Reading Gargada So By m Shakur Chapter 22 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

feel free ni da ke are one
kinji Best” hannunta Hawwa ta kalla saikuma tadauki paper bag din tana dubaw,a Ni’ima na kallon jakan
Hawwa tashiga ciro abubuwan ciki tana neman wayanta, wasu expensive designers perfumes ne sai box
na polo diamond watch da another box na LV brackets sai kuma cute note, ganin bataga wayanta ba
yasa tace “Innalillahi na manta ban karbi wayana daga hannunsa ba” abu Ni’ima ta danne dataji ya
tsayamata a kirji tace “wane?” Yatsine fuska Hawwa tayi kadan tace “Khaleel” murmushin dole Ni’ima
tayi tace “ohh wai mijinki, shiya baki gifts haka”? Gyadamata kai Hawwa tayi not paying attention to her
sabida yanda taji ranta yabaci yagama tabata yatafi da wayanta, hannu Ni’ima tasa tadauki note din ita
adole sun dawo kaman da tace “read note daya miki mana bari na karanta miki” tai murmushi tace
“yarubuta my first gift with love to Mrs Lee Kulu Yar Sanda” dan tsaki Hawwa taja tace “dan rainin
wayau” Ni’ima tace “he’s so romantic gurl common ina kukaje”? “Hawwa!” Ammi ta kwalamata kira
dayasa Ni’ima ta tashi dasauri tace “bari natafi har yanzu Ammi fushi take dani gobe zanzo maybe by
then yakawo miki wayan sai mu kirashi”gyadamata kai Hawwa tayi ahankali tace “take care” Ni’ima tace
“I love you Best” baki Hawwa tabude zatace love you too kaman yanda sukeyi da saita kasa furtawa
murmushi tamata ahankali mai taushi tace “thank you agaida Mama” juyawa Ni’ima tayi tayi zaure tana
tafiya ahankali hoping Hawwa zata kirata ko agogon nan ne tabata amman taji shiru tace shikenan
Hawwa ta chanza ba haka Hawwa takeba da ba, ko waya Hawa tasaya zata iya sadaukar mata amman
yau ko kudin ma datace batada su Hawwa bata bataba, ga gifts tagani but Hawwa couldn’t give her a
thing.
Komi Hawwa ta kwasa ta shiga daki da sallama Ammi ta kalli Ramla tace “fita zanyi magana da Yayarki”
fita Ramla tayi ganin yanda ran Ammi yabaci tana fita Hawwa tayi wajen Ammi dasauri tace “Ammi dan
Allah kiyakuri yazanyi I have to talk to her amman naji maganan ki bazan maida ita kawata kaman d’a
ba!” Kabar da hannunta Ammi tayi daga jikinta cikin tsananin fushi tace “you are very very very stupid
Hawwa!”Dasauri Hawwa ta kalli Ammi dan bata taba zaginta ba, rai abace Ammi tanuna kanta tace “is
something wrong with your brain? I expected you kice kinji kin yafe let’s end things kaman yanda ita tai
initiating at first ki sallameta but kin tsaya kina hugging Ni’ima are you mad?” Baki Hawwa tabude tace
“Ammi wlh bah……” “yimin shiru!” Ammi tafadi tana mata ihu, Hawwa tayi shiru tasauke kanta kasa
Ammi tace “imagine kun fita keda mijinki yabaki gifts wannan kawar kike nunamawa har tana tayaki
karanta note din da mijinki yarubata miki, you are telling her zaki ma Oganki magana kan licence dinta,
zaki tayata kiran Baban Yaseer what is your business with Ni’ima and her affairs sai Ni’ima ta kasheki
zakisan ta tsaneki ba kawar arziki bace?”

