dan tana son shi ba,tana son ganin shi da ta yafe shi, da ta manta itama tana da uba, kamar yanda ta dauka shima.ya manta da ita, hakuri su Abba sukai ta ba ta, Mama ta debo mata tuwon shinkafa,miyar taushe, ta sata gaba, da kyar ta iya ci, dan ji ta yi gaba d'aya bata son cin komai, bayan sun d'an taya ta hira ne suka bata waje, ta koma tai addu'ar kwanciya bacci ta shafa a jikin ta ta kwanta, baccin kasa d'aukan ta ya yi, sai tinanin Ahamd ne ya cika mata zuciya, ko me yake yi a yanzu? Ko su Baba sun san ya sake ta? Allah shine masani a haka bacci barawo ya dauke ta.
********************************
Da asubar fari Baba Garba da Yayah suka zo gidan Abbah, inda Suna buga qofar gidan tare da sallama daga baya Auwal ya zo shima, nan fa aka hau gaishe2, da jajanta wa juna abinda ya faru, can nesa da su kad'an suka ga Abba na tahowa ya dawo daga masallaci,yana isowa ya miqa masu hannu aka gaggaisa, sannan ya bud'e gidan suka shiga, parlour suka tafi dika, bayan sun zauna ne suka qara gaishe2, Baba Garba ne ya fara magana ya ce,
" Malam Hamza, bayan mun dawo gida jiya wajen magrib, muka ga Ahmad ba yanda yake,sai an kwantar se an tayar sai da muka kai shi asibiti, jikin shi zafi saboda zazzabi, sai sambatun kiran Atiyyaerh yake,yana fadin ya cuci kanshi,ya yanke hukunci cikin fushi, da sauran kalaman nadama, da na matsa mai da tambaya ya sanar da mu duk abinda ya faru, mahaifiyar shi yanzu haka tin jiya take kukan mummunan aikin da ya jiqa mana, yarinyar nan ta zama 'ya mace d'aya da bamu samu ba a tsakanin mu, ni da mahaifiyar su, tinda ta je ita ke mana komai, ita take taya mahaifiyar su aiki, ta zama abokiyar hirar ta, girmama ni take kamar ni na haife ta, ga Yayan su nan, bata taba gaida shi a tsaye sai ta durqusa, yaran shi duk rashin kunyar su sai da ta shanye har ta sa suka zama yaran kirki, tin jiya suma suke ta neman ta da suka ji abinda ya faru kuka sukai tayi, suna a dawo masu da Aunty Amaryar su, ba munzo bane dan mu bada hakuri a maida ta ba, domin mun san saki uku ne tsakanin su, munzo ne dan bada hakurin abinda yaro ya aikata mara kyau, a yi hakuri, a yafe mashi, tabbas ya yi rashin hankali, da rashin hakuri, wanda ya jefa kan shi a nadama da dana sani, kuma muna fatan zumuncin mu zai ci gaba ba zai yanke ba,"
" Wannan haka yake Malam Garba yaro ya yanke hukunci cikin fushi, wanda ya sa su gaba dayan su a tashin hankali, sai dai mu yi fatan Allah ya kiyaye gaba, ya sa hakan shine mafi alkairi," In ji Abban su Rasheedah, Auwal kuwa ya ce,
"Nima Dake ban dawo da wuri ba sai qarfe goma na dare, saboda wata kwangila da kamfanin bulo na ya samu kwanan nan, ko da na dawo ba a Sanar da ni da wuri ba, se da na nemi Afrah ban ganta ba, Ina shiga d'aki na gan ta tana kuka, da na yi bincike se na ji mummunan labarin, na so zuwa tin a daren amma na bari zuwa yau da safe na zo, to dama rayuwa bawa baya wuce qaddarar shi, muyi fatan yanda muka roqi auren ya zama alkhairi sakin ma ya zama alkhairi,Allah ya had'a kowa da rabon shi na alkhairi"
Amsawa dika suka yi da 'Ameen" sanan suka miqe da niyyar zasu tafi, zasu wuce asibiti, wajen Ahmad, Auwal ne ya ce
"Wanne asibiti ne inna tashi nima zan zo duba shi,"
Fada masa suka yi sannan sukai sallama suka tafi, bayan sun zauna ne Abbah ya kira Mama da Atiyyaerh, suka zauna, kan ta a qasa dan ganin Abban nata cikin damuwa, da alama shima bai yi bacci ba, gaida shi ta yi sannan ta gaida Abbahn su Rasheedah da Maman, bayan sun amsa ne Auwal yace,
