gida.
Rasheedah ta tarar zaune ta na Shan juice din orange, Suna kallo ita da Afrah, cikin zubar hawaye ta kalle ta ta zaro magungunan ta nuna mata sannan ta share hawayen ta da ke zuba ta ja majinar kuka ta ce,
" Umma me na miki a rayuwa tane? Me na tsare maki? Me kk so ki fad'a min na bar miki shi har abada? Ba zan iya daukar wannan baqin cikin ba, Ahmad ya sake ni saboda abinda ban san na aikata ba, ashe na koya mai karatu da rubutu ne dan ya saken da su, bana son shi amma na saba da shi, na saba da nunamin yanda yake so na, na saba da kalaman shi masu taushi, na saba da nuna min yafi sona sama dake, me zai sa ki lalata rayuwata? Wannan karon ba zan zauna da ke ba, ba zan bi wasiyyar Mummyna ba ke Kuma ki nakasa min rayuwa ta ba"
Afrah kanta ya kulle, d'aukar takardar ta yi ta bud'e, zubewa ta yi a qasa kwaraf, hawaye na zuba mata, kallon Umman ta ta yi ta kalli Ablaerh
"Meke faruwa ne, me ya sa ya sake ki daga komawar ki ko kin masa Wani abu ne kafin ki fito dama?"
" Ki tambaye ta, ban san me na mata ba, ta je ta nunawa Ahmad maganin tsarin iyali wai ni nake sha, Ahmad na da son haihuwa sosai fiye da komai a rayuwar shi, gashi ta sa ya yanke hukunci cikin fushi ya yi min saki har uku a lokaci d'aya, na rasa wace iriyar qiyayya take min, yau ko 'yar tsuntuwa ce ni ba Zaki na mata wannan abubuwan ba Umma, ballantana a ce ni d'in jinin ki ce ko kina so ko baki so, idan Kuma kin gaji da gani na ne a duniya ki kashe ni kawai ki huta"
Tana gama fad'a ta haye sama da gudu ta na kuka, Afrah qarasa zauna wa ta yi a wajen, ta saka kuka, tana kallon Umman su da take rarraba, ido, tabbas ita ta had'a komai, amma yanzu jikin ta ya yi sanyi,dan tina me zai je yazo da ta yi, in Auwal kuwa ya sani ta ta ta qare, sannan ga Yousuf da Sulaiman, tana tinanin nan ta ji sakkowar Ablaerh daga sama da ta hau cikin sauri da b'acin ran da bata tab'a nunawa a fuskar ta ba,ta dauki mayafin ta dake qasa, ta koma gidan ta ta kwashi kayan ta a kwati, ta kama hanya......
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 25:
Duka ya sake kai mata ta goce, Atiyyaerh ce ta ya yi sauri ta shiga tsakiyar su, ta kwab'e baki kamar na me Shirin yin kuka, dan kuwa ji take kamar ta Saka kukan Sam bata ji dad'in abinda ya faru ba a tsakanin su,se take ganin kamar za a ga laifin ta, tinda sa'insa bata tab'a had'a su ba balle ya ce zai Kai wa matar Yayan nashi duka irin haka.
"Dan Allah Bappan Umar ka yi hakuri ka rabu da ita, matar Yayah ce fa? In ka dake ta kamar ka d'au hannu ka daki Yaya ne fa, na san ba zaka iya dukan Yayah ba ai ko? To ka rabu da ita ta min qazafi ita da Allah,Allah baya zaluntar bayin shi sai dai su su zalunci Kan su"
Kallo ya bita da shi Yana masifar son salon da take magana da shi a yanzun, ba qaramin burge shi ta yi ba, sai kace irin qananan yarannan masu shegen kyau haka ta koma,tsaki ya ja mai qarfi zai wuce sashen su dan in ya ci gaba da zama a wajen ba zai kyale ta ba,ya na juyawa ze fita ya ga Yayan shi a tsaye da Baba Garba, dafa kafad'ar shi Yayah ya yi yace masa su je ciki ya na son magana da shi,cikin rausaya kai na irin fushi fa nake dinnan ya bisu, Yaya kuwa kallon matar shi ya yi da Atiyyaerh yace su biyo shi, wani d'aki suka shiga, ba komai sai tabarmi, da ledar tsakar d'aki, sai littattafai, na Baba Garba , bayan sun zauna ne, Atiyyaerh ta miqe ta deb'o masu ruwa, suka sha suka yi mata godiya, sannan Baba Garba ya yi gyaran murya, ya yi sallama suka amsa,ya ci gaba da magana kamar haka,
"Zancen gaskiya ban ji dad'in yanda mun fita dan mu je nemo maku abinci amma mu dawo mu taddaku kuna fad'a ba, har da kai namiji a fad'an, kenan zaman ka a gidan bai da wani amfani in dai mata zasu na fad'a ka shiga? Ina son sanin abinda ya faru daga bakin ki Atiyyaerh kuma bana son ki boye laifin kowa, ki fad'an gaskiyar me ya faru,"
Sallama ta yi itama kamar yanda ta ga Baba Garba ya yi Kan ya fara magana,se suka amsa mata sallamar, sannan ta labartawa Baban komai, bata rage ba bata qara ba, wani kallo mijin Hajar ya bita da shi, Wanda yasa ta sunkuyar da kai,
"Wato ke lab'e kike masu kenan, tinda da alama a maganganun da Atiyyaerh ta fad'a ya nuna ba yau din ne kawai kk lab'e masu ba tin da aka kawo ta kk masu labe'n, " In ji Baba Garba da ya kafe ta da Ido ya na jiran jin me zata ce.
