Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Wanda ba za su iya ba su na barin Maman su ta yi, budar bakin Yusuf kuwa sai cewa ya yi, "Abbah ai na ga Mama bata son Ablaerh dukan ta kawai take da zagin ta ko da yaushe" Auwal rasa amsar da zai bawa yaron ya yi Dan haka sai ya hau basu tarihin Annabawa har bacci ya d'auke su, su na nan kwance ya ji an bud'e qofa, Rasheedah ya gani sanye da wasu fitinannun kaya, sun bala'in mata kyau, da dane ba abinda zai hana shi zuwa gare ta, amma yanzu Wani irin kyankyamin sake kusantar ta yake gani yake tsabar munin halin ta duk ya manne a jikin ta ba zai so ya kwashi halin ta ba kuwa, Gani ta yi ko kallon azziqi bata ishe shi ba balle na tsiya, cikin shagwaba da tura baki ta ce, " ko ka tashi mu koma mu yi abun mu can dakin mu ko kuma muyi anan," Kallon baki isa ba ya mata,in Kuma ki na iyawa zo ki yi na gani, murmushin mugunta ta yi ta fara cire rigar saman Yousuf da be bacci ba ya kalle ta,zata cire zanin ta kenan Auwal ya yi sufa ya cafke cikin rad'a mata magana a kunne ya ce, "Baki da hankali ne? Meye haka kk yi a gaban yara? Muje can jarababbiya kawai mahaukaciyar banza wadda bata bawa abun kunya mahimmanci ba a rayuwar ta," Sallama ya wa yaran ya rufe su tare da dafa Kan su ya musu addu'o'i ya kashe fitila ya tura qeyar ta sika tafi, dariyar mugunta ce fal ranta,tin kan su isa ta qarasa cire zanin daga ita sai wata yaloluwar riga ciki babu komai, kallon ta ya yi cikin tsananin Jin haushin ta, kenan da a gaban yaran zata cire ta tsaya a haka? Lallai be tab'a sanin ya auri mahaukaciya ba sai yau,ita kuwa ko a jikin ta sai wani juyi take a gaban shi,kasa jure kallon ta ya yi ya fizge ta da mugunta ya wurga ta d'akin nasu ya banko qofa a ran shi ya na ayyana irin muguntar da zai mata tinda ta d'age se an yi🙊 Auwal tin Yana mata na mugunta har zuciyar shi ta yi laushi ta saki dan kuwa Rasheedah na da matuqar tasiri a wajen shi ta nan bangaren in dai zai kusance ta to damuwar shi na raguwa, halayen ta ya tsana matuqa dan se ka kwana tinani baka gano wanne ne na gari a halayen ta ba, da misalin qarfe uku na dare ya tashi ya zauna bakin gado ya na kallon ta ya na tinani kala kala akan halayen ta, ita kuwa  tana ta kwasar baccin ta, a hankali ya tashi ya nufi bathroom Dan yin wanka, ya na fitowa ya Sanya gajeren wando da vest ya Dora jallabiyya sannan  ya tafi kitchen ya hadawa Atiyyaerh madara, mai kauri, da ruwan dumi, sai ya dakko cake da ya gani a fridge ya je dakin su ita da Afrar,kwance ya ganta amma idon ta biyu, tana son yin kuka tana tsoro, hawaye sai zuba yake a gefen idon ta,tana ganin shi ta fara irin abunnan na hadiyar zuciya na masu kuka, da sauri ya isa gare ta ya rungume ta tsam a jikin shi tare da fad'in, "shsssssss, kar ki kuka kinji baby Ablaerh na," Qanqame shi ta yi sosai tana kuka, danna mata cup ya yi a baki,nan danan ko ta kama, ta hau sha, tana gama sha ya bata cake din taci kad'an can kuma ta fara bacci ragowar  cake d'in a hannun ta,tausayin ta ne me tsanani ya kama shi ya goge kwallar da ta taru a idon shi, ya dauke guntun cake din ya goge mata hannu da tissue, sannan ya goge mata baki, ya gyara masu kwanciya ya masu addu'a ya tashi ya fice, d'aki ya koma ya kwanta, yana tinanin wannan ruqo da aka basu, tabbas ba zai iya bari ana ma yarinyar nan horon yunwa ba, dole ko yaya ne yana kula da cin ta da komai nata, ko a bayan idon Rasheedah ne. Washegari