Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 1 FILIN SAUKAR JIRAGE NA ABUJA. BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Yanayin iskar dake busowa, suka haɗu da yanayin farincikin da take ciki, suka saukar da matsanacin farinciki mara misaltuwa a gareta. Rintse idanunta ta yi tana shaƙar daddaɗar iskan da ke busowa wace ke saukar da ni'ima mai daɗi da kashe jiki. Kyakyawar matashiyar wacce ba zata wuce shekaru sha tara a duniya ba. Ta miƙe da sauri tana duba agogon hannunta cikin yanayi na ƙosawa. "He has to arrived by this time, ban san dalilin da ya sanya jirgin bai ƙaraso ba, kamar yadda aka faɗi ba." Raurau ta yi da idanunta tana, kallon kyawawan fararen yaran da suke gefen ta fuskarsu ɗauke da damuwar rashin saukar ɗan'uwan na su da wuri. "Haba, kun cika ƙosawa! Ummu, cewa ta yi zai sauka sha ɗaya kuma yanzu sha ɗaya saura minti minti biyar. Oh are you blind, ko duk ƙosawar da kuka yi ku ganshi ya sa kuka kasa bambance lokaci?" Cewar Fu'ad cikin fushin wasa yana kallon su. "Ƙyale su Ya Abidin yarannan, na lura duk sun fi son Ya Huwais, ka na ganin Anty Hilah, ku san a weeks nake ta roƙonta ta yi mini wainar indomie, amma ta ƙi sai ga shi tun jiya bata zauna ba tana wa Ya Huwais girki." Ya ce cikin ɓacin rai abin da ta yi mishi. Dukan wasa ta kai masa tana dariya daidai lokacin da Abidin ya ce, "Ai bambanci suke nunawa kamar yadda shi kansa yake nun bambanci ya fi sonta." Kama bakinta ta yi cikin mamaki tana faɗin,"Kar dai kuce you guys are really jealous about how I do care about him?" "Absolutely we are." Su ukun suka haɗa baki gurin faɗin haka Anty Hilah, har yanzu jirgin su Ya Huwais bai ƙaraso." Ƙaramar yarinyar da ke kwance tana bacci, da tafarki, furta hakan wacce ba za ta wuce shekaru goma ba ta faɗi tana kallonta. "I really don't know what happen, kuma Ummu ta gaya mini saura lokacin saukar har ya wuce." Ta ce ba tare da ta damu da ƙorafin da suke musu na sun ƙosa ba. "Allah ya sa ba wata matsala bane ya sa bai ƙaraso ba, cus na zaƙu na ga Ya Huwais, it been two years kenan yana abroad." "And so do I." Ta ce wa Umnah tana kallonta." A hankali jirgin yake saukowa har ya sauka ƙasa mutane suka fara sakkowa daga sama. Huwais dake sauka daga matakalar benen, cikin ƙasaita da isa yayin da idanunsa na kan mutanen da suka zo ɗaukar 'yan uwansu. Shekaru biyu ya yi hijira saboda ita kuma, amma a tsawon shekarun babu wacce yake son gani sai ita, domin cike yake da son ganinta da begenta. Idanuwansa ya rintse, yana jin wani abu na tasowa tun daga ƙafafunsa, har tsakiyar ƙwaƙwalwarsa wanda ya sa shi ajiyar zuciya mai ƙarfi, bayan ya aminta da waɗannan abubuwa da yake ji game da ita, ba za su taɓa dainawa sai dai in ya mutu. "Anty Hilaah, Ya Huwais."Amnah ta furta tana nuna shi da ɗan yatsa wanda ya sanya suka kwasa da gudu har da ita. Gabakiɗaya sika faɗa jikin shi har da ita suna ihun murna. "You are welcome Ya Huwais, we really miss you." Suka faɗi a tare da ƙara rungume shi. Wani irin abu mai kama da shokin suka fara tartsatsi a kansa, suna jansa wanda ta sanya ya janye ta daga jikin shi da sauri, yana kallonta yana jin yadda bugun zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi tamkar za ta fito waje. "Ya kamata ki san kin girma Hilaah, dubi yadda kika ƙara girma, amma har yanzu ba ki daina yi mini oyoyo kamar su Umnah." Ya faɗa yana murmushi tare da lakuce mata hanci. Idanunta da suke dara-dara ta zuba masa a cikin nasa wanda ya sa shi