tsaƙon?" Abu ya ce masa yana waige-waige tare da kallon tsadadiyar motar cikin tsananin mamaki.
"Ranka ya daɗe, bayan ya gaya mini sai na je na gaya wa Hamsiya, kafin na dawo na neme shi na rasa kamar aljani."
Mamaki ya ƙara kamasa sosai yana mamakin ace wanda ya kawo irin wannan tsaƙon ya ƙi bayyana kansa.
"Ikon Allah!" Ya ce cikin mamaki tare da juyawa ya koma ciki wanda ya same su cirko-cirko ban da shi da yake ta cin abinsa hankalinsa kwance.
Zama ya yi kan kujera domin ya ji abincin ya gimshe shi.
"Ɗan tsaƙon ya tafi." Ajiyar zuciya ya saki domin ya ɗan ji fargabar kar su kama wanda ya turo, amma jin hakan sai hankalin shi ya kwanta tamkar ya yi baƙo ya mutu.
"Waye wannan ya yi mata wannan kyautar! Ke Hilah kin san shi ne?" Ummu ta jeho mata tambayar da ya sanya ta ɗago a razane tana girgiza kanta.
"Magana za ki yi mini ba girgiza kai ba, ko kin zama kurma ne? Ai na lura tun da aka gaya tsaƙon kika ruɗe. Uban me kike ɓoyewa."
"Um ni wallahi babu! Dama an um!" Ta shiga faɗin haka sai kuma ta fara in-ina sai ta saka kuka, wanda hakan ya sa ta zargeta ranta ya ɓace.
"Za ki rufe mini baki daga magana sai kuka ke ga ki mai fuskar kuka ko!" Ta daka mata tsawa tana faɗin hakan, wanda ya sanya ta haɗiyar kukanta cikin tsoro, don tsawar harta sauran 'yan'uwanta sai da suka razana.
"Haba Laila, ki yi mata a hankali."Abu ya ce tare da kamo hannunta ya zaunar da ita kusa da shi.
"Kin san shi ne?" Ya tambayeta cikin tautausar murya.
"Eh! A'a." Ta ba shi duka amsar cikin rawar murya sai kuma ta ɗora da cewa,
"Da ma ya turo mini da tsaƙo kwanakin baya da kyautar miliyan ɗaya sai kuma ranar da musabaƙa ya tura mini tsako, amma wallahi ban taɓa ganin shi ba." Ta ce cikin kuka.
Mamaki ya kamasu ƙwarai Ummu har da salati tana tafa hannu.
Ganin yadda suka ruɗe sai ta ci gaba da gaba da magana cikin inda-inda,"Na gaya wa Huwais, shi ne ya ce kar na sanar muku." Ta ce tana kallonsa cikin jin haushin komin kula da ya nuna kan lamarin ga shi an tsareta an tambayarta ko a jikin shi.
"Innalillahi! Yaushe kuka girma har kuke yanke shawara iya kanku? Huwais, shi ya haife ki, na ga dukkaninku ikonmu ne, amma ba ku sanar mana ba?" Ta ce cikin zafi zata mare ta wanda ta ɓoye cikin sauri bayan Abu tare da dafe ƙuncinta tana kuka.
"Karki taɓata ga babban kwabo nan, duk da cewar shin a yaro bane, wataƙila yana da dalillinsa."
"Dalilin me Abu? Wanda zai kasa sanar mana ai duk ƙarƙashinmu suke hakan da suka yi koyi suke yi wa na bayansu." Ta ce tana harararsa cikin zargi.
Shiru ya yi kamar babu ruwan shi, ko bai san da zancen ba." Ya ce yana hararsa wanda sai a lokacin ya ije.
"Ni fa ba da wani nufi na yi ba kawai na gaya mata ne, saboda ganin yadda ta tada hankalinta, kuma a lokacin gab da musabaƙarsu ne. Ba na son ta tada hankalinta ya sa na gaya mata hakan, dama na san in har da gaske ya ke yi zai ƙara tura tsaƙon."
"Wannan ba hujja bace Huwais, ya kamata komai na ku mu sani, domin mun cancanci mu sani."
"Ku yi haƙuri mun yi kuskure." Ya ce yana kallon Ummu da take masa wani kallo don gabakiɗaya ba ta yadda da shi ba.
"To yanzu mene ne abin yi?"Abu ya tambaye sa cikin rashin dubara.
