Reading Gargada So By m Shakur Chapter 9 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ban isa dake ba tunda
bani bakici bani baki sha banda kafafu kece ke nema ki bamu, Hauwa nizan kawo mutumi ki aika amai
dukan jina jina”? Masifan da Baba yakeyi yana magana da sauri yasa bama ta gane me Baba ke fadaba
hakan yasa tace “Baba maganan wa kake haka?” “Maganan uwaki nake!” Ya zubamata ashar yana
kumfan baki, yace “bakida mashinshini shekaranki talatin agidana nayi shiga nayi fita na nemo miki Alai
Kabiru kinsa yaran aikinku sunje sunmai jina jina daga asibiti nake yanzu” faduwa gaban Hawwa yayi
sosai yanzu su Hayatu dukan Alhaji Kabiru sukayi? No anya? There’s no way zasu dakeshi she knows her
team, yanda tai shiru hakan ba karamin batama Baba rai yayi ba yanuna kanshi yace “Hauwa nike miki
magana kika tsaya kina kallona ba uppan eh”? Umma tace “to kai waye banda abinka Malam, gaka ga ita
kadan kagani ai” kallonta Hawwa tayi saikuma takalli Baba da idanunshi sukai jajir yana kallonta ahankali
tace “Baba kayakuri nayi kuskure aika su Hayatu danayi su tsoratasa amman na tabbata basu tabasa ba
Baba karya yayimaka” Baba namata wani kallo yace “nafito daga asibiti yanzu ni da Malam Sama’ila kice
karya yamini”? Gyadama Baba kai tayi kafin ahankali tace “Baba kayakuri banason na batamaka rai yasa
nakasa fadamaka, banason Alhaji Kabiru, ni bazan iya aurenshi ba bazan iya zama dashi ba saisa nasa su
tsoratashi sabida yarabu dani”ihu Baba yayi yace “so kike na ninke hannu ina kallonki kikai shekara
hamsin agidana baki aure ba? Me kike nema ajikin da namiji da Alhaji Kabiru baidashi? Bakimaji dadi
kinsameshi ba keda kikai kwantai agida” lumshe idanu Hawwa tayi maganan Baba na mata zafi azuciya,
Baba yayi ihu da kusan duka yan anguwan na jiyosu yace “nagaji da zamanki agidan nan nagaji Hawwa ki
tattara ki barmin gıdana idan kinsan baki shirya aure ba gwara nasan eh zaman kanki kike da ki zaunamin
agida ahaka” bude idanu Hawwa tayi takalli Baba idanunta sunyi ja ahankali tace “Baba ni kake kora
daga gida?” Azuciye Baba yace “Abinda kikeso kenan tuntuni ban barkiba yanzu nabaki dama kije kiyi
zaman kanki” hawaye masu dumi suka zubomata dasauri tashare su takalli Baba tace “Baba tunda
nataso arayuwana bantaba nayi wani abin kunya dazai jamaka abin magana agariba, nakare mutunci na,
nayi karatu nadage nazama wani abu sabida na taimakama mahaifina, na dauke maka duk wani wahala
da tunani dazakayi da damuwa, Baba kadauka banson aure ne? Kadauka ban gaji da maganganun
dakakemin kullum ba? But ya zanyi banda mai sona banda mai nemana titi kakeso naje natare hanya
nace sai anzo an aureni dole eh Baba? Yakakeso nayi da raina Baba? Umma ta tasani agaba, kaima haka,
yan anguwa haka ina zansa kaina naji dadi Baba yakakeso nayi da raina? Banda me aurena” Baba yace
“karya kike Malam Kabiru dakikasa aka dakeshi fa? Shibamai son aurenki bane”? Hawaye Hawwa ta
goge tace “bana sonshi bazan aureshi ba” cikin fushi Baba yace “nikuma idan bazaki aureshi ba ki tattara
kibarmin gidana nasan banda y’a Hauwa nahuta” Hauwa zatai magana Baba yace “fita kibarmin gida”
kallon Baba Hawwa tayi sai kawai ta share hawaye ta tajuya tana huci sosai takoma dakinta, tanada
zuciya fa babban akwatinta ta sauko dashi kasa tabude sip tashiga kwashe kayanta tana zubawa ciki tana
goge hawaye masu zafi da bayan hannunta taje gaban madubi ta kwashe kayan shafanta tasa tahade
akwatin ta rufe taduki wuyanta tasa ajakan goyon ayanta tafito tanajan jakan da karfi Umma ranta
kaman an wanke da ruwan zamzam ta taho da sauri tace “au da gaske Hawwa tafiya zakiyi eh? Bazaki
bama Babanki hakuri ba ki yarda zaki auri wanda yakeso ki aura ba? Tafiya zakiyi yanzu da daddaren
nan” ihu Hawwa tayi. “Tashin mini daga gaba Umma!” Dasauri Umma ta tashi ko kallonsu Hawwa
batayiba taja akwatinta tafito waje ga mutane a kofar gidansu ko kallonsu batayiba tadinga jan akwatin
tana tafiya ranta yayi masifan baci, wlh da za’a tareta ace ina zataje batasani ba kawai dai tasan bazata
taba zuwa gidan Ni’ima ba, batason tana burdening Ni’ima da problem nata, tana fitowa ta tare keke
tashiga ciki tama rasa mema zata gayama keken inama motanta na tareda ita, samin kanta tayi da
gayama keken yakaita layinsu Excellency tun kafin su shiga wajajen aka taresu ahankali ta kalli keken
tace “dan Allah kajirani anan zan biyaka inason na shiga gidan nan nadauko motana ne” da dan saurinsa
yace “kai Hajiya, da akwai inda zani gaskiya bazan iya jiranki ba” gyadamai kai tayi tace “ba matsala
nawa zan baka”? “Dubu biyu” kirga kudin tayi ta bashi yatayata sauko da akwatin security dake
maingate din yace “Hajiya daga ina kekuma? Wakikazo nema anan”? ID card nata ta nunamai tace “I’m
officer Hawwa, dazu i came for work nabar motana anan” gyadamata kai yayi yace “hold on” tana tsaye
awajen yawuce yashiga office nasu yana waya kusan 10mins tana tsaye sannan yafito yace “kibar
akwatin ki anan u can go inside” gyadamai kai tayi tawuce ciki, almost kowani gate taje sai an tareta
haka dai at last tashiga compound din ga ma’aikata babu wanda yace mata wani abu tawuce wajen
motarta tana sauke jakanta na baya tana ciro car key dinta hakanan taji ajikinta ana kallonta samin kanta
tayi da dago kanta sama Khaleel ta hango tsayi a balcony dakinshi asaman bene yana huro hayaki daga
bakinshi ga wata ta rungumeshi da bataga fuskanta ba dan macen ta bata baya.



