Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daina ƙoƙarin zuba masa, jin abin da ya ce ta fara zuba masa. Miƙa masa ta yi sai kuma ta fasa ba shi."Bari na kai maka dinning." Ba tare da ya ce komai ba ya bi bayanta. "Thanks," Ya furta yana kallonta da ta miƙa masa ta tsaya a gabansa tana kallonsa. Bayan Sauwama fa gama haɗa wa ƴarta custard ɗin, sai ta ɗauki kofin ta yi cikin ɗakin Ummu wanda anan suka kwana. Ummu na zaune da carbi a hannunta, tana wa Allah godiya da ya nuna mata auren ta samu guri ta zauna. Lamarin Huwais sai a hankali." Ta ce tana dariya wanda ya sanya ta juyo da sauri yayin da gabanta ya faɗi. "Wai shi da yake da amarya, amma har ya baro ta yazo gidan nan yana ihun yunwa." Gabanta ne ya ƙara faɗi, wanda ya sa ta miƙe cikin ɓacin rai, tana jin kamar ta kifa masa mari. "Huwais ɗin ya baro gidan matarsa yana nan?" "Ki je yana falo yana cin abinci kika sheda, don har mun haɗa abin lari za mu je a kai mas..." Ba tare da ta ƙarasa jin abin da take faɗi ba ta wuce falo da sauri. Turus ta tsaya cikin tsananin ɓacin rai, tana kallonsa da ya kashe Hilah da ke xaune gabansa tana murmushi. Tsananin ɓacin rai ya ƙara kamata. Ji ta yi kamar ta rufe su da duka. "Huwais," Ta kira sunasa da ƙarfi tana huci. Gabansa ne ya faɗi, amma sai bai ce komai ba ya amsa yana kallonta. "Mai ya kawo ka cikin gidan nan da sassafe bayan matarka na gida?" "Ummu, kewarku na yi kuma yunwa na ke ji." "Huwais, zan yi maka rashin mutunci matuƙar ka ce za ka wulaƙanta ƴar yayata." Ta furta cikin tsananin ɓacin rai wanda ya sanya Hilah ta yi maza ta shige kicin. "Ummu, laifi ne don na zo gidan nan?" "Lai fi ne babba, domin yanzu kai magidancinne kuma matarka na buƙatar lokacinka." Shiru kawai ya yi, cikin takaici domin ya san dalilin da ya sa take faɗa. Ummu ta buɗe baki za ta yi magana, sai kuma ta fasa ta koma ta ɗauki wayarta da take kan gado. Numbar Wajnah ta fara kira. Ringing ɗaya biyu ta ɗauka dama tana kwance a saman gado tana hawaye. "Sakacin na ki har ya kai, ki bari mijinki ya yi sammakon barin gida a washegarin aurenku? Ka da wayewa ta sanya ki kasa kula da mijinki, saboda ga shi ya zo gida yana cin abinci wai yunwa yake ji." Takaici ya sanya ta rushe da kuka."Ummu, Ya Huwais ya toxarta ni jiya, saboda in kika ga yadda na ke buga ƙofarsa ina kuka ya buɗe mini, amma ya ƙi bayan ya yi mini zagin ƙare dangi ya sanar mini da wacce yake so a zuciyarsa." Maganarta suka ƙara ninka tashin hankalinta har ta fara ganin jiri-jiri. "Anya yaron nan na da hankali?" Ta yi wa kanta tambayar sai kuma ta kashe wayar fuuu!Ta yi sama tana huci. "Abu, yaron nan na lura ba zai taɓa nari na na samu sukuni a zuciyata ba. Ina murna na auren da shi hankalina xai kwanta, amma ga shi can a falo yana karyawa Hilah na gefensa." Wani gumi ya tsatso masa kallonta ya yi da sauri tamkar yana son sanin ko ƙarya ta yi masa. Gabansa ne ya faɗi da ƙarfi, saɓanin da tun da Ummu take zafafa lamarin sai yake ganin duk da sauƙi matuƙar aka yi masa aure, don shi a ganinsa sha'awace kawai take damunsa ya ɗora kan ƙanwarsa, amma yanzu da yake da matar da zai sauke buƙatunsa sai