bayan ta kammala komai da ya dace se ta shiga d'akin yaran ta tada su, suka yi brush, ta koma kitchen aka fara had'a abinci, hankalin ta kwance ga wata murna dake ranta, wai yau ita ke da wannan gidan? A haka ta kammala tana 'yan waqe waqen farin ciki, tana kammalawa ta jere a saman dinning table,yaran na zaune already Suna jiran ta kamar yanda ta umarce su, zuba musu abincin ta fara sannan ta zuba wa Kan ta da Afrar dan a baki take da niyyar bata, Auwal ne ya fito sanye cikin shadda Mai kyau da ta karb'i kalar fatar shi se zabga qamshin turare yake, ya na qarasa balle maballin rigar,yaran ne suka gaishe shi ya amsa Cike da fara'a zama ya yi ya ga be ga Atiyyaerh ba gashi ta tasa yaran ta a gaba da dankali da kwai da soyayyar kaza an had'a shayi Mai kauri ba 'yar masu gidan, "Ina Atiyyaerh?".......,.. [01/07, 12:42 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH Page 18: A tsorace Atiyyaerh ta ja da baya,cab'al qafar ta ta shiga cikin kashin, yanda Rasheedah ke matsowa tana masifa haka Atiyyaerh ke ja da baya, tana tattaka waje da kashin, wata tsawa Rasheedah ta sakar mata akan ta tsaya ta daina yad'a mata kashi a ko ina, gigitaccen kuka yarinyar ta saki mai qarfi jikin ta babu inda ba ya rawa, Yousuf kanshi sai da ya firgita, ya durqusa gaban Ummar tasu ya na kuka ya ce, " Umma dan Allah kar ki daki Ablaerh, ki yi hakuri, zan gyara maki wajen," Haushi ne ya qara kama Rasheedah ganin yanda d'anta ke kuka akan wannan sokuwar yarinyar, aiko sai ta ci uban ta yau, kallo ta watsa masa da ya sa shi miqewa ya yi gefe ba shiri, zuwa ta yi ta damqi Atiyyaerh da gashin kanta ta wanka mata mari biyu masu kyau, sannan ta kama kunnen ta ta yanka mata warning din daga yau kar ta sake ganin qafafun ta a parlor in dai ba ita ta kira ta ba, sannan ta tsaida ita gefe ta je d'akko abubuwan da zata gyara waje da shi, in banda a jiyar zuciya yanzu ba abinda Atiyyaerh keyi, dan ta kasa kukan ma, zuwa ta yi tana goge wajen tana zagin ta, bayan ta gama ta dauke ta a wulaqance tai bayi da ita, wanke mata ta fara yi da tsintsiya,a cewar ta bazata saka hannun ta ba bata son taba kashi, ko wa ya ke wanke wa Afrah Kashi oho? duk haka ta sossoke mata duwais da tsintsiyar yarinyar kuwa haka ta dinga kuka saboda azabar zafin da take ji, sai da ta rage kashin sosai sannan ta saka leda a hannun ta ta wanke mata, da ruwa mai sanyi, hankado ta ta yi waje tace taje ta kwanta ta yi bacci, cikin ajiyar zuciya irin ta wadda ta gaji da kuka Atiyyaerh ta tafi ta kwanta, jikin ta ba kaya sanyi duk ya dame ta, a fusace ta bar dakin, Yousuf ne ya shiga da gudu ya je ya rungume qanwar tashi suka yi ta kuka tare, tin daga nan ya dasa qiyayyar mahaifiyar shi a zuciyar shi, domin ganin mugun abun da take aikatawa qaramar yarinya, ruwan d'umi ya samo da taimakon Sulaiman a saman dinning na cikin flask dan basu Iya kunna ruwan zafin bathroom d'in ba da ruwan sanyi suka had'a daidai wanka suka mata wanka me kyau,Suna gamawa suka hau duba kayan da ya dace su Sanya mata a garin haka ne suka yi kaca kaca da wajen kayan sawar nata ba tare da sun Wani damu ba suka zab'ar mata wata riga da wando na sanyi suka sa mata,ba jimawa bacci Mai nauyi ya d'auke ta sai ajiyar zuciya take saki. Cikin tashin hankali Sulaiman ya kalli Yousuf dan ganin b'arnar da suka tafka na fasa flask din ruwan zafin da suka yi wa Atiyyaerh amfani da shi, Rasheedah na jin qarar ko ta fito kamar