bawa Atiyyaerh tea d'in da magani, sannan ta dakko towel da ruwa mai rangwamen sanyi ta yi ta goge mata jiki da shi, kafin minti 5 ta fara zufa bacci mai nauyi ya d'auke ta.
Bayan fitar Mama Yousuf ya qurawa mahaifiyar su ido, domin ta masu qarya, d'aga kafad'a ta yi tace wa yaron da ya kafe ta da kallo,
"Meye kuma kk tsare ni da wannan manyan idon naka,"
" Umma kin ce tana bacci a d'akin mu,"
"Eh mana fitowa ta yi dan munafurci amma ai a can na barta ta na baccin"
Sauka ya yi daga gadon ya fito ya zo wajen Kakar su ya zauna, nasiha ta hau yi masa sosai game da qanwar tashi kamar wani babban mutum haka yake sauraron ta kuma dik abinda take fad'a masa yana shigar shi matuqa, Rasheedah ce ta fito tana hura hanci ta zauna a d'age ta gaishe da Mama, ko kallon ta mama bata yi ba, ta miqawa Yousuf ledar su tace masa shi da qannen shi, wannan kuma na Atiyyaerh ne,Abba ne yace a basu, cikin fushi Rasheedarh ta fara magana,
"To baga shi ba, yaran ma sai kin nuna banbanci, tsakani da Allah ai da hadowa kawai za ai ace gashi a ba yara,ba kiyo ledar kowa daban ba, ta haka ne yara ke tashi kai a rabe,"
Cikin fushi Mama ta fara magana,
"Ai tinda dama zuciyar ki ba mai kyau bace dole ki ji b'acin rai akan hakan, haba ke kuwa, ki dinga sanyawa kan ki salama, ki sawa kan ki tausayi, da soyayya, ko kin mori kyaun da Allah ya miki, domin wannan baqar zuciyar taki ke tauye ki"
Kauda kai Rasheedah ta yi tana qunquni, Mama bata ce komai ba ta aje Atiyyaerh ta miqe zata tafi, sai da taje qofa ta juyo tace,
"Abinda kai a duniyar nan za a maka, wanda bai ba ma an masa balle kayi, kuma Allah ne shaida ban ma iyayena haka ba, mahaifin ku har iyayen shi suka rasu sina saka masa albarka,ki bi duniya a sannu shi haqqin maraya nauyi ne da shi, nauyin shi ya fi dutsen Dala Rasheedah ba Zaki Iya d'aukar nauyin haqqin marainiya ba ki samawa Kan ki salama ki ajiye qiyayyar nan mara tushe, kin Yi wa mahaifiyar ta hassada da zazzafar qiyayya ta bar maki duniyar, yanzu madadin ki yi karatun ta nutsu ki tina kema watarana Zaki inda mahaifiyar yarinyar nan ta tafi amma ki ke toshe kunnen ki ki ka rintse idon ki ki ke wa yarinya azaba, kar ki ce ban fad'a maki ba Rasheedah na fitar da haqqin da ke tsakanin mu na uwa da 'yar ta na fad'a maki gaskiya ruwan ki ne ki bi, ruwan ki ne ki barta kar ki bi"
Tana kaiwa nan a maganar ta ta fice, dan guntun tsaki Rasheedah ta ja sannan ta d'auki ledar Atiyyaerh ta debi kayan ciki ta qara a na su Yousuf, Sulaiman da Yousuf na tsaye suna kallon ta tare da Afrah ta debi biscuits da sweets ta basu, Yousuf qin karba ya yi, sai ita Afrah ce ta karba, Sulaiman kuma da aka bashi, zuwa ya yi ya aje gaban Atiyaerh ya koma ta bashi wani, cikin qara da hargowa ta fara magana,
" 'Yan iskan yara masu halin uban su kar ku ci d'in ku kuka sani,"
Ta kwashe ledojin zata shige d'aki sai ta ji muryar Auwal na fad'in,
" Allah na gode maka da basuyo halin ki ba duk da banji me ya faru ba, da sunyo halayen ki da na shiga uku na lalace da haifar mugun iri,"
Cike da rashin kunya ta murgud'a baki ta shige d'aki, Yousuf ne ya labarta masa dik abinda ya faru da baya nan,nan take ya d'ebe su a amota zai Kai Atiyyaerh asibiti, likita ta gani ya duba ta ya rubuta magunguna, sannan ya yi hani akan a rage yawan yi mata amfani da ruwan sanyi Kuma a kiyaye bata ruwan sanyin ta na sha,suna kammalawa da asibiti suka bi suka sai magungunan da aka bata, sai sukaje wajen cin abinci, aiko Atiyyaerh ta kwashi gara, taf ta cika cikin ta, sannan suka dawo gida, direct d'aki ya kaisu, dan basu buqatar abincin dare ranar, cikin Atiyyaerh ne ya motsa, ya yi qara, nan take ta sake wata muguwar tusa mai wari, su Yousuf ne suka toshe hanci suna tsokanar ta, wasa suke suna ta guje2, can kashi ya matse ta,
" Yaya zan yi kashi,"
"To bodara mu je ki gayawa Umma,"
kama hannun ta ya yi ya tafi da ita wajen Rasheedah, suna zuwa tsakiyar carpet din wajen Atiyyaerh riqon kashi ya kwace mata, tako sake shi a wajen, tana kuka, daidai Rasheedah ta fito dauke da kwanon data gama cin farfesun kifin da ta yi da basa nan,wani wari ne ya daki hancin ta,cikin toshe hanci da yatsina fuska ta kalli su Yousuf da ke zare Ido ta ce,
"Meye wannan? Me nake ji haka, Kashi ki ka min a qasa? kan ubancan kayyasa, yau se na ci kut......Uban ki Ina zuwa,...........
