sauri ta sha gabanta ganin ta miƙe zata wuce."Haba sahibata! Kar mu yi haka dake. Na fahimci yadda kike son shi."
Jin abin da ta ce ya sanya ta jata suka koma suka zauna suna fuskantar juna.
"Yauwa dama na san za ki fahimce ni. Soyayyaarsa ce ta sanya na yi miki haka, don ina jin duk wanda ya nemi ya raba ni da shi zan iya jan layi a tsakaninmu."
"Na yarda tun da ga zahiri kin nuna."Ta furta cikin mamaki tare da jinjina soyayya.
"Yanzu mene ne abin yi? Na kasa tunain komai. Kawai ji na ke yi sonsa zai kashe ni."
"Mu yi addu'a, amma ki duba lamarin don Allah. Musammam yadda Hamad zai ji. Kin ga Abu ya hana shi kula ki sai dai ya kira bai fi sau ɗaya a sati a. Cewar sai kin gama karatu, kuma haka ya ji ya amince. Tsawon shekaru nawa yana jiran.."
"Don Allah! Mu bar maganar nan, matuƙar ba shawarar yadda zai sanya ya bayyana kansa gareni ba."
"Addu'a ita ce kawai zan ba ki shawarar ki ci gaba da yi."
Da ta dawo makaranta kai tsaye sashinsa ta nufa domin ta san Ummu ba ta nan. Tun safe ta tafi ta'aziyar rasuwar da aka yi a family su.
Yana zaune da remote a hannunsa yana kallo. Mamakin ƙofarsa da ta gani a buɗe ta yi. Da ta shiga falon tsayawa ta yi tare da ƙura masa ido cikin mamaki.
Ƙurawa junansu idanu suka yi, yayin da take kallonsa cikin tsananin soyayya irin ta 'yan'uwanta, shi kuma kallon so yake mata. Wani irin abu yake fisgarshi daga cikin idanunta yana aika masa da maganaɗisu a cikin ƙwanyarsa.
A hankali ta tako ta ƙaraso zuwa kan kujerar da yake har suna gogon juna
"Ya faɗa min zan ce za ka je na ganka ka sha ado haka?"
Dariya ya yi jin abin da tace tare da sanya hannu sa ya karɓi wayarta da take ƙoƙarin ɗaukarsa hoto.
"Na yi miki kyau ne?"
"Sosai kuwa! Ka ganka ne? Tamkar wata a cikin taurari."
Murmushi ya yi sosai har kumatunsa suka lotsa wanda ya ƙara masa kyau.
"Zan ce zani ba ki ba na buɗe ƙofata ba. Najib ya sanar dani yana hanya zai raka ni zance."
Sosai ta bayyana farincikinta wanda ya ba shi haushi ganin ba ta kishinsa.
"Wow! Wace mai sa'ar ce Yaya? Ko da yake bai kamata na yi maka wannan tambayar ba, tun da na san akwai wacce ta tsaya ta kashe kuma ta tsare tsawon shekaru."
Kafin ta kai aya ta ga yanayinsa ya canza wanda ya sanya gabanta ya faɗi.
"To ba zan ce za ni ba. Najib xan raka mahaifin Samahatu ya ce ya zo." Ya yi mata maganar cikin ɗaure fuska.
Ganin yadda ransa ya ɓace ya sanya ta ji babu daɗi.
"Am sorry ina ɓata maka rai! Ka yi haƙuri ni fa adalci na ke son ka yi wa Anty Wajnah."Sai kuma ta yi shiru ganin ita kanta soyayya ya sanya za ta yi butulci.
Da sauri ta kama hannu sa da ya yi banza da ita yana canza tasha domin ta gama ba shi haushi.
"Na fahimci yadda kake ji Yaya, domin ni kaina ina cikin halin da kake ciki, wanda in zan auna da yadda nake ji zan iya maka adalci."