Ammi tai ihu she don’t care at this point uban kowa yaji Baba yashigo dakin yace “da kyau Zainabu
wanke miki ita tunda kunnen kashi gareta” Ammi tace “Uwarki ce Ni’ima ko ubanki da bazaki iya hakura
da ita ba can’t you leave with out her? Wlh kika kira Baban Yaseer kokikai magana kan licence dinta
sainayi mummunan saba miki, Hawwa kika kara jawo Ni’ima jikinki wlh saina zame hannuna a lamarunku
tunda ke kinsaka differentiating good people from bad, you’re a criminologist but kin kasa karantan
Ni’ima kisan criminal ce ita all she’s doing dake is friends with benefit bata taba sonki ba, yau tazo
wajenki sabida tasan u might be able to get her licence back for her, tasan mijinta na sonki kina karansa
kika cemai yadawo da Ita zai dawo da ita, this gurl has been benefiting from you right from day one,
Ni’ima tafi kowa cin albashinki saitaci tarage sauran mu yan uwanki kike rabamana” Ammi bambami
takema Hawwa bana wasaba, tace “yanda kike kashema yaranta kudi kanninki da yaran kanninki basu
samu haka daga jikinki suci, duka abinda kika mata arayuwa bai hana rana daya ta kwance miki zani a
kasuwa ba ta zagi ubanki ta zagi uwarki ta goranta miki yanzu shine still kike neman goyata abaya kiyi
Allah baki sa’a nina tafi zaria nafasa kwana gidan nan, Ramla zoki hada kayanmu mutafi”



Dasauri Hawwa tarike kafanta tana girgiza kai tace “Ammi dan Allah kiyakuri” Baba shima yace “Zainab
yakuri yamma tayi bani barinki kishiga hanya yanzu” kaman Ammi zatai kuka tace “Malam Hawwa na
batamin rai, tana bakantamin rai, haba haba dan Allah gamai sonta ta tsaya tana gayamana mashayi ne
menene menene, ga mara sonta takasa ganewa binta take ido rufe kaman makauniya,ana nuna mata
gaskiya tana kulle idanu ina dalili kasheni takeso tayi da bacin rai da takaici nagayamaka bazan kwana ba
Malam” Baba shima cikin masifa yace “shikenan kin batama mahaifiyar ki wacce ita kadaice bata fushi
dake aduniya rai, matarnan ni da ita bama hammata iska muke akanki sabida yanda bataso ina fada
akanki ina damunki, jibi yanda kika bakanta mata rai yau Hawwa kinji dadi ko”? Tashi Hawwa tayi sai
kawai ta rungume Ammi tafashe da kuka tace “Ammi dan Allah kiyakuri trust me I don’t consider Ni’ima
my friend anymore and namiki alkawari bazan kara bari tasan sirri na ba kawai tabani tausayi ne
somehow I feel responsible for her situation and condition da Baban Yaseer baiyi all abubuwan nan ba
da yanzu suna tare abinsu but bazan karaba kiyakuri Ammi na forgive me dan Allah” shiru Ammi tayi
saikuma ahankali tace “naji nahakura ya isa, kawai abin namin zafi arai ne yanda kike yunkurin dawo da
makashinki rayuwanka” Baba yace “Allah ya kyauta ai ta kuskura tai haka saitaga bacin raina” ahankali
Hawwa tace “bazanyiba Baba” wucewa Baba yayi yafita Hawwa takai Ammi gado ta zauna sai kawai ta
kara rungume Ammi, ahankali Ammi tanuna mata wasu shopping bags tace “kinga abinda Ramla tayi
taga opportunity” dan murmushi tayi kadan tace “yarinya ce Ammi” ahankali Ammi tace “ina kukaje?”
“Wani shagon dinki aka aunani hmm” ta tabe baki Ammi tai murmushi tace “muga abubuwan”.

