ki taɓa mallakarsu ba."
Duƙawa ta yi jin abin da ya ce. Jawaye ta fara tare da kai hannu za ta kama ƙafarsa wanda ya janye da sauri ya yana harararta.
"Don Allah mijina, ka soni mu zauna lafiya. Ka dubi tsarina da surata babu wacce mace da za ta tsere ni."
"Akwai ta ita ce wacce take zaɓin raina kuma na ke sonta. Ko da ace ba ta kaiki sura ba, amma ta fi ki komai a gurina." Ya faɗa tare da toshe hancinsa saboda ƙamshin turarenta dake hawa masa kai.
Ganin ya toshe hancin ya ƙara baƙanta ranta matuƙa. Ita da take tunanim ƙamshin zai karkato da hankalinsa, sai ga shi yana nuna baya son ƙamshin.
"Wallahi baka isa ba, matuƙar ina cikin gidan nan babu wata ƴar iskar da xa ta shigo gidan nan, in ba so kake mu yi mutuwar kasko dukanninmu ba."
"Karki ƙara zaginta domin a kanta xan yi mummunar saɓa miki."
"Ka kashe ni in ka so, ai xanfi jin daɗi ranar aurenmu ka yi mini shegen duka, kan babu abin da ya shiga tsakaninmu."
Hannu ya ɗaga, sai kuma ya fasa don ya san za ta iya gaya wa a gida.
"Dama na san ba ki da kunya, amma wallahi ba xan ɗauki rashin kunya ba."
"Matuƙar za ka rinƙa kiran wata banza a gidan nan, ni kuma abin da ya fi banxa zan kirata da shi."
"So kike na canza miki halitta." Ya ce tare da komawa ya kwanta.
"Ya Huwais, don Allah ka tausaya mini ka karɓe ni a matsayin mata." Ta ce cikin rawar murya jin mararta ya ƙara murɗawa.
Tsaki ya yi mata tare da komawa ya kwanta.
Ganin haka ya ta bin bayansa ta kwanata tare da rungumeshi ta bayansa.
Wani irin wawan ajiyar zuciya ta saki jin yadda gabakiɗaya tsigar jikinta ya tashi.
Da sauri ya miƙe yana mata mugun kallo da mamakin zallar rashin kunyarta.
"Tashi ki fita ko na saɓa miki."
Abin da ya faɗa, ya sanya ta ɗago idanunta, da ƙyar da suka rine suka canza kala.
"Don Allah ka taimaka mini ina cikin wani hali."
Hannunta ya kama, ya janyota har ƙofar ɗakin ya watsar da ita, tare da mai da ƙofarsa ya rufe.
Kallonta kawai ya yi, ya fahimci halin da take ciki. Sai dai inhar jikinsa zai mallaka mata ba zai taɓa ba, domin komai na sa mallakin Hilah ce.
Komawa ya yi ya kwanta, yana mamakin yadda ta nuna zalamarta da shan kayan matan da ta yi wanda ya san su suke ɗawainiya da ita.
Takaici da baƙinciki suka cika mata rai. Duba ga maza masu kyau da suka nuna suna son aurenta, amma ta nace sai shi. Ga shi ta aure shi yana wulaƙanta ta.
Ƙara ta saki jin mararta ya murɗa sai kuma ta fara ciwo.
Da kyar ta miƙe tana faɗin,"Na shiga uku! Ya Huwais, don Allah ka taimaka mini xan mutu cikina, marata."
"Ya Huwais," Ta kira sunan a gigice jin yadda mararta ta ƙara murɗawa.
Huwais kuwa yadda ya ji muryarta ya rikice sam bai damu ba. Kwanciyarsa ya yi tare da kunna karatun qur'ani, ta yadda xai daina jin buga ƙofa da sunansa da take kira.
Wayarsa ya jawo ya kunna data ya hau online.
Zuciyarsa ke kwaɗaita masa, ya tura mata da tsaƙo, amma wani bangare na zuciyarsa na yi masa gargaɗi.
