murmushi, take ta ji baqin cikin ta ya ragu, qarasawa ta yi tana masa murmushi dik da niqabin dake fuskar ta bai gaza gane me take mai ba, amma a hakan sai da ya gano zuciyar ta ba dadi a lokacin da ta shiga motar, saurin d'auke niqab din ya yi yace
"Me ta maki yau kuma, na kula kullum kk zo gidannan sai ta bata maki rai ke kuma baki son fad'a min, a gaskiya zaki daina zuwa in haka ne, ita ta dinga neman ki ba shikenan ba,"
"Sam ba za ai haka ba, in banje wajen yayata ba wajen wa zani? Kuma ni ban ce maka ta min wani abu ba ai ko? Ina son yayata ina qaunar ta, kome zata min yayata ce , komai zatai man ba zai taba canja wani abu daga son da nake mata ba,"
Ta qarasa muryar ta na rawa, idon ta taf kwallah,bata son ta kuma cewa komai sai ta jingina kanta a kujera bayan ta maida niqab din ta, jan motar ya yi yana hararar gidan Rasheedan, daidai lokacin da mijin ta ya ke qoqarin shiga gidan, ya na shiga kuwa ta miqe ta karb'e ledar hannun shi ta ce,
"Meye wannan a ledar?"
Miqa mata ya yi ya koma ya zauna a gajiye, aikin gini yake, gaba d'aya ya gaji, tsaki ta ja sosai sannan ta kalle shi,
"Yanzu Auwal meye wannan tsakani da Allah? Ya zaka kawon wani zogale sai kace tsohuwa? Ga abubuwan kwadayi da qarin jini nan da masu ciki ke ci amma ni ka ban wannan?"
Cike da takaici ya kalle ta, se kawai ya mata shiru dan in ya biye mata sai ya faffalla mata maruka, miqewa ya yi ya kewaye ta ya fita tsakar gida dan wanke hannu da qafa, sanin halin shi ne yasa tayi gum da bakin ta da ta ga ya miqe, se da ya fita ta dauki zogalen ta na mita ta kwadanta yawun ta har zuba yake ta yi maza ta goge da bayan hannun ta,ta zauna zata ci kenan ya fito, dariya ya barke da ita,sannann ya yi maza ya karb'e kwanon daidai lokacin da zata zira hannu dan diba ya kama hannun nata da qarfi ya sid'e , cikin kuka ta fizge hannun ta shi kuma ya shige d'aki da shi ya rufe qofar, ihu ta saka tana kiran ya bata ta ci amma ya qi ya na ta dariya ya ce
"Ba zan bayar ba ai ina kallon ki, jira dama nake ki gama had'a min tinda ke ba so kk ba, kin raina abinda na baki saboda kin fi qarfin shi ko? To ni da ban fi qarfin shi ba bari na ci abuna"
Cikin kuka take masa magiya shi kuwa ya yi kamar be ji ba, se kwasar zogalen ya ke ya na kaiwa baki, tare da lumshe idanun shi, hannun da ya sid'e ta kalla ta ga akwai saura se ta hau sid'e hannun nata,Wani irin dad'i ne ya gauraye mata baki har tsakiyar kan ta ta ji shi.
