Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suka shaƙu fiye da kowa a cikin family ɗin su. Har suka fita gidan babu wanda ya tanka ko da tari ne. Sun yi nisa sosai har sun hau kan titi, kasancewar unguwar da ɗan tazara, ya waiwayo ya kalleta da hankalinta yake kan titi. "Yaya, ba ya son ko wane namiji ya raɓe ni, amma mai ya sa sam baya nuna hakan ga mahaukacin masoyi?" Kafin ta masa tambayar ta ji muryarsa yana cewa," Na tsani wannan gayen, wallahi sam ba ki dace da shi ba!" Ya ƙarashe maganar tare da buga sitiyarin mitar yana huci. A tunaninka mahaukacin masoyi ya fi dacewa da ni?" Ta yi masa tambayar da ya sanya ya ja burki babu shiri yana kallonta. Tsoro ne ya bayyana a fuskarta, wanda ya sanya ya tuna a kan titi suke. Cigaba da tuƙin ya yi yana mamakin abin da ta ce. "A kan me zan faɗi haka? Karki manta mahaukacin masoyinki ke kaɗai ce kika yarda da duniyarsa, domin har yanzu ba mu san mutum bane ko aljani." "Mutum ne kuma na gari in sha Allahu. Wani lokacin ina mamakin yadda ba ka nuna haushinsa da mu'alamarmu." "Wataƙila don ban ganshi a zahiri bane, amma sauran karki manya yadda suke nuna tsantsan soyayyarsu yake sawa na ji haushi da tunanin watarana za su raba ni da ke." "Har abada muna tare kai fa ɗan'uwana ne na jini tamkar jini da hanta muke." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 12 BISMILLLAHI RAHMANINR RAHIM "Har abada muna tare kai fa ɗan'uwana ne na jini tamkar jini da hanta muke." Kaɗa kansa kawai ya yi jin abin da ta ce. "Ya Huwais, ba ka tunanin lokaci ya yi da mahaukacin masoyi zai bayyana kansa ya daina ɓoye kansa?" Ta yi masa tambayar idanunta a kansa. Ganin bai tanka mata ba, sai gabansa da ya faɗi ya sa ta ɗora da cewa,"Zan gayyace shi bikinka, in har ya ƙi zuwa zuciyata na bani shawarar na haƙura da shi, ko da kuwa son shi xai kashe ni, domin babu soyayyar da na taɓa ganin an yi aure ba tare da haɗuwa." Wani rin faɗuwar gaba ya ƙara ji dum! Sai ya jikinsa na rawa. Ƙoƙarin daidaita na tsuwarsa ya fara yi, don kar ta fahimci halin da ya ke ciki. Kaɗa kansa yake kamar ƙadangaren kutu!"Ya kamata gaskiya ki gayyace shi, amma kar ki ce za ki rabu da shi, don ya ƙi zuwa bikina in har kina sonshi, domin jikina yana bani mahaukacin masoyi shi ya fi dacewa ya aure ki. Wani ne can wanda ba ki taɓa tunanin yana sonki ba, ya ke fama da dakon soyayyarki tsawon lokaci. Da ya ke ƙanwata mai zafi ne kuma kyakykyawa dalilin da ya sanya ya kasa bayyana kansa gareki." "Ni ma haka nake ji musamman a duk lokacin da na yi istikhara." "Da kyau malamar ƙanwata. Daɗina dake komai sai kin nemi zaɓin Allah. Ki ba shi lokaci matuƙar bai bayyyana kansa ba, ni da kaina zan gaya miki ki haƙura da shi." "Amma kai ma Yaya kana da kyau, domin ban taɓa ganin namijin da yake da kyau kuma ya iya tsara rayuwarsa da kula da addini kamar kai ba. Jin abin da ta faɗa kansa ya fasu har ya ji kamar zai cika duniya. "Duk kyawuna, bai kai ƙanwata sarauniyar kyawu da kula da addini ba." "Wannan dalilin ya sa na ke jin matuƙar haushin mahaukacin masoyi da kike sonsa." Ta buɗe baki xa ta yi magana, ya rigata daidai