ya sa ta fasa.
Huwais da ya ji dawowarta ya taho da sauri don y ganta yana shigowa Ummu ta ji daɗin hakan.
"Sannu da fitowa Ummu." Ta furta cikin girmamawa.
Ummi da take a fusace ba ta yi wata-wata ba ta ɗuke ta da mari.
"Haba Ummu mai ta yi miki?" Ya yi tambayar cikin tashin hankali wanda kafin ya gama ta ɗaura masa na shi, sai ya riƙe kumatunsa cikin tsananin ɓacin rai.
"Haihuwarku na yi! A tunaninku za ku yi mini wayo ne? Kar nake ganin ku marasa tunani kawai. Na tambayeka inda za ka ka yi mini ƙarya she tare kuka fita? In har ba rashin gaskiya kuke ƙullawa ba uban mene ne na ƙin gaya mini gaskiya. Har da ke munafuka kin kwashi littafai za ki makaranta gidan uban wa kuka je?" Ta yi musu tambayar cikinn tsare ido.
Mamaki ya kama su duka musamman shi da yake tunanin wa ya gaya mata.
"Ummu kar ki yi zargi babu inda muka je kuma ni ba ƙarya na yi miki ba, da gaske tare muka fita da shi."
"Ok Hamsiya ƙarya ta yi maka da ta ganta ta yi parking ka shiga cikin motarta ko?"
Zare ido ya yi don ba shi da bakin magana, amma da ya tuna umurnin da ya ɓata, kar faruwar hakan ya sa ta ƙi bin umurninsa domin so yake ta saki da shi ya koya mata sonshi yadda babu wanda ya isa ya raba su.
"Eh, dama ita za ta rage mini hanya kuma abin da ya sa ban gaya miki ba, sam ba kya son kusantarmu da ita, wanda ban san dalili ba."
"Dalili kake nema na ga ko cewa na yi ba za ka fita ba, dole ka yadda tun da ni na haife ku?" Ta ce cikin zafi.
Abu da ya ji hayaniya daga sama ya saukkowa da sauri tare da ƙarasawa gurinta ya kama hannunta.
"Kai Huwais, tafi inda za ka. Hilah je ki yi wanka kici abinci." Ya basu umurni wanda ya sa suka juya suka fita.
"Ke kuma muje ciki ina son magana dake."
"Ni ma maganar nake son mu yi." Ta ce tare da juya babu musu ta haye sama ranta na tuƙiƙi.
Da ya shigo ya same ta a tsaye sai safa da marwa take yi. Hannunta ya kama tare da ƙarasawa da ita gaban frij ya ɗauko ruwa mai sanyi ya zuba a cup, ya miƙa mata wanda babu musu ta karɓa ta shanye.
"Kina zafafa wa yarannan! Ki tsani tun ka ba sa tunanin wani abu sai su yi zargi bayan babu komai a ransu illa shaƙuwa ta jini."
"Kai ne idanunka ya rufe kake ganin haka, amma ni na san mai nake ganin yaronnan a zuciyarsa. Ba ka san wane ne Huwais, ba ne shi ya sa kace haka, amma ni na haife shi na san abin da yake so da wanda baya so."
Ta yi shiru ko zai ce wani abu, amma sai ta ga bai ce komai ba wanda ya bata damar ɗorawa da ce,
"A lokacin da ya ji Hammad na sonta kamar zai yi hauka, wai ta fi ƙarfin shi kuma shi yake so ya zaɓa mata miji, amma a wannan ka ji ya yi ƙorafi? Ka na dai sane da irin haukan da yake nuna wa duk wanda ya bayyana soyayyarsa gareta, amma wannan ƙorafin me ya yi? Babu hankalinsa kwance har shawara yake bata. Na tabbata da ace babu sa hannunsa da yanzu ya tada hankalinsa. ko da ace ita babu komai kuma ba ta gane ba shi sonta yake."
"Don Allah ki daina wannnn haukar tunanin ta yaya za a yi ya so yar uwarsa wacce suka fito ciki ɗaya? Kawai shaƙuwar jini ne, amma babu wani soyayya tunanin ku ne na manta na rashin hankali." Ya faɗa cikin ɓacin rai yana kallonta.
"Humh ba za ka gane ba kamar yadda ba na fatan lokacin da zai ganar da kai hakan, amma mafita ita ce kawai ayi musu aure. Hankalina zai fi kwanciya tun dama shi Wajnaah tana nan tana jiransa har ta gama servise don kamar ta samu aiki ba ta fara zuwa bane.."
