Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dan ta ji me za a ce, Abba ne ya musu sallama ya Samu waje ya zauna suka gaisa da Hassan ya bashi baki akan ga abinda ke akwai na auren Yousuf da Atiyyaerh,  hankalin shi ya yi matuqar tashi a karo na biyu, hawaye ne suka zubo ya yi saurin d'auke su, amma ya makara a kan idon Yousuf, jikin Yousuf ya yi sanyi, dan ya tabbatar ba qaramin so yake wa qanwar tashi ba, amma sawun giwa ya take na raqumi, shima in ba ita rayuwar shi zata shiga hatsari, hakuri ya ba Hassan cike da dakewa ya nuna masu ya gode zai wuce amma yana son a mai alfarmar ganin ta ko da sau d'aya ne, kishin Yousuf ne ya motsa ya dan had'e rai, ya ce, " Minti 5 na baku danni sauri nake zan tafi nima," Murmushi Hassan ya yi dan ya gano Yousuf d'in kishi ke damun shi, se ya dafa kafad'ar shi yace , "Ni minti 2 ma ya ishen," Abbah ne ya yi murmushi ya miqe ya shiga ciki, tana ganin Abba ta miqe tana zaro ido da son Jin me ya faru, cikin tsokana Abbah ya ce, "ki je yayan ki na can na fada akan kin kawo wani," Hawaye ta fara tana yarfa hannaye, Abba dariya ya saka yace, "Matsoraciya waya fad'a maki ana tsoron miji? Ba tsoro tsakanin ma'aurata sai dai biyayya, da ladabi, in kina jin tsoron namiji sai ya ci kashi akan ki, amma in kina mai biyayya sai rayuwar ku ta zama abin burgewa, kin ji ko, share hawayen ki wasa nake maki," Sharewa ta yi, maganar Abbah ta shige ta sai ta samu gwarin guiwa ta fita, a waje ta tadda Hassan, Yousuf kuwa d'an d'aga labule ya yi yana leqen su, Atiyyaerh ta hango shi, amma shi bai kula ba, he is busy wajen kallon Hassan,murmushi ta yi mai sauti, har haqoran ta suka fito, Hassan yace, "Wato kina murna zaki auri dan uwan ki ba ni ba ko?" Cikin sauri tace " A'a ba haka bane, kawai naga yanda ka fahimci Abba da sauri ne," " To ba dole ba, wannan yayan naki kamar zai doke ni, sai muzurai yake," Dariya suka saka, a tare, ya taka zuwa wajen motar shi, ya d'akko wata leda da kwali a ciki ya bata ya mata fatan alkairi ya tafi, yana shiga mota ya kifa kan shi ya fara zirarar da hawayen rasa ta a karo na biyu, da kan shi ya rarrashi kan shi ya tafi, tana shiga ciki ta gan shi ya had'e rai sosai, itama jiman tawa Hassan take, kan ta tsaye ta je ta zauna akujerar dake kusa da tashi, miqa masa ledar hannin  ta ta yi tace, " Yah kaga Hassan ya ban ya tafi, sai na ji ya ban tausayi," " Eh shiya sa naga sai dariya kuke kamar kema kina son shi kar ya tafi ko?," Dariya ce ta kama ta amma ta dake,ta ce " Laaa Yah ya akai ka gani?" "Ina tsaye jikin labulen nan na ga komai ai," Dariya ta saka sosai harda duqawa, tin yana tsumewa shima ya saka dariyar,ya ce, " kinga laifina ne? Na sani ko ya yi yunqurin gudar min da amarya?" Dariya suka dad'a sawa, " kai jama'a ayi ai auren nan na huta, ina qailula gaba d'aya kun cika mana kunne da dariya, haba," "In kin gaji da ganin mu gobe ma a daura mana aure ki ga in ban d'auke mata ta mun tafi ba" Haka suka yi ta zolayar juna kafin daga bisani ta basu waje su ka sha hirar su ta masoya. Auwal ne a qofar wani gida, na masu qaramin qarfi,  yana tsaye da alama wani yake jira, wata budurwa ce da zata kai sa'ar su atiyyaerh , ko ta girme su da kadan, ta fito tasha kwalliya, anyi daurin ture kaga tsiya, sai taku take cikin isa da rausaya, tana leqowa waje sosai naga kyaun ta ba laifi,ta hadu, ga shape mai kyau, murmushi Auwal ya yi, ciki naga ta masa jagora suka shiga, a soron gidan an shimfida tabarma da abinsha a jug, da