Reading Gargada So By m Shakur Chapter 23 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

did she kiss this man cus batasan sanda akaiba, takai 20min tana kuka amota sannan ta tada
motan tabar wajen.

**



Ijiyan zuciya Momy tasauke cikeda damuwa tana kallon Salman daya gama koramata bayani acikin office
dinta hannu tasa ta zare glasses dake kan idanunta tashafa goshinta cikeda damuwa tace “why that
police girl in all matan dake duniyan nan dan Allah? Ko yar india Khaleely yake bukata zan iya auromai
why that girl? Akanme yake chasing nata up and down tell me the truth Salman sonta yakeyine?” Cikeda
girmamawa yace “I can’t say Hajiya gaskiya, but one thing is bantaba ganin Yallabai na bin mutum up
and down kaman yanda yakebin yarinyar ba shi kanshi ba lallai yasani ba but he’s giving her all of his
attention his time and komi Ma’am” table Mom tabuga tace “that’s wat I don’t want, yarinyar will take
my son for granted wlh, zata wahalar min dashi Khaleely baitaba bibiyan any girl aduniyan nan ba saidai
su suyita bibiyansa what is so special about tsohuwan yarinyar nan da he’s all over her eh? Hmm, u can
go Salman just keep me posted whenever he sees her and wat they discuss about” gyadamata kai yayi
yace yes Ma yawuce yafita.

Tashi tayi ta tsaya jikin window ta hango Khaleel din na buga ball da Noor he looks so happy haka Noor
ma Mom ta sauke ijiyan zuciya, bude kofan office din nata Mom tayi tashiga another elevator dake
wajen tasauka kasa tana tafiya zuwa garden da Khaleel ke buga kwallo Noor dake sanye da jersey na
Liverpool looking so cute tace “Granny join us” murmushi Mommy tamata tace “continue playing
Princess dina” takalli Khaleel dake wasa da kwallo abinsa kaman bai ganta ba tace “why do you keep
chasing that Police girl Khaleely?” Batare daya dagokai ya kalli Mom ba yana bugama Noor kwallo yace
“what is your business with my affairs Momy”? Dan shiru Mom tayi taji zafin amsan daya bata inda sabo
sun saba haka yake musu magana agantale, ahankali tace “common My Leely I didn’t train you to be
going after kowace kalan mace aduniya! You have everything na rayuwa babu wacce kakeso dabazaka
iya samuba” daidai lokacin yabuga kwallo araga shida Noor sukahau suna jumping suna ihu yadagata
yana ihu suna dariya sannan yasauke ta yace “go to your Nanny tamiki wanka” dasauri Noor tawuce tana
gudu shikuma yadauki kwallon cikeda iskanci ya wurgama Mom tai baya baya kaman zata fadi sannan
tarike ball din da kyar tana haki tace “Khaleely banson iskanci fa, karyewa kakeso nayi?” Khaleel ya
kwashe da dariya sannan yataho inda take yabata sidehug yana daura hannunshi akafadanta cikin
sangarci yace “Mom tsoro kike zan auro miki yar sanda?” Hade fuska tayi hakan yasa ya kwashe da
dariya again Mom ta tsaya tana kallonshi he’s so happy this days, Khaleel yace “Mom do you think she
will stop me from living my life? And enjoying myself?” Cikeda damuwa Mom tace “eh mana Khaleely
girls like her sunfi karfinka” dariya yayi yace “Mommy I’m man enough to control kowace kalan mace na
aura your Son is not a boy” yasaketa yawuce saikuma yadawo ashagwabe yace “Moma we will be having
wedding on 23rd get ready invite all your friends, I want my side furnitures change, sannan agayara my
main flat” yanuna wani arnen flat dake dayan barayin gidan dasauri Mommy tace “no Khaleel you will
never leave my sight gaskiya side dinka dake cikin flat dina zaka dinga zama not bangaren chan kaji ba”
wucewa yayi abinsa batare daya kulata ba yatafi sama gym dinshi yashiga yashiga yin exercise kafin daga
bisani yafada shower yayi wanka yafito Sam haryazo suka tafi party abinsu.