lokacin da suka isa ƙofar gidan, ya tsaya a get ɗin ba tare da ya yi hon ba. Kashe motar ya yi ya kalle."Please, na gaji da maganarsa as usual. Ke kullum damuwarsa kike kawo mini, da kuma na yi ƙorafi kice ba haka ba." Dariya ta yi tare da ce wa,"Kai Yaya," "Ki bani shawarar yadda zan zauna da Wajnah a matsayin mata." Kallonsa ta yi kamar ba ta gane mai yake cewa. "Yes, ina nufin wane irin zama za mu yi, domin kin san ba ta a cikin zuciyata. Tsoro na karna cutar da ita Allah ya kamani." "Ta ci albarkacin Mommy mahafiyarta. Ka yi adalci a zamanku." Kwantar da kansa ya yi kawai a saman kujerar motar domin ba haka ya so ta ce mishi ba. Gani suka yi an wangame get ɗin gidan. Najib ne da matarsa tsaye cikin mamaki suna kallonsu. "Kai! Wallahi kana da abin mamaki Huwais, na ɗauka amarya ka kawo mini kuka tsaya kana soyewa tun ɗazu a waje ashe ƙanwarmu ce." Ta faɗa daidai lokacin da ya shigo da motar cikin yana ƙoƙarin buɗewa. Hilah da ke dariya ya watsawa kallo ba tare da ya ce komai ba. Ya ɗauko pos ɗinta da ta barshi a motar ya miƙa mata. Najib da ya san dawar garin bai yi ƙorafi ba. Ya yi musu jagora suka shiga ciki. Hilah ta zauna a gefen kujerar da ya zauna bayan ta gaida matar Najib mai suna Samahatu. Cikin sakin fuska ta amsa mata, daidai lokacin da ta ije musu gorar ruwa da drinks a gabansu. Huwais ya sanya hannunsa ya ɗauki ruwan ya buɗe, tare da ɗaukar kofi ya zuba mata. Miƙa mata ya yi yana murmushi. Ita ma murmushin ta mayar masa tare da karɓa ta ce masa,"Thanks, Ya Huwais." Da idanu ya amsa mata tare da ije gorar yana mata wani irin kallo. Samahatu ne ta tsaya cikin tsananin mamaki tana kallonsa. Ta juya ta kalli Hilah da take kurɓan ruwan cikin yanga kamar ba ta son sha, yayin da hankalinta yake kan wayarta. Idanunta ta mayar kan Huwais da har yanzu ita yake kallo, duk da maganar da Najib ya ke mishi, amma hankalinsa ba shi a kansa. Ƙara kallonsu ta yi tana son ƙara ganin kamar su. Ta san cewa Najib ya taɓa nuna mata hotonta har ya sanar da ita ciki ɗaya suka fito. To amma wane irin kallo yake mata kamar na soyayya? Ƙwaƙwalwarta ta rikice sai kuma ta fara tunanin ko dai ba ita ba ce. Gyaran muryar da ta yi ya sanya dukanninsu hankalinsu ya dawo kanta. "Baby, bari na haɗo abinci." Ta ce tana sakar masa murmushi. "Ok, honey, please ki kawo wa Huwais juice ɗin goribar da na haɗa ya ji na iya abinci." Dariya ya yi jin abin da ya ce ba tare da ya ce komai ba. Zubbur Hilah ta miƙe tare da kallonsa."Yayana, let me help her." Ta furta cikin taushin murya. "Haba, ƙanwarmu karki wahalar da kanki ai na kusa gamawa." "No, kar ki damu in ba ki gama ba, ki ba ta ta yi girkin domin she is the best cooker in the world" Ya furta hakan cikin tabbatar wa. Murmushi ta yi." No, kar ki damu yanzu xan gama." Ta ce za ta juya. Hannunta Hilah ta kama tare da cewa,"Mu je Anty Samah, kar ki damu. Amarya ce ke bai kamata ki yi aiki ba." "Good girl, na gaya miki ƙanaata akwai hankali da son taimako, domin zan iya cewa tafi ko wace mace hankali da natsuwa da iya komi." Sororo ta yi sai kuma ta yi yaƙe kawai ta kalleta da take murmushin