Cikin jin kunya Atiyyaerh ta dan matsa gefe ta takure, lura da hakan ne yasa Baba gaggauta maganar da yake son yi,
"Da ga yau zuwa har a bada bana son na sake ganin fad'a a gidannan, bana son a sake taruwa anan, ran kowa zai ya b'aci, matan su tashi su je a ci gaba da aiki, kuma bana son gaba ko qananun magana, ina fatan kun gane, ke kuma Hajar bata hakuri,"
kallon Atiyyaerh ta yi cike da tabbb wannan zan ba hakuri dinnan, amma mijin ta na daka mata tsawa se ta ba Atiyyaerhn hakuri, Atiyyaerh kuwa sanar da ita ta yi cewar ba komai Allah ya kyauta na gaba komai ya wuce,kowa ya amsa da ameen suka miqe suka fita, bayan fitar su ne Baba ya ma yaran shi nasiha, akan kar su kuskura mata su had'a su, su b'ata masu zumunci, komai zai faru kuma suna zurfafa tunanin su da binciken su kafin yanke hukunci, godiya suka yi sannan Yayah ya bama qanin shi hakuri for his wife's behavior, nuna masa ya yi ai ba komai ya wuce, sannan suka fita.
Hajar ta rasa yanda zata yi dan ta dasawa mijin ta tsanar matar qanin nashi, dan haushin Atiyyaerh take ji matuqa,kowa na son ta a gidan, dan ita tin kan auren Ahmad ba son ta ake ba a gidan, balle yanzu an samu surukar so, tasan ita kam tata ta qare, duk wata hanya a 'yan kwanakin nan tabi amma shiru, dabara ce ta fad'o mata, tabbas tasan yaran ta basu da kunya da su zata yi amfani,dan in akwai abinda Muhammad ya tsana bai wuce wani ya tab'a masa yara ba......
*******************************
Afrah ce ke zaune a Parlour ta na kallo, Rasheedah ta fito ta ci uwar kwalliya,tinda ta aurar da Ablaerh hankalin ta ya kwanta, dan a zuciyar ta tana raya tana can tana fama da d'an wiwi, wataqilama ta sha duka yafi a qirga, ga faccala ga suruka, wahala goma da ashirin, murmushi ta yi da tai wannan mummunan tunanin, ta zauna a kujerar dake kallon ta Afrah da take daure fuska a duk sanda ta ga Mahaifiyar ta ta, dan tayi2 ta bar ta taje taga 'yar uwar ta amma ta hana ta, haushin hakan take sosai, ,
" 'Yar Umman ta me yake b'ata ranki ne? Sai na ga kina b'ata rai kwanakin nan, ko zaki gaida Mama da Abba ne?"
Cike da zumudi Afrah tace,
" Eh Ummana,"
Komawa kusa da Rasheedah ta yi ta zauna bakin ta ya qi rufuwa,
" Ummana dan Allah daga nan na biya gidan Ablaerh na gan ta?"