Sauka ya yi dafa kan gado tare da buɗe labulen windon ɗakin. Tsakar gidan yake kallo, wanda hasken wutan lantarki ya haskaka farfajiyar gidan tankar rana.
"Anya zan iya daina waya da ke? Kai ina ba zan iya ba, domin ta hakanne kawai na ke samun natsuwa a cikin raina." Ya tambayi kansa tare da furta hakan cikin ransa.
"Hilah, ina sonki." Ya ce yana kallon fuskarta a wayarsa, sai kuma ya sanya bakinsa kan nata, ya yi mata kis yana murmushi.
Har ya fara yi mata typing, sai kuma ya kashe wayar duka ya ja bargo ya kwanta.
"Ya kamata na ba ki lokaci."
Wayar kuma ya kunna tare da tura mata tsaƙo.
A lokacin da tsaƙon ya shigo, tana zaune a kan sallaya bayan ta idar da sallah tana kuka.
Sosai take jin zafin yaudarar da ya yi mata, domin ta ɗauka yadda yake kalamansa da natsuwarsa, da kuma kyautar ban girma da yake mata mutum ne mai nagarta. Ashe mayaudari ne.
"Wayyo Allahna! Haƙiƙa ka cutar da zuciyata." Ta furta cikin muryar kuka tana jin zuciyarta kamar za ta yi bindiga ta fito.
Wayarta ta ɗauka tana duba duk chatts ɗin da suka yi. Wasu ta yi dariya wasu kuma ta yi murmushi mai haɗe da kuka.
"Ina sonka, why za ka yaudare no?" Ta rubuta mishi hakan sai kuma ta ƙara da
"Don Allah ka bayyana mini kanka, wallahi na yi maka alƙawarin zan aureka matuƙar kana sona."
Ji fa ta yi da wayar, ganin duk tsaƙonnin da take tura masa babu amsa, domin tun jiya lokacin da suka yi alƙawarin xa su haɗu, ya kashe waya bai ƙara hawa ba.
Tana ije wayar tsaƙo ya shigo, wanda da sauri ta ɗauka a ranta tana addu'ar Allah ya sa shi ne.
Ƙaramin tsaki ta ja, tare da canzawar fuskarta ganin tsaƙon Yayanta ne.
"Ya Huwais, ya ke yi? Shi da ya kamata ya kasance da matarsa." Ta yi ma kanta tambayar hakan.
Tsaƙon ta duba inda ta ga ya rubuta jamar kamar haka;
Ƙanwata, na kasa bacci tunanin halin da kike ciki da kewar gida sun dame ni.
Murmushi ta yi sosai tana mamakin ƙarfin zuciyarsa, domin ta yi tunanin duk borin da yake yi da xarar sun keɓe a tare zai ba da kai bori ya hau, kasancewar babu namiji da zai kasance da Wajnah ba tare da ya kware mata ba.
Yayana, don Allah ka yi bacci. Ina hadda ne kuma ni ma yanzu zan kwanta.Ta rubuta tare da tura masa tsaƙon sai ta kashe wayarta ta kwanta.
A lokacin da tsaƙon ya shigo, hankalinsa ya tashi sosai don bai yi tunanin idanunta biyu ba.
Da sauri ya janyo wayar, ya karanta murmushi ɗauke a fuskarsa. Iska ya ja tare da fesarwa.
Juyawa ya yi ɗaya ɓangaren ya danna numbobinta don ya kira.
"Ba ta yi bacci ba, tana cikin damuwar da na sanya ta. Ki yafe mini Hilah sonki da ƙaunarki suka janyo mini haka.
Ransa ne ya ɓace, matuƙa jin wayarta a kashe. Ya san ta kashe ne don karya kirata.
Ƙaramin tsaki ya ja, tare da jan bargo daidai lokacin da ya ji Wajnah ta ci gaba da buga ƙofa.
Duk yadda ya so ya yi bacci ya kasa.Ji yake gidan kamar ba mallakinsa ba. Miƙewa ya yi ya shiga cikin bayin ya ɗauro alwala tare da shinfiɗa dadduma ya tayar da sallah.