[10/6,
4️⃣ 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣4️⃣
5️⃣




Ranan gabaki daya Hawwa jitayi batajin dadin komi, har Ramla saida taga Hawwa was not in good mood
sabida yanda tai shiru batama iya magana da kyau, sai lissafi take how zata fita daga this mess? Idan
yanuna video ko pictures yacema Baba tayi kokarin mai fyade duk zasu yarda ta ina kunya zai barta ta
kallesu dagashi har Ammi that means everything Ni’ima said is true about her.

Washe gari tsaf ta shirya ta tafi aiki around 12 DIG yakirata tashigo office nashi murmushi yamata yace
“okay Ogana gabaki daya yakirani yace nabaki leave sabida kiyi planning wedding naki da kyau an baki
60 days” zaro idanu Hawwa tayi tace “Innalillahi 60 days that’s 2month, mezanyi da all this time Sir”?
Dan murmushi DIG yamata yace “Hawwa have you seen abinda nafada miki jiya? Imagine danaje wajen
Babanki to, wannan da Ogana ne yakira yace abaki 2months wedding leave abinda 3weeks ake bayarwa
but naki is different, so zaki iya tafiya, we will see you on the wedding day in sha Allah idan kinyi inviting
namu, Hawwa May Allah bless your home, Allah miki albarka, nasanki da ibada da yawan azumi Allah
shine maganin komi so call on to him shine yasan wats best for you” kuka taji yana zuwan mata amman
tahadiye ta gyadamai kai ta tashi ahankali tafito tana tafiya zuwa office nata wani officer yace “Miss
Hawwa kinada bakuwa bamu barta tashigo nan ba tana chan” yamata pointing waiting room nasu, da
mamaki tadinga tunanin waye ko wacece zatazo wajenta, dudda Ammi na hanya dan yau zata dawo
amman ai baici ta iso ba tace mata by 11 zatabar gida, why is she even thinking of Ammi? Ammi bazata
taba zuwa wajen aikinta ba, hanyar waiting tayi ganin Ni’ima taci gayu cikin atampa mai kyau ta yafa dan
gyale ta rike handbag a hannunta yasa ta tsaya turus Ni’ima tamata murmushi kawai ta taso da gudu
tazo batai wata wata ba ta rungumeta tace “Best suprise” chak Hawwa ta tsaya without hugging her
back harsaida Ni’ima tadago ta kalleta tace “are you not happy to see me?” Dan girgizamata kai Hawwa
tayi tace “no is not like that” dasauri Niima tace “muje office naki anata kallonmu anan” kawai takama
hannun Hawwa, ahankali Hawwa tabita har zuwa office nata suka shiga idanunta ne suka sauka akan
iPhone 15 pro max na Hawwa dake kan table last she check Hawwa was using Samsung S10 harya
chanza mata wayane? Lallai gayen nan, abu taji ya tsaya mata arai dasauri tasaki hannun Hawwa tai
wajen wayan tadauka tace “wow kin chanza waya Hawwa? Kin koma iPhone? Ni fa banson iPhone ance
basu rike charge duk application saika saya? Baka iya downloading movies anyhow, komi kudi, Ke kika
siya ko mijinki ya saya miki”? Karasowa Hawwa tayi ciki tazauna ahankali tace “shi ne” wani irin
murmushi Ni’ima tana danne bakin ciki da zafi datakeji aranta tayi tace “awwwn lovebirds, ohh my my,
Hawwa I’m happy for you Allah yaga how patient you are yabaki mai sonki, wai yaushe kuka hadu ne
baki taba bani labarinsa ba, eh yaushe kuka hadu?” Baki Hawwa tabude zatai magana akai knocking
kofan da sauri dukansu suka kalli kofan Abraham ne ganin Ni’ima yasa ya tsaya yace “can I see you Miss
Hawwa”? Gyadamai kai tayi tace “sure” ta mike suka fice tarufe kofan dawani irin sauri Ni’ima ta danna
screen din wayan ganin babu password yasa tashiga cikin wayan dasauri tace “calls” call log tashiga d
only number datai magana dashi for long batai saving ba saina Ammi datai saving da Ammi hakan yasa
tashiga kwashe number da she’s sure Khaleel ne dan ya kikkirata bata dagawa daidai tana gama kwasa
tanaji ana taba kofan da sauri tafita tarufe wayan ta ijiye kan table Hawwa ta shigo rike da Maltina ta
ijiye gaban Niima, Ni’ima tace “thank you Best” Hawwa ta zauna Ni’ima tace “gist me Best ya shirye
shirye? Kayan daki kayan kitchen? Na kaiki wajen wanda yamin na dakina?” Ahankali Hawwa tace “Baba
da Ammi are in charge of everything bansan mesuke ba” gyadamata kai Ni’ima tayi saikuma tace “wai
har yanzu kin rikeni azuciye ne? Best I’m really sorry wlh ina sonki you mean the world word to me kinji”
dan lumshe idanu Hawwa tayi saita gyadamata kai tareda bude idon, Ni’ima tace “anko fa? Nafitar miki
da anko?” Shiru Hawwa tayi saikuma ta gyada mata kai, murmushi Ni’ima tayi tace “thank you, can you
call Baban Yaseer for me yanzu da wayan naki”? Shiru Hawwa tayi all maganganun Ammi nadawo mata
ahankali tace “Ni’ima banso nakara shiga lamarinki da Baban Yaseer I promise kaina that, for licence naki
nayi magana za’a samu nasara in sha Allah” murmushin karfin hali Ni’ima tayi tana danne abinda takeji
azuciyanta tace “shikenan hakan ma I’m grateful after kalan abinda namiki not everyone will even help
me that much, kinada zuciya mai kyau Hawwa, thank you” gyadamata kai Hawwa tayi, daidai nan wayan
Hawwa yahau ringing Ni’ima ta saci kallon screen din ganin number data kwashe ne kaman Hawwa
bazata dauka ba, but ganin Ni’ima and tanaso tanunama Ni’ima she’s cool with Khaleel kodan tacire
tunanin Baban Yaseer da ita aranta yasa gently tadauka takai kunnenta, murya chan kasa Khaleel yace “I
sent a delivery guy what’s your office number”? Shiru tayi chan tace “baza’abarshi ya shigoba” dan
murmushi yayi yace “no one can stop my delivery, office number Kulu” murya chan kasa tace “0040”
katse wayan yayi almost 1min saiga knocking anatse Hawwa tace “come in” bude kofan akayi wani
delivery guy ne rike da flowers na red roses da akai wrapping katon gaske, saikuma platter na yan gayu
na different intercontinental dishes da note ajikin both of them delivery guy din yace “I’m looking for
Mrs Hawwa Alhassan Ibrahim Khaleel” Ni’ima jitayi yawun bakinta yayi daci da kyar tahadiye, ahankali
Hawwa ta mike ta nunamai table din zuwa yayi yafara mika mata flowers din dake kamshi sosai like
Khaleel plus kamshin roses again, office din yacika da kamshi, karba tayi ta ijiye sannan yabata platter na
abincin shima ta ijiye yabata note nashi tai signing sannan ya tafi, kafin Hawwa ta zauna har Ni’ima tasa
hannu tadauki card dayayi note ajiki tace “love bird bari muga meya rubuta miki” dasauri kafin Hawwa
tace wani abu, tace “_I know you haven’t had breakfast banson matana looking skinny you are too light
for my liking, eat and get chubby, cheers to starting your leave today! Sowie about yesterday with love
Mijin Kulu❤️_”