[01/07, 8:47 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 19:
Auwal mamakin yanda Rasheedah ke ta hidima da shi a daren yake,ita ce Yi masa girki mai dad'i da ya fi so, had'a masa ruwan wanka har da su zuba kayan wankan da suka tarar a bathroom d'in masu gyara fata na maza, Yana fitowa ya tarar da kayan da zai Saka na jiran shi, ita ta taya shi shiryawa ta feshe shi da turaruka masu dad'in qamshi, ga wata uwar Kwalliya da ta fesa Kai ba zaka ce ta tab'a haihuwa ba ma balle ace ta ajiye Yara har uku,sai Wani yauqi da shisshige masa take, ya gaji da Shan mamaki qarshe dai ya kama ta suka zauna a bakin gado ya zuba mata idanun shi da ke bala'in burge ta, ya ce,
"Fad'a min wannan sauyin halin na menene, domin ke ba abar yadda bace Rasheedah"
Wani abu ta ji ya soki zuciyar ta me zafin gaske, Auwal baya fad'in abinda ba haka ne a zuciyar shi ba, hakan na nufin da gaske mijin ta me son ta da qaunar ta a da yanzu be yarda da ita ba?hakan fa na nufin ya dena son ta,dan se akwai yarda soyayya ke samun wajen zama,laifin waye dika wannan? Laifin Sakeenah da 'yarta ne? Tabbas laifin su ne, saboda da alama ya fi son su sama da ita da take matar shi, qoqarin danne baqin cikin ta tayi sannan ta yanko murmushin yaqe ta ce.
"Haba Abban Yousuf me na yi Maka a rayuwa Mai zafi haka? Ni dai dan Allah ka yi hakuri bana son tone tone, shi mutum in Yana aikata laifi ya gane kuren shi ai se ya gyara tin kafin a nusar da shi ko Kuma lokaci ya qure masa ko? Na gane kuskuren da na ke aikatawa gaba d'aya shi yasa nake so na gyara,ka yi hakuri ka dawo min da soyayyar ka da qaunar da ka ke min a baya"
Kuka ta fashe da shi Wanda ta tabbata sai ya lausasa zuciyar shi, duk fad'a ko dukan da zai mata tana sane da baya son kukan ta, taurin Kai ne irin nashi ke hana shi lallashin ta,a hankali kuwa ya ji ya yarda da neman gafarar da ta yi, amma be San me yasa ba ya kasa sakewa da ita, Yana Jin kamar akwai Wani abu da take qullawa, share mata hawayen ta ya fara tare da rungumar ta a jikin shi Yana lallashin ta.
"Shiiiii ya Isa haka, ki dena b'ata hawayen ki, kin San bana son kukan ki ko?"
Shessheqar kukan ta ne ya ragu, ta sake shigewa jikin shi, ta na Wani abu kamar qaramar yarinya, Auwal ya yi kewar ta da yawa, ya yi kewar shagwabar ta da soyayyar ta, tinda suka zo gidan komai yi yake cikin qunci da Kuma cewar ya zame masa dole ya mata abinda take so kar ta masa haukan ta, amma ba Dan Yana so ba, a hankali suka fara wasannin su, Rasheedah ta sake masa jikin ta sosai ya na yanda ya ga dama da shi, cikin wata iriyar muryar da ke rikita Auwal ta fara magana,
"Abban Yousuf da gaske kenan gobe za ka Kai Atiyyaerh da Afrah makaranta?"