Kamar kullum istikhara kan lamarin ya fara. Tun ranar da ya fara sonta yake istikhara kamar yadda ma'aiki ya umurce mu da mu yi in muna son aikata wani abu.
Istikhara
* Neman zabin Allah, wata sallah ce mai raka'o'ibiyu, wacce yinta sunnah ce mu'akkada (sunnahce mai karfi), wacce manzon Allah ya koyar dasahabbansa ita har tazo garemu kamar yadda al-qur'ani ya iso gare mu, sallace da akeyi yayin neman zabin Allah akan wani al-amari kamar;aure, sayan gida/mota aikin gwabnati da daisauransu, sai dai ita wannan sallar ba'ayin ta a kan abin da ya ke wajibi ko mustahabbi akan ka; kamar neman zabin Allah akan yin azumin ramadan, ko salloli biyar na yini, ko fitar da zakka, azumin alhamis da litimin da dai sauransu.
* Sai dai wurin Mustahabbi ana iyayi idan sun ci karo, misali: mutum ne yake son yaje umra karo na biyu a lokaci guda kuma yana so ya je wata kasa neman ilimi, to yana iya neman zabin Allah akan ya zaba masa wanda yafi Alkhairi a cikin su.
* Hakika Duk wanda ya nemi zabin Mahalicci,kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma yayi azama a cikin lamarin sa, to ba zai yi nadama ba In sha Allah. Domin Allah Madaukakin Sarki ya ce: "Kuma kashawarce su cikin lamarin ka, idan kuma kaquduri aniya, to ka dogara ga Allah" [Ali-Imran :159].
* Hadisi ya gangaro Jabir ibn Abdullah, Allah yakara yarda dashi da Maihaifin saya ce : Manzon Allah (SAW) ya kasance yana koya mana yin Istikhara (neman zabin Allah) a cikin dukkanin al'amura kamar yadda yake koyamana sura daga cikin surorin Alqur'ani. Ya kance: ''Idan dayanku yayi niyyar yin wani al'amarito yayi sallah raka'a biyu ba farillah ba sannanya ce:
"Allaahumma innii astakhiiruka bi ilmika,wa'astaqdiruka bi kudiratika, wa'as'aluka minfadlikal azeem, fa innaka takadiru wala akadiru,wa ta'alamu wala a'alamu, wa anta allamulguyube, Allahumma inkumta ta'alamu anna hazalamri kharal lii fii deenii wama'ashii wa'akibatiamrii, aajilihi wa'aajilihi faqadirhu lii wayassirhulii thumma baariklii fiihi, wa'inkunta ta'alamuanna hazar amra sharrullii fii deenii wama'ashiiwa'akibati amrii aajilihi wa aajilihi fasrifhu'anniiwasrifnii anhu wakadur liyal khaira haithu kaanathumma raddini bihi."
"Ya Ubangijina! ina neman zabin ka da ilimin Ka,kuma ina neman tabbatuwar ikon Ka, ina rokanfalalar Ka Mai gaima, Kai ke da iko ni banda shi,Kai ne Masani ni ban san (komai ba) Kai nemasanin abin da yake boye. Ya Ubangiji na! Inkana ganin wannan abu ('sai ya fadi abin da yakeistiharan a kai') shi yafi min a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, to ka tabbatar min dashi, ka sauqaqe min sannan ka yi min albarka acikinsa, in kuwa kana ganin wannan abu sharri negare ni a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, ka juyar da shi daga gare ni, ni ma kajuyar da ni dagagare shi, ka kudurtarmin da alkhairi sannan kaamintar min da shi" [Bukhari]
* Na tabbata banbanci ya bayyana a fili gama'abota hankulla da tunani tsakanin wannan karantarwar ta shugaban talikai SAW, da Tsirfe-tsirfe da shafi fadin, wasu marubuta littattafan koyarwa don neman kudi, da masu tsibbace tsibbace
* Ita dai wannan Sallah Mustahhabbi ce anso kayita (domin sunnah ce mai karfi, sannan zakasamu lada idan kayi), amma idan bakayi babalaifi.
