ce masa,
"Taso taso miji na gani na baka dama in ma cikin 'yan biyu zaka min yau d'in nan shirye nake da d'aukan shi ka haska min yau Wani duhu da na jima a ciki" Auwal bai fahimce ta ba shi dai murna ya hau yi ta yarda da shi dan haka ya kora ni waje suka rufe qofar su
Burin ta kawai yanzu be wuce ta sake samun ciki ba ko dan ta qunsa wa Sakeenah haushi kamar yanda Sakeenan ke qunsa mata haushi a kullum...........
Niko na ce ki ke qunsawa Kan ki dai
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Page 10:
Sakeenaah na had'a Ido da Rasheedah ta ji gaban ta ya yi wani irin mugun faduwa, saboda yanda taga tsantsar tsanar ta da qiyayyar ta a fuskar yayar tata, cikin rawar murya ta ce,
"Rashee....."
"Dakata min tsohuwar munafuka, dama had'awa ki ka yi da mijin ki in kunzo ku min wulaqanci gaban iyaye na ku min munafurci da annamimanci? Ku fada masu abubuwan da na maki dan su qara tsanata? Gaki an taba 'yar so Kuma 'yar gwal ko? To bari kiji na fada maki wani abu da wataqila baki sani ba Sakeenaah, ni Rasheeda na yi alqawarin ba zan tab'a son ki ba a rayuwa ta har abada,ko me ki ka zama, ko me zaki zama,ko me ki ka mallaka, ke zuri'ar ki ma ba ni ba su ko da kuwa duniya zaki haifa dan yawa nan gaba ni dasu ba zancen soyayya, na tsane ki ! Na tsane ki !! Na tsane ki !!!"
Numfashin Sakeenaah ne ke mata wahalar shaqa, ido ta lumshe wanda tin da Rasheedah ta fara magana take zubda hawaye, wannan wace irin rayuwa ne,wace iriyar qiyayya ce haka me zafi? Me ta yi mata? Anya Rasheedah bata da aljanu da ke had'a su fad'an ba gaira babu dalili? Dan ita har yanzu bata San menene takamaimai abinda ya janyo wannan mahaukaciyar qiyayyar me zafi ba a tsakanin su, a bayyane take nuna mata tsana, kyashi, hassada, da qiyayya, yau ko kafira ce ita ai se haka,abun takaicin shine tama qi sanar da ita asalin dalilin da yasa ta ke qin ta,dan dalilan da ta sani gani take kamar ba su bane, a wajen ta basu kai wanda za ai mata tsana haka ba, kuka take sosai, ta na nan tsayen ta wani jiri na d'iban ta, ta kuwa tafi luuu zata fadi, Rasheedah da ke saitin wajen kawai se ta buga tsaki ta kauce, ai kuwa ji ka ke 'tiimmm' Sakeenah ta fadi a qasa.
Zagaye Sakeenah Rasheedah ta yi zata shige toilet abun ta,tana gab da shiga toilet din ta ji muryar mahaifiyar su da ta je d'akko wa Rasheedahn hijabi saboda sallah, dan tin da ta shigo take kallon kayan sun yi tsiraici da yawa amma bata mata magana ba, da niyyar zata bata hijabi kalar kayanta ta dinga had'awa da shi, cikin matsanancin kuka ta ce,
"Yanzu ashe irin yarinyar dana haifa kenan ban sani ba? Ina murna ina da yara biyu kyawawa, ashe na yi kuskure, yarinya ta d'aya cekyakkyawa me kyan hali ce, d'ayar kuma baragurbi, yanzu da kan ki kike zayyana wa qanwar ki uwa d'aya uba d'aya wadannan abubuwan? Wace........"
Wani nishi da Sakeenaah ta ja ne ya yi sanadin rugawar Mama da gudu gare ta, tana danna qirjin ta, alamar dawowar su Abbah maman ta ji ta kuwa kwala masu kira a gigice, a firgice suka shigo dan sun ji kiran nata kamar da kuka a ciki, Adnan ne a gaba har yana tuntube da Hijab din da Mama ta kawo wa Rasheedahn, sauran qiris shi din ma ya fadi.