Auwal na Jin haka ya rintse Ido,ya fara qoqarin janye jikin shi da ya mata rumfa da shi Yana wasa da ita, Jan shi ta sake yi jikin ta ta na Masa wasanni masu rikitar wa, ta tabbata a yau ba zai iya fushi da ita ba saboda yanda ta sashi yake ji, ci gaba ta yi da magana daya gefen kuwa ta na Masa wasannin da ya sa maganganun ta ma basu wani shigar shi sosai,
"Abban Yousuf kar ka fahimce ni ba daidai ba, na tambaye ka ne saboda ni nake zaune da yaran nan a gida, na San me kowa ke so, Ita fa yarinyar nan Auwal ba ta son makaranta,na sha jin maganar su da yara tana fad'in ita tafi son yayan ta yana koya mata a gida, dan haka ni shawarata da ka barta a gida....in su Yousuf suka je suka dawo daga makarantar kaga sai yana mata karatun a gida,ta haka ne shima zai samu kwarewa sosai,"
wani kallon baki da hankali kuma ke bama ki iya makircin ba ma Auwal ya mata ba tare da ta sani ba, domin yanda yake Jin ta birkita shi ba zai iya jurewa ya yi fushi da ita ba, gurnani kawai ya mata da "Uhmmmmm" Jin hakan da Rasheedah ta yi se ta qara qaimi wajen rud'a Auwal, ni dai tattarawa na yi na basu waje, na koma d'akin Yara muka kwana.
Washe garin ranar kuwa Rasheedah na can na baccin gajiyar da Auwal ya tara mata, ya farka ya yi wanka ya yi sallah ya shirya sannan ya nufi d'akin yaran, da kan shi ya tada su suka yi brush suka yi alwala Yousuf ya ja su sallah Auwal na murmushin Jin dad'in yanda Yousuf ke da hankali,da kan shi ya shiga bathroom ya had'a ruwan wanka yayi wa yaran wanka har da Atiyyaerh da Afrah, qasa ya tarkata su suka sauka ya soya masu kwai ya had'a musu tea suka sha da bread, sai cake da ya siyo na tafiya makarantar yara da ya dibar wa kowa da juice da suke had'awa da shi, ya d'auke su sai makaranta, suna zuwa ya yi duk wani cuku2 na Saka Afrah da Atiyyaerh makaranta ya gama komai, sannan ya damqa su a hannun hukumar makaranta ya ja ya tsaya dan ganin ajin da za a Saka su, Atiyyaerh direct primary one aka saka ta, Afrah kuma suka bashi hakuri sai dai ta fara daga nursery saboda ita komai bata Iya ba Banda A zuwa F, Atiyyaerh kuwa har sunan ta da na Daddyn ta ta Iya rubutawa Yousuf duk ya koya mata, tana Jin turanci already, ta Iya had'a wasu kalmolin dik da ba dika ba,dan haka Auwal be Wani damu ba yace ba komai, don yasan qoqarin kowa a cikin su, zai tafi Afrah ta dinga kuka, da kyar aka bambare ta akai aji da ita, Atiyyaerh kuwa sai murna take sosai, tinda dama abun nema ne ya samu, dad'in dad'awa an aje ta aji d'aya da Sulaiman, hankalin ta kwance ta samu malamin ajin ya mata wajen zama kusa da wata yarinya mai kyau itama mai suna Amal wadda ba zata wuce sa'a da Atiyyaerh ba,murmushi suka yi wa juna, sannan Atiyyaerh ta maida hankalin ta in da malamin ke tambayar sunan ta, nan ta fad'a masu sannan ta qara da
"Mummyna na ce man Ablaerh, Daddy na na ce min Atiyyaerh, a gidan mu ma Atiyyaerh su Yaya ke kirana,"
Malamin su Murmushi ya yi, sannan ya ce,ta maimaita maganar da ta yi da turanci, tinda ta iya, nan da nan kuwa ta maimaita da turancin ta na Jin dad'i yau gata a makaranta,murmushi malamin su ya sake yi, yaran aji kuwa suka saka dariya, karatu suka fara, ta yi matuqar maida hankali akan abinda ake koya musu Dan sai ta ji kamar karatun makaranta da na Yousuf akwai banbanci wannan na da wahala, na Yousuf kuwa babu wahala Sam Sam,nan da nan take gane nashi, dan haka duk abinda bata gane ba bata bari a wuce wajen se ta yi ta tambayar malamin su, shi kuwa haka zai dawo baya ya mata bayani daidai fahimtar ta a haka ne ma wasu da basu gane ba suke shiru suke fahimta,a haka suka gama karatun su na wunin ranar har aka tashe su,iya malaman da dik suka shiga ajin shi Atiyyaerh sai da suka san anyi baquwar daliba.