[10/6,
1️⃣ 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣1️⃣
5️⃣




She wants to be Hawwarh’s best friend, wannan abubuwan da ada zatai sharing da Ni’ima gwara tayi da
ita, tabata labaran hakan zaisa ta manta da Ni’ima, Ammi ta karba tana budewa tarike baki tace “au dan
gidansu yartawa yake cewa Yar Sanda Kulu lallai Ibrahim yacika sarkin tsokana” Ammi tabude kwalin
agogon taciro tana kama hannun Hawwa ta dauramata tace “masha Allah cip cip idan gobe yazo saikisa
yaganki dashi yaji dadi haka akeyi ma miji” Hawwa tadan turo baki tana tauna baki batadai magana ba
gudun karta batawa Ammi rai Ammi tasamata bracelet din shima yamata kyau sannan ta bude turarukan
ta feffesa mata itama Ammi ta fesa anata jikin tace “uhm ni Maman Amarya nima nayi kamshi” dan
murmushi kadan tayi Ammi tace “kai gaskiya mijinki ya san kan turare Hawwa kinji kamshi” dasauri tace
“Ammi nabaki ki daukesu ni dama inada turare na” dakuwa Ammi tamata tace “kwal ubaki Hawwa mijin
naki yamiki kyauta zakimin, kaji yarinya inga kin bama wani saikin sani” turo baki tayi ta tashi kawai tana
rage kayan jikinta Aminu yayi sallama yashigo wani waya daban yakawoma Hawwa yace “Ya Ibrahim
yace nakawo miki” wayan takalla Iphone ne bamatasan wanne ba ganin Ammi na kallonta ta wutsiyan
ido yasa tasa hannu ta karba tace “to” ta ijiye tawuce bayi.



Around 10 duk sun kwanta ita Hawwa sabida zatai azumi gobe Ammi kuma sabida zatai tafiya gobe,
sabon wayan dataki bi takanshi tuntuni ne yahau ringing ita batamasan sim dinta ne ciki ko wani
dabanba hakanan dai taji bazata dauka ba, wayan na karewa yashiga ringing again Ammi tace “wai ba ke
ake kira ba Hawwa nafasan ba bacci kikeba” tashi tayi ta sauka daga gadon tasa hannu tadauki wayan
akan mirror tadawo gadon ta kwanta sannan ta danna wayan takai kunnenta sabida Ammi yasa ta
kwantar da murya sosai hakan yasa muryanta yayi wani irin dadi ahankali tace “hello” lumshe idanu
Khaleel yayi yana gyara kwanci afalo ashagwabe yace “I’m hungry Kulu” wani iri Hawwa taji yanda yayi
magana hakan yasa tayi shiru, Khaleel ahankali tace “I don’t feel like eating abinda chef namu suka dafa,
nazo kimin girki Kulu?” Runtse idanu Hawwa tayi tace “nace banson sunan nan” ahankali yace “but
Hawwah is Hawwa Kulu” Shiru Hawwa tayi the way yake kiran Hawwa dadi, sabida Ammi tadaure tace
“bacci zanyi zan tashi nayi azumi anjima good night” zata cire wayan daga kunnenta yace “but it’s not
Ramadan, azumin me kikeyi ramuwa?” Shiru tayi ta lumshe idanu kaman bazata amsashi ba tace “nafila
ina azumi Monday and Thursdays” cikin yar karaman murya yace “nima zanyi” yayi shiru jin batace
komiba Khaleel yace “sainai addu’a Allah karya baki ikon bata auren mu, I want to live my life with you”
yafadi ahankali baimasan mesa yake fadin hakaba but kawai yanaji ajikinshi bazai iya rabuwa da ita ba
dan juyawa Hawwa tayi ganin Ammi tayi bacci ga ijiyan zuciyanta tanaji hakama Ramla yasa ahankali
tace “you’re a liar! Kaida ke wulakanta mata bakasan darajansu ba, imagine locking your Baby Mama in
jail, Allah bantabaji I hate someone kaman the way na tsaneka ba” shiru Khaleel yayi sai kuma chan yace
“do you love my gift?” Cikeda tsana tace “I will never love anything that comes from you” shiru yayi
baice komiba Hawwa kawai tazare wayan daga kunnenta daidai yasake kira kaman bazata daukaba
tadauka kafin yayi magana tace “how could you send that video to Nursing Council don’t even deny it
nasan aikinka ne, why would you do that to my friend?” Hamma taji yayi yace “zan fita I know you don’t
have friends so bansan wat you are saying ba bye” Hawwa tace “aikin kenan party giya da mata”
murmushi yayi yace “gashi na aureki” zatai magana ya katse wayan jitayi ranta yana kuna yana susa
tasan yanzu club zaije maybe Allah kadai yasan time dazai dawo shiru tayi sai chan ta tuna yanda yamata
kiss a kumatu a mota dasuri takai hannu tashiga share kumatunta kaman yasamata dafi ahaka tai bacci.




