shi ya ga qirjin ta da wanne Ido zata sake kallon shi?
" Kin ji da shi dai ki ta tsokana nan ki ka fi kauri dama ai, laifina ne ma da qaiqayin baki na na fada maki,"
Cikin tura baki tai shigewar ta bathroom d'in, wanka ta yi ta d'aura alwala sannan ta fito, ta shafa Vassilin din ta, da yar farar powdern ta, sai kwalli data zizara, ba qaramin kyau ta yi ba. Afarah ta gani itan
ma ta cire kayan ta ta sa wasu ba tare da ta yi wanka ba,cikin jimanta lamarin Atiyyaerh ta ce,
"Wai ke meyasa baki son wanka ne? Munje mun dawo daga makaranta, mun gama shan qura a hanya mun dawo ga zufa amma ke baki san ki qara wanka ba,"
"Ke ni banni da shegen son wankan nan irin naki kamar agwagwa ba zan iya ba,"
Ta rausaya jikin ta mai kama da na Ablaerh, jerawa suka yi suka fita parlour kamar wasu tagwaye, direct dakin Yousuf da Sulaiman suka nufa, Sulaiman na kwance yana bacci, Yousuf yana zaune alamar tinda ya baro dakin su Afrah yake zaune a wajen, ya yi zurfi a tinanin Atiyyaerh Afrah ta taba shi,
" Yah gamu mun zo a bamu tsarabar,"
Murmushi ya yi ya sauke idon shi kan Atiyyaerh, ita kuma ta yi saurin juya baya tare da sunkuyar da kan ta qasa,dariya suka saka mata baki d'ayan su, miqewa ya yi yana tambayar su ya jarabawar ta yi sauqi kuwa? Haka dai suka yi ta hirar yaushe gamo, ya dakko tsarabar kowa ya damqa mata, Ablaerh yaa bata wata doguwar riga ne mai kyau baqa da ratsin pink a jiki, sai Afrah itama diguwar riga ce da rastin red a jiki, sai tsallen murna suke kamar wasu yara, dakko chocolate ya yi da tarkacen sweets ya ba Ablaerh, dan ya matuqar saba mata da shan su a boye, in baya nan tai kwadayin su har kuka take, ba mai bata, cikin murna sosai ta zube gaban shi, tana godiya,a nan ta bud'e ta fara sha ta rufe ido tana taunawa, tana wani girgiza kai, ba Yousuf ba dake namiji,har Afrah sai da ta yaba da kyaun ta, a hankali ta bude idon ta ta ga suna kallon ta,ta miqe ta fita cike da jin kunya, Sulaiman ne ya farka shima sai murna da ganin dan uwan shi yake, haka suka ci gaba da hira bayan ya amshi nashi tsarabar.
Yauce rana mafi muni a wajen Atiyyaerh, ranar da ta yi kukan rashin uwa da uba , kukan maraici, kukan Ina zata Saka ran ta da abinda ke tinkarar rayuwar ta ta gode Allah,😭😭........
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*Yesterday was our 15 years wedding anniversary my beautiful fifulll please say a prayer to us... thank you.*
Page 22:
komawar Yousuf makaranta da kwana biyu kenan, su Atiyyaerh na zaune a Parlour su uku, Rasheedah, Atiyyaerh, da Afrah, yaran na ta hirar makaranta da Kuma qawayen su, Rasheedah na zaune ta na danna waya ta na kallon su lokaci zuwa lokaci, a dik sanda zata had'a Ido da Atiyyaerh sai ta zabga mata harara, ita kuwa ta d'auke Kan ta ta ci gaba da hirar ta, in ana sabawa da mugun abu to Atiyyaerh ta saba da na Rasheedah,buga gate da akai ne yasa su dika ukun da suka saurara da hirar da suke suka nutsu dan su ji waye, kallon Atiyyaerh Rasheeda ta yi, in an buga gida irin haka mazan basa nan dama ita take zuwa duba waye, miqewa ta yi ta dauki hijab din ta ta saka tai waje, tana budewa ta yi arba da qatuwar motar Hassan a waje, cike da murmushi yake kallon ta,
"Ashe lallai bugun zuciyata bai kasala ba wajen sanar dake zuwana,"
kad'a ido ta yi sama sannan ta isa gare shi, bayan ta yi masa sallama ta gaida shi tace,
"A gaskiya ni ban da abin fada maka kuma daya rage wa bakina Hassan, soyayya tsakanin mu ba mai yuwa bace, ka taimaka ka rabu dani, wai wa ma ya fada maka nan ne gidan mu?"