Wani mugun kallo ta buga mata tare da harara kamar idon zai fado qasa ta ce ,
"Ki mata uwar ki in kin je? Tashi in zaki gaida iyayena ki je in bazaki ba ki bari,"
Ta jaye jikin ta ta bar parlourn, daf zata shiga d'akin ta ja burki ta tsaya, ko me ta tina oho ta juyo cike da fara'a tace,
" ki je amma kar ki dade, kin gano mana d'akin amarya da halin da take ci"
Cike da zolaya ta fad'i hakan, ta shige d'aki abinta, miqewa Afrah ta yi cike da murna ta shige daki, shiryawa ta yi, tai kwalliyar ta da ta saba, ta fice, direct gidan Mama taje, Mama ta yi murna da ganin ta, ta tambaye ta ta je gidan Ablaerh kuwa? Ta ce yau zata, saqo ta d'akko mata daga d'aki, a leda biyu ta fiddo ta miqa mata,tace,
"Wannan garin kayan qamshi ne dana niqa mata, komai zata ci ta saka ko a girki ko a abun sha, na zamanin nan da kuke hadawa da kayan marmari, wannan kuma ridi ne(kantu) na niqa mata shima, zata na sha da madara, sai wannan garin aya ne shima na niqa mata, zata iya sha da had'in kantunnan da garin ayar da kayan qamshinnan da madara, in kinje ki mata bayani dalla dalla, ciwon qafar nan ne ya ke damuna amma dana ji dama zan je na ganta,wannan Kuma turaruka ne da kayan ado naku na 'yan zamani, wannan kud'in Kuma ki bata ko zata buqata, maza ki je kun sha hirar yaushe gamo,"
Tashi Afrah ta yi cike da murna, ta ce ta gaida Abba in ya dawo ta fad'a masa in ji amaryar shi ta yi kewar shi sosai,yaushe zai je zance, dariya mama ta yi tace zata fad'a masa, bayan ta fita ne ta tsaida abin hawa ya maida ta unguwar su, direct gidan Ablaerh ta shiga, ta je Ablaerh na wanka, se ta shige har uwar d'aka ta zauna, sai kallon ko ina take, a gyare, ga kayan namiji nan aje wankakku a goge, da kayan Ablaerh shima a ajiye a wanke a goge, bata kawo komai ba tana zaune tana raba idanu ta jiyo dariyar Ahmad, yana tsokanar Ablaerh akan rashin sakewa da shi da take, kukan shagwabar ta yake koya, ita kuma tana murmushi, har yau ta kasa wani sakewa da shi sosai, ko dan ba soyayyar shi a ranta ne oho? da takalmin Afrah suka fara cin karo, wanda yasa Ahmad shiru cann yace,
"Ko dai baquwa muka yi ne?"
Atiyyaaerh ce tace bari ta duba to ta gani, Afrah dawowa ta yi parlor ta zauna, dan ta gama jiyowa ita da Ahmad ne suka dawo daga wanka, kunya duk ta kama ta, dama bata zo ba yau, ta rasa ina zata kai kunyar da take ji, bata son had'a ido da su, (kuji fa🤣🤣 saura ke Afrah kina layi) Atiyyaerh na ganin Afrah, ta tafi da gudu tana ihun murna ta d'ale ta, dariya suke ta yi tare, Ahmad ya leqo ya ga ita da wa? Sai ya ga Afrah, shima dariya ya yi yace,
"Ashe babbar baquwa muka yi, mu da Muke Shirin zamu bi ki har gida tinda kin yada mu kin qi zuwa,"
Cike da Jin kunya ta sunkuyar da kai tace,
"Lokaci ne ban samu shi yasa, nike taya Umma aiki,.....malama d'aga ni ni kin yi qiba kin zo kin zaune min 'yar siririyar cinya ta"
Qara zama Ablaerh ta yi tana dariya tace,
" Allah ni ba wani qibar da na yi, ni sai nake ganin ma kamar na rage nauyi,ko ?"
