yu ba,"
Cike da rashin mutunci na ba sani ba sabo take maganar, cikin kuka mai qarfi Sakeenaa ta dire yaron ta fita da gudun ta, tana kuka, Adnan ji ya yi kamar ya shaqe Rasheedah, wani mugun kallo ya watsa mata ya matsa daf da ita ya na nuna ta da yatsan shi manuni ya ce,
"Wai ke wace iriyar mahaukaciyar mata ce wadda bata San menene zumunci ba, bata San mene ne so da qauna irin ta 'yan uwantaka ba? Anya Rasheedah ki na da zuciya a qirjin ki kuwa? To ga d'an naki nan an bar maki Dan Allah ki jiqa shi ki shanye shi idan ana sha wawuyar banza kawai, kuma in Allah ya yarda in dai ni ne mijin Sakeenaah ba zaki qara ganin ta taka qafar ta ba a gidan ku, sai dai in kin canja hali, Allah ya cece ki na ga qafar ki Kuma a gidan masu halin ki ga yanda zan maida ki, shashasha kawai,"
Cike da fushi ya fice, Auwal kuwa daskarewa ya yi a wajen , kunya, tsoron halin matar shi, da kuma tausayin Sakeenaah ne danqare a zuciyar shi, kasa ce mata komai ya yi, dan yana ganin in dai ya yi magana ta mai shirme sai ya kirb'e ta kamar kubewa a turmi, d'aukan Yousuf ya yi da yake ta tsala kuka, ya zaro alawa a aljihun shi ya b'are masa ya bashi, da qin karb'a ya yi da fari, amma da wayo da dabara ya hakura ya karb'a ya yi shiru, nan da nan bacci ya dauke shi, a haka ya dauke shi suka je tare ya rufe gidan sannan ya wanke masa hannu da baki, daya ci tuwo dazun, ya kai shi ya kwantar da shi a shimfidar shi, ya dakko Sulaiman ma ya kwantar, sannan shima ya bi lafiyar gadon su ya yi masu addu'a dika ya fara bacci, gimbiyar na can tana d'aga wannan ta aje, ga murnar samun kaya, ga baqin cikin sanin Daga inda kayan suka fito danqare a ranta, wannan wai tsarabar su ce daga qanwar ta, Allah kada'i yasan ita wanne irin kaya ta lodowa kan ta, oh duniya, taya za a ce qanwarta ita ke da arziqi sai dai ta na sammata, amma ita tana zaune hmmm Allah ya kyauta,
Hassada kenan, kana nuna wa Allah be Iya rabo ba, subhanallah, to Duk me wannan halin ya shirya shiga tashin hankali duniya da lahira, hassada yanzu ta yi wa mutane yawa da katutu a zuciya, d'an uwa na yi wa d'an uwan shi hassada, miji ko mata na wa juna hassada, maqoci da maqoci hassada, yanzu a social media ma da baka tab'a ganin mutum ba, da ka ga Wani ci gaba ya same shi se ka dau hassada ka sa a ran ka akan shi, zaman lafiyan da wata ke yi da mijin ta ko da iyayen ta ko da maqotan ta ya zama abun hassada a wajen wasu, kar muna mantawa dai hassada na tattare da babban mummunan sakamako Allah ya mana tsari da ciwon hassada.