"Yauwa 'yar ƙanwata na manta ta faɗa son mahaukacin masoyinta." Ya ce mata cikin murmushi tare da jan hancinta.
"A soyayya ta ne ya hauka ce, amma shi mutum ne mai hankali, musamman yadda iya furta kalamai cikin baiwa da da hikima. Sannan duk ilmina sai da na sara masa gurin amafani da ayar Allah da hadisan manzon Allah."
"Au dama akwai namijin da za ki iya yabo kamar haka? Bayan kin sha gaya mini babu namijin da kika taɓa gani irin.."
"Come on, Yayana. Kai fa na daban ne, kuma ɗan'uwana na jini, shi kuma soyayyace a tsakaninmu. Har yanzu kana nan a matsayinka na musamman ne kai. Special and extraordinary."
"Hmmmmh!" Ya ce mata kawai amma ya ji babu daɗi yabonsa da ta yi."
"Da gaske na ke yi, kuma magana na ke son mu yi." Ta furta mishi tana kallonsa tare da kama hannunsa duka ta riƙe.
"Fita zan yi ki bari sai na dawo, don na san kan mahaukacin masoyinki za ki yi maganar." Ya ce domin har ga Allah kishi yake yi sosai, ganin ba ta san shi bane, amma ta faɗa son wani can.
Ta buɗe baki za ta yi magana sallamar Najib ta katse ta.
"In ka ga wata dole ka ga zarah. Ni dai har yau ban taɓa ganin ƴan'uwa masu tsananin ƙaunar junansu ba." Ya furta tare da ƙarasowa yana tafa hannunsa yana dariya.
Dariya suka yi tare da miƙewa."Barka da zuwa Ya Najib." Ta furta yayin da ta nufi frij ɗin sa ta ɗauko ruwa mai sanyi da drink ta ine, sannan ta nufi kicin don ta ɗauko cup.
Bayan ya amsa sai ya bita da ido kamar yadda ya ga ya raka ta da ido har ta ɓule.
Naunauyar ajiyar zuciya ya saki tare da shafa sumar kansa yana murmushi ya juyo yana kallonsa.
Hira suka fara yi har ta ɗauko kofin ta ɗaurayo ta ije masa.
"Ni bari na tafi, Yayana, sai kun dawo Allah ya tsare hanya ya dawo da kai cikin aminci." Da larabci ta furta tare da tsayawa tana kallonsa.
"Yauwa, ƴar ƙanwata. Allah ya yi miki albarka." Ya furta cikin jin daɗin addu'ar da ta yi masa.
"Amin." Ta amsa tare da ɗaukar jakarta tana yi wa Najib sallama.
A hanya Najib yake driving babu wanda ya fara magana sai ya waiwayo ya kalle shi ya maida hankalinsa kan hanya.
"Ina mamakin shaƙuwarku da ƙudirinka kan ƙanwarka, wanda na tabbatar da tsoron Allah da kake da shi ne yake rinjayar zuciyarka, amma da tuni ka yi abin da ba'a so."
"Ubangiji ga tsare ni Najib! Ka san ni ko wane ne? Soyayyar da na ke mata ko da zamu rage daga ni sai ita a duniya, matuƙar Ubangiji bai bani damar mallakarta a matsayin matata ba, ba zan taɓa aikata alfasha da ita ba."
TUNATARWA
Shin kina daga cikin matan da karatun Novels yake ɗauke musu hankali suke barin sallah ta wuce su? Ko kina daga cikin masu daina karanta Kur'ani ko azkar duk saboda karatun Novels? Don Allah yar'uwata musulma ki daina barin sallolinki na wuce ki saboda karatun litattafai Hausa, saboda ko mu MARUBUTA da muke yin typing da zarar lokacin sallah ya yi muke tashi mu yi sallah. A kiyaye da ibadu musamman sallah saboda ita ce farko da za a fara dubawa a cikin ayyukan mu. Da fatan za ki ji kuma ki hankalta. Fatanmu mu gudu kuma mu tsira tare. Allah ya bamu ikon aikatawa Amin. Taku Jamila lawal Zango.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 8
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Ubangiji ga tsare ni Najib! Ka san ni ko wane ne? Soyayyar da na ke mata ko da zamu rage daga ni sai ita a duniya, matuƙar Ubangiji bai bani damar mallakarta a matsayin matata ba, ba zan taɓa aikata alfasha da ita ba."
