ta sake shi tana ta godiya, yaqe kawai yake haka ta debi abincin ta suka koma parlour ta na ci ta na sake nuna masa dalilin da ya sa take son aikata hakan, Wanda shi Sam be dauki hakan a Wani babban dalili ba Banda takurawa abinda zata haifa da Sanya shi cikin damuwa da baqin ciki kamar yanda ta rayu a cikin su saboda yayar ta ta.
A kwana a tashi yau cikin Rasheedah da Sakeenaa ya shiga watan haihuwar su wato watanni tara cip2, wanda Sakeenaah ko alamar naquda bata ji, amma Rasheedah kam tin kwana biyu da suka wuce take fama da ciwon baya da mara, yau abun ya tsanan ta, cikin taimakon Allah Auwal ya kaita asibitin da ta saba haihuwa,bayan gumurzu da artabu a d'akin haihuwar ta sillub'o diyar ta mace mai kama da ita sak kyakkyawa masha Allah, labari ya iske ma su Sakeenaah, inda cikin zumud'i ta hau girke2 da shirin zuwa asibitin dan ganin jinjirar, Adnan kamar ya hana ta amma dai ya yi shiru, dan bai son ya b'ata mata rai a wannan stage d'in,haka ta gama ta shirya ya kaita, da sallama ta tura qofar suka shiga tare da Adnan, Rasheedah na bud'e idon ta ya sauka akan cikin Sakeenaah, wani uban ashar ta saki sannan tace
"Me nake gani kamar ciki a jikin ki Sakeenaah?"
Adnan cikin qasaitaccen murmushi yace,
" kwari kuwa, da yake Allahn da yake bayarwa ba ta hannun oo yake miqa abun ba sai gashi muma ya bamu,"
Sakeenaah ce ta dan dungure shi da hannu kan ya yi shiru , qarasa shiga suka yi,aiko Rasheedah ta had'e fuska, tana sababin ita bata son gayya haba abu a dami mutum daga haihuwa sekace ya yi shela? Ba wanda ya kula ta, Sakeenaah ta had'a mata tea mai kauri ta zuba mata farfesun naman kaji da yasha dankalin turawa, carrot, da green beans da kayan qamshi nan take wajen ya kuwa kaure da qamshi, yawu Rasheedah ta had'iya sannan ta leqa kwanon, tana miqa mata ta amshe tana wani yatsina,ta hau ci kamar mayya, sai Wani zaro ido take, dariya Adnan ya kunshe, Sakeenaah ta harare shi, Auwal ne ya so magana shima tare da yin dariya Sakeenaa ta hana da ido, haka suka qunshe dariyar su, har ta gama, ko kwana basu yi ba aka sallame su dan Suna cikin qoshin lafiya ita da jinjirar.
Yau kwanan Rasheeda hudu da haihuwa, Sakeenaa ta tashi da matsananciyar naquda mai tsananin azaba, gaba d'aya Adnan ya rasa jarumtar shi da kullum Sakeenah ke Kiran shi da JARUMIn ta kuka ya ke wiwi kamar shi ne ke naqudar, tausayin ta ya gama ragargaza naman jikin shi da tinanin shi
Bangaren Sakeenaah kuwa........
Ku d'an Jira ko zuwa anjima mun ji mi nana ka hwaruwaaaa....
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 12:
Wata iriyar wahalalliyar naquda Sakeenaah ke yi,ta wani fannin ta sanya matsanancin tsoro da fargabar shin zata rayu da abinda take ta fata Allah ya bata shekara da shekaru ko Kuma mutuwa za ta yi? Wannan dalilin ne ya janyo jinin ta ya yi bala'in hawa, ba abinda take sai addu'o'i, wanda kusan rabin addu'ar tana nemar wa kanta rahamar Allah ne, sai kuma daidaito a tsakanin zumuncin ta ita da yayar ta, anyi inducing din ta kafin ta samu haihuwa, kukan jaririyar su ne ya karade ko ina, na dakin har da Wani sashe na asibitin ma.