jin kunya ganin yadda yake kurantata. Harararsa ta yi cikin wasa shi kuma ya aika mata da kallo suka shiga kicin. "Huwais, kana cika zaƙewa fa! Ba ka tunanin abin da kake yi kowa zai iya gane sonta kake yi? Kuma yabon ta da kake yi ba ƙaramin matsala zai jawo maka da iyalinka ba, domin babu macen da za ta zauna ta ji kana yabon ko da ƴarka ce haka, ba tare da ta ji kishi ba." "Let her be. Ai dama ta shiga gonar da mallakinta ba ta shiga." No, absolutely you need to change. Wallahi za ka iya jawo ma kanka rashin zaman lafiya da iyalinka, kuma irin kallon da kake mata duk yana wuce gona da iri." "Hmmmmmh," Kawai ya ce tare da mai da hankalinsa kan tibi. "Don't be delusional Huwais." Ƙin tanka masa ya yi, wanda ya sa shi mai da hankalinsa kan tibin suka ci gaba da kallo. A kicin suna aiki Samahatu na satan kallonta, musamman da ta cire gyalen da ta yi rolling ɗin kanta da shi. Da ta ga gashinta sai da ta yi wa Allah tasbihi. Satan kallonta take yi ba tare da ta kula ba, da ta maida hankalinta gurin haɗa salat. "Ance mutum tara yake bai cika goma ba, haƙiƙa wannan halittar ta cika." Ta furta a zuciyarta ganin yadda take da tsatsan kyau. Babu abin da ya ƙara ɗaukan hankalinta irin yadda gashi ko ina ya kwanta a jikinta, kamar wata balarabiya. Ƙara kallonta ta yi daidai lokacin da take goga karot. Murmushi ta sakar mata tare da cewa,"Sannu da aiki." "Yauwa Anty Samahatu, kin ga Yaya Huwais, yana mugun son salat. In har na yi masa santi yake yi, don yau sai kin yi haƙuri domin sai na yi masa waigi." Dariya ta ba ta musamman yadda take maganar cikin tsigar tsokana. "Yauwa ba ni lemun tsamin na saka, domin ya ce ina ɗiga kaɗan kunninsa har zut!Zut! Suke masa, kar kuma na cika ban san ko kuna so ba?" Dariya sosai ta yi, jin abin da ta ce,"Ki sa shi ma ya sanar dani tun kafin mu yi aure yana ci, kuma Yayanki ya koya masa." "Eh, ai ban taɓa ganin aminan da suke ƙaunar junansu kamar su ba, don ban taɓa ganin sun samu saɓani ba." "Saboda sun haɗa ilmi da hankali ne." "Haka ne Anty Samah." Ta ba ta amsa tana juya salat ɗin. "Gaskiya kina ji da Yayan na ki, ko na ce kuna ji da juna, amma sai dai na shiga kokwanto ko ƙanwarsa ce wacce suke ciki ɗaya, ko matar da zai aura?" Dariya ta yi, ta tsaya da abin da take yi,"Saboda me kika tambaya?" "Kulawar ta yi yawa." "Eh, yana ji da ni sosai. A cewar shi ni ce mace ta farko, da ya fara samu bayan ƙanninsa maza uku. Yayana yana ji dani sosai, wanda hakan ya samu asali ne da shi ya yi ɗawainiya da ni tun ina ƙarama, kuma ya kamata ki ga kama, musamman diple ɗin mu, duk da shi ba shi da hasken fata sosai kamata." "Na shiga kokwanto ne irin kulawar da kuka ba wa junanku, kamar na ma'aurata, amma kuma jin yadda kuka taso, gaskiya kin cancanci fiye da haka." "Sosai kamar yadda ni ma nake ji da shi." Kaɗa mata kanta ta yi tare da ɗaukar tiren abincin suka fito falo, yayin da Hilah ta ɗauki tiren juice ɗin. Tashi ya yi ya karɓi tiren yana faɗin,"Ina fatan ba ki wahalar mini da ƙanwata ba?" "Ni na isa a kore ni a garin Abuja?" Ta ce cikin dariya. Zama suka yi a dinning suka fara cin