"Atiyyaerh ba zan iya rabuwa dake ba gaskiya,ina son ki sosai, duk da ni d'in ina fuskantar qalubale a gidan mu wajen neman auren ki da nake son shigowa, amma hakan ba zai hana ni na gwada sa'a ta ba,kuma dangane da tambayar ki na waya nuna min gidan ku, na biyo ki shekaran jiya da kuka raka yayan ku,"
Ajiyar zuciya Atiyyaerh ta sauke sannan ta bud'e baki za ta yi magana suka ji budewar gate da qarfi , tana juyawa ta yi Ido hud'u da Umman su, nan da nan ta rab'e gefe da niyyar ta shige gida, cikin fushi Rasheedah ta janyo ta baya,sannan ta ce,
"Ki jira na fad'i duk abinda nake so na fad'a a gaban ki Kan ki tafi, malam kalle ni nan, ni ce uwar ta, ba zamu baka auren ta ba, domin mun mata miji tin tini, in ma baka sani ba ka sani, kalli can, ka ga wancan gidan na kusa da mu?....."
Ta yi nuni da hanyar gidan su Ahmad ta ci gaba da magana,
"To a can gidan yaron yake,sunan shi Ahmad,tun Suna Yara suke soyayya kuma an yi magana gemu da gemu, iyayen shi sun kawo komai na aure,dama ana Jira ta kammala secondary school ne, Kuma alhamdulillah,da alama daga gidan mutunci ka fito dan haka kasan dai ba kyau neman aure akan aure ko? To ka tafi in da rabo sai kaga Allah ya kawo maka wata ta gari,"
Cikin tsananin daci da qunar rai Hassan ya kalli gidan su Ahmad, a ranshi yana jin haushin tsayawa Sanya da Wani bibiyar ta da ya dinga yi ba tare da ya d'au matakin neman auren ta ba,yau gashi wancan talakan ya riga shi, ko sallama bai masu ba yaja motar shi ya tafi, duk da ba son shi Atiyyaerh ke yi ba abun ba qaramin sosa zuciyar ta ya yi ba, ya za a ce wai yayar Mummyn ta ce zata mata wannan aikin, cikin kuka ta shige gida, tana zuwa zata shige daki ta ji Umman nasu ta daka mata tsawa da cewar,
"To uwar son maza, uwar jaye jaye, ke kenan baki da aiki sai jaye jayen maza ga Afrah nan ta kame Kan ta har yau ba Wanda ya biyo ta sai ke kin ballagazar da kan ki maza na faman binki dik inda ki ka shiga,yanzu gashi daga je ki duba waye shine kk tsaya sakin zance ko, to ki kwantar da hankalin ki in namiji ne sai kin gaji da shi, yanzu2 zan leqa gidan su Ahmad na yi ma Babar shi magana in da gaske suke to fito,"
Cike da tashin hankali Atiyyaerh ta kwasa da gudu ta tsugunna a gaban Rasheeda ta kama qafar ta cikin gunjin kuka ta ce,
" Ummana dan Allah ki yi hakuri, kar ki gurbatan rayuwa ta, zan shiga halin qunci fiye da kullum in aka ce Ahmad ne mijina, Umma ni na yarda ku barni na zauna ba aure har abada akan a hada ni aure da wancan jahilin ko islamiyya fa bai zuwa,"
"Iyyyeee lallai ne bari ki gani na ga alamar kin zaci wasa nake ko?"
Sama ta nufa a guje ta Sako hijab d'in ta, zata fita, Afrah da Atiyyaerh suna kuka suka riqe ta Suna bata hakuri, juyo wa ta yi ta hau kai masu duka dukkanin su a haukace, Afrah ta yi baya amma Atiyyaerh sam ta qi matsawa, kuka kawai take ta rasa me ke mata dad'i, fizgewa Rasheedah ta yi daga riqon da tai mata ta yi gaba, da sallama ta shiga gidan ba b'ata lokaci ta shige d'akin mahaifiyar Ahmad d'in, ta na zama aka gaisa sama sama sannan ta sanar dasu cikin nan da sati biyu su yi komai na Shirin auren Ahmad da Atiyyaerh su turo ai auren in suna so in basu so zata ba wa wani Atiyyaerh, cike da murna su ka yi godiya ta kamo hanya ta koma gida abunta kamar ta je bada auren 'yar tsana.
