mata doguwar rigar shaddar ta sannan ya miqa mata dankwalin kayan Dan ya San yanda take saurin nan ko Kwalliya ba zata tsaya yi ba,
"I am sorry My love, yanzu zamu tafi, ki ka sani ko jinkirin da muka Yi ya zama alkhairi Adnan ya zama Daddy?ko bakya so?"
Wata iriyar kunya ce ta kama ta ta saki murmushin jin dad'i ta kwantar da jikin ta a nashi,
"Allah ya nuna min wannan ranar da na fi kowa farin ciki a rayuwa ta"
"Ameen"
Qarasa shiryawa suka yi ta shafa lipstick da powder se ta sa kwalli ta kafa dauri me kyau, Kan ta gama ya qarasa shiryawa Shima se suka tada sallah, su na idarwa suka yi addu'ar su suka rufe sashen su sai gidan su Sakeenatuwa.
****************************
A gidan Rasheedah kuwa tun safe ta yi wa yaran wanka, amma sai bata saka masu kaya ba domin ta kwana da burin zuwa gida a ranar, yousuf ta yanka wa warning din kar ya fito tsakar gida ya b'ata jikin shi, Auwal na kallon su be ce mata komai ba, Dan shi yanzu gaba d'aya lamarin ta ya fita akan shi, haka ya gama komai ya shirya ya fita bata gama abin karyawa ba,a haka ta gyara waje sama2, ta dora masu abinci suka ci, cikin daya daga atampopin da ta siyo bayan ta Saida kayan da Sakeenah ta kawo mata tsaraba ta Kai aka dinka mata, se ta dakko mayafin da ya dace da kayan wani shara2 me bala'in kyau ta sab'a goyon ta sannan ta yafa mayafin, ba qaramin kyau Rasheedah ta yi ba, dama can ita me kyau ce rashin halin kirki ke sa ake mantawa da kyan nata,shape din ta ya bayyana sosai a waje, ta riqo hannun Yousuf da ta wa kwalliya da kayan da Sakeenaa ta had'o masu tsaraba, shima Sulaiman kwalliyar da ta masa kenan, ga takalmi mai tsini ta saka,ta feshe jikin ta da turarukan da Sakeenaa ta kawo mata tsaraba, Arebians, qamshi ko ta ina na tashi kamar wadda tai barin turaruka a jikin ta, haka ta tako fuskar nan ta sha ado, a haka ta ja qofar gidan ta rufe da makulli ta yi gaba.
Duk inda ta gilma haka zaka ga idon mutane na bin ta yuuuuu,a haka ta tako ta zo bakin titin unguwar su, ta dad'e tsaye tana neman abun hawa bata samu ba, masu manyan motoci sai qara rage gudu suke suna kallon ta, har wani fari take tana yanga, cikin ranta kuwa fad'i take,
"Kaiiii arziqi yayi a rayuwa, dube ni kalar babbar mota,Sam be kamata kamar ni ace yawo nake a qasa ba Mtseeww Allah ya tsinewa talauci,"
Dogon tsakin da ta ja ne ya sa Yousuf ya daga kai ya kalle ta, a haka ta samu adaidaita suka kama hanya sai gida,suna isa qofar gidan, suma su Sakeenaa na sako motar su, wani qululun baqin cikin ganin su ne ya taso mata, ji tai kamar tace a maida su gida, amma ba hali, sai su raina ta suga ko shakkar su take , ita ko Sakeenaa ta bangaren ta ba qaramin farin ciki ne ya lullube ta ba, yau zasu yi yini tare da yayar ta a gida,ta San Mama zata ji dad'i sosai, Adnan kam in ranshi yai d'ari ya baci,ji ya yi kamar su koma gida kawai, da yasan wannan uwar raqai din zata zo da basu zo ba yau, d'aure fuska ya yi sosai ya kalli yanda matar shi ke murnar ganin yayar ta, sai ya sassauta dan kar ya b'ata ran ta,ya San halin ta yanzu tana iya jin haushin shi, fita ya yi ya buɗe mata, ta sako qafar ta waje,sai da Rasheeda ta hadiyi yawu, dan ba qaramin burge ta suka yi ba, sannan ga wani arnen takalmi a qafar Sakeenaa, mai a daidaita sahu ne yai magana,
