Reading Gargada So By m Shakur Chapter 19 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki, Baba yayi shiru
saikuma yakalli Mama yace “Maimuna dubeni nan, ni ubane kaman yanda kike mahaifiya, hakkine
akanmu idan mukaga abinda zai cutar da yaranmu mu kauda abubuwan daga hanya” Baba yayi shiru
yana lumshe idanu yana tuna yanda Ni’ima take ikirarin kashe Hawwa yace “idan Hawwa zata yafema
Ni’ima bazan taba hanata ba amman idan Hawwa zata dawo da Ni’ima rayuwanta saina hanata!”Faduwa
gaban Mama yayi dasauri takalli Baba bakinta tafara rawa, Baba yadan kada kafa yace “wato Maimuna
jiya na karanci abubuwa da dama akan idanun Ni’ima, tundaga kissan data dinga ikirari zatama Hawwa,
da fatan mutuwa data dinga mata, da yanda dudda mijin natane mai laifi ina shiyabi Hawwa? Shi yake
sonta Hawwa bata sonshi amman batai kan mijinta ba kan Hawwa tayi, ga diyata agadon asibiti rai
hannun Allah Ni’ima bataji tausayin ta ba karasata takeso tayi” yayi jimm yace “Maimuna ansan mata da
kishi amman naga ko kishiyan ka ce take gadon asibiti zakadan tausaya karage wani abun” Dasauri
Mama tace “Malam kishi kala kala ne, akwai masu zafin kishi kafahimta” adan zafafe Baba yace
“Maimuna fahimtan danayi yasa nike miki bayanin nan, koda yaran nan sun shirya madaman Aliyu na
kaunar Hawwa Ni’ima bazata taba kaunar Hawwa ba duk karyace! Ni’ima tariga ta tsani Hawwa! Naga
kiyayya a idanunta kibar maganan nan kawai!”.

Mshakur🥰

[9/28,
2️⃣ 8:18 AM] +234 806 486 0007: EPISODE 4️⃣2️⃣
4️⃣
Rasa tacewa Mama tayi amman taki giving up ina sai inda karfinta yakare kawancen nan saisun dawo
dashi, ijiyan zuciya Mama ta sauke tace “Malam duk naji bayaninka kuma banki ba hujjujinka masu karfi
ne, konine naga wacce ke shirin cutar da yarana zan dakatar, amman kuma ka kalli abin ta wannan
fuskan mana, ina duk ba Aliyu ne sanadi, dalili, da haddasanan fadan ba? Malam ai komi yakare yanzu,
Hawwa tayi aure, babu sauran fada kuma” Baba yayi murmushi irin na manya yace “ke mace ce
Maimuna bazaki taba gane yanda zuciyan maza yakeba, idan namiji ya daurama kansa soyayyan wata
har abada soyayyan nan baya fita daga ransa, daukeni a misali har gobe ina matukar kaunar marigayiya
mahaifiyar Hawwa, shi son gaskiya baya mutuwa, inhar Ni’ima natare da Hawwa dole zata dinga ganin
dabi’u wajen mijin nata dazai dinga konamata rai daganan kishi ya motsa afara tunanin illata wani ko
kisan kai, maganin kar ayi karma afara naga Ni’ima, Ni’ima taganni, ayayyafe amman adawo tare ban
aminta ba, kawai ahakura Aliyu yariga yabata komi, Hawwa takamu da hawan jini hakkinane na kareta
gwara ta nisanci mutanen da zasu bata matsala arayuwanta wato Ni’ima da Aliyu dan haka kiyakuri
kawai Maimuna, ahakura da kawancen tunda yazo irin gabar nan, zanje nayi kari daganan naje asibiti”
yayi maganan yana mikewa bayason zancen bakaramin daurewa yayi yamata maganan hankaliba
amman ya tsani Ni’ima da dabi’un datayi, yarinyar ta basa tsoro baitaba sanın haka Ni’ima take ba, tashi
Mama tayi dasauri tace “dan Allah Malam ayakuri, Malam kabar yaran nan sudawo tare sunason
junansu Malam” dakin Umma Baba yafada Umma ta watsama Mama harara dan basa shiri sabida uwar
kawar Hawwa ce rai ba dadi Mama tawuce tabar gidan.



