zame jikin ta a hankali ta yi d'aki, ta na shiga ta rufe qofar da qarfi ta saki wani wahalallen kuka, yi take tana qarawa ba mai lallashi, haka ake ji a kishi, ko ita kad'ai ce ke jin haka?
Tinda ita bata son a had'a ta da kishiya a komai nata, sai ta ji baqin cikin duniya ya mamaye mata rayuwar ta, ashe kishin miji ya fi zafi akan kowanne kishi, da kyar ta daddafa ta hau gado,ta jima kafin bacci mai dad'i ya d'ebe ta.
Bayan sun gama ne sukai wanka,suka shirya cikin shiga mai kyau, zasu tafi gaidan su Abban, Leqawa Amarya tai dakin Rasheedah tace mata, ya kamata ta fara hada abincin rana zasu dan zagaya gidan su dawo,cike da umarni take fadan hakan, kuma fried rice za tai da coleslow, sai salad din dankalin daban, dan ita bata son ganye, Auwal yaci wancan, ita taci wannan, sai ta hada masu kunun aya, sannan ta gasa masu nama ya yi dan ruwa-ruwa,
" kinsan ni har yanzu ba wai na warke daga ciwukan da honey ya jiman bane, lallai kina fama dama haka yake? Ayi ta abu d'aya ba ya gajiya? Lallai ki na fama"
Cike da zolaya ta sa kai ta bar d'akin ta bar Rasheedah na sharar kwalla, a mota ta same shi, zaune ya na jiran ta, bud'e mata ya yi ta hanyar miqa hannun shi ta shiga ta zauna ya ja su sai babban gidan su Adnan, inda su Mama da Abban su Rasheedah ke zaune a yanzu.
Suna Isa Mai gadi ya bud'e masu gate, suka gaisa da Auwal da Khadeejah sannan suka qarasa ciki, hannun Khadeejah na cikin na Auwal suka Isa bakin qofar shiga sashen su Mama, da sauri ta karb'e hannun ta Cike da Jin nauyi ta yi gaba, abubuwan ta na ba shi mamaki, a gida ta zage ta na ta zuba masa soyayya, amma yanzu wai kunya take ji, Murmushi ya yi ya kad'a Kai ya bi bayan ta.
Zaune ya hango su Yousuf da Atiyyaerh wadda ta shagwabe ma Yousuf d'in kamar zata shige cikin shi shi kuma yana ta wani lallashin ta, suna ganin su Abba Auwal suka nutsu, suka durqusa su na kai gaisuwa, a hankali kowa ya hallara a parlourn da yake Babba sosai, Sulaiman da Walida, Daddy da Fauziyya ustaza wadda ta sha doguwar riga ta nade kan ta da mayafin ta,fuskar ta ba wata kwalliya sosai amma tayi kyau daidai ita,Mama da d'an tsohon mijin ta ne suka zauna a kujera Mai d'aukan mutum biyu, nan aka hau barkwanci da gaishe2 ana tsaka da gaishe gaishen kowa ya kula ba Rasheedah suka zo, Atiyyaerh ce tace,
"Abbah ina ummana?"