Chak Hawwa ta tsaya tanamai kallon kaman tazo wajen ta kasheshi tana tuna abinda yamata dazu,
shima haka comfortably yake kallonta bayako kyafta idanu yana zukan shisha daya daga cikin matayen
sa da aka kawomai yau na shafashi tana manmannamai kiss ajiki tana sanye da arnen kayan bacci abinda
yakirata kawai tamai kenan he just want mace ta matse shi, faduwa gaban Hawwa tayi ganin macen na
mannamai kiss a wuya da sauri ta daukekai jikinta na wani iri tawuce wajen motanta tabude kawai ta
shiga taja motan tafito daga parking space saikuma ta tsaya ta sauke glass na motan tareda dan leko da
kanta ta kallo saman still kallonta Khaleel yake kur yana busa hayaki da yatsu Hawwa tamai alamun f*ck
you sannan takoma cikin motan taja motan tai gaba abinta, hakanan Khaleel yasami kanshi da dan sakin
murmushi kadan, the first ever gurl datamai f*ck u aduniya, yarda pipe na shishan yayi kawai yajuya
yarinyar yasa ta rike glass na benen wajen, yaja zip din wandonshi kawai yaciro abin ya caka mata babu
tsoro ko kunyan ma’aikatan su ko yan aikinsu dudda suna sama ana ganin fuskokinsu da movement nasu
bai damuba, yafara yi yanadan murmushi yana kallon gate har saida yadaina ganin motanta yana nishi
sama sama yana dan sumbatu about 20min yayi sannan yatureta tafadi awajen tajuyo tana kallonshi
maida dick dinshi yayi cikin wandon yaja zip sama sannan yajuya yawuce ciki abinshi yafada gado sai
bacci.