Kari Baba yayi tareda Ramla sannan ta shirya suka fito tare wajajen 11 daidai motar Baban Yaseer na
parking Baba ya tsaya turus yace “je gida Ramla natashi tafiya saina kiraki” komawa ciki tayi, Baban
Yaseer yafito yazo wajen Baba cikeda mutunci suka gaisa Baba ya zauna kan kujera shikuma ya zauna a
tabarma yadan sosa kai yace “Baba zan fara da baka hakuri bisa ga abinda yafaru jiya, Baba kayakuri
yawancin maganganun da Ni’ima tayi na tabbatar cewa karya tama Hawwa, kowa yasan hakan ba halin
Hawwa bane, Baba dan Allah kayakuri” murmushi Baba yayi yace “bakomi nahakura komi yawuce” ijiyan
zuciya yasauke yace “saikuma ahhhhhmmm” yadanyi shiru yana sosa kai Baba yace “ina jinka” kanshi ya
sauke kasa yace “Baba inaso kabani daman auren Hawwa! Baba ina matukar son Hawwa, namaka
alkawari Baba zan kula da ita nakuma riketa amana Baba, Baba dan Allah dabi’un Niima kada su sa ka ki
bani wlh Baba zan kula da Hawwa namaka alkawari babu abinda Ni’ima zata iya mata”

Ijiyan zuciya Babayasauke anatse yace “Aliyu” dagokai Aliyu yayi yakalli Baba yace “Na’am Baba” Baba
yayi murmushi yace “Aliyu kai d’a nagari ne da babu iyayen dabazasuyi alfaharin samunka amatsayin d’a
ba, Kanada hankali natsuwa da kirki babu wanda bazaiso yahada zumunci dakaiba” yayi shiru chan yace
“Allah yana jarabtanmu da abubuwa da dama, wani zubin yana nunamana duk yanda mukakai ga son
abu bamu samuba sabida banamu bane” faduwa kawai gaban Aliyu keyi Baba yace “ina sonka Aliyu sosai
amman y’ata Hawwa bataka bace, jiya nadaurama Hawwa aure da Ibrahima, Hawwa tariga tazama
matar wani!” Faduwa gaban Aliyu yayi dasauri yakalli Bab idanunshi har twitching suke sabida bugawan
kirji yama kasa magana Baba ya lumshe idanu yabude, Baba yace “kayakuri Hawwa tayi aure, inaso
kaima kaje ka gyara rayuwanku da Ni’ima, ku daidaita kanku, ku shirya ku kula da yaranku, yanzu Hawwa
tafita daga tsakiya, babu wani abu dazai kara jawo muku fada, inaso naga ka koma yanda kake d’a da
Ni’ima gwanin ban sha’awa, ku manta da komi acigaba da rayuwa anama juna fatan alkhairi kaji
Aliyu”baki Aliyu yabude zaiyi magana saiga hawaye mai zafi sun sauko daga idanunshi dasauri yakai
hannu ya share yajuyar da kai yana huci zuciyanshi na kuna yanason Hawwa sama da tunanin kanshi,
waye Ibrahima? Yaushe Hawwa ta sansa? Ko sanarwan da Baba yayi sanarwa a masallaci ne yasa aka
samo Ibrahima? Zafi yaji ranshi namai hawaye suka kara zubowa ya share da sauri still yakasa magana,
ba karamin tausayi yabama Baba ba, kana gani kasan Aliyu na son Hawwa sosai, ahankali yace “kayakuri
Aliyu, nasan yanda so yake, baya neman shawara idan zai kamaka, amman kayakuri, ka rungumi
kaddara, ka gyara aurenku da Ni’ima ka rungumi iyalinka kaji” gyadama Baba kai yayi yakasa motsi Baba
yayi shiru yana kallonshi yakai kusan 20min ahaka sannan yatashi muryanahi narawa sosai kaman zai
fashe da kuka yace “natafi Baba” Baba ya gyadamai kai duk jikinshi yayi sanyi but this is the right thing,
yawuce yatafi Baba shima yayi shiru, saida yaga barinshi unguwan ya kwalama Ramla kira suka tafi
abinsu.