Yana ganin matar shi a kwance a qasa shame shame, ya yi saurin kallon Rasheedah wadda ta nuna ita fa yanayin da Sakeenah ke ciki ko a jikin ta, cikin ran ta da fari ta tsorata, amma daga baya da ta ga yanda hankalin kowa ya tattara ya koma Kan Sakeenaah cikin madaukakiyar damuwa da tashin hankali sai hakan ya qara sa ta jin tsanar Sakeenaah ta ninku a ran ta,wai akan ta ake wannan rawar duwais din, ji harda Abban su, kad'a ido sama ta yi ta ja gajeren tsaki zata shige, Mama ta yi wani kukan kura ta janyo ta, daidai lokacin Abba ya shafawa Sakeenaah ruwa ta dawo normal, kifa mata kyawawan maruka mama ta dingayi ta na kuka, tare da fad'in baqaqen maganganu akan Rasheedahn,ko gezau Rasheedah bata yi ba zuciyar ta ta bushe ta dake da qiyayya da hassadar qanwar ta, Adnan ne ya riqe hannun Mama yana bata hakuri,
"Ka barni kan ta kashen yarinya mai yi mana biyayya da son mu da kulawa da lamarin mu gwanda ni na kashe ta, ban tab'a sanin haka Rasheedah ki ke da baqar zuciya ba, a zato na d'an kishin nan ne dake tsakanin 'yan uwa Saqo da saqo,ashe ke kina nan kin gina zuciyar ki akan mummunar qiyayya me zafi haka,mu kuwa me za mu yi da mai halayya irin taki? Ta ina na gaza a baku tarbiyya ni da mahaifin ku har kk deb'o wannan mummunan halayen bamu sani ba? Wannan wacce irin yarinya na haifa? anya bata da mugayen aljanu a tattare da ita kuwa?"
Abba ne ya zaunar da Maman a gefen bakin gadon d'akin, ya rungume ta ya na lallashin ta,
"Zubar hawayen ki a gurin ta masifa ne,zai sa ta qara lalacewa ne kawai, ki kwantar da hankalin ki da izinin Allah zata so Sakeenaah, kwatankwacin yanda iyaye za su so 'ya'yan su, ki basu lokaci, ke Kuma Rasheedah mu na Mai baki hakuri akan dikkan abinda ki ke ganin mun aikata maki ba daidai ba da ya ja ki ka tsani qanwar ki da ku ka fito ciki d'aya har haka"
Sakeenaah da ta jingina da pillow, a hankali tace zata sha ruwa, ruwan Adnan ya bata, yana mata kallon so,qauna da tausayawa, kallon ta ya ci gaba da yi ya ga yanda take kallon Rasheedah, takaici duk ya ishe shi, a hankali ta Maida kallon ta zuwa ga Adnan ta ga yanda ya damu akan ta, shi Kuma bin ta yake da kallo tare da maganar zuci,
'Baki da wayo my love har yanzu ya Kamata ki farka ki gane wannan ba zata taba son ki ba,'
A hankali Sakeenah ta furta
" Rasheedah kiyi hakuri da dikkan abinda na miki, wanda na sani da wanda ban sani ba, ko menene shi ki wa girman Allah ki yafe min, rayuwar nan ta duniya ba komai cikin ta face rud'in shaid'an , ni ina son ki,ina son ki, ina son ki,ke yayata ce, bayan iyayen mu banda kowa bayan ke, sai mijina, in baki so na ya zanyi?"
Kuka ne yaci qarfin ta, haushin ta yanzu Adnan ya ke ji, na farko kenan ma baya list din masoyan ta na fari wannan banzar da bata son ta ta ma fishi matsayi, sannan ga shi sai wahala yake da ita amma ko kallo bai ishe ta ba, tari ne ya sarqe ta ta kasa qarasa maganganun da take yi,tsaki Rasheedah ta yi ta d'au gyalen ta da jakar ta ta bar dakin, parlor ta je ta tadda yaran ta duk sunyi bacci, goya Sulaiman ta yi ta dau Yousuf a hannu, ta yi waje, ranta baqiqqirin, da kulawar da ake bawa Sakeenaah, bayan ta manta itace silar koma me ya sami Sakeenahn har ake bata kulawar.