Murmushin dole Ni’ima tayi ta ijiye card din, taja platter box na abincin tana budewa tace “eat mana”
wow tafadi ahankali lafiyayen abinci ne aciki dat are very hot, mash potatoes da chicken wings, samosas,
Pasta sai Mandi rice, ga salad ga fruits juice very cold ga sweet da cingum na mentos, kallon abincin
itama Hawwa take, deep down she feels happy but then she don’t wanna feel d happiness ahankali tace
“ke kici idan zakici” dasauri Niima ta girgiza kai tace “a’a inacin abinci nafito” gyadamata kai Hawwa tayi
saita rufe platter ta matsar gefe idanunta suka sake saika akan rose din kawai ta tsaresu da idanu Niima
duk na kallonta, aranta tace “munafukar mugun son mijinta take amman tana bobboyewa, hala ma sun
riga sun sadu” wayan Hawwa ya shiga ringing dasauri ta waigo ganin Khaleel ne yasa ahankali tadauki
wayan takai kunne murya chan kasa Khaleel yace “have you eaten? Is the food good? Kona chanza mana
Chef? Shizai dinga mana girki bayan auren mu, abincin yayi”? Shiru Hawwa tayi murya ciki ciki tace
“mesa baka dafa da kanka ba”? Dan zaro idanu Khaleel yayi yace “Momy bata barina in kitchen I don’t
know me akayi a kitchen” murya chan kasa Hawwa tace “uhnn Moms boy” murmushi kadan Khaleel yayi
yace “do you like the rose?” Kin magana Hawwa tayi, ahankali Khaleel yace “but I said sowie about
yesterday” murya chan kasa Hawwa tace “sowie is not sorry” dan dariya kadan Khaleel yayi ahankali
yace “wa akace tana tareda ke a office?”

