Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bayan ya samu guri ya zauna kan kujera. Yadda ya yi maganar, ya baƙanta mata duk da cewar ta san ba zai ɗauki lamarin da girma ba, amma ya kamata ya tsawata masa. "Ya kamata ka yi masa faɗa, saboda wallahi kan wani banzar tunaninsa ba zan lamunta ya raba mana zumunci ba." Ummu ta faɗa tana kallon Abu da Huwais yake kallo, sai kuma ya juya yana kallon Hilah wacce take tsaye tana mazurai. "Kai ba yaro bane. Sam bai kamata ace mun tsaya, muna gaya maka abin da ya kamata ba. Da ga yau kar na ƙara jin ka yi faɗa da Hamad. Karka manta ɗan'uwanka ne na jini. Ku wuce ciki ku bani guri." Ya ƙarashe maganar cikin ɓacin rai. Jin abin da ya ce masa ya ƙular da Ummu cikin fushi ta miƙe fuuu! Ta yi cikin ɗakinta. "Ka tabbatar da ka je gurin amaryarka tsakanin yau da gobe, kuma ka bata duk abin da take buƙata." Abu ya ce masa daidai lokacin da ya miƙe zai fice. Kaɗa masa kansa kawai ya yi cikin takaici ya fice yana jin zuciyarsa na yi masa tuƙuƙi. Bayan sun tafi dariya ya yi ya girgiza kansa ya bita zuaa ɗakin. Hilah ta ji daɗi da Abu yake gida, domin ta san cewa wataƙila da sai ta sha mari. Tana shiga cikin ɗakin ta rage kayanta, daga ita sai silet da vest. Kan doguwar kujera ta kwanta tare da ɗaukar wayarta ta kunna data. Da ga kunna datar tsaƙon mahaukacin masoyi suka rinƙa shigowa. Da sauri ta mayar masa da tsaƙon, wanda duk yawanci kalaman soyayya ne. Yayana, wanda na ke masifar so fiye da komai a rayuwata zai yi aure, kuma ina gayyatarka bikin, domin saboda mahimmancin wannan ranar nake son ka bayyana mini kanka a ranar. Matuƙar ka ƙi bayyana mini kanka ba zan ƙara kula ba, kuma zan yi ƙoƙari na haƙura da kai ko da ace soyayyarka ita ce ajalina. Huwais da ke riƙe da wayarsa, yana ta dariyar a bin da ta tura masa, sai kuma zuciyarsa ta buga da tsoron da gaske za ta iya rabuwa da shi. Rubuta masa ta yi ta tura, sai kuma ta kasa jurewa har ya turo mata da amsa, ganin ya kara ta bai turo amsar ba. Kiran layinsa ta Whatsapp ta yi har ta katse bai ɗauka ba. Tana ƙoƙarin ƙara kira sai ga kira sa ya shigo. Da sauri ta ɗauka tare da doka masa sallama cikin sanyin murya. "Ina fatan ka ga tsaƙona?" "Eh, na gani amma kuma kalamanki na ƙarshe da hukuncin da kika yanke sun yi tsauri a gareni." "Kuma na riga na ya ke shawara. In har kan sona da aure ka bayyana kanka a ranar bikin Yayana, in kuma ka ƙi bayyana kanka na haƙura da kai, domin babu inda na taɓa jin anyi aure ba tare da anga juna ba." Ajiyar zuciya ya saki, wanda bugun da ya sanya zuciyarta har sai da ta kauda wayar a kunninta ta rintse ido. "Kin shirya ganina?" "Eh, kuma na yi maka alƙawarin aurenka ko da ace kai musaƙi ne." "Shikenan, zan yi tunani in har ya kamata na bayyana miki kaina zan bayyana." Yana faɗin hakan ya kashe wayarsa cikin tsananin tashin hankali. Safa da marwa ya fara yi a ɗakin, saboda yana jin ko aure ya yi ba zai iya daina jin muryarta da take kwantar masa da hankali ba. To amma kuma ta ya ya zai bayyana kansa kamar yadda ta buƙata? Shin inta gan shi wane hali za ta shiga, wanda ya san lamarin da ƙarshe ba xai yi daɗi ba, saboda yadda ta riga ta mutu a kansa. "Zuciyarsa ta ba shi shawarar ya tura wani da bata taɓa sani ba, amma sai dai kuma ta gargaɗe sa da aikata