Abun nasu ya zama wata iriyar jarabawa, Allah ya jarabci Sakeenah da tsananin son yayar ta ta, ita Kuma Rasheedah na tsananin qin qanwar ta ta.
(Dama haka Kan faru, sanda Wani yake tsananin son Wani, to shi wannan da ake so sai a yi rashin sa'a lokacin yake tsananin qin Mai son nashi)
Mai adaidaita Sahu ta tsare ta hau ta yi gida,Su kuma suka fito da Sakeenaah dan kai ta asibiti, suna zuwa likitoci suka karb'e ta suka kwantar aka gwada Bp din ta ya hau sosai, sannan aka d'ebi jinin ta suka yi gwaje gwaje, matsalar hawan jinin ta suka hau dubawa dan shine yafi, a haka Mama, Abba,da Adnan, suka shiga jinyar Sakeenaa,har kusan kwana sha d'aya a asibiti, Sakeenah ta d'ashe ta yi haske sosai, kusan kullum cikin amai da zazzabi take,amma kullum idon ta rufe taqi budewa kome ake tana ji tana sane, amma bata son yin magana, tinanin tin da ta fara wayo, zuwa 'yammatancin su take, har ranar auren su, ko akwai abinda ta yi wa yayar ta mara kyau da ya ja mata mummunar qiyayyar nan? Amma ta rasa,dawowar Abba daga kasuwa kenan ya biyo, ya na tambayar jikin Sakeenah a wajen Mama da Adnan da tinda Sakeenah ta kwanta be je ko Ina ba, dik abinda ake da buqatar shi ko signing ko ganin Wani file d'in se dai a kawo masa nan ya yi a mayar, tattauna wa suke akan matsalar musamman jinin ta da ya qi daidaita sai su ka ga hawaye na zuba ta gefen idon ta, Adnan da Abba har suna rige2n zuwa gare ta,Adnan ya kama hannun ta ya ce,
"My love pls ki yi magana mana ki fad'i abinda ke ran ki ki cire damuwar ran ki ko zamu samu ki ji sauqi, nasan kina jinmu ba wanda yace ki tsani yayar ki, amma baki ganin sata arai har ki samu matsala haka babbar illa ce ga rayuwar mu? Kin sani in Wani abu ya same ki ba zan rayu ba, ke kad'ai nake da a duniyar nan, ki yi hakuri ko dan abinda ke cikin ki?"
Da sauri ta bud'e ido tana kallon shi, dan duk abinda su keyi tana ji amma meyasa bata ji zancen ciki a jikin ta ba? Gyada mata kai ya yi idon shi tab hawaye,
" Eh ciki, jiya likita ya tabbatar mana kina dauke da qaramin ciki"
Sunkuyawa ya yi daidai kunnen ta nima ko na kai nawa naji me zaice amma inaaa ya iya qusqus banji komai ba☹ murmushi ta saki ta rufe idon ta, sai kuma ta saki kukan farin ciki, da kyar suka lallashe ta ta yi shiru, murna a wajen ta ba a magana,banda hamdala ba abinda ta ke maimaitawa, tini damuwar da take ciki ta Kau ta maye gurbin damuwar da farin ciki, roqon shi ta yi daya d'aga ta ta je toilet, alwala ta yi tazo ta yi sallah raka'a biyu ta godewa Allah da ya amsa addu'ar ta a wannan lokacin.
Se da suka qara kwana biyu aka tabbatar da lafiyar ta sannan aka sallame su, gidan su suka wuce, Mama da Abba ma suka wuce nasu, cike da farin ciki.
Makaranta ba sai na fad'a maku irin lelen da Sakeenaa ke sha ba wajen Adnan kai har ma da Mama da Abba ba, kullum cikin shagwaba ta suke, komai tace tana so sai sun bata, kan kuce me Sakeenaah ta zama Masha Allah barakallah, ta yi 'yar qiba me kyau ta masu ciki, jikin ta kamar ba ita ba, ta yi haske akan baqin ta se kalar ta ta zama Mai d'aukan hankali da idanun Mai kallo, Adnan in yasata a gaba da kallo, har sai ta soma shagwabar kallon ya yi yawa. Wani abu dake qara burge Adnan kuma shine her demand of sex increases, duk a harkar cikin wannan bangaren ya fi burge shi, kusan kullum ba fashi sai anyi wataran har sau uku,kai wataran har hudu ma, ba qaramin morewa yake ba,ji yake kamar ta tabbata haka ko bayan haihuwa, ita kuma in an gama sai ta hau bashi hakuri tana kuka, akan tasan tana takura masa, amma ba yanda zata yi ne, ya yi hakuri data haihu zasu koma normal, kawai sai ya gyada kai, a ranshi ko yace ba amin ba Allah sa a dawwama a haka mu na morar juna.
