ya kirata.Da sauri ta kalli fuskar a zuciyarta tana addu'ar shi ne.
Ga mamakinta sai kawai ta ga numbarsa da sitikar soyayya da ta yi saving da su.
Ɗauraye hannunta ta yi tare da danna amsa kira ta kanga wayar a kunnenta.
"Ina cikin damuwa masoyiyata rayuwata matuƙar babu ke! Haƙiƙa ba zam iya numfashi ba."
Wani irin tashin hankali ya ziyarce ta, domin in har ba gizo kunnenta suke yi mata ba, muryar Ya Huwais ta ji.
"Ya Huwais?" Ta kira sunan shi cikin ƙara da raji.
Saboda tsananin tashin hankalin da ya shiga bai san lokacin da ya yi wurgi da wayar ba, domin ya rasa yadda aka yi ta gane muryarsa.
Jikinsa na rawa ya ɗauki wayar cikin tsananin firgici da tsoro yana duba ko ya fita daga tsarin ne.
Salati kawai ya yi tare da dafe kansa yana jin shikenan ruwa ya ƙarewa ɗankada! Domin bai san wane irin kallo za ta yi masa ba, matuƙar ta gane shi yake kiranta.
Idanunsa suka firfito tashin hankali ya ƙara ninkuwa a fuskarsa. Jikinsa har wani mazari yake na tsananin tashin hankali.
Dafe kansa ya yi a lokacin da ya shiga gurin tsarin ya ga ashe saitin ya fita. Tsananin mamaki ya kamasa domin shi bai son lokacin da ya cire tsarin ba.
Dama masu iya magana sun ce kwana ɗari ba ɗaya na ɓarawo, kwana ɗaya na mai kaya. Yau asirinsa ya tonu. Wani irin kallo za ta yi masa? Yana wannan tunanin ya ƙara mai da tsarin, sannan ya danna numbarta don ya kira.
A lokacin da ya fita Ummu ta bi shi da kallo har ya ƙarasa fita. Dafe ƙuncinta ta yi cikin takaicin, ganin yadda ya takurawa rayuwarsa game da abinnda ya tabbatar wa kansa haramcin hakan. Ko wani lokacin ta ji haushinsa sai kuma tausayinsa ya dabaibayeta, wanda ba ta san dalilin yin sa ba.
Ɗaukar wayarta ta yi tare da nufar kicin don ta ga ko Hilah ta kammala abincin.
Ƙarar da ta ji na ta tare da sakin wayarta ta faɗi ƙasa, bayan ta kira sunan sa da ƙarfi.
A razane ta faɗa kicin tana tana salati.
"Lafiya, kike ihu da kiran Huwais?" Tsananin razana ya bayyana a fuskarta, domin ko kasheta Ummu za ta yi, ba za ta gaya mata dalili ba, saboda gargaɗin da ta yi mata kan kar ta sake ta kula shi.
Hawaye sosai suka wanke mata ƙuncinta, cikin rawar murya ta kalleta, da ta yi tsaye cikin ɓacin rai tana kallonta.
"L.a.f.i.ya l.au! Ƙawata ce ƴar ajinmu aka sanar da rasuwarta, s.h.i.ne na firgita." Ta tsinci kanta da shirga mata wannan ƙaryar wanda ta faɗa cikin in'ina da rawar murya.
"Sai ki rasa wanda za ki kira sai sunan Huwais?"
"Eh, da yi ke ya santa."
"Munafuka! Kin ji na gaya miki matuƙar na ji da abin da kuke ƙullawa. Wallahi sai na zama ajalinki, domin ba zan bari ku ja mini abin kunya ba."
Maganar da ta yi, da abin da ya yi mata suka rikita kwanyarta da take aiki bisa rashin ƙa'ida.
"Ko dai Ummu na tunanin ni da Ya Huwais, muna aikata masha'a?" Ta yi kanta tambayar cikin tsananin razana jin abin da ta ce.