hakan, saboda in har ta ɗauka shi ne mahaukacin masoyi ta kamu da son wancan, sai ya ce an yi ba ayi ba. A ransa ya ji ba zai iya bayyana kansa ba, domin a wannan lokacin yake son ya ɗauko rigimar da zata wargaza farincikin zuriyarsu ba, don haka a kwai sauran lokaci. Wayarsa ce ta yi ƙara alamun an turo masa da tsaƙo. Da sauri ya ƙarasa gurin wayar don ya duba tsaƙon "Yayana, na gaya masa cewar ya bayyana kansa gareni ranar bikinka, kuma na yi masa barazanar rabuwa da shi matuƙar ya kasa yin hakan, amma bai ce mini komai ba, sai ma ya kashe waya. Na san zai kira ni kuma ya amince, saboda na san yana sona. Wayarsa ya ije cikin damuwa ganin abin da ta rubuta. "Anya Hilah za ta yafe mini matuƙar ta san ni nake wasa da hankalinta?" Ya yi ma kansa tambayar cikin damuwa. Ga mamakinsa sai ya ji hawaye na bin ƙuncinsa. Kansa ya dafe da ke matuƙar yi masa barazana. Ta bangaren amarya gyara kawai ake yi babu kama hannun yaro. Tun a ranar da aka sanya bikin ta kama shan kayan mata ba tare da ta bi ƙa'idansu ba, saboda so take bayan biki, ya raina kansa. Wannan ji da kai da sham ƙanshi da yake mata ya gane kuransa. Wajnah na cikin jadawalin mata da ba su tausayawa namiji a bangaren soyayya da aure, domin a tsarin rayuwarta. Ta auri namiji da zai zamo bawanta wanda za ta rinƙa juyashi yadda take so. Wato ta samu miji janitalau, wanda ta ci alƙawarin ko da ba ta samu ba, sai ta maida shi hakan ta hanyar shaye-shayen maganin mata. A burinta ta so auren namiji wanda yake masifar sonta, don ta yi amfani da soyayyarsa ta juya shi yadda take so, amma cikin rashin sa'a sai Allah ya jarrabce ta da son Huwais, wanda shi ko a cikin family ta san basa shiri, saboda yadda take nuna wayewa da yawa. A rayuwarsa ya tsani mace wacce feminism ɗinta ya yi yawa. Tun kafin ta fara nuna tana son shi, ya gane ita mace ce wacce take ganin mata sun samu daraja ne ta hanyar buƙatar da namiji yake da shi a garesu, wanda hakan ya sa take ganin kamar namiji bawa yake a garesu, kuma suna da damar da za su juya su yadda suke so. Tun lokacin ya ɗaura mata karan tsana sam baya shiga sabgarta. Yana ganin ta a mara hankali da ƙarancin ilmin addini, domin duk wani gata da daraja mace Allah ya bawa mace, saboda ita ma halitta ce wcce ya halitta don su bauta masa. Zaune take a cikin falon ƙawarta mai suna Fahima, da waya a hannunta tana zaɓan kayan mata da Hajiya zamzam; wacce take saida kayan mata a online ta tura mata. Bayan ta zaɓi kayan da yawa wanda zaɓen yawanci Fahima ce ta taya ta, kasancewar ita matar aure ce har da yarinya ɗaya. "Kin ga wannan sha ka ga aikin wallahi ki ɗauka yana da kyau, domin Hajiya Zamzam in har kika ga ta kawo kayan mata na gargajiya yana da kyau, saboda kayanta kin san duk na bature take siyarwa. Kuma da bikina na sha irinsa, shi ne na gaya miki Baban Amrah ya bani kyautar hajji, saboda duk lokacin da na sha ni kaina da ƙyar nake iya riƙe kaina." Dariya ta kwashe da shi suka tafa. Aikuwa ya zama dalo na siye shi. Don so na ke Ya Huwais ya raina kansa. Ni fa so na ke ko kara na ije ya kasa tsallakawa, domin ya san in bai yi mini abin da na ke so ba, ba zan faranta masa rai ba." "Eh, gaskiya. Ke ai magani sosai ya kamata ki siya saboda wannan miskilin da za ki aura. Kin ga in ba tsaye kika yi masa ba, wallahi