kusan mutuwar tsaye. "Tun ranar da ka ce mini you would be back to Nigeria na shiga cikin murna da ɗoki, and now ka dawo Ya Huwais is that what za ka saka mini da shi. All I do is caring, kar fa ka manta kai ɗan'uwana ne wanda muka fito ciki ɗaya, Ya in ban rungume ka don farinciki ba what do you want me to do." Ta ƙarashe maganar cikin sigar tambaya tare da hawaye a fuskarta. "To don Allah mene ne na kuka, da za ki yi mana asarar hawayenki?" Ya ce yana kallon su Abidin. "That is how Anty Hilah, is always crying ita fa ko abin murna ne kuka ne. Ranar da Abu, ya canza mata mota sai ta kama kuka." Kwashewa da dariya suka yi suna kallonta tare da faɗin,"Me bakin kuka." Wanda ya sanya ta yi fushi ta kalle su tare da kaɗa key ɗin motarta ta juya zuwa gurin motarta, wanda ganin haka ya sanya suka rugo da gudu su shidda ɗin suna faɗin, "Sorry Anty Hilah," Har da su Abidin da Fu'ad don su sanyata dariya. Rungumar ta kai masa a maimakon ta yi musu dariya."Farincikina ba zai iya ɓoyuwa ba akan dawowarka Ya Huwais." Ta ce tare da ƙanƙame shi wanda ya sanya ya ji tamkar zai fita daga hankalin shi, domin ji ya yi jikinsa ko ina ya ɗauki rawa. Wasu hawaye suka gangaro zuwa fuskarsa wanda ya yi sauri ya goge don kar su gani, yana ji a cikin zuciyarsa ƙaddararsa ta yi masa girma. Girman da yake jin tamkar girmar duniya akansa, domin bai san yadda zai kalli duniya ya bayyana musu ya kamu da son ƙanwarsa wacce suka fito ciki ɗaya, kuma ya raine ta tun daga ranar da aka haife ta. Ji ya yi tamkar ya haɗiye ransa ya mutu, domin yana jin samunsa a cikin family ɗin da suke rayuwa cikin farinciki da kwanciyar, hankali tamkar tsinuwa ne a garesu, domin matuƙar bai daina jin waɗanannan euphoric feelings ɗin ba akwai matsala, matsalar da yake ganin zai iya zama bala'i da musifa ga ahalinsu bakiɗaya. Duniya ta la'ance shi ya zamo abin tsinuwa da tur a rayuwarsa, kasancewar babu macen da yake a matsayin matarsa sai ƙanwansa wanda suka fito ciki ɗaya. A duk lokacin da suka haɗa ido, sai ya ji tamkar ya rungume ko ya samu sausaucin matsanancin sha'awarta dake ɗawainiya da shi, tun lokacin da ya fara mallakar hankalinsa, wanda bai taɓa jin haka ga waya 'ya mace ba." Ya rintse idanunsa yana faɗin,"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un." Daidai lokacin da suka haɗa ido da ita tana kallon shi cikin tsanannin so na 'yan'uwan ta ka. Ummu da Abu tsaye a farfajiyar gidan suna jiran isowarsu, wanda jin ƙarar hon ɗin motar ya sanya suka zaƙu cikin farincikin son ganinsa. Idanunsu na kan kataferen get ɗin gidan daidai lokacin da Inusa mai-gadi ya taso a hanzarce, ya wangame get ɗin dake ƙoƙarin fin ƙarfinsa. Cikin zaƙuwa Huwais ya buɗe motar ya fito tare da ƙarasowa gurin iyayensa ya zube yana gaishe su. Abu ya miƙar da shi, tare da shafa bayansa yana murmushi sai kuma ya rungume shi, wanda ya ba shi damar shiga jikinsa sosai yana jin ɗuminsa da ke ƙara masa sonsa. "Barka da dawowa son." Abu ya ce daidai lokacin da ya koma gurin Ummu tana shafa kansa. "Haƙiƙa zuciyata ta yi kewarku matuƙar gaske." "Ai ka san Allah son? Daga wannan babu inda zan ƙara barinka ka tafi. Saboda gida bai ƙoshi ba, ban ga dalilin da za a bawa waje ba. Ka tsaya ka kular mini da company nina da kasuwancina, don haka ko da miliyan za a baka duk wata ba zan lamunta ba, saboda na fara tsufa ina buƙatar wanda zai kula da dukiyata. Na kuma samu lokacin da zamu sha soyayya da Ummunku." Ya ƙarashe maganar cikin sigar