Dik halin nan da Sakeenah ke ciki Adnan na gefen ta ya na riqe da hannun ta ko yatsina fuska ta yi sai ya mata sannu,in ko ya ga hawaye a idon ta na gangara haka Shima nashi idon zai ta zubar da ruwa addu'a kuwa bai San Iya adadin abinda ya roqar mata ba da abinda zata haifa, sai da naqudar ta taso gadan gadan ne aka tada shi d'aga wajen ta ya tsaya a gefe, ma'aikatan lafiyar suka duqufa dan taimaka mata ta haihu.
A lokacin da kukan jinjirar ta su ya shiga kunnuwan shi kuwa rikicewa ya yi da murna da kuka, ba b'ata lokaci ya dora goshin shi a qasa dan godiya ga Allah, ya na d'agowa ya je jikin gadon ko gama gyara Sakeenaah ba a yi ba ya rungume ta ya hau sumbatar ta yace,
"Sannu my love dama na fad'a maki ke Jaruma ce, kin ga qoqarin da ki ka yi ko?Allah ya miki albarka, Masha Allah Atiyyah (Kyauta )ta iso Allah ka raya mana ita da imani,ka ba maihaifiyar ta lfy, ni kuma ka qaran arziqin kula da ita,"
Murmushi Sakeenaah ta yi mabayyani, bayan an dora mata yarinyar tasu a jikin ta ta kalle ta ta sake murmusawa a karo na biyu sannan ta ce,
"Tabbas Ablah(cikakkiya daga kyaun halitta) ta iso, Masha Allah ka ga yarinyar nan ba inda ta baro mu,"
Ta daga kai tana kallon mutane hud'u dake dakin, Doc. Midwifes biyu, da mijin ta Adnan, dan ta samu tabbacin maganar ta, gaba dayan su kad'a kai suka yi cikin yarda da maganar ta sosai,
"Tabbas wannan gaskiya ne madam, barakallah yarinyar nan ta na da kyau anya mun tab'a karbar kyakkyawar haihuwa irin wannan kuwa?" inji likitan,
"Gaskiya tinda muke bamu taba karbar haihuwar kyakkyawa irin wannan ba, kalar ta daban ne, Allah ya raya maku ita da imani," in ji d'aya d'aga cikin midwifes din,
" Ameen"
Suka amsa dika, nan take Adnan ya karbe ta ya mata addu'oin da suka zo a sunnar Annabi Muhammad ana yi wa jarirai, sannan ya miqa ta ga Sakeenaah ta tauna dabino ta bata, nan danan ko ta tsotse shi tass, tana gamawa aka bata nono ta sha, sannan Doc. Yace su bada ta ai mata wanka a kawo masu ita, dai dai nan Mama da ta gaji da Jira a bakin qofa ta shigo, itama ta na ganin yarinyar sai da ta yi sujjada dan godewa Allah, sannan tace a basu su dika su tafi ba maganar wani wankan asibiti tinda sun goge ta tas, haka kuwa aka yi Sakeenah da baby na gama cika awannin da ake bayan an haihu a asibitin aka sallame su suka yi gida, gidan ta aka wuce da ita, dan basu shirya tafiya wankan gida ba, Adnan tuni ya sanar da ita baya so, shi a barshi komai a nuna masa zai mata Mama ta ce inaaa zaman biqi ba aikin namiji bane, ya dai bari a mata anan d'in tinda baya so ta je gidan ita ta zauna mata dan Maman ta kula da gaske baya son ta yi nesa da shi,suna isa kuwa ya daura ruwa a qatuwar tukunya, Mama ta shiga ta mai sannu tana tsokanar shi angon qarni, yana sunkuyar da kai yana shafe qeya, fita ya yi yaje d'aki, ya isko Sakeenaah na ta bacci, tea ya hada mai kauri ya tada ta ta amsa tasha,su Shamsiyya kuwa dama ba yau suka Saba ganin yanda yake wa matar tashi hidima ba, Adnan mutum ne da ke kyautata wa matar shi kwatankwacin yanda take kyautata masa koma a ce fiye da hakan.