"Malama ki ban kudina nai gaba ina da abin yi in ke ba ki da shi,"
Da ya San wacece Rasheedah da be tsokano wa Kan shi jidali ba, kamar Jira take kuwa duk wani haushin dake ranta ta fara sauke masa shi a ka, hayaniyar su ce ta ja hankalin mazan dake zaune a d'an nesa da su, daidai Sakeenaa da Adnan sun dakko warmers da suka sako abinci suna takowa wajen, sun riga matasan isowa dan haka Mai adaidaita Sahu ya maimaita me ya faru ita Kuma ta ce qarya yake zagin ta ya yi, Adnan na ji ya San me adaidaita sahu ya fita gaskiya, matasan na zuwa suka fara hayya hayya za su daki me adaidaita Adnan ya hana ya sallame su, sannan ya sallami Mai adaidaita ya bashi hakuri shi kuwa Mai adaidaita ya ja adaidaitan shi ya yi gaba ya na fad'in
" 'Yar bala'i da baqin ciki tinda ki ka hango su a mota luqeqiya ki ka hau hanqoron nishin baqin ciki ke da shiga irin motar nan kuwa se dai a qiyama in ana shiga shegiya 'yar has,"
" Uwar ka ce 'yar has d'in dan uban ka matsiyacin banza ni Wani ya Isa na Masa hassada ne kaf duniyar nan, shege mara mutunci kawai,"
Hannun ta Sakeenaa ta riqe ta ja da niyyar su shiga ciki ta fisge ta kama hannun Yousuf,
"In ki ka kama hannuna wa zai kama na d'ana? Ko dan baki san zafin su ba sai na shige na bar shi anan?"
"Ke ! ko da wasa kar ki kuskura ki b'atawa mata ta rai, ba dan ke ta zo ba, ni da na san yau zaki zo ma da ban bar ta zuwa yau ba, to ki kiyaye ni, duk abinda ya samu iyalina ta dalilin ki ranki sai ya yi mugun baci shashasha kawai"
Cikin fushi ya wuce cikin gidan ya barsu tsaye har Sakeenaah be kula ba Dan ya San a hakan ma haushin shi take ji ya yi wa yayar ta ihu,cikin yaqe Sakeenaah ta kama hannun Yousuf suka shiga, ita kuma 'yar jarabar tana ta fama, suna isa suka tadda Adnan gaban su Abba, suna gaisawa, Mama bakin ta har kunne ganin yaran nata ga jikokin ta, cikin ranta godewa Allah kawai take tare da fatan Allah ya azurta Sakeenah itama da haifi nata, suma zama suka yi a qasa suka gaida iyayen nasu, Yousuf Abba ya kira,yana zuwa kuwa ya kama guiwa shima ya yi gaisuwa, dariya aka sa a wajen dika, banda Rasheedah, Sakeenah cikin dariya ta ce,
"Lallai Yousuf ka gaji ni wajen gai suwa ko Maa? Haka kk ce ina yi sanda ina qarama ko?"
" kwarai kuwa haka kk yi, ko wa kk gani har wanda baki sani ba sai kin dafe guiwa kin kai gaisuwa,"
Dariya aka qara sawa, Rasheedah kuwa da haushin maganar su ya kama ta se ta kyab'e baki ta ce,
"Hmmm to ai sai ki bari in kk sillibo naki sun yi koyi dake, amma wannan mahaifin shi ya gada, dan baban shi ma haka yake,"
Ta qarasa maganar ta tana wani marmara ido, baki iyayen suka sake, Sakeenaah ko yaqe ta yi tace,
"Auu habaa, Allah sarki,"
Ba ta son iyayen su San cewa har yanzu basu jituwa, amma Abba sai da ya gane, cikin d'an had'e fuska ya ce,
"Ke wai dan Allah yaushe zaki yi hankali, yaushe zaki gane irin son da qanwar ki take maki, bazaki na koyi da kyawawan halayen ta ba kema ki zama ta gari? Kullum qara baud'ewa kike kamar saniya?"