barkwanci, wanda ya sa suka kwashe da dariya gabakiɗayansu . "Barka da dawowa ƙaramin maigida." Inusa ya ce lokacin da ya ƙaraso gurinsa ya durƙusa cikin girmamawa bayan ya kulle get ɗin gidan tare da ɗaukar jakarshi. "Barka, Inusa mun same ku lafiya?" Ya amsa yana faɗin haka. Gabakiɗaya suka rankaya zuwa haɗaɗɗen falon su mai matuƙar kyau da tsafta. Tun kafin su tafi ɗauko sa Hilah ta shirya masa lafiyayan abinci mai daɗi sosai. "Ya Huwais, wanka ko abinci?"Ta ce tana kallon shi bayan ta ƙarasa kan kujerar da yake ta zauna, har suna gogar jikinsu tare da jin numfashin junansu. Murmushi ya yi yana kallonta sosai ganin yadda ta ƙara kyau da cikar haiba. Abin sai ya ƙara ba shi mamaki ƙwarai, domin har yanzu kallon yarinya yake mata. Wacce ya yi rainonta da kanshi, tun tana ƙarama ya ci kashinta da fitsarinta, amma shi ne ta girma ta zama babbar mace da zata iya sace ko wane zuciyar ɗa namiji. Hannunsa ya zare daga nata, sakamaon jin wani abu mai kama da shokin yana zagaye ilahirin jikinsa. Haɗi da maganaɗisun ƙaunarta na bin duk wani bargo na jikinsa. Bugawar da zuciyarsa ke yi ba a bisa ƙa'ida ba, ya sanya shi ya matsawa tare da zare hannunsa yana kallonta. "Sis, bari na yi wankan kamar zan fi jin daɗi kuma abincin ya shiga. Ɓata fuska ta yi ganin ya janye hannunsa sai kuma ta miƙe tana faɗin, "Ok, bari na haɗa maka ruwan." Tana jin wani daɗin dawowarsa. "Karki damu je ki huta tun da na dawo kike ɗawainiya da ni, ma za je ki huta zan yi da kaina." Ya ce tare da miƙewa. "Akan me Yaya, na ga ko da can ni nake haɗa maka?" Ta ƙarashe maganar cikin damuwa. "Allah ya ƙara Anty Hilah dama sai wani murna kike na dawowarsa, sai ka ce ke kaɗai kike ɗoki. Ga shi nan..." "Ke ni sa'arki ne?" Ta nufe ta tare da ɗaga hannu za ta kai mata duka, wanda ganin hakan ya sa ta ruga ta ɓoye a bayansa. "Ke da ma baki da kunya sam! Shi ya sa na fi shiri da Umnaah ai." "Duk ku bar maganar bari na je na yi wankan, Abincin ma kisa Abidin ya kawo mini" Ya faɗi tare da kama hanya zuwa ɗakinsa. "No Yaya, gaskiya ya kamata ayi lunch a tare. Ka daɗe outside country, ya kamata ace ko ɗan ƙwarya-ƙwaryar liyafa mun haɗa." Ta ce mishi cikin damuwa. "Ke!" Ta ji muryar Ummu ta daka mata tsawa da take saman bene wanda sai da ta ji cikinta ya murɗa. "Kin san na tsani shegen kaɗifirin ki da iya surutu marasa kan gado. Ya dawo ba za ki barshi ya huta ba? Ke ce za ki gaya masa abin da zai yi?" Ta ce cikin tsananin zafi tana huci Shiru ta yi tare da sunkuyar da kanta sai ta fara ruwan hawaye tana jin babu daɗi a ranta. Huwais sai ya ji babu daɗi duk da hakan ba sabon abu bane, amma yayi tunanin Ummu ta daina ashe ba ta sake zani ba. "Wuce ka tafi ka yi wanka, zan sanya a kawo abincin sai ka ci ka yi baccin gajiya." Ta ba shi umurnin haka wanda ba shi da zaɓin da ya wuce ya bi. Kallon Ummi ya yi ba tare da ya amsa ba sai kuma ya juya ya kalleta har yanzu hawaye ta ke yi ya fice yana jin babu daɗi a ransa. Yana fita ta sakko ƙasan tare da ƙarasowa gurinda take tsaye kamar icce. "Ki kiyaye ni Hilah na gaya miki bana son wannan kusancin tsakaninku, duk da cewar nina haife ku, amma cases nawa ka samu na aikata ba daidai ba tsakanin 'yan'uwa. Ina kiyaye haƙƙin tarbiyarku da Ubangijina ya bani ne, don haka na gaya miki ki daina shishshige masa." Ɗaga mata kai ta yi alamun ta ji, a ranta take tunanin Ummu ta kasa fahimtar 'ya'yanta, ba su daga cikin irin waɗannan 'ya'yan. Ta yadda ta amince sun shaƙu da shi fiye da ƙanninta