" Auwal kai min rai ka bani na ci, cikinnan zai iya zubewa in ban ci abinnan ba,"
"Wa ya yi cikin da izinin Allah? Ba dai Allah ni ya bawa ikon dura abubuwan da cikin ya samu ba? Kar ki damu ya zube na qara maki wani,"
kuka ta zube a wajen tana yi,dan tabbas ta san ba zai tab'a bata ba, sai da ya gama tass d'an burbudin kwanon ya dangwara a gaban ta ya yi wajen taliyar da ta dahu har ta dan fara qauri, saukewa ya yi ya d'iba ya dawo parlorn ya na ci , kallon shi ta yi cike da harara da tsiwa, ranta na suya dan ba qaramin b'ata ranta ya yi ba daya cinye,
" Allah sai ya saka min Mugu azzalumi kawai tinda ai ka san sarai ina da buqatar irin wadannan abubuwan a jiki na tin da ciki gar..,"
Kan ta rufe baki ta ji ya bige mata baki da bayan hannun shi, nan take kuwa ta buga ihu ta Kai hannun ta baki se ga jini, qara rikicewa ta yi da kuka, shi Kuma ya miqe ya na nuna ta da yatsa ya ce,
"Ni kk zagi ki ke had'awa da Allah?dan ma kin samu ina maki qoqari ko? za ki ga iskanci kuwa ganin idon ki mun d'aura daga yau, tin da qoqarin da nake a ban da shi kin raina muje zuwa da Auwal kk magana,"
Wajen tukunyar ya nufa ya kwashe sauran naman tass ya wuce uwar d'aki ya zauna ya sa gaba yana ci, wani yunquri ta yi da sauri dan ta je ta ci itama,Wani mugun kallo ya wurga mata se da hanjin ta ya kada, qunquni take ta na ja masa Allah ya Isa kamar wata qaramar yarinya,Auwal na ganin haka ya janye kwanon zai miqe ta kwasa waje da gudu,
"Da ki tsaya mana qaramar mara kunya, kwatakwata baki da hankali baki San me duniya take ciki ba, zan koya maki zaman duniya ne, shashasha kawai"
A tsakar gida ta ja ta tsaya, can Kuma ta qarasa ta ja tukunyar taliyar ta hau cin abinci tana kuka, ko gamawa bata yi ba ta tuna da abubuwan da Sakeenah ta Kai mata, da sauri ta nufi parlour ta dauki ledojin ta hau bubbud'ewa,da soyayyan nama ta fara yin karo se fruits da fresh milk,sannan kud'in da ta aje mata, d'aya ledar Kuma rigar bacci ce da turare da man shafawa se d'ankunne, kyabe baki ta yi tace,
" Ko banza na mora, duk da ba haka na so ace wai qanwata ke min ba, ai kyanta ace ni ce zan dinga bata ta na karb'a ba wai ni ta dinga kawon ba"
Ci ta hau yi ba ko bismillah, ko me ta tina oho, se ta miqe ta shiga daki ta zauna gaban Auwal tana ci tana waqe2n habaici, ko kula ta bai ba, dan ya san wa ya kawo, shi a nashi b'angaren dik da yasan ya mata qarya wajen auro ta, amma yana tsananin son ta, sannan in ta bishi a sannu zasu zauna lfy, kuma iya qoqarin shi zai mata duk abinda ya sawwaqa tinda harkar gini watarana a samu me yawa ne watarana kad'an amma ita inaaa bata San wannan ba, sai da suka yi aure duk wasu halayen ta da bai ma san ta da shi ba musamman na tsanar qanwar ta da duk wani wanda ya fita qumbar susa suka fito masa fili se ya dauki hakan a matsayin Allah ne ya tura shi wajen ta dan ya yi maganin ta, halayen munana bai rage masa son ta ba sam, sai ma qaruwa da yake, dan ko ba komai yana morar ta ta wani wajen.
***************************
Cikin dare Sakeenah ta miqe tana safa da marwa a d'aki, juyi Adnan ya yi se ya ji bata jikin shi,idon shi ya bud'e kad'an da magagin bacci ya kalli gefen shi ya ga ko ta mirgina gefe ne ya jawo ta jikin shi se ya ga bata nan, sun riga sun Saba wa junan su kwana a manne da juna,rashin ganin ta a gadon ne ya bashi damar bud'e ido sosai a tsaye ya gan ta tana safa da marwa, cikin damuwa ya sauke qafafun shi tare da zira takalmin shi ya riqe kafad'ar ta ya ce,
" My love lafiya ki ke kuwa? Me ya same ki, ko na maki wani abu ne da ya b'ata ran ki ban sani ba?"
