Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwalliya da atampa kalar red da fari, sai ratsin baqi,ta yi kyau sosai itama ba laifi ba makusa,se ta yafa farin mayafi a saman Kwalliyar ta, ta qawata qafarta da farin takalmi, dan Auwal ya sanar da ita dawowar  Adnan da yake yawan bata labarin shi,dan haka ta san komai game da rayuwar su, bayan sun gaisa itama ta masa ta'aziyyar rashin Sakeenaah, yaji matuqar dad'in hakan,suka taba hira kafin su tafi itama Adnan ya bata ledar da ya yi mata tsarabar turaruka,sannan suka rabu kowa ya yi gidan shi. Rasheeda na zaune ido tarwai bata ko Jin alamun bacci a cikin su, qarfe goma daidai ya yi sallama ya shiga gidan, "Daga ina kk malam? Ohhh daga wajen karuwar da kk son kawo min cikin gida a matsayin kishiya ka ke ko? To bari kaji na fad'a Maka Auwal, ba zan zauna da kishiya ba, sai dai ka zab'a,ko ni ko ita," Ta kame hannu a qirji tana girgiza qafa,sanye take da doguwar rigar bacci mai santsi da ta daurawa zani a saman ta. "Ke dai zaki zab'a zama dani ko tafiya gidan Abbah, ni dai na wa qanwar ki 'yar aljannah da yardar Allah alqawarin ba saki tsakanin mu, amma in kina ganin zaki tafi ko kina son sakin zan iya baki, aure kam kamar na yi na gama, yanzu ne zaki tantance a Ina ake yin kishi Rasheedah,a tsakanin soyayyar zumunci da soyayyar miji, sannan da wasa kk sake ce ma matar da zan aura karuwa tabbas sai na barar maki da haqora, in yaso kin ji dad'in yin kishin da b'ab'urarren baki, sokuwa kawai," Kuka ta d'ora hannu aka ta rusa, yaran su na d'aki suna jiyo su, kowa dariya fal ciki, Afrah da take ita d'aya a d'akin ta kasa jurewa ta yi,ta kuwa hau kwasar dariya abin ta, dan ji take kamar ta matso da ranar auren Abban nasu, Yousuf bai son ya yi dariya saboda Sulaiman ba'a sirri da shi dan ya na fasa dariya zata Jiyo su,in kuwa  ta ji su se sun sha jarabar ta akan su zata juye haushin uban su, ai ko suna had'a ido suka fashe da dariya a tare,Sulaiman da ba a sirri da muryar shi har waje, tana ji kamar mahaukaciya sabon kamu ta yi hanyar d'akin tana zage2 ta na fad'in sun raina ta,ba laifin su bane laifin ubansu ne daya sai mata raini a wajen su, kafin ta idasa shiga d'akin Yousuf ya yi tsalle ya datse qofar ya rufe da key, ta gaji da fadan ta a bakin qofa tai gaba, dariya suka ci gaba da yi,suna maida zance. A lokaci d'aya, Adnan ya shigo masu da lefe,har na Atiyyaerh shi ya had'a tinda Allah ya hore masa arziqin yin hakan, sadakin Atiyyaerh da  Sulaiman Auwal ya d'auki nauyi, Adnan ya sanar dasu, dukkan su a gidan shi sabo da ya sa aka gina tin kan ya dawo zasu zauna, har Abbah da Mama duk zai dauke su daga nan tsohon gidan,mijin Afrah ne kawai zai dauki matar shi ya Samar mata muhalli dan kar su ga an musu katsalandan a lamuran su,dik da cewar Adnan ya fara yi wa mijin nata tayin komawa sabon gida amma ya nuna masa ah ah ,ya fi so su zauna a inda ya gina da kan shi,dake yana da zuciyar nema shima, ya ce A'a yana da gida,in dai Afrah zata iya zama, d'aki uku ne, kitchen da toilete a kowanne daki, ga toilet a tsakar gida,sai babba parlor da dinning area, ga parking space, da ba zai wuce wajen zama  mota d'aya ba, ba laifi, gidan ya yi sosai,Afrah ta aminta, inda ta nuna mai ita ko da gidan qasa ne zata zauna da shi,albarkar auren suke nema. Sati biyu da kai lefe aka d'aura auren su, gaba daya, an sha shagalin biki ba kadan ba, nera kam ta koka, kuma sun koka rashin Sakeenaah a wannan rana, wanda Rasheedah ce ta fara kokawa har abun ya ba su mamaki, har ma ta dinga yi mata addu'a, mutane ma akai ta yi mata addu'a, 'yan uwan Adnan ma sun nuna bajinta