"Ban sani ba mu jira lokaci, in dai ba aljani bane, dole ya bayyana kansa tun da babu wani identity na sa, da zamu mayar masa da kuɗin." Ya ce musu yana kallonsu.
"Ai ya makaro ko ma waye, domin Hilah na da masoyi kuma na yi na'am da shi, sam ba ta da wani miji sai shi." Ummu ta ce cikin ɓacin rai!
"Hilah tawa ce don in ina raye babu wanda ya isa ya mallaketa sai ni, domin kanta zan iya zama makashi ko ɗan dan daba Ummu. Ki jira lokacin da zan bayyana kaina na yi yaƙi da duk wanda zai hana ni mallakarta." Ya ce a ransa amma a fili bai ce komai ba sai ya fice daga falon wanda Ummu ta raka shi da idanu hankalinta a tashe.
Ganin ya fita sai haushinsa ya kamata domin bai taɓa ɓata mata rai ba irin yau. Ɗakinta ta shige ta kulle ƙofa tare da faɗawa kan gado ta sakin kuka.
"Wane ne wannan mahaukacin masoyin da yake so ya kawo mini rashin zaman lafiya da iyayena? Domin irin kallon da Ummu take mini ya girgiza ni." Ta ce cikin damuwa.
"Anya mutumin nan ya san ciwon kuɗi ji motar da ya kawo mini da waya? Zuciyata ta fara zargin ɗan shan jini ne ko mai safarar mutane." Ta ce cikin ruɗani.
Tana kwance kiran Hammad ya shigo wanda har sai da ya yi ringing uku sannan ta fahimci ana kiranta ta ɗaga. Jin yadda take amsa masa ya fahimci ba ta cikin hankalinta ya yi mata sallama ya kashe wayar, wanda ita ma jifa ta yi da wayar ta kifa kanta kan filo tana mai da numfashi.
A haka ta wuni sukuku lokaci guda ta ji ta ƙara zaƙuwa da ta ga wannan mahaukacin da ya kamata a kaisa Dawanau.
Ko da ta zo bacci duk iya satar bacci a wannan lokacin sai dai ya ganta ya haƙura, domin idanunta sun soye tamkar an soya gyaɗa mai gishiri
Ta yi juyin har kan kujera ta dawo ta kwanta amma gwanin satar ya kasa sace ta.
Duk da cewarta ba mai son rayuwar social media ba ce, don sai ta haɗa sati ba ta hau whatsapp ko facebook ba in dai ba relevant abu za ta duba ba. Don ita ba ta ɗauki wannan platform amatsayin wanda zai ɗauke mata kewa ba, sai dai amfani da shi da wasu gwara gurbin mutane suke yi suna watsa alfasha da ƙarerayi. Duk da cewar ko wane abu akwai merits ɗin sa da demerits ɗinsa.
A wannan lokacin ta tsinci kanta da son hawa whatsapp musamman da ta tuna Muktar classrep ɗinsu ya gaya mata ya tura houndout that is meaningfull.
Sai ta tsinci kanta da kunna datar wanda a lokacin ƙarfe ɗaya da rabi daidai. Tana buɗewa ta fara duba tsaƙon
Huwais dake zaune idanunsa babu bacci ko kaɗan. Bayan ya kammala ayyukansa ya tura musu sannan ya kashe lap ɗin ya koma kan gado ya kwanta tare da jan bargo.
Tunanin halin da ta shiga lokacin da scene ɗin ya faru yake yi. Mamakin iya basarwa na sa ya nuna tamkar bai damu da lamarin ba ya kama shi, wanda a wannan lokacin Allah kaɗai ya san halin da yake ciki, domin da ace Abu ya ɗan matso kusa da shi sai ya fahimci halin da yake ciki. Sai dai Allah ya taimake shi Ummu ne kawai ya ɗan zargi wani abu domin ta san shi fiye da kowa.
Sai ya ƙara tasbihi ga Allah, da ya rufa masa asirin domin da sun gane wata maganara ake ba wannan ba. Ya san an riga an yi disowning ɗinsa agidan duba ga wutar da yake so ya kunna a gidan.
Ɗaukar wayarsa ya yi ya kunna data wanda yake son ko bacci ya kama shi.