"Ablaerh ki yi hakuri da wannan mummunan abu da ya faru,jiya na dawo gida na tadda mummunan labari akan abinda ya faru, wanda ba kowa ne sila ba illa Rasheedah, na zo ne domin na baki hakurin komai da take maki, daga wannan lokacin inshaa Allah komai ya qare ba zan sake saka ido ta b'ata rayuwar ki ba, dan haka nake baki hakuri da ki zo mu koma gida,"
Kan ya qara bude baki ta riga shi da sauri ta ce,
" Abbana ka yi hakuri,ba zan iya komawa qarqashin inuwa d'aya da Umma ba, irin qiyayyar da take min ban zaci ta kai haka ba, sai jiyan, na ci alwashin ba zan sake zama guri d'aya da ita ba, in kuwa wannan karon kuka kafe sai na zauna da ita dan cika wasiyyar Mommyna to tabbas zan bijire maku, zan iya barin gidan nan akan na zauna da ita,"
Ta qarasa maganar cikin kuka, wanda gaba d'ayan su saida suka tausaya mata,
"Shikenan yanzu magana ta qare ba inda zata tafi, ina nan tare da ita, nima ina son kasancewa da ita tin fari, kawai dan an fi qarfina ne yasa na hakura, amma tin fil'azal da anbi tawa da Atiyyaerh ma bata zauna da Rasheedah ba a wannan qiyayyar da take mata, dan haka mu yi fatan alkairi a rayuwar ta kawai ta ci gaba da zama nan"
"Haka ne, kema kin kawo hanzari mai kyau Hajiya, dan haka abinda kk fada yayi daidai ta ci gaba da zama anan kawai,"
Abba Auwal ba haka yaso ba amma shima addu'ar fatan alkairi yayi suka ci gaba da tattaunawa da Abbah akan matsalar Rasheedah,anan ya karya sannan ya tafi,kafin ya Isa gida se da ya tsaya ya biya asibiti wajen Ahmad,ya tadda Ahmad cikin mawuyacin hali, duk ya fige kamar wanda ya yi ciwon watanni, bayan ya gaida shi ne ya wuce gida, kwata2 ya dauke wa Rasheedah wuta, baya kula ta baya cin abincin ta, baya komai da ita na ma'a malar aure, dan gaba d'aya ta fice masa a rai, Afrah ma ba kula ta take ba banda gaisuwa, sai ta qarata zage2n ta da fadace2n ta amma ko mai ba zata ce ba, Sulaiman a satin ya dawo, lokacin da ya ji labarin kasa cewa komai ya yi ya qurawa mahaifiyar tasu ido, saida jikin ta ya hau kyarma, ba dan komai ba dan bata tab'a ganin fushi da tsana a idon d'an nata ba irin wannan lokacin, tinanin ta ya kai kan me Yousuf zai ce kenan idan ya ji????
*BAYAN KAMMALA IDDAR ATIYYAERH*
Atiyyaerh na zaune a Parlour ta na hutawa bayan kammala aikin gidan da ta d'auke wa Mama tin zuwan ta, zaune take cikin Kwalliya mai kyau da d'aukan hankali wadda ta jima ba ta yi irin ta ba, haka kawai yau ta ji ta na sha'awar yin Kwalliya, wayar da Abba ya sai mata take dannawa,wani qamshi ne mai dad'in shaqa da kwantar da hankali ya daki hancin ta, sannan sallama ta biyo baya da muryar da ba zata tab'a mantawa da ita ba a rayuwar ta, d'aga kan ta ta yi a hankali idanun su ya had'e dana juna, sun dad'e suna kallon juna kafin ya katse kallon da cewa,
"Ba za ki min iso ciki bane, anan zaki bar baqon naki?,"
Cike da jin kunya ta kauda kan ta daga kallon shi, ta yi masa nuni da ya shigo, miqewa ta yi ta shiga ciki,shi kuwa ba abinda yake face bin kyakkyawar surar ta da kallo,wani yawu ya hadiya da qarfi sannan ya ce,
" Allah ka mallaka min qanwar nan tawa a matsayin matar aure na a wannan karon"
Dawo wa ta yi sanye da mayafin da ya rufe jikin ta yanda ya Kamata,hannun ta d'auke da farantin da ta d'ora jug din da ta zuba zob'on da ta had'a ba jimawa Wanda ya sha kayan qamshi da cucumber da abarba, sai lemon zaqi da na'ana'a, ta aje masa a gaban shi,sannan ta sanar da Mama zuwan shi ta dawo, zama ta yi ta gaida shi, ya amsa idon shi kamar zai fad'i qasa Dan kallon ta,
