Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mataki. In aka yi musu aure hankalinmu zai kwanta." "In sha Allahu, zan kira mahaifinsa na yi masa magana, amma kafin nan ya kamata mu kira shi Huwais ɗin, sai mu sanar mishi da za a sanya mata rana, in ya so sai muga yadda zai yi." "Wane hujja kake son ka tabbatar? Karka manta haukar da ya yi lokacin da Hamad ya nuna yana sonta kuma aka bashi damar ya rinƙa kiranta sau ɗaya suna gaisawa." "Duk da haka mu ƙara kwatanta sa mu gani." Bayan ya dawo da su gidan Najib ya wuce. Yana ganinsa ya kwashe da dariya suka tafa. "Ango kasha ƙamshi." Tsaki ya yi jin abin da ya ce sai ya zauna yana kallonsa. "Ina madam? Ta kawo mini abinci yunwa na ke ji." "Ikon Allah! Ango kamarka yana ɗauke da yunwa." "Hmmmh! Ba za ka gane bane. Yau korar kare Ummu ta yi mini ni da gidammu." "Dama ta haɗa maka da duka, saboda na tabbata ba yunwa ya kai ka ba." "Kamar ka sani, amma ai a banxa nama na jan kare. Saboda ita wacce na je gani tare muka koma gidana." "Hmmmmh! Iska na wahalar da mao kayan kara." Ya ce yana ƙoƙarin kunna tibi. Banza ya yi da shi daidai lokacin da Samahatu ta fito daga kicin. "Baby, kamar ango na ke gani." "Shi ne ba gizo idanunki suke miki ba. Ki taimaka masa da abinci karya mutu." "Haba! Mai amarya guda yake neman abinci. Ko da amarya na hutun girki, ai ya kamata a restourant za su yi oder. "Ki taimaka masa, ƙila kuma amaryar ce ya yi mata laifi ta yi masa horar yunwa." Harararsa ya yi, ba tare da ya ce komai shi kuma yana dariya. Abincin ta kawo masa sannan ta shiga cikin ɗakinta. "Ina fatan jiya ka bai da kai bori ya hau? Saboda yadda na ga amaryarka jiya, na san cewa ba za ta yi wasa da wannan ranar ba." Ƙaramin tsaki ya ƙara ja."Ni kuma da yake shashasha ne sai na biye mata ko? Kana ganin irin iskancin da ta fara yi mini. Kulle ƙofata na yi, domin mace mai arha ba ta birgeni." Takaicin abin da ya faɗa ya kama shi."Arha fa ka ce Huwais? In kai ba ka kai kanka ba sai ta kawo matarka ce fa." "Please, don Allah ni ban zo gidanka ba don ka dame ni da surutu. In kuma abincin ne ba ka son na ci sai ka gaya mini." "Gaskiya ce dai ba ka so, amma kuma dole a matsayina na abokinka, na tuna mala da haƙƙin da ke kanka." Ture abincin ya yi yana harararsa."Ga abincin ka nan sai ka cinye, ai na lura dama ba ka so a kawo mini ba." Ya faɗa tare da miƙewa zai fice. Dariya ya yi tare da kama hannunsa bayan ya miƙe."Ka dai ƙoshi amma ai na san ba za ka yi fushi ba, saboda ba ka wasa da abinci." Tare suka fito yana ta bashi baki kan ya yi haƙuri su zauna lafiya. Bayan ya fita daga gidan sai ya ji baya son komawa gida. Sam ba ya ƙaunar ya ganta a cikin gidan. Gidan abokinsa Isma'il ya wuce. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya kwanta. Da yake ba shi da mata. Bacci mai ƙarfi ya ɗauke shi. Wajnah bayan fiyarsa, tun tana sanya ran xai dawo da wuri har ta cire. Tana kwance a falo da wayarta a hannunta cikin ɓacin rai. Baƙin da ta ke yi suka ɗan rage mata damuwar da take ciki. Sallamar su Wahida ya sa ta miƙe da sauri ta tare su. "Amarya ba kya laifi." Suka haɗa baki gurin faɗin haka. Taɓe bakinta ta yi, sannan ta shiga kicin ta kawo musu