Da yake gb whatsapp yake amfani fa shi. Yana hawa ya ga an rubuta; little sis online. Wanda matuƙar mamaki ya kama shi domin a iya tarihin rayuwarsa sam ba ta hawa online da daddare ko assignment za ta yi tana ɗauko wa ne tun kafin dare, ballanatana wannan lokacin da yake ƙarfe biyu vai wuce awa ɗaya ta tashi ta fara haddarta ba.
Ɗayan wayar da yake tura mata tsaƙo ya ɗauko can ƙarƙashin gadonsa tare da kunnawa ya kunna data.
Sallama ya yi mata wanda ya matuƙar razanata, a lokacin da ta ga tsaƙon ganin an ɓoye lambar ya sa ta gane ko wane.
"Matar mahaukacin masoyi! Ba ki yi bacci ba, mai kike yi a wannan lokacin? Wataƙila kuma soyayyata ce ta fara kama ki, kamar yadda ta hana ni bacci sai tunaninki nake yi." Ya turo dogon tsaƙo kamar haka.
Tsoro ne ya fara kamata domin tana tunanin anya ba aljani bane? Dama ance suna soyyaya da mutane ko ita ma hakan zai faru da ita? Saurin kawar da tunanin nan ta yi, domin a yadda take addu'a ta san in sha Allahu babu Aljanin da zai iya wasa da rayuwarta.
"Waye kai kuma mai ya sa kake ɓata lokacina?" Ta yi masa tambayar cikin haushi.
"Da sannu za ki sanni ki kwantar da hankalinki. Domin watarana zamu yi aure na kwantar dake a ƙirjina ina miki fifita. Wannan pinky libs ɗin ki zai zama sweet ɗina."
Kunyar abin da ya faɗa ya sa ta rintse idanunta tare da kawar da wayar tana mamakin lailai bayan zama mahaukaci tantiri ne shi.
"Aiko ka yi kuskure domin zuciyarka yaudarar ka take. Ina da wanda zan aura don haka maza ka zo ka karɓi tsiyarka don ka san ko ni ina da kuɗin da zan siya duk abin da kake tunanin za ka iya siyata da shi."
"Ina! Ke ɗin tawa ce ni kaɗai duk wanda ya yi gigin shiga gonata. Ina miki albishirin zan kashe shi na kuma kashe kaina."
Miƙewa ta yi da sauri sai ta kashe datar ta tura wayar can tsaƙon filo domin wani irin tsoro ne ya kamata.
Ta fara karanta addu'a tana son ta yi bacci don ta fara jin tsoron shi, amma idanunta sun bushe tamkar tekun da ya ƙafe da bazara.
Huwais kuwa ganin ta sauka sai ya tabbatar da maganar da ya gaya mata ne ya ruɗata wanda ya san yanzu tana nan cikin tashin hanakali saninta muguwar matsoraciya ce.
Dariya ya yi sosai har yana buga filo, ya sannan ya rungume wayar yana kallon hotonta yana murmushi.
Mamakin jawo wayarta da ta yi ta kuma kunna datar ta yi.
Ganin bai yi mata magana ba sai ta tsinci kanta da tura masa stiker na gargaɗi.
Yana ganin lokacin da ta hau online ɗin shareta ya yi, ya ƙyaleta domin ta sauka ta yi karatu ganin uku daidai, amma da ta tura masa da hakan sai ya turo mata da ma soyayya.
"Ki kular mini da kanki kuma ki tashi kiyi sallah ki yi istikhara kan lamarin." Ya kashe wayar.
Ba tare da tunanin dare bane ta lalubi numbar Huwais ta kira domin ta tabbata zuwa wannan lokacin ya tashi yin sallah.
Yana ganin kiran ya saki dariya tare da ɗaukar wayar ya yi shiru na ɗan lokaci. Jin shirun ya sa ta fara magana.
"Ya Huwais ya yi mini magana ta whatsapp, amma ya ɓoye numbarsa still. Mutumin nan ya raina mini wayo sosai. Ya yi magana da ni sanda ya ga dama ya turo mini da presents ɗinsa alokacin da yake so.
"To shine za ki tashe mi ina tsaka da baccina kan wani mahaukaci can masoyinki! Kar fa ki manta mahaukaci ne shi." Ya ce mata cikin fusji da kuma muryar da ya yi kamar daga baccin yake.
Jin abin da yace ya ɗan sa ta tsorota domin bai cika bayyana fushinsa ba, musamman a kanta.