"Ni ma tunanina hakan, amma shi kawai ita sai ta gama karatun don ba zan yi mata aure tana karatu ba, duka guda nawa take."
"Ko shi ɗin ne a fara masa hankalina zai fi kwanciya." Ta ce tana yarfar da hannunta cikin rashin dubara, yayin da zufa ke keto mata.
"Kwanta ki huta zan yi mishi magana na ji ra'ayinsa sannan zan yi wa mahaifinta magana."
"Kan me za a ji ra'ayinsa uzurin da ya bayar ai ya je kuma ya dawo. Yarinyar ma ta yi haƙuri, duk da tarin masoyanta ta zauna ta jira shi har na tsawon shekaru biyu, ai ta yi masa halacci in ba butulci xai yi mata ba." Ta ce tare da kwantawa kamar yadda ya bata umurni.
Kamar yadda ya bata shawara sai ta ƙi yi har aka yi kwana uku duk da tarin tsaƙon da mahaukacin masoyi ke tura mata, amma da ta tuna ko don ta fita da ga zargin Ummu da take ganin kamar ta san mutumin ɓoyewa ta ke yi, sai ta saka a ranta gara ta yadda ta yaudare shi don ya bayyana kansa.
Ta fara kula shi da kalamai mai daɗi har ta sanar mishi da tana son shi wanda ya yi dariya da stikers tare da nuna farincikin sa ya ce,
"Jikina na bani kamar bakya sona kin amince ne don na bayyana kaina, amma ki sani ina da hankali da wayau, domin a iya sonki kawai na haukace don haka zan gwada soyayyarki na ga mizaninta."
Tun daga ranar bai ƙara yi mata magana wanda har aka kwashe sawon sati biyu.
Tun ba ta damuwa har ta fara shiga, sai ya zamana kullum cikin tunanin yaushe zai kira to ko ya daina sonta ne, in kuma haka ne kan wane dalili zai sanya ta fara tunaninsa sannan ya fita daga rayuwarta.
Ire-ire waɗanɗan tarin tambayoyin suke damunta kullum wanda ta rasa amsarsu.
Zaune take ta rafka uban tagumi hannu biyu-biyu. Idanunta cike fal da hawaye.
Kamar dai kullum tunanin mahaukacin masoyi take yi. Bayan haukarsa ta lura mutum ne mai izza da girman kai. Domin a tarihin rayuwarta ba ta taɓa yi wa wani magana ba ya gani, amma babu reply. Sai ga shi yau ta yi duk kimarta da ji take ita ma wata ce. Ya ga messeges ɗinta amma bai duba ba.
"Anya ma yana sona?" Ta yi wa kanta tambayar tare da miƙewa ta fara taku a ɗakin.
Tabbas a ranar musabaƙarsu ta yi tunanin ya shigo rayuwarta ne don kar ya barta ta yi nasara, amma bayan ta dawo ya kawo mata kyauta sai wannan tunanin na ta ya kau.
"Ƙanwata!"Ta ji muryar Ya Huwais da ya ƙaraso har cikin ɗakinta tare da rufe mata fuska.
Ɗan murmushi ta yi wanda iya kansa saman leɓenta. Da hannunta tasa ta kamo hannunsa ta jawo shi gabanta.
"Ya Huwais ka yi kyau matuƙa! Ina zuwa haka?" Ta ce masa tare da tambayarsa.
Ba tare da ya amsa mata tambayar ba ya zauna a gabanta tare da kama hannunta ya rungume a kirjinsa yana jin kamar ita ya rungume, wanda ya sanya ta maza ta janye hannun.
"Ina tsoron Ummu domin mundin muka ƙara shiga hannunta ba za ta yi mana da sausauci, don a wancan ranar Abu ya ce ce mu. Kuma ina zargin ta saka Hamsiya ta rinƙa spying ɗinmu"
Kallonta ya yi cikin tausayawa. Ummu ta fita dubiya ita da Abidin dalilin da ya sa nazo kenan."
Jin abin da ya ce ya sa ta saki ranta ta na yaƙe masa baki.
"Meke damunki? Na lura kwana biyu ba kya magana, duk da cewar ba ki da yawan magana, amma shuru-shurun ya yi yawa."