[10/6,
5️⃣ 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣5️⃣
5️⃣




Faduwa gabanta yayi jin tambayan daya mata, hakanan sai takasa magana, “answer me” yafadi da
kakkausan murya still kin magana tayi sai kawai ta zare wayan daga kunnenta takatse ta ijiye takalli
Ni’ima ahankali tace “zan tafi gida natashi” tashi Ni’ima tayi tace “toh nima bari natafi, bari natayaki
daukan rose din saike ki dauki platter” wani iri Hawwa taji amman saita daure ta mike tashiga hada
abubuwanta tadauki car key suka fito tare ita tana rikeda platter Ni’ima na rike da rose din har zuwa inda
motar Hawwa yake, Ni’ima sai kallon motar take tanaji kaman tahadiye zuciya ta mutu idanunta harsun
kada sun chanza, abayan motan sukasa komi Ni’ima na kallon motan irin wannan fa ba tokunbo car
Hawwa ke dashi ba no, asalin sabuwa gal ce, komi na motan ba ariga an daye mata ledaba, maida kofan
bayan Hawwa tayi tarufe tace “bye” tawuce ta shiga gaba Ni’ima na tsaye tana kallonta, Hawwa taja
mota tabar wajen abinta, da kyar Ni’ima ta iya wucewa zuwa wajen tata motar zuciyanta kaman an
barbada busheshen barkono da danye tsabagen azaban radadi dayake mata, sai kawai ta tsaya tana
kallon motan ta, motar Hawwa tada Toyota Camry ce 2006/2007 ita lokacin da Baban Yaseer yabata
Camry nan na 2014 kaman zata haukace dan tafi na Hawwa kyau da tsada gata latest, but yanzu dataga
motan da Hawwa keja benz datakai irin 150M sai taji ta tsani tata motar, saitaji ta rainata, wai tayaya ma
rana daya Allah zai dauki miji mai bala’in kudi yabama Hawwa ne? Eh? Within a blink of an eye rayuwan
Hawwa ya chanza kakap, big phone iPhone 15 pro max, ita tana fama da Samsung S21 dinta da ada
takejin dadi yafi na Hawwa S10, Hawwa ce big car, ga sadaki mai tsoka, ga gwalagwalai, Hawwa ko sisi
taki bata, da dane da hala yanzu Hawwa tabata like 20M from that sadaki wlh dan Hawwa bata kyashin
bata abu, Hawwa is going to big house now and yaron seems to love her alot, jibi yanda yake bata gifts,
ranan su diamond agogo dasu turare yau abinci da flowers masu tsinannen kamshin dadi, he’s so
romantic, she thought babu miji that will be as sweet and romantic as Baban Yaseer yanzu taga wanda
yafisa.

Hawwa ta hadu da irin gayen kan taki fadamata har sai bayan tayi hauka? The way suke soyayya hakan
nan she can swear Hawwa tadan jima da sannin gayen? Wannan dayaketa bata gifts sunyi sex ne?
Hawwa is so happy she wants her to be sad, tafison taga hawaye da bakin ciki da bacin rai da damuwa
akan fuskanta, wannan gayen ya shigo rayuwanta yasa Hawwa ta chanza bata damu da itaba yanzu,
imagine wai ita Hawwa ke shama kamshi, what will she do yanzu? Da kyar ta lallaba tashiga motan ta
tada tabar wajen tana tana tafiya akan titi tazo ta wajajen banex ta kalli masu bara dake wajen, sai kawai
tayi parking motan tafito taje wajensu tace “zan baku kyautan kudi sosai amman saikun bani wayanku
na tura wani sako” har rige rigen bata wayan ake, kakkarba tayi marasa kati har tana samusu ta bank
dinta, sako tashiga turama number Khaleel da kusan duka number su sannan ta basu 5k suraba tawuce
takoma mota tana murmushi taja abinta zuwa gida.