"Am sorry. Na kasa haƙuri safiya ta yi." Ta ce kamar yana ganinta sai kuma ta tsinci kanta da jin haushin cewa mahaukacin da ya yi, wato itama mahaukaciya ce tun da ta biye masa.
Tsaki ya ce, "Me kike yi a wannan lokacin ma za ki tashi kiyi sallah ki yi hadda, kina jina da safe za mu yi maganar, kuma ina son ki cire wannan maganar a ranki."
"Ai ban sa a zuciyata ba. Hammad nake so kuma shi zan aura mai zan yi da mahaukaci." Ta ba shi amsa domin tunaninta kar ya ɗauka ko ta fara sonsa.
Ya ji babu daɗi tun da shi ya jawa kansa sai ya ɓoye kishinsa ta hanyar cewa,"Ok, shikenan. Wataƙila a gida ba zamu samu damar yin magana sosa ba, ki shirya in sai na kaiki school."
"Ummi ba za ta barni na hau motar haya ba, ko na ce mata motata ta lalace za ta ce na ɗauki nata ko na Ya Naufal. The worse part ɗin ma za ta iya saka direba ya kai ni. Zan fita da motata sai na jira ka gaba da gidanmu."
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 6
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Ummu, ba za ta barni na hau motar haya ba, ko na ce mata motata ta lalace za ta ce na ɗauki nata ko na Ya Naufal. The worse part ɗin ma za ta iya saka direba ya kai ni. Zan fita da motata sai na jira ka gaba da gidanmu."
"Yauwa haka ma yafi kai waye, kin ga sai na dawo a ta haya, kuma zamu fi samun natsuwa domin akwai shawarar da nake son na baki. In a gida ne ba zamu samu damar zantawa sosai ba. Ni kam na rasa mai ya sa Ummu ke son sanya shamaki a tsakaninmu!" Ya yi maganar cikin tsananin fushi da damuwa.
"Wataƙila tana da haujjar hakan, kuma ita uwace dole ta kula da amanar da Allah ya bata." Ta gaya masa hakan.
"Wataƙila ta gano soyayyar da nake miki tana tsoron abin da zai je ya dawo ne." Ya faɗa a ransa wanda har ya fara tunanin ko a fili ya faɗi hankalinsa ya tashi, amma sai ya ji ta yi ajiyar zuciya ta ce,
"Tom Allah ya kaimu bari na tashi na yi karatu ga shi har past three." Ta miƙe da nufin shiga bayi ta ɗaura alawala.
"Ok, bye." Ya ce tare da kashe wayar.
Bayan ta yi karatun ta yi sallar asuba ta zauna ta ci gaba da karatu. Tana ƙoƙarin miƙewa sai Ummu ta tura ƙofar ta shigo hannu ta riƙe da carbi.
"Ina kwana Ummu." Ta ce tana mamakin zuwanta duk da ta sa baya wuce ta yi mata ƙorafin kalacin safe, amma ai ta shi da wuri.
"Lafiya kau." Ta amsa a daƙile sai ta ɗora da cewa,
"Na zo kiji tsoron Allah ki gaya mini wane ne mahaukacin masoyi? Domin zuciyata ba yarda da ku biyun ba, kamar a kwai abin da kuke ɓoyewa."
Zare ido ta yi tana mamakin kalamanta da abin da za su iya ɓoyewa don ba ta fahimci komai ba.
"Ummu wallahi babu komai da muke ɓoye wa kuma kamar yadda ma gaya muku initially, bayan kyautar da tsaƙon da ya turo mini na farko babu komai tsakaninmu." Ta ƙarashe maganar za tai kuka.
"Idan hawayenki ya zuba saina tsintsinka miki mari! Shashashar banza, da an yi miki magana sai ki ce za ki yi kuka kamar ke kika fi kowa hawaye. Allah Ubangiji ya sa na ji wata maganar bayan wallahi dake da shi sai ranku ya ɓace. Kuma ba ki da miji sai Hammad. Ni uwa ce ina da ikon zaɓa miki wanda za ki zauna da shi. Allah ya sa mahaukacin masoyi duniya zai baki ko ya bayyana na haramta miki aurensa matuƙar ina raye."