qaramin cup, sai flask da alama abinci ne a ciki,cikin zazzaqar muryar ta ta ce, "Sannu da zuwa," washe Baki Auwal ya yi ya ce, "Ke za a yi wa sannu da qoqari, sai kace wani babban baqo ko Wani saurayi zaki min wannan tarba ta musamman haka," Dariya ta yi mai cike da jan hankali sannan ta ce, "Ai kai saurayi na ne, dama ba na kowa ba," Se ta yi wani farrr da ido,habaaaa suman xaune Auwal ya yi, (Hahaiiiii cassssss Auwal ya je zance💃🏻💃🏻💃🏻) A haka dai suka gama hirar su Auwal ya bata kud'i ta qi amsa, shi kuwa ya matsa da kyar ta amsa, ta masa godiya ta shige gida, Auwal ma ya ja motar shi ya koma gida cike da farin ciki, Rasheedah ya gani tsaye ta riqe qugu, cikin rashin kunyar ta da ta Saba ta ce Masa, "Wai ni ban gane maka ba kusan yau sati biyu kenan, sai ka na kaiwa dare, in ka fita, ko kana zaune ka shirya ka ci kwalliya ka fita Ina ka ke zuwa? " Ko ci kan ki bai ce mata ba, dan har yanzu baya kula ta, domin ya kula sam bata risina ba sai ma abinda ya yi gaba, cire kayan shi ya yi ya shiga wanka ya fito ya juya mata baya ya kwanta abin shi, ta yi ta bambami bai ce mata bari ko ci gaba ba. Washegari da yamma ,Sulaiman ne ya shiga gidan shi da wani abokin shi,se da  ya nuna ma baqon nashi wajen zama sannan shi kuma ya shiga ciki, dakin Abban su ya kwankwasa, Rasheedah ce ta fito, ya ce mata Abban su na nan, fuskar shi ba walwala, kallon shi ta yi na wasu 'yan  sakonni sannan tace masa yana ciki, kafin ma ya ce mata komai Abban ya fito cikin shiga ta kamala, yace, "Mu je ko," Gaba Sulaiman ya yi shima Auwal ya bi bayan shi, Rahseeda ce ta kama haba, ta ce, " Yau nake ganin ikon Allah, akan waccan shed'aniyar yarinyar kowa ya juyan baya, lallai dani take zance," Juyawa ta yi ta koma dakin. Bayan Abokin Sulaiman mai suna Qaseem ya gaida Abba ne, ya gabatar da kan shi a matsayin wanda yake son Afrah, kuma yana aiki da Aminu kano Teaching Hospital tare da Sulaiman, sannan iyayen shi suna nan a unguwar Kabuga, bayan ya gama ma Abba bayani ne, Abba ya masa izinin ci gaba da zuwa wajen Afrah dan su fahimci juna, kuma in da hali yana son had'a auren ta dana dan uwan ta, Qaseem ya yi matuqar farin ciki da hakan,dan godiya ya dinga yi kamar zai kwantawa Auwal,Suna gama tattaunawa Auwal ya miqe ya koma ciki, Auwal d'in na shigewa Qaseem ya miqe ya daka tsalle, ya fad'a kujera ya na murna,Sulaiman ya Kai masa duka a kafad'a ya ce, "Kaiiii shegen a gidan surukai kk dai a rage wannan rawar kan," "Kai ka ga haka, ni yanzu na gama zama d'an gida, je ka kiran masoyiya ta mu gana," "Tab yaro ni yayan ka ne ai ba wai qanin ka ba," Durqusawa Qaseem ya yi a qasa yace, "Dan Allah yayah kiran qanwar ka na zanta da ita," D'age kai sulaiman ya yi ya dora qafa d'aya kan d'aya, yana kad'a qafar shi a dole ana neman alfarma wajen shi, kwafa Qaseem ya yi ya miqe tare da zama a kujera ya ce, "Kar kaje d'in nima za ka zo zance wajen walida na ga uban da zai kira ta, ni haka nake maka?" Ai da sauri Sulaiman ya miqe ya shiga dakin Afrah ya sanar da ita zuwan Qaseem, " Yah wane haka?" " Abokina da kk ce ya taimaka maki kwanaki, shine yazo, Abba ya masa izinin ganin ki," Cikin tsallen murna ta sakko daga gado, ta rungume Sulaiman, tana murna, kiss ta masa a kumatu ta fad'a toilet, hab'a ya kama, sannan ya kama qugu ya tokare qafa d'aya ya bud'e baki yana kallon qofar da ta shige, Murmushi kawai ya yi sannan ya fita waje,wato dai kenan itama tana son shi, kad'a kai ya yi ya sanar da abokin nashi tana