" Yah Kallon fa? "
Cike da shagwaba ta fad'i hakan shi Kuma cikin kashe murya ya ce,
" Ya ba zan kalli dimond dina ba, sannan kina Wani abu kamar baquwa? Ko gaisuwa ma Babu, any way na yafe gaisuwar, kallon ki ma da na yi ya wadatar da ni,na San ke Baki ma yi kewa ta ba, dama wanene ni a wajen ki da Zaki kewa ta? Ni kuwa kin ga kullum cikin kewa da tinanin ki nake,na jima rabona da na saki a Ido na,ke Kan ki yaushe rabon da ki ganni? Tin lokacin da na dawo na tadda daddad'an labarin nan,na wuce kaduna wajen abokina, na hau fafutukar neman aiki, har Allah yasa na dace, a kullum sai na yi waya da Afrah na ji ya kk, takan ce min tazo kun yi hira kala kaza da kaza, nai ta jin dad'i, saboda so nake na dawo da kwari na Ablaerh bana son rasa ki wannan karon,akwai sanda na sa ta ta yi min recording muryar ki inda kk ta dariya akan labarin miyar da ki kai wa Mama mai yaji, na ji matuqar dad'i kasancewar fara'ar ki ta dawo, na qudurta dawowa tin a lokacin to kamfanin da nakewa aiki, na sarrafa kayan gine2 ba zai ban damar tafiya daga fara aiki da su ba,sai da na yi wata hud'u da su sannan na dawo, tinda na dawo na so zuwa amma ina tsoron me zaki ce game da buqata ta a wajen ki,"
Cikin sauri ta daga kan ta tace,
"Wacce buqata ce zata tsorata ka zuwa waje na Yayah, kasan yanda na yi kewar ganin ka kuwa, a lokacin da komai ya faru na so kana nan, nasan zaka ban kafad'ar ka na koka baqin ciki na amma baka zo gare ni ba Yayah , nasan zaka min tattausan lafazin ka domin na kwantar da hankali na ammma shiru ba ka zo gare ni ba Yayah Babu kai babu dalilin ka, Yayah na zata kai zaka taimaka ka dawon da farin cikina amma haka ka tafi ka barni ba wata kulawa Daga wajen ka, sannan yanzu ka zo da wata buqata a gare ni?"
Kuka take sosai dan tinawa da yanda ta tsallake ramukan baqin ciki ita d'aya ba mataimaki a gare ta, hawayen ta duk ya bata mata kwalliyar da ta yi, tashi ya yi ya zauna kusa da ita, ya goge mata fuska, sannan ya dafa kafad'ar ta yace,
"Ablaerh my dear ki daina kuka,ki yi hakuri ki yafewa Yayan ki, na sani ni Mai laifi ne a wajen ki,amma inshaa Allah komai yazo qarshe, ni zan maye maki gurbin duk abinda ki ka rasa a rayuwa, Ina fatan na zama *JARUMIN KI* "
" Yayah na san da hakan sanin cewa *KAI NE JARUMI NA* ne yasa na ji takaicin rashin ganin ka a lokacin da nake da buqatar ka,babu Kai babu Daddy na, Yah ka taimaka min Daddy ya dawo gareni na kasa yin fushi da shi dik yanda zuciya ta ta so tsanar shi sai na kasa, ka taimaka min yayah "
"Share hawayen ki nace ai ko? yanzu gani na dawo, kuma ba zan sake barin ki ba ko mai rintsi komai wahala, ina tare da ke, ina fatan zaki qarawa Yayan ki matsayi ya tashi daga Yayah ya koma masoyi?"
Wata kunyar shi ce ta kama ta ta miqe ta shige ciki da gudu, a hanya suka had'u da Mama, mama ta ce,
"Ke meye haka zaki ture ni na fadi?"
Bata kula ta ba ta shige d'aki ta rufe ta jingina da qofa, tana ajiyar zuciya, tare da murmushi,ta dafe qirjin ta dake bugawa da sauri da sauri, hawayen ta ta share ta ce,
" Oh Ya Allah kasa Yayah ya zama farin cikin rayuwa ta, nima ina son ka Yayana na baka dama ka zamo masoyi a gare ni,"
Da qarfi ta fada gado ta hau juyi tare da murnar kalaman shi a gare ta, bayan ya gaida Mama sun tab'a wasanni na jika da kaka ya yi mata sallama ya tafi, dan yasan yanda Atiyyaerh ta tafi ta na Jin kunyar shi ba zata dawo ba.
