Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅 Page 20: Tin daga wannan ranar, ko hanya ce ta biyo da Atiyyaerh ta inda Rasheedah take sai dai ta bar wajen da kuka, danko sai ta mata wani abun muguntar da zai saka ta kuka, kullum Yousuf dayasanin fad'a ma mahaifin shi abinda ya faru yake, sannan ya qudurta a ranshi sai ya kama Ahmad ya baje qarfin shi akan shi, tinda shine silar abinda yake faruwa da Ablaerhn shi . Kwance take a d'akin su bayan sun dawo daga islamiyya, ko kayan ta ta kasa cirewa, ashe da empty lunch box ta tafi ranar, sai da ta je zata ci abinci taga wayam, gashi da safe iya tea ta sha, tea din ma ba wani had'in kirki aka masa ba, Auwal tin da ya kula the more yana shiga harkar su the more Rasheedah na qara haukacewa da musgunawa yarinyar sai ya ja baya da shiga lamarin nasu,saboda ya kula idan zai jinyata Rasheedah ne akan Atiyyaerh da ta samu dama sai ta ninka abinda ya mata akan yarinyar,kawai sai ya koma yi mata addu'ar shiriya,dan haka lokuta da dama yana ji Kuma ya na ganin ta tana mata mugunta amma haka zai kasa tanka mata,yau har ya tashi zai Saka wa Atiyyaerh extra cake a jaka sai ya ga ta saka mata lunch box a jakar sai ya fasa aiwatar da qudirin shi,hakan kuwa shi bahaushe ke Kira da rashin sani ya fi dare duhu dan kuwa ba komai a cikin lunch box d'in,ko da suka dawo Atiyyaerh ta tambayi abinci Rasheedah ce mata ta yi ta je d'aki ta cire kaya tazo su ci da 'yan uwan ta, tana shiga ta biyo ta d'akin, tace in ta sake ta koma parlourn sai ta ji a jikin ta,ta zauna har sai ta kira ta, su Yousuf basu gane komai ba, suka zauna jiran ta, " Afrah ku ci abinci mana ko kun cinye akwai da yawa a kitchen zan qara maku na zuba mata wani, maza kuci," Fara ci suka yi, amma Yousuf kwata2 bai jin dad'in ci ba tare da Atiyyaerh ba, a haka ya tura suna gamawa tace su je daki su yi wanka, su huta kafin lokacin islamiyya ya yi,'yan mazan tashi suka yi suka tafi d'akin su, Afrah ma ta nufi  d'akin su ita da Atiyyaerh, se ta ga Atiyyaerh kwance tana kuka, ta riqe ciki, yunwa duk ta gama rarake mata ciki, Afrah ce ta je ta zauna a gefen ta ta tambaye ta meye, cikin kuka ta fad'a mata yunwa take ji, " Umma tace mu cinye zata zuba maki wani,ki je ki ci naki a wajen Umma" Cikin jin dad'i da kuma tsoron me zai je ya zo Atiyyaerh ta miqe ta fita, zaune ta ganta ta d'ora qafa d'aya kan d'aya ta na kad'a ta, rara gefe ta fara cikin sanyin jiki da murya tace, " Umma yunwa nake ji, kamar zan mutu," " Laaaaa kaji munafukar yarinya,yanzu ke a ina kk san mutuwa? Iyyeee, waya fada maki ana mutuwa in an ji yunwa, wahala kawai zaki sha ba zaki mutu ba in ma tsoron mutuwa kk kar ki bi uwale, matsa ki ban waje munafuka ki je ki shirya, ki saka kayan ki,na islamiyya lokaci ya kusa," "Umma abincin fa? Yunwa nake ji yau ban ci abinci ba fa" "Dan uban ki Adnanu ba Zaki bar nan wajen ba se na b'ab'b'alla ki? Dan munafurci salon Wani ya ji a ce bana baki abinci ko? Kin b'ace min da gani ko se na mammake ki?" Tini hawaye ya gama wanke fuskar Atiyyaerh, hankalin ta a matuqar tashe, dan ba qaramin yunwa take ji ba, haka ta koma d'akin,ta fara saka kayan ta na islamiyya, tana sharce hawaye, Afrah ma kukan ne ya kama ta, dan ta ji komai, haka suka gama shiri suka fita, Afrah ce ta gaya ma Yousuf komai, hankalin shi ya tashi sosai da jin haka, gaba d'aya tausayin  qanwar tashi ya gama lausasa zuciyar shi,dan bai san ya zai ya bata a binci ba tare da Umman su ta gane