"Babu komai." Ta ba shi amsa tare da raurau da idanunta sai hawaye.
"Wai ke baki da hanyar da za ki sanar ma mutum kina cilin damuwa sai kuka?" Ya yi mata tambayar cikin takaici ganin hawayen sun ci gaba da zuba.
TUNATARWA
Shin kina daga cikin matan da karatun Novels yake ɗauke musu hankali suke barin sallah ta wuce su? Ko kina daga cikin masu daina karanta Kur'ani ko azkar duk saboda karatun Novels? Don Allah yar'uwata musulma ki daina barin sallolinki na wuce ki saboda karatun litattafai Hausa, saboda ko mu MARUBUTA da muke yin typing da zarar lokacin sallah ya yi muke tashi mu yi sallah. A kiyaye da ibadu musamman sallah saboda ita ce farko da za a fara dubawa a cikin ayyukan mu. Da fatan za ki ji kuma ki hankalta. Fatanmu mu gudu kuma mu tsira tare. Allah ya bamu ikon aikatawa Amin. Taku Jamila lawal Zango.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 7
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Wai ke baki da hanyar da za ki sanar ma mutum kina cikin damuwa sai kuka?" Ya yi mata tambayar cikin takaici ganin hawayen sun ci gabaa da zuba.
Ƙoƙarin sharewa ta yi tare da kallonsa da yake tsaye shi ma ita yake kallo.
"Kin san fa ba kya ƙarya wannan dalilin ya sa da kin yi nake gano ki, ko a yarinyatarki." Ya ce mata wanda ya sa buɗe baki za ta gaya masa haskiyar damuwarta.
"Mahaukacin masoyi ya daina kir..." Maganar ta maƙale mata sakamakon wani birkitaccen kallo da ya yi mata.
"To kuma kan me za ki damu kanki don ya daina saboda dama neman hanyar rabuwa muke yi da shi, cikin sauƙi kuma ya kori kansa? Ni banga dalilin damuwar hakan ba." Ya faɗa ransa a ɓace.
"Ni ma haka nake gani, amma ban san dalilin da ya sa zuciyata ta damu da hakan ba, domin sati biyun sa bamu waya sai na ke jin na kasa sukuni. Duniyar ta yi mini zafi." Ta ba shi amsa cikin wauta wanda hakan ya sa ya yi sororo yana kallonta.
"To kan me za ki yi tunaninsa na ga kina da wanda kike so? Ke da bakinki kin gaya mini ba ki da ra'ayi akansa?"
"Eh, haka nace. Ni ma haushin zuciyata na ke ji a bisa abin da ta bijiro mini da shi."
"To wannan ba damuwa bane, kuma da yau kar na ƙara ganin kin saka kanki damuwa, domin kamar kin tsose ƙwallon mangwaro ne kin huta da ƙuda."
"Har yanzu ka kasa fahimta ta Yaya, na gaya maka zuciyata ta aminta da shi."
Kallonta ya yi kamar na baki da hankali tare da zare idonsa.
"What! Mai kika ce? Kin ko san girman abin da kika saka kanki a ciki? Ni fa cewa na yi ki nuna masa soyayyar ƙarya, don mu gane wanda yake wasa da hankalinki amma ban ce ki aminta da shi ba, domin in har bai bayyana kansa ba bani da hanyar nemo miki shi." Ya faɗa yana kallonta da mamaki tare da kishi sosai a ransa ganin haka take da sauƙi da yawa, don ya ɗauka zai sha wuya sosai. To in da kuma ba shi bane shi ke nan ya rasa ta kenan.
"Ba laifina bane laifin zuciyata ce. Kuma in har za ka iya ganin laifina tabbas za ka iya ganin laifin jaririn da ya faɗo duniya a mace."
"Humh." Ya ce don ya rasa bakin magana sai kallonta yake yi.
"Yanzu to mene ne abin yi?" Ya tambayeta cikin rashin dubura.
"Ni ma ban sani ba kuma na ga kai ka ga kawo sharawar." Ta ce tana watsa hannunta.
"Mu bar maganar yanzu ma za ta shi ki haɗa mini abincina ki bawa wannan munafukar ta kai mini ɗaki."
Duk halin da take ciki sai da ta murmusa."Ba ita ta kashe zomonn ba, rataya aka ba ta. Tun tana yarinya Ummu ta ɗauko ta. Cinta da shanta duka kanta yake, idan ba ta yi mata biyayya ba ta butulce."