Ta kalli Ahmad, da sauri ya daga kai,
"Sosai ma, aike baki da wani nauyi, tinda inna daga ki ji nake kamar baki fi a hada nauyin Umar da sadiq ba,"
Kunya suka qara ba Afrah,
"Ni dai gaskiya in haka kuke a gidannan ba zan din ga zuwa ba, first kun fito wanka tare,second kunzo kuna min wani maganar manya anan,"
Dariya suka saka dikkan Su, Ahmad ya wuce d'aki yana tsokanar ta da cewa,
"sauran ke yarinya,"
Atiyyaerh ce ta bishi,suka shirya sannan yace mata,
"Ina son fita na je a gaisa da abokai Kuma an kwana biyu ba a had'u ba, yanzu har fushi suke da ni wai tinda na yi aure na yada su, Ina nuna masu na fi qarfin su yanzu ko Kiran nawa ma sun dena"
Nan da nan idon Ablaerh ya kawo kwalla,gani kawai take in ya fita cikin abu biyu sai d'aya ya faru, ko ya je wajen matan da yake harka da su a da , ko ya tafi wajen shaye2, kamo fuskar ta ya yi ta kalle shi, ya sumbaci bakin ta a hankali ya ke lumshe ido Yana kallon ta, itama idon ta ta lumshe ta sauke akan nashi da har lokacin suke a lumshe,a hankali ya bude idon shi sosai ya sarqe shi cikin nata,
"Na miki alqawarin ko kina tare dani, ko baki tare dani, na canja rayuwa ta,har abada bazan komawa sab'on Allahn da na bari ba,na bar aikata sab'o dan Allah ba dan kowa ba Ablaerh,ki sani ke mace ce d'aya tamkar da ba iyaka, kin isar min Kuma kin wadatar Dani daga duk wani hayaqi da kuma matan banza, kin shayar dani ruwan daya kauda min wadancan qishin, kuma har abada ba zan dai na jin qishi daga ruwan da kk shayar dani tin a daren farkon mu ba, Ina fatan za ki ci gaba da kashen qishirwa ta a dik sanda na buqaci hakan, dik da na San har yanzu ban da Wani cikakken matsayi a ran ki, amma ba zan gaji da gode miki akan hakuri da ni da ki ke ba"
Murmushin gamsuwa da kalaman shi ta yi sanna tace,
"Allah ya Karen Kai ka je lafiya ka dawo lfy, ka kula da kan ka, in lokacin sallah yayi a duk inda kk ka tashi kayi, sannan lokacin cin abinci in yayi ka dawo gida ka ci"
Sumbatar shi ta yi a kuncin shi dika biyun, shi kuma ya mata a goshi da lips, suka fito, Afrah kan ta na qasa, dan d'akin nasu ba wani sirri ana Jin abinda suke tattaunawa akai,Ahmad Kuma sallama ya wa Afrah cikin barkwanci har ya fita yana tsokanar ta akan yanda take Jin kunyar shi,bata ce masa komai ba,yana fita ta sauke ajiyar zuciya,
"Ba zan sake zuwa gidan ku yana nan ba, wannan sai kun qarar wa da mutum kunyar shi,"
Dariya Ablaerh ta yi, gaisawa suka yi a tsakanin su,se Kuma suka hau hirar yaushe gamo, ta bata saqon Mama, kwalla ce ta cika mata ido,tana kewar su sosai, musamman Yayah, gashi Afrah ta fad'a mata tinda ya tafi ko waya bai sake wa kowa ba, gwanda Sulaiman ya dawo sau daya shima, kuka take yanzu kam, dan gaba d'aya sai ta ji kewar su da take qoqarin dannewa kullum tana taso mata, har Rasheedah dake azabtar da ita dai sai ta ji tana son ganin ta,balle Abban su da ke son ta,share mata hawaye Afrah ta yi tace,
"Taso muje na gaida surukan ki, in ce dai ba mai takura maki a gidan?"
D'aga mata kai ta yi ta bata labarin ya suke mata a gidan, sai dai ta boye mata halin faccalar ta,farin ciki ne ya kama Afrah da jin hakan, ta miqe suka shiga wajen Inna, Baba na nan duk suka gaisa, sannan ta kaita wajen Hajar, sun gaisa ba yabo ba fallasa, suna komawa bangaren su Afrah tace,
"Anya wannan matar Yayan naku na son ki kuwa Ablaerh?"
Ce mata ta yi,
"Tana sona mana, me ki ka Gani? in ma bata so na to ni dai ban sani ba,"
"To in ma bata nuna maki ba to tabbas bata son ki, sai ki kula,"
D'aga kai ta yi tai murmushi, hira suka sha abun su kamar kar su rabu, daga baya Afrah ta yi mata sallama zata tafi, da kuka suka rabu dan basu san yaushe zasu sake haduwa ba, bayan ta koma ne Rasheedah ta ke tambayar ta ya taga Ablaerh, cike da zumud'i ta fada mata komai, ran Rasheedah baqiqqirin dan haushi ba haka taso ba, amma bata ce komai ba ta shige kitchen tace Afrah ta je ta taya ta aiki.