* Wannan Addu'a ta istikhara ana yin tane bayan ka sallame, sallar nan da kayi mai raka'a biyu,duk da wasu malaman na ganin ana karanta tane,bayan tahiya da salatin manzon Allah SAW kafinSallama, domin mafi Al-khairin bijiro da addu'aacikin sallah shine sujuda da bayan tahiya, saidai magana mafi rinjaye shine bayan Sallama.Allah shine Mafi Sani..* Babu Laifi ga mutum ya maimaita istakharasama da daya, hakam ya tabbata daga cikinmagabata, kamar Abdullahi dan zubair Allah yakara yarda dashi yayi istakhara sau ukku.[Muslum - 970].
* Babu wani hadisi daya inganta da yazo dasurorin da ake karantawa, a cikin sallar nemanzabin Allah.
* Haka kuma babu wani hadisi da yazo daga Annabi cewa idan mutum yayi istakhara zaiyimafarki ko zaiga wani mutum yana yi masa bayani al-amarinsa.
* Babu shakka duk wanda ya yi zai samu natsawa cikin abin da Allah madaukakin sarki ya zaba masa.
* Ba mafarki ake yi ba kamar yadda mutane dayawa suka dauka, ana ganewa ne da yanayin nutsuwar zuciya, idan aure ne sai kaji zuciyar kata qara nutsuwa da yarinyar, idan sana'a ne kakeso ka farasai kaji zuciyar ka tanutsu da sana'ar.
* Za'a iya yin wannan sallah raka'a biyu da rana,ba dole sai da daddare ba, sannan zaka yita ne daga lokaci zuwalokaci har sai ka sami biyan buqata, sannan Ana yin tane ko da lokacin da aka hana yin sallah ne,idan bukatar hakan ta taso, domin ita tana daga cikin "Nawafilul Asbab" - "Nafiloli masu dalili".
* Wannan kenan don gane da abunda ya shafi Sallar neman zabin Allah madau kakin Sarki,Muna fatan Allah ya bamu damar Aiki Abin da muke rubutawa da karantawa.
Still yanzu ma natsuwa fiye da ta, da ya samu wanda ya ƙara ninka masa ƙaunarsa.
Ajiyar zuciya ya saki tare da janyo filo ya kwanta a sallayar.
Wajnah kuwa tun tana buga ƙofa, tana kuka tana kiran sunansa, har ta kasa sakamakon mararta da ya riƙe ya murɗe ko numfashi ta kasa.
Kallonsa kawai xai sanya ta rikice ballantana da ta haɗa jikinsa da nata.
Rintse idanunta ta yi cikin azaba tana kiran sunan Allah. Ta haƙura ne saboda duba agogo da ta yi ƙarfe ɗaya har da kwata. A lokacin ta gane ko kwana ta yi tana buga wa sam ba zai buɗe mata ba.
Jikinta ya yi sanyi matuƙar gaske! Domin bata taɓa tunanin bayan auren ba zai iya ɗauke kansa daga jikinta har ya wulaƙanta ta ta.
"Wace ce wannan da ta sace zuciyar mijina?" Ta yi wa kanta tambayar tare da jifa da filon da ta danne mararta.
Kuka sosai take yi yayin da wani sashe na ɓangaren zuciyarta yana gaya mata Huwais ba zai so ta ba.
Hawaye masu zafi suka ƙara kwaranya a idanunta, daidai lokacin da mararta ta ƙara murɗawa. Gurmususu a ƙasa ta shiga yi, tana kiran sunan Allah har ta samu sauƙi.
A hankali ta miƙe tana jan ƙafa ta shiga cikin ɗakinta. Kan gado ta kwanta tana nishin wahala da ƙyar.
Ta daɗe a haka har zuwa ƙarfe uku. Wayar Wahida kuwa ta kira yafi cikin kwandon masaki.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 20
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Ta daɗe a haka, har zuwa ƙarfe uku. Wayar Wahida kuwa ta kira yafi cikin kwandon masaki.