ba, dabara ce ta fado masa,yace su yi gaba zai taho. Sallama ya yi ya shiga gidan ya riqe ciki, da gudu ya yi band'aki, ta bi shi, "Yousuf lfy? Meya same ka? Ko gudawa kk ne?" " Eh Umma, inna fito zan bi kitchen na sha magani na koma makaranta," "To Allah ya sawaqa, ni nayi d'aki ka tabbatar ka ja min qofa sosai kan ka fita," " To Umma" Murmushi ya yi, bayan ta haye sama da dan mintuna kamar biyar ya fito ya yi kitchen ya nemo leda, ya d'ebi abinci, da ruwa a roba, ya d'au maganin gudawa ya fice da gudu, Atiyyaerh ta jingina a jikin windon ajin su tana hawaye tana kallon waje yunwa take ji ba ta wasa ba,can  ta hango Yousuf na gudu, da leda a hannun shi, mamaki ne ya ishe ta,bata gama tambayar kanta meye a ciki ba ta ga ya shiga ajin su yana neman izinin an aiko shi wajen Atiyyaerh dan ta taho bata ci abinci ba aka ce ya kawo mata, " Ablaerh ki taso yayan ki na neman ki a waje kar ki dade," in ji malamin su da ke tsananin son ta, saboda qoqarin ta, bayan haka Atiyyaerh yarinya ce Mai shiga rai, sannan Kuma ba Wanda ya qi yaro me kyau ai. Cikin hanzari da rashin kuzari ta isa, suna fita ya bud'e mata abincin a wata 'yar kwana a yunwace ta hau d'iban girkin ta na ci idon ta na kwalla, haka ta cinye abincin tas ta sha ruwa, Yousuf kuka yake har da majina, ba qaramin tausayi ta bashi ba,samu ya yi ya goge mata bakin ta sosai da ya yi maiqo, "In mun koma gida Umma ta baki abinci ko kin qoshi ki karba, in ba haka ba zata gane na baki abinci ta dake ki ta dake ni, kin ji," kad'a kai ta yi alamar ta ji,sannan a hankali cikin sanyin murya tace, " Na gode Yaya," Murmushi suka yi wa juna sannan suka tafi ajujuwan su, Yousuf sai da ya sha bulalar latti, sannan aka barshi ya shiga. *Bayan shekara bakwai* Atiyyaerh an fara zama budurwa ita da Afrah, Sulaiman da Atiyyaerh na  JSS 2, Yousuf Kuma  ana SS 2, Afrah na JSS 1 daga baya ta Maida hankali a karantun ta dik da cewa har yanzu bata Kai Atiyyaerh hazaqa ba amma ta fi da fahimtar abinda ake koya musu a makaranta, Atiyyaerh ta zama budurwa me cikar halitta da haiba, duk da cewar ba qaramar wahala take sha ba a gidan duk wanda ya ganta zai d'auka ta fi shekarun ta, tana da girman jiki, Afrah ma hakan take a bangaren ta ba laifi sun yi gadon kyau wajen iyayen su maza da mata, duk wani aikace aikacen gida Atiyyaerh ke gabatar da su kama daga kan wanke2 share2, wankin kayan ta na gida da uniform, watarana har na Rasheedah da Afrah haka za a sa ta yi dole, dik da cewa akwai washing machine a gidan, wataran in za su gidan Mama gaida ita, in ta ga ta je can musamman a week end sai ta ce ita a barta zata yi mata weekend to anan take samu ta huta da aikace2, ta samu ta maida hankali a kan hardar ta ta Qur'an da karatun bokon ta. Kayan kwalliya wajen Afrah ba a magana, ko abun wankan ta daban ne, daidai misali Auwal harka ta bud'e masa ga aiken kud'i da baya yankewa daga wajen Adnan, kudin da Adnan ya bar masa ya kula da Atiyyaerh ma juyawa yake yi Yana yin blocks da Saida siminti tinda ya fi kwarewa a wannan harkar, dan haka Yana qoqarin wadata iyalin nashi da duk Wani abu da suke buqata, Atiyyaerh kam har ta cire rai da amfani da kayan kwalliya, domin tasha gargad'i wajen Umman su akan kar ta sake ta ganta da kwalliya, ko ta ji ta yi amfani da tirare ko abun wankan Afrah, roll on kawai take sai mata Shima acewar ta kar ta kashe su da warin balaga, duk qoqarin Afrah na ganin Atiyyaerh tayi amfani da su ko a boye ne amma inaa