Yau tin safe Atiyyarh ta shirya take gyara gidan, har bangaren su Inna, bayan ta gama sharewa da gyarewa ne, ta d'ora girki, Ahmad na maqale da ita duk inda ta yi, tayi2 ya ma je d'aki ya jira ta gama yaqi, sallama wata budurwa ta yi ta shiga gidan, daidai lokacin Afrah na tankad'en gari, kallon ta Ahmad yake kamar zai kife qasa, yarinyar siririya ce ta sa ka dinkin da ya d'ame ta sosai, yan qananun bootyn ta sun sha d'ama da kyau, tana tafe tana kada su, tana tauna cingam, sai d'an qaramin mayafin ta dake rataye a kafad'ar ta, fuskar nan har ta qone tsabar shafe2, qafar baqaririn da hannayen, haushi ne ya kama Ablaerh, ko da bata son shi ai mijin ta ne, a hankali ta zame zanin ta cinyar ta da take zaune ta sha mai ta yi luwai2 ta bude, ko mace ta kalla sai ta yaba, tari ta yi sosai kamar irin ta kware d'innan,nan da nan Ahmad ya dawo da hankalin shi kanta da sauri, aiko yana arba da cinyar nan a bud'e sai ya daburce, ruwa ya deb'o mata a randa ya bata, d'akin Hajar baquwar tayi, tana shigewa Atiyyaerh ta bata rai tace,
"Ni ka tafi d'aki nace, inna gama ai zan shigo ko,"
Nan take ya gane me take wa hakan, dariya ya quntse yace ,
" To ina jiran ki kar ki dad'e,"
D'aga masa kai ta yi ran ta a d'an b'ace ta rufe cinyar ta da ya qurawa ido, ta d'an murguda lips dinta, dariya ya saki yanzu kam ya kasa riqewa, bayan ya shiga d'akin ne ya fara taka rawar murna, Atiyyaerh na kishin shi, tsalle ya yi ya d'ale gado, yana ta birgima kamar qaramin yaro, Allah, Allah yake ta shigo........
*Kuna tinanin Ablaerh na son shi kuwa? Ko dai kawai tai haka ne don hana mijin ta kallon wata?*
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN .BY HAERMEEBRAERH
Page 27:
Gidan Mama ta samu abun hawa ta hau ta nufa, kuka ta saka kanta a cikin mayafin ta ta ke ta yi ba qaqqautawa har suka isa, tana fita ta miqawa mai adaidaita sahu 200, wanda zai bata canjin 150,amma ko canjin bata tsaya karb'a ba ta wuce ciki, shi kuwa Mai adaidaita se magana yake mata ba ta kula shi ba ta fada gidan, da kuka ta shiga, Mama dake bakin pampo tana wanke alayyahu ta isa wajen ta da sauri tana gyara zanin ta a rud'e ta ce,
" Lafiya Atiyyaerh ki ka shigo ki na kuka haka ,Meya faru, me aka miki, ke da uwar taki ne ko Kuma mijin?" Mama ta jero mata wadannan tambayoyin.
Bata kula Mama ba ta sa kai ta wuce d'akin da tin asali yake mallakin Iyayen nasu, in tazo nan take sauka, tana shiga ta danna qofar ta rufe ta da jam lock, Mama tsaye ta yi ta yi ta bugun qofar tare da Kiran sunan Atiyyaerh amma ta qi budewa, kukan ta ta zauna a gado ta na yi, sai da ta ji ana kiran sallar magrib ta miqe tana had'a hanya saboda yanda take Jin kan ta kamar zai fashe dan ciwo, ga zuciyar ta dake mata wani irin zafi wai yau ita aka yi wa saki har uku, dika dika nawa take? Shekarun ta ba zasu wuce ashirin da biyu ba,an Maida ta qaramar bazawara a banza a wofi,alwala ta yi tai sallah, sannan ta yi azkar na yamma kamar yanda ta saba, karatun qur'ani ta fara rerawa da ka har aka kira sallar isha'i, sannan tai sallah ta silale a wajen ta kwanta ta na lumshe ido,ji ta yi mama na magana cikin Shan majina ta na fad'in,
"Eh tana ciki, tin da ta shigo da kuka ta zo ta rufe kan ta anan bata bude ba na yi Kiran na yi magiyar amma ta qi bud'ewa,amma dai na jiyo ta na karatun qur'ani, sai kuma yanzu naji shiru ba alamar motsi, Ina Jin tsoro Abban su dan Allah ko b'alle qofar ne ka sa a yi"