snaks da drinks Hira da ta yi daɗi daga falo suka koma cikin ɗaki suka yi ɗare-ɗare kan gado. "Wai ina angon ne? Tun da muka shigo bamu gansa ba, irin maganin da kika sha, ai kamata ya yi yanzu yana maƙale dake." Ta faɗa tana kallonta Ƙaramin tsaki ta ja sannan ta yi ƙuta ta ce,"Ya fita tun ɗazu nake jiransa amma shiru. Ni fa ina cikin damuwa, saboda gabakiɗaya hankalinsa ba shi a gareni." "To tsayawa xa ki yi kina gani ya wulaƙanta ki? Zagewa xa ki yi ki nuna masa ke wayyayace ƴar boko. Sai ka ce ba mace ba, wallahi in ni ne duk yadda zan yi ya faɗa tarkona sai na yi, saboda yadda kika shirya kanki da zarar ya ɗanɗani zumarki shi ke nan." "Ba za ku gane ba! Ya ƙi yadda ya kusanta kansa da ni. Jiya fa kulle ɗakinsa ya yi." Ta faɗa tana kallon Maryam da ta gama magana. "Yau da daddare ki ɗauki safaya na makullin ɗakinsa, kar ki shiga ki bari sai dare can bacci ya fara ɗaukarsa. Ki cire kunya mijinki ne kar ki ji shakkar yi masa komai. In kuma hakan ba ki ci nasara ba, zan siyo miki maganin tada sha'awa ki sanya nasa a cikin abinci, wanda dole shi zai kawo kansa gareki. "Ba na tunanin zai iya cin abincin da zan girka ba ku san shi bane." "Shi ke nan zana za ki yi kina kallonsa yana miki ƙwalele?" "Hmmmmmh!" Kawai ta ce musu. Ƙara zugata suka yi tare da gaya mata yadda xa ta jawo hankalinsa. Sun daɗe a gidan suna jiran ya dawo, har suka gaji suka shirya gab da magariba suka tafi. Wajnah ganin bai dawo ba ta rinƙa kirabsa amma ya ƙi ɗauka. Miƙewa ta yi bayan tafiyarsu ta shiga kicin ta ɗora abinci. Girki ta yi mai daɗi ta jera a dining sannan ta shjga wanka. Bayan ta yi wankan, ta shirya cikin wata doguwar rigar da ta matseta kuma ta yi mata kyau. Falo ta dawo ta zauna ta kunna kallo, amma hankalinta ba shi a kallon. Ganin ya ƙi ɗaukar wayarta ya santa yi masa text message. Huwais bai tashi dawowa gida ba sai gab da magariba. A wajen gidansa ya yi parking ɗin motarsa ya yi alwala ya shiga massalaci. Ko da aka idar sai ya yi zamansa yana karanta qur'ani har aka yi isha. Bayan an idar da sallar ya tuƙa motarsa zuwa ciki. Tana jin dirin motarsa ta saki ajiyar zuciya tare da leƙa shi ta windo. Tana kallonsa ya kashe motar ya fito daga motar ya nufo cikin gida. Sakin labulen ta yi, tana gyara zaman rigarta sai kuma ta ruga da sauri ta ɗauko turarenta ta fesa. Ta fito daga ɗakin daidai da ya buɗe ƙofar. "Sannu da dawowa baby." Ta furta cikin salon jan hankali tana kallonsa. Ba tare da ya amsa ba ya ƙarasa shigowa ciki. "Ya Huwai.." Ta daina kiran sunan ganin ya shige ɗakinsa. Fara diddira ƙafafunta ta y,i cikin takaici tana zaginsa a zuciya. Haƙuri ta bawa kanta ta jera abincin a faranti ta ɗauka ta nufi ɗakinsa. Da sallama ta shiga cikin falon tana riƙe da farantin abincin. Ganin ba shi a falo ya sanya ta ije abincin ta nufi ɗakinsa. Murɗa ƙofar ta yi da sallama."Ya Huwais, ga abinci na kawo maka." Ta faɗi tana kallon ƙirjinsa da ya cire rigarsa zai shiga wanka.... "Ke! Ba na hana ki shigo mini ɗaki ba? Ma za fita." "Don Allah ka tausaya mini ni fa matarka ce." Ta furta cikin muryar kuka sai kuma hawaye suka wanke mata fuska. Ƙaramin tsaki ya ja ya wuce bayi ba tare da ya ce mata komai ba. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 23 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Murɗa ƙofar ta yi da sallama."Ya Huwais, ga abinci na kawo maka." Ta faɗi tana kallon ƙirjinsa da ya cire rigarsa zai shiga wanka.... "Ke! Ba na hana ki shigo mini ɗaki ba? Ma za fita." "Don Allah ka tausaya mini ni fa matarka ce." Ta furta cikin muryar kuka sai kuma hawaye suka wanke mata fuska. Ƙaramin tsaki ya ja ya wuce bayi ba tare da ya ce mata komai ba, wanda gabin haka ya sanya ta zauna a gefen gadonsa. Bayan ya fito kai tsaye ya wuce wandrop ɗinsa, ya ɗauki kaya ya wuce bayi ya sanya sannan ya fito zuwa falo Ranta ya ƙara ɓaci, amma sai ta danne ta ɗauki abincin zuwa falon. Yana zaune da remote a hannunsa ta ije abincin ta xauna gefen shi. "Ya Huwais," Ransa ya ɓace ya juyo yana kallonta."Sau nawa xan gaya miki bana buƙatarki cikin rayuwata?" Duƙawa ta yi a ƙasa tare da ɗaga hannunta cikin muryar kuka ta ce"Don Allah ka tausaya mini ka soni, wallahi ina matuƙar sonka, kuma zan yinduk abin da zai faranta ranka." Shiru ya yi ba tare da ya tanka mata ba. Ganin haka ya sanya ta miƙe tare da ɗaukar filet ta zuba masa abinci. Duƙawa ƙasa ta yi ta miƙa masa. "Mijina ga abinci." Juyowa ya yi yana kallonta. A rayuwarsa baya ƙaunar wulaƙanta mutum, musamman mace da suke da daraja, wannan dalilin ya gargaɗeta da kar ta yarda ta shigo rayuwarsa. Miƙewa ya yi zuwa ɗakinsa saboda zuciyarsa ta fara karyewa. Ɗaki ya koma ya sanya ɗan makulli ya kwanta cikin damuwa. "Ya zan yi na manta da ke Hilah na karɓi Wajnah a matsayin matata?" Ya yi wa kansa tambayar yana sosa fuskarsa. Damuwa ta ƙara kama shi, yana jin yadda take buga ƙofar cikin muryar kuka, tana kiran sunansa. Ganin ba zai buɗe ba, ya sanya ta shiga ɗakinta ta ɗauko ɗan makullin za ta sanya, amma sai ta ji ya ƙi shiga saboda akwai ɗan makulli a ciki. Tana ta buga ƙofar da kiran sunasa amma ya ƙi buɗewa. Da ta gaji a gurin ta xauna har zuwa ɗayan dare, sannan ta tashi ta koma ɗakinta. Kuka ta fashe da shi a zuciyarta tana jin ba za ta iya jure wulaƙanci ba.Kwanciya ta yi cikin damuwa, ta kasa bacci har zuwa ƙarfe huɗu. Huwais kuwa yana jin tana buga ƙofa amma ya yi biris da ita. Jin ta daina bugawa ya miƙe ya shiga cikin bayi ya ɗauro alwala. Sallah ya fara yi yana roƙon Allah ya kawo masa ɗauki a rayuwarsa. A karo na biyu ya sake janyo wayarsa tare da yanke shawarar tura mata da texts na ban haƙuri. "Ina son ki Hilah ba zan iya haƙuri da ke ba." Ya ce tare da rubuta mata tsaƙo kamar haka. "Haƙuri da rarrashi ba za su ta ɓa wanke laifin da na aikata ba. A shirye na ke da na karɓi duk wani hukuncin da za ki yi mini tauraruwar zuciyata. Ki gafarce ni rashin haɗuwarmu, maihaifiyata ce ba ta da lafiya aka kira ni wanda ya sanya dole na je. Amma in sha Allahu zan bayyana kaina gareki. Tura tsaƙon ya yi zuciyarsa na zillo. Ya san cewa abin da yake yi bai kyauta ba, amma ya xai yi kece kaɗai wacce ya ke son ya yi rayuwa da ita. Ya furta hakan cikin damuwa. Hilah na kwance da waya a hannunta ta na yin assigment tsaƙon ya shigo. Da sauri ta miƙe tana zare ido. Jikinta na kyarma ta fara karantawa. Ta karanta ya fi sau uku sannan ta ije wayar