Da sauri ta fada jikin shi tana kuka sosai,
"Mine abun nan na damuna sosai, ka duba ka ga qawayena da akai auren su bayan namu duk da ciki, Rasheedah da aka mana aure rana d'aya ciki ne da ita ba wai baqin ciki nake ba ko Wani abu makamancin haka ka fahimce ni kawai nima na so ace Ina da shi amma shiru har yanzu,"
Ta qarasa maganar cikin matsanancin kuka, sake baki ya yi da farko yana kallon ta, sannan daga baya ya yi murmushi ya kamo ta ya dora a kan cinyar shi,
"Habaa my love, yanzu ina ilimin ki ya tafi, ki dinga zance irin na Wanda suka manta Allah na yin yanda ya so a lokacin da ya so Kuma akan Wanda ya so? Habaa gaskiya ban ji dad'in Jin haka daga gare ki ba, ke da na sani ki na da tawakkali da aiki da ilimin ki na addinin da na boko ma, Ina hankalin ki ya tafi ?habaa kar kina saka wannan a ran ki, Kuma dai na ga ni ban ma gama cin amarci na ba"
Ya na fad'a yana sunsunar wuyan ta, yana shafa bayan ta, sannan ya yi amfani da d'ayan hannun shi yana qoqarin janye mata rigar dake jikin ta, itama cikin zaquwa da abinda mijin nata yake mata ta juya ta bashi hankalin ta dika, wasanni suke kamar zasu cinye juna, ina ganin haka nace tooooo Haermee an zo wajen manya fece🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Page 3:
" Wayyo Allah na shiga uku na lalace, da nasan haka zan sha wahala da ban auren ba ma, wayyo mama na Abbana ku taimaka min,Auwal ka cuce ni ka Kai ni ka baro Allah ya saka min, ga talauci ga ciki ka had'a ni da shi zan mutu wajen haihuwa Auwal Allah ya tsin..."
Midwife d'in da ke karb'ar haihuwar ta ce ta rufe mata baki da sauri ta ce,
"Subhanallahi baiwar Allah ya ki ke abu kamar ba musulma ba ne? Se zage zage ki ke yi tinda aka kawo ki, yanzu mijin naki Zaki tsinewa kamar wasu Wanda suka samu cikin ta haram? Kin manta ma da addu'o'in da ya Kamata ki yi, kin manta da buqatun ki da ya Kamata ki roqi Allah a wannan yanayi da ki ke ciki saboda Allah na karbar addu'ar masu naquda, me yake damun ki? Ga ki kamar wayayyiya amma kina abinda jahilai ma basa yi, mtsss"
Takaici da haushin Rasheedah ya gama cika nurses da midwifes tare da likitan dake cikin d'akin haihuwar, gaba d'aya kamar Jira suke kuwa suka yi mata caaaaa, banza ta yi da su ta ci gaba da zage zage ta na Kiran dan ba su bane suke Shan wahalar shi ya sa,Allah ya d'ora musu masifar da take ciki su ji idan da dad'i,Auwal na waje ya na Jiyo dik abinda take yi, ya yi zukud'i ya zabga tagumi se fata yake Allah ya sauke ta lafiya, gaba d'aya tausayin ta ya gama cika masa zuciya, ta Wani fannin kuma haushin ta yake ji,tinawa ya yi da abinda ya faru kafin su zo asibitin....