zuwa shi ya shiga in sun gama ya masa waya. Tana can ta rasa ma wacce kwalliya zata yi, daga qarshe ta yanke kawai bari ta shafa powder ta shafa mai a bakin ta da kwalli, dan bata son bata masa lokaci, tana gamawa ta saka doguwar riga ta yane kan ta da mayafin rigar, ta fesa turaruka masu sanyi ta fito, ta zo ta same shi, kan ta a qasa sai murshi take shima haka, zama ta yi a kujerar da ke d'an nesa da shi sannan suka gaisa, ya qara jaddada mata me ya kawo shi, ta yi na'am da shi, suna cikin hira ne Rasheedah ta fito, ta gan su, kallon inda suke ta yi ta tsaya turus, wadannan kuma yaushe suka jone, dan ta san yaron, amma ita wannan had'i sam bai mata ba, yaron fa ba wani mai arziqi bane, ita ko so take Afrah ta auri hamshaqi, yanda zata fantama itama, kan ta gama nazarin ta taji yana gaida ta cike da girmamawa, amsawa ta yi ta shige kitchen ta fara abubuwan da zata yi, ba su jima ba ya mata sallama ya fita,ya kira Sulaiman suka tafi, Kamar daga sama Afrah ta ji Rasheedah ta ce, " ke meye had'in ki da wancan kuma? Yaron da bai aje ba bare ki saka ran zaki mori wani abu a wajen shi shine ki ka tsaya b'ata lokaci da shi?," "Umma tinda ya mallaki soyayyata ba ruwana da abinda ya tara, Abba ya aminta da shi, Yayah da Yah sulaiman sun aminta da shi, haka Atiyyaerh ta san da zaman shi, Umma ke me zai sa ki nuna rashin amintar ki? Saboda ba shi da abin duniya? Har yanzu zamana a gidan ba mashinshini be ishe ki ba ko? " Auwal ne da ke Jin dik abinda suke magana akai ya ce wa Afrah " Ba ita zata aurar da ke ba dan haka shige ki kama abinda zaki ni na fita anjima in na kusa dawo wa ki hadan kunun ayan nan da kk min rannan, Allah ya miki albarka," wuce wa suka yi suka bar Rasheedah a tsaye baki sake. *DUBAI*............ *Allah ya sa Daddy ya dawo😭😭* [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 30: Iska ya shaqa tare da lumshe ido, ya d'auki a qalla second fiye da 20 kafin ya bud'e idon shi, kallon filin jirgin Aminu Kano yake kamar wani baqo a qasar, yayi matuqar kyau, fuskar shi ta yi fresh ya aje gemu me tsaho me sheqi kamar Wani baqin balarabe,fatar shi mai ruwan chakulan ta yi luwai luwai irin na 'yan hutu, ba qaramin kyau ya yi ba, yana kalle2 ne ya buge wata matashiyar yarinya, da ba zata wuce shekara 27 ba, juyowa ta yi cike da nutsuwa fuskar ta sanye da niqab ba a ganin komai a jikin ta sai idanuwan ta, hatta da hannayen ta da qafar ta sanye suke cikin safa, doguwar rigar da ta Sanya ta yi mata das a jikin ta gwanin sha'awa sai ta yafe Kan ta da mayafi baqi, Ido suka had'a da wanda ya buge ta, tsayawa ta yi tana kallon shi, ba qaramin tafiya ya yi da ita ba,tin bayan rasuwar Sakeenaah be tab'a tozali da idon macen da ya fizgi hankalin shi ba sai yau,yarinyar ta yi matuqar burge shi, yana yin shigar ta sai ya tina masa da margayiya, nan take ya d'auke kan shi, tare da bata hakuri, dan a tinanin shi matar aure ce, murmushi ta masa ta nuna mai ba komai, bayan ya fita ne ya tadda drivern shi, sai washe baki yake ,bakin nashi yaqi rufuwa, da gudu ya isa ya rungume uban gidan nashi, har hawayen farin ciki sai da suka zuba masa, shima cike da murna ya rungume shi, budurwar nan tana kallon su cike da sha'awa, itama motar da zata d'auke ta ne ta tsaya gaban ta, shiga ta yi drivern ta ya ja ta,Adnan Shima ya shiga tashi suka fara tafiya, drivern shi na ta bashi labarai akan abubuwan da ya Saba Sanar da shi tin bayan tafiyar shi ba tare da kowa ya san shi d'in ido da kunnen