Khadeejah ce ta amshe da cewa,
"Tana bacci ne da za mu fito se naga bai kamata mu tada ita ba, shiyasa muka taho,"
kallon ta Atiyyaerh ta yi tai murmushin yaqe,dan gani take kamar ba gaskiya ta fad'a ba, ana ta hira ta yafici Yousuf suka zame jikin su suka bar gidan, a motar Yousuf d'in da Adnan ya sai masa suka fita, ko da suka shiga gidan sun same ta ne a zaune, Umman nata ta rafka uban tagumi tana kuka dan tin da amarya ta gama mata bayanin me zata dafa take zaune take kuka,ba abinda ya bata ranta sai kalmar ta ta qarshe, akan halittar mijin da take taqama nata ne ita daya, yau ga wata 'yar cikin ta na yabawa halittar shi a gaban ta, tina hakan ne ya sa ta fashe da kuka,
Da gudu Atiyyaerh ta Isa gaban ta ta durqusa tare da kama hannayen ta ta ce,
"Subhanallahi, Ummana me ya faru? Me matar can ta yi miki, dan da ganin matar nan za ta yi mugun hali, "
Cikin tsananin kuka Rasheedah ta sake riqe hannun Atiyyaerh da kyau ta na qoqarin durqusawa a gaban ta ta ce,
" Atiyyaerh ki yafe min, in baki yafe min ba ba zan tab'a ganin daidai ba a rayuwa ta, matar nan so take ta sa zuciyata ta tarwatse, ban tab'a sanin haka kishi yake da ciwo ba sai yanzu, ashe da hassada ce ke d'awainiya da ni, na rasa gane tsakanin cutar hassada data kishi waccece tafi zafi, gaba d'aya ina da su Yousuf, tabbas ina daf da fad'awa jerin masu ciwon zuciya, Atiyyaerh ba kiji yanda qirji na ke bugawa ba,"
Tana kaiwa nan a maganar ta se ta tina d'azu da Amarya ta dorawa Auwal hannun shi akan qirjin ta,wani kuka ta saki me qarfi kamar wata qaramar yarinya, hakan da ta yi ya yi matuqar ba Atiyyaerh tsoro, kar Umman tasu ta kamu da wani ciwon fa, kamar wadda aka mintsine su ka ga umman sun ta miqe ta daura dankwali ta yi waje,bin ta Atiyyaerh ta yi itama, a kitchen ta same ta, tana qoqarin d'ora abinci, haduwa suka yi ta taya ta suka yi komai a tare suka gama, Atiyyaerh ce ta dinga d'iban abincin ta na sa wa a motar Yousuf , sannan suka shirya har Rasheedah suka nufi can babban gidan.
Khadeejah na ganin Suna shiga da warmers na abinci se ta yii murmushi kawai, tare da jinjinawa zuciya mai kyau irin ta Atiyyaerh, dan in itace sai Rasheeda ta gane shayi ruwa ne, bata ce komai ba ta yi mata sannu da aiki, itama bata nuna mata komai ba ta amsa, da yauwa,
Atiyyaerh ji ta yi an dafa kafad'ar ta sannan aka ce,
"Abun haka ne Aunty Atee ba gayya a aikin? Yaushe ma ki ka bar gidan?"
Ta na juyawa se ta ga walida ce ashe matar Sulaiman, Murmushi ta mata kawai, ta ce,
"Ba komai amaryar mu ki huta,wataran kema zaki yi naki ai,"
Tashi suka yi dikan su suka gyara inda za a ci abincin, kallon Rasheedah da ke rakub'e a kujera Atiyyaerh ta yi kamar kazar da kwai ya fashewa haka ta biyo su zalo2, gaisuwa ta kai wajen su Abbah da Adnan da hankalin shi ke kan matar shi,ita kuma sauran yaran suka gaida ta,ana ta hira amma banda ita ta yi shiru kamar marainiya, Auwal na ta saka ta a hirar amma shiru kk ji, dan ita yanzu tsoron su take, in sunkoma kuma su gasa ta, bangaren Mama kuma ta ji dad'in ganin sauyawar ta, a tinanin ta jan girman ta take yi.
A haka suka tashi bayan sunci sun sha, mazan suka wuce masjid matan suka tattara wajen suka gyara kowa ta yi bangaren ta, Atiyyaerh ta taya su Rasheedah debe kaya suka mayar mota su Rasheedah suka shiga mota suka bar gidan.