Gama surutan ta ta yi ta miqe ta shige d'akin nasu bayan ta rufe akwatin, tana shiga ta hau cire kayan ta ta kwanta kusa da Auwal, duk sha'awar da ya ke ji, kan ya shigo gidan, yanzu ta kau, me zai da ita yanzu? Shi tsoro ma take bashi yanzu, in dai zata iya nunawa qanwar ta qiyayya haka to shi waye? Shafa shi ta somayi, ya rintse ido, nan da nan jikin shi ya fara karbar saqonnin ta,amma saboda kafiya da dauriya, ya tura ta,
"Dalla malama meye haka? Kar ki ban haushi kici dan banzan duka da daren nan,ki ja zumman jikin ki ki yi bacci, sai da safe, ke kin ma San me? Gaba d'aya kin fara fita a raina Rasheedah, ban San kalar zuciyar da ki ke da ita ba,qanwar ki uwa d'aya uba d'aya ki ke wa irin wannan qiyayyar? Bayan yarinyar nan bata da burin da ya wuce na ta ga ta kyautata maki da iyalan ki, amma ke kullum burin ki ki nuna mata hassada qiyayya da kyashin da kk ke yi mata a fili, kar fa ki manta ko iyayen da suka haife ta bata je ta gani ba ta zo nan, dik da sun fara zuwa ne dan nan ne a hanya amma da ta so da can gidan ku ta wuce, ashe rabon ki b'ata mata rai da farin cikin ta ke cikin ran ne,tirrr da halin ki Rasheedah, magani na kenan na bin auren kyau, kyan ki ya rud'e ni na aure ki, kyan ki ne ya sa ni yi miki qarya har se da na mallake ki, ashe kyan d'an maciji ne, gashi nan ki na ta sarar kowa a hankali, Allah ya shirye ki, ki janye jikin ki kafin na lakad'a miki na jaki a Daren nan na fad'a miki"
Ya na magana ya na nuna ta da yatsa, kafin ya juya mata baya, amma da yake yar duniya ce, ta san Auwal baya tab'a wuce tayin jikin ta komai fushin da ya yi, ita ce ma ke hana shi Kan ta lokuta da dama, se ta ce se ya siyo mata kaza ko tsire ko balangu kamar tsohuwar mayya, in Yana da shi ya siyo, in babu ya banqare ta kamar kazar ya gama abinda zai da ita, daga baya ya lallashe ta su yi baccin su dan haka ta San lagon shi sosai,yau Kuma gashi itan ma a buqace take da shi, binshi tai ta zira hannin ta a jikin shi tana shafa sensitive areas din shi, tare da bashi hakuri da 'yan surutan soyayya a kunne, tini ya juyo,........
Sai da sika lafa tana kwance a qirjin shi yana wasa da gashin kan ta yace,
"Dan Allah yau Ina son sanin menene dalilin ki na nuna wa qanwar ki uwa ɗaya uba ɗaya qiyayya haka?,"
Numfasawa ta yi ta gyara kwanciyar ta sannan tace,
"Na fara tsanar Sakeenaa ne tin muna yara, ba dan komai ba sai dan soyayyar da iyayen mu ke bata ya bambanta da nawa, suna nuna banbanci kwarai ainun a tsakanin mu, ni ce babba amma kamar Sakeenah ce gaba da ni, saboda yanda ake d'aukan girman da qanqantar dik a bata, in bata da lafiya gaba d'ayan su yi suke kamar sune ba lafiyar, amma in na kwanta ciwo ba Mai zuwa inda nake se dai ana min sannu Daga nesa,a ban magani a min allurai shikenan ba wata kulawa da nuna tausayawa, kafin a sai min Abu sau d'aya an sai mata sau biyar, komai suke da shi za ka ji sunce na Sakeenaa ne, ko ka ji su na cewa sakeenaa ta fiki hankali,Sakeenaa ta fiki ilimi, Sakeenaa ta fiki tausayi, Sakeenaa ta fiki kyau, Sakeenaa Sakeenaa Sakeenaa, sunan ta ya min yawa a kaina, sunan ta ya cika zuciyata da baqin ciki, duk qoqarina iyayena da malamai na dama kowa baya gani sai na Sakeenaa, akan me? Ni ba halitta bace,ko ba su suka haifen ba,gashi saboda mugun bakin da suke min kullum akan ta fini komai na b'ige da auren ka a matsayin talaka,ba wai kai na tsana ba ko nake dana sanin aure,A'a ina jin haushin babun da kk ciki ainun, ita tana cikin halin yalwa, na baka labarinnan ne dan kasan dalilin qiyayya ta akan ta, ba dan ka ban shawara ko ka qara min abinda zai sa na ninka tsanar ta a zuciya ta ba, dan haka yanda ka ji kai shiru da bakin ka,"
kad'a kaii kawai Auwal ya yi yana mamakin wannan wauta ta Rasheedah,duk da yasan laifin ya samo asali daga mahaifan su ne, domin duk son da kk wa d'a a cikin yaran ka ba a son kana yawan nuna wa, ka danne kowa ya zaci shi kafi so a yaran ka, ana so kowanne yaro ya ji cewa an fi son shi sama da d'an uwan shi har se da Kan su sun gane cewar ashe fa Mama da Baba Suna son kowannen mu equally ba banbanci, amma ku a ranku Kun San wa ku ka fi so,da Kan su zasu fahimci cewar ashe mahaifan mu na son mu ne gaba daya ba wanda suka ware? To sai soyayar ku ta mamaye zuqatan su, sannan kuma su samu had'in kai mai girma,( Allah ka sakawa iyayena da alkairi da dik iyayen da suka zamanto masu adalci a wajen yaran su, Allah ka yafe wa iyayen da suka nuna wa yaran su banbanci Ameen). Juyawa ya yi ya kwanta, ita ma ta kwanta,amma idon ta biyu, ko wanka basu yi tinanin zuwa suyi ba, kullum sai a suba suke yin tsarki su.