Da kyar cikin ikon Allah Baban Yaseer yakai gida gateman dinsu na gaidashi ko iya amsawa baiyiba
yawuce yabude flat nasu yashiga yashiga bedroom nasu yazauna yafara fuzar da iska da baki sosai,
hawaye masu dumi suka shiga zubomai yasan da Ni’ima duk batai haukan nan ba wlh Baba zai iya bashi
Hawwa, yanzu ga shi Baba yaki, yasan rigiman Ni’ima yasa Baba yaji gwara ya aurar da Hawwa ga
kowama ko wutan da Ni’ima ta kunna tamutu, iska yakara fuzarwa hawaye masu zafi suka zubomai
baitaba sani rana zaizo dazaiji yanajin tsanan Ni’ima ba sai yau jiyayi ya tsaneta completely, bazaima so
yaganta ba ko ya kalleta sai iya shaketa, yana ahaka wayanshi yahau ringing share fuskanshi yayi ya daga
wayan Ni’ima yagani na kiranshi harta katse wayan bai daukaba tanamai kira na biyar ya daga yakai
kunne baiyi magana ba, murya chan kasa tace “Baban Yaseer dama nakira nacemaka kayakuri ne da duk
abubuwan dana maka natuba dan Allah let’s forget the past and move on for the sake of yaranmu” Wani
kaluluwan abu Baban Yaseer yaji yana tasomai yana zuwa wuya Ni’ima tace “Babyna kaji nasan bazaka
iya fushi dani for long ba please kayakuri” kasa rike abun dake wuyan nashi yayi cikin tsantsan tsana
yace “bazan taba dawo dake ba, and for yarana ko da ke ko bake zasu rayu, na tsaneki Ni’ima na tsaneki
da ko muryanki banso na sake ji, I hate you with everything in me, na tsaneki” yazare wayan ya katse ya
jefar yazauna akasa yana dafe kanshi yashiga kurma ihu sosai kaman mahaukaci he’s so heartbroken,
gateman yazo yana buga kofansu yana “Alhaji lafiya, Alhaji Alhaji”.



