Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shawara sai ka jira lokaci ya yi. Ka sani a wannan karo. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 9 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Mun riga mun gama yanke shawara sai ka jira lokaci ya yi. Ka sani a wannan karon sam ba zan lamunta ka watsa mini ƙasa a idanuna, don haka ba za a sanya lokacin bikin da tsawo ba, saboda in har muka biye maka, ban san lokacin da za ka yi aure ba, kuma kullum ƙara girma kake." Ajiyar zuciya kawai ya saki ba tare da ya furta komai ba, sai kaɗa kansa da yake kamar ƙadangaren kutu. "Maganar aikin da za ka fara a companyna ya kamata ka fara shirye-shiyen duk da kai za ka zama c.e.o na wurin. Cikin rashin ƙarfin jiki ya amsa masa wanda ganin yadda ya yi, sai ya ba shi tausayi, amma yi masa auren shi ne kawai mafita a gare shi da su duka, musamman Ummu da kullum take ta da hankalinta. Shiru suka yi babu wanda yake magana har suka shawo kwanan gidan. Huwais hankalinsa a tashe yana ta tsaƙawa da kwancewa. Idanunsa suka kaɗa sosao ji yake kamar ya ɗora hannu a sama ya rinƙa ƙwala ihu. Tunaninsa yadda zai yi rayuwa da wata ƴa mace a matsayin matarsa ba Hilah ba, domin ba ya jin zai iya mallakawa wata gangar jikinsa da zuciyarsa, don an halicce su saboda ita ne, domin matuƙar ta aminta da aurensa aka yi. To tamkar ta siyar da farincikin rayuwarta ne, don gangar jikinsa kawai ta aura, amma zuciya da ruhi suna gurin ƙanwarsa abin begensa, wacce da ita kawai yake jin zai iya rayuwa har ya shayar da ita madarar ƙauna. Abu kuwa bayan ya sanar masa bai ɓata lokaci ba, ya kira Kawu Sule kamar yadda ya gaya masa aka tura don a tsayar da rana. Wannan lamari ya yi wa Wajnah daɗi, domin da fari ta ƙi aminta sai take gani kamar mafarki ne. Lokaci guda kuma murnarta ta koma ciki tuna, wancan lokacin da har an sanya rana ya bar ƙasar, saboda haka sai ta rage murna ta bari sai ranar da ta wayi gari ta ganta a cikin gidansa. Tabbas ranar babu macen da ta kai ta sa'a a duniyar nan. Sai ya rinƙa jin kasa kamar zai rabu gida biyu. Yana isa cikin ɗaki ya faɗa kansa. Wani irin ƙunci yake mamaye zuciyarsa, ganin duk guje-gujen da ya yi wa auren bai hana yi ba. Kwanciya ya yi yana jin ransa babu daɗi don ƙirjinsa har wani fat!Fat! ya ke yi tamkar za ta fito waje. Kawu Sule a ranar ya shirya aka je suka ji magana wanda nan take aka tsaida biki wata ɗaya. Gabakiɗaya kowa murna yake yi in ka ɗauke uban gayyar. Zaune suke a dining ana cin abinci inka ɗauke Huwais da yanzu ya yi sallama ya shigo. Sallamarsa ya sanya Hilah da take bawa Umnah abinci a baki ta ije spoon ɗin tana kallonta da ya shigo fuskarsa tamkar ta shanu. Ummu kuwa murmushin jin daɗi ta ji, tuna cewar yanzu hankalinta zai kwanta domin da ya bar gidan shi kenan ba ta da wata matsala da shaƙuwarsu. In kuma sha'awa ke damunsa har yake ɗora ƙwaɗayinsa kan ƙanwarsa auren zai kawo ƙarshen matsala. Don haka hankalinta kwance take cin abincinta don har wani murmushi fuskarta ke ɗauke da shi. A hankali ya jawo kujerar da ke kusa da Abu ya zauna yana faɗin,"Barka da hutawa Abu, Ummu sannu