Washegari around 8 suka fito dudda tanajin bakin cikin shiga motan nan haka ta shiga Ammi tafara
kaiwa park sannan tawuce office.



Tundaga gate ake mata yajiki ana mata Allah kyauta tana zuwa direct office na DIG tayi tai knocking
yabata izinin shigowa yana ganinta yadakatar da rubutun dayake yace “Hawwa are you sure you’re
strong enough kidawo aiki?” Murmushi tamai tace “yes Sir thank you” anatse yace “welcome back”
gyadamai kai tayi ganin ta tsaya bata wuce ba yasa yace “akwai wani abu ne?”




Gyadamai kai Hawwa tayi cikeda damuwa, seat dake gabanshi ya nuna mata hakan yasa ta zauna akan
kujeran ya ijiye pen na hannunshi yace “I’m listening Miss Hawwa” gyadamai kai tayi anatse tace “Sir I
have a very serious problem I need your help” gyara zama DIG yayi dan yana bama Hawwa respect da
girma dan ijiyan zuciya ta sauke tace “Sir I’ve never been to Senate President house banda time din nan
damukaje aiki, I know nothing about them or household nasu” with so much anticipation DIG yace
“what’s with Excellency Hawwa?” Ijiyan zuciya ta sauke cikin raunin murya sosai tace “Sir ranan danai
accident ina hospital Babana yabasu aurena, sai bayan mun dawo gida anyi discharging dina ake
sanardani wai wannan yaron nasa Khaleel aka auramin” tayi maganan hawaye mai zafi na sauko mata
DIG kanshi was in shock yazaro idanu yana kallon Hawwa yace “you mean Khaleel Baban Noor”?
Gyadama DIG kai tayi bakinta na rawa tace “I have no idea me suka gayama Babana, banso Khaleel yake
yakarani acikin sahun matansa sabida yayi using dina and dump me bayan 1 or two weeks” Ko kadan DIG
baiji dadin news dinba but still cikeda damuwa yace “Hawwa akanme mahaifinki zai bada auren ki batare
dayayi bincike ba? I’m not saying that because maybe zasu miki mugunta or something no su basa
wannan, kawai dansu baisan menene aure ba, baisan darajan auren ba, mata are like papers zai iya bude
this page ya yaga and open another page, so why will your father get your married to such kind of
man”? Bayan hannu Hawwa tasa tagoge idanunta tace “sabida he’s tired of me, yagaji da yanda nake
zaman mai agida ba miji” DIG ko kadan baiji dadi ba yasakeyin shiru sai chan yace “to wani help kike
magana zan miki”? Share fuskanta tayi tass kaman batai kuka ba takalleshi tace “I want you to come
with me Sir muje ka gayama Babana the type of Man Khaleel is cus wai on 23RD this month za’ayi biki
zan tare, I don’t want this marriage I don’t want to be victim of circumstance na gayama Babana all I
know yaki yarda I’m sure ka tayani gayamai zai yarda”.

[10/6,
2️⃣ 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣2️⃣
5️⃣




Kallonta DIG ya tsaya yana yi kaman mai lissafi na kusan 2min sai chan ya sauke ijiyan zuciya yace
“Hawwa listen ki fahimceni keba yarinya bace I will be very raw in whatever I will tell you now” yadan
sauke ijiyan zuciya yace “I’m a father inada yara mata babu wanda ya isa yazo yace zai aure yarana
nabashi batare danayi bincike ba, for mutanen nan suzo mahaifinki yadauke ki sharp sharp batare daya
damu dako kinaso ko bakiso, ko kinsan guy din ko baki sansa ba yabada ke only mean one thing” yadanyi
shiru yana kallon Hawwa yace “just like rest of the victims parents kema maybe mahaifinki just did it for
money ne so kina gani koda zanzo nace gashi gashi mahaifinki zai yarda akashe auren?” Hawwa tai shiru
yace “saikuma second abu, Hawwa you’ve been in this job kinsan yanda aikin gwamnati yake, Baban
yaron nan sune Nigeria gabaki daya do you want me to be on the bad side of such kind of people?? Naje
nace kaza kaza ko baban ki baice ni ba ne las las zasu gano nine kinsan abubuwan da hakan can cost
me?”