Atiyyaerh ta kasa bacci cikin dare, sai juya abinda ta gani take a ran ta, ta San irin rayuwar kana so ka yi abu amma a hana ka, ta yanda ko magana ba ka da izinin yi sai an Hana ka, juyi ta yi ta rungume Yousuf da ya yi shiru ya na kallon sama, a hankali ta ce
" Yayah ni kam nace ko za a samo wa Umma yar aiki ne, kasan bata wani saba da aiki ba,gashi yanzu ba ita kad'ai bace akwai kishiya, kar aiki yazo yana mata yawa,"
"Batta kawai zata iya, aikowa neman ladan aure yake itama a barta ta nemi ladan nata auren"
Ya ja ta jikin shi da kyau,ya kwantar da ita, gaba d'aya hankalin ta baya jikin ta, ya na can wajen tunanin halin da Umman ta ke ciki.
Cikin ikon Allah Walida da Atiyyaerh nada wata biyar a gidan suka samu ciki,cikin walida nada wata uku, Atiyyaerh na da wata hud'u, ba qaramin murna kowa ya yi ba da samuwar cikin nasu, musamman ma cikin Atiyyaerh Mama ta ji tsoron kar itama ta yi jinkiri irin na Sakeenaah se gashi cikin qanqanin lokaci ta samu,se da ta yi wata rashin lafiya ne kowa ya San ta na da cikin dan boyewa take, wai kunya take ji, Sulaiman ya sha fadawa Yayahn shi hasashen shi na anya Atiyyaerh bata da ciki kamar walidan shi? Sai Yousuf d'in yace,
"kaii anya kuwa ! Yanzu Kai wannan marar ce za a ce akwai d'an mutum? Inaaa bana Jin ta na d'auke da ciki gaskiya"
Haka Sulaiman ke barin maganar ba dan ya yarda cewar babu d'in ba,to fa sai da ta yi wannan zazzabin mai zafi aka je asibiti aka tabbatar akwai sannan Yousuf ya yarda,ranar kuwa kowa ya ga rawar Kai a wajen shi ji ya dinga yi kamar zai hadiye ta dan murna, ta roqe shi ya rage rawar Kai ya qi, Suna barin asibiti basu zame ko Ina ba sai gida, a babban parlour ya kwaza labarin samuwar cikin nata, ta hanyar tsokanar Mama zata samu d'an jikar ta ta wajen su ba da jimawa ba, aiko Atiyyaerh ji ta yi kamar qasa ta bud'e ta shige dan kunya.
"To da ka ke ta fad'a wa mutane ai ba ni kad'ai bace, har da Walidah da Afrah,"
Ta fad'a ta na tura baki, dariya aka Sanya Baki d'aya, Mama na ta godewa Allah a cikin zuciyar ta da bakin ta, ganin yanda ta gama rayuwa da Ahmad ba labarin ciki ya Sanya ta tsoron ko itama zata yi jinkirin haihuwa irin na Sakeenah se gashi abun farin cikin ya samu da wuri, Daddy Adnan kuwa kallon 'yar tashi yake Cike da so da qauna da tausayawa irin ta d'a da mahaifi, fatan alkhairi da Sanya albarka iyayen nasu suka musu, tsabar kunya ko amsawa bata yi ba ta gudu d'aki aka bar Yousuf da amsawa da bada labarin sunan da yake so a Sanya in macece, in namiji ne ga sunan da yake so,dariya kawai akai ta mishi saboda sai halin shi na 'yan fari ya bayyana a ranar, Sulaiman ne me Jin kunya shi kuwa Sam be ga abun kunya ba a wajen.
Sanda labarin ya riski Rasheedah kuwa ta yi murna sosai,ta Sanya albarka tare da fatan Allah ya sauke su lafiya.
Bayan shekara shida, gidan su Atiyyaerh ya zama babban gidan iyali, Atiyyaerh na da yara hud'u,haihuwar ta ta fari ta samu d'iya mace suka Sanya mata sunan marigayiya wato Sakeenah sai Kuma aka samu Mai sunan Abbah daga baya Kuma ta haifi 'yan biyu mata, Walida Kuma nada yara uku,dika maza, babban dan Afrah a nan gidan yake da zama, mai sunan Adnan, takwaran daddy kenan, khadeejah na da Yara biyu mace da namiji aka sake maimaita sunan Sakeenaah namijin Kuma Hisham, sai Fauziyyah wadda ke dauke da cikin fari yanzu, Adnan yana fatan ta haifi mace ya Sanya mata sunan Sakeenaah,gani yake in za a cike gidan da suna Sakeenaah ba laifi bane.