'Yanzu baza ki daina wannan iface2n ba ki kira sunan Allah? Sai kin gama tara mana mutanen unguwa a zo jin me ke faruwa, Ki qoqarta ki tashi na kai ki asibiti nan ma kin qi, kin san sarai ni ba iya d'aga ki zan ba saboda yanda ki ka yi qiba se na taimaka maki mu taka zuwa waje ga me adaidaita can na kira ya na ta Jira, Iya jiran shi Iya kud'in da zan bashi Kuma gashi bamu je asibitin ba balle mu ji nawa zan kashe,'
Hannun shi ta damqo ta matse tare da gasa masa Wani wawan cizo tin qarfin ta, ihun shima ya saki, d'aga hannun shi ya yi da niyyar wanke ta da mari sai ya hakura ya sauke, yace mata,'
'Bashi kk ci zan rama ne nima,'
A haka ya qoqarta d'aga ta, ya shirya ta da kyar tana fizge2 kamar wata 'yar bori, a haka suka shirya zuwa asibitin Imam Wali dake cikin Jambulo, suna zuwa malaman asibitin suka ji yanda take ihu suka san akwai darga da wannan rikitacciyar da tin a zuwa awo wasun su suka San halin ta,da kyar ta bari aka shiga da ita dakin haihuwar, suna shiga ya lalubi qurqurar wayar shi ya kira surukan shi da Sakeenaa ya sanar da su suna asibiti haihuwa ta zo, doguwar ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama wannan tinanin, a Fili ya furta,
"Allah ya kyauta, Allah Kuma ya sauke ki lafiya ya bamu masu albarka"
Tinda Auwal ya Sanar da ita maganar haihuwar ta ke a cikin tsananin zumud'i tare Kuma da tausayin yayar ta ta, shiryawa ta yi Adnan ya dakko ta dan ya Kai ta asibitin, kan ta fito sai da ta dakko kayan shayi, da dik wasu abubuwan da tasan za a buqata Wanda ta dinga tanadi kamar ita ce zata haihu, hatta da kayan jariri se da Sakeenah ta tanada, dan tasan halin Yayar ta ta,ba lallai tai hakan ba, suna isowa tana haihuwa, murna a wajen su ba a magana, Sakeenaa kam har da kukan dad'i, aka buqaci kayan da zasu gyara yaro a saka shi nan Auwal ya yi qifi2 da ido, miqawa ya ga Sakeenaa tayi, nan take zuciyar shi ta bata waje mai katuqar girma da mahimmanci, dan ya tabbatar ita mace ce me kirki ba kamar yayar ta ba, murmushi ya sakar mata na godiya dan bai da bakin yin ta, Adnan ne ya bi Doctor bayan ta fita daga dakin, Office yaje ya tambayi kud'ad'en da za a biya be fito ba kuwa se da ya biya kudin komai, fitowa ya yi ya miqa ma Auwal receipt fuskar shi ba yabo ba fallasa,dan shi haushin yanda Rasheedah ke wa matar shi yake, shiyasa haushin Rasheedan ya shafe shi, hawayen da yake maqalewa ne ya gangaro masa, nan take ya hau godiya ba iyaka, sai can yamma aka sallame su suka wuce gida.
Sun isa gida lafiya, nan da nan Sakeenah ta Maida hankali ta dora ruwan wanka, Rasheedah na d'aki ta saka baby a gaba ta na kallo, cike da so da qauna irin ta d'a da mahaifiya.
Can gidan iyayen su kuwa tinda maman su ta ji an sauka lafiya, se ta yi musu girki mai rai da lfy ta aiko masu da shi, Sakeenaa ita ce ta ke wuni a wajen ta tin da akai haihuwar dan gidan d'aki d'aya ne ba zai Yu ta kwana ba shi ya sa sai dare ta ke tafiya, komai da ya kamata a ce ta tanada kan haihuwa ashe babu, ran Auwal ya yi matiqar baci, ashe duk 'yan kud'in na shi da take tattarewa ta ce zata sai abu saboda haihuwa ba siya take ba? Qwafa ya yi yace Allah ya basu rai da lfy se ya yi maganin ta.
Ranar suna Sakeena akwati daya qarami ta yi musu na kaya a shaqe yake da kayayyaki na jariri da na uwar, sai dubu ashirin da ta kawo ta ba wa Rasheedah, har yanzu ta kasa reading face din yayar ta ta, fatan ta Allah yasa daga wannan lokacin qiyayyar da take mata ta tafi, Allah ya maye gurbin qiyayyar da son ta a zuciyar 'yar uwar ta.