Yasake shiru yace “banda haka this is personal matter not work related, maganan aure ake ni as Oganki
ko Boss dinki baikamata na shiga ba sai inzo naji kunya nan gaba cus of What If dayawa dana hararo in
the case, what if ke bai sakeki like the rest of the matan ba? What if ya zauna dake har abada? Hawwa
you have power what if you somehow influence him ya gyara all those hali and changed? Idan ya chanza
is a good thing since he’s not a murderer ko wani kidnapper” Ahankali DIG yace “just think it through but
I don’t think is proper for me to interfere Hawwa, kiyakuri but I don’t think hurumina ne tunda har
Babanki ne yabada ke da kanshi just pray and seek Allah guidance Allah sadaki da alkhairinsa” hawaye
Hawwa taji ya zubomata sharrrr tai shiru a office din anatse DIG yace “so sorry Hawwa” tadade ahaka
sannan ta share fuskanta tamike tace “is it okay nai resuming gobe Sir I have to be somewhere”?
Gyadamata kai yayi yace “sure take your time” wucewa tayi tafita yabita da kallo tawuce tashiga
motanta ta tada Maman Noor kawai tafado mata arai, she’s her only second hope.

Sanin tana prison hakan yasa tawuce prison na mata, parking tayi tana zuwa ta nuna ID card nata
tawuce office na prison warden din ta zauna bayan sun gaisa da Matar Mrs Adebayo tace “wakikeson
gani yau Miss Hawwa”? Anatse Hawwa tace “Hadiza Muntari wacce was convicted sabida kidnapping
yarta datayi that senate president case ish” dasauri Mrs Adebayo tace “ohh Hady we call her Hady anan,
ai jiya an fitar da ita, wasu yan sanda sukazo da clearance from court they withdrew the case against her
wlh she’s so lucky” sosai Hawwa ke kallon Mrs Adebayo Khaleel ne ya yafemata sabida jiya ta gayamai
she will find evidence against him? Mrs Adebayo tace “why are you looking for her”? Murmushi kadan
Hawwa tayi mai ciwo tace “kinsan nine nai investigating case din but well that aside nace ko kunada
home address nata yar wani gari ce kinsani”? Girgiza mata kai tayi tace “no gaskiya yar Bidda ce but
bamu da address nata” Shiru Hawwa tayi saikuma chan tamike tabata hannu suka gaisa tace “thank you
very much” tawuce tafita.



Tunda tafito tana tafiya zuwa parking space ta hango Khaleel tsaye jikin motarta tsaye yana sanye da
dogon wando da shirt dabai saka boturan sama ba, faduwa gabanta yayi akwai tracker a motarshi ne
datake ja yanzu? How did he know tana nan? Daurewa tayi ta karasa ko kallo bai isheta ba tazo zata
wuceshi tabude motan ya fizgota tadawo baya kaman paper azuciye Hawwa ta buge hannunshi tace
“don’t touch me again! Stop touching me!” dan zaro manyan fararen idanunsa Khaleel yayi yace
“someone is in a bad mood today wow!” Yadanyi dariya yana kallon yanda tahade fuska tana kallonshi
yace “smile it’s Sunna!” Hararanshi tayi jin abinda yace tace “so kasan sunna” tashiga fizge hannunta
yaki saki sai kawai yabude bayan motanta dan tariga tai unlocking car din da key hannunta tun dazu
datazo wajen, yaturata cikin motan yashigo shima da sauri ta matsa baya tamai ihu. “Wai mehaka?
Leave me alone!” Dan cute smile yamata yace “sabida kinga matar nan an saketa is that why you’re in
this bad mood?” Ja idanun Hawwa sukayi takalleshi azuciye tace “even if it means me bringing down the
whole world searching duk lungu da sako I will do it! I will get Evidence and I will show Baba and my
entire family the kind of person you’re! Khaleel just know this and keep it at the back of your mind
bazan taba zaman aure dakai ba, you’re a worthless boy da baisan darajan mata ba! You don’t value
mata! You treat us like trash! And I refuse to be one of your victim”Khaleel na kallonta yadan rage murya
yace “konama wasu kenamawa? Why do you hate me?” Ihu Hawwa tamai tanaji kaman ta shakesa tace
“I hate you sabida you’re a piece of thrash! I hate you sabida you’re a f*ck boy! I hate you sabida you’re
a playboy! I hate you sabida you think life is just about women, money and parties! Kace nikamawa
dazan tsaneka?” Tadanyi shiru kadan takalleshi da masifa eyes nata tace “kasan abinda ake cema ciwon
y’a mace na y’a mace ce? I hate you sabida abinda kama all those women daka wulakantar” dan tabe
baki yayi yace “I don’t want them why should I keep them?” Hawwa afusace tace “you don’t want them
why did you marry them and ruined their life eh Pop boy”?.