Kitchen ya sake komawa ya bud'e fridge da freezer dan ya tabbatar in akwai komai da suke da buqata ko Kuma akwai buqatar qarowa, ya na tsaye ya na nazarin wajen ya hango wata roba da aka shaqe da farfesun kayan ciki dakkowa ya yi ya bud'e ya ji yanda qamshi ke tashi Shamsiyya ya kwalawa Kira ta zo cikin hanzari ta durqusa ya miqa mata tare da bata Umarnin ta dumamawa Sakeenaah.
"To uban gida na ni ai da Ina Jira in ka fita ne ma in sama mata abinda zata ci, amma tinda ga wannan shikenan,"
"Kar ki damu a dumama wannan din ma ba komai, anjima sai a yi sabo,"
Mama na can na wanke jinjira, shi Kuma ta cikin matar shi yake, wata tukunyar ya gani ta tafaso ya ji qamshin abubuwan be tab'a Jin irin shi ba, tambayar Shamsiyya ya yi menene wannan? Amma dai ba matar shi za a bawa ta sha ba ko?
Murmushi ta yi sannan ta ce,
"Uban gida na wannan ai ba na sha bane, na zama ne, ruwan wanka tinda dama akwai na zafin a tolas d'in ku ba se an d'ora ba shine Hajiya Mama da ta zo se ta dora wannan d'in, tinda cikin Uwar d'aki na ya Kai wata takwas Hajiya Mama ta aiko da su"
"To amma dai ba a tafashen zata zauna a ciki ba ko?"
"Ah ahhhh Uban d'aki na, se ya huce daidai yanda zata iya zama"
Sanda aka gama dumama farfesun Adnan da kan shi ya karb'a dan ya Kai mata, ruwan tea Mai kauri da ya sha kayan qamshi Shamsiyya ta dafa ta sake had'a mata ta d'ora masa saman trey ta bashi, ya na Kai mata kuwa ba b'ata lokaci ta gyara zaman ta a saman gadon,yunwa ta ke ji sosai dama, sannu ya yi mata ya zauna gefen ta ya fara bata a baki be bari ba sai da ta qoshi sosai.
Doc. Ya bada Umarnin kar a sa mata ruwan wanka mai zafi sosai saboda hawan jinin ta dan haka ruwan da baida zafi Mama ta had'a mata ta taya ta wanka suka fito, Adnan na can d'ayan d'akin d'auke da jinjirar ya na ta kallon ta Cike da so da qaunar yarinyar,Kafin awa uku Baby da mama sun yi fes sun fito shar da su.
Adnan da Mama waya suka dinga yi wa 'yan uwa da abokan arziqi Suna Sanar da haihuwar, cikin qanqanin lokaci gida ya cika da dangi da ke kusa da su both na Adnan d'in da Sakeenaah,har su Rasheedah sai da aka sanar wa ta hanyar Kiran Auwal da Adnan ya yi amma daidai da Allah ya raya bata San ta ce ba, ta dai tambayi abinda aka haifa aka Sanar da ita, can se ta kyab'e baki sannan ta cewa Auwal da ke mata albishir d'in haihuwar,
"To da ka ke Wani fad'a min barin tawa jinjirar zan na tafi wajen tata jinjirar kenan ko me? Ni fa bana son jaraba haba"
Kallo Auwal ya bita da shi, dan yanzu abin nata ya d'auke shi a matsayin bugun mugun baqin aljani ba yin kanta bane, magani ya Kamata ya nemar mata ko Allah zai sa a dace.