wulaƙanci za ki sha sosai. Musamman da ba ya sonki." Ƙuta ta yi cikin ɓacin rai." Ki barshi zai raina kansa sosai. Ba ni yake cika yake sharewa ba, saboda kawai na ce ina son shi. Wallahi sai na maida shi namijin ta ce babu boka babu malam. Don kawai Ummu ƴar'uwar mom ce, amma da ko ita sai na shiga tsakaninsu babu boka babu malam." Dariya ta saki." Ai gara ki je da shirin ki maza yanzu babu tausayi a tsakaninmu da su, saboda kina musu sakwa-sakwa sai wulaƙanci da rashin mutunci. Sam bana son na kasance daga cikin irin matan da suke hide my identity a sirrin ƴa mace groups, kin ga kuwa dole na dage na kashe kuɗina na gyara jikina, don na siyawa kaina daraja da mutunci." Dariya suka kwashe dashi suka tafa, ban da Habiba ta take kallonsu cikin mamaki tana murmushi. "Ke dai sha'anin rijalu sai su. Ƙiri-ƙiri sun mayar da mata mahaukata sun sanya musu depression." "Ai wallahi su suka so. Ke ni fa duk macen da ta zauna namiji na wulaƙanta ta ta ji za ta iya ne, don haka in har kuɗi na aiki zan siya maganin mata na gyara jikina, wanda kafin na ba shi haɗin kai sai ya yi kuka." "Lallai ba ki da imani wallahi." Habiba ta kalle su da suke ta magana ba ta sanya baki sai a lokaci ta yi murmushi ta ce," A tunaninku shan kayan matan shi zai gyara rayuwar auren ku? Ba zan fasa gaya muku ba a matsayina na ƙawarku aminiya. Wallahi ku guji shaye-shayen kayan nan da kuke yi, saboda ba ku san da me aka haɗa su ba musamman da bature, domin zai iya kai ku tashar dana sani. Kuna cusawa kanku abin da ba ku da tabbaci a kansa, don kawai ku juya mazajenku. To daga ranar da kuka daina shan kayan matan, ko kuma ya daina muku aiki shi kenan kun rasa damarku? Ni a ganina wannan kuskure ne, domin in har za ku riƙe biyayya da haƙuri za ku juya mazajenku yadda kuke so." "Hmmm!Ta fara ni wallahi ban san dalilin da ya sanya kika na ce za ki zo yau ba." Wajnah ta ce tana aika wa Habiba da mugun kallo. "Ki barta ta ci gaba bakinta ne ai. Gajiya da maganar ne ba ta yi ba, kuma kema in ban da abinki har akwai abin da za ta faɗa ya dame ki. Ita da take yi wa mijinta biyayya ai kin ga sakamakon da yake mata. Ƙiri-ƙiri ya muzanta ki a gabanmu, amma kike wannan maganar. Habiba ki zauna ustazanci ya kashe ki, kar ki nuna wayewa kina abu kamar ba graduate mai digiri da masters ba." "Sai ilmina ya sa na kar na yi wa mijina biyayya? Faɗa ya yi mini kan na yi dare ban dawo ba, kuma in har da bai yi mini faɗa ba, sai na yi tunanin baya sona, saboda duk namiji mai hankali da kishin matarsa ba zai ƙi yi mata faɗa ba a lokacin da muka dawo." "Eh, ai kin san ni mijina baya kishina, baya ƙaunata shi ya sa bai ce mini komai ba. Ki yi ta zama yana kashe rayuwarki kina fakewa da sunan biyayya." "Ki ƙyaleta Fahima ta yi ta yi dama ta saba. Cewar Wajnah da take harararta. "Ni har mamakin yadda muka kasa daina ƙawance dake na ke yi, domin Hausawa sun ce sai hali ɗaya ya zo ake ƙawance, amma sam ke ba ki wayewa kina abu kamar ba cikakkiyar wayyaya ba." "Ni dai ba zan fasa daina gaya muku haskiya ba. Don haka shawara ya rage ma mai shiga rijiya. In kun ga dama ku daina shaye-shayen kayan mata. In kuma ƙun ƙi ina jiye muku ranar da za ku yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada don za ku tsinci Talatarku a Laraba." "Ke ce