"iKon Allah to me ya same ta haka da girma har ta kasa tsayawa ta sanar da ke damuwar ta, kin tabbata bata ce miki komai ba ta wuce? Saboda ba halin Ablaerh bane irin haka"
"Haram bata ce min komai ba ta wuce ni"
"Ikon Allah, Allah ya sa lafiya to,muje na ji,"
Hannu ya daga da nufin kwankwasa qofar ya ji tace,
"Ni ku barni kawai, ba zan magana da kowa ba yau, i just want to be alone, sai gobe mayi magana, dan ko na fito ba zaku gane komai daga waje na ba,"
kuka ne ya ci qarfin ta, juyawa Abba ya yi zai tafi,Mama ta kalle shi, itama idon ta ya cika da kwallah ta ce,
" Yanzu tafiya zamu yi mu barta? Abban su ya kamata mu tsaya mu ji meke damun ta, in mace tace a kyale ta ba wai tana nufin hakan bane,tana buqatar kulawa, ko mai zata ce hakuri za ka yi har ta daidaita,mu qara gwadawa,"
Komawa ya yi ya fara mata magana,
" Haba yar gidan Abban ta Auwaluuu,ki bud'e ki fad'an me ya same ki, me aka miki, na maki alqawarin wannan karon ina bayan ki, ba zan bari kowa ya cutar da ke ba, ina tare dake,"
Tana jin haka ta ja jikin ta ta jingina da qofar ta kwantar da kan ta a jiki hawaye na ci gaba da zuba, a hankali ta ce,
" Abba kayi alqawarin kana bayana fa kace a wannan karon,ka tabbata komai na fad'a ina so zaka min shi?"
"Na yi alqawari,domin na san tabbas cutar dake aka yi da yawa abinda ki ka yi d'innan ba halin ki bane,baki tab'a hakan ba,"
Miqewa ta yi a hankali ta bude qofar, Mama na ganin ta ta nufe ta ta rungume ta,ita kuma ta ci gaba da kukan ta,cikin kukan ta ce musu,
" Mama Ahmad ya sake ni sakin wulaqanci saki har uku a lokaci d'aya ba tare da haqqina ba, ban masa laifin komai ba, Mama Umma Rasheedah ce ta min sharri a wajen shi ya sakeni,saki Uku, Mama na saba da Ahmad, koda bana son shi, me na yiwa Umma Rasheeda da bata so na,in wani tarihi ne da ni da yasa ta tsane ni ku sanar dani, in wani abu ne take so dana mallaka ku fad'a min shi na bar mata shi bana son abun, na tsane shi, Na shane shi, bana buqatar shi in dai zai ja min tsana irin wannan a wajen Ummana,"
Kuka take kamar wadda akai wa sabuwar mutuwa, Mama ma kukan take, Abba ne cikin tausayawa ya kamo ta suka zauna bakin gadon ya ce,
"Atiyyaerh bari na tina maki ma'anar sunan ki, ke takwarar Maimunatou ce,Mahaifin ki ya sa ka maki suna Atiyyaerh ma'ana kyauta, Mahaifiyar ki ta sa maki Ablaerh, wato mai kyau, wadda kuma aka tsara wajen halitta, dukkan nin su basu yi qarya ba, qiyayyar da Rasheeda ke maki ba komai bane illa hassada, hassada kuwa mummunan ciwo ne mara kyau,in ya kama mutum maganin shi na wahala, dan haka wannan ciwo ke damun Umman ki, fatan mu mu zama masu mata addu'a Allah ya yaye mata, ba akan ki ta fara ba, ta fara da qin mahaifiyar ki ne abun ya dawo kan ki, ba abinda kk mata, ba abinda kk riqe mata, ina fatan kin gane, dan haka ki kwantar da hankalin ki, game da sakin da Ahmad ya miki, ina mai baki hakuri, da fatan Allah yasa hakan shine yafi maku alkairi da ke da shi"
A da zuciyar ta cike take da qunci, amma yanzu komai sai ta ji ya kwaranye mata se abinda ba a rasa ba na kewar Ahmad, ta samu sauqin baqin cikin ta,cikin nutsuwa ta musu godiya, sannan tace,
" Abba Mama dan Allah zan zauna da ku ba zan koma wa Umma ba, zan zauna nan har Daddyna ya gaji da zaman can in ya tina yana da 'ya ya dawo,har ya...,"
Kasa qarasawa ta yi saboda kukan da ya sarqe muryar ta, bata son tina wai tana da uba amma ya banzatar da ita sabida wani shirmen dalili, tabbas ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 21