wata mahaukaciya, "kan uban can , a cikin ku waye ya fasan flask, ko uban ku ne ya siyo da za ku fasa min?" " Umma ni ne na fasa ba da sane na ba, amma kuma ai kema ba ke kk siyo ba, Mummyn Ablaerh ce ta siyi abin ta," in ji Yousuf da ya kafe ta da Ido Shima cikin rashin kunya. Mari ta daga hannu zata kai masa, Auwal da ya shigo da manyan ledoji niqi niqi a hannu ya ce, "kina taban yaro yau na lahira sai ya fiki jin dad'i, dan se na maki dukan da ban taba maki irin shi ba jakar banza wadda bata da hankali, Rasheedah a kullum garin Allah ya waye se na zagi Kai na na Kuma yi wa kaina Allah ya qara dan son zuciyata ya kaini yi maki qarya na aure ki, ga sakamakon abinda na aikata nan Ina girba, ke din wata iriyar jarabawa ce mummuna a gare ni, a kullum Ina danasanin sanin ki a rayuwa ta, yanzu me ya faru? Me ya miki ki ke so ki dake shi? Ina Afrah da Atiyyaerh?" Ido ya zuba mata Yana son Jin qarin bayani, Kalaman shi sun yi matuqar sukan zuciyar ta,ta ji zafin kalmar shi na ita d'in mummunar qaddara ce a gare shi, hawayen ta ta mayar ta na sauraron Yousuf da ke rattaba masa bayani akan abinda ya faru, kallon ta kawai ya yi da takaici ya ja hannun yaron suka wuce ciki, Yousuf Jin shi yayi kamar wani JARUMIn maza, da qananan shekarun shi ta dasa masa qiyayyar ta, da son kare Atiyyaerh ko da zata dake shi shima,ya qudurta ko kashe shi ma zata yi sai dai ta kashe shi amma ya dena shiru in tana zaluntar Atiyyaerh,shi yanzu ma ya dena son ta Mummyn Ablaerhn shi yake so, in ta dawo daga tafiyar da Abban su yace sunyi ita da Abban Ablaerh wajen su zai koma da zama. *BAYAN SHEKARA UKU* Yousuf ne ya fito da shirin zuwa makarantar *AL-ANSAR* da ke unguwar maqotaka da su, Atiyyaerh ce ke kallon shi Cike da sha'awa, Yousuf d'in ne ya Sanya ta zamo Mai tsananin son karatu, tinda  yana koya mata karatu idan ya dawo ko sanda baya komai a gidan, Atiyyaerh na ganewa sosai kuma ta na da saurin daukan karatu,dafa Auwal ta yi da yake Saka takalmin shi a zaune a gefen kujerar da ke kusa da qofar fita daga parlourn, " Abba nima ina son a sani a school din su yaya," Murmushi Auwal ya yi sannan ya d'aga ta sama yana mata wasa suna dariya, Afrah na gefe tana tsotsar hannun nata da ta saba, Rasheedah ce ta fito ta kalle su ta kalli d'iyar ta a gefe dake kallon su tana murmushi tana tsotsar hannu, "Ikon Allah, wannan shine agola yafi dan gidan," Sannan ta wuce kitchen, sai da ta dawo ne Auwal ya bata amsa da, "Tabbas wannan shine agola yafi d'an gida, domin ke da kk zo da gayyar ki gidan yarinya har da mijin ki, ke kk neman mallake wa yarinyar gidan ta, makaranta nake son saka ta, da kud'in ta, dan ubanta ya bada kud'in zuwan ta makaranta, har jami'a, sannan ya had'a da naki yaran, dama lokaci nake jira, dan haka gobe2n nan ba jibi ba zan d'auke su ita da Afrah na kai su makaranta suma," Tsallen murna Atiyyaerh ta saka, Yousuf na mata dariya, ya ja hancin ta, ita ko Afrah kuka ta saka, ita bata son makaranta, duka ake in ji Yah Sulaiman, da kyar Auwal ya rarrashe ta ya mata bayanin yanda lamuran makaranta yake in baka Jin magana baka karatu to fa zaka daku, amma in kana Jin magana Kuma ka na da qoqari se dai a baka kyauta amma ba duka ba, ta na Jin haka se ta yi shiru, had'e su ya yi dika ya fita dasu ta ci kanta dan tinda ya ce zai Saka Atiyyaerh a makaranta ta ke bala'in kashe kud'i za a yi a banza,se da ya qara saiwa yaran abun kwalama sannan ya aje