Adnan d'in bane,cike da jiman ta sabbin abubuwan da ya ji a yanzu ya ke jinjina Kan shi,har suka isa wani jibgegen gida Mai matuqar kyau da tsaruwa, bud'e masu gate d'in aka yi, tin kan motar ta gama shiga gidan wannan motar da ta d'auko yarinyar nan ta shiga gidan dake kallon gidan da Adnan ya shiga, juyawa ta yi ta kalli gidan, kan a rufe gates d'in kowanne gidan a tsakanin su, Mai gadi ma da sauri ya duqe gaban Adnan yana kukan farin cikin sake ganin shi, "Ashe da raina Allah zai nufa na sake saka ka a ido na, kaiii Allah na gode maka," Daddy ne ya d'aga shi, ya miqar da shi, ya rungume shi suka gaisa a haka, sannan baba Mai gadin ya koma ya qara tabbatar da rufe gidan suka dunguma suka shiga ciki baki d'ayan su, direct d'aki Adnan ya shiga,ya rage kayan jikin shi, ya shiga bathroom ya yi wanka, ya dad'e yana zubawa kan shi ruwa, yana tsaye yana tina masoyiyar shi wadda bata tab'a barin zuciyar shi ba ko da da minti d'aya ne, haka ya fito ya shafe jikin shi da mayuka, ya fesa turaruka, ya saka jallabiyya, ya fita dinning dan kukun shi ya yi masa waya ya sanar da shi abincin is ready, zuwa ya yi yaci ya sha, sannan suka zauna dika suka sha hirar yaushe gamo, suma wannan abincin da yaci shi suka ci, Adnan ne ya ce, "Da daddare zamu je ka kaini gidan mu na ga Abbana, da Mama na, ba qaramin kewar su na yi ba, ni yanzu Atiyyaerh ce babbar damuwa ta,ka na ganin in ta ganni ba zata ji haushi ba? Wanne irin reaction ka ke ganin za ta yi?" Ya na gama fad'in haka se ya sadda kai qasa, idon shi, ya cika da kwalla,cikin tausayawa driver ya ce, " Ranka ya dad'e kar ka saka wannan a rai ya dame ka, inshaa Allah fushin ta ba zai wuce yau ba, ka kwantar da hankalin ka, yarinya ce da ta haifu daga wajen marigayiya, yarinya ce mai biyayya da hakuri da yafiya, indai zata yafewa Waccan shaid'aniyar to ko zata yafe maka," Adnan ya gamsu da bayanin driver ya kad'a kai, a haka suka d'an taba hira ya je ya yi sallar la'asar, bayan ya idar ne ya fita dan shan iska, daga saman balcony ya hango wata kyakkyawar halitta, baqace doguwa mai shape mai kyau, ta saka riga mai siririn hannu, fara sol, sai gashin ta da yake a d'aure, ya zauna a dokin wuyan ta irin gashin nan ne na 'yan Afrika Mai cika da tsaho,hannun ta riqe da mug ta na kora baqin shayin da ke turiri, sai d'ayan hannun tana danna wayar ta, direct wajen wata kujera ta nufa, da qaramin table a wajen, ta aje mug d'in ta ci gaba da danna wayar ta, band din da ta d'aure gashin kanta ta cire ta baza gashin, tai gaba da shi sannan ta saka hannun ta ta baza qasan shi, kamar mai susa kamar me son shan iska a cikin gashin nata, Adnan bakin shi a sake ya na bin ta da kallo, d'agowar nan da zata yi, tana lumshe ido dan dad'in susar da take wa Kan ta,idanun ta suka sauka akan fuskar shi, dake kallon ta, cike da kunya ta fara dabur2 din me zata yi, d'aga hannu ya yi alamar ta yi hakuri, murmushi ta yi tai saurin miqewa ta nufi hanyar da zata shigar da ita d'akin ta, ko mug d'in bata tsaya d'agawa  ba tai gaba, daidai zata shiga ciki ne ta juyo suka sake had'a ido, murmushi suka yi wa juna ta shige ciki, Daddy ne ya shafa gemun shi, mai cilli2n furfura a jiki, ya yi murmushi, ya koma d'akin shi, fuskar ta kawai yake hangowa,can ya ce, "Subhanallah in tana da aure fa?" Tashi ya yi daga kwantawar da ya yi, yana nazari, nan jikin shi ya yi sanyi, dan yanayin ta ya mai kama da marigayiyar shi, "Allah kasa bata da miji, tabbas zan gabatar ma da su Abba