zabura ya taso da niyar bugunta, Salame tayi saurin rikoshi wai tana bashi hakuri, "haba Malam da girmanka ina kai ina biyewa yara marassa kunya kuna ja'in'ja? Don Allah kayi hakuri kada kayi fushi. Ni dai kawai na kawo maka maganar ne ba wai don

Chapter 1 of 36