[9/28,
3️⃣ 8:18 AM] +234 806 486 0007: EPISODE 4️⃣3️⃣
4️⃣
Ammi na zaune wuraren 11 tana duba wani littafin azkar while Hawwa na bacci sosai mai nauyin gaske
taji kamshi ya daki hancinta mai dadi har saida tadago kanta ta kallo kofa Khaleel ta hango jikin kofan
dago kan datayi yasa ya matsa da sauri gefe, shiru Ammi tayi saikuma ta kalli Hawwa dake bacci mai
nauyi massage din yamata dadi ga drip ana samata ta lullube mata tundaga ciki har kafafu da bargo daga
cikinta zuwa kai abude kanta babu dankwali tayi kyau sosai, she’s sure shine yaron jiya shine mijin
Hawwa kunya yakeji ne kome? Lallai yaron kam akwai kunya yana abu saikace barawo, Ammi tayi
murmushi tana tashi ta taho wajen kofan tabude tafito, Khaleel na tsaye jikin kofan yana sanye da riga
da wando masu kyau milk adan hankali yace “good good morning Mom” saikuma yajuya zai tafi dasauri
batare daya jira amsan Ammi ba, ahankali Ammi tace “Ibrahim” chak ya tsaya yadan juyo kanshi akasa,
dan murmushi kadan tayi tace “bazaka duba matar taka ba? Dan zauna da ita nima kafafuna sunyi tsami
bari nadanyi tafiya cikin asibitin kadan” kafin yayi magana ta wuce yabi Ammi da kallo saida yaga tafice
sannan yajuyo ya kalli dakin kafin ahankali yabude kofan ya shiga maida kofan yayi yarufe ya tsaya jikin
kofan yana kallon Hawwa dake bacci mai nauyi hakanan kawai yaji kirjinshi na bugawa sosai dum dum
dum! Gently yadaga kafanshi yataka zuwa gaban gadon ya tsaya tareda folding hannu a kirji yana
kallonta, she looks very sick and beautiful a hospital gown din, har lokacin akwai bandage a goshinta but
an cire na hannuwanta ga ciwuka a hannu, ahankali yadaga hannunshi yakai gently yadaura kan left
hand dinta wani kalan shock yaji baisan sanda yarike hannun gam ba tareda sauke ijiyan zuciya sannan
ahankali yakai yatsanshi yana shafa ciwon hannun wanda yasan Ni’ima ne tamata cus yana mota data
tattake mata hannu haka murya chan kasa yace “why will you love a girl this much?” Yabi hannun da
kallo that felts super soft kaman hannun little Noor ga nails nata so long and white and clean looks so
sexy, mirginowa Hawwa tayi kanta zai fadi daga filo dasauri yakai hannunshi yatare fuskanta yafado cikin
palm dinshi tana sauke ijiyan zuciya daya huro a hand nashi cikin muryan bacci tace “Ammiiii” wani irin
lankwasa kai Khaleel yayi yana kallon fuskanta dake cikin hannunshi

Her face is so damn soft, baitabajin wani excitement dan mace ta shiga jikinshi ba but right now he’s
feeling so good, tsareta da idanu yayi yana kallonta ya duko a tsaye fuskanta na cikin hannunshi, kaman
mai whispering yace “Hawwah!” Kar Hawwa tabude idanunta saida gabanshi yayi wani mummunan
faduwa yanda take kallonshi da very very bright eyes saikuma tamaida idanun tashiga kullewa suna
juyawa, muryan Baba yaji awaje dawani kalan sauri yazare hannunshi fuskan Hawwa ya kife anan kasan
filo daidai Baba na bugo sallama yana shigowa tareda Ammi da Ramla dakuma wasu mata guda uku,
biyu daga cikinsu goye da yara abaya daya babu yaro abayanta somehow somehow they look like Baba,
Ammi ta wuce tana gyara fuskanta, Baba yace “Ibrahima kana nan? Ka kannin matarka Hawwa ku gaisa
Khadija” Babban wacce ita kebin Aminu Khadija tace “ina yini Yaya Ibrahim” akunyace Khaleel ya
gyadamata kai, Hafsa tace “ina yini Ya Ibrahim yamai jiki” Maryam tace “ina yini ya Ibrahim” Ramla
itama tace “Ya Ibrahim ya jikin Ya Hawwa” kaman bai iya magana baisaba da mutane haka ba ana
kiranshi Yaya Yaya yace “da…da sauki” yakalli Baba akunyace yace “Baba zan tafi zan dawo anjima” Baba
yace “muje na takamaka” shida Baba suka wuce suka fita suna fita Khadija da Hafsat da Maryam da
Ramla suka shiga tafi saikuma sukahau rawa, Hafsa tace “wlh mijin Ya Hawwa yahadu Wayyoo Allah na
I’m so happy for Yaya Hawwa” Ammi tace “kunga karku tadamin yarinya da surutu” duk dariya sukayi
sukahau hira.
Around 4 DIG yazo hospital din tareda Abraham da Hayatu Baba yamusu iso suka gaisa sosai, suka ijiye
kudi da basket na so many goodies sannan sukama Baba sallama suka tafi.



Shima Aminu around 4 yashigo asibitin Baba yadingamai fada akanme zaibar school yazo….