daddad'an labari na samun matar da zan aura na San za su yi farin ciki sosai, baffana har ya yi fushi ya dena d'aukan wayata saboda sun bani Umarnin neman mata na yi aure na qi, in Allah ya cika min buri na sai dai na je Sanar da su maganar aure"  Da wannan zantukan ne ya miqe ya fad'a bathroom dan d'aura alwalar sallar magrib da ya ji ana ta Kira, sannan ya fita masjid dan yanzu ba gajiya a tare da shi kamar d'azu, ya na fita suka had'u da wani dattijo da in zai girme shi bai fi da irin 4 to 5 years dinnan ba, suka gaisa, suka shiga masjid d'in a tare, bayan anyi sallah ne sun fito zasu koma gidan su, suka qara gaisawa, inda mutumin yake sanar da shi shi maqocin shi ne ashe, sanar da shi ya yi sunan shi Alhaji Haladu Gwandu, yana da mata da d'iyar su da ta dawo ba jimawa d'azu daga Dubai  mai suna Fauziyyah a can ta yi karatun ta, ita d'aya Allah ya basu, shima sanar da shi ya yi taqaitaccen tarihin shi,nan take mahaifin Fauziyya ya masa ta'aziyyar rasuwar Sakeenaah, sannan ya masa fatan samun mace ta gari, sukayi sallama da juna kowa ya shige gida, direct d'aki ya je ya shirya cikin shigar da kowa ya gan shi sai ya qara, dan kuwa komai ya ji, fitowa ya yi yana baza qamshi, ya yi wa Auwal waya yace su had'u a gidan Abba, fita ya yi inda motocin shi suke ya shiga wadda driver ya tada, Baba me gadi ma tini ya bud'e gate shi kad'ai ake jira dama, driver ya ja su sai gidan Abba. Kowa ya shirya cikin shiga mai kyau da Kamala kamar masu zuwa Wani event, Rasheeda ta tambayi inda za a je yafi sau ba adadi ba wanda ya kula ta, haka suka d'au hanya, ana tafiya ta gane ina za a ta ja tsaki da qarfi da yasa kowa kallon ta, "Da ace min gidan gyatumin nawa za a ake ganin asarar hakan Allah ya kyauta to," Ko ci kan ki ba wanda ya ce mata, suna isa suka tadda wata jibgegiyar mota me numfashi a qofar gate d'in gidan, kowa sake baki ya yi yana kallon motar musamman Rasheedah da ta dinga zuba santin motar, suna tsayawa Auwal ya fito, shima Adnan ya fita daga cikin motar da taimakon driver ta hanyar bud'e masa motar ya tsaya a gefe Suna wa juna murmushi, dan tinda yazo gidan suke a tsaye a nan saboda ya rasa ta ina zai fara sa qafa ya shiga cikin gidan, kallon shi su Afrah suke, Yousuf kam tabbas ya san wannan shine Daddy, Auwal kam hawayen dad'in ganin Adnan ne suka wanke masa fuska, shima Adnan d'in haka,Rasheedah da ta fito daga baya tana mitar tsaiwar me suke, tana ganin Adnan d'in kusan zama ta yi a qasa a wajen, Afrah da Sulaiman ne suka taro ta, Cikin wata iriyar murya me rawa ta ce, "Waaa nake gani haka kamar Adnan?" Cike da jin d'acin labaran da ya ji daga mutanen shi ya kalle ta,ya kauda kai, ya kalli Auwal ya taka ya rungume shi, shima qanqame shi ya yi kamar wanda aka ce wa zai sake komawa inda ya fito,yaran ma rungume shi suka yi,banda Afrah da ke gefe hawaye na ta zarya a idon ta, dama wannan shi ne Daddy kenan? Shine abinda take ayyanawa a ranta, me zai sa ya tafi ya bar Atiyyaerh, ta sha wahala wajen Umman su? Bayan da ga dukkan alama yana cikin rufin asiri, kauda kai ta yi ta shige gidan da gudu, dan in Atiyyaerh bata yafe masa ba itama bazai ga fara'ar ta ba, a ranshi ya tabbatar da labarin da yaji game da shaquwar Atiyyaerh da Afrah, jikin shi ya yi sanyi sosai da ganin hakan, ya tabbata akwai had'in kai,a tsakanin su, d'unguma suka yi ciki baki d'ayan su, har lokacin Rasheedah bata daina kallon shi ba. Da kuka Afrah ta shiga, ta fada cinyar Atiyyaerh da take zaune ta