Aiko ran Rasheedah in ya yi dubu ya baci da Jin Kalaman mahaifin nata akan ta, wato ita ce ma saniyar? Adnan kuwa na Jin haka ya yi caraf ya cafe maganar da cewa,
"Ai Abba dama ina da niyyar zuwa na fad'a maku irin wadannan abubuwan da Rasheedah ke yi wa Sakeenah, amma in na tuna Sakeenaa ta ji na kawo qarar Rasheedah wajen ku ranta zai b'aci yake sa na bar maganar,amma damuwar da Rasheedah ke kunsawa Sakeenaa ba kad'an bace da kuwa kwanaki har likita cewa ya yi ta rage damuwa dan ko gab take da kamuwa da hawan jini, kuma wannan baiwar Allah itace sanadi,"
Dik abubuwan da ke faruwa Adnan be rage ba ya sanar da iyayen nasu, wanda hakan ba qaramin kuka ya saka Sakeenaah ba, sannan ta ji haushi matuqa da Adnan ya zayyana wannan abu gaban iyayen su, a nashi bangaren ya fad'a ne dan wataqila in iyayen suka yi ma Rasheedah fad'a zata nutsu ta kyale masa matar shi ta dena hantarar ta da nuna mata tsanana fili, bai san cewa duk fad'an da za a wa Rasheedahn ba qara mata tsanar Sakeenaahr ze yi fiye da da, ji take kamar ta tashi ta shaqe ta ta mutu kowa ya huta, hakuri iyayen suka bata bayan sun gama wa Rasheedah fada, hira aka koma yi, ana raha amma zuciyoyin su ba dad'i,musamman Sakeenaah data ke jin haushin Adnan na fadan wannan abun, ga kuma yanda hankalin ta ke tashe da kallon da yayar tata ke mata,a haka dai aka kira la'asar suka tashi zasu masjid Abba da Adnan kenan sai Yousuf da shima yace zashi, Sakeenaa da Rasheedah ne suka miqe zuwa tsohon d'akin su dan yin sallah,Mama kuwa d'aki ta tafi Dan d'akko ma Rasheedah hijabi, tinda mayafin jikin ta ya yi shara shara da yawa ba zai sallah ba, Sakeenah na ninke Hijab din ta ta ji an dafa kafadar ta, tana juyowa taga Rasheedah wadda fuskar ta ke d'auke da Wani irin yanayin da ba zai fad'u ba,
"Rasheedah lafiya?".........
😱😱😱😱😱😱
*Meke shirin faruwa ne? Jama'a ku kawo dauki*
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Page 8:
Sakeenaah ta ji sauqi sosai, ta dawo normal kamar bata yi ciwo ba a kwanaki ukun da suka gabata, duk da cewar period take ba abinda ya canja na ma'amalar auratayyar ta da Adnan sai abu daya, (Saduwa) ban da shi ji yake kamar ma bata priod d'in saboda irin kulawar da take bashi, ba qaramin gwana bace wajen iya kwantar ma da mijin ta buqatun shi, dan ba ta son tauye shi ko tawace fuska saboda Shima yanda yake kyautata mata, sabanin mutuniyar ku Rasheedah, ita sai tana so ma aka fi yin abun, in ko tana period ko hannun ta ya tab'a da sunan wasa to pa kamar ya aikata sab'o,ta dinga nana ta masa she is on her period fa, kwata2 baya wani samun yanda yake so a wannan lokacin.
Yau Sakeenaa ta gama period din ta, Adnan yana wajen harkokin kasuwancin shi abubuwa sun masa yawa duba da tsawon lokacin da ya d'auka baya zuwa kamfanin nashi guda biyu d'aya na sarrafa rake a Maida shi zuwa sugar, d'aya Kuma shigowa suke da kayayyakin sawa daga qasashen waje kala kala,yau kayan su da suka yo order daga Hong Kong za su iso,shi yasa Adnan ke son zuwa gani da Kan shi, kan ya fita dama ya fad'a mata yana sha'awar tuwo,saboda haka yau tuwo zata Yi masa tinda shi yake so.