da hutawa." Ya ce tare da ije wayarsa kan dining. A tare suka amsa sannan ƙanninsa suka haɗa baki gurin gaishe shi. Ba tare da ya amsa ba, ya ɗauki wayarsa jin alamun tsaƙo ya shigo. Tun da ya zauna gabakiɗaya hankalinta ya tashi, musamman da ko kallon inda take bai yi ba. Miƙewa ta yi za ta sanya mishi abinci, amma sai ya dakatar da ita ta hanyar karɓar serving spoon ɗin ya ce," Thanks." Ya yi maganar ne ba tare da ya yi dubi gareta ba. Komawa ta yi ta zauna tana kallon yadda yake cin magani, bayan ya saka cokali ɗaya na dafadukar shinkafa da ta ji bushashshen kifi. Wani irin tauna yake mata tamkar yana cin magani, tare da juya abincin filet ɗin yana jin kamar guba yake ci, duk da irin daɗin da ta yi. Abu da Ummu duk abin da yake yi suna kallonsa, amma sam ba ta ji wani iri ba, ji take kamar da ma yanzu aka yi auren don ya tattara ya bar mata gidanta. "Kyakykywar albishir! Duk wanda ya canka zan canza masa waya." Ummu ta ce cikin tsananin murna tana dariya. "Ummu, ni zan faɗa." Cewar Azerhl tare ɗaga hannnunta. "No Ummu, ni zan faɗa." ya saukar da hannunta yana faɗin haka. Umnah ce ta miƙe ta isa ga Ummu tana dariya ta ce,"Ni ce Ummu, ni zan cinka." Sai ta kwashe da dariya ganin yadda suka cika falon da ihu. "Ke Hilah, ba za ki cinka ba?" Abu ya ce yana dariya. "Abu, ai na ga duk suna son su cinka ne, shi ya sa na bar musu." Kowa ya faɗa duk wanda ya canka mota zan ba shi kyau, in kuma Abidin, Naufal da Hilah ne canzawa zan yi. Jin abin da ya faɗa ya sanya su ƙara saka ihu kowa yana faɗin shi ne har da Hilah. "To shikenan, bari a fara kan ƙanana sai kowa ya faɗa." "Ok, bari a fara ta kan ƙanana, Umnah ki fara." "Abu, zai koma Ummara." "Ba ki ci ba." Ummi ta ce tana dariya. "Amnah, ina jin ki." "Ya Huwais, zai koma abroad." "Ke ma kin faɗi." Ta furta cikin dariya. "Abu ya canza mana gida." Dariya Abu ya yi. "Kai ma ka faɗi, saura Abidin." Ya faɗa yana kallon Huwais da ya wani ƙara cin magani, saboda ya san me za su faɗa. "Za mu yi relocating zuwa abroad." Ya faɗa da fatan ya ci. "No, kai ma ka faɗi. Saura Hilah." Kallon Huwais ta yi ganin yadda baya ko kallonsu, hakan ya sanya mata zargin ko maganar aurensa ne ya tashi, aanda ta san abin da zai sanya shi a cikin mood ɗin kenan. Ta yi shiru kamar ba za ta yi magana ba, tana tsoron kar ta faɗi, amma sai ta daure ta ce,"An sanya ranar bikin Ya Ayaan." "Yes, ta ci." Ummu ta furta tana tafa hannunta wanda jin haka ya sa gabakiɗaya suka miƙe suna ihun murna tare da nufar gurinsa za su rungume shi, har da Hilah da ta manta gargaɗin Ummu saboda tsabar murna da ya cikata. Da sauri ya miƙe tare da daka musu tsawa."Wannan wane irin sakarci ne? Sai ka ce gidan biki. Ku yi mana shiru."Tsit suka yi suna zare idanu. Ummu bakinta ta taɓe ba ta ce komai ba ta ci gaba da cin abincinta. "Ƙyale su Huwais, murna ce su yi, saboda mahimmancin wannan ranar anjima ku shirya zamu fita." "Yeeeee! Suka haɗa baki suna faɗi cikin murna. "Our Ya Huwais, is gonna be married. We can wait to see!" Umnah ta furta tana ihun murna. "We need to celebrate Anty Wajnah will be part of us! Ya Huwais happy for the engagement." Hilah ta furta tare da miƙa mata hannu. Saboda tsabar takaici na rashin kishinsa da ba ta yi, bai san lokacin da ya ɗaga hannu ya wanka mata mari ba. Gabakiɗaya falon suka miƙe cikin razana. "Are you mad! Kanka ɗaya kuwa? Saboda me za ka mare ta?" Abu ya furta cikin tsananin ɓacin rai yana kallonsa da ya haɗa girar sama da ƙasa. Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba sai kuma ya juya ya fice ba tare da ya damu da kiran da Abu ya ke masa ba. "Ƙyale shi aure babu fashi." Ummu ta ce tana hararar inda ya wuce. Abu ya kama hannunta ya zaunar kusa da ita yana rarrashinsa. A hankali ta miƙe tare da share hawayenta ta kama hannun ƙanninta da suke jin kamar su yi kuka ganin marin da ya yi mata. Abu ya bi bayanta da kallo tare da farin zargin abin da Ummu ke faɗa masa gaskiya ne. Yana shiga ɗaki ya shige bayi tare da sakar ma kansa ruwa. Haushn marin da ya yi masa da ihun murnar da suke yi ya dame sa. Wani irin haushi ta ya ƙara mamaye shi ganin yadda take murna, sai kuma ya fara jin haushin kansa, saboda tunawa da ba ta san yana sonta ba, kuma dole ta yi murna saboda a matsayin ɗan'uwa ta ɗauke shi. Ya ɗauki tsawon lokaci yana watsa ma kansa ruwa har sai da yaji sanyin ruwan ya fara damunsa. Tawul ya janyo ya ɗaura iya ƙugunsa sannan ya ɗauki ƙarami yana tsane kansa. Bayan ya gama tsane kansa, ya shirya kansa cikin doguwar farar jallabiya da gajeren wando, ya zauna a falo yana tunanin yadda zamansu zai yuwu da Wajnah a matsayi matarsa. Yarinyar da sam tsarin rayuwarsa ba ta yi mishi ba, domin ko a cikin ƴan'uwansa ba ya shiri da ita, saboda yadda take nuna tsantsar wayewarta. Hannu ya sa ya tallabe goshinsa yana jin yadda tempareco na shi ke hawa. Hilah kuwa bayan ta shiga ɗaki gefen gado ta samu tana zubar hawaye. Mamakin marin da ya yi mata take yi, don kawai ta taya shi murnar samun iyali da zai yi. Maganar da ya gaya mata ya faɗo mata da ya ce mata yana son wata. Zubbur ta miƙe tare da ɗaukar hijabinta. Kai tsaye ɗakinsa ta nufa. Yana zaune ta tura ƙofar ta shigo. Da idanu ya raka ta har ta ƙaraso gefensa ta zauna. "Yayana!"Haƙiƙa ban kyauta maka ba, kuma na cancanki fiye da mari." Ta yi shiru ko zai ce wani abu sai kuma ta ga ya ƙara cin magani, bai ce mata komai ba, sai juya kansa da ya yi zuwa wani gefen. Tashi ta yi ta koma gefen da ya juya kansa. "Yayana." Ta furta cikin sanyin murtasai kuma ta ɗora da cewa," Don Allah ka yi haƙuri." Ƙaramin tsuka ya ja saboda muryarta ta rikita shi tare da gusar da fushinsa. Wani irin kallo ya yi mata yana faɗin,"Dole ba za ki damu da auren dole da za a yi mini ba, tun da kina tare da mahaukacin masoyinki." Dariya ya ba ta da yadda ya yi maganar da kuma abin da ya faɗa. "Ka yi haƙuri, sam na manta ka gaya mini akwai macen da kake so." Maganar ta ƙara bashi haushi ganin ba ta damu da abin da ke damunsa ba. Sai kawai ya ƙi tankawa yana kallon sama. "Haba Yayana, ka zama mai rangwame gare ni don Allah." Ta ce tare da kama hannunsa. Hannunta ya ja ya ɗora daidai saman ƙirjinsa."Ki ji yadda zuciyata take tafasa da begen abar ƙaunata. Gashi kuma iyayena