Atiyyaerh taqi Sam domin ta ma riga ta Saba da rashin kwalliyar, in ta matsa sai tace mata "Afrah kar ki damu, ni Kwalliya bata gabana yanzu, fatana na gama da duniyar nan lafiya ko so kk na saba umarnin Ummana? Wace irin yarinya kk so na zama kenan an hana ni yin abu Kuma na aikata? A haka ma alhamdu lilLAAH bana buqatar Kwalliya na gode da nuna kulawar ki a gare ni, best friends for everrrr," Sai ta Kai wa Afrah runguma ta na dariya,lokuta da dama da sabulun wanki take wanka, sannan ta shafa  basilin, har cikin ranta bata Jin Wani damuwa akan hakan,duk randa karambanin Afrah ya Kai ta ta saka wa Atiyyaerh tiraren ta a jiki kuma Rasheedah ta ji qamshin ranar Atiyyaerh sai ta daku, Afrah kuwa haka za tai ta kuka tana bada hakuri tare da Yi wa Umman nasu rashin kunya, Auwal ya sha yo musu shopping ya siyo kayan Kwalliya da turare domin Atiyyaerh amma haka Rasheedah zata kwashe, Yana so ya yi magana, ya na gudun ja wa yarinyar duka ko Wani zagin a wajen muguwar Auntyn tata. Watarana ba da niyya ba Afrah ta dauki hijabin islamiyyar Atiyyaerh ta feshe shi da turare a zaton ta nata ne tinda iri d'aya ne, sai da ta gama shiri zata fita daga d'akin Atiyyah ta fito daga wanka d'aure da towel, ta kula da hijabin ba Wani baqin ruwan biro a jiki, fari ne qal, se ta tsayar da Afrah ta mata bayanin wannan nata ne, Dan kuwa na Afrah ya baci da ruwan biro, hakuri Afrah ta bawa Atiyyaerh ta miqa mata hijabin ta, ta koma ta d'auki nata ta Saka,sannan ta sauka ta ce wa Atiyyaerh Suna jiran ta a qasa, bayan kammala Shirin ta ne tsaf ta Sanya hijabin ta sauka qasa itama Gani ta yi Afrah ce kawai su Yousuf sun yi gaba, ta na zuwa kuwa hancin Rasheedah ya shaqi qamshin turaren Afrah a jikin Atiyyaerh, tini ta kama masifa da bala'i ta na fad'in Atiyyaerh ta raina ta bata Isa ta hana ta abu ta hanu ba, bud'e baki Atiyyaerh ta yi dan ta mata bayani, ta kuwa tashi a fusace ta Kai mata duka, bata kyale yarinyar nan ba se da ta lallasa ta tas sannan ta barta ta haye sama ta na ci gaba da zagin Atiyyaerh, kallon Afrah da ke kuka kamar ita ake duka Atiyyaerh ta yi sannan ta ce, "Afrah in dai kina so na da gaske baki son ana dukana kamar mara gata ko galihu, ko dake bani da gatan ma ai, Dan Allah da son Annabi ki daina qoqarin sai nayi amfani da kayan ki, na gode da qaunar ki a gare ni yayata, bana fatan Allah ya gajiyar dake a wajen tausaya min keda Yayah Da Yah Sulaiman amma Dan Allah ki dinga taya ni kiyaye abinda za a dinga dukana akwai zafi, ba wai iya zafin jiki ba, Ina Jin zafi a nan d'ina, Ina Jin zafi Afrah a cikin zuciya ta, ba zan iya kwatanta miki ya zafin yake ba, ba na fatan ki ji irin wannan zaf'in Afrah akwai ciwo sosai,na riga na gama yarda Mommy na ta rasu Daddy na Kuma baya so na saboda Mommy na ta rasu shi yasa ya barni anan na sha wahala, na ji na amince zan jure komai, zan shanye komai, amma dan Allah ki taimaka min zamana anan ya min sauqi, ba zan iya ci gaba da jure irin wannan wulaqanci da quncin ba Afrar akwai ciwo sosai," Afrah ta kasa magana sai kuka, da gudu ta fad'a jikin Atiyyaerh ta rungume ta sosai kamar zata tsaga jikin ta ta shige ,banda gunjin kukan su baka Jin qarar komai a parlourn, Yousuf da Sulaiman tini sun Isa makaranta saboda a tinanin su Afrah ce ta tsaya kyale kyalen ta da ta Saba zata sa su makara, dan haka basu San wainar  da aka toya aka cinye ba,sai da suka yi kuka suka gaji suka tsaya a tap din tsakar gida suka wanke fuskar su sannan