( wanda ba daidai bane hakan, ba a ce hakan haramun bane amma rashin dacewa ne,ka kwana cikin rashin tsarki, akwai mugayen da in kai me riqon ibada ne sun rasa hanyar cutar ka to da wannan damar zasu cuce ka, sannan baka San yaushe ne lokacin mutuwar ka ba, ai ko ba komai da dad'i a same ka cikin tsarki,dan haka ko haila mace keyi ake son ta na yawaita tasbihi, da karanta qur'ani kai koda iya qulhuwallahu ahad ta haddace tai ta maimaita wa)
Bangaren su Sakeenah kuwa Adnan
na fita waje ya tadda ta jikin motar su ta kifa kan ta sai kuka take, bud'ewa ya yi ya saka ta ciki, ya ja suka wuce gida, suna isa gidan motar na tsayawa ta bude ta faɗa gidan da gudu tana kuka, d'akin ta ta wuce ta rufe qofar ta kwanta a gado tai ta kuka, tana dana sanin zuwa a ranar, biyo ta ya yi ya murda qofar ya ji ta a rufe, bugawa ya hau yi, yana mata magiyar ta bud'e, amma sam taqi, bata taba fushi haka ba, Kuma bai tab'a ganin b'acin ranta irin na yau ba, ta bangaren ta kuwa tinani take, me taiwa yayarta data tsane ta haka,tin tasowar su, ba ta san soyayyar 'yar uwar ta ba, sai dai ta ga wasu suna son junan su abun na bata sha'awa da burgewa amma banda su, in ta mata abun burgewa sai ya dawo na rashin mutunci da cin fuska, me ya yi zafi haka? Kukan ta ne ya qaru nan da nan zazzabi ya rufe ta dama ga gajiyar hanya bata ko bari ta huta ba wai ita me 'yar uwa ta tafi wajen ta, se abun ya taru ya saukar mata da ciwo biyu, quncin zuciya da zazzafan zazzabi, ta na cikin kukan ne ta ji qarar abu ya fashe se Kuma ta jiyo Adnan yayi qara,ai da gudu ta sauka daga gadon ta na ganin jiri ta yi waje, shi kuma ya yi haka ne dan ta fito tinda ya saka key din shi ya ji akwai Wani a jikin qofar bazata bud'u ba kenan,se kawai ya je ya dakko plate ya sake a qasa ya tarwatse sannan ya ya yi qara, ya dawo bakin qofar ya tsaya, aiko budewar nan da za ta yi suka yi karo, a gigice ta fito tana kwada masa kira,cikin gaggawa ya rungume ta ya maida ita d'akin ya na mata dariya tare da fad'in,
"Wa na kamaaa, yau se kin karb'i hukunci mai girma a waje na, hukuncin rufen qofa da kuma kukan da ki ka yi kika wahal min da jikin ki ji jikin ki yanda ya yi zafi fa, Dan Allah ki kwantar da hankalin ki kar ki jawo mana Wani ciwon"
Bata San sanda ta sake barkewa da sabon kuka ba sakamakon tinawa da abinda ya faru a gidan Rasheedah da ta yi,bai hana ta kukan ba,sai kawai ya rungume ta yana buga bayan ta a hankali, sai da ta yi ya ishe ta sannan ta fara ajiyar zuciya dik jikin ta ya saki, ga Wani mugun zazzafan zazzabi da ke nuqurqusar ta,ji ya yi nauyin ta ya qaru jikin ta ya sake, yana dubawa yaga ashebacci ne ya d'auke ta, juyar da ita ya yi ya fara zame mata kayan ta hankali, cikin nutsuwa ya qarasa cire mata kayan jikin nata dika, dubawa ya yi yaga pad din ta ta baci, ya dakko wani pant din ya sauya mata wata,ya zame na jikin ta ya aje gefe ya sa mata wanda ya haɗa, daukan wancan ya yi ya kai toilete, ya cire pad din ya nannade ya sa a dustbin,sannan ya wanke mata pant ya shanya ya d'ebi ruwa me rangwamen sanyi da qaramin towel ya je ya goge mata jikin ta ko zai samu zafin ya ragu, bayan ya gama ya Sanya mata sassauqar rigar bacci, ya koma bathroom din ya yi wanka ya je ya kwanta a jikin ta,(namiji d'an gaske Kuma JARUMI ne kawai zai iya kyautata wa matar shi haka) ji ya yi jikin ya rage zafin da ya yi sosai, tsananin tausayin yanda take son yayar ta amma bata samu hakan ba in return yake, ji ya yi cikin bacci tana magana, daya kasa kunne ya ji tana,