[9/18, 7:39 AM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫




✍🏻M SHAKUR




EPISODE
2️⃣
3️⃣ 2️⃣3️⃣
FOLLOW MY ACCOUNT ON AREWABOOKS GUYS BANDA FOLLOWERS AWAJEN😭



IDAN LINK DIN BAIYIBA KU SHIGA AREWABOOKS KUYI SEARCHING SUNANA MSHAKUR ZAKU GANNI SAI
KUYI FOLLOWING THANK YOU❤️



GARGADAN SO:: https://arewabooks.com/book?id=66e1430aa85339246a463225




Tana fita ta tsaya ta dauki box ta loda a boot sannan taja motan tana danna waya ta turama DIG
message kan bazata iya zuwa aiki gobe ba, tunda dama gobe Friday zataje zaria wajen Sister Mom dinta
batada lafiya, baidauki lokaci ba yace permission granted, agidan mai ta tsaya ta cika motanta kawai
tafada titi da daddaren nan tayi zaria daga Abuja.



Wasa wasa fa Hawwa ta tafi, da farko Baba ya dauka zai iya daurewa amman ya kasa wayanshi yadaga
yashiga neman number Baban Yaseer, da kyar ya gane number yayi dialing, Baban Yaseer na zaune a falo
yana aiki da system dinshi Ni’ima na gefenshi tana kallo a Zee world su Yaseer kuma na wasa da IPad
dinsu wayanshi yahau ringing kallon wayan yayi ganin Baba yasa yakalli Ni’ima da hankalinta ke tv yace
“Baba is calling me wife” dan faduwa gabanta yayi cus ba kasafai Baba ke kiran Aliyu ba, katse wayan
yayi yakira Baba da kanshi Baba yadaga yana gaishesa ma bai tsaya ya amsa ba yace “Aliyuu unnn nace
ba mutuniyan taku na wajenku ne”? Yana kallon Ni’ima yace “Baba meke faruwa?” Cus baiso yace “eh
ko a’a batare dayasan abinda ke faruwa ba” ahankali Ni’ima tace “sa wayan a speaker” wayan yasa a
speaker yace “Baba wani abu ya faru ne?” Da dan damuwa kan muryan Baba yace “eh to kusan hakan,
daman na sanar da aminina Malam Sama’ila cewa yadan sakamin sanarwa ina nemawa Hawwa miji,
kowa yafito yanuna yanaso zan bayar” haderai tamau Baban Yaseer yayi Baba yashiga bada labarin har
karshe, hannun Ni’ima har rawa yake ta shiga kiran Hawwa amman bata dagawa, Baba yace “kawai so
nake naji inda take hankalina ya kwanta amman dai inhar bata yarda da auren Alhaji Kabiru ba kam
saidai tabar gidan nawa tayi zaman kanta” adan fusace Baban Yaseer yace “Baba wai mesa kake haka?
Idan kaje ka jefa Hawwa cikin wani hali fa? Ita yarinya ce dazaka mata dolen dole saita auri wanda
kakeso Baba, bazaka bata dama ta kawo wanda takeso ba, Baba an gayamaka batada mai sonta ne”?
Ranshi ya bala’in bacci harya nuna akan fuskanshi yakalli Ni’ima dake kallonshi still tana dialing number
Hawwa yace “did she answer your call wife? I need to know inda take” daga ta dayan bangaren yace
“saida safe Baba bata gidanmu zamu gwada kiranta idan mun gano intda take zamu sanar da kai” ya
katse wayan ya ijiye laptop yatashi da dan zafi yasa hannu ya karbi wayan Ni’ima yayi dialing number
nata da kanshi Ni’ima na kallonshi luckily Hawwa tadauka tace “Best ina driving ne, I know Baba ya kiraki
don’t tell me anything” dasauri Ni’ima ta tashi takarbi wayan tace “naji I don’t want you to tell me
anything and nima I will not tell u anything Hawwa, but just tell me kina Ina yanzu naji kina hanya, ina
zaki”? Shiru tayi kaman bazatai magana ba tace “wajen Ammi zani a zaria” faduwa sosai gaban Ni’ima