Tun da take ba ta taɓa kwanar wahala ba, domin yadda ta ga dare haka ta ga rana. Har zuwa kiran sallar farko ba ta rintsa ba
Kiran sallah na biyu ta ɗauki wayarta, tana dafe da mararta ta kira numbar Wahida, tana adduar Allah ya sa ta ɗauka.
Ta cika da farinciki jin wayar na ringing.
"Wash! Fahima ki taimaka mini mutuwa zan yi." Ta furta tana nishin wahala.
"Innalillahi lafiya?Ai sai da na gaya miki kar ko sha maganin nan da yawa, saboda shegen kafiyarki kika kai kanki kika baro. Allah ya sa bai illata ki ba." Ta faɗa tana mata dariyar mugunta.
"Ni in da ma ace wannan ne ya sanya ni wahala sai na ji daɗi, saboda na tabbata kwana zan yi mala'iku suna rubuta mini lada. Wahida ban san wane irin kalar miji na aura ba, domin wallahi jiya kallon kirki ban samu ba, daga ƙarshe ya tura ni waje ya rufe ƙofarsa." Ta ƙarashe maganar tana share hawaye sai kuma ta ɗora da cewa jin ta yi shiru.
"Na rantse sai Hajiya Zamzam ta biya ni kuɗina, saboda da na shafa turaren kin san Allah, toshe hancinsa ya yi, baya ta gaya mini haka zai rinƙa bina sai yadda na yi dashi."
Matuƙar mamaki ya kama ta matuƙa jin abin da ta ce.
"Anya mijin ki ba aljana ta aure shi ba? Domin na ga ko ni da na ke har na haihu, wallahi ina shafa turaren haka oga yake bina ina shan ƙamshi."
"Babu wata aljana tsabar ƙiyayya ce da taurin kai. Ba ki ji yadda ya rinƙa kushe ni yana yabon wacce yake so ba. Ni da ya kamata jiya ya zamar mini rama memorable sai ga shi na yi kwanar wahala." Ta ƙarashe maganar tana cije baki.
"Ikon Allah, ni kam ban san wane irin miji kika aura ba, amma duk ƙawayenmu da suka yi amfani da shi sun ce ya yi musu."
"Wash! Ki taimaka ki gaya mini abin da zan sha na samu na rintse. Jiya sam ban rintsa ba."
"Kai amma wannan gayen ya ɓata mana show. Ni da na kasa bacci sai zumuɗi na ke yi Allah ya kaimu gobe musha labari. Kuma wallahi ya ja miki abin kunya, saboda duk ƙawayenmu kowa sai ya ba da labarin first night ɗinsa a group sai ke? Kin san yau daren farkon ki shine topic of discussion ɗinmu."
Tsuka taja tare da jin wasu zafafen hawaye sun wanke mata fuska, saboda yau ta yi ninyar babu abin da za ta rage wanda ya faru a tsakaninsu."
Wa'iyazubillahi
"Ya zan yi? Haka nan zan shirga musu ƙaryar period ɗina ya zo kafin na gama na san yadda zan yi seducing ɗinsa."
"Gaskiya ya kamata domin hakan kamar wani abin kunya yake son ya ja miki."
"Ya ma isa ina babban yarinya kamata ya ce zai toxarta ni gurin ƙawayena."
"Allah ya kyau abu dai yi daɗi ba." Cewar Wahida cikin takaici.
"Ko gaya mini abin da zan sha."
"Ki sha kanwa za ki samu sauƙi." Ta ce tare da yi mata sallama ta kashe wayar.
Sororo ta yi cikin takaici da damuwa. Sai yanzu ta fara dana-sanin gaya mata da ta yi. Ta so ace ƙarya ta shirga musu sai dai kuma hakan ba zai yiwu ba, kasancewarsu ta san su da shegen bin ƙididdifi har sai sun gano gaskiya.
Miƙewa ta yi tana tunanin inda za ta samu kanwa amma ba ta gani a kicin ɗinta ba.