"To Ummu, ai dama ina son Hammad ɗin ba zan iya rabuwa da shi ba." Ta ce da sauri don ta kwantar mata da hankali ganin yadda ta fusata da lamarin
"Gargaɗi nake miki ai." Ummu ta faɗa a ranta ta ji daɗin abin da ta faɗa.
Bayan ta kammala ta shirya ta sanar masa da ta gama shiryawa.
Ummu dake falo ta fito ta same ta tana karwa ..
"Ummu zan wuce school sai na dawo."
"Ki dawo lafiya." Ta ce fuska a ɗaure.
Tana ƙoƙarin fita Huwais ya yi sallama ya shigo, gaishe shi ta wanda ya amsa ko kallonta bai yi ba ya shiga cikin falon ita kuma ta wuce.
Ummu ta amsa gaisuwarsa, tana kallon yadda ya yi kyau sosai ya ƙara zama wani handsome da shi. Kallonsa take cikin tsananin ƙaunar ɗan nata ganin yadda girma da kamala ya kama shi.
"Ummu zan fita ni da abokina doctor Khair, ba zan daɗe ba."
"Ok, ba komai sai kun dawo amma ga su Umnaah sun shirya ka wuce dasu school."
Da sauri ya kalle ta jin abin da ta ce ganin tana son ɓata masa shiri.
"Ba da mota zan fita ba don Allah Abidin ya yi mafani da motata ya kai su fita ce ta gaggawa, in tashi babu mai."
Kallonsa ta yi cikin rashin yarda da maganarsa.
"Anya kai ɗinne za ka fita ba da mota ba? Ko dai da inda za ka kake ɓoye mini?Domin ma san in dai ba lalura ba ba ka ko iya fita in ba a abin hawa ba."
"Ummu a ƙofar gida zan jira shi yanzu haka ya ce miniti biyar zai ƙaraso."
"Ai sai ku wuce da su Khair baƙo ne ƙanninsa ne." Ta ce mishi.
"Don Allah Ummu ki sa Naufal ko Abidin ya kai su bari na je kinga har ya ƙaraso yana kirana." Ya ce tare da saurin ficewa ba ya ji abin da za ta ce ba.
Yana fita sai ta ji ba ta yi na'am da maganarsa ba.
Hamsiya ta ƙwala wa kira wanda ta fito ta durƙushe a ƙasa tana jiran umurni.
"Ma za ki bi Huwais ya fita ki ga wa zai ɗauke shi a mota. In kika bari ya ganki sai na ɓata miki rai."
"To." Ta ce tare da fita da sauri.
Sai da ya yi nisa sosai ya hangeta a lokacin tana ƙoƙarin kiransa ganin ya buɗe motar ya shigo ya sa ta yi murmushinta ja motar.
Hamsiya da take bin bayansa tana raɓewa a jikin gini, sai da ta ga ya hau motar da ta tabbatar na Hilah ce ta koma gida tana mamakin dalilin da ya sanya ta ce ta bishi, kamar wani ƙaramin yaro da dalilin da ya sa bai shiga motar ba, sai da suka fito waje. Taga ita ɗin 'yar'uwarsa ce ta jini. Tunanin kuma irin ɗan takurawa mata da take yi ya ɗan faɗo mata, amma kuma da ta tuna ƙaton enlergment na hotonsu da suke tun yarinta wanda ita Hilah, a lokacin har da na jarintaka, sai ta cire komai kamar yadda dama ba ta wani zargi komai ba.
"Motar Hilah ya shiga wacce take ta jiransa tun da ta fita." Ta bata amsa wacce jin hakan sai da ta yi suman wucin gadi.
"Amma yarannan sun yi masifar raina mini wayo.Huwais, za ka ja wannan karon ka yi tafiyar da harbabada ba za ka dawo ba, domin inta yi ƙamari zan yi maka aure na turaka Ƙasar waje tare da yi maka baki matuƙar ka dawo Ƙasar. Domin abin da kake shirin yi tamkar so kake ka ruguza farincikin iyalina. Ban taɓa ji ko a mafarki an taɓa soyyaya da ƙanwa ba." Ta faɗa tana wani irin zafafan hawaye yana bin ƙuncinta a ranta ita kaɗai ta san abin za ta yi musu in suka dawo.
Hilah ta juyo tana lallonsa da yake kallon waje ganin ya ƙi magana kuma har ta kusa kai get ɗin da za ta shiga makarantar su.