Atiyyaerh ce zaune a qasan carpet ta jingina da kujera, kanta na qasa ta na shassheqar kukan baqin ciki, da kewar iyayen ta,Auwal na zaune saman kujera ya raba qafafun shi daya ɗora hannayen shi akai ya haɗe yatsun hannayenn shi waje d'aya, sai kad'a jikin shi yake Cike da masifar da ke cin ran shi, anya Rasheedah bata yi nasarar Sanya masa ciwon hawan jini ko na zuciya ba kuwa saboda yanda yake ji a zuciyar shi? A d'aya gefen nashi kuwa Afrah ce zaune a qasan carpet itama tana ta kuka,da sallama ta qarasa cikin parlourn, tana isowa ya miqe ya ja wuyan rigar ta daf da shi, ya na zare mata idanu, ya ce,
"Ke mahaukaciyar ina ce? Ke zaki aurar da ita da har zaki je ki yi wa iyayen yaron can magana akan auren ta? Banda zagin cin mutuncin da ki ke mata a kullum safiya,meke damun rayuwar ki ne gaba d'ayan ta Rasheedah?"
Cike da hargowa ta fara magana,
"Ina ce dai da uwar ta zata mutu duk ta sanar daku ni ke da iko akan wannan yarinyar? In dai ka tina haka ka barni nai abinda na ga ya dace da ita in dai ba sab'a wa wasiyyar ta ta da kuka dame ni da sai na cika za kayi ba,"
Iya abinda ta sanar da Auwal kenan ta sa kai ta haye sama zuwa daki abinta cike da fushi,yo bama dole ta aurar da wannan shegiyar yarinyar ba? Na farko tinda take bata tab'a jin Afrah ta yi saurayi ba, na biyu kuma duk da kyaun Afrah in ta jera da Atiyyaerh sai ka ga Atiyyaerh ta zarta ta, sannan ga samari da Atiyyaer ke yawan yi amma Afrah shiru, amma in ta tafi zata samu itama ta samu mai kud'in da zai kula 'yar ta ta, sannan haushin ta dik samarin Atiyyaerh masu kud'i ne, Ahmad ne kawai talaka, kuma jahili, dan haka shine daidai ita.
"Ki yi hakuri Atiyyaerh tabbas Rasheedah ta fini gaskiya, wannan umarnin mahaifiyar ki ne akan mu barwa Rahseeda ke da duk Wani abu da zata zartar akan ki, ban tab'a zaton Rasheedah rashin Imanin ta ya Kai haka ba, ban San me Sakeenaah ta tsare mata ba dik da bata rayen ma, na rasa yanda zan shawo Kan wannan qiyayya da matsala da ke afkuwa a tsakanin ku, na yi nasihar, na tsawatar, na yi duka, na yi addu'a amma shiru,ni yanzu ban san dalilin ta na wannan qiyayyar ba har yanzu,domin na raina dalilin da take bayarwa, ko da yake ita hassada mugun ciwo ne, ita ke Kai mutum da aikata manyan zunubai Dan kawai ba ya son Wani ko baya qaunar ci gaban shi ,babu komai kar ki damu Atiyyaerh na, Wani hanin ga Allah baiwa ne Kuma ina kyautata zato ga Allah ya sa kome zai faru ya kasance mai kyau, dan haka ki rungumi qaddarar ki Allah ya miki albarka,"
Cike da tashin hankali take kallon shi,me yake nufi, bari zai yi a mata auren dole da jahili? Ita fa ko masallaci bata tab'a ganin shi ya je ba sai majalisar su ta shaye2, kuka take sosai ta miqe ta yi d'aki da gudu, Afrah ce ta bi hanyar da Atiyyaerh ta bi da Ido cikin tsananin tausayin 'yar uwar tata, cikin kukan tausayin Atiyyaerh ta ce,
" Abba ka tausaya mata, ka duba ka gani tin tasowar mu take Shan wahala a wajen Umma, bata tab'a roqon kowa akan ya taimaka mata ba, wannan fa maganar aure ake yi a tsakanin ta da wannan d'an iskan, Abba in ni ce zaka iya bari haka ta faru akai na? Haba Abba ka sa baki mana, Atiyyaerh bata cancanci wannan tozarcin Daga wajen ka ba Abba,a yanzu ne lokacin da ya Kamata ta huta tinda aure za a mata ta bar gidannan da yake a matsayin kurkuku a gare ta,Abba ai ya kamata ace zata kasanace ne cikin farin ciki ko? Abba pls do samething"
Afrah ta qarasa cike da kuka, Auwal ya yi shiru, zuciyar shi na tafasa, ji yake daya sani da bai dau alqawarin nan ba, da ya sani ko mai nacin da Sakeenah ta masa ya qi amincewa da buqatar ta, tabbas da ita kanta Sakeenah ta San 'yar uwar ta ba zata tab'a sakkowa daga d'okin da shaid'an ya dora ta akai ya bata fadawan shi take ganin ta kamar wata sarauniya a duniyar ta ta zalunci da bata bata gudan jinin ta ba, ba abinda zai iya yi a yanzu, sai dai ya bi lamarin da addu'a, Yana roqon Allah da ya sa hakan ya juye ya koma alkhairi ma Atiyyaerh.