Ta"awizi ta fara tare da jin wasu zafafan hawaye suna sauka da ga ƙuncinta, ganin rashin yaddar da mahaifiyarta ta yi mata, amma kuma da ta duba abin da ya yi mata, sai kuma duk ta ɗora masa laifin in har abin da ta gani a idanunsa, wanda ya sa take nesanta ta da shi.
"Ummu, wallahi babu abin da ya shiga tsananina da Yaya. Shaƙuwarmu soyyaya ce ta jini." Da sauri ta danna wayarta ta kasheta gabakiɗaya ganin kiransa na shigowa. Ƙirjinta ne ya ƙara dukan tara-tara.
"Rufe mini baki." Ta ce tare da sakin tsaki ta buga ƙofar da ƙarfi ta wuce.
"Sha'anin yarannan kullum cikin damuwa suke sanya ni. Gara ayi auren su hankalina ya huta." Ta ce cikin tsananin damuwa.
Tana fita ta kashe gas ɗin tare da rugawa zuwa harabar gidan. Can cikin shuke-shuken gidan ta ɓoye sannan ta kunna wayarta.
Kafin ta yi ƙoƙarin kira kiransa ya shigo.
"Ya Huwais!" Ta kira sunan cikin tsananin tashin hankali da ɓacin rai. A ranta ji ta ke in har shi ne yake kiranta sai ta cire kunyarsa ta yi masa rashin mutunci, domin ya cuci rayuwarta. Idan ya yi da wasa ne haƙiƙa ya sanya mata tabon da ba za ta taɓa mantawa ba. Tana matuƙar son mahaukacin masoyi da take jin a yanzu son shi ya zama tamkar maganaɗisu a rayuwarta, domin in har babu shi rayuwarta kamar gangar jiki ne da babu numfashi.
"Kin san ni mutum ne mai tsananin kishi! Duk da cewar na san shi yayanki ne, kan me za ki danganta muryarta da ta sa. Shi yana da kishiyoyi, saboda kina da wasu ƴan'uwan, amma ni kuwa Allah ya halicce ki ne don ni kaɗai, ko mutuwa na yi ba za ki taɓa aure ba!"
Tsananin mamaki ya sa ta kasa cewa komai, jin muryarsa ta rikiɗa ta koma muryar mahaukacin masoyi. Cire wayar ta yi daga kunnenta ta duba ko Huwais ya kira ta ba ta lura ba ta ɗauka shi ne, amma sai ta ga da numbarsa dai ya kira ta.
"Kenan muryar Ya Huwais ne take mini gizo ta koma kamar na mahaukacin masoyi?" Ta yi ma kanta tambayar cikin ruɗani!
Ta ɗan ɗauki mintina tana auna hakan a mizanin hankalinta. Har zuciyarta ta amintar da ita gizo muryarsa ta yi mata.
"Wataƙila don na damu da halin da yake ciki ne." Ta furta hakan a cikin ranta a fili kuwa buɗe baki ta yi ta ce,
"Ka yi ha..."
Ƙit ya kashe wayar, yana hamdala tare da saituwar zuciyarsa da ke dukan tara-tara. Dama so yake ta yarda. Hankalinsa ya kwanta yana ajiyar zuciya ganin ruwa bai ƙarewa ɗankada ba.
"Hmmmmmh! In har da ta gane yau na shiga uku! Domin girmana da ƙimata zai zube a gurinta, wanda ba zan iya lamuntar hakan ba."
Ƙwanciya ya yi, yana mai da numfashi saɓanin da yake ta safa da marwa, yana ta share zufa duk da A.C dake cikin falon.
Bin layin ta yi, amma a kashe wanda ya ƙara tada hankalinta matuƙa, domin a yau ya yi mata alƙawarin sanar da ita sunansa.
Hawaye masu zafi suka wanke mata fuska. Hannu ta sanya ta share. Da sauri ta ruga zuwa ciki tuna rage gas ɗin kawai ta yi ba ta kashe ba.