cikin damuwa. Tura tsaƙon na sa sai ta rasa gane farinciki za ta yi ko baƙinciki. Wataƙila in ta ƙara aminta da shi ya yi mata abin da ya fi haka. "Wannan mutumin ya raina mini wayo." Ta furta cikin ɓacin rai tana ƙara karanta tsaƙon sau ba adadi. Tsaki ta yi, sai ta yi wurgi da wayar, amma kuma hankalinta na kan wayar. Tura tsaƙon da ya yi, sai ta kasa samun natsuwa a zuciyarta. Sonsa ne da take ƙoƙarin ɓoyewa ya fara bijiro mata. Hawaye masu zafi suka wanke mata fuska. Tana cikin wannan halin kiransa ya shigo. Jikinta ya ɗauki rawa tana kallon wayar har ta tsinke, amma ta kasa ɗauka. Wayar na tsinkewa ta ɗauki wayar. layin Huwais ta kira. Ganin kiran wayar ya sanya shi sakin murmushi domin dama ya xargi za ta kira. Ƙin ɗaukar wayar ya yi har sai da ta kira sau biyu. Tana gabda tsinkewa ya ɗauka. Cikin muryar bacci ta fara magana."Hello Hilah," Jin yanayin muryarsa ya sanya ta yi dana sanin kiransa. Ta manta shaf yanzu yana da mata. "Ya Huwais, mahaukacin masoyi ya kira ni." "Kin manta ina da mata shi ne xa ki kira ni da tsakar dare?" "Yi haƙuri halin da na ke ciki ya sanya na manta." Ta faɗa tare da kashe wayar ba tare da ta jira ya ce komai ba. Dariya ya yi ganin ta datse kiran. Layinta ya kira, amma har ta katse bata ɗauka ba. Ƙara kira ya yi. Tana gabda katsewa ta ɗauka. "Am sorry Yaya, ka kwanta za mu yi maganar gobe." "Ok, ki ɗauki wayar ki ji mai zaice." "Ba zan ɗauka ba zuciyata cike take da ɓacin rai na wulaƙancin da ya yi mini. Sai da safe." Ta ce tare da kashe wayar. Murmushi ya saki yana kallon wayar. Zan shigo makarantarku mu yi magana. Ya tura mata da tsaƙon ya kashe wayarsa ya kwanta. Tunani fal a zuciyarsa. Bacci ne mai ƙarfi ya kwashe shi. Hilah kuwa kasa bacci ta yi. Gani take kamar mahaukacin masoyi ya mai da zuciyarta abin wasa. "Anya da gaske yake xai aure ni?" Ta yi wa kanta tambayar haka. Kiran sallar farko ya miƙe ya shiga bayi. Wanka ya yi sannan ya canza kayansa ya wuce masallaci. Bayan ya yi sallah, ya zauna a masallacin yana karatun qur'ani har gari ya yi sha, sannan ya miƙe ya shigo ciki. Falo ya sanya karatun qur'ani ya wuce ɗakinsa. Kan gadon ya hau ya ja bargo. Bai farka ba sai ƙarfe tara, ya yi wanka ya shirya. Falo ya fito daidai lokacin da Wajnah ta ƙara shigowa. "Ina kwana Ya Huwais?" Ba tare da ya amsa ba ya nufi hanyar fita yana gyara hularsa. "Don Allah ka tsaya ka ci abinc..." Maganar ta tsaya ganin ya fice.Maigadi ya wangale masa get ya fice. "Ka gama guje-gujenka dole ka shiga hannu tun da aka ɗaura ai an yi mai wuyar. Ba ka da matar da ta wuce ni. In sha Allahu ni ce uwar ƴaƴanka." Ta furta tare da sakin labule ta shiga kicin. Karyawa ta yi sannan ta ɗan gyara gidan ta yi kwanciyarta. Wayarta ta ɗauka ta hau online suka fara hira a group ɗinsu. Nan kowacce ta fara kawo rayuwar gidanta da abin da mijinta ya yi mata suna dariya suna shewa da tsinewa rijalu. Maigadi yana buɗe masa get ya shiga cikin gidan. Ganin Abu da jaka a hannunsa da alama gurin aiki xa shi ya sanya shi fitowa da sauri. "Ina kwana Abu." Ya ce yana kallon Ummu da ta fito daga ciki hannunta riƙe da ƙaramar wayar Abu da alama ya manta da wayar ne ta ɗauko masa. "Ina kwana