abincin. Yana kai abincin bakinsa ya tauna ya lumshe idanunsa yana kallonta. "Ƙanwata, ke kika haɗa salat ɗin nan ko?" "Please, Anty Samah, ki bani waigi na yi masa kar ya faɗi." Dariya suka kwashe da shi, ban da shi da yake harararta cikin wasa. Suna cin abincin kiran Hajiya ya shigo wanda ya tabbata Hamad ne ya gaji da jira. Dama tun da suka shigo ya fakaici idanunta ya ɗauki wayarta ya kashe. Kiran Hajiya bai daɗe da tsinkewa ba, na Ummu ya shigo. Zuciyarsa ne ya buga ya kalleta da sai wasa fa cokali take yi, domin ba ta jin yunwa. "Ki yi sauri ki gama za mu tafi."Ya ce zuciyarsa na bugawa, don tun da ta kira hankalinsa ya tashi abincin ya fita a ransa. Kasa ɗauka ya yi, don ba shi da abin da zai ce mata, kuma in ya kashe wayar hukuncin da za ta yi musu, sai ya fi muni sosai, musamman Hilah laifin duk a kanta zai ƙare wanda ba zai so hakan ba, don gara ta hukunta shi. Bayan sun kammala suka miƙe za su tafi. Samahatu ta shiga cikin ɗaki ta ibo mata kayan kwalliya da yawa ta miƙa mata a leda. Hannu ya sanya ya amsa yana faɗin," Kawo kar ki wahalar mini da ƙanwata."Miƙa masa ta yi tana dariya ba ba ta ce komai ba. "Ina fatan za ki dawo sis ɗinmu za ki dawo kin burge ni." "Zan dawo Anty Samah."Ta ce tana ɗaga mata hannu har suka fita. "Baby, na shiga cikin ruɗu! Wannan soyayyar da abokinka yake nuna ma ƙanwarsa na aure ne ko jinintaka?" Ta yi masa tambayar daidai lokacin da majgadi ya rufe get ɗin gidan. Kallonta ya yi ganin yadda ta ɗauki maganar serious, dama yadda ta ke musu kallo ya san sai ta tambaya. "Mu shiga ciki mai kika gani?" "Abin ne da mamaki suna rayuwarsu, kamar masoya ko dai akwai aure a tsakaninsu ne." "Ƙanwarsa ce uwa ɗaya uba ɗaya. Karki manta na gaya miki bikin shi ya rage kwanaki, ita kuma da zarar ta kammala karatunta akwai wanda za ta aura a family ɗinsu yake." "Ikon Allah! Gaskiya wannan soyayyar tasu akwai lauje cikin naɗi!" "Please, kar ki sanya kokwato a zuciyarki shaƙuwar jini ce." "Hmmmmmmh!" Kawai ta ce tare da fara tafiya sai kuma ta tsaya ta kalle shi ta ce,"Karka manta psychology na karanta so zan iya fahimtar komi. Kamata ya zo mana da wacce zai aura ba ƙanwarsa ba, amma har ya tashi ban ji ya ambaci sunanta ba." Shiru kawai ya yi, don ba shi da amsar da zai ba ta don haka shirun yafi, domin masana iya magana sun ce shiru ma magana ce. A mota ya miƙa mata wayarta da Ummu ta ƙara kira."Ummu ce take ta kirana shi ya sa na taho, amma bacin haka sai na tabbata wancan mai kama da mayen ya tafi." "Zai iya kwana tun da ɗan gida ne." Ta furta masa hakan. Harara ya wurga mata ba tare da ya ce komai ba ya ci gaba da tuƙi. "Innalillhi! Ka ce Ummu ta kira?" "Eh, sai ki san yadda za ki kare kanki, ai duk ke kika ja, wa sani ko ke kika sanar masa da zuwanki ya wani kwaso jiki ya taho?" "Wallahi bani ba ce Ya Huwais." Banza ya yi da ita ya ci gaba da tuƙunsa, wanda ganin hakan ya sanya ta kama bakinta, tana tunanin darun da Ummu za ta yi. Ba su ƙara magana ba har suka isa gidan. Hajiya da ta yi kici-kicin da ranta yana ƙarasowa ta buga masa dundu a baya. Dariya ya kwashe da shi,"Wayyo yar tsohuwar nan