Wuraren 7 Khaleel yashigo asibitin Salman na binshi da shopping na kayan kwadayi daban daban yarike
hannun Noor data isheshi da maganan Hawwa ga teddy a hannunta looking so pretty sukai ciki, tundaga
glass na kofan ya hango Hawwa zaune kan gado an ijiyemata table da abinci daban daban kekai Ammi na
kaimata abinci abaki tana kaudakai tana yatsine fuska idanunta sun kumbura na kuka da bacci, ga Baba
shima tsaye kansu suna fama dataci abinci murya chan kasa Khaleel yace “she’s such a child” dasauri
Noor tace “Daddy mekace?” Kallon Noor yayi baiyi magana ba tace “Daddy let’s go inside I want to see
FAA” dan ijiyan zuciya ya sauke yasa hannu yayi knocking tareda bude kofan Noor tasaki hannunshi tai
ciki da gudu tace “My Fairy Angel Anty” Hawwa tadan bude idanu tana kallonta kawai Noor tahau gadon
ta gefen Ammi ta tattaka tafada jikin Hawwa ta rungumeta tsamtsam da karfi Hawwa itama ta
rungumeta yarinyar is freaking cute and adorable.

Baba yace “Ibrahima shigo ga wuri” yabashi plastic chair shi Baba yakoma kan dogon kujera ya sauna su
Salman suna shigo suna ijiye jakunkuna suka fice ahankali Khaleel yace “ina yini Mom” murmushi Ammi
tamai tace lafiya lau Ibrahim, aran Hawwa tace “Ammi na ne Mom” da sick eyes tadan kalleshi tana
rungume da Noor tana mamakin meya kawo dan iskan yaron nan asibitin nan taki gaidashi, tasowa daga
jikinta Noor tayi tace “FAA ya jiki? That day of accident my Dady was taking me to school I saw wat you
were doing” Noor tashiga gwadama Hawwa, tace “I told my Dady, Dady yafita yadinga bin car naki da
gudu he removed you from the car you were biting my Dady hand” tanuna hannun Khaleel dake zaune
da sauri yajuyar da hannunshi Baba yace “aiko naga ciwon dama Hawwa ce ta jimaka?” Kin magana
Khaleel yayi, Noor tace “we brought you here FAA are you fine now? U will not fall sick again ko?”
Gyadamata kai Hawwa tayi ahankali tace “yes” dasauri Noor ta rungumeta tace “I love you FAA” tashi
Baba yayi cikeda hikima yace “bari na karbi sako wajen mai keke” Dasauri Ammi ta tashi tace “muje na
bika nafadamai abinda zai fadama Ramla” kawai suka fice.