su a makatanta,  yawatawa ya yi ta yi da su Afrah,kafin su nufi hanyar gida Afrah ba wani ci take ba dan tafi ganewa tsotsar hannu, Atiyyaerh kam ta dage ta yi ta ci, dan ta san wataqila da sun je gidan shikenan ta gama ci kenan, ya maida su gida ya yi shirin fita aiki, ya qara jan kunnen Rasheedah akan amanar da aka bata, yana fita kuwa tace da wa Allah ya had'a ta bada Atiyyaerh ba, dukan ta ta hau yi tana zagi, "Munafuka mai halayya irin na uwarta sak, ku dinga simi2 da kai, kamar na Allah, kuna cutar da wanda kuke tare da su, sarai kin san Afrah bata son makaranta kike wani tsalle, dan za a saka ku, dan kija ace ke mai hankali ko? Ita mara son makaranta ko? Kuma wane munafikin ne ya ce ki ce asaka ki ? Yau sai kinci ubanki, gobe in ya ce zai kai ku kice zaki kigani yanda zan kakkarya ki a gidan nan" Sai da ta mata lilis sannan ta tura ta d'aki ita d'aya, Afrah ma miqewa tsaye ta yi zata bi bayan Atiyyaerh, Rasheedah ta daka mata tsawa akan ta koma ta zauna, aiko ta saka kuka sosai, taqi komawa ta zauna d'in, hannu ta miqa dan ta ja ta jikin ta ta hana ta, yarinya kuwa ta kwasa da gudu ta yi dakin, tana shiga ta kulle, kuka ta tadda Atiyyaerh nayi, bata ce mata komai ba ta zauna gefen ta ta saka hannun ta a baki tana tsotsa hawaye na zuba mata, a haka har su ka yi bacci suna ajiyar zuciya. Bayan Yousuf sun dawo ne yake tambayar ina suke , Auwal ma tambayar ta ya yi inda yaran suke da ido ta yi nuni da d'akin su,kallon su ta yi ta ga yanda suka bi hanyar Suma da idanun su, se kawai  ta yi murmushi, dan ta san qaryar da zata yanka masu, kwata2 bata son Atiyyaerh taje makaranta, bata son ta samu Wani abu na ci gaba a rayuwar ta sam........ [01/07, 12:42 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN   BY HAERMEEBRAERH Page 17: "Ina plate din Atiyyaerh?" "Bata tashi ba in ta tashi na had'a mata nata," Tinawa ya yi jiya yarinyar bata samu bacci da wuri ba, ya tabbata bacci ne mai nauyi ya d'auke ta yanzun, se kawai ya ce, "Ok," kafin su gama Atiyyaeh ta farka, ta fito, tana murza ido, gashin ta duk ya hargitse, ya sauka a saman kafad'un ta, direct wajen Rasheedah ta nufa,da sauri Rasheedahn ta hankada ta baya, yarinyar ta bige cup din tea da yousuf ya d'aga zai Kai bakin shi,zafin tea d'in da ya zuba a hannun ta ne ya Sanya idanun ta cika da hawaye, kallon Rasheedah Atiyyaerh ta yi sannan ta fashe da kuka, "Shiiiii ki rufen baki,mai shegen kukan tsiya, uban wa zaki zauna wa a cinya? Ko Afrah ga ta nan a zaune tana karyawa da kan ta,ko kuwa se ke 'yar  gwal zan d'auka? To maza samu waje zauna nan na hada maki abinci, kuma ki min shiru ko ki daku yanzunnan" Miqewa ta yi rai a b'ace taje ta hado mata shayi tsalalo ba Wani wadataccen Madara da millo balle sugar, sannan ta soyo kwai guda d'aya, ta kawo ta dangwara mata ta yanko bread ta dora a saman K'wan ta ce, "Ga shi nan ki cinye dan in kk tsaya min shegen kukan nan naki zane maki jiki zan kina ji na ko," kyab'e baki Atiyyaerh ta yi kamar zata yi kuka tana ci gaba da kallon Rasheedahn, cikin wata iriyar murya mai tsananin nuna gajiyawa da halayyar Rasheedah Auwal ya ce, " Rasheedah ki ji tsoron Allah, wannann yarinyar da ko kyakkyawar magana mai ma'ana ba zata iya maki ba sai ta had'a da shirme kasancewar ba ta da cikakken wayo, ita ki ka zauna ki na wa wannan abubuwan na zalunci, dubi abinda kk bamu dubi wanda kk bata,ita da gidan ubanta, kayan abincin ubanta, kaiii