hankalinsa ya tashi kwatankwacin kayan masarufi. "Nufinki yanxu yana gidan nan?" "Ka je ka ganin ma idannunka, wallahi in har ba mu yi wa Hilah aure ba, sai ya janyo mana abin da xai wargaza farincikinmu." Miƙewa ya yi, ba tare da ya ce mata komai ba, ya zura jallabiyarsa fara ƙal, ya fita wanda ganin haka ta bishi. Huwais ganin ta yi hanyar ɗakinta gabansa ya faɗi. Shi kansa mamakin ƙarfin halinsa yake yi, domin duk abin da yake aikawatawa yana jin tsoron iyayen na sa. Gyaran muryar da Abu ya yi, ya sanya shi tashi da sauri gabansa na faɗi ya ce,"Ina kwana Abu?" "Kana da hankali Huwais? Kan me za ka baro ƴar mutane da sassafen nan ka zo gida?" "Umm..." "Bana son sakarci." Ya katse shi yana faɗin haka sannan ya ɗora da ce wa,"Ma za ka tashi ka tafi gida." Miƙewa ya yi ba don ransa ya so ba zai fice. "Da kun barshi ya karya, sai in ya so idan ya gama ya kaimu ni da Hilah da ma za ku kai abinci." "Sai dai ke da su Umnah, amma Hilah za ta yi mini aiki." "Ai ba daɗewa za mu yi ba ki barta ta je, saboda tun da muka tashi take murna za ta je ganin gidan Yayanta." Ummu ta buɗe baki xa ta yi magana Abu ya ce,"Ki barta ta je amma kar ku daɗe." "Ba zan daɗe ba saboda yau na ke son na koma Gobbe." "Ok, Allah ya kaiki lafiya." Abu ya furta wanda ta amsa da amin sannan ya juya zuwa ciki. Harararsa Ummu ta yi sai ta juya ta bi Abu. Sauwama Hilah ta ƙwala wa kira, tare da sanar da ita ta ɗauko mayafinta. Cikin murna ta juya ta shige ciki. Yana jin da Hilah za su je abincin ya fita a ransa. Ture abincin ya yi tare da faɗin,"Anty Sauwama mu je." "A,a ka gama cin abincin mana." "Karki damu na ƙoshi." Bin sa da kallon mamaki ta yi ganin bai ci abincin da yawa ba. Azerh da ta ke saukowa daga sama, tana hamnar sauran baccin da bai saketa ba, ta ƙara so da sauri. "Ni ma Anty Sauwama zan biku, amma sai yamma zan dawo." Ta furta daidai lokacin da ta ƙara so. "Ok, yi sauri ki ɗauko mayafinki sai ki same mu a mota." "To," Ta amsa tare da komawa sama da sauri. Hannu ya sanya ya karbi yarta, sai da suka je gurin mota ya miƙa mata bayan ta buɗe motar ta shiga. Lakuce mata hanci ya yi, yana dariya ganin yadda take wangale masa bakin da babu haƙora. Kafin ya tada motar, Hilah ta karɓe ta tana ta yi mata wasa tana dariya. A mota Anty Sauwama ce a gaba, sai ita da su Umnah suna baya. Tana riƙe da ƴar Sauwama tana mata wasa. Sai satan kallonta yake yi ganin yadda take ɗaga yarinyar sama tana dariya. Zuciyarsa ta raya masa ina ma ace ƴarsa ce. Yana ta satan kallonta ta madubi, in aka yi rashin sa'a suka haɗa idanu sai ta sakin masa murmushi, shi kuma ya ɗaure fuska yana harararta cikin wasa. Suna isa cikin gidan, ya yi parking tare da buɗe wa Sauwama murfin mota. "Yauwa ɗana ashe kana son albarka." Ta faɗa tana fariya. Harararta ya yi domin kusan sa'oin juna ne, kuma a hannun Ummu ta tashi. "Kuma fa haka ne bai kamata na rinƙa girmama ki ba, saboda na san lokacin da kike yawo ba wando." Wani irin dundu ta sakin masa a baya har sai da ya duƙa. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 21 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Kuma fa haka ne, bai kamata na rinƙa girmama ki, ba saboda na san lokacin da kike yawo ba wando." Wani irin dundu ta sakin masa a baya, har sai da ya duƙa. "Kai Anty Sauwama, wallahi tsaf zan iya rama dundun nan, saboda ba ki ji yadda na ji zafi ba." "Ashe kuwa zan ƙara maka wani, ka san dai ko lokacin da muke yara kuka nake saka ka." "Ni kuma na saki birgima ba." Dariya suka kwashe dashi suna tuna yarintarsu. Wajnah da take laɓe a windo tana kallonsa, suna wasa sai matuƙar baƙinciki ya kamata. A ranta take mamakin dariyar da yake yi. Ganin Hilah ranta ya ɓace sosai, domin har ga Allah ta tsane ta, musamman jiya da ya sanya ta ba da tarihin rayuwarsa. Sakin labulen ta yi, ta xauna a kan kujera tana gyara xaman guntun hijabinta. Da sallama suka tura ƙofar suka shigo. Turus Sauwama ta yi tana ƙare mata kallo. "Lafiya kike Wajnah? Kin ga yadda kika dawo kamar wacce ta yi ciwon shekara?" Kuka ta fashe da shi, tare da faɗawa kan jikinta. Shi kuwa tsaki ya yi, zai wuce ciki sai ya fasa yana kallon Hilah da take kallon Wajnah. "Anty Ya Huwais ba ya ƙaunata! Duk yadda na so na faranta masa, amma kulle ɗakinsa ya yi ya bar ni na kwana a falo." "Falo?" Ta faɗa da ƙarfi tana kallonsa da ya yi halin ko in kula da su yana kunna tibi. "Kai Huwais, kana da sukuni kuwa? Amarya sukutun da guda xa ka bari ta kwana a falo?" Ɗago idanunsa ya yi, ya kalle su sai kuma ya mayar gurin Hilah, da ta yi jugum tana kallon ƙasa. "Fitina ta sanya wa ranta ai na gaya mata bana son..." "Kul kar na ƙara ji ka faɗi haka musamman a gaban ƙanninka. Ke Wajnah mu shiga bangarensa." Ta ce wanda babu musu ta riga su murɗa ƙofar. Harara ya bita da shi sannan ya miƙe. Zama ya yi a kusa da Sauwama, yana sauraren Wajnah da take gaya mata ƙarya da gaskiya. "Ya gaya mini ya tsane ni ba ya ƙaunata, yana da wacce yake so. Jiya Anty na yi burin da ma mutuwa na yi, kan baƙar rana da na gani." "Kar ki ƙara faɗin haka, kuma ki kasance mai biyayya da haƙuri za ki ci ribar hakan. Kai kuma Huwais abin da ka yi sam ba ka kyauta ba.." "Laifin me na yi? Gaya mata na yi bana buƙatarta a rayuwata, kamar yadda tuntini na sanar mata, amma ta yi kunnen uwar shegum Ta shafa ma idanunta toka a dole sai ta aure ni." "Mene ne laifina don na ce ina sonka? Ko ba ka soni don soyayya ba, ai ka soni saboda dangantakar da ke tsakaninmu. Ni na sam wannan tsinannanniyar da kake so ne take sanyawa kana mini wulaƙanci, kuma wallahi idona idanunta sai na yi ajalinta in ya so ka kashe ni nima, don matuƙar ina raye babu kai ba wata ƴa mace..." "Anty kina jin abin da take cewa ko? In har za ta rinƙa zagin xaɓin raina, wallahi watarana sai dai ku zo ku ɗauki gawarta." "Eh ka kashe ni zan fi buƙatar hakan da na yadda wata ta ƙwace mini kai. Na san wacce kake so ba wata bace face kilayar karuwa, saboda in ta gari ce ai ya kamata ka nuna ta." Miƙewa ya yi cikin zafi zai ɗaura mata mari, wanda ganin hakan ya sanya Sauwama shiga tsakiyarsu. "Kuna da hankali kuwa? A washegarin aurenku kuke wannan sa'insar? Kai Huwais, biye mata za ka rinƙa yi kuna cece kuce a gidanku?" "Amma ki na jin abin da take cewa ko? Ba marinta ya kamata na yi ba farfasa mata jiki