yayi tace “Hawwa going to zaria da daddaren nan ke kadai a mota are you okay? Kin manta yanda ake
kidnapping ne a hanyan” ahankali Hawwa tace “I will be fine karki damu” cikeda damuwa Ni’ima tace
“Hawwa why can’t you come to me eh kika kama kik……” key mota dataga Baban Yaseer yadauka yayi
kofa yasa dasauri tazare wayan daga kunnenta ta katse tace “Baby ina zaka”? Slippers yashiga sawa yace
“zaria” tahowa wajen tayi dasauri tace “zaria this night”? “if anything happens to Hawwa wani abu zai
iya samuna!” Yafadi da karfi dayasa chak Ni’ima ta tsaya shima ya tsaya yana kallonta jin abinda yafito
daga bakinshi saikuma yadan dafe kanshi yace “just stay with the kids, text me her aunt home address”
yana maganan yafice tana tsaye awajen taji ana budemai gate, hannunta da aka rike yasa tai firgigit
tajuyo tab dinta Yasmeen tabata tace “Mommy I want to sleep” dan murmushi ta kakalo ta mata ta kalli
Yaseer ma tace “okay muje ku kwanta” kama hannunsu tayi tawuce dakinsu dasu bayi ya kaisu sukai
fitsari sannan tahau gado dasu tace “addu’an bacci” addu’a sukayi taja bargo ta rufesu tana kashe musu
wuta ta rungume su, wasu hot tears taji sunabin kuncinta hannu takai ta share amman sun kasa daina
fitowa jin alamun sunyi bacci yasa ta tashi tafito daga dakin tazo falon ta zauna tana kallon system nashi
very important aiki yake da Oganshi yasashi yayi yaturomai by 11 na daren nan, gashi yanzu 11 saura,
zama tayi tasake fuzar da ijiyan zuciya sannan tadauki wayan nata hannu tasa ta goge fuskanta tass
sannan ta shiga turamai address din, kafin tai dialing number Hawwa amman harya katse bata dagaba
message ta shiga ta turamata. “Be safe Hawwa, I’m worried about you, Allah tsare hanya” kusan 2min
saiga reply na Hawwa tace “I know you are worried, don’t be nakai zan kiraki, love you Best” love you
best din takalla sai taji wasu hawaye masu zafi sun sake zubomata tashi kawai tayi tafada dakinta iPad
dinshi dake saman drawer side nashi na bed ta kalla yawanci yana daukanshi da daddare yadanyi
karence karance, samin kanta tayi da dauka, hoton family portrait nasune ne as wall paper, tadade tana
kallon Baban Yaseer a hoton sannan tai kokarin duba wayan taga password shiru tayi tana tunani sai
kawai tasaka birthday na su Yaseer taga yabude tashiga cikin wayan, tana dube dube chan ta shiga
gallery wayan, hotunan Hawwa taci karo dasu a gallery, dasauri ta shiga ciki hotunan duka na wayanta
ne wanda ko Hawwa batadasu dan ita ke snapping nata, tun hotunan su na primary and secondary
school, da hotunan datake mata occasionally, da hotuna datama Hawwa adakinta tana sanye da rigan
bacci mai kyau ga boobs nata da sukai showing dasauri takai hannu tai deleting wannan, saikuma
hotunan datagani wayanda Hawwa nafitowa daga gidansu da hotunanta in different places kaman
stalking dinta ma yake yana bibiyanta batare data sani bama ita Hawwan, ganin zuciyanta zai buga yasa
tashiga marking pictures din tai deleting everything ta maida iPad din ta ijiye tana sauke ijiyan zuciya
saikuma tafashe da kuka sosai na tausayin kanta.