A can d'akin su Atiyyaerh kuwa ta na can ta na cin kuka, kamar wadda aka yi wa rad'a Kuma ta miqe tsaye, da hanzari ta had'a Kayan ta dika a jaka, ba tare da ta fad'a wa kowa ba da sassafe kowa na barci ta gudu gidan Mama, tana shiga ta fasa kuka,Mama ta fito daga daki a firgice,
"Me zan gani haka, kukan me ki ke haka Atiyyaerh? Me ya same ki? Waya mutu?"
" Mama ku taimaka min, Umma zata min aure da Ahmad maqocin mu, Mama in aka auran shi an tauye rayuwa ta,ku taimaka min, ni bance sai mai kudi zan aura ba amma a qalla aban mai ilimi musamman na addini,"
Kamota ta ji anyi ta baya tana juyawa taga Abban su Rasheedahn, fadawa ta yi qirjin shi ta saki sabon kuka, hakuri suka had'u suka bata, dan basu da abin yi akai Suma, umarnin mahaifiyar ta ne akan kar a sawa Rasheeda baki akan kome zata yanke akan Ablaerh,Kuma sun kula so take ta nuna masu iyakar su, wato tinda an dage se an cika wasiyyar Sakeenaah bari ta yi wannan rashin mutuncin, fatan su kawai Allah ya sanya albarka a rayuwar ta ya kare ta daga sharri kowanne iri ne,kallon su kawai take cikin share hawaye ta na Murmushi Mai ciwo da qona zuciya ta ce,
"Yanzu kenan ban da gata? Banda mai taimako na a cikin ku, banda wanda zai tsaya min? Kome zai samen ba ni da wanda zan fad'awa na ji dad'i? Na tab'a kawo qarar Umma a dik irin abinda take min? Ah ah ban taba kawo maku qara ba sanda take dukana, ko sanda ta ke hanani abinci, ko sanda take zagina da iyaye na, ban taba fad'a maku komai ba, amma yanzu na kawo kukana akan future life d'ina kun kauda kai, Allah shi ne Mafi sani an cutar dani, an zalinceni, amma Allah na nan,"
D'aukan kayan ta ta yi ta fita a gidan suna kiran ta amma ko juyawa bata yi ba, kuka kawai take suma kukan suke, kwarai zasu so su hana faruwar komai, za su mata magana su lallashe ta ko zata sauya qudirin ta akan wannan mummunan lamarin da take so ta zartar,basu tab'a zaton rashin Imani da tausayin Rasheedah ya Kai haka ba.
Atiyyaerh na komawa ta tarar da Rasheedah na tsaye ta na masifa akan rashin ganin ta da kayan ta da ba ta yi ba,cikin had'e fuska da baqin rai ta ce,
"Gidan uban wa ki ka je da sassafen nan?"
" Umma ki yi hakuri wajen Mama naje,"
"Ohhhh kin je ne ki fad'a masu ne dan su kashe ni ko su tsine min? Uwar ki ma ta yi ta bari indai had'a ni da iyaye na ne,ke bari ki ji in kk ga ba ai auren nan ba kin mutu, ko kin mutu a dakin ki za ai maki wanka,na gidan Ahmad, wuce ki ban waje ni,"
Shigewa ta yi tana ta kuka gashi bata da waya balle ta gayawa Yayan ta,wataqila ya sama mata mafita, alwala ta shiga ta d'auro ta hau salloli tana kuka tana sanar da Allah, Afrah tsabar taya ta baqin ciki itama ta amshi maruka biyu bayan fitar ta, da taje ta mata magana akan auren.