Ban garen Afrah kuwa, da ta gama kukan sai ta saka hannu a baki ta hau tsotsa abunta har baccin ya d'auke ta,an tada ta yafi sau nawa, qarshe in suka dame ta ta saka kuka, haka suka barta ta sha baccin ta.
*******************************
Rasheedah bata tashi farkawa ba sai qarfe tara na safe, agaggauce ta gama wanka ta yi sallah ta sauka qasa, ji tayi gidan ba kowa shiruuu, d'akin Yaran ta nufa ta ga wayam ba kowa, wajen kayan Atiyyaerh ta duba ta ga alamun an tab'a kayan, Murmushi ta yi ta zauna bakin gado tana Jin Wani b'acin rai na yunquro mata, wato ita Auwal zai yaudara? Ya gama more ta jiya ya qi bin maganar ta? Lallai za a yi tashin hankali kuwa, Cike da b'acin rai ta hau watsar da kayan Atiyyaerh qasa ta na tattakawa, ta na gamawa ta fita daga d'akin cikin fushi, zata sauka qasa ta ji alamun bud'e qofa, tsayawa ta yi ta hard'e hannayen ta a qirji ta na kallon qofar, idanun ta sun kad'a sun yi jawur dan b'acin rai,Auwal da ya shigo ya Maida qofa ya rufe, ya ajiye key din motar a center table sannan ya kalli yanda take Wani cika tana batsewa, Murmushi ya yi a ran shi a fuska kuwa ya kalle ta da kulawa ya ce,
"Ah ah Rasheedah lafiya na ga fuskar ki ta sauya haka? Ko dai Kashi ki ke ji ne? Dan na San ki ke da shiga toilet kamar akwai amana kamar wata quda haka ki ke dan shegen yawan kashin ki"
"Kan uban can, ni ce ma me yawan Kashi? To malami dakata ka ji,idan ma ka d'akko wannan shirmen ne Dan na manta me ka yi to wasan ka be karb'u ba, ni zaka yaudara? Ni zaka ci wa amana?"
"Amana Kuma? Rayuwar auratayyar mu ki ka ji na yayata a duniya ko me? Ko so ki ke na Sanar da duniya yanda mugun abun ki be tsaya a Iya fatar baki ba har se kin Yi amfani da jikin ki kamar wata wadda bata San ciwon Kan ta ba? Ke Rasheedah ki kiyaye ni ni ba banzan namiji bane,ba Kuma soko bane ni, sarai na San me yasa ki yin abinda ki ka yi jiya, kin ga kenan duk wahalar da ki ka sha jiya Baki samu lada ba,ba lada ba la'ada, kin Yi asarar lokacin ki da energy din ki wajen kyautata min na qarya da yaudara, ke ba dan Sakeenah ce da kan ta ta yi wasiyyar ki kula da Atiyyaerh ba saboda tana maki kwadayin samun Rahamar Allah akan Wanda suke sada zumunci ai ganin yarinyar nan ba me barin ki kiyi muguwa azzaluma kawai, wato ke naki yaran su je makaranta su samu ilimi ita da kud'in uban ta da uwar ta ta zauna da jahilci ko? Sannu muguwa"
Zagaye ta ya yi ya wuce ta gaban ta zai shige d'aki, har ya gota ta ya dawo baya ya ce mata,
"Rasheedah ki sauya halin ki da wuri da gaggawa, kar ki zo ki na danasanin da bashi da amfani,"
"Ba zan sauya halin nawa ba, azzalumi me cin amana kawai, ta je makarantar na ga yanda ilimin zai zauna a Kan ta, aikin banza kawai "
A fusace Auwal ya juya Dan ya lallasa ta ta na ganin ya na biyo ta ta zura da gudu qasa ta shige kitchen ta rufe, tare da ci gaba da fad'a masa baqaqen maganganu, kwafa ya yi ya koma d'akin su ya kwanta a gado ya rintse idanun shi Yana Jin qiyayyar Rasheedah na samun wajen zama a zuciyar shi, be fita ba ranar se da aka tashi yaran ya wuce ta a parlour har ta zabura zata gudu taga ko kallo bata ishe shi ba, ya wuce d'akko Yara, ya biya da su restaurant suka ci suka sha suka qoshi, sannan ya dawo da su gidan, da kan shi ya yi wa su Afrah da Atiyyaerh home work, sannan ya fita ya bar gidan tare da mummunan gargad'in daidai da harara aka wa yarinyar in ya dawo Shima zai d'au mummunan mataki sannan ya fita, Rasheedah kuwa ji ta yi kamar ta yi bindiga, shi yasa ta Saka hijabi ta fita zaga unguwar da qafa Dan ta rage baqin cikin da ke ran ta.