Itama Noor dasauri tasaki Hawwa ta sauko daga gadon tai wajen Khaleel dake kallonta tace “Dady I
forgot my second teddy in car I brought it for FAA” ahankali yace “meet Salman to take you” dasauri tai
wajen kofa tajuyo takalli Hawwa dake binta da kallo tace “FAA I’m coming” Gyadamata kai Hawwa tayi
tawuce tafita dakin yarage daga Hawwa sai shi, kafa daya yadaga yadaura kan daya yayi shiru yana
kallonta, yanda Hawwa taji ajikinta ana kallonta yasa tadan juyo ta kalleshi hada ido sukayi zata ballamai
harara komi daya mata nadawo mata arai, da yanda yayi attempting tabata but yanda taji shiya ceceta,
plus dazu Baba nata cewa Ibrahima yakawota asibiti yabiya kudin komi da motocin data bata yasa softly
da dan kyar tace “thanks” tadanyi shiru ta dai daure tasaki muryanta tace “thank you for saving my life”
tasakeyin shiru ahankali tace “once nakoma aiki i will find a way to pay you back every penny daka
kashe” tasakeyin shiru chan tace “all this daka kawo kasa atafi dasu banso, i hate favors barinma na
mutane like you! So I will pay back everything” Murmushi kadan yayi batare dayayi magana ba wato
tana sick bed still masifa take, Noor tadawo dakin ta tafi wajenta da sauri tabata teddy tace “FAA take,
Dady said you will soon move to our house kikazo i will give you more and more teddy kinji” dan
murmushi kadan Hawwa tamata tace “thank you beautiful Noor” tana mamaki uban me zai sake kaita
gidansu dayake gayama yarsa zata” kusan 10mins yayi sannan yakalli Noor daketa zuba yace “let’s go”
kiss ta manna ma Hawea tace “bye FAA” murmushi sosai Hawwa tayi tace “bye Noori” wucewa tayi
wajen Khaleel yarike mata hannu sukai wajen kofa hakanan Hawwa samin kanta da kallonshi tayi, the
way he walks, he way he held Noor’s hand, everything looks soo….ta tsaida tunanin, saida yakai daidai
kofa ya tsaya Noor ta fita dan juyo da kanshi yayi karaf suka hada ido dasauri Hawwa ta dauke kanta,
cikin dan iskan murya Khaleel yace “see you soon cry cry Kulu” dawani irin sauri Hawwa tajuyo ta
kalleshi kaman zakanya, gira daya yadaga mata yace “see you very very soon Kululu” kawai yasa kai
yafice daga dakin Hawwa tawani yunkuro tace “sunana Hawwa not Kulu or kulul whatever” Khaleel na
jinta yayi murmushi yawuce abinsa.