suka tafi makarantar. A haka Atiyyaerh ta saba da rashin kwalliya,ta Saba da azabar Rasheedah har ta dena wa duk Wani duka ko zagi kuka, sai dai ta yi Murmushi me ciwo ta bata hakuri,bangare guda kuwa duk wanda ya ganta zai rantse bata da damuwa, Atiyyaerh na da natural kyau Mai d'aukan hankalin me kallo, gata da nutsuwa da kamun kai. *DUBAI* Kwance yake a makeken gadon shi, yana ta tinani kamar kullum, har wannan lokacin bai yi aure ba, wayar shi ya lalubo ya danna kiran Abba, Abba na gani ya yi murmushi, ya d'aga kiran, bayan sallama da gaishe2, ne yace "Abba akwai Wani abu da kuke buqata? Ka San bana so a wannan shekarun naka kana wahalar da kan ka, hutu ka ke buqata a yanzu Abbana" "Alhamdulillah bamu da matsalar komai sai ta kewar ka, satin can na sama Ablaerh tazo mana  hutun qarshen mako,kullum tazo zancen ta bai wuce mu bata labarin mahaifan ta ba, ka daure ka dawo ka ganta,domin kwanciyar hankalin ta dan ita gani take kamar baka son ta ,in ka dawo mu ma namu hankalin ya kwanta, gashi kaqi aure, wannan shine matsalar mu Adnan, to a gaskiya zan fad'a Maka bamu da wata matsala a yanzu se wannan, ka daure ka jure ko dan raya sunnar Annabi Muhammad ka yi aure, Kai fa ba ma'asumi bane Adnan, akwai lokacin da dole Dan Adam Yana buqatar mace,dan Allah ka daure ka yi aure,babbar soyayyar da zaka nunawa Sakeenah kenan ka tsare Kan ka daga fad'a wa halaka ta hanyar yin aure," Rintse ido Adnan ya yi cike da jin zafin mutuwar matar shi da kullum ke tab'a shi, ga kewar d'iyar shi dake dawainiya da shi, amma baya jin lokaci yayi da zai je ganin ta, " Abba ka yi hakuri zan zo ne, amma ba yanzu ba, inshaa Allah zan zo ne,Kuma maganar aure zan duba na gani, Abba na kasa dena tuna ranar da ta barmu, Abba wa ka ke ganin zan aura bayan zuciya ta bata da Wani ragowar gurbin da wata zuciyar zata samu mazauni a cikin ta? Ina tsoron na yi aure na zama silar zubar hawayen wata Abba, Abba ku ci gaba da taya ni addu'a Allah ya sauqaqa min ya min zab'in alkhairi" "To Adnan Allah ya kare mana kai, ya sa da rabon ganawa,Allah ya sauqaqa Maka radad'in da ka ke ji a zuciyar ka, Allah ya Maka zab'in alkhairi, ka kula da kan ka,ka kare kan ka daga zina,da shayen²n matasan yanzu in an ga kud'i da wadata sun samu se a dinga shaye shaye da neman matan banza, in ka ji wani abu na son mace na taso maka ka yi azumin alkhamis da litinin, ko ka samu ka yi auren ka,kar ka jefa kan ka halaka bayan Allah ya rufa maka asiri Adnan," Cike da jin dad'in addu'o'i da nasihar Abba Adnan ya yi godiya suka yi sallama ya koma ya kwanta, yana matiqar jin dad'in yanda Abba ke matuqar son shi,yake masa nasiha da take ratsa masa jiki ta dasa masa tsoron Allah. ****************************** Shirin tafiya kitso Atiyyaerh take ita d'aya, gobe akwai makaranta, Afrah ta riga da ta yi nata tin jiya, tana cikin tafiya ta kusa shiga gidan ne ta ji ana kiran ta, cike da b'acin rai ta d'aure fuskar ta, dan bata qaunar ko da jin muryar shi ne balle ganin shi.. . . . *Thank u guys for ur comments ina jin dadi sosai, kuma yana sa na qara sambada maku typing ba tare da naji gajiya ba. ME LOVE U DA YAWA❤*[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERHMEEBRAERH Page 21: Tsayawa ta yi cak a inda take, dan bata son ya bita cikin gidan yana mata surutai marasa tushe da ma'ana a cewar ta,su Kuma matan gidan na biye masa ana cewa budurwar sa ce ita, da fuskar ta mai d'auke da gajeren Murmushi na ba yabo ba