"To ta ya ya, za ka mallake ta? Kar ka manta ciki ɗaya kuka fito. Na sha gaya maka sheɗan ne kawai ke son wasa da zuciyarka, da yi mata ingixa mai kantun da xai sanya ka aikata abin da duniya za ta la'ance ka."
"Shiru ya ƙara yi kawai ba tare da ya ce komai ba, domin tuntuni shi ma yana tunanin haka.
"Gujewa haka don Allah ka tausaya Wajnah, ka aureta ka daina jiran gawon shanu, domin ko jiya sai da ta kira ni tana kuka, sam bai kamata ka yi mata haka ba."
Shiru ya yi bai furta kalami ba wanda ganin hakan ya sanya ya kunna ƙira'ar Sulaiman Ahmad Suratul Isra'i.
Bayan ya dawo ya yi wanka yana cin abinci ta shigo domin so take ta nemi shawarar shi.
"Am sorry, na dame ka ko Yaya? Kan dai maganar mahaukacin masoyi ne."
"Wannan dalilin ya sanya na ke kishi da shi, domin tun daga lokacin da ya ɓullo cikin rayuwarki, kika daina mini wata hira da magana sai na shi." Ya yi maganar yana tauna abincin a kasale.
"Ka yi haƙuri bani da zaɓi ne." Ta ba shi amsa tare da zama a gefensa.
"Ina son ya bayyana mini kansa kuma na buƙaci haka ya ƙi." Ta ce tare da ƙura masa ido tana kallon shi.
"To ni mai zai ce miki Hilah?."
"Saboda me? Karka manta kai ka bani shawarar na yi soyayya da shi."
"Soyayyar wasa ko?"
"Ya zuciya ba ta da zaɓi, ka san soyayya gaskiya ne. Kamar yadda ka kamu da son wannan budurwar kake ganin za ka iya mutuwa, matuƙar ba ka same ta ba, haka ni ma zan iya rasa raina in har ban auri mahaukacin masoyi ba..."
A zabure ya miƙe daga ƙwanciyar da ya yi cikin tsananin mamaki.
"Kin san me kike cewa? Anya ƙanwata ce? Wacce na santa da tausasa lafazinta a gare ni?"
"Ka yi haƙuri bani da zaɓi ne, domin kan son shi na kurumce kuma na makance zuciyata ba ta ji, ba ta gani. Burina na rayu da shi, saboda yana da addini da iya kalamai."
"Wane tabbaci kike da shi? Bayan baku taɓa haɗuwa na zahiri ba, kuma ba ki san ko musaki bane, wanda ƙila hakan ya sanya ya kasa bayyana miki kansa?"
"Ni fa ko ya yake zan rayu da shi." Ta ba shi amsa kai tsaye wanda hajan ya sanya ya cika da mamaki da tashin hankali.
"Ki dai sake tunani domin ko bayan wannan Ummu ba za ta taɓa yarda ki yaudari Hamad ba?"
"Kai da kullum kake kushe sa, shi ne yau za ka faɗi haka. Na yarda da kaina Yaya. Yadda na ke tsananin roƙon Allah da ya ba ni miji na gari, ba zai haɗa ni da mutumin banza ba, domin Allah ma ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki.
Shiru ya yi ya kasa cewa komai domin ko zai yi maganar bai san me zai furta ba.