Shamsiyya me aikin ta ta sa ta jiqa mata shinkafar tuwo daidai yanda zata ishe su ,ta Kuma Sanya ta b'arza mata wake a blander tare da bushe shi sannan ta jiqa mata,ita Kuma ta wuce d'akin Adnan ta na gyarawa dik da ba Wani datti ya yi ba ma, da ta gama ta wanke toilet, sannan ta koma nata ta gyara , mai yi mata shara Harsa'u dama ta share parlour da dika gidan ko Ina qalqal se d'aukan Ido yake, sai da ta fara dora tuwo ta had'a miyar waken ta da ta qara da gyad'a dan ta yi qard'i,ta kawo ganda da busasshen kifi ta zuba da kayan qamshi da dik abinda ya Kamata dai,se ta fara tinanin yin farfesu,dake Adnan na son farfesun naman zabo kawai sai ta yanke shawarar shi zata masa, deep freezer ta bud'e ta d'akko naman zabon ta gyara Shima ta yi masa had'in da ya dace da shi ta zuba masa kayan qamshi na MummyJaf miscellanea special curry ya na matuqar d'auke qarnin kaza ko kifi da Kuma naman zabon, idan Miya kuwa ka ke yi da shi har maqotan maqotan ka sai sun Jiyo qamshin ta, (sai an gwada akan San na kwarai 08039469116 shine no da Zaku Kira Dan mallakar naku) sannan ta wuce wanka.
Cikin gayun ta ta fito sanye da Wani material Mai laushin gaske kalar makuba da ratsin fari a jiki, ta kafe dauri me kyau da dankwalin shi, ta saka siririyar sarqar ta ta zinare me siririn abun hannu da zobe, ta yi wa fuskar ta saussauqar Kwalliya se tashin qamshi take, masu aikin ta sai yaba mata suke, ita kuwa Murmushi ta yi ta yi musu godiya, tambayar ta suka yi ko akwai abinda take so a mata? Kallon su ta yi ta ce,
"Shamsiyya kin tace min zob'on kuwa? "
"Eh Hajiya na ma so na qarasa had'a shi sai na ga kamar kin fi son had'a wa Alhaji abun sha da Kan ki, amma fito maki da kayan marmarin na wanke su Suna nan aje se dai in kin shiga kin ga akwai abinda za a maki Kuma se a yi Uwar d'aki na"
"To na gode,ku na iya tafiya kawai ai Kun yi qoqari,da fatan Kun d'iba ko?"
"Eh Hajiya ai wannan girki qamshin shi kawai ya Isa mutum ko ba a bashi ba ya d'iba ballantana ma komai ki ka ci a gidan nan muma sai kin bamu"
Dariya suka yi gaba d'ayan su, Shamsiyya akwai barkwanci, gata ba wata babba bace sosai da kad'an ta girmi Sakeenah dan dika dika ba zata fi shekara ashirin da takwas ba sa'anni ne ita da Rasheedahn Sakeenah, bazawara ce mijin ta rasuwa ya yi ya barta da Yara biyu mata, dik weekend ta na kawo su gidan su zauna da ita a can sashen masu aiki, sanda Sakeenah ke Jin nishad'i sai ta sa a shiga da su su yi wasan su wajen ta.
Sallamar su ta yi suka koma bangaren su, ta shige kitchen dan qarasa had'a zob'on da ya sha abarba da cucumber da kankana, ga kayan qamshi da na'ana'a, goruba da ta zuba a ciki, hummm makaranta wannan zobo da gani se ya yi dad'i, fruit salad ta had'a ta Saka a bowl ta rufe ta Saka a fridge se ya dawo zata d'akko Dan a sha shi da sanyi sanyin shi.