Sosai Hawwa ke gudu akan titi da daddaren nan zuciyanta gabaki daya yazo mata wuya, bini bini take
goge hawaye, she can’t even explain d kind of pain datake ciki today has been a bad day for her, daidai
ta shigo kaduna around 12 tayanta ya faci gangarawa gefen hanya tayi kawai tai parking tadaura
hannayenta asaman fuskanta tafashe da kuka sosai tace “Ya Allah maisa ban sami mijiba? Nayi imani da
kaddara mai kyau da mara kyau, I accept whatever you choose for me Ya Allah, ina salla, ina azumi, ina
nafilfilu, ina karatun Al Qur’ani, bantaba fasikanci ba, bantaba shan giya ko wani abu na maye ba, inama
iyayena biyayi, ina taimakon mutane, daidai gwargwado ina bautamaka Allah” cikin murya mai rauni
sosai tace “Ya Allah kaji tausayina kaji Ya Allah, Ya Allah kabani mijina nima, Ya Allah ka kawomin mijina
nima, Ya Allah ka aurar dani da gaggawa banson yanda hankalin Babana yake atashe sabida ni, nazaman
mishi abin kunya, dani ake kwatancen shi, Ya Allah ka tausaya mini kaji” tafashe da kuka sosai she
missed mamanta she missed her, kusan 1hr ita kadai a motan nan babu tsoro ko fargaba aranta koma
yatakama takama din kawai, idanunta a lumshe bawai bacci takeba but jikinta duk ya saki taji ana
bubbuga marfin motanta “Hawwa Hawwa, Hawwa talk to me, Hawwa” kaman ana kiranta daga nesa
hakan yasa tadan bude idanunta kadan, ganin hasken flash na haskota yasa gently tajuyo da rinannun
idanunta ta kallo glass na motan shima ganin haka yasa Baban Yaseer ya haska mata fuskanshi sabida
taga shine, wani irin kafeshi da idanu Hawwa tayi batun yauba taga soyayyanta a idanun Baban Yaseer
but koda mistake bata taba saran zamata bashi chance ba saisa bata cika zuwa gidansu ba saidai ta sami
kawarta awajen aiki kosuyi outing tare, She will never ever betray her friend koda baban Yaseer ne d last
man aduniya, but yau for the first time ganinshi cikin tsakiyan daren nan yazo yabi wannan hanyan
tundaga Abuja yazo nemanta bayan he came to her rescue earlier today yasa ta tsareshi da idanu tana
tambayan zuciyanta could Baban Yaseer be the man she just finished asking God for? Is Allah testing
her? Mijin best friend dinta? She rather hakura da auren gabaki daya aduniya tayi alahira, sosai take
kallonshi hankalinshi amugun tashe yake buga kofan ganin yanda take kallonshi yana Hawwa open,
kusan 2min tadauka tana kallonshi kafin gently ta danna lock motan yayi unlocking kanshi yabude motan
da sauri yaduko yana kawo fuskanshi daidai nata cikeda tsantsan so da kulawa da damuwa yace
“Hauwa’u! Are you okay?” Tsare shi da idanu tayi sai kawai hawaye ya gangaro daga idanunta dasauri
yashiga ciro handky daga aljihunshi jikinsa har rawa yake yace “don’t cry and don’t be afraid I’m right
here, Aliyu is here”.