Kwana biyar tsakani su Ahmad suka kawo kudin aure dubu goma, sannan da akwatinan lefe biyu, dika kayan ciki basu fi goma ba, sai takalma biyu, da jaka biyu,mayuka ne da yan kayan kwalliya kamar an roqo gasu nan, komai a tsiyace, a wannan lokaci kowa yaga Ablaerh sai ya mata kuka, komai ya k'wace mata, bata immm bata imm imm, wani lokacin zaune za ka ganta ta yi zurfi a tinani kawai hawaye na bin fuskar ta, d'an gyaran nan na amare wa take da shi da ma zai kula ya mata? Kullum tinanin ta ina mahaifin ta yake tinda an ce shi Yana raye, me yasa ya tafi ya barta? Meyasa bai taba waiwayar ta ba? Wata irin qiyayyar mahaifin ta ne ta d'arsu a zuciyar ta, a wannan matakin ta cire komai ta qudurta auren Ahmad kuma zata masa biyayya,kawai yanzu tafi qaunar ma ta bar gidan ta huta.
Sauran kwana biyu biki Yousuf ya dawo daga makaranta, Sulaiman ya zo shima daga Hostel, dan sunyi magana da Yayan shi Abban su ya neme su, akan wata mahimmiyar magana, tin a hanya gaban Yousuf ke tsanan ta bugawa, ya tambayi duk wanda yake ganin zai samu haske akan kiran Abban su amma ba wanda ya fada masa komai, lokacin da ya shigo gidan dare yayi, Sulaiman ya tarar idon shi ya yi jawur, kamar wuta, kasa kallon qanin nashi ya yi, dan bai tab'a ganin shi cikin tsananin fushi haka ba, yasan ko ya masa magana ba zai kula shi ba, wannan dalilin ne ya sa shi tambayar Afrah dake gefe tana kuka meke faruwa?
Sanar da shi komai ta yi, cikin tsananin b'acin rai ya ce ,
" Inaaaa ba zai yu ba, ba zai tab'a yuwuwa ba, taya za ai a Yi irin wannan kwad'on, ni na kai son Ablaerh ina? Ya za a min haka, ya za a zauna ta qarfi da yaji sai an cuci marainiya?"
Wani mugun kallo Rasheeda da ta fito daga kitchen take bin Yousuf d'in da shi,
"Sannu ubana, sannu mad'aurin auren ta, waya damu da son ta da kk? Ko kana son ta wa zai zauna da ita cikin gida d'aya? Kai wama zai yarda ta zama surukar shi? bari kaji, yanda d'an uwan ka ya zauna ya yi shiru to kai ma ka sa min ido, mahaifin ku ya kira kune dan bai son ai auren baku nan, dan haka ku kiyayen dikkan ku zan matuqar sab'a maku akan wannan haukan da kuke, kana Ina take tarawa mutane samari a qofar gida kamar gidan magajiya? Ka na Ina samarin ke tare ta a hanya da sunan soyayya? Kai kana ma da tabbacin wannan yarinyar bata San Wani namijin ba?"
Cikin qunar rai Yousuf ya bud'e Baki zai magana Dan ya San wacece Ablaerhn shi ba ta aikata abinda ake fad'a akan ta ba,amma Atiyyaerh ta riga shi,
" Nifa Yayah komai ya wuce Allah ya sa hakan shine Mafi alkhairi a gare ni, i can not stop her from doing what she wants, komai ta ce daidai ne akaina, and i will obey her command indai bai sabawa Allah ba, ka kwantar da hankalin ka Yayah, rayuwa ta bazata wulaqanta ba indai zaku na min addu'a,"
Tana kaiwa nan ta shige d'aki da sauri tare da toshe bakin ta da take shirin kuka, zama ya yi dab'ar a kujera mafi kusa da shi, tare da rintse idon shi da suka yi jawur, ya dafe kan shi dayake jin kamar zai tarwatse, shassheqar kukan sulaiman ne da Afrah kawai ke tashi a wajen, tambayar su ya yi Mama da Abba sun sani? D'aga masa kai suka yi alamar eh sun sani, me suka ce ya sake tambaya, Afrah ce ta labarta masa duk abinda Atiyyaerh ta fad'a mata, shima kukan ya fara sosai, anya irin wannan wasiyyar ya halatta a cika ta? wacce irin qiyayya ce tsakanin Umman su da Mummyn Atiyyaerh as much as he could remember mummyn Atiyyaerh was a very kind hearted woman, she is so loving, caring , and beautiful, she is so cool and sweet,me ya sa Umman su bata son ta? Miqewa ya yi ya ce masu sai da safe,
" Yah ina zaka?"