****************************
Kusan wata biyu kenan suna zuwa makaranta batare da wata matsala ba,yanzu mutuniyar ku Atiyyaerh in za ta yi magana sai da turanci take yi dik da dama sun Saba yi da iyayen ta, amma lokacin bata da Wani wayo sosai yanzu ne take gane komai dalla dalla turanci ya zama second language d'in da ta ke ji ta Kuma kware akai sannan larabci dan ana yi musu shi a makarantar, Afrah kuwa bata san bihim ba da ake koya musu dan bata Wani Maida hankali akan karatun, kullum taje daga kukan banza sai bacci, in kuwa aka matsa za ai karatu a gida sai ta gudu wajen Umman su,ta ce ita bata so, Rasheedah ko ji take kamar ta mata dukan tsiya dan haushi kullum gori take mata da cewa,
"Shiritacciya kawai,ke ba zaki Maida hankali ki yi abinda zai amfane ki ba kin tsaya shiririta, ga waccan mara galihun ma tana karatu balle ke, so kk ta girma ta fi ki ilimi tana aiki ke kina zuwa maula ko? To ki tsaya ki ji da kyau daga yau se yau, bana so na sake ganin ki na wannan wawancin so nake ki fita komai da komai ma ni ba karatu kad'ai ba kin ji ko?,"
Ita dai Afrah sai dai ta tsotsi hannu ta ci gaba da kallon ta kawai.
Yau Lahadi, zasu je gidan kitson dake maqotaka da su, Atiyyaerh bata son zuwa ko kadan, duk da yawan gashin dake kanta, bata qin kitso, amma dalilin yaron gidan kwata2 ta tsani kitson da zuwa gidan, yaro ne sa'an Yousuf,mai suna Ahmad, ba qaramin son ganin Atiyyaerh yake ba shi kuma a rayuwar shi,dan yara abokan shi ma cewa suke budurwar shi ce,ya yi ta jin dad'i kuwa, in ya ganta ya je ya yi ta mata surutu,kala2, gashi baya zuwa makaranta shi, se ball da wasa a unguwa dad'in dad'awa kuma qazami ne , haka gidan da suke zuwa kitson ma qazamai ne matan gidan, Suna shiga gidan Atiyyaerh ta labe bayan Yousuf daya rako su shida Sulaiman, aiko Ahmad na hango su ya tashi ya je inda suke,yana jan hannun ta Atiyyah, kallon Yousuf ta yi ta kyab'e baki zata yi kuka, aiko yana ganin haka ya kaiwa hannun Ahmad duka yace,
"Dalla sake mata hannu, wani qazami da kai,"
Aiko da jin haka Ahmad ya saki hannun ta ya kaiwa Yousuf naushi, dambe ya kaure a tsakanin su, Afrah ta matsa gefe tana tsotsar hannu tana kallon su, ita ko Atiyyaerh saka hannu ta yi aka fara damben da ita sosai, Ahmad ya fisu qarfi, Sulaiman mugun matsoraci ne, baya ya yi yana ta zare ido, idon shi sunyi jawur yana son yin kuka, wani abokin Ahmad ne ya taso suka hadu suka zane Yousuf, ana gama damben Ahmad ya fizge hijab din Atiyyaerh aiko gashin ta da ke dunqule a matsattsen hijab din ya baje, kuka take sosai da qarfi, wanda ya ja hankalin matan gidan suka leqo soron, Maman Ahmad ce tace,
"Me zan gani haka, Yousuf waya fasa maka baki? Me ya faru haka?"