[9/18, 5:03 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫




✍🏻M SHAKUR




EPISODE
2️⃣
4️⃣ 2️⃣4️⃣



LUKUKU GENERAL ENTERPRISE gidan spices kenan da abubuwa daban daban, babu kalan spices din da
basuda shi, tundagakan su ginger, garlic, tea different kind da sauransu, this is tasted and trusted brand,
chat them up kisai spices now!!!!!
wa.me/+2348095660030



EPISODE
2️⃣
4️⃣ 2️⃣4️⃣




Kawai tausayi taji tabama kanta saisa takasa rike hawayen dan tana cikin jarabawan rayuwa, she’s 30
batai aure ba babu miji, kowa is pressuring her, her biggest support, her biggest fan is her best friend
Ni’ima da tun suna yara suke tare, kawancen amana da iyayensu sun zama daya ma, she’s not a small
girl when she sees love she knows love, wani irin kaddarane wannan? Baban Yaseer can never be her
amsa nooo please Ya Allah not my best friend’s husband, ganin hawaye yakasa tsayawa daga idanunta
asanyaye Aliyu yace “I’m here for you, I will forever be right here! Ina taredake Hawwa in good times
and bad times, dare da rana, I’m right here” ahankali yadaura hanky kan fuskanta wani sanyi taji dayasa
ta lumshe idanunta da sauri takai hannunta i ta karbi handky tana goge fuskanta, tadanja majina dadan
ragowan karfin zuciya tace “maisa kabiyoni Baban Yaseer? Nace kabiyoni ne must u follow me
everywhere? Must you get involved in my issues? An gayamaka I can’t take care of myself ne ko I need
your protection”? Ataushashe yana kallonta ganin ranta abace, cikida zazzafan kauna yace “sabida bazan
taba iya bacci ba bayan nasan kina irin wannan hanyan, I care for you” ahankali Hawwa tace “wat if
something happens to you”? Asanyaye yace “I don’t care koma menene yasameni I just wanna keep u
safe” abu tahadiye a wuyanta sai kawai ta juyo ta yunkuro tace “I need to change my tire, spare tire na
booth” matsamata yayi tafito tai booth yabi bayanta tana bude booth din takai hannunta zata dauki
tayan yarigata dauka yace “let’s go muje motana ki zauna” tsayawa tayi tana kallonshi, “muje dan Allah
Hawwa dare ne mu kadai a titi” batai musu ba yayi wajen motanshi da ita yabude mata gaba ta shiga ta
zauna ya maida yarufe sannan yadawo booth nata yaciro supanu yaje gaban motan yana kwance tayan
dayay less, sosai Hawwa take kallonshi kaman yauta fara ganinshi abubuwa da dama suna yawo aranta,
tana zaune awajen saiga yan sanda sunzo wajen fitowa tayi ta nuna musu ID card dinta tayasu gyara
tayan sukayi, suna gamawa Baban Yaseer yabar musu motanshi yabasu kudi su tsaremai sannan yashiga
na Hawwa, hakan yasa ta zagayo ta zauna ya kunna motan yaja waje tajuyar da kanta tana kallo ahankali
yace “do you think is right kije kidan Anty ki middle of the night? Kodai idan mukaje zaria namiki booking
hotel, idan gari yawaye saikije”? Tana kallon waje batare data juyoba tace “zan iya zuwa wajen Ammi na
anytime anyday” gyadamata kai yayi bai sake magana kusan 30min sai chan yace “Hawwa it’s okay not
to be okay” lumshe idanu tayi tabude anatse yace “you got this! Karki bari kalaman Baba natabaki, karki
karaya, I hate seeing you like this” yadan kalleta yanda take kallon waje yace “kinji” gyadamai kai tayi
daganan basu sake magana ba harsukakai zaria, nunamai hanya tadingayi har zuwa wani gida a wani
anguwa mai dan kyau da mutunci, saukowa tayi ta zagayo tadan kalli Baban Yaseer dake kallonta tace
“dan bani car key” zare key motan yayi yabata yana kallonta, a gate tasaka wani key dake jikin motan
tabude kofan tashiga ciki tana sallama tsakar gida ne mai fadin gaske, tourchlight taga an haskewa taji
muryan yan dattijuwa na “waye awajen gate din nan” ana bude kofa da gudu Hawwa tai wajen kofa
matan na bude kofa dadan charbi a hannu Hawwa ta rungumeta da karfi tace “Ammiiii na” ririketa
matan tayi tace “Hasbunallahu wa ni’imal wakeelu Hawwa kece da daddaren nan, ke tashi kiga na ganki
lafiya Hawwa” tadago Hawwa daga jikinta murmushi Hawwa tayi tace “Ammi baban Naseer na waje
bani key gate na bude ya shigo da mota saiya dan zauna zuwa safiya yakoma Abuja” wani dan kallo
Ammi tamata tace “Baban Yaseer kuma? Aliyun Ni’ima”? Gyadamata kai Hawwa tayi Ammi tabata key
fita tayi Ammi itama tafito tana haskawa bude gate din Hawwa tayi yashigo da motan ta maida gate din
tarufe Ammi tace “maraba da Baban Yaseer, sannunku sauko sauko” Saukowa yayi kanshi akasa cikeda
kunya yace “Ammi mun sameku lpy” cikeda fara’a tace “Alhamdulillah ina jikokina? Da y’ata Ni’ima hope
duk suna lpy”? Akunyace ya gyadamata kai yace “Alhamdulillah” murmushi tayi tace “muje nakaika side
din su Baffa ka kwanta bazakabi hanya da tsakar daren nan ba sai idan Allah ya kaimu da safe akawo
maka abinci ne”? Dasauri yace “a’a Ammi dare nayi bana iya kara cin abinci” satan kallon Hawwa yayi
dake gefen Ammi tana wasa da hannunta yamika mata car key ta yace “take” dan dagokai tayi kafin tasa
hannu ta karba Ammi tace “muje” suka wuce suna hira itakuma tawuce wajen motar ta booth taciro
akwatinta ta gu huri ta shiga dashi ciki, bayin Ammi tafada tana cikin wanka Ammi tashigo tasami waje ta
zauna yanda ta ganta haka tasan dawani abu.