Sororo ta yi ganin Ummu a kicin ɗin dama tum kafin ta shigo ƙaurin kuskus ya cika gidan.
Wani irin kallo ta watsa mata tare da kai mata mari. Da sauri ta matsa cikin muryar kuka.
"Ummu, ki yi haƙuri ba..."
"Fita ki bani guri! Sakaryar yarinya kawai." Ta furta cikin ɓacin rai wanda ya aanya ta ruga zuwa falo tana hawaye.
Yana kwance a kan kujera yana ta tunani har yanzu zuciyarsa ba ta gama bugu ba.
Su
Tashi ya yi jikinsa babu ƙwari ya shiga bayi don ya watsa ruwa su tafi gidan Hajiya.
Bayan ya yi wankan ya shafa mai sannan ya sanya dakakkiyar shadda ruwan sky blue. Shaddar ta yi matuƙar ɗaukarsa domin ya yi kyau sosai duk da damuwar da yake ciki, bai hana fito da zallar kyawunsa ba.
Turarensa mai daɗin ƙamshi ya fesa sannan ya kulle ɗakinsa.
Ya shigo falon da sallama zuciyarda na dukan tara-tara. A ransa yana fatan Allah ya sanya ta yarda ba shi ya ke kiranta ba.
Ita kaɗai ce a falo tana tsaye a gaban dining da tsumma a hannunta tana goge kan dining ɗin da ta gama ba Umnah abinci.
Sallamar da ya yi ta ji zuciyarta ta buga wanda ba ta san a tare suka buga da na sa ba.
Kallonsa ta yi cikin ido tana son ta ga rashin gaskiya a tare da dashi, domin har yanzu zuciyarta na ƙara tanbatar mata da muryarsa ne.
"Ya Huwais!" Ta kira sunan daidai lokacin da ya ƙaraso gurin dining ɗin cikin daurewa.
Basar da kallon da yake mata take yi."Ina su Umnah? Ummu, ya gaya muku zamu fita."
"Eh, amma ta ce ban da ni."
Kallonta ya yi ba tare da ya ce komai ba. Sai kuma ya zauna yana kallonta.
"Je ki gaya musu su fito kuma ke ma ki shirya."
Jim ta yi kamar za ta yi masa magana sai kuma ta jiya ta sanar musu tare da dawowa da sauri.
Ganin da magana a bakinta ya sanya shi miƙewa da sauri tare da ije remote ɗin da ke hannunsa.
"Ki ɗauko mayafinki bari na ɗauko abu na yi mantuwa."Tsaya ya yi ganin Ummu ta fito da carbi a hannunta.
"Ka shirya ne Huwais?
"Eh, Ummu. Su yi sauri domin ina son na je gidansu Najib."
"Amma daga nan za ku je gidan su Wajnah ko?"
"No Ummu, ba yau ba." Ya furta cikin ɗaure fuska.
"Ma za ki kira su Amnah." Ta ce.
"Na sanar musu Yaya ya fito." Kafin ta gama maganar suka fito dukannninsu a shirye.
"Bro you look gorgeous!"Naufal ya ce cikin murmushi yana kallonsa.
Ba tare da ya amsa ba, ya fara ƙoƙarin tafiya ganin sun kama hanyar fita, sai kuma ya juyo ya ce,"Ummu, Hilah ba za ta je ba ne? Ko ranar da muka je Hajiya ta yi maganar tana son ganinta." Ya yi maganar cikin basarwa.
"Eh, ku barta kawai jibi in zani sai mu tafi tare." Ta ce wanda ya sa ya ƙara ɗaure fuska ba tare da ya kalle ta ba.
"Ok,." Ya ce amma a ransa a jagule ji yake kaman shi ma ya fasa zuwa.
"Please Ummu, don Allah mu je da Anty Hilah." Umnah ta ce wanda jin haka ya sanya Amnah ta ce,
"Please Ummu,"
"Hilah, ki ɗauko mayafinki ku je." Ta ce tare da juyawa cikin ɗakinta wanda ya sa yaran suka saka ihun murna.