Ganin yadda ta tsare shi da idanu sai tsoro ya kama shi, tunaninsa ko ta gane shi ne. Ya tattaro hankalinsa da natsuwarsa ne, sakamakon tuna in har da ta gane shi ne, sam ba za ta yi masa magana cikin natsuwa ba, kasancewar yadda za ta ɗauki abin daban.
Tsoro ne da damuwa suka bayyana a fuskarsa har ya firgita sosai. Gudun kar ta gane shi ya ɗaga mata hannu yana ce wa,"Please, ki je zan yi tunani na ba ki shawarar da ya makata, amma don Allah kar ki tambaye ni abin da na yanke har sai na neme ki." Ya furta cikin gundurar magana da ita.
"Ok, ba zan tambaye ka ba, sai dai ina roƙonka da ka yi mini adalci, gurin yanke shawarar, domin matuƙar ka ce za ka bani shawarar na rabu da shi, zan fallasawa su Ummu ina son shi, tare da sanar musu da kai ka bani shawarar na fara ƙaunarsa."
Mamaki ya sanya shi zaro idanunsa musamman yadda take maganar babu tsoro ko firgici.
"Hilah!" Ya furta cikin razana ganin za ta fice, amma bai gama shanye ruwan mamakin da ta ba shi daga farko ba, ya ga ta rufe ƙofar ta fice ba tare da ta juyo ba.
Dafe kansa ya yi tare da dunƙule hannunsa ya kai wa bango nushi. Naushin da yake jin dama ita ya kaiwa, saboda tsabar rainin da ya hango a idanunta.
Fara tafiya ya yi zai bita sai ya ga kuma babu amfanin hakan ya dawo ya zauna.
"Lallai na ibo ruwan dafa kaina!" Ya ce tare da sakon ajiyar zuciya mai ƙarfi. Da sauri ya miƙe ya ɗauki gorar ruwa ya buɗe murfin tare da saka murfin a dusbing ya fara sha. Sai da ya shanye tas ya saka robar a cikin mazubin sharar ya shige ɗakinsa cikin tunani.
Hilah kuwa tana fita ɗakin ta saki dariya sosai, ganin yadda ya ruɗe sosai. Godiya ta yi wa zuciyarta na ba ta shawarar ta yi masa wannan barazanar, wanda gashi tana son ta yi tasiri ganin yadda ya ruɗe, saboda ya san ba ƙaramin hauka Ummu za ta yi masa ba.
Saboda abin da ta gaya masa da daddare kasa hawa online ya yi, har sai lokacin da ta tura masa da tsaƙon karta kwana na cewar tana jirar sa.
Ƙarar shigowar saƙon suƙa ƙara rikita duk wani tunaninsa kuma ya gaza sukuni.
Ya kasa komai har sai da ya kunna data suka fara hira. Ba su daina hirar ba sai ƙarfe ɗaya, wanda shi ya umurce ta da ta kashe datar ta yi hadda.
Ganin ba ta sanar da kowa ba ya sanya hankalinsa ya kwanta. Tamkar ya yi baƙo ya mutu. Don haka ya shareta suka ci gaba da soyayya.
A cikin kwanakin ya ji yana buƙatar ya rinƙa jin muryarta, wanda ya san faruwar hakan kamar da wuya.
Dubara ta faɗo masa wanda take ya ɗauki wayarsa ya shiga cikin Ai. Ba tare da ɓata lokaci ba ta canza masa muryarsa kamar yadda ya buƙata. Bayan ya gwada kiran Najib ya tabbatar masa da babu wanda zai gane muryarsa sannan ya bari zuwa dare ya yi surprizing ɗinta.
Da daddaren misalin ƙarfe sha ɗaya saura tana tsaye a gaban madubi ta fito daga wanka tana ɗaure da tawul.
Kiran wayar da Hamad ya yi ya sanya ta fasa sanya kayan baccin da ta fito da su ta ɗora kan gado.