Towel din Ammi ta dauro tafito Ammi ta kalleta tace “zonan Jidda” kayan shafanta tadauka tazo kusada
Ammi ta zauna tana bata cream dinta a hannu Ammi ta karba tana sauke ijiyan zuciya tace “meya faru?”
Dan shiru tayi sabida kawai taji komi yadawo mata sabo, hannunta Ammi takama tana shafa mata mai
kafin takalleta strictly tace “ya akayi kike tare da mijin kawarki at this type of time and day Hauwa’u”?
Baki tabude zatai magana saikuma tadan sauke ijiyan zuciya Ammi tace “speak” anatse tace “Ammi wlh I
don’t know cus ni ko kiran Ni’ima ma banyi da abun yafaru ba, probably Baba ne yakirasu to check ko ina
gidansu, saita kirani daga gayamata ina hanya zanzo wajenki hala to shine ta turoshi” Ammi na kallonta
ta sauke ijiyan zuciya tace “Hawwa babu wani naki dabaisan relationship dinki da Ni’ima ba, yarinyar nan
kawar amana ce, yanda kika daukeni haka tadaukeni, don’t ruin friendship naku under no circumstances,
you know maganan danake” gyadamata kai Hawwa tayi tace “nasani Ammi” saikuma ya tashi daga
gadon ahankali zuwa akwatin nata tadauki dogon riga na bacci tasaka ta zare zanin wankan ta shanya ta
dawo gadon tahau ta daura kanta kan cinyan Ammi tareda sauke ijiyan zuciya tabude watsapp tama
Ni’ima chat “Just got to Ammi’s place, Ni’ima why did you send Baban Yaseer? Why” tura chat din tayi
taga yayi layi biyu alamun datan ta a kunne amman ba’a budeba jira tayi ta amsata but shiru ijiye wayan
tayi ahankali tana lumshe ido kafin kaceme bacci yayi awon gaba da ita dan tagaji yau.