"Duk da haka zan yi maganinta."Ya ce yana danna wayarsa.
Da ta fita sai ya bita da kallon mamaki yana jin sam bai kyauta mata ba.
Ko da ta dawo zama ya yi, ya rinƙa kwantar mata da hankali da ƙarfafa mata gwuiwar mahaukacin masoyi zai dawo.
"Damuwata ya hana ni numbar da xan kira na ji ko da wani abu ne ke damunsa, sannan na yi masa magana ba zai kula ni ba kuma alamun ya gani."
Da ƙyar ya samu ya rararsheta har ta daina kukan.
Da fari ta jure amma daga baya sai ta ji ta kasa ta koma ruwa. Abin duniya ya haɗu ya yi mata yawa. Ga exam da zata fara saura kwana biyu.
Lokaci guda ta rame ta fice hayyacinta ko abincin kirki ba ta ci. Ta zama tamkar amarya, don ko fitowar da take yi su yi hira da daddare ta daina.
Ganin halin da ta tsira sai suka fara ƙorafi musamman Umnaah wanda hakan ba ƙaramin takurara ya yi ba, domon suna matuƙar son junansu. Amnaah ƙaracin shekaru bai saka ta gane ba, sai dai ƙorafi da take mata ta daina mata wasa. Dama ita Azerh cele ce ba ta damu da rayuwar kowa ba daga kallo dai chatting.
Ganin hakan su Abidin suka tuntuɓi Yayan na su tare da tsare shi da tambayoyi.
Take ya ji babu daɗi ganin a dalilin biyewa muradin zuciyarsa ya ɓata farincikin kowa.
"Ni fa ina zargin patiality da Ummu ke nuna wane ya fara damunta. Which isn't good at all, domin ina agains ita dukanninmu ita ta haife mu." Cewar Naufal.
"Don Allah Ya Huwais, ka yi mata magana domin duk mun yi mata, amma fa ce babu komai. Muna damuwa da yanayinta ko abinci kirki ba ta ci, domin breakfast sai ta kai har 11 ba ta yi ba."
Sosai ya ji babu daɗi yayin da zuciyarsa take gasgata masa ya tabbata azzalumi mai son zuciyarsa.
"Ku yi haƙuri in sha Allahu, za ta daina I will talk to her. I think distressed na karatun exam ne."
"You have to, kuma bana tunanin haka domin exam baya bata tsoro saboda kafin lokacin ma ta gama karatun shi, ina ga dai kamar yadda Ya Naufal ya faɗa haka ne." Cewar Abidin
Binsu da kallo ya yi har suka fice daga ɗakin.
Daga ɗakin na sa kai tsaye gurinta suka nufa, tana kwace da waya a hannuta tana kallon tsaƙon da ya yi mata kafin ya daina mata magana.
Kuka take sosai tana jin matuƙar kewarsa da ƙaunarsa na mamaye zuciyarta.
"Anty Hilah kuka? Ummu ne ta dake ki?" Amnaah ta furta wanda ya sa suka yi saurin hawa gadon suna tallafo ta.
Share hawayenta ta yi tana girgiza musu kai sai kuma ta tsinci kanta da ƙara sakin kukan wanda dukansu suka rungumeta suna taya ta.
Bayan fitarsu ya miƙe tsawonsa a kan gadon yana dana-sanin biyewa zuciyarsa, na ba shi shawarar ya fara mata magana, domin ga shi yanzu ya afka kogin nadama.
Miƙewa ya yi ya ɗauko wayar duk da gargaɗin da zuciyarsa take masa amma ba shi da zaɓin da ya wuce ya yi mata maganar.
Tun da suka shigo suka gama kukan, sai ba su fita ba suna ta hira da ƙoƙarin ɗauke mata damuwa.
Kiran sallar magariba ce ta fitar da su wanda Huwais ya ja su a Masallacin gidan su.
Ko da suka dawo ɗakinta suka koma, ba su bar ta ba har sai da Ummu ta kora kowa ya je ya kwanta.
Bayan sun fita ta yi shirin kwanciya, ta janyo wayarta tare da jero addu'in da ta saba zubawa kan ya kirata.
Buɗe datar da fara shigowar tsaƙon sai na sa ya shi go kamar haka:
"Barka da Juma'a kyakyawa mai farar aniya. Ina mai baki haƙuri bisa ƙin kiran da na yi, wanda na yi ne don ki fahimci soyayyar gaskiya kike mini ko ta ƙarya."