[9/28,
4️⃣ 8:18 AM] +234 806 486 0007: EPISODE 4️⃣4️⃣
4️⃣




Yau Hawwa ta tashi da karfinta sosai tun asuba Dr yazo yace “za’a sallameta yau but sai Ogansu Mai
asibitin yazo” aka ciremata bandage na goshi da hannuwa ciwukan sun warke tanada jiki mai kyau sosai,
wanka tayi tasa wani simple gown da aka kawo mata na atampa red dayamata kyau sosai, ta rame
idanunta kana gani zai nuna maka tayi ciwo but takara kyau skin nata sai glowing yake na drip datasha,
tun wajajen 7 Aminu yazo dan daga masallaci yazo basai Baba yazo ba daya shigo dakin Ammi bata ciki
taje karbo magunguna daga pharmacy sai Hawwa dake zaune ta kishingida hannunta rikeda wayanta
tana dannawa tana replying messages na DIG dasu Hayatu, ganinshi yasa ta dago kanta dasauri yayi
wajen gadon yana murmushi yace “ya karfin jiki Ya Hawwa?” Murmushi kadan tamai tace “Alhamdulillah
I’m fine yaushe zaka koma school why did you even come back”? Zama yayi gefenta yace “yayata that is
the strongest person I know a duniyan nan tana rashin lafiya why won’t I come?” Shiru Hawwa tayi tana
kallonshi tadan harareshi kadan tace “mutum sai dadin baki” dan dariya yayi yace “Ya Hawwa nasha
fruits dinnan”? Gyadamai kai tayi yadauka da sauri yana sha Ammi tashigo tace “Aminu jinya kazo ko cin
dadi jiyafa haka komi kuka raba naka yamafi na su Khadija” murmushi yayi yace “Ammi to nine babba”
hararanshi Ammi tayi ta ijiye magungunan tace “maza gamaci mu hada komi Dr na zuwa za’a sallamemu
wai” tai maganan tana mikawa Hawwa red veil nata Hawwa tasa hannu ta karba tayafa saman kanta
daba dankwali, duk suna zaune har wajajen 9 wayan Hawwa dake hannun Aminu yana connecting
hotspot nata danashi yahau ringing dasauri yabata wayan yace “Abraham office” hannu tasa ta karba
tana kwanciya ta danna wayan tana sawa a speaker daidai lokacin ana knocking tareda turo kofan
Abraham yace “Hello Miss Hawwa how are you feeling” magana kasa fita yayi daga bakin Hawwa sabida
Khaleel data gani ya shigo yana sanye da labcoat ajikinshi an rubuta Dr Khaleel Mangal, ga stethoscope a
wuyanshi hannunshi rike da file na Hawwa dakuma office pad da pen idanunshi kyar akanta ga Dr daya
saba duba Hawwan tareda shi sai Nurses guda uku daidai Abraham yasake cewa “Hello Hawwa are you
there?” Firgigit Hawwa tadan farga daga kallon Khaleel, adan rude tace “uhn” Aminu yasauka dagakan
gadon cikeda murmushi yace “sannunku ina kwnan ku” gyadamai kai Khaleel yayi kanshi akasa yace
“good morning Mom” kafin ta amsa yayi wajen gadon daidai lokacin Abraham yace “huhh wat a relief!
I’m so glad you’re okay I’ve been so worri……” wayan Khaleel yasa hannu ya dauka tareda katsewa
Aminu yadaura hannu a bakinshi yana makale dariya Ammi tadanyi murmushi kadan tace “muje waje
Aminu” suka wuce suka fita, wani kalan kallo Hawwa tama Khaleel irin who gave you the authority to
end my call amman mutanen data gani wajen yasa tadaure tadauke kai batai magana ba, professionally
Khaleel yace “can I have your hand Mrs Lee?” Wani kallo Hawwa tamai shekeke irin is something wrong
with this guys head, dayan Dr yace “Dr Khaleel she’s the patient I consulted you for kace nakara mata
dosage na wannan medication din nan and BP ya sauka sosai” “hand” Khaleel yafadi fuska ahade har
wani daci daci Hawwa keji abakinta yanda zata bama dan iskan nan hannu da kyar kaman ta kurma ihu
ta bashi hannun tadauke kai tana kallon gefe, daura mata abun auna BP Khaleel yashiga yi sannan ya
makala stethoscope a kunne da gangan yawani zauna abakin gadon yana facing nata arude tajuyo zatai
magana yace “shiii idan ana auna BP ba’a magana” hadiye maganan Hawwa tayi wannan wani irin
mutum ne, pulse nata da heartbeat ya saurara sannan ya zare stethoscope din yakalli Dr yace “she’s
good” yakalli Hawwa yace “any complain Mrs Lee”? Dauke Kai tayi tareda girgiza mai kai bataso ta
disgashi gaban abokan aikinshi ganin he’s not jobless ashema yayi school, gyadakai Khaleel yayi yace “in
that case I can discharge you” yashiga rubuce rubuce a iPad din da pen sannan yabama Dr yace “zaku iya
tafiya” wucewa sukayi suka fice saida Hawwa taji an rufe kofan sannan tajuyo hada idanu sukayi yana
mata dan iskan kallo azuciye tace “katashi daga kusadani” cikeda kakkausan murya yace “anki” iyyee
wow just wow irin kallon da Hawwa kemai kenan ganin karfin halinshi, rage murya sosai yayi yace “idan
kika kara kuka kika sa kanki damuwa BP ki yatashi sabida that mad, crazy, babaric woman of yours mai
kama da gumakan Egypt mesuem I will reap your heart off your chest kimutu gabaki daya nayi donating
all organs naki to mabukata, starting from heart, liver, kidneys with this eyes etc” wani irin kallo Hawwa
kemai baki bude ikon Allah, tadaure tarufe bakin tace “you’re nobody in my life dazakamin detecting
what I should do and what I shouldn’t, you’re nobody to me Pops boy!” the way she talks shit! he can’t
even explain but he enjoys it, dan matso da fuskanshi dab da nata yayi dasauri takoma baya gabanta na
faduwa sanin su Ammi na waje tace “me..me….mehaka?” Ahankali Khaleel yace “I want to actually
shows you who I’m in your life” dasauri yakawo fuskanshi kaman zai mata kiss Hawwa batasan sanda ta
mika duka hannayenta biyu ta daura a kirjinshi ba hakan yasa ya tsaya chak kirjinshi ya buga dum!
Hawwa tace “is this abinda ku kema patient naku a hospital dinnan? I will sue you Allah” dan murmushi
yayi cikeda tsokana yace “koni i will sue you for touching my chest, index finger naki on my breast kina
tabawa!” Abala’in haukacewan sauri Hawwa ta janye hannunta dagakan kirjinshi jikinta yahau rawa
tama kasa magana, she just hates dan iskan yaron nan, did he say breast uban wani breast zata taba
ajikinshi? Murya chan chan kasa Khaleel yace “do you have crush on me? Cus you were trying to take
advantage of your handsome Dr duk kin gama mammatse mini this” yataba nonuwansa yana mata very
cute smile da white hakoranshi ke showing yamata wani irin kyau a idanu.
[9/29,
8️⃣ 3:42 PM] +234 806 486 0007: EPISODE 4️⃣8️⃣
4️⃣