fallasa ta juyo, yana tozali da fuskar ta ya ji wani sanyi a ranshi,ba kadan yake son Atiyyaerh ba,shi in za a taimaka mishi yanda baya makarantar nan ba wata uwar yake tsinanawa ba sana'a se d'aukan magana to a bashi auren ta kawai,cikin washe dikkan haqoran shi ya ce, " Hajiya Atiyyaerh, meye na sauri kawai dan kin ji ina kiran ki, ki kwantar da hankalin ki, in Allah ya nufa nine mijin ki ko ba dad'e ko ba jima sai na aure ki," Cikin jin haushin kalaman shi ta gyara tsayuwar ta ta kalle shi Ido cikin ido, amma dake bata son ya gane meye a zuciyar ta sai ta sake fuskar ta ta, ta shanye b'acin ran ta sannan ta ce, "Haba Ahmad yaushe ka ga Ina sauri ni? Sannan a gani na tinda ka san da haka me zai sa mu yi ta bata lokacin mu mu dika muna tsayuwa hira a titi? Mu Jira mu gani in har akwai qaddarar aure a tsakanin mu, sannan dika dika ma nawa nake? Kai Kan ka shekarun ka nawa har da ka ke hango aure? To gwanda gwanda ma ni mace ce tinda ana wa mata aure da wuri kafin maza, ballantana ma ni yanzu karatu nake, bana buqatar soyayya yanzu,ka bari inna gama makaranta munyi maganar soyayya da auren ma gaba d'aya dan Allah, ka dena bina kana surutan da ka ke please" "Da gaske kin amince  za mu yi magana in kin gama karatun ki? Hakan fa na nufin zaki ban dama na shiga neman auren ki?" D'aga masa kai ta yi da murmushi, suka yi sallama ta shige gidan nasu. A tiyyaerh na da samari a wadannan shekarun nata, dan kowa ya ganta zata yake tafi ainahin shekarun ta, duk sanda manyan motocin masu hannu da shuni suka tsaida ta a hanyar islamiyya ta kanyi murmushi ne kawai ta ci gaba da tafiyar ta, a haka ne ta samu wani, Hassan, ba qaramin son ta yake ba,iyayen shi manyan masu kudi ne, ba zai wuce shekara 25 ba, ya takura ta matuqa, Afrah kan ce mata "ki bashi dama, ko da secondary ne ki ka gama a aurar dake ki huta, wannan rayuwar gidan in baki barta ba zaki samu ciwon zuciya wata rana," Takan yi murmushi tace, "Afrah nawa muke ne da muke tinanin aure ne, we are still young,getting married at young age will not solve my problems, kawai zan ta addu'a Allah ya zaban mafi alkairi," Afra kan amsa da " Ameen" amma tana matuqar tausayawa qanwar ta ta, ta wani bangaren kuwa Yousuf ba qaramin tausaya mata yake ba, ya qudurta inshaa Allahu zai jiyar da Ablaer daɗi fiye da yanda take tinanin samun sauqi a rayuwar ta, to taya zai samu wannan damar? ******************************* A kwana a tashi asarar mai rai, yau su Ablaerh ke rubuta jarabawar su ta qarshe a makarantar sakandire ta Al'ansar, Atiyyaerh da Amal na hango sun had'e kai tare da rungume juna suna ta kukan rabuwa da junan su,sun bala'in ba wa qawayen su tausayi, dan kowa ya san yanda suka shaqu, babban abinda ya sasu kukan dama shine an saka ranar bikin Amal, kuma ba a qasar nan zata zauna ba ma, Ghana za a kaita, can dangin mahaifin ta, biki ma a ta can zasu yi shi  na al'adun su ba anan ba balle ta samu damar zuwa, da kyar aka raba tsakanin su kowa ta tafi cike da kewar 'yar uwar ta, sun iso gida kan Atiyyaerh na matuqar ciwo, ta rasa ina zata saka kanta ta ji dad'i, dan ko magani tasan ba ta da arziqin da za a bata a gidan, shigewa d'akin su ta yi bayan ta gaida Abban su da Umma dake zaune, Abban su ya taya su murnar kammala secondary school da suka yi, sannan ya na burin saka su a makarantar gaba da sakandire in har results din su ya yi kyau dik da bashi da tantama akan yaran nashi musamman Atiyyaerh, sai dai bai fad'a