ashe akwai sauranki! Kin ji hannu kaman guduma." "Amma sam ba ka da kirki Huwaisu, sai ka ɗauke ta ku tafi, bayan ka san yana jiranta?" Satan kallonsa ya yi da ya ɓata fuska zuciyarsa a tuƙe, domin da ace bai yi wa mahaifiyarsa alƙawarin ba zai ƙara kula shi ba, babu abin da zai hana bai kai masa mari ba. Miƙewa ya yi ya kalleta da ta yi tsuru-tsuru tausayinsa ya kamata, domin abin da suka yi ta san cewa ba ta kyauta ba, amma ya za ta yi? Ɗan'uwa ta yana gaba da komai kuma takan hana kanta farincikinta ta ba shi na sa. "Gimbiya, muje waje ina son magana da ke!" Ya furta da murya mai sanyi da kuma ɓacin rai. "Babu inda za ta je domin gida zamu je, Ummu na ta kiranmu." Ya ba shi amsa yana kallon agogo fuskarsa a haɗe. "In ina magana ka daina sa mini baki da iyalina, domin ba zan duba tazarar da ka bani ba, wallahi yanzu za a yi ɓatacciya." Ya furta cikin zafin rai. "Mara kunya dukana za ka yi? Karka manta ƴar'uwata ce na jini, na fi ka iko da ita, domin ina da isan da zan hana aurenku." "Inda kuma ka yi kaɗan kenan, domin Hilah tawa ce, duk son da kake mata da nuna kishinka sai dai ka yi a banza, saboda kana ji jana gani zan ɗauketa a matsayin iyalina ta haifa..." Marin da ya kai masa ya hana shi ƙarashe maganar, amma sai bai same shi ba saboda ya kauce. Huwais jin ya kirata da matarsa ya sanya shi yin marin babu shiri. "Au, tarihi ne zai maimaita kansa? Har yanzu ba za ku daina wannan haukan ba? Duk fa ƙaunar da kake mata gidan wani za ta Huwaisu. Anya kana da hankali kuwa?" Ransa ne ya ɓace jin shika kaɗai ta bawa laifin. "Please, Ya Huwais ku daina. Don Allah Ya Hamad, ka je za mu yi waya." Ta furta cikin muryar kuka bayan ta shiga tsakaninsu. "Ki barshi rashin kunya zai yi mini." Ya furta yana huci. "In ba za su daina ba kai Affan, kira mini Babansu Hamisu ya zo ya yi wa abin tufka." Wani wulaƙantaccen kallo ya watsa masa har zai yi magana sai ya fasa, domin ya san abin da ya shirya yi masa sai ya ƙuntata masa fiye da maganar da zai yi masa. "Zan wuce Hilah. Ki kular mini da kanki ina sonki, na tura miki kuɗi a account ɗinki sai mun yi waya. I love you." Ya furta mata a kusa da kunninta ya watsa masa harara da zuciya ta kai masa wuya ya wuce. Ilai kuwa, kamar yadda ya yi tunanin sai ya fi baƙanta masa haka ya faru. Har ya fara taku zai bishi ta kama hannunsa tana kuka. Fita ya yi daga falon zuwa motarshi ba tare da ya yi ma Hajiya sallama. "Umma ta gaida ashsha! Ja'irin yaro kawai. Wannan kishin da kake nunawa da a kan matar da za ka aura kake yi sai armashi zafi fiye da ƙanwarka." Hon ɗin da yake yi musu babu ƙauƙautawa, ya sanya suka kwashi kayan su suka fito da sauri. Figar motar ya yi a guje suka bar harabar gidan. A gida kuwa Ummu ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ta kira wayarsa ya fi a ƙirga, amma ya ƙi ɗagawa, wanda hakan ya ƙara baƙanta ra ta ainun. Numbar Abu ta kira ta fara yi masa ƙorafi. "Ina kan hanya na kusa gida ki jira ni." Ya kashe wayar bayan ya ce mata haka. Yana mamakin yadda take zafafa lamarin. Shi a tunaninsa duk abin da take hange bai kai nan ba, domin yana da hankali