Kan ta gama tambaya Ahmad ya kwasa da gudu da abokin shi sun bar wajen, Sulaiman ne da yanzu ya fara kuka ya fad'a mata komai, Yousuf ya kumbura sai nishi yake, bai ce komai ba, ya d'aga Atiyyaer, ya kama hannun ta suka yi gida, Maman Ahmad na ta kwala mai kira yaqi juyowa, suka shige gida Afrah ma bin su ta yi, sannan Sulaiman, suna shiga Rasheedah na kitchen ta fito, ganin fuskar Yousuf da jini ga shi sun yi biji biji shi da Atiyyaerh sai mamaki ya kama ta ta ce,
" Ah kunyi saurin dawowa lafiya? Me ya faru na gan ku haka?"
Sulaiman ne ya mata bayani, aiko kan ya qarasa ta gane Atiyyaerh ce ta ja aka ma Yousuf haka, wani irin Mari na rashin Imani ta sakar ma yarinyar da ke kuka, ta kamo ta ta hau duka ba ji ba gani tana fad'in,
"Dan uban ki da ya gudu ya bar min wahala kashen d'an ki ke so a yi? dubi yanda jini ya ke zuba a bakin shi,shegiyar yarinya tin yanzu kin fara hulda da maza ko, to bari kiji in aure ne ki bari ki tasa aurar dake zamu yi da wuri mu huta da wahala, shegiya mai kama da mayu,"
Ta wurga ta gefe ta shige ciki ta na Kiran yaran nata, Yousuf kuwa kuka yake sosai, duk abinda aka masa bai ji kuka ba sai da aka dake ta, ranshi ya yi mugun b'aci da hakan, d'aki ya kwasa da gudu ya shige, Sulaiman ma ya bi shi, kallo Rasheedahn ta bisu da shi,
"Shashashai in ban da ku ma,kuna gani yanda kowa ke nuna yafi son ta akan ku, kuke manne mata, har wani haushi ka ji kenan dan na hukun ta ta akan dukan da ta sa aka ma? Kai ka sani wawan yaro kawai,"
Ta yi shigewar ta kitchen ,ta ci gaba da aikin ta, kuka sosai Atiyyaerh take, Afrah ta je ta zauna kusa da ita, tana shan hannu, bata ce mata komai ba amma sai kallon ta take,idon ta ya cika taf da hawaye itama.
Da daddare bayan Auwal ya dawo sun gama cin abinci Suna kallo,se na ga Yousuf na yi wa Abban su rad'a a kunne, cikin fushi sosai kuwa ya shiga d'akin shi, tana kwance ta yi d'aid'ai a gado tana kwasar rab'a , aiko ya samu qaton hannun shi na magina ya yanka mata duka a cinya, a gigice ta farka,
"Wayyo Allah,waya d'anan Iron a cinya me zafi haka?"
Tana kuka ta na murza wajen tana yarfe hannu,
"Ni ne nan na dake ki, mai shegen son kai kawai, ke wace irin mata ce da baki san Annabi ya faku ba? Meke damun ki ne, wannan yarinyar marainiyar Allah me ta ci maki? Ki shiga hankalin ki ina fada maki baki ji ko? Zan mummunan saba maki akan ta,"
"Kan uban can akan waccan yarinyar ka daken? To bari kaji, wahala a hannuna yanzu ta fara shan ta kala2, indai ni ce Rasheedah, sai dai ka kashe ni inna dake ta, ta zabura tai waje da gudu har zanin ta na kwancewa, bin bayan ta ya yi shima,tana zuwa ta samu Atiyyaeh na home work, ta dauke ta da mari, ta sake dauke ta da wani, yarinya ta gigice gashi marin da bata san da zuwan shi ba, ta kasa ma kukan, bude baki ta yi tana qaqalo kukan ya qi zuwa, Rasheeda bata ankara ba itama ta ji maruka na sauka a kuncin ta, yana dukan ta tana dukan Atiyyaerh tana zage2, d'aga ta ya yi cak, ya yi d'aki da ita ya rufe ya shiga kirbar ta, kamar an aiko shi,
"In kince ba zaki fasa dukan ta ba baki haifu ba, ko bana nan kika dake ta na dawo sai kin karbi naki dukan kema tinda kin zama baqar jaka, muguwar banza kawai,"
kuka take sosai, tana jin wata muguwar tsanar Atiyyaerh sabuwa na sake kama ta,
" Lallai Auwal ka ja mata, ka ja mata d'and'anar azaba a wajena kala2, baka san me zan iya aikatawa da wanda ba zan iya ba har yanzu,"
Ta tashi da kyar ta fada toilet tana kuka......
*Hummmmmmmm*
[01/07, 8:47 pm]
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 21