Gidan Mama

Jin parking mota a kofar gida yasa Mama dake kokarin shanya zani a igiya tace “waye yazo duka duka ko
awa daya cikakke Ni’ima batayi da fita ba yo ko Aliyu ne”? Tana fadin haka tacire hannunta daga kan
zanin datake kokarin shanyawa daga igiya tai wajen gate din nasu tana kokarin bude kofan aka turo
Ni’ima ke shigowa ga fararen uniform nata ajikinta sai abaya asama dayake abude, ga wani katon
envelope a hannunta sai jaka da wayanta da car key a hannunta idanunta sunyi jajir ga ruwa ruwa ma
kaman tai kuka, faduwa gaban Mama yayi rass dasauri tace “lafiya naganki gida? Bayanzunan kika tafi
aiki ba sai dare zaki dawo? Yanaga kaman kinyi kuka Meya faru”? Envelope din hannunta tadaura akan
hannun Mama tawuce tazauna gaban dakalin dakinsu kawai tafashe da kuka mai ciwo da zafi, Mama ta
kalleta saikuma hannunta yashiga rawa sosai ta bude envelope din da sauri ta zaro paper ciki ta yarda
envelope din akasa ta iya karatu tadanyi makaranta bakinta har rawa yake tace “lICENCE REVOKED
LETTER FRON NMCN” takasa karanta surutun data gani sai kawai ta taho wajen Ni’ima tace “ke meke
faruwa fadamin bazan iya karatun nan ba tell me” da kyar harshenta har karyewa yake tace “NMCN
shine Nurses and midwifery council of Nigeria, sune suka aikomin da letter nan ta asibitin mu wai
Leadway hospital sun turamusu video evidence of ni Nurse Ni’ima nazo hospital ina threatening patient
nasu da murder, they saw everything a video, and I’ve caused lot of unrest among other patients, some
even had panic attack due to tantrums dina, so according to code of conduct Nurses represent life,
hope, not threat and fear, plus attempt murder danayi dan haka sunyi revoking licence dina” bakin
Mama bari yashiga yi sosai tace “m….me….menene revoking license Ni’ima? Yimin bayani dalla dalla ke”
fashewa da kuka sosai Ni’ima tayi mai ciwo, cikin kukan tace “Mama revoking license yana nufin bazan
kara iya practicing nursing a any government hospital ko any accredited private hospital ba, Mama infact
any registered hospital bazan taba ita aiki dasu ba saidai irin banzayen local quack hospital wanda
gwamnati batasan dasu ba ko da zamansu, kuma till further notice sukace babuma ranan dawomin da
licence dina, asibitin mu kuma they fire me wai zan bata musu suna” hannu Mama tadaura aka tana
kallon Ni’ima data fashe da kuka sosai cus she love her job tanason nursing, it has always been her
dream to become a nurse, so taking her license jitayi kaman batada wani purpose kuma, kaman part of
her is gone” share hawaye tayi tana huci tace “Mama kuma duk sabida Hawwa ne, nasan ita tasa

Please Login or Register in order to submit comment