[10/6,
3️⃣ 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣3️⃣
5️⃣




Dan shiru Khaleel yayi yana kallonta ganin yanda zuciyanta ke tafarfasa, she’s really angry today, and as
far as he’s concern he didn’t ruin any girls life rather he makes their life even better and colorful, all of
them and family nasu are living large yanzu, lumshe idanu yayi yabudesu kadan ya kalleta murya chan
kasa yace “I can’t stay 2days without having s*x!” Wani irin yammm kunnen Hawwa yayi jin abinda
yafadi tadan dauke kai daga kallonshi da sauri, murya chan kasa yace “I started getting married at 24yrs,
call me anything ni ba mazinaci bane Mommy na auramin su ne nayi s*x” runtse idanu Hawwa tayi da
kyar tabudesu zuciyanta na radadi yanda yake magana akan mata tace “sannu Moms boy! Mata sun
dawo maka toys for your selfish satisfaction eh dan gata”? Kallonta Khaleel yayi asanyaye Hawwa taji
kaman zata kama da wuta ganin yanda hankalinshi kwance tace “okay nima so kake na shiga cikinsu tell
me I will be your 10th wife ko 20th?” Anatse kai tsaye kuma yace “14th wife actually!” Wani zuciyane ya
debi Hawwa batasan sanda tayo kanshi takama gaban riganshi ba fearlessly ta jijjigashi ranta na kuna
tace “how dare you marry me Khaleel? Sabida kaga nakai 29yrs banyi aure ba is that why you took
advantage of desperate state na Baba na and use the perfect timing ka aure ne eh talk?” Tayi maganan
Hawaye na cika idanunta sosai tana kallon fuskanshi ta rike gaban shirt nasa gam gam, Khaleel yayi shiru
yaki magana ganin ranta abace yake yau sosai cikeda bakin ciki ganin yaki magana Hawwa tace “how
dare you take away the only evidence danake sa ran zan samu na nunama Baba wayekai eh? Khaleel I
don’t deserve you, after good 29yrs banyi aure ba clocking 30 I’ve been so patient cus nasan Allah will
reward me for imanin danayi, why will I end up with the worst person dana sani aduniya you!? I’m too
good to be your wife, you are a bad bad badddd person Khaleel I hate that kai Baba ya auramin!” Tai
maganan hawaye na saukowa daga idanunta tana kallon cikin kwayan idanunsa kaman yanda yake
kallonta shima, all this while batai kuka ba sabida tanasa ran she will have something to show Baba but
yau da Khaleel yayi outsmarting nata sai taji duniya yamata zafi, duka takaimai a robust chest dinshi
hawaye na dauka daga idanunta tace “I hate that kai Baba ya auramin! I hate you Khaleel I hate hate
hate you na tsaneka! Na tsaneka” tafashe da kuka tana kaimai duka sosai akirjinshi duk yana kallonta
asanyaye, cikin kuka tace “I remembered the day daka fadamin one day sainai kuka ina begging naka for
mercy agaban that super market” cikin kuka har shesheka take hawaye har gemunta tace “you won! You
won! You won Khaleel, I’m sorry for everything Ibrahim! I’m sorry for being rude, for insulting you calling
you jobless, I’m sorry for everything dan Allah kasakeni! Please divorce me dan Allah” tashiga kuka sosai
bana wasaba, bata taba sanin zata iyama Khaleel kuka hakaba, ahankali Khaleel ya lumshe idanunshi da
hannu daya ya fizgota yasata ajikinshi “leave me leave me” Hawwa tai ihu amman saida yasata ya
kankameta sosai tun tana hargowa hartai shiru ajikinshi tana kuka ahankali.