da addini ba zai aikata wa ƙanwarsa mummunan abu ba, amma sai ta ɗaga hankalinta ta gadda za ta kasa sukuni. Yana shigowa ta fara hawaye tare da buɗe baki za ta ce. Dakatar da ita ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu. "Duk ke kike rikita lamarin nan Lailah har yaran nan suka fara zargin wani abu, tun da an kusa bikinsa don Allah ki ƙyale shi har ayi bikin nan ya koma gidansa mu huta." "Laifi ne don na sanya idanu a kan tarbiyar Ƴaƴana? Karka manta yarannan amana ce Allah ya bamu domin ya ce dukkannnin mu masu kiwo ne, kuma rabar gobe kiyana sai a an tambaye mu. Kuma kula da kaya, ai yafi ban cigiya. Musamman yadda shi yake nuna soyayyanta ɓalo-ɓalo." "Duk ban ga laifin ki ba, amma kina zafafa lamarin ne, kuma hakan zai iya haifar da wata matsalar. Don Allah na roƙe ki in suka zo dawo kar ki hausu da faɗa ki yi musu kyakyawar fahimta." "Hmmmh!" Kawai ta ce tare da komawa ta zauna, tana jin haushinsa na ƙin ganin abi da da take hangowa, wanda tun a wancan lokacin take nuna masa, amma ya kasa hangowa ga shi hakan ya haifar da ɗa mara ido, kuma har yanzu bai fahimta ba. "To ai shike nan, tun da laifina kake gani, sai na daina sanya idanuna a ka su, kuma duk abin da ya faru kar ka yi kuka da ni." "Babu abin da zai faru sai alkhairi.Na yarda da tarbiyar da na bawa yarana, ba za su aikata abin da duniya za ta la'ance su ba, duk da shaƙuwar dake tsakaninsu." Suna isa ƙofar gidan gabansu ya buga a tare, domin sun san ba za su ji da daɗi a gurin Ummu ba. Ajiyar zuciya ta saki da sauri, ta buɗe motar ta bi bayan su Umnaah, da suka ruga da gudu suna murnar tsarabar da suka dawo da ita. Yana zaune a cikin motar yana hangen ta har ta shige cikin gidan. Kamar ba zai fito ba sai kuma ya buɗe motar ya bita ciki. A falo suka samu Ummu, da ke riƙe da waya a hannunta tana magana da Hajiya. "Yanzu dama abin da yaronnan ya aikata kenan? Shi ya sanya ya na ce sai sun tafi tare? Ki bar ni zai dawo ni da shi ne." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 13 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Yanzu dama abin da yarannan ya aikata kenan? Shi ya sanya ya na ce sai sun tafi tare? Ki bar ni zai dawo ni da shi ne, domin ina ji ina gani ba zai ɓata mana zumunci ba." Hilah ta tsaya cikin tsoro tana zare idanu jin abin da take faɗa. Ta yi sallama a cikin falon, daidai lokacin ta gama wayar, tare da kashewa ta ije a kan kujerar da take kai. "Sannu da hutawa Ummu." Wani mugun kallo ta watsa mata daidai lokacin da Abu yake saukowa daga saman bene. "Ina kuka je?" "Ta raka ni gidan Najib." Ta ji muryar Huwais ya amsa, a maimakon ita da aka yi wa tambayar. Idanunta ta mayar kansa, da yake shigowa hannunsa riƙe da ledar costimetics da matar Najib ta ba ta. "Sai yaushe za ka daina sa ni damuwa Huwais? Yanzu abin da ka aikata ka kyauta kenan? A tunanin shekarun da ka ɗauka a waje zai sanya ka daina sanya ni cikin damuwa." Ta furta cikin ɓacin rai tana kallonsa. Kafin ya amsa ta ɗora da cewa,"Kam me za ka tafi da ita, ba tare da ka sanar mini ba?" "Huwais, zauna magana za mu yi." Abu ya furta

Chapter 9 of 17