suna son su tilasta mini auren Wajnah. Sam ba ta a cikin tsarin macen da na ke so." "Ka yi haƙuri ka yi wa iyayenka biyayya sam ba za ka taɓe ba, kuma za ka ga alfanun hakan." Ta ce masa cikin taushin murya. "Yanzu duk yadda kike son mahaukacin masoyinki za ki iya rabuwa da shi?" "Bana jin zan iya haƙura da mahaukacin masoyi. Hakazalika, ba zan bijirewa iyayena ba." "Kenan, wane mataki za ki ɗauka?" Ya yi mata tambayar cikin zaƙuwa domin amsar da ta ba shi ba ta gamshe sa ba. "Zan yi addu'a ne in har mijina ne zai zo gare ni, domin babu abin da ya gagari Ubangiji." Cikin tsananin ƙauna ya ci gaba da kallonta jin abin da ta ce. Yana dafa cikin halayenta da suke ƙara zurfafashi zuwa ƙasan tafkin ƙaunarta "Yanzu nufinki na yi haƙuri na aminta da aurar Wajnah?" "Eh, kuma ina tabbata maka da in sha Allah, za ku yi zaman lafiya har ku ƙaunaci juna. Sannan kuma in wancan da kake so rabon ka ne za ka samu." "Wane tabbaci kike da shi zan so ta?" Zare hannunta ta yi da ya riƙe a saman ƙirjinsa jin yadda yake shafa hannun. "Za ku so juna Ya Huwais, saboda kullum Ya Hamad, cewa yake in muka yi aure zan so shi." Ƙaramin tsaki ya ja jin ta sako shi a cikin maganarsu. Mai da kansa ya yi ya kwanta tare da rufe idanunsa. Kaman yana ganinta lokacin da ta buɗe baki xa ta yi magana ya tari numfashinta yana faɗin,Ki je zan mu yi magana."Jim ta tsaya sai kuma ta juya ta fita. Bayan fitarta ya juyo yana kallon ƙofar da ta wuce. Ko babu komai magana da ita da ya yi ya samu sauƙi a zuciyarsa. Don ta tuna masa da darajar da Allah ya ba shi na ɗa namiji zai iya auren mace fiye da huɗu. Zuciyarsa ta fara lallaɓasa da ya amince da auren. Ta yadda idanun Ummu zai ɗauke daga kansu, wanda hakan zai ba shi damar mallakar abin ƙaunarsa hankali kwance. Miƙewa ya yi cikin ƙwarin gwiya ya fice daga falon zuwa gidan amininsa Najib da yake ta kiransa. Ba ƙaramin bajinta Ummu take a lokacin da watan bikin ya tsaya Ummu da kanta ta shirya tafiya London don ta haɗo kayan lefe. Su Hilah ma ba a bar su a baya ba gurin shirya yadda bikin zai kasance da events ɗin da za a yi, domin tafi kowa farincikin auran ɗan'uwanta. Gani take kamar auren zai kawo masa kwanciyar hankalin da ya rasa, duba ga yadda ya lalace duk ya fita hayyacinsa, sai ka ce amaryar da za a yi mata auren dole. Kullum cikin kwantar masa da hankali take yi, tare da bashi shawarar ya yi ƙoƙarin manta soyayyarsa, tun da shi kansa ya tabbatar da ta yi masa nisa. Suna zaune a falo suna zaban kayan da Ummu ta kawo musu. Kayan ne masu tsananin tsada da kyau! Bayan sun gama zabar wanda za su sanya ranar Kamu, dinner, lunchean da wedding day ɗin. Ummu ta umurce su da su kwashi kayan zuwa ɗaki, kafin tela ya zo ya karɓa. Hila na ƙoƙarin kwasar kayan ya yi sallama ya shigo. Yana sanye cikin doguwar jallabiya ruwan madara. A hankali yake shigowa cikin falon tamkar ba ya son ya shigo. Tun da shigo ya ga kayan jibge a gabansu ya sanya ransa ɓaci matuƙa, domin ya tsani ya ga abin da zai tuna masa da bikin. Yana ƙoƙarin juya wa Ummu ta lura da shi, domin bai yi sallama da ƙarfi ba. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 10 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Yana ƙoƙarin juya wa, Ummu ta lura da shi, domin bai yi sallama da ƙarfi ba. "A'a, ango ka shigo mana." Ta yi masa maganar cikin raha da tsokana. Haɗe ransa ya yi, tamkar an aiko masa da mala'ikan mutuwa. Kaman ba zai fasa juyawa ba, sai kuma ya tsaya yana ƙarewa falon kallo. Ba tare da ya so ba ya ƙarasa shigowa cikin falon yana yi wa Hilah wani irin kallo, wacce ganinsa ya sa ta tsaya tana kallonsa cikin damuwa. Wani iri ta ji game da kallon domin ba ta taɓa tunanin yana da sexy eyes ba. Ƙasa ta yi da kanta tana ta ya Wajnah murnar samun ingarman namiji kamarsa, domin ita kanta ta tabbatar Yayan na ta ya kai maƙura gurin haɗuwa, saboda samun irinsa a cikin maza sai an tona. Damuwar dake ɗauke a fuskarsa suka tayar da hankalinta har ta ji ta kasa jurewa, amma tun da Ummu a gurin ya sa ta yi ƙasa da kanta, don ta kaucewa mayataccen kallon da ta rasa dalilin yinsa. Gyaran muryar da Ummu ta yi, ya sanya ya dawo cikin hankalinsa tare da sakin ajiyar zuciya yana shafa kansa cikin kunya. Sam ya manta a gaban Ummu yake, domin zuciyarsa da idanunsa ba su hango masa komai sai ita. Ƙasa ya yi da kansa daidai lokacin da Ummu ta kalle ta cikin ɓacin rai ta ce,"Kwashi kayan nan ki kai ɗaki, kuma ki wuce kicin ki ɗora girki." "To," Ta amsa tare da saurin wucewa har ta kusa tuntuɓe tana kallonsa. "Sam na tsani na ga Yayana, a cikin damuwa. Allah ka kawo masa mafita ka sanya masa soyayyar Anty Wajnah, ka zaunar da su lafiya."Ta furta tare da zuba kayan a kan gado ta zauna tana mai da numfashi. Bayan ta shige Ummu ta dawo da kallonta garesa cikiin tashin hankali. Ji take kamar za ta yi hauka, duk a lokacin da ta hango ƙaunarta a cikin idanunsa. Gashi har an kai mizanin da ba ya iya ɓoyewa, domin idanunsa kawai zai tabbatar masa da tsaƙon da ke zuciyarsa. Ta tabbata dalilin da ya sanya Hilah ba ta fahimci abin da ke cikin zuciyarsa ba, domin ko a duniyar mafarki ba za ta taɓa sanya tunanin zai so ta ba, wanda ya sa sam ta gaxa fahimtar halin da ya ke ciki. "Ka daina kula kowa a gidan nan, sannan ba ka son cin abinci, kuma ba ka dariya ka canza ba kamar yadda na san ka ɗana mai ladabi da biyayya ba?" Ta yi masa maganar cikin raunanniyar murya tana jin tamkar ta fashe masa da kuka, domin ta wannan hanyar ne wataƙila zai gane abin da zuciyarsa ke tsaƙa masa ya kaucewa tsari na addinsa da kuma al'adarsa. "Ummu, ke ma kin daina sona. Korata kike yi, ba kya son rayuwa da na ke yi daku. So kike ki yi mini aure na bar miki gidanki." Ya bata amsa cikin murya mai sanyi. Kuka yake son ya yi mata wataƙila ta fahimci girman jarrabawar da yake fuskanta ya wuce mizanin hankalinsa. "Saboda ka kai mumzalin aure ne Huwais. Ka girma kana da buƙatar ka ije iyali, kuma mun ga ba ka da ninyar hakan shi ya sa muka yi maka zabi na gari." "Amma Ummu na gaya miki Wajnah she isn't my type. sam yarinyar nan tsari ta bai yi ba, domin ta cika rawar kai. Ni kuma mace mai aji da hankali da natsuwa nake son na aura kamar dai Hilah." Maganarsa ta duki ƙirjinta daram! Domin har sai da ya ga