Amsa wayar ta yi kamar yada ta saba. Ba su wani jima ba ya kashe, don babu wata shaƙuwa a tsakaninsu. Shi kansa ya san ba ta son shi, amma sam bai damu ba, domin irin su mutum zai yi burin aurensu ya xauna da su, ko da ba sa ƙaunarka. Ballantana ya san yana cikin jadawalin mazajen da Allah ya yi musu tagomashi da kyawu da iya sace zuciyar mace da kalamai. Wannan ba matsala bane a gurinsa, domin yana sanya rai watarana za ta so shi ta shayar da yaransa.
Bayan ta gama wayar ta ije tana tausayin halin da zai shiga.
Kayan baccin ta sanya tare da ɗaukar wayarta ta kunna data.
Mamakin ganinsa da ta yi yana online domin wani lokaci sai ta jira shi ya hau.
Ba ta gama shaanye ruwan mamakin ba kawai ta ga kiransa, wanda saboda tsananin farinciki da mamakin kiran ya sanya ta kasa ɗauka.
Miƙewa a zabure ta yi, har tana bugewa da gefen gado, amma ba ta kula ba, ta dawo falo don kar ta tashe su.
"Mahaukacin masoyi ya kira ni? Ko dai mafarki na ke, ko kuma mantuwa ya yi?" Ta tambayi kanta cikin tsananin mamaki, tare da ci gaba da kallon wayar har sai da kiran ya tsinke.
Ganin ya yanke bai sake kiran b,a takaici da jin haushi da kuma wautan rashin ɗaga kiran ya kamata, wanda ba tare da sani ba ta ji hawaye na sintiri a ƙuncinta.
Da sauri ta lalabu layinta da har ta fara bacci.Kiran ya farkar da ita ta miƙe tama mutstsuka idanunta. Ɗaukar wayar ta yi tana mamakin dalilin kiran da addu'ar Allah ya sa lafiya.
"Hello." Ta furta cikin muryar bacci tare da sakin hamma.
"Sahiba! Mahaukacin masoyi ya kira ni."
Jin abin da ta faɗa da kuma muryar da ta yi amfani da ita, ya sanya ta watstsaƙe cikin tsananin mamaki.
"Haba! Da yaushe kuma mene ya ce?" Ta yi mata tambayar a jere.
"Yanzu, amma abin takaici na kasa ɗauka har ta katse." Ta furta tamkar za ta yi kuka.
Wani irin baƙincikin da takaici ya mamaye ta jin abin da ta ce, musamman da ba su yi magana.
"To yanzu mene ne amfanin gaya mini, kuma ke da kike jiran wannan ranar, ban ga dalilin da zai sanya ki kasa ɗauka ba."
"Tsoro ne da fargaba."
"Bai kamata ki ji ko ɗaya daga ciki ba, tun da kin ji kin gani xa ki iya. Ni wallahi na ɗauka ma kin ganshi a zahiri ne. Ƙila ya ga ɓoye-ɓoyensa ya ga babu amfani zai bayyana kansa. Allah ya sanya ba tsoho bane wanda ya takwarƙwashe."
Takacin abin da ta ce ya sanya ta saki tsaki za ta kashe wayar, daidai lokacin da kiransa ya ƙara shigowa cikin wayar.
"Kashe yana kirana don Allah." Ta furta wanda ya sanya ta daƙile wayar tana mata dariya.
Wani irin kyarma hannunta yake yi wanda ta rasa dalili. Garin ta danna inda ake masa kiran ta kashe, saboda takaici kawai sai ta sanya kuka, tare da jifa da wayar.
Ba a ɗauki lokaci ba kawai ya sake kira.Cikin rawar hannu ta yi nasarar danna gurin amsawa.