Lokacin da cikin Sakeenaah ya kai wata bakwai, Adnan ya na yawan ganin ta tana rubuce2, in ya yi qoqarin gani,ta saka kukan shagwaba akan yana mata leqe, haka zai hakura ya je ya hau yin wani abun ya barta, a girman cikin da take da shi haka take ci gaba da dukkan ayyukan da muka san ta da shi, sai dai kawai wannan karon akwai sauyi, in kasala ta rufe ta sai ta hakura sai ta ji normal sannan ta tashi ta yi ayyukan ta.
Cikin ta na wata takwas ta shirya ba da sanin Adnan ba ta tafi gidan Rasheedah.......
*Kai ni ku ban madoki na tsane Sakeenaar nan, me ya kaita kuma zuwa gidan Rasheedah, mara zuciya kawai😡*[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 11:
Tana zuwa ta yi parking nesa da gidan kadan, daga inda take ta na ganin duk Wani Mai shige da fice a layin,ta yi wajen minti ashirin a zaune a motar da ta kunna wa karatun qur'ani gefen ta ruwan sha ne a 'yar robar ta me kyau da take saka abun sha a duk sanda zata fita saboda yawan Shan ruwan da take,hango shi ta yi ya dawo daga aiki, tin daga nesan ta gane shi, da sauri ta bud'e motar ta ta fita cikin d'aga murya yanda zai ji ta ta kira sunan shi, jinkirtawa ya yi da tafiyar da yake ya waiwaya,Murmushi ya saki dan kuwa ya gane ta,ita ce macen da ya sani ta na saka niqab da dogon hijab ko kuma doguwar riga da niqab d'in, matsawa ya yi fuskar shi na sake fad'ad'a murmushin, can Kuma ya koma yaqe dan ya tuna abubuwan da Rasheedah ta yi mata a baya, ya so k'warai ya je har gida ya bada hakuri Rasheedah ta dinga ci masa mutunci ta na Kiran shi da d'an kalan dangi da sauran munanan sunaye dan haka se ya fita a maganar ya dinga musu addu'ar Allah ya daidaita tsakanin su,amma fa tun lokacin Auwal ke jin kunyar Sakeenaah ko da kuwa sunan ta aka ambata Kuma duk tsahon lokacin nan basu hadu ba, sai gashi yau ta bashi mamaki da zuwan ta,
" A'a Sakeenaah ke ce yau a unguwar tamu, ya baki qarasa ciki ba? Bismillah mu shiga ciki mana"
Murmushi ta yi ta gyara tsaiwar ta sosai, yanda cikin ta zai fito, aiko yana gani ya fadada fara'ar shi tare da d'aga hannayen shi sama ya na godewa Allah, tsananin farin cikin da ta gani a tattare da shi ya sa ta kwad'ayin dama ace Rasheedah ce haka da sauri ta kawar da tinanin nan dan yanzu ta na qoqarin kiyaye duk wani abu da zai tada mata da ciwon ta, Cike da murna Auwal ya ce,
"Kaiii masha Allah, Allah maji roqon bayin shi, Allah ya raba ku lafiya ya sa ki haifi mai albarka, lallai in mace ce na yi wa Yousuf kamu tin yanzu, kuma ina fatan ta yo gadon halayen ki Sakeenah na ji dad'i na yi farin ciki da ganin ki d'auke da ciki, dole ne na yi wa waccan mara hankalin albishir,"
kwallace ce ta taru mata a ido ta qara murmusawa sannan ta fara magana,