razana a fuskarta. A razane ta ɗago tana kallonsa, wanda ya sanya ya firgita ainun domin ya ɗauka ya yi suɓutar baki ne ya sanar mata da yana sonta. "Ummu, na ga kin ruɗe mai irin halinta na ce." Ya faɗa da sauri cikim rawar murya. Ga mamakinsa sai ya ga tana hawaye." Dole ne sai ka auri mace mai irin halinta? Mata nawa ne suka fita hali da natsuwa da kyawu? Huwais, ka da kyawun 'yar uwarka ya kai ka duniyar dana sani, domin abin da kake tunani ba zai taɓa faruwa ba. In har ba ka son Wajnah, ba zan yi maka dole ba, amma zan dawo maka da maganar da mahaifinka ya yi maka cewar ka tabbatar da wacce kake so kuma zaɓinka.'" Rintse idanunsa ya yi cikin hawaye."Shin Ummu ta gane yana sonta ne, ko kuma tana masa kallon mugun nufi a zuciyarsa? Zarginsa take da zai iya ɓata rayuwarta. Ko tana tunanin sha'awarta da kyawun surarta suke ruɗansa? Ina son Hilah, daga Allah ne domin a yadda na ke addu'a da sadaka da kuma saukar qur'ani Ubangijina ba xai sanya sheɗan ya yi galaba haka a cikin rayuwata ba." "Ummu, in har auren Wajnah, shi ne farincikin ki na aminta." Ya ce tare da miƙewa zai fice. Har cikin zuciyarsa yake jin zai haƙura ko da a ce son na ta zai zamo ajalinsa, da ace ya zama sanadiyar ɓacin ran mahaifiyarsa gara ya haƙura. In ya yi ajalinsa ya huta da baƙincikin da yake ƙurba a dalilin sonta.Ya miƙe yana layi tamkar zai faɗi. Bin shi da kallo ta yi cikin tsananin tausayawa. Tana matuƙar son ɗan na ta, saboda yaro ne mai matuƙar biyayya. "Huwais," Ta furta cikin sanyin murya. "Na siyo maka kayan da za ka ci biki da su set biyar. Na bawa Telanmu gayu. Ka duba kayan na tura maka a wayarka, in ba su isa ba sai na ƙara. Sannan ya kamata ku shirya kai da ƙannenka ku je ku gaida Hajiya, domin tana mini mitar baka son zuwa gurinta." "In sha Allah, za mu je. Bari na gaya wa Hilah su shirya bayan sallar la'asar sai mu je." "Kar ka damu je ka zan gaya mata, kuma ga kamata ka samu lokaci ka je zance, saboda Mommyn Wajnah ta gaya mini ba ka taɓa zuwa ba, don yarinyar na son ka ne ba ta ƙorafi." Maganar ƙarshe ya baƙanta ransa, domin ya kasa cewa komai sai kansa da ya kaɗa, tare da watsa mata kallon na rashin yadda da har yanzu ta kasa yi da shi. Wataƙila tunaninta zai iya cutar da Hilah ne, ko kuma wani abin take hasashowa a ranta. Sai dai kuma har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin matuƙar ta yi masa aure shi kuma sai ya san yadda zai yi ya ƙirƙiro abin da zai sanya Hilah ta koma rayuwa a gidansa, kafin ya samu hanyar da za ta zamo mallakinsa. Ɗaki ya shige tare da zama bayan ya ƙara ƙarfin A.C ya zauna kan kujera. Remote ya ɗauka ya kunna labarai. Wayarsa ya janyo ya kunna data. So yake ya yi hira da ita, tun da suke magana bai taɓa kiran ta da rana ba, amma yau a yadda ya a ganta cikin abaya baƙa sai ya ji ba zai iya haƙurin har dare su yi waya ba. A lokacin tana kicin tana yanka salat kiran ya shigo. Ba tare da ta kalli wayar ba, sai ta ci gaba da aikinta domin ba ta ƙaunar abin da zai katse mata girkin, musamman da ta yi ranar yin girkin. Ƙara kiran zuciyarta ta raya mata ko mahaukacin masoyi

Chapter 7 of 17