shafa hadin Cinnamon da lemon tsami,kwai, zuma da d'an sugar kad'an a ciki ta shafe a jikin ta, tana ta danna waya,tana kallon hotunan Yayahn ta, daga ita sai qaramar riga iya guiwa, data matse ta daga sama, sannan ta sake daga qasa, mai siririn hannuwa,rigar na da aljihu a jikin ta, kalar yellow, ta daure gashin ta ta nannade shi, ta yi masifar kyau, wayar ta ta zira cikin aljihun rigar  hankalin ta tashe take tambayar Afrah me ya faru? Amma ta kasa magana, sallamar Abban su Auwal ne ta katse mata tambayar, tafe dashi akwai wani mutum mai cikar kamala, da zati wanda ta kasa tantance waye, amma zuciyar ta sai qara qarfi take wajen bugawa......[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼          WRITTEN   BY HAERMEEBRAERH *Ina masu tambayar yaushe za a gama Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA?   To ina mai yi maku albishir da samuwar Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA dan kuwa ya kammalu ya zama ready, ga masu so su mallaki nasu ku yi min magana ta 09031416423 idan an yi payment ɗin #500 ta wannan account ɗin 0006366584 Ja'iz bank, Hamida Sanusi Ahmad,zan tura wa mutum nashi da yardar Allah...kar ku bari labarin Muid'o da Jiddah ya wuce ku💃🏻❤️* *Duk mai son ta koyi yanda zata haɗa kayan gyaran jiki domin  sana'a ta neme ni a 09031416423 Dan ta mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA A FARASHIN #1000 kacal* Page 31: Mama ce ta fito  daga d'akin su Abbah na biye da ita a baya, tana neman Atiyyaerh dan ta raba masu musun da suke akan kwanan wata, " ke zo ki raba mana wannan gaddamar, yau nawa ga watan bat......." Dakatawa ta yi da zancen ta,dariyar Abbah ce ta d'auke lokaci d'aya mamaki ya maye gurbin ta, "ADNAN" Suka had'a baki wajen fad'a,Juyawa Adnan ya yi daga barin kallon Atiyyaerh ya Maida idon shi Kan dattijan guda biyu, Cike da tsananin farin ciki ya tafi wajen Abbah da Mama da idanun su suka ciko da kwallar farin ciki,rungume Abbah ya yi, ya fashe da kukan murna, Abbah ma kyakkyawar runguma ya Masa ya na bubbuga bayan shi,bakin Mama ya qi rufuwa saboda farin ciki, "Shekara 19 kenan rabon mu da Sanya ka a idanun mu Adnan sai yau Allah ya yi zamu sake saka a idon mu, ya ilahi kullum tinani na baya wuce Allah kar yasa na mutu ban sake ganin ka ba, mu nemi yafiyar ka akan sakaci da kuma cika wasiyyar da bata zamo alkhairi ba, dan babu abinda Atiyyaerh ta tsinta wajen Rasheedah sai uquba da bala'i gashi ita wadda aka yi domin ta har yau Imani da tsoron Allah da son zumunci be shiga zuciyar ta ba,a qoqarin cika wannan wasiyya Adnan mun zalunci marainiyar Allah,ka yafe mana Adnan, ka yafe mana," Kuka ne ya ci qarfin Mama a dole ta yi shiru da maganganun da take ta zubawa, Abbah ne ya samu waje a kujera ya zaunar da ita, yana lallashin ta, don yasan kusan kullum sai ta yi kuka akan hakan , ko yana gida ko ya fita, "Mama ni ne zan nemi yafiyar ku, ku yi hakuri da saku cikin kewa da tinani da na yi, inshaa Allah na dawo gare ku kuma na dawo wajen 'yata ba abinda zai sake rabamu da ku, ina fatan kun yafe min?" Atiyyaerh ce ta ke bin shi da Wani irin kallo, cikin qasa da murya ta fara magana, " Yafiya? Yafiya fa kace Daddy? All this years? What have you been doing that is so important da ya sa ka yi abandoning din mu? u ar there leading a luxery life, ni ina nan ina azabtuwa, kamar marainiya mara gata, mara galihu, mara dangi, sai mariqiyar da ta min riqo kamar bamu had'a jini da ita ba,me na muku,

Chapter 18 of 21