amma baki da imani Rasheedah Sam sam" ya na kaiwa nan ya ja kujerar da yake Kai ya miqe da niyyar barin wajen. "To a min gori tinda Ina gidan uban ta, na ga dai gidan qanwata ne Kuma Ina da gadon qanwata dole na zauna na ci azziqi na bar azziqi a mazaunin shi,sannan ba ni na roqi uban nata da ya ban wajen zama da abincin da zan ci ba, haqqin ka ne ciyar dani me kyau da ban wajen zama mai kyau,sutura mai kyau da kulawa, amma ka gaza wasu mazan sun tara kaima ka zauna cin azziqi, dan haka daga yau kar a sake min gorin azziqi da ka tara da ban ci na wasu ba, Kuma na ga ai zaka iya bata naka in kana so ba Wanda ya hana ka ai, da ta tashi da wuri ai da haka bata faru ba," komawa mazaunin ta ta yi ta ci gaba da cin abincin ta, gaba d'aya abun da Rasheedah ke yi a Kan idon Yousuf Kuma ya na gane halin muguntar da take wa Atiyyaerh da rashin azziqin da take wa mahaifin su,yaron yana da wayo sosai, shekarar shi bakwai, tashi ya yi da dan guntun tea din shi a hannu ya je ya had'e waje d'aya  dana Atiyyaerh sannan ya sake raba masu, nata yafi yawa sosai, sannann ya miqa mata k'wan shi, ya d'au guda d'ayan da aka soya mata, ya na juya shi sai ya ga a qone ma yake ta baya, kawai sai ya hau cire qonannen Yana zubawa a gefen plate d'in shi ya na cin Wanda be qone ba, hakan da yaron ya yi yayi bala'in burge Auwal,komawa saman dinning d'in ya yi ya d'auki nashi Shima ya yi mixing da na Atiyyaerh ya sake raba musu Sulaiman ma ya aikata irin abinda ya ga Yayan shi da Abban shi sun yi,Afrar ce ta tashi dugui dugui zata yi itama Rasheedah ta daka mata tsawa, "Meye haka? Meye wannan zaku dinga wa mutane qazanta wai ku masu tausayi,hana ta abincin aka yi da za ku dinga wa mutane qazanta? Ko dake wannan ma ai tausayin munafurci ne, ba za ku burge ni ba sai na ga kun fasa cin abincin kun bata naku dika," Buga tsaki Rasheedah ta yi sannan ta miqe zata wuce d'aki, Atiyyaerh na zaune ta na Shan tea ta dafe hannun ta a qasa,Cike da masifa Rasheedah ta wuce ko ganin gaban ta bata yi ta kuwa take hannun marainiyar Allah da ke zaune a qasa,wata iriyar razananniyar qara ta saka ta d'auke hannun ta ta na yarfewa tare da Kiran Mommyn ta, Auwal ba qaramin qoqarin danne zuciyar shi ya yi ba na barin ta be mata dukan tsiya ba, d'aukar Atiyyaerh ya yi ya lallashe ta ta yi shiru, sannan ya bata abincin, tare duk sika hade k'wai da dankalin turawan a plate d'aya suka qarasa karyawa, bayan sun gama ne ya shirya ya fita, fitowa ta yi ta kama kan yaran ta ta masu wanka, Atiyyaerh na ganin haka ta hau murna, tsakanin ta da wanka akwai amana, kayan ta ta hau cirewa a d'akin su Wanda a da na Sakeenah ne a yanzu Rasheedah ta maida shi na yaran, d'akin Kuma da yake mallakin Atiyyaerh sai ta maida shi na Afrah, kamar yanda Atiyyaerh ta ke Jin su Yousuf na ce mata Umma itama haka ta fito daga d'akin ba kaya, a bakin qofar toilet suka had'u da Rasheedah wadda ta dakko  Afrah a hannu kamar wata jinjira, da kallo Rasheedahn ta bi yarinyar ,ita kuwa se dariyar farin cikin za a mata wanka take, cikin muryar ta mai dad'i ta ce, " Umma nima a min wanfa" Fuskar ta d'auke da  fara'ar da ta ke qara mata kyau, b'ata rai Rasheedah ta yi sosai sannan ta ce, " Uwar ki ce zata miki wankan? maida wandon ki mai shegen iyayin tsiya kawai," Ta wuce gado ta ajiye Afrar kamar wata jinjira sannan ta fara shirya ta, Yousuf da Sulaiman already ta shafa musu mai ita suke Jira ta basu kayan