dai za ki tsinci Talatarki a Laraba, saboda yadda kike nuna kina tsoron Abban Iklas, watarana sai ya sanya ki kuka, don sai dai ki ji a shanun tashi ya yi auresa." "Wannan tsakaninsa da Allah ne. Ƙin gaya mini shi ne kawai laifin, amma ni ba zan iya hana shi abin da Ubangiji ya ba shi dama ba." "Allahu Akbar! Sannu mai sani. Allah ya sa da gaske kike kar kizo mana kina kuka. Ni da kika ganni mijina da kishiya sai dai na ƙiyama da ba ni da ikon hanawa, amma bai isa ya ce zai yi aure ba." "Lailai ko kina da aiki in har mazan zamanin nan ne." "A'a Habiba, kar ki yi mata baki. Ko ni da Ya Huwais baya sona ba zan taɓa bari ya yi mini kishiya ba, saboda ko ƙanwarsa da yake ji da ita wallahi ina shiga sai na raba shi da ita. Ballantana wata kishiya can." "To Allah ya ba ku sa'a. Ni tafiya zan yi kar habibi ya dawo don zan yi masa tuwon shinkafa." "Hmmmh! Kina wahalar da kanki ga masu aiki, amma ki je aiki ki dawo ki yi girki." Cewar Fahima. "Ai ni kuma in dai abinci ne bani da matsala, saboda ni a shegen kishina ko abincin Ummu ya ci ba nawa ba, za a samu matsala." "Ni dai ba zan iya girki ba, haka kawai da girkin zanji ko da rainon yarsa da ɗaukar ɗawainiyarsa?" "Duka ai bautar Allah kike yi." Habiba ta ba su amsa tana riƙe da ɗan makullinta. "Bar ni na ji da ɗaya haka kawai na ɗaura wa kaina wahala. Yawancin full house wife duk a ƙanjame suke, saboda ba sa samun lokacin da za su huta ga ɗawainiyar gida ga miji da yara." "Allah dai ya bamu lada kawai." Cewar Habiba don ta guddura da maganar. Wayarta ta yi ƙara, wanda ta kalla ganin numbar mijinta ne, ya sa ta ruga da gudu zuwa gurin motarta tana ɗaga musu hannu. Bayan fitarta suka dawo cikin falon suka zauna. "Ni fa Habiba mamaki take ba ni, yadda ta yi sakaci mijinta na ba ta lokaci in xa ta fita, domin duk yadda nake son Ya Huwais ba zan aminta da wannan dokar ba." "Ita ta ga za ta iya, ai sai ta yi." Fahima ta ce tare da zaunawa a gefenta suka ci gaba da zaɓen kayan matan. Huwais ransa a ɓace yake, tun lokacin da Abu ya tursasa shi zance zuwa gurinta. A ransa yana jin bai san abin da zai ce mata ba, domin shi ko kallon kirki baya tunanin zai iya mata. Tsaki ya ja tare da ɗauko wayarsa da ke maƙale a soket yana caji. Numbar Najib ya kira wanda ringing ɗaya ya ɗauka da sallama. "Abu ya tursasa ni zuwa gurin Wajnah, please gobe da yamma zaka raka ni." Ya na faɗin haka, ya kashe wayar don baya son ya ce masa komai. Da ƙyar Abu ya shawo hankalin Ummu, har ta bar maganar don ta yi ninyar hukunta Hilah, amma maganganun da ya gaya mata, ya sanya ko a fuska ba ta canza mata ba. A mota suna tafiya shi da Najib babu wanda ke magana. Najib ne yake tuƙi da motarsa, shi kuma hankalinsa na kan wayarsa da yake chatting da Hilah. Duk da cewar da ɓacin rai a fuskarsa, amma duk tsaƙon da ya tura mata ta turo mishi da reply sai ya murmusa. "Ya kamata ka sanar mata da zuwan mu fa." Najib da ya waiwayo ya kallesa yana faɗin haka. Ganin bai tanka masa ba, wanda hakan ya tabbatar masa sai bai ji shi ba. Hannunsa ya kai ya fisge wayarsa tare da duba abin da yake yi. "Iska na wahalar da mai kayan kara. Wallahi Huwais, ya kamata ka farka daga mummunar mafarkin da ka yi na mallakar ƙanwarka, da ka san ba za ku taɓa zama a inuwan ma'aurata ba. Ka rungumi ƴar kyakyawar matarka ku zauna lafiya." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 14 "Iska na wahalar da mai kayan kara. Wallahi Huwais, ya kamata ka farka daga mummunar mafarkin da ka yi na mallakar ƙanwarka, da ka san ba za ku taɓa zama a inuwan ma'aurata ba. Ka rungumi ƴar kyakyawar matarka ku zauna lafiya." "Please, bana son wulaƙanci ka bani wayata. Tun da ka ga Allah ya jarabce ni da sonta babu makawa sai na auret.." "Ta ya ya Huwais? Tun da kake ka taɓa ganin an yi irin wannan auren? Sheɗan ne kawai ke ruɗarka kaɗa maka gangar sheɗan." "Mu bar maganar kana ɓata mini raina." Ya furta cikin ɗaga murya. "Zan yi shiru ne don kar ka ɗora laifin a kan Wajnah, da ba ta ji bata gani ba, amma ba zan fasa gaya maka gaskiya ba, a matsayina na amininka, amma ka sani auren ka da Hilah sai dai in ana mutuwa a dawo, sai ku dawo ba a matsayin ƴan'uwa ba." "In kuma Allah ya ƙaddara sai ka mutu." "Ta ya ya?" "Ni ma ban sani ba amma jikina yana ba ni matata ce!" "Hammh!" Kawai ya ce cikin takaici ya ci gaba da tuƙi ba tare da ya ce masa komai ba. Da suka isa ƙofar gidan maigadi ya buɗe musu sula shiga. Wajnah na zaune a cikin ɗakinta mai dillah na dirzanta. Ƙanwarta Batula ta ƙwanƙwasa ƙofar. "Waye?" Ta yi tambayar cikin ɗaga murya. "Anty Wajnah, Batula ce. Mommy ta ce in gaya maka Ya Huwais na falon Daddy." Da sauri ta ture hannunta jin abin da ta faɗa. "Ok, ki ce gani nan zuwa." Ta bata amsa yayin da fuskarta ya cika da farinciki. "Ana dilkan za ki fita? Ki gaya mishi ya jira ki." "Mijin nawa zan shanya ya jira ni? Kin san da yadda na samu ya zo?" "To asarar dilkan za ki yi?" Ta yi mata tambayar a maimakon ta ba ta masa. "Eh, wankewa zan yi in ya tafi na dawo." Ta ba ta amsa tare da shigewa bayi. Saboda tsabar murna ɗauraye jikinta kawai ta yi. Cikin ƴan mintina da bai fi goma ba, ta shirya kanta cikin riga da siket masu kyau ta sanya mayafi ta fice zuwa falon. Da sallama ta shiga, idanunta na kan Huwais, da yake riƙe da waya har yanzu chatting yake yi yana murmushi. Murmushin da yake yi ya sa ta yi tunanin ko ita yake yi wa. "My baby, na yi tunanin ba za ka zo ba, sai an kawo maka ni a matsayin mallakinka." Ta furta cikin kissa tare da samun gefensa ta zauna har suna gogan juna. Ba tare da ya jinkirta ba, ya matsa can ƙarshen kujera bayan ya haɗe rai, ya ɗan tsaki ƙaramin tsuka, wanda ya sanya jikinta ya yi sanyi. Wataƙila da ta shigo ba ta yi tunanin da wani yake ba, domin ba ta lura da Najib da yake kujera one seater, sai da ya yi gyaran murya. Kasancewarta wayayyar mace sai ta basar da abin da ya yi mata. "Laah, ka ce da abokinmu kake tafe?" Ta yi masa tambayar tana kallonsa, sai kuma ta mai da hankalinta kan wayarsa da yake kallo. Datar ya kashe ba tare da ya tanka mata ba yana kallon gefe. Najib ne ya ce,"Amarya bakya laifi ko da kin kashe ɗan masu gida." Dariya ta yi tare da jin farinciki na kirarin da ya yi mata, wannan kirarin ya sanya kika shanya mu ko? Ko da yake laifinmu ne da bamu sanar miki ba." "Ku yi haƙuri ana mini dilka ne sai dai na wanke." "Mun haƙura dama ba mu yi fushi ba." Murmushi ta yi jin abin da ya ce tana satar kallonsa da ya ƙara kici-kici da fuska. "Ina wuni?" Kamar ya amsa kamar kuma motsi kawai da bakinsa ya yi. Ganin haka ya sanya Najib ya miƙe,"Ni bari na