Ɗaki ta koma cikin tsallen murna ta sanya abaya ja tare da rolling ɗin ɗankwalinta. Ta yi kyau sosai kamar ka sace ta gudu.
Wayarta ta ɗauka sai ƙaramar pos ɗinta ta fito.
Bayan sun shiga cikin motar har ya tada mai-gadi ya buɗe Umnah ta ce,
"Ya Huwais, Ummu ta bar Anty Hilah ta bi mu. Shiryawa ta ke yi."
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 11
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Ya Huwais, Ummu ta bar Anty Hilah ta bi mu. Shiryawa ta ke yi."
Ransa ne ya yi fari kamar farar takadda, ba tare da ya ce musu komai ba. Ya kashe motar yana shafa sajensa.
Ba ta ɓata musu lokaci ba ta fito tana tafiyarta cikin sanyi.
Ta madubin motar ya hangota yayin da ya ƙura mata idanu ganin yadda ta yi kyau kamar ka sace ka gudu.
"Ya Allah!" Ya furta da ƙarfi tare da dafe zuciyarsa daidai inda ta buga.
A hankali ta ƙaraso, ta shiga bayan motar wanda sai da ya ɗan ɗauke numfashinsa, jin yadda ƙamshin turarenta ya cika masa hanci yake rikitar da kwanyarsa.
Ba tare da ya kalleta ba ya ja motar yana sauke gwauron numfashi.
A hanya tafe suke shi da ita babu wanda ya yi wa juna magana. Kowa da abin da yake tsaƙawa a ransa musamman ita. Da take son sanar masa da incident ɗin da ya faru da ɗazu.
Shi kuwa hankalinsa na kan hanya, amma tunaninta yake yi, satan kallonta yake yi wanda ba ya son su haɗa idanu, domin za ta iya fahimtar wani abu, musamman yadda idanunsa suka canza.
Su Naufal ne kawai suke ta hirar su, wanda yawanci suna sako su a ciki. Hilah ce kawai take sanya musu baki, amma shi da ga um sai a'a.
Kafin su isa ya tsaya ya siyawa Hajiya Fruits sannnan suka wuce.
A ƙofar gidan ya tsaya tare da yin hon, wanda Ilu maigadi ya taso da sauri ya buɗe masa, ya shiga da motar cikin ƙaton harabar gidan.
Bayan ya yi parkinng sun fito ban da Hilah da ta tsaya nawa tana ƙoƙarin sanya takalminta.
Saboda murna suka ruga cikin gidan ba tare da sun jira ta ba.
Ta ɗauki takalmin tare da buɗe murfin ƙofar za ta fita, ba tare da ta ce masa komai ba, da hannunsa dafe da sitiyarin mota yana kallon gefe.
Ganin za ta fita ya sanya shi juyowa da dara-daran idanunsa ya watsa mata.
Wani irin faɗuwar gaba ta tsinci kanta da shi. Sai kuma ta rikice domin ba taɓa ganin ya yi mata kallon ba.
"Yaya," Ta ce sai hawaye suka wanke mata fuska.
Ƙaramin tsuka yaja don jin haushinta, domin shi ya kamata ya yi kuka ba ita ba.
"Ba na hana ki sanya turare ba?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai.
Ganin ba ta ce masa komai ba, domin ita ba wannan maganar take son su yi ba ya ɗora da cewa," Ke malama ce kina da sanin ki, kuma kin san hukuncin sanya turare wani namijin da ba muharraminki ya shaƙa ba."
Ya Huwais, mahaukacin masoyi ya kita ni da rana." Ta yi masa maganar tana kallonsa ko zai ce wani abu, amma sai ta ga ya tsuke fuska hankalinsa na kan wayarsa da yake shafa bayanta.
Gyaran murya ta yi, wanda ya ɗan juyo da idanunsa ya yi mata wani jirgitaccen kallo.