******************************
Zaune suke dikkan nin su a parlour kowa da abinda yake yi, Muryar Yousuf ta karad'e parlourn da....
" Abba game da maganar na nemo mata da ka min ina son sanar da kai cewar Atiyyaerh itace macen da ta kwanta min a raina Kuma nake son na aura," a zabure Rasheedah da ke jefa inibi a baki ta hau tari sakamakon Wani guda d'aya da ta jefa Dan ta tauna ya wuce mata maqoshi da kyar ya fito, cikin Maida numfashi ta ce,
"A ina za a yi hakan, a wanne gidan, sai dai bayan raina kai da ka auri wannan yarinyar Yousuf na fad'a Maka, gwanda ma tin wuri ka janye wannan banzar maganar mara amfani da ka yi "
"Sannu uban shi me Iko da gidan Baki d'aya, Kuma in ji waye ya ce ba zai auri Atiyyaerh ba? Ke? To in kece dan Allah yanzu ma ki fad'i mana, mu kuma ana arba'in din mutuwar ki zamu d'aura auren Yousuf da Maimunatou,shashasha kawai, Kai Yousuf ka kwantar da hankalin ka wannan karon da kaina zan tsaya Maka sai ka auri Ablaerh"
Miqewa ya yi ya shige d'aki,ya bar Yousuf da sauran 'yan uwan shi a wajen, yana ganin zata fara surutu ya miqe shima ya yi dakin su, fad'a take kamar zata ari baki, ba mai kula ta
"To a yi mu gani, in dai ni Rasheeda ina raye d'an dana haifa ba zai aure ki ba Ablaerh...
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 28:
" A gaskiya ba zan lamunci abinda ka ke shirin aikatawa ba na fada maka,ta ya za a ce d'an nawa ya auri ragowa yana saurayi? Ba zai yu ba ba zan lamunta ba, saboda nima ina da haqqi akan shi, ni nai cikin shi wata tara ba tare da kowa ya taya ni da riqon shi ba, ina da 'yancin zabar ma d'ana abinda ya fi dacewa da shi,"
"Zaki matsan a hanya ko sai na make ki? Domin ke ba matar da za a ragawa bane saboda qima ko daraja, dan baki tare da su, in ba a taya ki daukan cikin shi ba ai bake kikai wa kan ki cikin shi ba ko? Sannan abubuwan da kk ci a cikin nashi da kulawar da kk samu ko da kudin asibitin da aka biya na haihuwar d'an naki iyayen ta ne suka biya in kin manta na tina maki butulu, matsan ni malama ina da abin yi,"
Matsawa tai tana qunquni, dan rabon da ta ga ya b'ata rai haka ta manta,amma wannan karon komai da gaske yake d'aukan shi.
Afrah ce ta shirya ta nemi izinin Abban ta zata gidan Mama, amince mata ya yi tare da bata dubu d'aya,yace ta tsaya a hanya ta d'an sai masu ko da lemo ne, godiya ta yi,ta fice, ta dad'e a bakin titi tana jiran abun hawa kafin wani matashin saurayi, mai matsakaicin kyau da haske ya tsaya a gaban ta, motar shi kadaran kadahan ba wata me tsada bace, shi ba talaka bane da alama kuma ba mai kudi bane, sallama ya mata ta kauda kai gefe tare da amsawa a hankali, qara gaba shima ya yi inda ta tsaya ya sunkuyar da kan shi daidai tsahon ta ya ce,
" Malama Afrah bismillah mana, kina tsaye rana zata maki illa ai"
Cike da mamakin sunan ta da ta ji ya ambata a bakin shi ta matsa gefen shi tace,
" Malam ina ka sanni?"