Babyn Rasheedah taci sunan Farhah, bayan kwana bakwai itama Sakeenaah babyn ta taci sunan Mama, Haleema, inda Baban ta ke kiran ta Atiyyah, maman ta ke kiran ta da Ablaerh, Mama tace wannan sunan sai su ita ba ruwan ta Hali dubu zatana kiran takwarar ta, Abba yace Matas zai na kiran masoyiyar shi, Sakeenaah kam sai dai tai dariya, domin gata da so ba wanda bata gani wajen miji da iyayen ta, ga shi Kuma 'yar ta ma ana nuna mata soyayya Mai qarfin da ta fi wadda ake mata
" Mama ya kamata ki je wa Rasheedah, kin ga zaman da kk min zai dad'a ja min qiyayyar ta, amma ki hakuri inna Fad'i ba daidai ba,"
"Zan tafi na je mata, amma da na je ba jimawa zan yi ba zan koma gidana tinda kin ga ita haihuwa ta uku ce fa ta San Kan komai,ke din ma tinda dai ga masu aikin ki dattijai biyu da Shamsiyya sun Iya komai Suna da amana Suna qaunar ki ga kuma mijin ki da yake Jin zai iya komai ma da kan shi dik za ku Iya kula da wannan mai manyan idon, Rasheedah kuwa tin da ta haihu na je wajen ta ta nuna bata buqata ta, amma shikenan ai bana biye mata ba, zan je d'in kamar yanda ki ka ce, Allah ya miki albarka,"
"Ameen Mamana, sai dai akwai wata alfarma danake son na nema a wajen ki,"
Qasa ta yi da murya sosai ban ji me tace ba, amma naga Mama ta miqe cikin fushi,
"Dama jira nake ki min wannan maganar banzan da Abban ku yace kin masa tin wata biyu da suka wuce,shi ya hane ni da tinkarar ki da maganar duba da rashin lafiyar da ki ke fama da shi, idan shi ya maki alqawari, to ni ban yi ba, kuma ba zan taba yi ba, sanin kan ki ne Rasheedah ta tsane ki, da duk wani abu daya dangance ki, hauka kk da zaki ce haka,"
Kuka ta fara sosai, harda shessheqa, hankalin Mama ba qaramin tashi ya yi ba,dan ko kad'an bata son damuwar Sakeenaah, Sakeenah irin yaran nan ne da ke da shiga rai saboda tsananin biyayyar su da kyawawan halayen su, shi ne dalilin da ya sa suke son ta ainun, cikin sassauta murya Mama ta ce,
"Abun har ya kai haka,to tsaya, ki bar kuka mu yi magana, fad'an dalilin ki kwakkwara na aikata hakan?"
Hawayen ta ta share ta fuskanci Maman ta ce,
" Maa ni nafi son koma meye dalilina daga baya kun gani, ni bana son furta meye uzurina, alfarmar nan kawai zaku min ku nuna min soyayyar ku cikakkiya a gareni bayan ba ni a doron qasa, Ina so wannan abun da zan yi ya zama wasiyya a gare ku kin ko San Mama wasiyya indai ta alkhairi ce dole ne a cika ta ko?,"
" Akul na kuma jin maganar idan bake dinnan kina karyan zuciya sosai Sakeenah, wa ya ce maki Zaki mutu yanzu? Dan Allah ki dena wannan maganar mara dad'in ji"
murmushi ta yi kawai sannan ta rungume Maman,hawaye na bin kuncin ta, a haka ta samu ta fara gyangyadi, Adnan ne ya dan leqo ya gaida Mama, da hannu ta masa nuni da ta yi bacci, a hankali ta zame jikin ta daga na Sakeenah ta gyara mata kwanciya shi Kuma ya gyarawa Baby Atiyyah kwanciya sannan suka ja masu qofa suka fita, daukan Mama ya yi a mota dan ya Kai ta gidan Rasheedah,ya zauna a qofar gida dan tace a yau zata koma gidan ta ba zama za ta yi ba,
" Aaa Mama ce a gidan namu yau Kuma,to sannu da zuwa, ya kuma kk bar mai jego da jikar so,"
Baki Mama ta saki ta bi Rasheedah da ta yi maganar da kallo, lallai wannan rashin kunyar ta ta na buqatar gyara,har da ita abun zai tab'a ashe
"Gidan ku Rasheedah, ni kk kalla ki fadawa haka? A jikokina wa na ware, haihuwar ki nawa? Ita haihuwar ta nawa? Meyasa kk haka? Ke yanzu ba zaki daure ki sawa zuciyar ki salama ba,to sai anjima dama leqowa nayi a gaisa naga jaririya, Allah ya raya mana da imani"
Cikin maganar shi ta yara Yousf yace zai bita, daukan shi ta yi ta fice tabar Rasheedah na mata Allah ya kiyaye, dan ita a ganin ta ta fadi abinda ke ranta, dama lokaci zuwa lokaci Yousuf kan je mata ya yi kwanaki, duk da ba safai Rasheedah ke yarda ba.