"Ni mutum ne mai tsananin kishi! Sam ba zan lamunta wacce Allah ya halicce ta don ni kaɗai tana waya da wasu ƙarti suna ji mini muryarta ba." Ta ji muryar ta yi magana cikin wani jrin zaƙi da daɗin saurara a zuciya, wanda ya sanya ta nemi natsuwarta ta rasa.
"Eh a'a ba.... Ka yi haƙuri ba za ka sake kiran wayata ka ji ina waya ba." Ta furta cikin wani salo da muryar da bai taɓa tunanin tana da shi ba, don ko ita ba ta tunanin ta taɓa magana da muryar.
"Ya kamata ki kiyaye domin a kanki zan iya kashe duk mazan duniyar nan, matuƙar za su raɓe ki."
Nauyauyar ajiyar zuciya ta saki tana son inda ta taɓa jin muryar nan, ko za ta gane wane ne mahaukacin masoyinta, amma iya tunaninta ba ta taɓa jin muryar ba.
"Am sorry gimbiyata! Kamata ya yi na yi miki sallama kamar yadda addinimu ya sharanɗa, amma sonki da ya yi mimi dabaibayi ya hana ni sukuni da kishinki ya sanya na manta hakan."
"Ok, na fahimta kuma.."
"Ki kwanta ki yi bacci zan kira ki gobe." Ɗif ya kashe wayar yana riƙe da ita tare da sakin tsadadden murmushi.
Sororo ta yi na ƴan sakanni ganin ya kashe wayar. Halinsa ɗaya da ta tsana kenan, nuna isa da yanke shawara ba tare da ya ji ra'ayinta ba, domin ta so ace sun kwana suna waya.
Cikin sanyin jiki ta kwanta a kan gadon ruf fa ciki tana kallon wayar tamkar zai fito a cikin.
"Oh, Allah ka jarrabace ni da soyayyar wanda ban san asalinsa ba." Ta furta cikin hawaye.
Ta yi iya ƙoƙarinta don ta yi bacci, amma ta kasa domin muryarsa, ke yi mata amsa kuwwa a kunenta. Tunani take yi kamar ta taɓa jin muryar, amma duk iya tunaninta ta gagara tuno inda ta ji ta.
Wajnah zaune a ƙaton falonsu da ya sha kayan alatu. Wayarta a hannunta tana dannawa, wanda gabakiɗaya rabin hankalinta na kan wayar, tana duba wasu kaya da ƙawarta ta saro daga Dubai za ta siya.
Kayan dogayen riga abayas da gyaluluwa sai kuma takalma. Bayan ta gama zaɓen kayan ta ije wayarta kan stool ɗin da ke gefenta, tana kallon mahaifiyarta da take zaune da aminiyarta Hajiya Fatiha suna hira.
"Mom, na kammala abincin kuma is ready. Na kawo miki nan ke da Momy Fatiha ko a dinning?"
"No, ki kawo nan sai ko kira Binta ta haɗa mini salat ta kuma kawo mini yajin da na siyo jiya."
"Mom, ai na shirya duka har salat ɗin."
"Masha Allah! Yarinyar kirki ma za ki kawo mana nan." Mom ta furta tana kallonta cikin so da ƙauna.
"Wai ni Hajiya Fati, ya maganar haɗin auren da za a yi da ɗan ƴar'uwarki? Na ji shiru tun lokacin da za a yi Engagement aka ce biki sai ya dawo daga Turai?"
"Eh, wallahi haka ne. Ai ta nan ɓangaren duk mun shirya, amma shi yaron ne yake wasa da hankalin iyayensa."
"Anya haka ne, ko dai ba sa son haɗin ne?" Ta yi mata tambayar tana kallonta.
"Kai bana tunanin Lailah, za ta ƙi auren, saboda duk wani ƙoƙari ita take yi."
"To ai abin ne da mamaki domin ya kamata ace an yi tuntuni."
"Haka ne wallahi kin san komai lokaci ne."
"Eh, amma da zafi-zafi a kan bugi ƙarfe! Saboda samun irin namiji kamarsa sai an tona."