Atiyyaerh da Yousuf ne Kwance a babbar kujera a parlourn su Suna ta hirar wajen aikin Yousuf d'in Yana Sanar mata qarin matsayin da ya samu ta na ta zuba masa addu'a, suka Jiyo kukan Little wato Auwal qarami, Wanda shi ne autan Atiyyaerh, Rasheedah ce ke d'auke da shi a hannun ta, ta na tafe ta na mitar ya hana su bacci,kwanan ta goma sha uku a gidan ta zo wajen Mama dan jinyar ta saboda fama da take da ciwon qafafu ,kukan da ya sake tsanyarawa ne ya sa Atiyyaerh tashi zaune da kyau dan ta ji shin shi din ne ko yaya? Da sallama ta shiga parlourn ta miqa wa Atiyyaerh shi sannan ta ce,
"To ga shi nan na dawo da Kai wajen Ammin taka,dan nema me rikicin tsiya, in sake zuwa ka ce zaka bini, ya hana mutane bacci,sai kace a dawa yake, ba a cikin gida ba,"
Dariya Atiyyaerh ta yi ta rungume shi sannan ta ce,
"Yi shiru Babana na kainaaa, Umma dai haushi take ji ka ce baka auren da ita, shi yasa rabu da ita ba za ka sai mata ragon sallah ba bana"
"Yo wannan Banda aukin zuba Kashi da fitsari a tsaye me ya sani?"
A hankali Atiyyaerh ta lallab'a shi ya koma bacci sannan ta je d'aki ta kwantar da shi ta dawo,
"Haka yake yi fa ko cikin dare sai ya baro d'akin su yazo wajena,Abbin su ya yi ta fad'a wai ni ke sangarta shi shi ya sa ya cika d'afa,ko yaron ma nawa yake oho"
"Aiko dai ya cika d'afa da gaske haba, Ina ne baya shiga da wannan siraran qafafun nashi kamar na sauro, amma da ya yi bacci a Wani wajen se an kawo miki shi"
Dariya suka yi dika Yousuf ya ce
"Ai gobe zai je ya ga budurwar shi can gidan Afrah Yaya zai Kai mu mu yini mata an kwana biyu ba a had'u ba" Yousuf ne ya kalle ta ya had'e gira sannan ya shafa gemun shi da ya ke tsaye a saman fuskar shi, sannan ya ce,
"Wai ke waya baki izini ne har ki ke lissafin fita? Tabbas kin tambaya amma ban fa ce na yarda ba,"
Cike da shagwab'a ta kalli Umman tasu da ke bin su da kallon burgewa ta ce,
" Ummaaa,"
Ta tura baki gaba ta na jiran taimakon Rasheedahn, cikin Murmushi Mai sauti ta ce,
"A'a Yousuf, ka barsu su sada zumunci mana ni Rasheedah na ga illar rashin son zumunci a rayuwa ta Wanda bana fatan daidai da daqiqa d'aya Allah ya sa Wani a zuri'a ta ya yi irin wannan halin, ko da wasa kar kana son raba abinda Allah ya riga ya had'a yake son kuma a dabbaqa shi,"
Cike da ladabi ya amince masu da tafiyar, Umman su na fita Atiyyaerh ta haye cinyar shi ta na murna,dan ita fa a kullum Jin ta take kamar wata qaramar yarinya bata Jin ta girma Sam sam,
"Dole ne a baka tukuicin barin mu zuwa unguwa da ka yi Mijin Ablaerh,"
Tini Atiyyaerh ta hau birkita masa lissafin kan shi, cikin in Ina ya ce,
"Daga yau ki dinga tambayar unguwa dik qarshen wata zan dinga barin ki indai wannan ne tukuici na"
Ta bangaren Rasheedah da amaryar ta kuwa komai ya wuce kamar Wani saba'ni be tab'a shiga tsakanin su ba, girmamawa sosai Khadeejah ke Yi w