****************
Atiyyaerh da Farhah na da saurin girma da ga wayo, sai dai Atiyyaerh tafi Farha girman jiki, kamar itace babba, in Mama ta fada ace ai ta yi son kai,bayan abun a buɗe yake, amma Rasheedah na jin an ce Atiyyaerh ta fi Farhah jiki sai ta fara fad'in "To abinka da jikar so", Mama ta yi nasiha ta yi zagin,ta yi fad'an ,amma inaaa, ita haka take ganin anfi son Atiyyaerh bisa ga Farhan ta, a kullum Sakeenaah qara zama shiru take, duk da Adnan baya son hakan, amma haka take roqar shi ya kaita gidan yayar ta,cin ranshi ji yake kamar ya yi bindiga, ita ko Rasheedah in sun je ba ta da aiki sai habaici da mugayen kalamai akan Atiyyaerh, dan kawai taga ko ta ina ta wuce Farha, hasken fata kawai Farha zata nuna ma Atiyyah, kamar dai ita da Sakeenaa.
Yau yaran suke cika shekara biyu cip, inda Sakeenaah ta saka yarinyar ta a gaba mai tsanain wayo da magana kamar ta shekara uku ta na ta yi mata addu'o'i, Abban ta ne ya shigo ya dawo daga shopping ya siyo mata wasu sarqoqi masu kyau sosai na zinare da wasu kayayyakin na sawa, Sakeenaa ta yi ta mitar kaya sun mata yawa ya dinga tinawa akwai wasu yaran a dangi Yana taimaka musu mana, sannan ya daure ya dena shagwaba ta haka,yakan ce,
"Haba My love ita kadai fa muke da ita,in ban mata ba wa zan yi wa?"
Rausayar da kai kawai ta yi, ta qawata fuskar ta da murmushi, sannan ta ce,
" Allah ya qara maka bud'i Abu Ablaerh,"
"Ameen, Zo ta nan ki zauna kusa da ni, nifa sai na ga kamar kin d'an fara kyallin goshi, ko dai Atiyyaerh ta yi qani ne,"
Ya qarasa ya na mai sumbatar kuncin ta, rungume juna suka yi Adnan ya d'aga Kai ya kalli qofar d'akin Atiyyah dake a rufe ya ce,
" Ni fa na kula tin da aka haifi yarinyar nan wasan parlour ke gagarar mutum, tashi ki gani muje na duba ki, ko akwai ajiyata a jikin ki"
Dariya ta yi sosai,
"Ka duba ni ka ga akwai ajiya ko kuma ka yi ajiyar yau, dan dai ni nasan ban da komai,"
"Muje dai an gani duk kin gama rudan rutsuwa da wannan qamshin naki, " ni ko na ce tooooo da kyau Sakee baby☹
Maganar Adnan ta tabbata, ashe Sakeenaah dai ciki har ya yi wata uku ba su sani ba, sun gano hakan ne ta hanyar amai da ta gama sheqawa bayan ta sha tea da safe ta na kukan yanda take Jin kasala sai Adnan ya ce,
" Na fada maki na yi ajiya kin qi yarda ko,"
Bata fuska ta yi ta ce,
" Ni ba wata ajiya da nake da shi,"
"Tinda baki yarda ba to tashi muje asibiti in ba tsoro ba,"
Dariya ta yi tace ta dai ji tsoron take, a qasan ranta tana godewa Allah, in dai hakan ya zama gaskiya,a nutse ta futa
"Na yarda muje "
"Bismillah mu je"