Ummu?" "Lafiya lau, ya kwanan Wajnah?" Ta yi masa tambayar cikin sakin fuska. "Tana lafiya." Ya ce yana kallonta. "Abu, fita aiki za ka yi?" "Eh, amma da ma ina son magana da kai. Tun da ka zo mu koma ciki mu yi maganar." Gabansa ne ya faɗi a tunaninsa ƙararsa Ummu ta kai na zaman gidansa. "Ok," Ya ce tare da bin bayansu ganin sun juya za su shiga ciki. Abu ya yi gyaran murya ya ce,"Game da ƴar'uwarka Hilah." Gabansa ne ya ƙara faɗi tun bai san mai ya faru da ita ba. "Tun da ka yi aure, sai muke ganin ita ma ya kamata mu ɗaura mata aure da Hamad, in ya so sai ya kama mata gida a Kaduna har ta ƙarasa karatu..! Zubbur ya miƙe yana xare idanu cikin tashin hankali. "Aure Hilah?" Ya furta cikin ɗaga murya wanda ya tabbatar nusu da zarginsu. Ummu ne ta kalli Abu, sannan ta kalle shi da yake share zufa da ke keto masa. Jijiyoyinsa suka miƙe yana jin wani tashin hankali na ziyartarsa. "Abu, kan me xa a yi mata aure bayan ba ta kammala karatun ba?" "Saboda gaka ya kamata. Kuma ya kamata mu tausayawa yaron nan, tuntuni yake jiran ta kammala ba tare da ƙorafi ba. Yanzu semester biyu ya rage, ai karatu ya zo ƙarshe." "Gaskiya bai kamata ayi mata aure ba, saboda za dakusar da karatunta. Kuma Hilah ɗin ba ta da ra'ayin haɗa aure da karatu. Don Allah ku yi haƙuri har ta kammala karatunta." Ya furta kamar xai yi kuka. "Ita ta gaya maka haka? Ka san irin son da Hilah ke yi wa Hamad. Ko bakinta za ka ara ka ci mata albasa?" "Hilah ba ta son Hamad, ni na sani sam ba ta ƙaunarsa." "Ko ba ta sonsa, dole ta aure shi mun sanar maka ne a matsayinka na ɗan'uwanta." Tashin hankali ya ninku a fuskarsa idanunsa suka firfito ji yake kamar zai yi hauka. "Kai ina!Hilah tawa ce ba za ya taɓa auren wani ba ni ba." Ya ce aransa yana firfita da hannunsa. Abu ne ya miƙe ganin yadda ya riƙice ya kasa cewa komai. "Ni zan wuce ofis kar na yi latti. In sha Allahu yau zan yi wa mahaifin yaron magana." "Abu, ka bari ka ji bakinta.." "Babu wani bakinta da za mu ji ai ta san da maganar aurensu." Ummu ta faɗa. Miƙewa ya yi, yana jin kamar ƙasa ba zata iya ɗaukarsa ba. Siraren hawayen da suƙe ƙoƙarin saukommasa yake son mayarwa. Gfen hannunsa ya sanya ya share hawayen Ba tare da ya ce musu komai ba ya miƙe xai fita, saboda in har ya yi magana za su fahimci halin da yake ciki. Binsa da kallo suka yi ganin yadda yake tangaɗi kamar zai daɗi. "Na gaya maka wallahi wannan mahaukacin yaron sonta yake yi. Gara mu yi mata auren shi ne kawai sanun kwanciyar hankalinmu.". "Ummh! Biri ya yi kama da mutum." Abu ya ce cikin tsananin mamakin halin da ya shiga. Huwais na fitowa ya shiga cikin motarsa. Kifa kansa ya yi kan sitiyarin motar. Wasu irin zafafen hawaye suka sauka a ƙuncinsa. Ba tare da ya share ba ya kunna motar ganin maigadi ya buɗe masa ƙofa. Sai da ya yi nisa da gidan sannan ya faka motar ya tsaya. Hawaye ke bin ƙuncinsa yana jin tashin hankalin na ƙara ninkuwa.. "Ba zan taɓa barin ki auri wani ba matuƙar ina raye. " Ya furta tare da duka sitiyarin motar. "In har ba zan aure ki ba mai ya sa ba ke son ki?" Ya yi wa kansa tambayar cikin tashin hankali. "No, Hilah tawa ce an halicce ta don ni. Matuƙar ban aure ta ba sai na kashe duk