" Yah Auwal, nazo nan ba dan komai ba sai dan na roqe ka wata alfarma, guda d'aya zuwa biyu, ka san dai dik abinda ke faruwa tsakanina da yayata, to wannan dalilan dake tsakanin mu ne yasa nake son dan Allah kar ka Sanar da ita Ina d'auke da ciki a yanzu, sannan Ina roqon alfarma inna haihu lafiya 'yata ko d'ana zai dawo hannun ku da zama, dan yanda nake jina Ina jin kamar ba zan rayu da abin da zan haifa ba, ina son yaro ko yarinyar su dawo hannun Rasheedah,sannan alfarma ta biyu kome zata yanke akan abinda na haifa karka musa mata, kome zata ma abinda na haifa karka mata fada,tsakanin ku ya zama nasiha, domin so nake ko ta wanne hali Yayata ta so ni da abinda na haifa, sannan ta gane mene ne kalmar so na 'yan uwantaka, so nake ta san mahimmancin zumunci, na roqe ka ko wanne hali abinda na haifa zai shiga indai ba sabon Allah bane ta sanadin yayata kar ka rabu da ita, kar ka tsawatar mata na bata abinda na haifa halak malak,ban San me yasa ba jiki na na bani rayuwa ta ba zata Yi tsaho ba Yah Auwal, dan Allah ka riqe min wannan wasiyya ko bayan ba raina,in Kuma Allah ya sa na haihu lafiya da raina da rayuwa ta, Ina so in abinda na haifa mace ce a qulla zumunci mu had'a su aure, Ina fatan zaka min wannan alfarmar"
Kuka ne ya ci qarfin ta ta kifa kai a jikin motar ta tana kuka, shi ma kukan yake sharb'a a daidai wannan lokacin,yana jinjina irin soyayyar da Sakeenaah kewa Rasheedah, inama Rasheedah zata fahimci haka,
"Kar ki damu na d'aukar maki wannan alqawarin komai zai faru ba zan rabu da Rasheedah ba, kuma ba zan hana ta komai akan riqon da zata yi wa abinda kk haifa ba, sai dai dole ko taso ko bata so ba zan saka abinda kk haifa a makaranta, sannan batun mutuwa da kk danganta kan ki da ita ba lallai bane, Allah ne kawai yasan gawar fari,Allah ya raba ku lafiya ya bamu Mai albarka"
kad'a kai ta yi tana murmushi,ta masa godiya sosai sannan suka yi sallama, tana qoqarin tafiya ne ya ce mata,
" Af na manta ban sanar dake ba, ai ko itama Rasheedan tana can dauke da cikin ta shiga watan haihuwar ta dai yanzu amma bata yi nisa ba,"
Murna ta yi sosai da Jin hakan, sannan ta yi mata fatan ta haihu lafiya, suka sake yin sallama ta ja motar ta ta nufi asibiti, wajen likitan ta taje aka auna jinin ta, nan suka hau mata fada sosai,akan tana saka tinani da damuwa a ranta sosai, ko meye matsalar ta ya kamata ta aje ta a gefe ta samu lafiya,in ta haihu qalaou sai ta yi facing damuwar ta ta warware ta, consultant guda ce ta samu ta yi ta bata shawarwari tare da kwantar mata da hankali ta nuna mata yanda zata kula da Kan ta da abinda ke cikin ta, aiko ta sake samun sauqin damuwar ta sosai, haka ta fito ta kama hanyar gida, a hanya ta na tafe ta na tunani, ita ta san ta rage damuwa sosai, tinda a baya bata da aiki sai kuka da baqin cikin halin da suke ciki ita da yayar ta, amma yanzu se ta wuni ma bata yi tunanin ta ba, ta dai rasa me ke yawan sanya ta fad'uwar gaba da Jin tashin hankali, wannan abun da take ji shi ke sanya ta ganin kamar ba zata rayu da abinda ke cikin ta ba, hakan Kuma ke qara jefa ta cikin damuwa.