a wannan gagarumin ruguntsumin bikin aure me dimbin tarihi da aka gudanar na tsahon kwana hud'u,bayan kammala dinner da aka gabatar a rana ta hud'u mutane da dama suka koma gidajen su,Wanda za su Kai amare da Kuma Wanda za su kwana washe gari su wuce suna nan ana ci gaba da harkokin azziqi. Amare da angwaye ne zaune a qasa a gaban Abbah ya tara su a babban parlourn shi dan yi musu nasiha da addu'o'i kowa zaune kusa da matar shi,amare sai 'yan koke koke suke na al'ada, Atiyyaerh kuwa kukan ta ya had'a ma'anoni da yawa, tinawa da auren ta na fari, rashin mahaifiyar ta,da  murnar samun auren zab'in ran ta. Abbah da Mama sun ce za su bar angwaye da amare su gama amarcin su kafin su koma sabon gida, Dan haka ba da su za a tare ba. Rasheedah kuwa kamar zata mutu haka take jin kishin nan na tab'a qoqon ranta,cike da takaici ta shige motar Auwal ta na jiran shi ya je ya ja su ya Maida su gida, a gaba ta qame qam ta na jiran ta ji an ce ta koma baya ta sauke kwandon rashin mutunci, ba Wanda ya kula ta, Auwal ya bud'ewa amaryar shi baya ya Saka ta ya koma mazaunin driver ya ja su suka wuce gidan su. Adnan kuwa da motocin shi akai ta zirga zirgar Kai amare da shi kuwa da kan shi ya ke son ya Kai amaryar shi gidan ta, dan daga wajen Dinner a gidan Abbah dik suka taru har Baffanin shi da Kawunan su akai addu'a da Sanya albarka. Bangaren Rasheedah kuwa ko da suka Isa gidan qin fita ta yi a motar ta na so ta ga kwal uwar daka, Auwal be kula ta ba ya je ya kulle gate ya yi addu'a, sannan ya ja hannun amaryar shi ya ce ta kulle gidan in ta shigo suka shige suka barta a wajen,a tsaye ta tadda Auwal ya qanqame amaryar shi kamar za a kwace ta sai Wani shinshinar ta yake yi, amarya kuwa kunya duk ta hana ta kwakkwaran motsi,bakin shi ya Kai saman nata ya sumbata a hankali narkewa ta yi a jikin shi ta na b'oye Kan ta a qirjin shi, motsin Rasheedah ne ya sa amarya ta janye jikin ta daga nashi,tana kallon Rasheesah da ta cika ta yi fammm, Abba ne ya yi masu magana akan yana son ya yi magana da su, ganin irin kallon da Rasheedah ke wurga wa amarya se ya bawa Amarya haushi, dama ta na da labarin Rasheedah kaff Dan haka sai ta koma ta sake lafewa jikin Auwal cikin shagwab'a ta ce, "Gaskiya ka bari sai gobe ka yi mana  maganar please baby, saboda ni dai ....ni daiiiii Ina buqatar mijina yanzu ka ji baby," Cike da shagwaba ta qarasa maganar kamar wata 'yar qaramar yarinyar da bata gama Iya magana ba, gaba d'aya Auwal ya rud'e, ya susuce, janta ya yi kawai suka fad'a d'akin su, Amarya ce ta rufe qofar, tare da watsawa Rasheedah mugun kallon da ta ga ta na bin ta da shi itama, sannan ta ce mata "Yah dai na ga ki na biyo mu ko da ke za a shiga d'akin amarya da angon ne?" Ta ja guntun tsaki sannan ta doka qofar ta shige,wata qara Rasheedah ta sake, ta durqushe a wajen tana kuka, da kan ta ta rarrashi kan ta ta yi shiru,ji ta yi sun tada sallar su ba Wanda ya kula ta,daga nan taji Auwal na yi wa amarya addu'a suka ci kazar da bata San sanda aka siya ba balle sanda aka Kai ta d'akin,to Ita Ina tata kazar? Amma dai Auwal bai da adalci in dai haka ne,  sai hirar su take ji sama sama, dik da dai Auwal ne ke ta zuba amaryar ta koma Jin kunyar shi, can Rasheedah ta ji  ya sauya salon nishin shi da kalaman shi, da gudu ta bar wajen ta yi daki ta na mugun gunjin kuka tare da fad'in, "Na shiga uku ni Rasheedah, dama wannan ne kishi, kenan da gaske Hassada nake wa qanwata uwa d'aya uba d'aya, a da bana jin wannan qunar zuciyar da na ke ji a yanzu, wayyo zuciyata , Sakeenaah ki yafe min, tabbas kin yi gaskiya,abinda kk so na gani na