wanda ya aureta." Ya furta hakan tare da figan motarsa aguje. Ikon Allah ne kawai ya kaisa gida. Hon yake yi babu ƙauƙautawa. Da sauri maigadi ya buɗe masa get yan kallonsa. Gaisuwar da ya yi masa bai amsa ba ya buɗe motar ya shiga cikin gidan. Ko motar bai kulle ba ya shiga gidan. Wajnah da ke zaune tana kallo da saurinta miƙe. "Ya Huwais, lafiya?" Ta yi masa tambayar ba tare da ya kula ba ya wuce ciki. kai tsaye bayi ya shiga ya kunna shower. Ga mamakinsa sai ya ji wasu irin zafafen hawaye suna sauka daga ƙuncinsa. Ya daɗe yana sakarwa kansa ruwa, har sai da ya ji ɗan dama-dama a zuciyarsa sannan ya fito ya sanya kaya. Key ɗin motarsa ya ɗauka ya fito falo. Wajnah da ke tsaye hankalinta a tashi tana jiran ya fito ta sha gabansa. "Matsa ki ba ni guri!" Ya furta cikin kakkausar murya. Da sauri ta kalle shi jin muryar da ya yi amfani da ita. Tsoro ya bayyana a fuskarta, amma sai ta dake. "Don Allah ka sanar da ni abin da ke faruwa. Ni fa matarka ce dole na damu da lamarinka." Jin abin da ya ce ya sanya yaja tsaki tare da tureta xai wuce. Gefen rigarsa ta ja cikin ɗaga murya ta ce,"Dole sai ka gaya mini abin da ke damunka, ai ni matarka ce ina da haƙƙi .." Maganar ta maƙale mata, sakamakon marin da ta ji ya wanke ta da shi, wanda ya sanya ta sake shi da sauri tare da dafe ƙuncinta. "Marina fa ka yi?" Ta furta cikin muryar kuka. "Abin da yafi mari xan yi miki matuƙar kika ƙara yunƙurin dakatar da ni." Ya furta cikin ɓacin rai xai fice. Wani irin ƙara ta saki saki ta ruga da gudu cikin ɗakinta. Tsaki ya ja yana kallonta."Wawiya kawai!" Ya furta sannan ya murɗa ƙofa ya fice. A hanya tafe yake yana tsaƙa da warwara. Gani yake sam iyayensa ba su yi masa adalci ba, amma kuma in ya tuna lamarin da yake shirin ibo ma kasa sai ya ji damuwa sosai. Shi kansa ya sani ihu yake bayan hari. Ko da ace ba a yi wa Hilah aure ba, ba shi da damar da xai bayyana yana sonta. Wayarsa ya ɗauka da ya sanya a caji. Numbar Hilah ya nemo sannan ya danna kira. Hilah da ta fito daga lectured kenan suna tafiya da Affrin za su je Cafateria. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 08144072423 '*RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 24 Jin wayarta na ringing, ya sanya ta buɗe jakarta ta ɗauko. Ganin Huwais ne, sai ta tsaya tare da danna gurin kiran, ta kanga ta a kunni. "Hello Yayana." Ta furta da muryarta da ya bayyana, tsantsar gajiyar da take ciki. Jin muryarta ya sanya shi rintse idanunsa, yana jin wani abu yana yawo a kwanyarsa. "Hilaaah, kina ina?" Ya yi mata tambayar tare da jan sunanta. "Ina school mun gama lectured zan nemi abinci." "Ok, ki yi ma za ki ci abincin zan jira ki a bakin get ina kan hanyar makarantarku." Daɗi ta ji a ranta sosai, dama tuntuni take son ya sanar mata da ranar da za su huɗu. "Ok, sai ka zo amma Yaya lafiya kake?" "Lafiya lau." Ya ce mata tare da kashe wayar yana sauke numfashi. Bin wayar ta yi da idanu, tamkar za ta ga abin da ke damunsa a wayar. "Ya Huwais, ne ya kira ni yana kan hanyar zuwa makarantarmu. Mu yi sauri na mu ci abincin kafin yazo." "Yayanki yana matuƙar ji dake. Ina ma ace ni ce na samu wannan gatar. Na ɗauka zai canza in

Chapter 16 of 17