"Damuwarki mahaukacin masoyinki, sam ba ki damu da rayuwar ɗan'uwanki da ake shirin yi masa auren dole ba."
Yadda ya yi maganar da abin da ya faɗa suka sanya ta sakin dariya babu shiri.
A hargitse ya juyo yana kallonta ganin dariya take. Ransa ne ya ƙara ɓaci ya buɗe furfin motar zai fita.
Ganin haka ya sanya ta gimtse dariyar tare da kama hannunsa ta riƙe.
"Please, Ya Huwais, don get me wrong." Ta fura tare da riƙe hannunsa duka biyu.
"Ina cikin damuwa, amma ba kya tausayina. Tun da kika samu mahaukacin masoyinki kin daina kula da ni."
Rau ta yi da idanunta."Kai ma ka san babu wanda na damu da rayuwarsa kamar kai. Bayan ƴan'uwanta ka ta jini har da shaƙuwa da soyayyar jini, wanda ta kai da har muryar mahaukacin masoyi tana rikiɗa tana zama irin taka."
Gwauron ajiyar zuciya ya saki jin abin fa ta ce. Zuciyarsa ta yi fari ƙal tare da hamdala ganin ba ta gane ba.
Da mamaki ya kalle ta ya ce,"So kike ki yi mini wayo na ɗauka kin damu da ni, amma na tabbata da ace babu son mahaukacin masoyi a rayuwarki, sai ki tausaya mini halin da na ke ciki."
"I do care you! Wallahi kana raina ko da yaushe, amma ka sani Ummu, gata take yi maka, domin duk wanda ya auri mace kamar Anty Wajnah ya yi dace."
Ƙara ɓata rai ya yi tare da buɗe murfin motar ya fito."Please, akwai buƙatar mu tautauna sis, ina tsananin buƙatar shawarki."
"Haɗuwarmu xai yi wuya Yaya, Ummu sam ba ta son ganinmu a tare."
"In mun gaishe da Hajiya ki same ni
a waje ki raka ni gidan Najib."
Kallon sa ta yi da nufin ta musa, amma kallon da ya yi mata ya sanya ta kasa tare da sauke kanta ƙasa.
Ganin ya fita ya sanya ita ma ta fito tare da rufe ƙofar suka jera suna hira.
Hajiya na zaune a falon, su Umnah sun sanyata a tsakiya sai hira suke mata. Sallamar su ya katse dariyar da suke yi mata.
Ganin su ya sanya ta washe bakinta da ke cike da goro tana tafa hannunta.
"Lale marhaba da zuwan jikokina!" Ta furta cikin tsananin farinciki domin tana matuƙar son jikokinnata.
Huwais da fara'a ya isa gareta, tare da zaunawa a gefenta ya ciro wayarsa da ke gana aljihun rigarsa zai ɗauke su hoto.
"Bari na yi hoto da gimbiya autar mata." Ya ce cikin tsigar tsokana.
Hannnunta ta sanya ta ka masa duka da carbin da take ja, ta ture shi tare da kai hannu kamar za ta buge shi, wanda hakan ya sanya ya miƙe yana dariya.
"Bari na gudu domin hannunki kamar icce yake."
"Eh, ai gara ka gudu in ba haka ba, sai na karyaka saboda kishi. Don za ka yi aure sam ka daina zuwa inda na ke. To daɗin abin ba a canzawa tuwo suna, kuma tsohuwar zuma da ita ake magani"
Fara'arsa ta ragu jin abin da ta ce, amma sai ya share ba tare da ya ce komai ba.
Hilah kuwa rungume ta yi cikin tsananin ƙauna ta ce,"I miss you ƴar tsohuwa mai ran ƙarfe."
Murmushi ta ƙara saki tana cewa,"Sannu malama tun da kika ci gaza kika yi kuɗi kin guje mu."
"Kai tsohuwar nan kin iya rigima. Kana jin abin da take cewa Ya Huwais, bayan ko da na dawo sai da na kawo mata nata kason."