Babu jan aji kamar ba ita mai daraja da kima ba. Ta tura masa stiskers na kuka sau ba adadi. Sai kuma ta ƙara da rubuta
"Eh na faɗa soyayarka saboda iya kalamanka da adinin ka , don Allah kar ka ƙara guje mini."
Tun daga wannan lokacin suka manne da juna a waya. Hilah da ba ma'abociyar waya ba, amma a yanzu datarta a kunne take barin shi, saboda dakon jiran tsaƙon mahaukacin masoyi.
Wani lokacin sai dai ta danna waya tana murmushi. Gabakiɗaya ya sanya ta canza ɗabi'unta. Don Allah ya yi ta da kwanya da ta samu matsala a karatunta da haddarta.
Tsananin mamaki wani lokacin take yi, tare da ganin wautarta na faɗawa son mutumin da ba ta taɓa ko jin muryarsa ba. Ballantana haɗuwa na zahiri, amma tana jin a ranta ta kamu da ƙaunarsa damu-dumu.
A da duk maganar da suka yi sai ta gaya wa masa, amma da ta ga yana mata faɗa ta daina biye masa haka, sai ta daina sanar masa da komi, wanda hakan ya yi matuƙar ɗaure masa kai.
Ganin ƙaramar magana na nema zama babba sai ya yi tunanin dainawa, saboda ranar yasha mamakin kukan da ta sanya masa, tare da yi masa magiyar ya tura mata hotonsa ko ya kirata ta ji muryarsa.
Da sauri ya kashe gabakiɗaya tare da jifa da wayar yana gumi.
Safa da marwa ya shiga yi a cikin ɗakinsa. Lokaci guda ya birkice saboda ya yarda cewar ta kamu da sonshi.
"In har ta buƙaci mu haɗu ya zan yi?" Ya yi ma kansa tambayar cikin tsananin tashin hankali tare da kaiwa bango naushi har sai da ya ji zafi a hannunsa.
Saboda tsananin zafin da yake ji rage kayan jikinshi ya yi. Ya rage da ga shi sai singileti da gajeren wando.
A ransa ya yi ninyar daina kiranta gabakiɗaya a yau, amma kuma ya san da kamar wuya,gurguwa da auren nesa. Don yadda soyayyarta ta yi masa kamun kazar kuku, ba ya tunanin akwai a bin da zai iya dakatar da shi soyayyarta.
"Ta ya ya zan bayyana kaina a gareta, shin in har ta san nine mai zai faru? Na san babu aure a tsakaninmu, amma to ya zan yi da soyayyarta da yake ƙara ninkuwa a cikin zuciyata? Kuma wane mataki iyayena za su ɗauka?"
Irin tarin tambayoyin da suka cunkushe ƙwaƙwalwarsa kenan, wanda ke aiki bisa rashin ƙa'ida. Sai dai, kuma a ra sanya ya ɗauki ninyar duk wuya duk rintsi ko ana ha maza ha mata! Ba zai taɓa barin ta kuɓuce masa ba. Ko da Ummu za ta yi gunduwa-gunduwa da naman jikinsa ne. Kuma duk wani ɗa namiji da zai yi gigin kula ta shi e ajalinsa.
Ga mamakinsa sai ya tsinci kansa da fashewa da kuka. Yayin da zuciyarsa ke harbawa tamkar za ta fito waje. Ya san cewa kukan nan zai ta yi har ƙarshen rayuwarsa matuƙar bai mallaketa.
Hilah kuwa ganin ya sauka ta shiga cikin matsananin tashin hankali har sai da ta ji zafafen hawaye sun gangaro mata.
Da sauri ta fara tura masa da tsaƙo, amma ganin ya sauka gabakiɗaya ya sanya ta fasa tare da riƙe wayar tana ji kamar ta kwaɗa wayar da ƙasa.
Jikinta a sanyaye tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki, ta fara gwada kiran numbar duk da ta san cewa ba ɗauka zai yi ba.
Ganin wayar ta ƙi shiga, ya sanya ta kashe wayar tare da jifa da ita kan kujera. Hannu ta sanya ta tallabe kanta da take jin yana sara mata tamkar zai rabu gida biyu.
"Ina jin son mahaukacin masoyi shi zai xamo ajalina." Ta furta cikin tsananin damuwa tare da kwaranyowar zafafen hawaye daga kwarmin idanunta.