Yaro yaci suna Yousuf, ya ci sunan mahaifin Auwal se dai mu ce Masha Allah yaro ya ci sunan dan kuwa akwai kyau, mahaifin Auwal mutumin kirki ne sanda ya na raye shi yasa ya Masa takwara, Auwal saboda maraici ya sha wuya a rayuwa sosai, ga ba wani ilimin zamani sosai,gwanda ma na addinin, yana da shi, shima ba wani sosai ba, a qalla dai ba za a kira shi jahili ba, yace suna kiran yaro da sunan shi bai son wani iyayin b'oye suna, haka ko ake kiran shi da Yousuf din shi.
Yau kusan shekara ɗaya da rabi kenan da haihuwar yousuf, Rasheeda na dauke da wani cikin ba tare da ita Kan ta ta kula da hakan ba, Yousuf ya yi wayo sosai, yawon shi yake ko ta ina, ga surutu Dan dik abinda ya gani ya San sunan shi, zai iya baka labari tsaf ka fahimci abinda yake fad'i kowa na mamakin wayo da qoqari irin na Yousuf.
Sakeenaa kuwa a wannan lokacin hankalin ta in ya yi dubu ya tashi, saboda rashin haihuwar da bata samu da wuri ba har qasashen waje sun je, ance lafiyar su qalaou su dika,a dik sanda Adnan ya gan ta cikin damuwa ya Kan zaunar da ita ya ce,
" Haba my love ki daina kukan nan haka ya isa, ki zama mai tawakkali ga Allah kar ki nuna wa Ubangiji ke kinfi qarfin ya jarabce ki, haihuwa ta Allah ce fa, in ma tsoro kk zan qara aure na maki alqawarin ke daya kin ishe ni rayuwar duniya, ni har qasan zuciya ta ban da sha'awar tara mata da yawa, sai dai in Allah ne ya qaddara min, ki yi hakuri kin ji My love?"
Kukan ta kan ragu amma ba dan ta daina ba ba kuma dan ta daina jin zafin rashin haihuwar da batai ba.
Hankalin ta bai qara tashi ba sai wata rana da ta ziyarci Rasheedaa ta gan ta, ta tabbatar ciki ne da ita, a cikin zuciyar ta ta hau godewa Allah da neman gafarar shi sannan ta yi wa yayar ta addu'ar Allah ya qaro mata zuri'a ta gari me albarka.
Hira suka ta sha wanda gaba d'aya akan qorafin Babu da talaucin Auwal ne, qaiqayin baki ya Kai Sakeenah da fad'a wa Rasheedah hasashen ta na ko dai Wani cikin ne da ita? Shiru Rasheedah ta yi ta na tinanin rabon ta da period da Kuma hali na kasala da yawan amai da zubda yawu da take, Wani irin tashin hankali ne ta ji ya mamaye ta,nan da nan ta fara zage zage da qudirin zubar da cikin,Sakeenah ta yi data sanin Sanar da Rasheedah hasashen da ta yi, tin Rasheedah na fad'a da zage zage Sakeenah na gane wa har ta dawo ta dena gane komai, kalmar Rasheedah ta qarshe ce ta daki kunnen ta, da sauri ta kalle ta da kallon amma baki da hankali ko? Sanan ta ce mata,
"Kin kuwa San me ki ke fad'a? Wai ke me ya sa a kullum ki ke adawa da dik wata ni'ima ko jarabawa da Allah ya ke maki a rayuwa? Kin kuwa San hakan da ki ke babban laifi ne? Ki kalle ni mana ban ishe ki misali bane, tare fa aka mana aure amma ko b'ari ban tab'a yi ba, ga qawayen mu da aka wa aure a bayan mu dik sun haihu, shine ke dan kin samu Allah ya baki ki ke so ki masa butulci?"