Murmushi kawai ya yi,ba tare da ya ce komai ba, ya zauna gefen da Hilah ta zauna hankalinsa na wayarsa da Najib ya turo masa da tsaƙo.
"Ai kya faɗi haka saboda ba ki da gaskiya. Bari mutuminki na nan zuwa, tun da ya ji muna maganar zuwarki ni da Fatima ya ce ba zai koma Kaduna gurin aiki ba sainya ganki, yanzu haka yana hanya. Ni duk na ƙosa ayi auren nan duk mu huta."
Da sauri ya ɗago kansa jin abin da ya ce. Zuciyarsa ta yi baƙinƙirin tare da jin wani irin ɓacin rai. Wani irin ɓacin rai ya ziyarce shi har baya gani sosai.
"Ai ko ya zo wahala zai yi domin zamu bar su Umnah fita za mu yi."
"Ku je ina? Lailai ba wuni ta ce mini za ku yi ba?" Ta yi masa tambayar da sauri.
Miƙewa ya yi tare da ɗaukar makullin motarsa ya kalli Hilah da shi take kallo ganin yadda ya yi fuskar shanu.
"Eh, wuni za mu yi, amma sai ta raka ni anguwa. In zai iya sai ya yi ta jira ɗan wahala kawai. Ni wallahi haushi yake bani, saboda yadda yake wani nuna son mace da nace mata kamar maye." Cikin tsananin xafi ya furta cikin ɓacin rai tare da yi mata nuni da su tafi.
"An gaya maka kowa irin ka ne? Mata ai dole a kula da su, domin sune tushen kowa. Don kai ba ka damu da matar da za ka aura ba, sai aka ce maka kowa haka yake? Ka ji tsoron Allah Huwais, yarinyar nan tana sonka, kuma masoyiyarka ce ta haƙiƙa. Ka tuna iya tsawon lokacin da ta rinƙa jiranka, amma tun da aka sanya ranar ka kasa zuwa ko sau ɗaya ne."
"Saboda bana sonta kun na ce sai na aureta. Ana soyayya dole ne? Na ga ko ke kin sha bani labarin ke da Alhaji auren soyayya kuka yi da mijinki. Sai ni a ayi mini cushenta? Don tana sona sai a tilasta mini, bayan na gaya muku ina da wacce na ke so."Ya ce cikin zafi.
"Sau nawa ake baka damar ka kawo ta amma ka kasa Huwaisu? In dai ba aljana kake so ba, ko kuma aurenta kake son ka yi cikin haramci, ai ya kamata ka nuna mana ita iya tsawon lokacin da aka ba ka."
Haɗiye miyau ya yi da ƙyar, tare da kallon Hilah da ta yi zuru tana kallonsa, a ranta tana son ya aminta da zai nuna musu ita, domin ita kanta tana son sanin wace ce ta sace zuciyarsa har yake fargabar tunkararta?
Hannunta ya kamo yana faɗin,"Zo mu je Hilah, ƴar tsohuwar nan lokacina kawai za ta ɓata."
"Ba dai ka son gaskiya kawai, amma ka sani ko ba ka so Wajnah don kai ba, ka sota saboda ita ɗin ƴar'uwarka ne, saboda karka manta da mahaifiyarka da mahaifiyarta ciki ɗaya suka fito."
"Wannan dalilin zai sanya na aminta a kashe ni kenan?"
Kafin ta ba shi amsa muryar Hamad ta daki kunnuwansu ya shigo da sallama.
Gabakiɗaya suka ɗaga idanu suna kallonsa.
Namiji ingarma da shi kuma mai cikar haiba da kyawu. Yana sanye cikin kaftani mai kalar maroon. Kayan sun yi masa kyau kuma sun dace da jikinsa.
"Yauwa ga shi nan ma ya iso da kake shirin ɗauke masa mata." Hajiya ta furta tare da ƙara fafaɗa fara'arta bayan ta amsa sallamarsa.