Tambayar da suka hada baki suka yi masa kenan,
"Makaranta zan koma zamana baida amfani,"
" ka yi hakuri Abba ya dawo shi ya kira mu fa,"
"Bazan iya ba, shima hakuri kawai zai ban, and i don't want to hear it from him, zanga matuqar gazawar shi, ku bari kawai na koma,"
" Yah in ka tafi baka ma Ablaerh sallama ba abun zai mata ciwo sosai"
Jingina ya yi da bango ya d'age kan shi sama dake barazanar tarwatse masa, tabbas yasan haka ne in ya tafi ba su yi sallama ba ba zata ji dad'i ba,a hankali ya fara taku ya je d'akin nasu, kwance take tana kallon sama, hawaye na gangare wa a idon ta, ko motsawa bata yi ba, wurga idon ta ta yi gefe inda ta ji motsin shiga d'akin ta ga shine, bud'e mata hannu ya yi akan ta je gare shi, kukan ta ne ya qaru, a hankali ta miqe ta je ta fada jikin shi for the first time a rayuwar ta bayan ta girma, kuka take sosai, kamar zata hadiye zuciya, shima kukan yake, baisan yana son ta ba sai yanzu, itama bata zaci wannan yaba shi da zuciyar ta ke yi ba sone sai yanzu, suna tsaye a haka Rasheeda ta banko qofar ta shiga....
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 23:
Hannu ta sa ta damqi damtsen Atiyyaerh ta janye ta daga jikin Yousuf ta kwad'a mata mari, cikin qanqance Ido da d'aga murya ta ce,
"Ai dama na San za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, tinda na ga gilmawar ka kayo nan jikina ya ban akwai Wani abu, a gidan nawa zaki nuna min karuwanci? To ki kwantar da hankalin ki kwana nawa neèe ?daga gobe ne fa za a yi bikin naku, jibi an daura aure an kai ki gidan mijin, kin je can ki ci uwar da zakici a can amma ba a nan ba,"
Ran Atiyyaerh da Yousuf ba qaramin b'aci ya yi ba, musamman kalmar karuwancin nan da ta ambata ta sosa zuqatan su, amma dake Atiyyaerh akwai hakuri, tin kallon farko da ta mata na b'acin rai bata sake ko da kallon ta ba,ta juya ta koma gado ta kwanta ta dora pillo a kanta, sannan ta ja bargo ta rufa, Yousuf ne har yanzu ya ke tsaye ya kuma tsare Umman tashi da ido, yana son ya yi magana amma ya rasa mai zai furta da Allah ba zai fushi da shi ba, tabbas in zai magana ko ashar ya dura ba zai ji sauqin zuciyar shi ba, wannan matar me mummunan halin da be tab'a ji ko gani ba a rayuwar shi mahaifiyar shi ce, kalaman shi dole su zama masu taushi a gare ta in Yana son Rahamar Allah, a wannan gab'ar kuwa bai da kalamai masu wannan taushin, hadiye wani abu ya yi mai mugun d'aci ya sa kai zai fice,
"Ina zaka je kuma?"
"Makaranta zan koma,"
kafin ta furta wani abun ya fice, daidai zai bude qofa Abban su shima ya kama zai shigo, murmushi Abban ya masa amma ya kasa maida masa da martanin Murmushin, dan haushin Abban ma yake ji sosai ai ba kowacce wasiyya ake cikawa ba, wannan akwai cutarwa a cikin ta, ace shi bai isa da gidan shi ba,saboda kawai wasiyya sai kowa ya rufe ido, fadar Allah nawa sike takewa duk da ba zai iya nunawa ba, amma tabbas yasan suna aikata Wani abun mara kyau ko da a b'oye ne, sai wata wasiyya ce zata hana su kyautata wa marainiya, wannan ko uwar ta na da rai ba zata so hakan ba, komai son ta yi mending abubuwa tsakanin ta da Umman su, kafad'ar shi Abban ya dafa ya d'an matsa kad'an,ai kuwa kamar ya matso da kuka, kuka ne ya kwacewa Yousuf, wanda Abban nasu ya ji dad'in zuwan kukan, dan ya kula tin ba yau ba d'an nashi yake son Atiyyaerh, sai dai a wancan zuwan da ya yi ya tabbatar da zargin shi ,se kuma ga wannan mummunan had'in aure da ake son
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 21