"Dalla malama rufe min baki, tinda Allah ya wanke miji d'an gaske ga dukiya ya baki dole ki ce haka mana, ni da ni ke cikin daular da ki ke Kuma bana haihuwa me zai damen, ba se kawai na ci duniya ta da tsinke ba, amma ki dube ni fa ki gani, dik gayu na da kyau na na b'ige a auren magini, maginin ma qaramin magini talaka, haka kawai se na hau tara Yara tsufa ya kamani da wuri, ga babu ga tsufa nan da an kwana biyu ya ce zai qara aure ko? To ba zai Yu ba,idan ba zaki goyi bayana ba ki kama gaban ki dama ban gayyace ki ba, ni banda baqin naci ma ban ga me ya sa ki ke min sintiri a gida ba, mtsww aikin banza"
Sakeenah na zubar da hawaye yau ma ta bar gidan yayar ta ta, ta na qudirta anya ba zata bi shawarar Adnan ba ta dena zuwa tinda ba ta San darajar ta ba.
Tafiyar Sakeenah ba jimawa Rasheedah ta hau kukan baqin ciki da data sani ta yi tsarin iyali, a qalla Yousuf ya qara wayo Kuma wataqila Kan nan arziqi ya same su, se ta ji dad'in sake jiki ta haihu, amma ga talauci ga taron Yara kamar a idi, inaaa ba zata Iya ba.
Auwal na shiga gidan ta je da gudu ta fad'a jikin shi, se kuka take ta na shagwaba tare da buga qafa a qasa, ya na mugun son wannan bangaren nata na shagwaba da runguma da narkewa da take a jikin shi, ya na sa ya ji kamar shi kad'ai ne Wanda ta jingina a jikin shi take neman ya warware mata wata matsala ko damuwar ta, qara rungume ta ya yi shima tsam a jikin shi, ya ja ta suka shiga d'aki, a bakin gado sika zauna ya hau tambayar ta meyake damun ta,
" Auwal na kasa cin abinci yau, zuciya ta na ta tashi, ga jiri danake yawan gani, wai shine fa daga zuwan yarinyar nan ta kallen wai ciki garen,"
Ta qarasa cikin matsanancin kuka, murna ce ta kama Auwal, ganin haka yasa ta tsagaita da kukan ta, ta kalle shi,
" Ya naga kana murna?" Amsa ya bata da,
"Ba dole ba Allah mai kyauta da qari ya qaran, Allah na gode maka, Allah ka sauke ta lafiya ka raya mana abinda ke cikin ta"
yana ta zabga addu'o'in shi ta ture shi tana bin shi da wani mugun kallo,
"To ni yaushe ma na warke da zan sake wata haihuwar? dika2 ko shekara biyu ban ba da haihuwa na sake wata? Ehhh tin da ba da duwawun ka za ai haihuwar ba kuma ba a cikin ka za a kwanta ba kayi murna mana"
Cikin kuka ta fice tana surutai, shidai bai ce mata komai ba, dan tabbas ya san ta wahala, ci gaba da cire kayan shi ya yi yana ta murna,ita ko parlor taje ta kwanta tana ta rusa kuka,har Yousuf yazo yana kuka sosai shima dan ganin ta na kuka, daka masa tsawa ta yi ta kore shi, shiru ya yi yaron yaqi tafiya kuma yana ta kallon ta, daga baya haka ta yi bacci a wajen, Auwal gyara mata kwanciya ya yi ya rab'a mata Yousuf ya fiddo mai cikakkun nonon ta ya bashi ya yi ta sha,har shima baccin ya dauke shi.
*****************************
Sakeenaa ce kwance ta yi zugum idonun ta sai tsiyayar da hawaye su ke, ko dai zuwa za ta yi wajen Maman ta ta sanar da ita rashin haihuwar ta wataqila zata sama mata wata mafita, Kai koma ba ta samu mafita ba a qalla zata samu ta yi sharing damuwar ta da Wanda zai damu da damuwar tata, ba kamar Rasheedah ba da bata damu da dik Wani hali da take ciki ba, shawara kawai take da zuciyar ta wani tinanin ya fad'o mata........
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 21