Wayarta ta ciro tare da sanar mata ta aiko direba da kanwar.
Huwais kiran sallar farko ya tashi farka daga baccin da ya ɗauke shi. Miƙewa ya yi bakinsa ɗauke da addu'ar tashi daga bacci, sai kuma ya yi salati yana miƙa.
Bayi ya shige ya yi wanka sannan ya fito masallacin gidansa. Shi ya ja musu sallah suka yi sannan ya ɗan zauna a masallacin har gari ya yi sha.
A lokacin da gari ya waye ya fito daga masallacin ya shiga gida, daidai lokacin da Wajnah ta fito direba ya kawo mata kanwar.
Cikin rashin sa'a ya kalle ta wanda ya sanya shi ɗauke kansa da sauri. Dariya ƙeta yake mata a zuciya ganin yadda ta yi wujuju da ita, alamun sam ba ta rintsa ba.
Wucewa ɗakinsa ya yi, yayin da ta bishi da kallo tana ji kamar ta jawo shi ta rufe shi da duka. Da idanu ta raka shi har ya shige ɗaki ya rufe ƙofar. Ajiyar zuciya ta saki sannan ta wuce kicin ta kaɗa kanwar a kofi tasha.
Sai a wannan lokacin ta ɗan fara sanun natsuwa ta shiga bayi ta yi wanka da alwala ta fito.
Bayan ta yi sallar tana idarwa ta ɗauki waya ta kira Mommy. Tana ɗauka ta fashe da kuka.
"Mommy, ban san cewar ƙiyayyar da Ya Huwais, ya ke mini ba ta kai haka! In kika ga yadda ya wulaƙanta ni sai kin tausaya mini. Momy kulle ɗakinsa ya ya bar ni a falo."
Tausayin ƴar tata ya kamata da ma ta san xa a rina, wai an saci xanin mahaukaciya. Sam ba ya ƙaunarta su ne suka nace auren.
"Kina jina ko Wajnah? Dole sai kin yi haƙuri kin zama jaruma, domin kin san babu so a tsakaninku. A hankali cikin kissa da kisisina irin ta ƴa mace za ki karkato da hankalinsa."
"Hmmmm! Ba ki san shi bane, jiya na tsorata da lamarinsa."
"Sam karki tsorota ki ci gaba da yi masa duk abin da kika san zai faranta ransa, kuma karki nuna masa kin ji haushi. In muka ga yaƙi canxawa sai mu sanar da mahaifiyarsa ayi wa abin tufka hanci, amma bai kamata daga aurenku afara kai mata ƙorafi ba."
"To Mommy, yaushe za ki zo? Har na fara kewarki."
Dariya ta yi jin abin da ta ce. "Ina nan zuwa ni da Anty ki Hibba, za ta kawo sauran kayan turaren wutan da ba gaba ma."
"Sai kun zo na gode Mommy." Tana gama wayar bacci mai ƙarfi ya kwasheta.
Huwais kuwa alla-alla yake gari ya waye ya bar gidan. Tun da ya farka idanunsa suke masa gizagonta, musamman da ya kwana mafarkinta.
Yana dawowa daga masallaci, ya shirya cikin shiga mai kyau ya shiga motarsa ya fice daga gidan.
Ƙarar buɗe get ɗin, ya tashe ta wanda ya sa ta miƙe a zabure tare da jaye labulen ɗakin tana hangen harabar wajen
"Kan uba! Ina wannan ɗan rainin wayon xai je da safiyar nan?" Ta yi wa kanta tambayar cikin mamaki a zuciyarta tana ji kamar ta danna masa ashar.
Sakin labulen ta yi, daidai lokacin da ya fice maigadi ya rufe get ɗin yana ɗaga masa hannu.