baku guri da fatan za ki kula mini da shi?" Yaƙe kawai ta yi ganin yadda yake cisgata, amma a zuciyarta ta ji daɗin fitan nasa, musamman da tun da ta shigo ta nemi natsuwarta ta rasa, yayin da kayan matan da take sha suka fara aikinsu. Ji ta yi kamar ta rungume shi ko ta faɗa jikinsa. Tana mishi wani irin so musamman yanzu da take jin baba so akwai buƙatar ta ji ta a jikinsa. "Ya Huwais don..." "Please, ba na zo bane don ki ɓata mini rai. Bisa tursasawar iyayena nazo. Na sha gaya miki bana ƙyaunarki. Sam ba ki a cikin jadawalin matan da na ke so, amma kin na ce dole sai kin aure ni, don haka ki shiryar kurɓar ruwan guban da yafi na maciji dafi a cikin gidana, saboda ba za ki taɓa samun farinciki a cikin gidana ba." "Eh na ji kuma na amince, matuƙar zan rayu a ƙarƙashin inuwar aurenka, a shirye na ke da ko wane irin zama a cikin gidanka." "Shikenan, sai ki je gidan ga shi nan ki zauna, amma ni ba za ki taɓa mallakata ba, kuma na gaya miki ina da wacce nake so, nake burin ta zamo uwar ƴaƴana." "Don Allah Ya Huwais, ka taimaka mini wallahi a shirye na ke na ba ka farinciki, domin ina matuƙar sonka."Ta ce bayan ta duƙa ta kama rigarsa. Fisge rigar ya yi cikin ɓacin rai," Ba za ki taɓa mallakar zuciyata ba, domin ba ki da matsuguni a cikinta." Kukanta ya ƙaru jin abin da ya ce. Fara tafiya ya yi. Tsaye ta yi cikin damuwa tana kallonsa. Lokaci guda ta ji ranta ya ƙara ɓaci, wanda har ta gwammace da bai zo ba. Yana ƙoƙarin fita Najib ya murɗa ƙofar ya shigo. Kallonsa ya yi da ya fice ba tare da ya tanka masa ba, sai kuma ya kalli Wajnah da har yanzu hawaye take sharewa. Kunya da takaici suka lulluɓe shi, ya kasa ce mata komai sai dai ya juya ya fice. Wajnah ji ta yi kamar ta kashe kanta. Wani tangaras da aka yi kwalliyar fulawa da shi, ta ƙwada shi da ƙasa tare da fashewa da kuka ta yi sashin Mommy. "Ya Huwais ba ya ƙaunata mommy." "Ki daina ɓata hawayenki mai wuyar ki shiga cikin gidan, domin kina da kyau da babu namijin da zai wulaƙnata ki." Abin da ta faɗa ya ɗan sanyaya zuciyarta, amma har yanzu tana jin tana mata ƙuna. Rintse idanunta ta yi tana kin kamar ta mare shi lokacin da yake gaya mata yana da wacce yake so, wani irin mugun tsanarta ya shiga cikin ranta har take jin za ta iya ajalinta. "Yanzu abin da ka yi ka kyauta? Don Allah ka tausayawa yarinyar nan, masoyinka ba ya taɓa zama maƙiyinka." Najib ya furta cikin ɓacin rai ya ɓna kallonta. "Yanzu mu da muka zo yin maganar abin da za mu ba su da biki ga shi nan ka ɓata komai, wallahi kunyar yarinyar na ji ya sanya na kasa magana." "Duk abin da na yi mata laifinta ne ai ba a aure dole." Tsaki kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba cikin takaici. Haƙiƙa Ummu ta shirya wa bikin nan domin kayan lefen da aka haɗa kaya ne na gani na faɗa. A falo aka baza kayan suna ta gani cikin sha'awa. Hilah ita kanta kayan sun yi mata ƙwarai! Don Ummu ta yi ƙoƙari sosai. Gidan da Huwais zai zauna gida ne mai tsananin kyau da tsari. Gidan part biyu ya kuma haɗu sosai. Daga sashin Wajnah sai na shi mai ɗauke da ɗaki biyu da dining kamar dai Wajnah. Abu ya gina masa gidan mai kyau da tsari. Iyayen Wajnah sun yi matuƙar ƙoƙari, domin hatta sashinsa sai da suka cika da kaya, duk da cewar Abu ya hana domin Huwais zai gyara

Chapter 10 of 17