zan yi, don wallahi matuƙar ta ƙara xagin abar ƙaunata sai na zama ajalinta." "Ka kashe ni ai ba kanka farau ba namiji ya kashe matarsa, amma ba zan fasa zaginta ba." "Wawiya mara tunani! In har da zan kawo miki zaɓina wallahi sai kin raina kanki, domin ita ɗin mai tarbiya ce, na san duk abin da na yi mata ba za ta yi sa'insa da ni ba, saboda ta fiki hankali da natsuwa." "To ka nuna ta mana in har mutuniyar kirmi ce." "Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Ni kam na yi matuƙar dana sanin zuwa gidanku, domin da na san abin da zan tarar gara na tafi ban zo." Ta furta tare da fashewa da kuka. "Ki yi haƙuri raina ne ya ɓace." Ya ce tare da zama kusa da ita yana huci. Wajnah ita ma zama ta yi tana harararsa ta gefen ido. Matuƙar haushinsa take ji, saboda da ace ya yarda ya kwana da ita da yanzu yana nan yana rawar jiki a kanta, amma saboda wulaƙanci ya toxartata a ranar daren amarcinsu. Ga shi ko da ta faɗa a group, cewa ta fara al'ada sun ƙi yadda haka kawai ya zubar mata da mutunci. "Ke Wajnah fita ina gama magana da shi xan kira ki." Ta faɗa mata haka domin ta lura ta tara su babu abin da zai ƙara sai rigima. "Kai Huwais, irin tsarin da xa ka ɗauka a zaman gidanka kenan?" "To ya kike so na yi Anty Sauwama? Kin san sam bana son raini. Tun daren jiya mara kunyar yarinyar nan take ta gaya mini maganganu marasa daɗi, kuma wallahi ba zan ɗauka ba don ƙasa-ƙasa zan yi da ita." "Ai ko ina ba ka shawara ka canza, in ba haka ba maƙota za su jiyo ku kuma sa'insa.". "Jikinta ne zai gaya mata sam ba zan ɗauki raini ba." "Amma ka san ba daidai bane ka ƙi kwana da ita ko? saboda Allah ya ɗora maka haƙƙi a kanta dole ka sauke." "Ni fa bana sonta ina da wacce nake so. Ba zan iya ɓoye miki komai ba, ba zan iya haɗa jiki da ita ba, kuma bayan haka na tsani mata masu shan kayen mata, saboda jiya abin da tasha kenan ta wahalar da kanta ta koma kamar mahaukaciya." Kasancewar babu kunya a tsakaninsu ya sanya ta kalle shi ta ce. Tun da muka mallaki hankalin kanmu kake gaya mini kana sonta, amma kaƙi sanar dani wace ce. Huwais a tunanina babu abin da xa ka iya ɓoye mini." "Ba zan iya gaya miki ita ba." "Don haka babu amfani wulaƙanta matarka kan wacce na za ka iya bayyana ta ba, in kuma aljana ta aureka sai na sanar wa Ummu ta yi maka ruƙiya." Dariya ya saki tare da kai mata duka yana faɗin,"Eh ina ga hakan ki sanar mata, amma har da wannan ƙyamushshshen mijinki xa a haɗa ayi mana ruƙiya." "Ba na son iskanci Huwais ni fa a matsayin mahaifiyarka na ke kake dukana." "Kin manta sanda na ke zane ki a makaranta kenan? Ai ƙaramar uwa abokiyar wasa." Dukan ta rama, sai kuma ta kalle shi tare da mai da hankalinta gare shi. "Don Allah ka canxa tsarin gidanka ku, xauna lafiya karka barinta raina ka." "Hmmmmh!" Ya ce tare da miƙewa ganin ta miƙe. "Bari na je na yi mata magana." "To," Ya ce sai ya miƙe, ya biyo bayanta don ya yi kiran su Hilah su shigo sashinsa. Hilah wacce tun da ta shigo suka fara sa'insa ta tsure da lamarin Wajnah. Mamakin ƙarfin halinta take gani na rashin kunyar da take yi masa. Ta san cewa yana wasa da ita, kuma duk ya fi sakin mata, amma