Lumshe idanu Khaleel yayi yana shakan cool kamshin datakeyi dayamai dadi sosai tana kuka yakai
bakinshi saitin kunnenta yana matseta ajikinshi ta yanda bazata iya fitaba murya chan kasa yace “I’m
glad kinyi admitting defeat Kulu Khaleel never loose a fight! Mace bazata taba winning dina ba!” Zatai
motsi yariketa gam ahankali yace “I will never divorce you Kulu! This Khaleel you hate so much saikinyi
rayuwa dashi har abada!” Yadanyi dariya kadan mai sound yace “maybe da baki tsaneni ba danai letting
naki go” awani irin hankali yace “and I will sex you just like yanda nakeyi da all the rest of those girl
creatures, I will add you to the collection of women I slept with!” Yanda Hawwa ke fizge fizge kaman
zata tashi amman yahanata fita daga jikinshi, yakara kai bakinshi wajen kunnenta yace “kinata neman
evidence akaina bayan nine keda evidence akanki” yayi wani makirin murmushi yace “imagine Baba yaga
video or pictures of when you were trying to rape me kina shamin baki, grabbing my shirt just like yanda
kikayi dazun nan, trying to reap off my shirt and strip me naked, how will Baba feel?” Fizgo kanta Hawwa
tayi daga jikinshi ta sauka gefe takalleshi da jajayen idanunshi tace “wat are you talking about? Ko zanyi
raping maza aduniya trust me i will never go for national cake irinka da karabama all matan garin nan
jikinka!” Shiru Khaleel yayi yana kallonta babu macen data taba gwada kalan zagin da Hawwa kemai, she
just called him national cake, dan ijiyan zuciya ya sauke, wayanta dake inda take zaune yanuna mata
yace “check your phone?” Dasauri Hawwa ta dauki wayan tabude, tana dubawa taga yatura mata hoto
ta iMessage guda daya inda take saman kanshi bakinta akan nashi tarikemai gaban riga duka jikinsu ajike
hannunta yahau rawa takalli Khaleel da sauri cus she’s confuse, kanshi yadan sosa irin na iskancin nan
yace “I have the video inhar u finally took off the shirt kina shamin this” yanuna mata nipples dinshi
cikeda iskanci, yadan kalli saman motan kaman mai tunani yadaura yatsa abaki saikuma yacire yakalleta
yace “I will just start crying to Baba ince yarshi beat me up ta turani cikin ruwa tafito dani kawai tahau
kissing baki na and kikayi threatening dina kan cewa dole saina aureki, nazo nagayama Baba, Baba will
easily believe me daman that crazy woman tace zaki iyama maza fyade so I’m your first victim” yakashe
mata ido daya a iskance Hawwa na kallonshi hawaye na cika idanunta, Comfortably Khaleel yace “idan
bakija bakin nan that talks like parrots kinyi shiru anyi bikinmu an kawomin ke gidana ba I will expose
this” yanuna mata wayanta yace “family naki will lose all respect for you and zama dani dole, anyhow u
look at it I’m still the winner, ko kinaso ko bakiso saikin zauna dani, don’t forget you started this war
with me Kulu!” Glass nashi ya warware ya sanya a idanu sannan ya kalleta yace “see you Kululuwa Yar
Sanda bye” yabude kofa yafice abinshi yawuce nashi motar aka budemai brabus dinshi yazauna aka ja
motan harsaida Hawwa ta daina ganinshi tafashe da kuka sosai tana kallon hoton tana mamaki what
happens to her? How come is this picture photo shop ko sun bata wani abu ranan ne tunda yan kwaya
ne how

Please Login or Register in order to submit comment