Tashi suka yi suka shirya tsaf sai asibiti, gwajin farko aka gano ciki dan wata uku, murna kam ba sai na fada maku irin wadda suka yi ba ranar,biyawa ya yi da ita super market, ta kwashi kayan zaqin ta, suka dawo gida, suna isa ta sauke Atiyyaer, dake cin biscuit, sannan tai kitchen, tea ta hado ta zauna zata fara sha kenan, Atiyyaerh ta zubar mata da shi wajen qoqarin itama sai ta sha, fada ta mata ta kora ta wajen Abban ta, ita kuma tai kitchen dakko mopa, ta dawo tana ma Adnan bayanin kukan Atiyyaerh bata kula ba santsi ya kwashe ta, ta fada kan center table, kanta ya bugu, qafarta ta zame ta kifu ta gaba, wata qara ta sake tana kiran sunan Allah, Adnan da gudu ya qaraso,.........
*wayyooooo niiii Ummu Ablaerh plssss don't die, makaranta zasu sambaden wallah,ki tausayan😭😭😭*
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Dan Allah masu tambaya daga farko ku yi hakuri a gama gaba ɗaya a haɗa document sai a tura maku...masu tambayar KUN MAKARO daga farko dan Allah ku tambayi mutanen group ɗin da kuke ciki maybe ba za a rasa wanda ba ya clearing chats ba sai a Baku ko ku buɗe document da na tura group ɗin da kuke ciki ku karanta ta nan. Kar ku manta KYAKKYAWAR FAHIMTA ne kawai sabon littafin da nake yi a yanzu waɗannan dika reposting nake yi na jima da yin su...Na gode*
Page 13:
Kafin Adnan ya isa ya taimaka mata ta Kai qasa,gaba daya jini ya jiqe wajen, daukan ta ya yi suka yi waje dan zuwa asibiti,ganin halin da take ciki ne ya sa aka shiga emergency room da ita aka shiga duba ta, hankalin Adnan ya Kai qololuwa wajen matuqar tashi, jikin shi sai rawa yake ya kasa yin komai, so yake ya yi kuka ma ko zuciyar shi ta sake daga qullin da ta masa, amma inaaa hawayen sun qafe sun qi zuba,suna nan a haka ya yi tinanin Ablaerh ya baro ta ita d'aya a sashen su ga su Shamsiyyah na can wajen su ba lallai su ji me ke faruwa ba, wayar shi ya zara jiki ba kwari ya kira Shamsiyya ya Sanar da ita ta dauki Ablaerh su koma shashen su da ita, sannan ya yi wa Mama waya ya sanar da ita komai, a sannan ne ya ji Wani kuka ya zo masa sosai, kashe wayar ya yi ya kife fuskar shi a tafukan hannayen shi, ya na jin matiqar tsoro, domin yanda yaga jini na bin qafafun ta da kanta,in dai daga jikin ta ya fito to tabbas tana buqatar wani ko kuma Wani abu mara dad'i ya same ta, yana tina hakan ya miqe da gudu ya yi inda aka kwantar da ita, yana masu magana da qarfi yana kuka, akan su bude ya ga matar shi, da kyar aka rirriqe shi ya samu ya zauna ya had'e kai da guiwa yana ta zubda hawaye, ba a fi minti 20 ba Mama da Abba suka zo, tare da Yousuf, sai Ablaerh da suka biya suka d'akko, yana nan zaune suka tadda shi, Abba ne ya dafa kafad'ar shi, ya d'ago rinannun idanun shi ya kalle su, kad'a mashi kai kawai Abba ya yi, domin shima daurewa kawai yake,
"Ka yi hakuri ka k'warara zuciyar ka, kai mata addu'a kaji,"