Zubbur ta miƙe tare da leƙawa falo ta duba ko Ummu na nan. Ganin babu kowa sai tangamemen tibin bangon da ke barazanar mamaye bangon falon, ya sanya ta ruga da sauri ta nufi sashinsa.
Da sauri ta fara ƙwanƙwasawa a hankali tamkar wata mara gaskiya. Knoking ɗaya ya gane wacce take buga ƙofar.
Hannu ya sanya tare da share hawayen da suke zubo masa ya miƙe. Har zai buɗe ƙofar sai ya kasa ganin kansa a madubi da ya yi. Idanunsa sun nuna alamun ya yi kuka.
"Yaya ka buɗe ni ce." Ta yi maganar tamkar wata mai raɗa.
"Ki je zan shigo."Iya abin da ya furta kenan tare da komawa cikin ɗakinsa.
Mamakin kalar muryar da ya yi magana ya kamata, har ta fara tunanin ko ya fara shaye-shaye ne.
Juyawa ta yi cikin takaici ta koma ɗakinta ta kwanta. Filo ta ɗauko tare da rungume shi a ƙirjinta tana ganin wauta da wawancin da ta yi har ta fara son shi.
Washegari da safe bayan ta haɗa break ta karya ta wuce school.
Suna zaune sun gama lectured suna jiran lokaci ya yi, don za su yi sha ɗaya zuwa ƙarfe ɗaya.
Ta kalleta wacce ta ke riƙe da drink na exotic tana sha.
"Lafiya Hilah?" Ta yi mata tambayar tare da dafata ganin yadda ta shiga kogin tunani.
Firgigit ta yi kamar wata mai bacci ta yi tana kallonta. Sai kuma hawaye shar! Suka fara zuba a ƙuncinta.
"Ya zan yi? Son mahaukacin masoyi yana neman ya yi ajalina."
Zaro idanunta ta yi cikin mamaki jin abin da ta faɗa.
Miƙewa ta yi cikin damuwa tare da kallonta sai kuma ta zauna ta kama hannunta.
"Kamar na san mai zai je ya dawo Hilah! Wannan dalilin ya sanya na ƙi aminta da shawarar ya da baki."
"Ki fahimce ni sam bai yi da wata manufa ba, domin ya yi ne don mu gano wane n..."
"To yanzu wa gari ya waya? Kuma mai hakan ya jawo? Kin faɗa son mutumin da ba ki sam wane ne ba. Musaki ne ko mummuna duk ba ki sani ba."
"Ko ya ya yake ina son shi. Ji nake kamar zuciyata za ta kasa daurewa, akan shi zan yi fito na fito da iyayena su nemo mini mahaukacin masoyi."
"Innalillahi! Hilah, kin san abin da kike faɗi kuwa? Bijirewa iyayenki za ki yi kan wani banza wanda ba ki san waye shi..."
"Kar ki ƙara zagin mini masoyi domin zan iya ɗaukar mummunar mataki a kanki duk da alaƙar dake tsakaninmu."
Tsananin mamaki ya kamata matuƙa gamin ta ɗaga hannu xa ta mareta.
Saukar da hannun ta yi daidai lokacin da ta riƙe kumatunta tana faɗin,"Marina za ki yi?"
"Zan iya miki abin da ya fi haka. Wataƙila ba ki san yadda nake son shi bane. Gab nake da na yi fito na fito da kowa."
"Hmmmm!' Ta furta cikin tsananin mamaki tare da jan ajiyar zuciya mai ƙarfi.
"In har za ki iya ɓatawa da kowa sai na ce kin ɗauko wa kanki dala babu gammo. Sanin kanki wace ce Ummu da kuma irin zafin da take da shi. Tana gani ba za ta yarda ki ƙi auren Hamad ba, saboda wani da ba ta san shi, kuma bayan hakan ba ki yi wa Hamad adalci ba, domin masoyi ne shi na haƙiƙa."
"Allah ya sanya duniya da sama zan ɗauka. Sannan duk abin da zai faru a shirye nake."
Lamarin sai ya yi matuƙar ba ta mamaki da ɗaure mata kai. Ta san wace ce Hilah, domin tana da haƙuri da matuƙar biyayya ga iyayenta. Za ta iya cewa wannan shi ne karo na farko da saɓani ya shiga tsakaninsu.
Da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 17