da suke mata, amma karta manta shi ɗin ta fara sani a lokacin da ta girma domin ya ci kashinta da fitsari. Shi ya fara ba ta abinci da shi ta yi wayo har ta girma." "Ma za ki wuce ki bani guri." Ta daka mata tsawar da ta fi wancan. Shiga ɗakinsa ya yi wanda yasha gyara yana ƙamshi turare mai daɗi. Ɗakin ya bi da kallo ya san cewa ita ta gyara ba masu aiki ba, domin gyaranta daban yake da na kowa. Ta san tsarin da yake so a ɗakinsa da yadda yake son a ije masa takalminsa da kayansa. Kai hatta hulunansa da dressing mirrow Hilah duk ta haddace yadda yake son su kasance. Ɗakin ya ƙara bi da kallo takaddun ne da bulunbulun masu kyau ta yi kwalliya da su, haɗe da sunansa tana masa murnar dawowarsa. Ɗaya daga cikin bulun-bulun ya ɗauko tare da rungume shi a ƙirjinsa yana jin tamkar ita ya rungume. Ya daɗe yana ƙarewa ɗakin kallo sannan ya miƙe zuwa bayi tare da shiga bayi. Wanka ya yi ya fito dga shi sai tawul ɗaure a ƙirjinsa. Tsayawa ya yi yana shafa mai daidai lokacin da Abidin ya yi sallama da tiren abinci ya ije tare da fita. Bayan ya gama gyara jikinsa ya feshe jikinsa da turare mai ƙamshi. Yana cikin riga da wando jeans da tishet ruwan bula domin shi ma'abocin ƙananan kaya ne, kuma suna mishi matuƙar ƙyau sosai tare da karɓar fatar jikinsa, da take ruwan tarwaɗa. Gashin da yake kwance a jikinsa ya ƙara ƙawata jikinsa, domin hatta yatsunsa ga shi ne kwance a jikinsu. Haƙiƙa yana da kyau mai ɗaukar hankali da rikita zuciyar 'yan mata. Yana da idanu amma ba manya sosai ba. Sai dai, duk macen da ya kalla sai ta ji tamkar ta yi tsuntsuwa ta ɓace daga gurin, domin wani irin ƙwarjini da haiba da ke cikinsu. uwa uba maganaɗinsu da suke da shi tamkar an zuba zaiba. Bashi da hasken fata, amma kuma yana mafani da mayuka masu kyau da tsada, waɗanda suke ƙara fito da ainihin kalar fatarsa da kyansa. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 07072971093 CALL: 008144072423 *RANAR WANKA...* NA JAMILA LAWAL ZANGO "JAMCY" ☀️ *First Class Writers Asso* ☀️ Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation *GARGAGAƊI* Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️ JAN HANKALI Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne. SADAUKARWA Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a. PAGE 2 BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM Ba shi da hasken fata, amma kuma yana mafani da mayuka masu kyau da tsada, waɗanda suke ƙara fito da ainihin kalar fatarsa da kyansa. Sajensa da ya zagaye duniyar fuskarsa, da ɗan gemunsa mai kyawu. Shi yake ƙara rikitar da duk macen da ta yi tozali da shi, har ta ji ba ta wata addu'a face samun miji ko saurayi kamarsa. Dogo ne sosai yana da ɗan jiki kaɗan, wanda ya ƙara kyautata kyawun surarsa da halittunsa. Ƙirjinsa mai faɗi irin wanda mata suke kira da gadon bacci. Abin da zai fi ɗaukar hankali a halittunsa; idanunsa. Tabbas yana da wata irin idanu irin wanda turawa suke laƙabi da golden eyes, domin in yana kallon, sai ka rasa natsuwarka. Hakika kyawun idanunsa baiwan ne da Allah ke bawa wanda ya ga dama. Kasancewarsa mai rahma mai yin kyauta na baiwa ga wanda ya so, ba tare da ya duba cancantar hakan ba. Mutun ne mai yanga. Eh tabbas yana da yanga sam bai cika shiga rayuwar wasu ba, amma kuma yana da sauƙin mu'amala domin ba shi da zafi sosai, ko 'yan'uwansa shedane, saboda tun suna ƙanana har suka girma bai taɓa ɗaga hannu ya doki wani ba, sai dai faɗa wanda shi ma ba kasafai ba. Ballantana Hilah da take