ba ta taɓa ko da gigin masa rashin kunya ba, domin ba halinta bane, kuma shi ma ba ya ba da fuskar da za a raina sa. Tana cikin wannan tunanin, Wajnah ta buɗe ƙofar ta fito cikin ɓacin rai tana share hawaye ta yi ɗakinta. Sororo ta yi tana tunanin irin zaman doyan da za su yi, domin matuƙar ta ce raina shi za ta yi, ba za ta ji daɗi a gurinsa ba. Anty Sauwama ta tura ƙofar ta fito yana biye da ita. Bangaren Wajnah ta yi sh,i kuma ya kama hannun Umnah da Amnah yana faɗin, "Ku zo muje sashina." Miƙewa suka yi zuwa ciki. "Wow! Gaskiya gidanka ya yi matuƙar kyau Yaya." Hilah ta ce tana zama a gefensa. Azerh tana kallon falon admiringly. "Allah ko?" Ya yi mata tambayar idanunsa cikin nata. Yes Ya Huwais the house is fine." Hilah ta bashi amsa tana zama a gefen kujerar da yake. "How about mace mai irin ki tsafta da iya decorating ɗin gida take a ciki. Na san the house would be finer than this?" "Anty Wajnah ma za ta yi koƙarinta. Yar gayu ce itama." Taɓe bakinsa ya yi, yana shafa kansa tare da kallonta har ta zauna. "Hilah, akwai maganar da na ke son mu yi kan maganar mahaukacin masoyinki, amma ba anan ba ya kamata na zo makarantarku." Jikinta ya kama ɓari jin abin da ya ce." Kallon Azerh ta yi wacce sam hankalinta ba ya kansu. "Yaya..." "Ba yanzu za mu yi maganar ba. In kin samu lokaci ki kira ni." "To," Ta ce amma ba don haka taso ba. "Please Yaya tsakaninka da Anty Wajnah..." "Ke yarinya ce ba ki san komai ba don haka kar ki interfering." Kama bakinta ta yi, ba ta ƙara cewa komai ba kan lamarin, suka ci gaba da hira, amma hankalinta na can tana tunanin abin da xai gaya mata. Anty Sauwama kuwa, ɗakin Wajnah ta tura ta sameta ta yi wanka tana shafa mai. "Ashe ba ki da hankali? A haka za ki gina rayuwar auren na ki, kuna sa insa? Wallahi matuƙar ba ki canza ba zai iya illata ki, kin san shi da baƙin xuciya. Kin kwana da sanin baya sonki dole aka yi masa, amma kike gaya masa magana son ranki." "Anty to ya kike son na yi? Inda kin ga rashin mutuncin da ya yi mini, sai kin tausaya mini. Ƙiri-ƙiri ya barni cikin mawuyacin hali jiya." "Eh, ai gara ma da ya yi miki haka, saboda ki daina biyewa waɗannan sheɗanin ƙawayen na kina ɗirka wa kanki maganin matan da xai cutar dake. Kina sane da shan maganin da yawa babu alfanu kuma daga ƙarshe xaki yi nadama mara amfani. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 22 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM "Anty to ya kike son na yi? Inda kin ga rashin mutuncin da ya yi mini, sai kin tausaya mini. Ƙiri-ƙiri ya barni cikin mawuyaci hali jiya." "Eh, ai gara ma da ya yi miki haka, saboda ki daina biyewa waɗannan sheɗanin ƙawayen na kina ɗirka wa kanki maganin matan da xai cutar dake, saboda shan shi da yawa babu alfanu, kuma daga ƙarshe xaki yi nadama. Ina Gobbe aka kira ni, aka sanar da ni cewar tun da aka sanya ranar kike bankan maganin bature. Kin kuwa san illar da kike yi wa kanki? In maganin matan za ki sha, ga ba ƴaƴan itatuwa nan ba da kuma na gargajiya wanda baya cutarwa." Tura bakinta ta yi, ta ci gaba da kwalliya tana faɗin,"Ni na san Anty Hibba za ta gaya miki munafuka