Zama ta yi tana huci kamar mesa, sai kuma ta shige ɗaki fuuu! Ta jawo waya. Har ta fara neman numbar Wahida za ta gaya mata, sai ta fasa tuna yadda take ta cika musu baki, wanda sanin zaman doya da manjar da suke yi, zai iya sanya wa su yi mata dariya, da gulmanta ko da a bayan idanunta ne. Fasa kiran ta yi ta fara neman numbar Ummu sai kuma ita ma wata zuciya ta hana ta musamman da ta tuna maganar da Mommy ta gaya mata.
Wayarta ta yi jifa da ita, tare da kwanciya a kan gadon tana birgima!
Huwais kuwa, a hanya yana tafe yana tunanin yadda za su kwashe da Ummu, in ta ga ya yi sammakon zuwa gidan, amma duk abin da xai faru sai dai ya faru, domin idanuwansa babu wanda suke son gani sai ita. Saboda tsoron kar ya tashi mutanen gidan a waje ya yi parking ɗin motarsa ya shiga ciki. Kai tsaye falo ya shiga, amma babu wanda ya gani sai ɓuruntu da ya ji a kicin. Ba tare da ɓata lokaci ba, ya nufi kicin ɗin domin ya san ita ce a ciki.
Hilah bayan ta tashi ta shiga bayi sai ta ga ta fara fashin sallah. Gyara kanta ta yi, ta fito daga bayin ta shiga ɗakin su Umnah ta tashe su, sannan ta wuce kicin don shirya abin karyawa.
Ita da autar su Ummu, Sauwama suka fara haɗa abincin karyawar suna yi suna hira.
Bayan sun gama kammala abincin, suka sanya a cikin fulas sannan suka sanya wanda za su kai gidan Huwais a basket.
Hilah na gyara zaman abincin yayin da bakinta ɗauke da tasbihi tana faɗin Subuhanallahi wa bihamdihi wa subuhanallahil azeem. Hadisi ne inagacce wanda ya yi maganar cewa,
Kalomi masu sauƙin faɗi a harshe, kuma mafi soyuwa a gurin Allah masu kuma nauyaya mixani.
Da wannan hadisi take amfani yawanci bakinta ɗauke da shi.
Tana ƙoƙarin ɗaukar basket ɗin ta kai mota ta ɗago idanunta.
Turus! Ta tsaya cikin tsananin mamaki tana kallon agogon da ke manne a saman bangon kicin ɗin. Mamaki ya sanya ta kasa magana sai kallonsa take yi.
"Yauwa ma za ki je ki kai mota. Ni ma bari na gama dama wa Fitha custard sai na ɗauko mayafina muje, saboda yau nake son na koma Gobbe.
Jin ta yi shiru ba ta amsa mata ba, ya sanya ta ɗago idanunta, tana kallon inda take kallo.
"A'a ango da sassafe haka, lafiya ko dai Wajnah ce babu lafiya?"
Shafa kansa ya yi cikin jin kunya yana kallonta da har yanzu ta kasa magana.
"Lafiyarta lau, kewar gida ne kawai ya dame ni.
Dariya ta kubce mata jin abinnda ya ce." Daɗi ne ya yi maka yawa kawai Huwais. Kuma in ban da abin ka namiji ne da kewar gida? Ai kamata ya yi a ce Wajnah ta faɗi haka."
"Please Anty Sauwama yunwa na ke ji, ni fa tun jiya rabona da abinci." Ya faɗa yana shafa cikinsa.
Daga ita har Hilah suka zaro idanu."Ace jiya bikinka amma ka zaina da yunwa? Ita Wajnah aikin mai take yi da ba ta tabbatar ka ci abinci ba kafin ka kwanta?"
Taɓe bakinsa ya yi yana ƙoƙarin ɗaukar filet.
Hilah kuwa karɓar filet ɗin ta yi cikin damuwa tana faɗin,"Yayana, don Allah karka ƙara horar da kanka da yunwa."
Watsa mata kallo ya yi bai ce komai ba.
"Kamata ya yi ya tafi da abincin sai su je can su ci, wataƙila Wajnah ba lafiya ba za ta iya musu abin kari ba"
"No bari na ci nawa anan."Ya ce yana kallon Hilah wacce ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 17