"Me na yi miki ne da baki sona? Ni ina son ki Rasheedah ta"
Tab'a ta ya yi dan ya farkar da ita Daga mafarkin da take, ta na Jin saukar hannun shi a jikin ta ta juya gaba d'ayan ta ta qanqame shi, ji ta yi zuciyar ta na tashi,a hankali ta fara bud'e ido can Kuma ta miqe da gudu ta yi toilet, tana sheqa amai bin bayan ta ya yi shima ya riqe ta, jikin ta zafi kamar wuta, amai take tana qarawa,tana gamawa ta zame a wajen za ta kwanta ya yi maza ya riqe ta, ta kwanta jikin shi, sai ta saka kuka,
"Sannu my love, ko zamu je asibiti ne?"
Da sauri ta girgiza masa Kai bata so su je asibiti,
"To sannu bari mu bari gari ya waye se mu je ko?"
'Daga masa kai ta yi ya kama ta suka koma d'akin ya kwantar da ita shi Kuma ya koma ya gyara wajen da ta yi aman.
Washe gari......
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Page 4:
Da sauri ta girgiza Kan ta, tare da tashi ta zauna da kyau a fili ta ke fad'in,
" kaiii inaa da kunya na je ina cewa Mama ta nema min magani na haihu, kaii ba zan iya ba ma, to ya zata kalle ni ma? Ai se ta ce bani da kunya ma"
Tana nan zune har qarfe hudu na rana ta buga ga kiraye kirayen sallar la'asar nan dik ya karad'e ko Ina, gani ta yi zaman ba zai yi mata maganin komai ba ga lokacin sallah ya yi kawai se ta fad'a bathroom ta dauro alwala ta fito ta zira doguwar riga da hijabi ta tada sallah, ta dade tana addu'ar neman gafarar Allah, da yiwa mijin ta da iyayen ta addu'a sannan taiwa dikkan musulmi addu'a kafin ta yi wa kan ta ta neman haihuwa me albarka ta dad'e sosai cikin sujjadar ta ta na maimaita addu'ar ta, sannan ta d'ago tai tahiya ta yi sallama, tana idarwa ta faɗa kitchen ta haɗa masu abinci dan qarfe shida Adnan ke dawowa, tana girki tana qara gyara gidan, ta je toilet din shi ta qara wankewa, ta fidda masa kayan da zai saka in ya dawo, sannan ta fito,bayan ta kammala girkin ne da gyare gyaren ta koma d'akin ta ta cire kayan ta ta d'aura towel ta shige bathroom dan yin wanka, had'a ruwan wankan ta yi cikin kwamin wanka ta zuba dik wasu abubuwa da take amfani da su wajen wanka, ta d'aga qafarta kenan zata shiga ta ji motsi alamar Adnan ya dawo kenan,Murmushi ta yi na farin cikin dawowar mijin nata ta qarasa shiga, kafin ta zauna ya bud'e qofar ya shiga, da sauri ta zauna ta na dariya, dan Sakeenah mace ce Mai kunya,har yanzu bata Iya bari Adnan ya gan ta ba kaya, se dai ta na saka qananan kayan da za a ce da su da babu dik d'aya ne, to ta fi son haka akan ta zauna ya gan ta ba komai a jikin ta, Murmushi ya yi Shima ya qarasa shiga bathroom din ya hau cire riga, se ni Kuma Hamidatuwa na jaaawo musu gambu na koma Ina jiran su a parlour.