" ke ba qanwar Sulaiman bace? Sulaiman abokina ne ai, tare mukai makaranta, muka gama, naga hoton ki ne a wayar shi, ba Yousuf ne yayan ku ba, kuma kina da qanwa ne ko yaya me suna Ablaerh?,"
D'aga masa kai ta yi ta d'an murmusa lallai wannan ya san ta, bud'e mata motar ya yi ya ce ta shiga,
"Na gode matuqa, amma gaskiya ba zan shiga ba, na ji dad'in tayin da ka min, ba ya daga cikin dacewa mace ta shiga motar wanda ba muharramin ta ba a wannan zamani da muke ciki, domin kuwa kamar misalin kasancewar su ne a d'aki d'aya na ukun su zai iya zama shaidan,"
Ba qaramin burge shi ta yi ba, cike da jin dad'i ya bud'e motar ya fito, adaidaita sahu ya sama mata, ya biya kud'in, ta masa godiya, ta tafi.
Tin a hanya take tunanin fuskar ajnabin da bata tambayi sunan shi ba, data tuna murmushin shi sai itama tai murmushi, a haka suka isa ta sauka ta shiga, tana shiga ta tarda Mama da Atiyyaerh, Mama na wanke wa Atiyyaerh kai da kalkashi, da kwai, tare da man shampoo, sai dirza kan take tana mitar,
"Gashi sai uban yawa da tsaho baza ki gyara ba, gashi nan duk amosali ya danqare maki akan ai, in ba dan kina tare da tsohuwar da kullum ki ke tsokanar na tsufa ba wa zai baki wannan maganin amosalin dake danqare akan ki? "
"Kaiiii jama'a dad'i na dake mita, "
Dundu Mama ta d'ima mata,ta kuwa gantsare tana kukan shagwaba?dariyar Afrah ce ta sa su duba inda take tsaye ta na Jin dramar su duk da idon Ablaerh a rufe yake ta san ita ce, oyoyo ta fara mata, itama ta wuce daki ta yi ta cire kayan ta ta daura zani, tazo ta zauna a kujera 'yar tsuguno ta gaida Mama ,bayan sun gaisa ne tace,
" Mama nima a wanken da karkashin, kaina se ya yi ta qaiqayi ya na kuma karyewa,"
"To taho, kk min raki kisha d'ima kema, ai rashin sani ne, wanke kai da karkashinnan yana da amfani sosai, gyara kai yake da qarawa gashi tsaho, sannan ya yi maganin amosali, kuma yana sa laushin gashi,"
Bayan sun gama wanke kai ne, suka tafi d'aki suka fara drying gashin su da hand dryer, suka mulke shi da man kwakwa, mai had'in man rid'i da na alayyadi, da man habbatussauda, sai man zaitun, ba qaramin kyau gashin su ya yi ba se sheqi yake ya yi baqi sosai, ga santsi da yake, Ablaerh ce ta nade shi cikin shower cap ta shiga wanka, ta dirje jikin ta sosai, tare da shafe tsakanin cinyoyin ta da Alovera, dan ya yi haske, ( shafa alovera, lemon tsami, lemon zaqi, kindirmo asalin mai kyau, tomeric da lemon zaqi ahade, yana saka tsakanin cinyoyi ya yi haske, ko kuma duk inda yake baqi a jikin ka kana son ya yi haske mai kyau in ka shafa duk d'aya daga ciki ya yi kamar 30mnts yana haskaka wajen, amma tomeric da lemon zaqi hada su ake a shafa) fes ta fito kamar a dauke ta a gudu, Allah ya ma Atiyyaerh kyau mai ban sha'awa, sannan ga gyaran jiki natural da Mama ke mata kullum, Afrah ta gani tana ta murmushi ita daya,
" Hmmm who is the lucky guy?"
In ji Atiyyaerh na tabbatar da wannan Murmushi na tinanin masoyi ne
Dagowa ta yi da idon ta masu kyau ta kalli 'yar uwar ta ta, ta sake sakin murmushi bata ce komai ba, itama zuwa ta yi ta qara watsa ruwa, dan jikin ta ya dan baci da kumpa, bayan ta fito ne su ka yi kwalliya,sannan Afrah ta nisa tace,
"Ammm game da abinda kk tambaya dazu ki ka ji na yi shiru banda amsar da zan baki ne, domin ban san me zance ba, zan fada maki how stupid i am to fall in love with a stranger? Ko zan fada maki cewar ko sunan shi ban sani ba? Amma shi yasan sunan mu ya san Yah Sulaiman,"
Cike da murna, Atiyyaerh ta daka tsalle, ta rungume ta, ,
" U ar not stupid my love, so haka yake, banga laifin ki ba, fatan mu ubangiji yasa shine mafi alkairi a rayuwar mu, baki daya, ki fad'awa Yah sulaiman cewar kin ga abokin shi har ya taimaka kk samu abun hawa da sauran su ya mai godiya kinga in ma ya manta ki ai ya tuna ki, dan ba zamu bari ya kufce mana ba yanda naga alamar son shi a tare dake,"
Murmushi Afrah tai sosai daya bayyana haqoranta masu kyau, suna haka Mama ta shigo suka ci gaba da hira da ita, Afrah a gidan ta kwana dan kwata2 yanzu bata son bud'e ido ta ga Rasheeda, da ana canja uwa da ta canja ta ta amma ba a yi sai dai tai mata addu'ar mai canja zuqata daga mummuna zuwa kyakkyawa ya canzawa Umman nata halayen ta.