Adnan na jin kalmar addu'a ya tashi kamar wanda aka mintsina, ya samu waje ya zauna ya daga hannaye sama, yana ta roqon Allah akan ya bata lfy, ko abinda ke cikin ta bai tsira ba yana roqon Allah ya bar masa matar shi, ba qaramin tausayi ya ba Mama da ke ta kuka ba a gefe, suna haka likitoci biyu sika fito, dayan ne ya cire glasses din shi, ya sharce zufa, miqewa suka yi a tare baki d'ayan su suka nufe su dan jin me ke faruwa, d'aya daga cikin likitocin ne ya kalli Adnan ya ce,
"Alhaji Adnan Bismillah Ina son magana da kai" Abbah ne ya kalli likitan ya ce,
"Zaka iya fad'a mana ko me ke faruwa baki d'ayan mu Doc. ni mahaifin ta ne, wannan mahaifiyar tace,"
"Ok to ku biyo ni,"
Shigar su office din ke da wuya suka samu mazauni suka zauna, inda Adnan ya samu gefe ya tsugunna ya yi jugum kawai, Doc. Ya fara magana kamar haka,
"Gaskiya 'yar ku na cikin hadari sosai Alhaji domin kuwa ta zubda jini sosai ba kadan ba, mun samu mun qara mata da hanzari, dan bari sai an nemo a dangi ma bata lokaci ne, i am very sorry to inform u that we have really tried to save the baby amma mun rasa shi, sannan ta samu rauni mai zurfi a kanta, wanda a qallah zai dau wani tsahon lokaci kafin ta warke,..... Sannan Kun San dama tana d'auke da hawan jini"
Tin da ya fara magana salati kawai Abba yake, Mama na share kwalla, tinani kawai take, ita kuma Sakeenaah haka Allah ya jarabce ta da faruwar al'amura haka, addu'a take mata na samun cin wannan jarabawa,
" Eh mun san tana dauke da shi," in ji Abbah da ya ji yanda wajen ya d'auki shiru, banda shassheqar kukan Adnan ba a Jin komai sai qarar AC.
"Ya na da matuqar mahimmanci a kula da lafiyar ta saboda a wannan yanayin da take ciki bamu da buqatar abinda zai dame ta in har Allah ya sa ta farka, hakan ba zai faru ba har sai Kun taimaka mata ta hanyar yi mata dik Wani abinda take so, kar ana dinga sanya ta cikin damuwa,... zata iya farkawa daga nan zuwa gobe amma sallamar ta sai yanda muka ga jikin nata ya yi sauqi dan haka ku kwantar da hankalin ku a yi Imani da Allah shine Mai warkar wa Alhaji zata samu lafiya, ka daure ka ci gaba da bata kulawar da muka sanka da shi, ni anjima zan tafi d'an uwan ka zai zo ya ci gaba da bata kulawa,(cousin din Adnan dake aiki a wajen) Inshaa Allah zata samu lafiya, Allah ya bata lfy,"
" Ameen" suka amsa dika, miqewa suka yi zasu fita,har a wannan lokacin Adnan na tsugunne, Abba ne ya kama hannun shi suka fita, d'akin da aka kwantar da ita suka leqa ga tanan kwance kamar matacciya, wasu hawaye ne masu zafi suka wanke fuskar Adnan, zuwa ya yi ya zauna kusa da gadon a kujera, ya jingina kan shi da gadon, ya kama hannun ta, kuka yake kamar qaramin yaro, Ablaerh ta matsa kusa da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 21