da za su Saka, a ran ta ta na ayyana dole ne a sauya musu kaya, dan ba zai yuwu Suna a cikin Irin wannan qaton gidan a ce yaran ta na Saka gwanjo ba, kayan sawar su yousuf ta d'akko ta basu,ta hau taya su Sanya wa, Atiyyaerh kuwa ganin ana ta yi ba ita sai ta zuba mata Ido ta na bin ta da  kallo, can  ta kuma cewa, " Umma wanfa," wannann karon idon ta ya kawo ruwa dan tsaf ta na Jin me Rasheedah ke fad'a ai, ta Gane bata so ta mata wankan ne, cikin fushi Rasheedah ta ja ta suka fad'a bathroom d'in, Atiyyaerh kuwa na ta murnar za a mata wanka, tap ta kunna ta tara ruwa a robar da ta yi wa Afrah wanka, ta na gamawa ta d'auke ta ta tsumbula ta cikin ruwan sanyi zata yi mata wankan da shi,kara ta sake ta miqe tsaye tana karkarwa, dariyar mugunta Rasheedah ta saki kamar wata qaramar yarinya me mugunta,zare Ido ta yi ta umarci Atiyyaerh da komawa cikin ruwan ta zauna, qi ta yi ta ci gaba da kukan ta a tsaye, da qarfi ta zaunar da ita cikin ruwan , yarinya na kuka ta qarasa mata wankan, daga ranar ruwan sanyi ya koma na wankan Atiyyaerh, se dai idan ruwan zafin wankan yaran ya ragu, tsabar mugunta ce ta sa ba zata kunna tap din ta sake had'a mata me zafi ba, tinda akwai heater a bathroom d'in,ta gwammace ta d'ebi na sanyi ta yi wa yarinyar amfani da shi. ******************************* Mama  na zaune ta na tinanin ko ya Atiyyaerh take ? Dan ta riga ta San halin Rasheedah bata Jin zata Iya kyale yarinyar ta wataya a gidan su,se kawai ta yanke shawarar zuwa dan ganin ya suke tafi da riqon amanar da aka bar mata, bayan ta sanar da Abba ya bata izini,sannan ya fita shago a unguwar ya siyo abubuwan kwalama na yara yace akaiwa Atiyyaerh da su Afrah, sallama suka yi ta hau abun hawa sai gidan su Atiyyaerh. Tana isa gidan ta bud'e gate da kan ta ta shige, tinda ba mai gadi yanzu, harabar gidan ta kalla ta ga ba motocin gidan hatta da ta Auwal d'in babu, alamu ne na ya fita kenan, da  sallama ta Isa qofar shiga cikin gidan, ta kama hannun qofar ta murd'a, sai ta ji ta a bud'e, sallama ta ci gaba da yi amma ta ji shiru ba Wanda ya amsa, a can ta hango Atiyyaerh k'wance akan kujera ta takure waje d'aya, ta na rawar sanyi,ga parlour ya d'auki wani duhu saboda kashe fitulu da aka yi Kuma labulaye a sake suke, zuwa ta yi da sauri ta Isa gaban yarinyar ta d'aga ta tana tab'a jikin ta, zafi taji rauu, nan danan ta d'aga ta hankalin ta tashe, kwalawa Rasheedah kira ta hau yi amma shiru, miqewa ta yi ta bubbud'e d'akuna biyu na farko da maibin shi taga wayam, sama ta hau can inda d'akin yaran yake a nan ta gansu, Rasheedah ce a tsakiya yaran sun kwanta a jikin ta sun rufu suna kallo, kwalin popcorn zaune a gaban su suna kallo suna ci, mamaki ne mai tarin yawa a ran Mama, "Me nake gani haka Rasheedah? kin saka yaran ki a gaba Kuna kallo amma kin bar wannan tahalikar ita daya a waje, da Wani barawo ne ko me mugun abu ya shigo gidan fa? Shikenan sai a cutar da ita ke kina nan Kuna more rayuwa da yaran ki? habaa Rasheedah, a ina ki ka koyi wannan rashin imanin ne haka? Wacce iriyar zuciya ce a qirjin ki? Tinda ki ke da ni Rasheedah baki taba gani koda bera na wulaqanta ba, haka mahaifin ki, me zakice wa Allah randa ya tambaye ki amanar marainiyar da aka bar maki?" Cike da takaici mama ta bar d'akin, zuwa ta yi tana hawaye ta na tina Sakeenaah baiwar Allah, ta duba kitchen ta d'akko maganin zazzabi na Yara ta had'a tea Mai d'umi ta

Chapter 10 of 21