Tin safe suka gyarawa Mama gidan Afrah ta shirya komawa gida, a hanya ne Ablaerh na dawowa daga rakiya Tsohon saurayin ta Hassan ya tare ta, tayi mamaki sosai daya gane ta, gaisawa suka yi ya fad'a mata yana sane da mutuwar auren ta, yasha wahala kan ya gano inda take, yau dama ya so zuwa gaida Kakan nata ya gabatar da kan shi, sai kuma gashi sun hadu,
"Mu qarasa gidan dan na kula maganar ba ta tsaye bace ko malam Hassan?"
" wannan haka yake , bismillah na qarasa dake,"
" A'a ba damuwa, ai mun kusa,ba sai na shiga ba, muje kawai,"
A gefe ya yi parking d'in motar tashi sannan ya kulle ya bi bayan ta......
*Hahaiiiii casssssss, Malam Hassan samawa kan ka lfy muna da miji a hannu*🙄
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 29:
Parlour ta bude mishi ta mai izinin shiga sannan ta shiga ciki ta sanar da Mama, kafin ta d'ebi zobo mai sanyi da meatpie da suka yi ita da Afrah ta kai mishi, sai da ta koma ciki ta d'an bashi waje sannan ta dawo, ya d'an ci kad'an dan shi damuwar shi bai wuce tazo su yi magana ba, ita kuma ta rasa ta yanda zata b'ullo masa, zaman ta keda wuya Yousuf ya yi sallama ya shiga, ganin baqo kuma ga Dimond d'in shi a zaune ta sha kwalliya ya sa ya yi kicin2n da rai, fuskar nan kamar bai tab'a dariya ba, hankalin ta in ya yi goma ya miqe tsaye, a daburce ta furta,
" Sasssannu.. da zuwa Yayah,"
ko kallon ta bai ba ya amsa, idon shi na kan Hassan, yana jiran qarin bayani, daga tsayen ya harde hannayen shi a qirji yana kallon su,
"Ammm dama wannan shine Hassan.."
Se kuma tai shiru, Yusouf yace ,
" Ehemmm? Sai yazo yin me?"
Hassan ne ya miqe tsaye ya je ya ba ma Yousuf hannu dan su gaisa, kamar ba zai miqa masa nashi hannun ba, ya miqa mai ya koma d'aya daga kujerun parlourn ya zauna ya hard'e qafa, qasa ta yi da kan ta, da a ce zasu kasa kunne da sun ji yanda zuciyar ta ke bugawa, Abbah ne ya yi sallama a tsakar gida, nan da nan ta yi wata ajiyar zuciya me qarfi, fit ta tashi da sauri ta fita waje, zuwa ta yi ta kama hannun Abba suka shige dakin su, tana shiga ta fara buga qafa irin na shagwab'ar da ta Saba yi wa Abban,
" Abba tin d'azu nake jiran ka, Hassan yazo ga Yayah can yana ta b'ata rai , yayi fushi, ni kuma bani na kawo Hassan ba, ganina ya yi a hanya muka gaisa, na zo da shi dan bana son mu tsaya a waje, ina son na masa bayani, akan ina da wanda nake so, amma Yayah kamar ba zai gane hakan ba gaba d'aya ya b'ata rai,"
Hawaye ne ya gangaro mata, Abba murmushi ya yi dan ya gane a rud'e take sosai,
" kwantar da hankalin ki ina shi Yousuf d'in yake? Muje na gan su"
Noqe kafad'a ta yi ta zauna gefen Mama da ta fara bacci,
," A'a Abba ni dai bana son na sake ganin Fuskar Yayah sai ya sakko, tsoro nake ji,"
Dariya ta ba Abban ya fita, ta kama hannun ta ta saka a baki tana cisgar farcen ta tare da qurawa qofa ido, ta kasa kunne sosai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 21