Gani ta yi sun qarasa tuqa mata tuwon sun kwashe miyar ma ta yi sun zuba a inda ya dace sun jera mata komai a dinning table har ruwa sun aje, ajiyar zuciya ta yi ta yi Murmushi Shamsiyya ta na matuqar taimaka mata a gidan nan sosai, ganin ba abinda ya rage da za ta yi se kawai ta koma parlour ta zauna ta hau tasbihi a ranta, kalmar La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,se Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faqeer, da rabbana hablana min azwajina wa dhurriyatina qurrata a'ayunin waj'alna lil muttaqeena imama ke fita a bakin ta, in ta gama tai hasbulallahu wa ni'imal wakeel, haka haka dai, har taji tsayuwar motar mai gidan, dai dai ana kiran magrib hijab din ta ta saka tana murmushi, tasan tana da alwala in yazo ya ganta ba sallah take ba sai ya bata kwalliyar nan bai mata gani mai kyauba,dan haka sallah ta tada, sai da ta kai raka'a daya ya shigo, kallo ya bita da shi, baki sake, dan a hakan ma ba qaramin kyau ta masa ba, wucewa ya yi yana shaqar qamshin gidan yana lumshe ido, aje jakar shi ya yi tare da wucewa kan dinning table direct Dan kuwa ya dawo da matsananciyar yunwa a tattare da shi tin Karin safe ko ruwa be sha ba da ya fita, warmers din ya hau bud'ewa Wani qamshi ya daki hancin shi, yawu ya hadiya nan da nan kuwa cikin shi ya fara kukan yunwa ya ga abinci, ji ya yi kamar ya fara ci kan ta zo, amma ya daure ya zauna zaman jiran ta,tana idarwa ta yi istighfar sau uku se ta miqe ta je gare shi ta na takun ta me burge shi, d'an rankwafawa ta yi ta sumbace shi a Kuncin shi sannan ta gaishe shi tare da Yi masa sannu da dawowa, Shima sumbatar goshin ta ya yi tare da yaba Kwalliyar ta, godiya ta masa ta na Wani yauqi ta hau zuba musu abincin, d'an duqawa ta yi Cike da tsokana ta ce,
"Bismillah me gida ka ci abincin kada ya huce"
"My love yau Kuma Wani sabon salo ne hakan? Wai me gida kamar a qauye"dariya suka saka a tare,
"Ka San da yake yau gidan ya koma na gargajiya shi yasa ka koma me gida kaima"
"Ohhhh haka neeee"
Gira ta d'aga masa guda d'aya Murmushi ya yi me sauti suka yi Bismillah suka fara cin abinci, ko magana Adnan ya kasa tsabar yanda abincin ya yi masa bala'in dad'i, hannu kawai yake d'aga mata ya na jinjina mata, ita Kuma ta na Masa dariya,
"Yau santin kurma ake kenan, ka San a makaranta an koya mana Santi kala kala, to Kai yau na kurma ka ke yi ko?"
(Hauwabuna can relate) Kai ya d'aga nan ma be ce komai ba, sai da suka kammala dika ne ya dinga Sanya mata albarka ya na yabon abincin daki daki, kama daga Kan yanda tuwon ya yi dad'i Kuma ya tuqu, zuwa yanda farfesun naman zabon ke Wani fitar da d'ad'anon me dad'i da qamshi me gamsar wa, zuwa yanda miyar ta yi zaqwai,Sakeenah godiya ta yi masa, suka miqe a tare, jakar shi ta koma parlour ta d'akko suka wuce d'akin shi.
Ba abinda Adnan yake banda kallon yanda take sarrafa mazaunan ta wajen tafiya, ya shagala sosai a kallon ta har suka Isa d'akin ma be kula ba, in dai Sakeenaa na gaban shi yakan manta komai, wanka suka shiga ta taya shi daga baya ta fita ya yi alwala, ta fidda masa kayan da zai saka kafin ya fito, daya fito bai gan ta a d'akin ba ya San ta wuce nata ta bashi waje ne ya samu damar yin sallahr da be ba, kan ya fita ta d'akko ragowar zobo ta aje musu a center table na parlourn su ta kunna kallon Wani indian film na 'Hamara Rishta' ya na idarwa inda take ya nufa, Adnan shi da kallo bai wani dame shi ba yafi so ya Kai channels TV ko NTA, gani ya yi ita Kan ta sarkin kallon yau hankalin ta baya Kan TVn ta qura masa ido ta na kallon shi daga saman har qasa
"Yau Adnanu ya zama TVn Sakeenatuwa"
Murmushi ta yi ta rufe fuskar ta alamun ta ji kunya ya kama ta ta na kallon shi, dariya suka saka a tare ya lakuce mata hanci, harara ta sakar masa, dan ita bata so ana lakuce mata hanci, dariya ya sa ya d'aga hannu yana bata hakuri, tace sam sai ta rama ,
"Habaa my love yanzu tsakanin mu ba yafiya?"