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Ina masu tambayar yaushe za a gama Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA? To ina mai yi maku albishir da samuwar Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA dan kuwa ya kammalu ya zama ready, ga masu so su mallaki nasu ku yi min magana ta 09031416423 idan an yi payment ɗin #500 ta wannan account ɗin 0006366584 Ja'iz bank, Hamida Sanusi Ahmad,zan tura wa mutum nashi da yardar Allah...kar ku bari labarin Muid'o da Jiddah ya wuce ku💃🏻❤️*
*Duk mai son ta koyi yanda zata haɗa kayan gyaran jiki domin sana'a ta neme ni a 09031416423 Dan ta mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA A FARASHIN #1000 kacal*
Page 32:
Yau kwana hud'u kenan da dawowar Adnan daga Dubai,tin sanda ya je balcony d'in shi ya ga me kama da marigayiya be sake komawa ba, saboda ya na so ya gujewa hana ta fita nata balcony d'in dan Shan iska, idan ya ji ya na buqatar fresh air sai ya ja glass door d'in ya bud'e ya ja labulayen a haka iska zata shiga ta na kad'awa gwanin dad'i, ita kuwa Fauziyya zuwa balcony d'in ta ta tsaya ya zame mata kamar ibada,kullum sai ta je balcony d'in nata ta tsaya ko zata ga bawan Allahn nan me kyau da ta gani rannan, takan Sanya kaya masu mutunci wani lokacin harda mayafi dan bata so ya sake ganin ta a yanayin da ya gan ta a baya,to her biggest disappointment Adnan ya dena zuwa wajen,a kullum ta je bata gan shi ba tana shiga matsananciyar damuwa,a ranar sai ta zama wata iriyar shiru shiru bata son kula kowa bata son Kuma a kula ta.
Adnan ne sanye cikin qananan kayan da suka matuqar karbar jikin shi rigar shi ruwan chakulan wando Kuma baqi, sai qamshi ke tashi a jikin shi sakamakon feshe jikin shi da ya yi da turarukan shi masu dadin qamshi da tsada, se ya qawata kyakkyawar qafar shi da baqin takalmi, ya d'auki wayar shi ya fita, balconyn shi,da niyyar shan iska, ( Daddyyyy da niyyar dai ganin Fauzy🤣) yana zuwa da minti kamar 4 sai gata, ta fito, sanye cikin riga da wando, sai ta yafe kanta da mayafi, fuskar ta ba walwala ta fito ta tsaya ,dan a zaton ta yauma bazata gan shi ba, amma bata cire rai ba, kallon wajen shi ta yi cikin yanayin da ke nuna saddaqarwa akan ba ganin shi za ta yi ba yau ma, amma mamakin ganin shi da farin cikin ganin shi ya sa ta kusa sake wayar ta a qasa, wani murmushi ta saki mai nuna tsantsar farin cikin ta, d'aga masa hannu ta yi ba tare da ta sani ba, sai da ta kula da abinda ta aikata ta yi saurin saka d'aya hannun ta sauke wancan, dariya ya yi irin ta manya,ya d'aga mata hannu shima, alamar gaisuwa ta masa, da kai da hannu, shima ya amsa, nuni ya yi mata da yana son ya zo wajen ta,itama ta masa alamar amincewa, cikin kunya ta juya tai dakin ta da gudu,tana shiga ta haye saman gadon ta tana tsallen murna, a haka maman ta da take kira Mum ta shigo, tana ganin Mum d'in ta ta tafi da gudu ta maqalqale ta tana murna,cikin 'yar dariya mahaifiyar ta ta ce,
" Meye haka Baby zaki balla ni fa,"
"Mum ya zo yau, har munyi magana, ya ce zai zo anjima,na amince masa da ya zo, mom I can't wait to see him, I want to hear his voice, I want to know him mommy,"