Cikin kamala ya ƙaraso cikin falo, tare da zama gefen Hajiya idanunsa, na kan Hilah da ta yi mutuwar tsaye tana kallon Huwais.
A ranta ta sanya cewar matuƙar da ta san zai zo sam ba za ta yarda ta biyo su ba, domin ta san in har suka haɗu ba su kwashewa ta daidai, wanda hakan mamaki yake bata, saboda ta duba tare da mahangarta ta rasa dalilin da ya sanya ya tsane shi, saboda kaf Family nasu an shede shi yana da natsuwa da hankali, amma ba shi da maƙiyi da kamarsa.
Huwais ya watsa masa mugun kallo ta ƙasan ido. A ransa haushinsa matuƙa yake ji, saboda da za a iya ba shi takubba tsaf zai sare kanshi, don ya tsane shi baya jin ɗigon ƙaunarsa, duk da ya kasance ɗan'uwansa, kuma dangantaka na jini mai ƙarfi.
Ƙaramin tsuka ya ja tare da ji kamar ya kifa masa mari. Tuna karanbantar da suka sha ana gobe zai bar Ƙasar ya dawo masa. Haushi da takaici suka ƙara kama shi ya ji kamar ya shaƙeshi.
Bayan Hamad ya gama gaisawa da Hajiya da ta cika da farincikin ganinsa, sai ya miƙa wa Huwais hannu da ya sha kunu kamar ba zai bayar ba. Hannunsa ya noƙe ko mai ya tuna oho ya miƙa masa kamar yana gudun kar ya shafa masa ciwo.
"Ranki ya daɗe gimbiyar mata." Hamad ya furta hakan cikin tautausar murya, wanda ya ji kamar ya soke shi ne.
Ɗan gyaran murya ta yi can ƙasan maƙoshinta tare da tattaro natsuwarta ta ce,"Ina wuni?" Ta furta ba tare da ta iya ɗago idanunta ta kalle su da suke kallonta kamar za su cinyeta.
A maimakon ya amsa sai ya ɗan sakin mata murmushi tare da ƙara masawa kusa da ita."
"Gimbiya da fatan kina lafiya?"
"Hajiya, mu zamu wuce ba xamu jima ba, zamu dawo." Ya ce tare da kama hannunta za su fita.
"Kai Huwaisu, ba na son rashin mutunci. Ɗan'uwan na ka za ka barshi ne a nan, bayan saboda ita ya zo."
"Bai sanar da zuwansa ba, kuma ni na riga na tsara fitarmu."
"Karya damu zan jira shi." Cewar Hamad tare da zama a kujera hankalinsa kwance, saboda tun ranar da suka yi faɗa mahaifiyarsa ta gargaɗesa da karya ƙara kula sa, Hilah dole za ta kasance na sa, domin ko da ace sonta yake yi, ya san cewa babu aure a tsakaninsu ko da sun kasance su kaɗai. Don haka, duk son da yake mata dole ya haƙura ya ɗauke idanunsa a kan zinariyar ƙanwarsa ya bar masa ita, saboda shi Allah ya yi wa wannan tagomashin da samun mace kamarta.
"Huwaisu, ina gaya muku ku sasanta kanku ku rage tsanar da kukewa junanku, musamman kune manya in har ƙanninku suka taso suka ga abin da kuke yi ba za su yi zumunci."
"Hajiya, sai mun dawo." Ya ce tare da kama hannunta suka fara tafiya.
Suna fita ya saki hannunta ya buɗe motar ya shiga.
Hilah kuwa kallonsa take yi cikin mamaki. Ta san yana sonta fiye da kowa duk a cikin ƙanninsa, amma dalilin sa na ƙin yarda da auren Hamad yake ba ta mamaki. Yana da hankali da addini uwa uba ga ƴaƴan banki. A tunanin ƙarfafata zai yi ta amince musamman da yake ɗan'uwa, kuma wanda suka tashi tare
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 17