"Ni dai gaskiya banda ta nan bangaren ai ka San bana so ana tab'an hanci amma kullummmmm se ka yi"
"To gashi zo ki rama," ai kuwa da sauri ta miqe zata Kai hannun ta ta rama ya miqe ya yi d'akin shi, ya na tafe ya na fad'in,
"Ki biyo ni nan ki rama in kin Isa"
"Ai kuwa gani nan zuwa yau se na kusan gutsure Maka hancin ka dama ya yi tsawo da yawa"
Tsaye ta gan shi saman abun sallah ya na qoqarin tada sallah,
"Auuuu ta nan ka biyooo? To bari na je na sake alwala sai ka jamu"
Shi Kan shi ba shi da alwalar ya yi haka ne dan ta bari su yi sallahr isha'i, in ya so ta masa koma me ta ga dama, ta na fita ya shiga bathroom ya yi alwala ya fito, tsaye ta sake tadda shi, dan haka se kawai ya tada sallah suka yi sallar su tare, su na idarwa suka fara karanta qur'ani suka yi ma iyayen su addu'a da musulmi baki d'aya da kan su, a zuciyar ta ta yi addu'ar...
'Ya Allah ka bamu zuri'a Mai albarka idan alkhairi ne a tare da mu da addinin mu, idan ba alkhairi bane Allah ka bamu hakuri da juriya da dangana Ameen'
"Ameen"
Adnan ya fad'a ya na kallon ta da tausayawa, dan ya San hawayen da ke zuba mata baya rasa nasaba da addu'ar da take a zuciyar ta, addu'ar kuwa ba zata wuce ta neman haihuwa ba, matsawa jikin shi ta yi ta kwantar da kan ta a qirjin shi sannan ta ce,
"Yaushe zaka kai ni naga Mama da Abba? Ka ga su suka zo duba ni da banda lafiya a madadin ni na je gaishe su da muka dawo"
"karki damu gobe ma sai mu je ai,"
A hankali yake shafa bayan ta, ta d'aga Kai su ka qura wa junan su Ido Cike da so da kulawa daga nan salon su ya sauya, nace to bari na leqa yaya babba naga me take yi ita Kuma?
Kwance take ta yi d'aid'ai a gado sai hura hanci take ita ga mara M, Auwal Kuma sai bin kanta yake akan ta taimaka ta bashi hadin kai,ko yayane ya samu ya rage zafi amma taqi sam,
"Ni fa na jima da sanin ba so na ka ke ba, jiki na ka ke so,wato so kake ka cuceni ko hutun shekara biyu ni ba zan samu ba a rayuwa ta na zama kamar akuya bini bini haihuwa ko? dika2 yaronnan sherar shi fa d'aya ne,haka kawai ka wani zo ka maqalen ka dirkan ciki ni Kuma inzo ina ta fama ko? ga goyo ga laulayi kamar yanda na yi na Yousuf to gaskiya ni kam na gaji ba zan iya ba, ni ba akuya bace ko mage ehe" Cike da lallashi Auwal ya ce,
"Haba mata ta abar so na uwar 'ya'ya na, naga in ma Cikin ya samu ke ba mai wahalar laulayi bace,Imma fa ya samun kenan, Dan Allah ki taimaka min kar ki bari na fad'a halaka, Ina da mata na tsaya wajen matan banza,yanzu ke Rasheedah Dan Allah baki ganin Sakeenaah neman haihuwar nan take bata samu ba har yau tare fa akai auren ku, gashi ke Allah ya baki amma kina qi? Ki daure ki taimaka min a matuqar matse nake,"
Cikin muryar tausayi ya yi maganar ba dan ba zai iya murd'e ta ya yi abinda yake so ya tashi ba, sai dan kawai ya na so su gyara zaman su su dena abu kamar wasu 'yan bariki, wannan abun daya fad'a ne ya bata qarfin guiwar gyarawa da kyau ta yi tunani, wato ita se yanzu ta gane ma ni'imar da Allah ya mata,ya bata haihuwa ya hana Sakeenah, Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyar ta, ko ba komai itama yau ta fahimci akwai abinda take da shi Wanda Sakeenah bata da shi a duniya murmushi ta yi ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 21