gane a yanzu na ganshi Kuma na gane wayyoo ni Rasheedah na shiga uku na lalace," kuka take kamar ta had'iyi zuciya take ji, kanta kamar zai cire qasa dan ciwo, a nan qasan ta yi baccin wuya, kamar a mafarki ta ji an bud'e qofar d'akin ta an shiga, dukan qafar ta ta ji ana yi kamar tashin ta ake Daga bacci, bata gasgata ko me ke faruwa ba ita dai zaton ta ya bata mafarki take, muryar Amarya ta ji a kan ta ta na fad'in, " Malama ya ya dai naga har yanzu kina kwance ki na bacci baki soma qoqarin had'a mana abin karyawa ba, ko so kk in ya dawo daga masjid ni da nake amarya na fito had'awa? Sarai kin san, ban da lfy, qafafuna ciwo suke,sai na sake shiga ruwan zafi tukunna,zan ji dama dama saboda yanda baby ya hana ni bacci jiya, gaba d'aya gabb'ai na ciwo suke" Hawaye ne ke Malala a idanun Rasheedah da ta gama tabbatar da cewa idon ta biyu ba mafarki take ba, Wani abu ne mulmulalle take ji ya tokare mata wuya tsabar baqin kishin da take ji na dawainiya da ita,gashi wani kwarjini yarinyar ke mata har wani tsoro tsoron ta take ji, Auwal ne ya shigo, amarya na ganin shi se ta yi  kamar miqewa ta yi daga tsugunnon gaida Rasheedah, da sauri ta saki wata 'yar qara, Auwal na ganin haka ya yi sauri ya nufe ta ya qarasa d'aga ta, "Sannu, ni bana ce maki kar ki fito bane, sai kin gama warke wa? Gashi nan zaki qarawa kan ki ciwo ai, wuce mu je na sake sa maki ruwan zafi ki shiga wataqila za ki fi Jin dad'in jikin ki, sannu Allah ya sawaqe," Cike da shagwaba ta fad'a qirjin shi, ya tallabe ta yana shafa bayan ta,cikin kissa da maqale murya ita a dole ga mara lafiya ta ce, "Wai da zuwa na yi mu gaisa da Yaayaah, se na ga kuma kamar sallah ta ke shine na Jira ta idar na gaishe ta," Baki Rasheeda ta saki dan tsananin mamaki, lallai akwai aiki a gaban ta babba ashe?.......... *Woo ke Woo ke  Amaryar Auwal, sha sha'anin ki duniya ce samaaaa*💃🏻💃🏻💃🏻👄👄👄 [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: Ta bangaren Rasheedah da amaryar ta kuwa komai ya wuce kamar Wani saba'ni be tab'a shiga tsakanin su ba, girmamawa sosai Khadeejah ke Yi wa Rasheedah, yaran amaryar ma gaba d'aya Rasheedah ke kula da su, a kullum bata da aiki, sai yiwa qanwar ta Sakeenaah addu'a da fatan samun rahamar Allah, ta tabbatar da cewa Sakeenah na can ta samu ladan gyara zumuncin da ta yi sanadin shi, ta gode wa Allah da ya bawa Sakeenaah JARUMIN miji kamar Adnan, Wanda ya yi hakuri ya jure rashin 'yar shi a kusa da shi dik da labaran da yake ji na azabtarwa da ta yi mata, ta gode wa Allah da ya sa ta gane halayyar da take na hassada da kyashi da kishi ba abu bane me kyau tin kafin ta mutu, a yanzu rayuwa suke Cike da so da qauna da girmama juna ita da Auwal tabbas Auwal SHINE JARUMIN ta na har abada, ba zata gaji da gode masa ba a bisa hakuri da ya yi da halayen ta marasa kyau. Ahmad kuwa na can ya Maida hankali wajen neman ilimi da kasuwanci, ya na matuqar kewar Atiyyaerh wannan dalilin ne ya sa ya kasa neman mata da kan shi ya aura, sai Hajar ce ta sama mashi mata cikin qannen ta aka aura masa, Yana da Yara biyu Shima mata dika, ta farko ta ci sunan mahaifiyar shi, ta biyu Kuma ya Saka sunan Atiyyaerh, gaba d'aya gidajen ana zumunci da juna daidai misali. *Alhamdulillah....Nan na kawo qarshen novel dina mai suna,KAI NE JARUMI, ina riqon Allah daya gafarta min kuskuren dake ciki,alkairin da ke ciki ya yad'a shi a dika duniya ya bani lada, ya bama makaranta ikon amfani da saqonnin dake ciki na alkairi Ameen.* *A cikin mazajen nan na labarin KAI NE JARUMI wanene Jarumin ki/ka?* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 21 of 21