Yanda bacci ya shigeta yasa Ammi bata tadataba ta shiga dakin yammatan ta su biyu Amina da Ramla ta
tadasu don salla itama tayi sannan tasa suka shiga kitchen cus taji Baban Yaseer yafice salla.



Wuraren 7 yashigo gidan a tsakar gida yaga Ammi tareda Ramla datake gwadama yanda ake buga kosai
sun hada gawayi dan basu soya kosai a gas, ganinshi yasa Ramla tace “ina kwana Baban Yaseer”
murmushi yamata yace “lpy lau” yace “ina kwana Ammi” murmushi tamai tace “an tashi lpy sannu da
kokari fa Aliyu, Allah ya maka albarka, bari yanzun nan zan kawoma kosai nariga an dama kamu saina
kawoma kayi karo kafin kashiga hanya” girgixakai yayi yace “no Ammi bazanyi kari ba bana kari da wuri
yan sanda na barma motana chan hanyan kaduna dole nafita yanzu Ammi” yayi maganan yana ciro kudi
daga aljihunsa daya samo a ATM fitan nan nasa a kujeran tsakar gida dake gefen Ammi ya ijiye kudin
yace “aba Hawwa idan ta tashi, wannan kuma aba su mai girki” cus baisan sunan Ramla ba, hade fuska
Ammi tayi tace “kaga dauki kudaden nan karna saba maka Baban Yaseer” dasauri yajuya yayi gate yace
“Ammi nagode” yafice dasauri dudda har ranshi yaso yaga Hawwa kuma sarai ta tashi tun dazu har salla
ma tayi kawai bataso ta ganshi ne kawai yasa bata fitoba, tanajin fitanshi tafito falo Amina dake gyaran
falo na ganinta tai ihu sosai “Ramla Ya Hawwa ta tashi” tawani zo dagudu tai tsalle tafada jikinta Hawwa
tai dariya sosai Ramla tasaki kosan datake ta rugo dakin aguje itama tai tsalle kawai Hawwa tai kasa suna
kanta, Ammi ta shigo dakin ta kwadamusu duka abaya tace “Oya ku dagamin ita bance ku karyamin diya
ba” kankamesu Hawwa tayi tace “Ammi I missed my babies” hararansu Ammi tayi tawucewarta tafito
tashiga soya kosan da kanta tunda taga shirme suke Hawwa tafito tareda su tana Ammi wai ina su
Hamza da Ahmadu? “Hamza na school, Ahmadu yace anjima zaizo da matarsa su gaidake, Baffan ku na
dayan gidan sai gobe zai dawo nan amman hala anjima ki gansa” murmushi tayi ta karbi kosan tana
soyawa su Ramla nabata labari she looks so happy Ammi tayi murmushi ganin ayanda idanunta sukadan
kumbura jiya sabida kuka sun sauka sosai yanzu kaman batayiba.




Wuraren 12 Ni’ima taji ana bude gate, tunda tasan Hawwa bata taba taga miss call na Hawwa taki
kiranta back ba sai yau, nor tai replying message nata, jiya tamata message shiru, da safen nan takirata
sau biyu ba amsa sai tamata magana tace “call me idan kin dawo daga hospital Best, su Ramla nata
tambayanki”.



Jin ana

Please Login or Register in order to submit comment