masu hakan ba, ya bar abun a ran shi,  yanayin yarinyar  yasa yana son ya je ya ji me ke damun ta, amma yana tsoron iya masifa tace yana banbanci, addu'ar samun sauqin koma meke damun ta ya yi mata a ran shi. Tana shiga ta fara cire kayan ta, ta ninke ta saka a basket din wankin su, daga ita sai pant da brah, da dogon skirt, a hankali ta warware gashin ta ko zata samu sauqi daga daurin da ta masa, ya zubo a bayan ta, ta sa hannu a can qasa ta buda shi sosai,dan ta sha iska, tana cikin haka aka bude aka shigo, a zaton ta Afrah ce, " Ban San me yasa ki ke son shigo wa waje ke ba sallama ba kullum, sai kin tsorata mutum kizo kina Wani yi hakuri my sister," Tana nuna yanda Afrahn take mata, juyowar da zata yi idon ta ya shiga cikin na Yousuf, cikin in ina tace, " Yah....yah..yayah?" Daga mata kai ya yi, cike da murna ta tafi da gudu da niyyar rungume shi kamar yanda ta Saba da tana yarinya,sai kuma ta tsaya agaban shi, tana ta dariyar farin cikin ganin shi, yau wata shida kenan daya koma makaranta, a zariya, " Yayah yaushe ka zo, ba ko sanarwa?" Shiru ta ga yayi har lokacin bai motsa ba, bai kuma kifta ido ba, sannan kuma bai ce mata komai ba, kallon inda ya qurawa ido ta yi ta ga ya hadiyi wani yawu , daidai qirjin ta ta ga yana kallo, wata siririyar qara ta saki, ta juya tare da dafe wajen,tana zare ido, gashin ta ta barbaza a jikin ta ya rufe mata kafadu , cikin tafiyar sauri ta sunkuya tana jan bedshit din su, sun irin cusa shi can cikin nan, ya qi fita, kawai sai ta duqa a wajen cike da kunya ba kadan ba, dariya yake sosai, harda kama ciki, "Yayah go out pleaseeeee," " No, i can not just go out,In kuwa na fita sai dai na koma zariya kin yarda?" Cike da tsokana ya fad'i hakan, " Yayahhhhh pleaseeee manaaa" Ta qara fad'a cike da shagwaba da muryar dake nuna alamun gaf take da Saka masa kuka, dariya ya yi sannan ya ja qofar ya fice,kan ya qarasa fita yace mata, "In kin shirya ki samen a dakin mu na baki tsarabar ki," Bayan ta amsa shi da "To" ne ta ji dariya ta kama ta, nan da nan ta nemi azababben ciwon Kan ta rasa se sama sama take Jin shi,ta na Saka kaya ta na tinanin irin kyaun da yayan nasu ya qara kamar ba shi ba, dafe qirjin ta ta yi, data tina wani kallo daya mata, sannan ta tina inda ya kalla, buga qafar ta ta yi a qasa, tana tirje2, tana kukan shagwaba, jikin ta na ta motsawa,Afrah ce ta bude qofar zata shigo, tana shigowa ta ga Atiyyaerh na hakan, "Ke kuma lfy, me yake damun ki?" Cike da shagwaba ta bud'e baki ta fara magana da cewar, " Ba yayah bane ya shigo mana daki ba ko sallama kuma ban maida kaya a jikina ba," Dariya ce ta kama Afrah sosai, cikin dariyar ta ce, " Ayyaa so sorry love, kuma gashi ya gama gane maki wannan tula tulan naki, kaiiii sorry u," Zaro ido Atiyyaerh ta yi dan ta tabbata ba da jimami qaramar yayar ta ta tayi maganar ba, ( in baku manta ba Afrah ta ba Ablaerh kwanaki ne) cike da shagwaba ta miqe ta maka mata pillon dake hannun ta, ta wuce wajen kayan ta,dake cikin wata jaka , dan Rasheedah ta hana ta saka kayan ta a wajen na Afrah,duba doguwar riga ta yi, a kayan ta aje a gefen gado,ta dauki duk abinda take buqata in ta yi wanka zata saka ta aje, sannan ta wuce Afrah da har yanzu bata daina dariya ba tana tsokanar ta, dan ta san yanda Atiyyaerh ta tsani a ga jikin ta,musamman qirjin ta, dan Allah ya hore mata su, sannan ga shi wai Yayahn su da take tsananin jin kunya tin da suka fara girma,yanzu kuma

Chapter 12 of 21