rayuwarsa gabakiɗaya, domin tun a ranar da aka haifeta Allah ya sanya masa sonta na mutuwa, wanda ada yana tunanin saboda ƙanninsa uku duk maza ne, sai ita ta zo a na mace shi yasa yake mutuwar sonta. Amma da tafiya ta yi tafiya girma ya kamasa sai ya fahimci soyayar aure yake mata, wanda yake kallonsa mahaukaci wanda bashi da cikakken hankali. Zama ya yi yana buɗe kular abincin. Wani irin ƙamshi ya ziyarce sa, wanda ya sa ya lumshe idanunsa da ake kira sexy eyes. "Anya yana ganin kwai macen da tafi Hilah ɗinsa iya abinci? Kai da wuya domin in har akwai to bayanta take, domin Hilah ɗinsa gwanace gurin iya girki sam ba ta da ƙiwa, a gurin haɗa abincin da mutum zai ci ya samu natsuwa. Tabbas duk namijin da ya same ta ya more rayuwarsa domin an gama ba shi rabonsa na duniya sai na lahira. Take ya ji wani irin tsananin kishi mai zafi, ya taso masa tun daga kan ƙafafunsa har i zuwa kansa, ya mamaye shi har baya iya ganin abincin sai dai dishi-dishi. Sai ya miƙe yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa, tamkar ruwan xafin da aka ɗora na mai jegen da ta yi haihuwan fari ake shirin sauke mata don ta yi wanka. Idanunsa suka kaɗa har ya ji abincin da yake sha'awarsa da muradinsa sun gimsheshi ba tare da ya ɗanɗana ba. Zuciyarsa na tururi tamkar ya haɗiye kansa ya mutu. "Ni dai na shiga uku! Allah ka jarabce ni da abu mafi girma soyayya kuma ƙanwata wacce muka fita ciki ɗaya. Tabbas wannan girman jarrabawar ta zarce tunanina." Wani irin sha'awarta da ƙaunarta suka taso masa, har suna ƙoƙarin kawar da hankalinsa. Musamman yadda ya ga ta canza ta girma ta zama babbar mace. Duk wata halitta da zai sa a kira mace da cikakkiyar budurwa ta kai, domin in har memerinsa will served him well, ranar Juma'a 20/02/25. Za ta shiga shekara sha tara a duniya. Wato birthday ɗinta wanda ya shirya wa ranar domin ya tana ji kyauta ta musamman a ranar. "Allahumma gafirli, warahamni, waj burni, wahdini warazuqni." Ya fara faɗi a zuciyarsa yana maimaita domin tabbas Allah ya jarabce shi. Miƙewa ya yi, domin a halin yanzu babu abin da idanuwansa suke kwaɗaita masa son gani face ita, don samun natsuwar zuciyarsa. Ba tare da ya ci abincin duk da yunwar dake ƙwaƙularsa ya mai da abincin ya rufe. Ko da ya shiga falon sauran yaran ne a falo, amma ban da ita wanda ya san tana kicin domin ɗora girkin dare. Yana mamakin yadda Ummu ta hana rayuwarta saƙat ta mai da ita kukun gidan, duk da tarin masu aikin da suke cikin gidan. A cewarta abincin ta yafi daɗi kuma gata take mata, amma abin da yake ɗaure masa kai sam ba ta barin Azerh, Umnaah da Amnaah su shiga ko kaɗan. Don ance mutum tara yake bai cika goma, ba da sai ya ce takai. Ta fannin addini malama ce wacce ta samu tropy da yawa na gasar karatun alqur'ni har waje ta je. Sannan a makarantar boko ita ce best student a fannin computer Jami'ar Abuja birnin tarayya. "Laa Ya Huwais ka dawo mu yi hira?" Umnaah ta miƙe da sauri ta isa gare shi tare da kama hannun shi tana murna. "Taɓ! Ta ya ya zai iya cin abinci Ummu ta taɓa 'yar gidansa? " Azerh ta yi maganar tana kallonsa da ya ƙarashe shigowa falon. "Ya Huwais, tana kicin tana dinner." Cewar Umnah da ta kama hannunsa, ganin yana ta waige-waige. "Eh, yana da gaskiya domin a gaskiya abin da Ummu take yi sam ba ta kyautawa. Anty Hilah 'yar'uwammu ce biogically, amma sam ba ta barin ta huta kullum cikin aiki, kuma ta hana mu taimakon ta. Ta manta karatunta yana buƙatar lokaci." "You

Chapter 1 of 17