kawai." Duka ta kai mata tana faɗin,"Don ubanki ƴaƴar ki kike zagi? Ai ita tafi ki hankali, ko da yake laifin Anty Fati ne, da ta barki kike abin da kika ga dama." "Yanzu laifina duka za ki gani Anty?" "Eh mana tun da kin zubar da mutuncin kanki kike roƙonsa ya taimaka miki." "Ni ban ga abin kunya ba domin mijina ne." "Shikenan, ki ci gaba da zubar ma kanki da mutunci." Ƙara tura bakinta ta ƙara yi, ta ba ce komai ba ta ci gaba da kwalliayrta. "In ɗauki shawarar da na ba ki, sai ki canza taku ta hanyar yi masa biyayya, in kuma ƙin ƙi sai ki xauna fitsara da rashin kunya ya ƙwatar miki darajar ki. Miji dai yana da babban matsayi da kima a gurin matarsa, kuma dole sai ta ƙarƙashin ƙafarsa za ki samu ya ɗaga ki shiga aljanna. A yanzu da aure ya zama a lallaɓa auren zamani, waɗanda suka yi auren soyayya ya suka ƙare? Ballantana ke da kin san yadda aka yi aure. In zawarci kike son yi Allah ya taimaka, kin san dai namiji na da dama sosai a rayuwarsa. In yau ya rabu dake xai iya auran mata huɗu duka ƴan mata. Don haka in kunni ya ji, gangar jiki ya tsira. Miƙewa ta yi yayin da jikinta ya yi sanyi jin abin da ta ce. Sashinsa suka shiga, inda suka same Hilah da su Azerh suna ta kallon hotunan biki. Shi kuma hankalinsa na kan wayarsa, yana duba chatts ɗin da suka yi a matsayin mahaukacin masoyi, yana murmushi sai kuma ya ɗago ya kalleta ya girgiza kansa. "To ni zan wuce, don Allah ku rinƙa haƙuri kar ku ɓata zumunci." Ta ce tana kallonsu duka. "In sha Allahu Anty Sauwama, Allah ya kiyaye hanya." Ta ce mata cikin sakin fuska kamar babu abin da ya faru. "Hilah ku tashi muje." "Ki barsu mana na kai ki, zuwa anjima sai su koma." "Ƙafata kafarsu tun da ka ga Ummu ba ta so zuwan ba." "Ni ma zan biku." Cewar Wajnah tana kallonsa da tun da ta shigo bai kalle ta ba. "To ka ji Huwais ta raka ka sai ku dawo tare?" "Ina da inda za ni." Ya faɗa fuska a ɗaure tare da hanyar waje. "Ki yi haƙuri da kanshi zai kaiki kin ga duka jiya aka kawo ki, kuma mutane ma ba su gama watsewa ba, sannan ki xama mai biyyaya kin ji?" "To,"Ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa ta bisu zuwa waje. Abu da ya koma ɗakinsa wayarsa ya ɗauka ya yi kiran Ummu. Shi kansa lamarin ya rikirkita shi tare da tabbatar da zargin Ummu, wanda yake ƙoƙarin ƙawar da zargin da yake yi. Ummu ce ta shigo fuskarta a ɗaure ta zauna a gefensa. "Ni kaina na fara tunanin abin da kike zargi." "Tun tuntuni na ke gaya maka a ɗauki mataki tun kafin ruwa ya ƙarewa ɗankada." "Amma yaron nan ba shinda hankali. Wane hauka zai sa ya rinƙa kallon ƴar'uwarsa da kallon soyayya. Tuntuni na ke ganiin haka daga gare shi, amma sai na watsar da batun." "Wataƙila dalilinsa na ban shayar da Hilah ba..." "Kan me zai ɗauki wannan a matsayin hujja har ya fara sonta? Yana gani ko Umnah ciwon mama bai bari an shayar da ita ba. A gaban idanunsa aka yi cikinta kuma aka haife ta. Yaron nan ba shi da hankali. Tun kafin ya ja mana abin kunya, ayi mata aure kawai xan sanar da Hamad ya turo ayi auren in ya so ya kama mata haya in ta gama karatun su koma Kaduna." "Hakan shi ya fi. Tuntini na ke gaya maka ka ɗauki

Chapter 15 of 17