Ina zaune na ji dariyar su tare da maganar Sakeenah ta na fad'in,
" Zaka fara ko? ko wanne kyau na yi a hakan, bayan ka dawo da wuri, ni da na so se na tsara kwalliya irin ta 'yan gayu se ka dawo"
"Tabb ashe kin shirya sumar da bawan Allah marayan Allah se Kuma Allah ya dube ni ya dawo da ni akan Kari, Sakeenah ni Adnan zan iya rantsuwa da Allah ban tab'a ganin macen da ta min kyau Kuma take min kyau a kowanne yanayi take ba sama da ke, ko kin yi wanka, ko baki wanka ba ke Mai kyau ce, ki dinga godewa Allah domin kuwa se a tara mata dubu kafin a samu irin ki goma"
Idan Adnan na kod'a kyan ta se ta dinga Jin ta kamar ta fi kowacce mace a dik duniya kyau da kyakkyawan hali, saboda ba ya barin wata kafa ta jikin ta ko ta halayyar ta ba tare da ya yaba ba,
" hmmm na gode" shine kawai abinda ta Iya furtawa ta na Wani tsadadden murmushin da ta San ya na sake rikita shi, su na cin abinci a saman dinning ma Adnan be shiru ba, ci gaba ya yi da ziga ta da yaba dad'in girkin da had'uwar shi,
"Mine ka dena sa wa Ina Jin kaina kamar zai fashe dan girma, wannan irin yabo haka? Ai dik yanda na zama a gidannan Kai ma ka na da babban kaso a Kan hakan, saboda mace na zama ta kirki ne a wasu lokutan gwargwadon irin adalci da kulawar mijin ta a gare ta, kenan ka ga Kai ya fi cancanta a yi wa yabon da ka ke min"
"Ba Zaki gane matsayin da ki ke da shi a zuciya ta ba ne, ke dai Allah ya qara min lafiya da arziqi na ci gaba da Baki kulawa kamar sarauniya "
"Ameeen, Ina son ka mijin Sakeenah,"
"Ina son ki matar Adnan"
Murmushi ta yi kafin su miqe Daga saman dinning din su yi masauki a kujera Mai cin mutum biyu, kunna TV ya yi ya Kai NTA, kwantawa ta yi a jikin shi ta na shafa qirjin shi sannan ta ce,
"Yauwaa my love dan Allah bana muje hajji mana, kaga sai mu samu mu yi ibada kuma mu yi addu'ar da muke da buqata akai ko"
Lakace hancin ta ya yi sannan ya sumbaci tsinin hancin nata ya ce,
" kamar kin karanci zuciya ta,anya baki min leqen asiri a zuciya ta ba?wannan na cikin tsari na a shekarar nan inshaa Allahu zamu koma hajji ni, ke, Abba da Mama ma duk zamu da su, dan ba zamu tafi ba muje da iyayen mu ba ko,"
Wani irin dad'i ne ya kama ta ta miqe ta kwanta rubda ciki a kan shi, tana facing din shi tare da rungume shi sosai, shi Kuma sai dariya yake fitarwa a hankali ba abinda ke bashi farin ciki sama da ya ga Sakeenah na farin ciki a rayuwa, kallon shi ta ke cike da tsananin so da qaunar shi da suka ninku a zuciyar ta, d'an qaramin leben ta na qasa ta ciza a hankali cikin kashe murya da kashe Ido ta ce,
"Bani da bakin da zan Maka godiya mine sai dai na ce Allah ya jiqan iyayen mu da suka gabata ya kyautata makwancin su ya sa su yi alfahari da samun ka a matsayin d'a na gari Ameen"
"Dama ai ba godiya nake so ba, Dan nima iyaye na ne, addu'ar ki kawai nake buqata Dan kuwa addu'ar ki a gare ni haske ce, Kuma alkhairi ce, Dan tinda na had'u Dake alkhairai kala kala ke bibiyata wadannan addu'o'in naki na daga cikin abinda ke qara min ci gaba a rayuwa, kin ga kuwa ni ne ma zan maki godiya ko?"