"Haka ne, in sha Allahu za a yi auren."
"Allah ya tabbatar da alkhairi."
Wajnah bayan ta kammala jera musu abincin ta haye sama.
Kan gado ta hau tare da sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi.
Tana matuƙar sonsa amma sam hankalinsa ba ya gareta.
Wayarta ta jawo ta danna nambobinsa da tuni ta riga ta haddace. Sai dai har ta gama ringing ba'a ɗauka ba.
"Da ma na san ba zai ɗauka ba, Ubangiji ka karkato mini da hankalin bawanka." Ta furta cikin hawaye tare da shiga Whatsapp ta shirya mishi kalaman soyayya ta tura mishi.
A lokacin da tsaƙon ya shigo yana zaune a cikin bedroom ɗinsa yana aiki a cikin laptop ɗinsa.
Tsaki ya yi ganin saboda rashin zuciyarta bayan ƙin ɗaga kiran sai da ta tura masa da tsako.
Ba tare da ya karanta ba ya goge tsaƙon tare da riƙe wayar ya faɗa kogin tunani.
Abu ne zaune a gaban mota suna tafiya. Huwais ne ya ke jan motar cikin natsuwa.
Abu da ya ke karanta magazine na daily trust ya ije jaridar, tare da juyowa ya kalle shi, da hankalinsa yake kan tuƙi.
"Huwais," Ya kira sunan shi tare da gyaran murya.
"Na am Abu,"Ya waiwawo yana faɗin hakan.
"Maganar yarinyar nan ƴar gidan Alhaji Tukur. Shiru muna ta jiran bayan dawowarka za ka yi maganar bikin ku, amma shiru?"
Jin abin da ya faɗa ya ɗaga hankalinsa ainun. Da sauri ya waiwaya ya kalle sa cikin tashin hankali.
Ya buɗe baki xai yi magana sai ya rasa abin da xai faɗa, domin a wannan karon bai san uzurin da zai bayar ba.
"Umh! Eh..."
"Dakata." Abu ya ce masa yayin da lokaci guda fuskarsa ta canza.
"Ka san cewa a wannan karon ba zan lamunci duk wani uzuri da za ka bayar ba ko? Domin in har da na ɗauki maganar mahaifiyarka, ba za ka yi tafiyar nan ba sai da matarka?"
"Eh, Abu. Don Allah a wannan karon ina son a ƙara bani uzuri, domin sam Wajnah ba na jin ƙaunarta a cikin zuciyata."
"Kana da zaɓinka kenan?" Ya yi masa tambayar kai tsaye.
"Eh, amma akwai abin da na ke son na tabbatar. Don Allah Abu ka ƙara mini lokaci." Ya faɗa tamkar zai yi kuka.
"Ba ka da wani mafita wanda ya wuce ka amince, domin ba za ka mayar dani ƙaramin yaro ba. Haba, Huwais, ka yi wa yarinyar adalci mana. Tsawon shekaru na wa ta ɗauka tana jiranka."
Ransa ne ya ɓace ya rasa mai zai furta domin shi kasa ya san ba shi da hanyar da zai ce mafita ce a gare shi. Kawai zuciyarsa ce take ƙarfafa masa da kuma tabbatar masa da Hilah ta shi ce kuma watarana zai aurenta.
Ganin ya yi shiru ba tare da ya furta kalami ba ya sanya shi gyaran murya a karo na biyu ya ce,
"Mun gama magana da mahaifiyarku in sha Allah gobe zan tura su Kawunka Sulaiman su je su ji magana.
Wani irin tsau ya ji a kansa wansa ya sanya shi juyowa cikin sauri yana kallonsa.
"Don Allah Abu, kar a yi gaggawan yin lamarin nan, saboda na gaya muku bani da ra'ayin zama da ita."
"Mun riga mun gama yanke
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 17