"Ya Huwais, ka yi shiru na zaƙu na ji shawarar da ka yanke." Ta ce mishi tare da shan kwana.
"Jiya na yi mafarkin mahaukacin masoyi kuma har an nuna mini shi a mafarki." Ta ce tana kallonsa ta gefen ido.
"Kim gane shi?" Ya jeho mata tambayar cikin mamaki.
"A'a na gane wasa da hankalina kawai yake son ya yi, saboda na yi ta mafarkin shi ina ɓata lokacina.
"Yauwa kin jina?".
Ɗaga masa kai ta yi ba tare da ta kalle shi ba.
"Na ce mu yi wani abu mana shi mahaukacin masoyi ki nuna masa kin amince da soyayyar shi, domin ta haka ne kawai zamu iya gano wane ne."
Da sauri ta kalle shi jin abin da ya ce sai ta ci gaba da tuƙi ba ta ce komai ba.
"Akan me zan fara soyayya da wanda ban sani ba ko aljani ne, musaki ne duka ba ni da matsaniyar hakan?"
"Ni ma ai ba wai son gaskiya nake nufin ki yi masa ba. So nake ya yarda kina sonsa har ya bayyana kansa." Ya ce mata yana kallonta.
"A'a, wannan ba mafita bace." Ta ce tare da kallonsa sai ta mai da hankalinta kan tuƙi ta ci gaba da cewa,
"Hakan ba mafita bane ina tsoron kar na ƙara amincewa, abu ya kwaɓe ka zo ka barni a ciki irin wancan. Kuma Ummu yau ta yi mini kashedi mai ƙarfi kan ko waye kar na kuskura na amince masa. Don haka mu bar maganar in ya gaji da haukarsa zai daina. Da zarar na kammala karatuna na yi aure ai dole ya haƙura ya zo ya karɓi kayansa ko?" Ta ƙarashe maganar tana tambayarsa.
"Over my dead body! Ke tawa ce kuma an halicce ki saboda ni." Ya faɗa a ransa ganin kallon da ta tsaresa ya ba ta amsa da cewa,
"Mu gwada hakan wataƙila ma dace. Kuma na yi miki alƙawarin a duk lokacin da lamarin ya kwaɓe zan karɓi hukuncin duka."
"Promised?" Ta tabbaye shi.
Ɗaga mata kansa ya yi wanda ya sa ta ce,
"To shikenan zan gwada. I will do as you said." Ta ce daidai lokacin da ta ƙaraso ta yi paking tare da kashe motar tana kallon shi.
"Yauwa ƙanwata. Ma za ki shiga aji bari na koma gida."
"A motar haya? Na san fa ba ka son hawa. Kawai ka je da motata sai ka sanya direba ya kawo mini amma a waje za ka ije karka shiga ciki da ita saboda Ummu."
"Mai zai kai ni bayan na san ƙaryar da na shara mata." Ya ce yana dariya.
Tsayawa ta yi har ya tada motar ya fara tafiya, sai ta ɗaga masa hannu tana kallonsa cikin tsananin ƙauna. Tana son yayan nata don ya damu da lamarinta. Rungume laptop ɗinta ta yi ta shige departmen ɗinsu.
A lokacin da ya dawo, Ummu ba ta ce masa komai ba har ya ci abinci ya fita. Don ma ƙin fitowa ta yi ko da ya tambayeta tana bacci.
Bayan Hilah ta gama lectured ta tuƙa motarta ta dawo gida.
Ta shigo da sallama tana kallon su Umnaah dake zaune suna kallo.
Gefen su ta zauna bayan sun yi mata sannu da zuwa.
"Ke Azerh ba kin ce Malamin kunya gaya miki in har ba ki kai masa haddarki ba zai zane ki, shi ne kika tsaya kallo?"
"Ƙyale shi Anty Hilah, ya cika takura haka jiya na ƙi ƙallah don na yi haddar, amma da na kai masa cewa ya yi ba ta zauna ba. Duka ne ya saba mini, don maimaici ne in ban kalla ba ya wuce."
"Lailai haka kika ce? Ai ko kya ta shan duka kamar jaka." Amnaah ta ce.
"Allah ya shiryeki, wasa kike yi wa haddar shi ya sa, randa kika yi ninya ai tana zama." Ta ce tare da miƙewa za ta shige ɗakinta daidai lokacin Ummu ta fara saukowa ƙasa wanda
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 17