Lips din shi ta kama da yatsan ta ta Dan ja, ta miqe ta gudu d'aki, da qarfi ya furta,
"Invitation aka bani in zo kenan? To Gani nan zuwa" da sauri ya bi ta d'akin suka rufe qofar abin su, Bai fito ba sai da aka kira magariba, ya wuce masallaci.
Sallah ta gabatar da azkar ta sake gyara abubuwan da suka b'ata, ta Dan watsa ruwa ta saka rigar baccin ta Mai kyau, ga tirarukan da ta Sanya masu sanyin qamshi, sai ta Dora hijabin ta ta na jiran a yi isha'i, bayan ta idar da sallar isha'in ne ta shiga kitchen ta sama masu fruit salad da chicken and potatoes salad sai Dan abun sha da ta had'a na abarba qarfe tara na dare ya shigo, ya na hamma,
"Wai kin San ana idar da sallar isha'i kawai se bacci ya dauke ni, maqocin mu ne da zai tafi ya tashen shine muka taho"
"Ai dole bacci ya dauke ka, ka wuni aiki, ka dawo ban barka ka huta ba, I am sorry mine"
Kamo ta ya yi ya na Murmushi ya ce,
"Ni fa da na gan ki da qaton hijabi haka na San akwai wata harkar a qasa, zo nan in gani ba wata I am sorry,"
Guduwa ta yi suka hau zagaye kujerun Suna dariya, da kyar ya kama ta suka zube a kujera su na dariya,
"Dan Allah zo mu je mu ci abinci yunwa nake ji, na San kaima yunwa ka ke ji"
Da kyar ya barta suka jera ya na riqe da qugun ta, sai da ya fara ja mata kujera ta zauna sannan ya zauna Shima, ta zuba musu abinci suka fara ci.
Bayan sun kammala a tare suka gyara waje Wanda suka rage suka saka a fridge ya taya ta wanke kwanukan, suka kashe kayan kallo suka wuce d'aki, ni dai ban bi su ba dan lamarin su Adnan in kana binbini se ka ji kunya.
Bayan ya tafi aiki da safe ita Kuma da hantsi ta shirya ta ja motar ta ta yi gidan su ta sanar da iyayen su game da tafiyar da Adnan ya ce za su yi zuwa Hajji, ba qaramin murna suka yi ba, cikin tsananin farin ciki Mama ta sa waya ta kira Rasheedah ta Sanar da ita abin farin cikin da ya same su dan ta taya su murna,wayyo Allah, Rasheedah ji ta yi kamar ta mutu dan baqin cikin daya kama ta, tana kashe wayar ta hau kuka, Auwal ne ya riqe ta yana tambayar waya mutu cikin tashin hankali, banza ta yi da shi sai da tai kukan ya ishe ta sannan tace,
"Wannan banzar yarinyar ce zata makka,da su Mama, zan so ace ni na fara kai su, ba ita ba, amma dubi yanzu sabida auren talaka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 21