Cike da fara'a mahaifiyar ta ta ce,
"To Alhamdu lilLAAH na maki murna Baby, fatana Allah ya sa ya zama alkairi a rayuwar ki, ya sa SHI NE JARUMIN KI da ki ke Jira, lallai a cikin kaff Wanda suka nemi auren ki ki ka qi su to wannan ya yi sa'a dan da alama da za a bar ki ke Zaki je neman auren shi da kan ki,"
Cike da shagwaba ta ce,
"Mommyyyyy! Ko da yake gaskiyar ki ne fa,nice na yi sa'a in kk ganshi tabbas zaki fi gane dalilin da ya sa na shiga wannan yanayin akan shi, he is so handsome and gentle, ya hadu Mum, i think i am deeply in love with him, Ya Rabby Allah kasa shine alkairi na,in ba alkairi bane a rayuwata da addini na, Allah ka min sauyi cikin sauqi ba tare da na wahala ba,"
A sanyaye ta qarasa addu'ar ta, Mahaifiyar ta ce ta shafa kanta, tare da sumbatar goshin ta ta ce,
" Allah ya amsa baby, ki kwantar da hankalin ki, rabon ka baya tab'a wuce ka,sannan abinda ba rabon ka ba baya tab'a samun ka,in Allah ya yarda alkhairi ne a gare ki shi yasa Allah ya had'a ku a airport Kuma ya Sanya kuka zama maqota"
D'aga kai ta yi ta na Murmushi da Kuma gasgata maganar mahaifiyar ta,suna tsaka da hira ta zabura ta ruga toilet tare da fad'in,
"Mum i have to look beautiful Ina zuwa na yi wanka na zo ki min kwalliya,"
Dariya maman ta ta yi tace,
"Baby ai ke dama can kyakkyawa ce baki buqatar makeup, sannan ma ke me Zaki da Kwalliyar tsofaffin, ki gama ki dai zo ki yi da kan ki tinda kin fini iyawa nima watarana ke kike mini,"
Tashi ta yi ta shiga duba ma yarinyar ta ta kayan da ya kamata ta saka,wata doguwar riga ce,Fara sol,da ratsin golden color a jiki,ta sha aiki ta wajen wuyan ta da hannu, ta tsuke ta sama sai ta yi fad'i sosai ta qasan ta, sai mayafin rigar shima kamar rigar ya sha ado ta d'akko mata, ta feshe mata rigar da turaruka masu sanyin qamshi, ta d'akko mata wani golden color takalmi, mai dan tsini amma ba can ba,ta aje mata,sannan ta yi murmushi tace,
" Allah ya bada sa'a Baby bari na je na had'a maku abun motsa baki kafin ki kammala, na fi so na yi da kaina kar mu fara da bashi abincin masu aiki ko"
Tana gama magana ta fita,Fauziyya kuwa ta na can tana qalqale fata, kamar ance mata tabawa zai yi ya ji ta fita ko da datti, bayan ta gama ta fito d'aure da towel tana ganin kayan da Mom d'in ta ta fiddo mata sai ta yi murmushi tace,
"Thanks Mum,"
Gaban mirror ta je,ta hau gayu, kwalliya ta yi sama2,wadda ta qara fitar da sirrin kyan ta, gyara gashin ta ta yi, sannan ta saka kayan ta, Masha Allah, duk wanda ya kalle ta dole ya yi marmarin qara wa,tana zira takalmi, Daddyn ta ya kwankwasa d'akin nata tare da sallama ya bud'e qofar ya shiga, kallon ta ya yi daga sama har qasa ya ga yanda ta yi masifar kyau, sai kawai ya tsaya a kan qafar shi d'aya ya na bin ta da kallon tuhuma,hannun shi d'aya a qugun shi sannan ya ce,
"Wannan gayun fa, ko dama can kina da masaniyar zuwan baqo wajen ki ne?"