Mai gadi ne ya wangale mata gate ta shiga, masu aikin gidan na ta gaishe ta ta na amsa wa, Shamsiyya ce ta bud'e mata qofa ita Kuma ta yi sallama ta shiga gidan,a parlourn ta ci burki Dan ganin Adnan a tsaye ya na ta safa da marwa,yana ganin ta ya aje robar ruwan dake hannun shi ya kamata ta zauna, da alamar gajiya a tattare da ita ta furta,
"Mine ka yi hakuri na fita ban sanar da Kai zani asibiti ba, na ji bana d'an Jin dad'in jiki na ne shi yasa na tafi dan na ga likita"
"Haba My love ai da kin min ko da text message ne in na gani shikenan ba zan shiga halin damuwa da tashin hankali irin haka ba, gaba daya kin sani damuwa da fargaba, hankalina ya tashi,na zaci Wani abu ne ya same ki"
" kwantar da hankalin ka Mine gani na dawo ai ko? Jiki na ne ban gane masa ba shine na tafi na San in na Sanar da Kai kana Iya barin aikin ka ka taho bayan zan iya Kai kaina, ai hakan be Kamata ba ko? Alhamdulillah zuwa na ya yi amfani dan kuwa na samu shawarwari masu mahimmanci daga wajen likita, na samu kwarin guiwa da kwanciyar hankalin da nake buqata, amma har yanzu Ina da damuwata guda d'aya,"
Cikin sauri ya ce,
"Meye damuwar ki?"
Murmushi ta yi mai ciwo,
"Damuwa ta ka riga ka santa ka qi kawai ka karb'e ta ne, bama ka so na dinga fad'a, kuma ina kyautata zaton in ban samu wannan alfarmar daga wajen ka ba ko mutuwa na yi ruhina ba zai samu nutsuwa ba,"
Kuka ta saka sosai harda shessheqa,
"Ki daina kuka mana, amma kin san abinda kk nema a wajena mai wahala ne, kar ki manta fa nima banda kowa makusaci a yanzu sai ku, ya zan iya hakuri ina kallon abun da na san nawa ne zai wulaqanta kuma na kasa tab'uka komai, dan na yi imani da Allah zuri'ar ki ta shiga hannun wannan muguwar yarinyar ba za su ji da dad'i ba, sannan wa ya fad'a maki ma zata yarda ta riqe maki yaro ko yarinya? Kuma wama ya Sanar da ke ba Zaki rayu da abinda Zaki haifa ba? Kar ki manta fa ni da ke abu d'aya ne, ba ke kad'ai ke so na ba, nima Ina son ki, to ta ya ya Zaki dinga yin maganganun da za su kassara zuciya ta, ko so ki ke Nima na kamu da Wani ciwon?"
Cikin kuka ta ke kad'a Kai alamar Ah ah, rungume ta ya yi ya na shafa bayan ta a hankali ya ci gaba da fad'in,
"Haka aka ce maki daga haihuwa d'aya mutum zai mutu ko me? ko kuwa mutane nawa ne masu hawan jini kuma sike haihuwa su rayu? Ni ki daina ma wannan maganar dan Allah kina sawa ina shiga damuwa sosai,"
Share hawayen ta tayi sannan ta qoqarta tashi zaune da kyau ta shige daki, sai magana yake mata bata kula shi ba,ai kuwa hankalin shi ya tashi, ko dai da gaske mutuwa zata yi ta bar shi? komawa ya yi ya zauna ya fasa bin ta, hannun shi biyu ya Sanya ya tallabe fuskar shi ya saki kuka mai d'aci, zuciyar shi ya ji ta matse masa waje d'aya ta na quna,
" Ya Allah kar ka raba ni da mata ta, ina son ta, Allah ka sauke ta lafiya da abinda ke cikin ta Allah ka fini son ta Allah ka mana zab'in alkhairi,"
Abinci ta fito zata deb'o ta Jiyo kukan shi da addu'ar shi, sai ta koma da baya ta jingina da gini,itama kukan take,daga baya ta share hawayen ta ta fita, kitchen ta wuce ta fara diban abinci,zuwa ya yi ta bayan ta ya kwantar da kan shi a bayan ta cikin matacciyar muryar da ba a son yin magana da ita ya ce,
"Na amince da buqatar ki ki daina saka damuwa a ranki, Allah ya sauke ki lafiya"
Murmushi ta yi ta juyo ta hau sumbatar shi, sai da ta dangana shi da jikin gas sannan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 21