Cike da jin kunya ta rufe fuskar ta, murmushi ya yi ya bata hannu akan ta je gare shi, miqa masa hannun ta yi, suka fita a tare, sai da suka je babban parlourn nasu sannan ya zaunar da ita kujerar dake d'an nesa da ta Adnan,da Auwal, dan ya sanar dashi zasu zance,Auwal ya yi ta tsokanar shi, daga qarshe yace in sun gama da nan shima zashi yaga tashi budurwar, kallon ta kawai suke,kamar sunga sabuwar halitta, Daddyn ta ne ya zauna kusa da ita suka qara gaisawa da su, itama ta gaida su, sannan Daddyn ta ya fara magana kamar haka,
" Alhaji Adnan, da Alhaji Auwal,naji dad'in zuwan ku matuqa, da kuma abinda ke tafe da ku,kamar yanda na sanar da ku d'azu in dai ta b'angare na ne ban da matsala akan hakan, sai ma fatan alkairi da zan yi a gare ku,amma ina son ku san wani abu d'aya,dik yanda zan baka goyon baya in baka nemi soyayyar ta ba lamarin ba zai yuwu ba dan ba zan yi mata dole ba,duk duniya bayan mahaifiyar ta, ita nake gani na ji dad'i, itace sanyin idaniya ta, ka ga kuwa duk yanda na kai da son ka in Fauziyya ba ta yi na'am da Kai ba gaskiya sai dai na baku hakuri, ina fatan zaka riqen amanar ta, kuma bazaka tirsasa min ita ba?"
" Inshaa Allah Alhaji ba zaka samu sabanin abinda kk so ba daga wajen mu,kamar yanda na Sanar da Kai nima ina da Yara ka ga ba zan so na yi wa taka ba daidai ba, Allah ya shige mana gaba a wannan lamarin,"
"Ameen, to ni bari na shiga daga ciki"
Sallama ya musu ya basu waje, kunya a wajen Fauziyya kuwa kamar tace qasa bude na shige,duk jin ta take a takure, ta saba zama gaban maza ayi hira ayi karatu amma wannan karon sai take jin ta wani iri,gaishe su ta sake yi suka amsa ta ja baki ta yi shiru,masu aiki ne suke shigo da kayan motsa baki, bayan sun gama ajewa sun tafi, Auwal ya gabatar da kan shi sannan ya gabatar da Adnan a matsayin Wanda yake son ta da aure ba da wasa ba, bayan kammala yad'a manufar su da Auwal ya yi Adnan na ya karb'e ya qara jaddada mata manufar shi akan ta sannan suka yi shiru suna jiran jin ra'ayin ta, cike da kunya ta ce,
"Na amince da Kai da Kuma abinda ke tafe da Kai waje na,Allah ya tabbatar mana da alkhairi,ya kare dikkan abin qi a lamarin"
Ta na gama fad'in haka ta rufe fuska da siraran yatsunta,
"Ameen"
Shine abinda suka had'a baki suka amsa mata da shi cikin murmushin ganin yarintar ta,hira suka ci gaba da yi a nan ne ta ke Jin taqaitaccen tarihin shi,se dai ya b'oye mata kamannin da yake ganin ta na Yi da marigayiya gudun kar ta yi zaton ko shi yasa ya zab'e ta, ba zata ji dad'i ba, kowacce mace ta na so a so ta dan ita d'in ake so ba dan wata alaqa ba, Fauziyya ta tausaya mashi sosai, dan ta kula akwai soyayyar matar shi sosai a ranshi,ta yi masa ta'aziyya sannan Kuma ta masa uziri rashin masoyi tabbas ba dad'i,daga baya suka mata sallama suka tafi, bayan ya aje mata tsarabar daya kawo mata, na turaruka.
Gidan budurwar Auwal suka je daga nan, ta sha
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 21