**



Khaleel na cikin mota tareda Sam wayanshi yayi kara daukan wayan yayi yaga messages guda 5 from
different numbers hardly unknown ke kiranshi ma talk more of sako, kaman bazai budeba saikuma
yabude daya.

“_Hawwa is a whore! Tsohuwan karuwa ce she sleeps with everyman dayake zuwa yace yana sonta saisa
suke guduwa basa aurenta sabida tabasu abinda suke nema_”



Chak Khaleel ya tsaya yana kallon messege din to be very very honest he doesn’t care idan Hawwa
sleeps around or not cus yasan tun zamanin da wato old days aka daina samin virgins, konji is real babu
yanda za’ayi yataso maka baka nemi wanda you will sleep with ba so what ai d’ane tayi, baida right to
judge her life is not easy takai this years 29 without a man, shi tun yana 24 yafara ai, but dudda haka
saiyaji still zuciyanshi namai wani iri sai kawai ya ijiye wayan da sauri without opening sauran messages
din ahankali yace “park the car” Dasauri Sam yace “lafiya? We are not there yet” dan murmushi Khaleel
yamai yace “just give me a moment” fita yayi daga motan yafara tafiya zuwa chan gefen titi baitaba sani
akwai randa za’a gayamai wata yar iska ce harma yaji abun yadameshi ba, ko yadingajin ciwo aransa ba,
duk sai yaji wani iri, who even send the message? What if is Hawwa? He don’t think she will ever defame
kanta dudda yasan batason auren su but Hawwa is someone that value self respect and image nata, ko
kadan batason compromising self respect and imagine nata saisa he even use that picture and threaten
her with it, cus yasan she will not want him to expose that koda ba gaskiya bane dan she values her self
respect, juyowa yayi yakalli Salman daya fito daga motan yana kallonsa da hannu yama Salman alamu
daya daukomai wayansa amota daukowa yayi yazo wajen yakawomai dasauri ya karba yabude second
message din.

“_Hawwa babe din boss dinta ne DIG she slept with him in order ya dauketa yasata a task force din nan
dan she was an ordinary police girl before without any star_”

Sai another message. “_Officer Hawwa sleep with yaran office example Abraham data girmeshi da
shekaru slept with Hawwa countless times_”,

Yanda zuciyan Khaleel ke bugawa kasa cigaba da bude sauran messages din yayi ya manna ma Salman
wayan a kirjinshi yace “track those numbers all of them for me, track them! I need information
uuughhhhh!” Ya dunkule hannu yayi punching air yawuce fiuuuu yatafi mota ya shiga da kanshi yarufo
da mahaukacin karfi akaja motan Sam yace “lafiya are you okay”? Lumshe idanu yayi yaki magana har
sukakai party saukowa yana shiga yadauki about 5 shots na tequila yana sha Sam yace “Lee are you
okay? Why are you drinking like that” ko kallonshi baiyiba shaye shayen dayahau yi saida yabama duka
abokanshi tsoro saida yayı total out sannan Sam da Moh suka kaishi sama aka kwantar dashi agado Moh
yace “kasan what’s wrong with him”? Girgixamai kai yayi suka wuce suka fita daga dakin aka barshi
warwas agado.

[10/6,
6️⃣ 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣6️⃣
5️⃣




Washegari Khaleel yafarka adakinsa da kyar ya lallaba yaje yayi salla wuraren 9, ko wanka baiyiba yafito
yasauko kasa Mommy na falo tace “good morning Son” ko kallonta baiyiba Noor ta taho wajenshi da
gudu tace “Daddy” kanta yashafa kadan yace “go to grandma I’m coming Noor” yafice idanunshi sunyi ja
duk sun nuna alamun bacci, yayi waje yana kallon Salman daya taho da sauri Khaleel yace “ya?” Salman
yace “we tracked the numbers duka numbers din beggars ne dake hanyar banex, da kyar bayan nabasu
kudi suka iya sanar dani wata mace ce tazo tabasu 5k tayi amfani da wayansu” dasauri Khaleel yace “did
you ask them description nata?” Salman yace “yeah wai batada tsawo sosai she’s very fair and da Toyota
tazo” shiru Khaleel yayi kaman mai tunani, kawai yawuce wajen motar sa Salman yabiyosa ya shiga
driver ma yashiga sukabar gidan, ahankali cikin muryan gajiya da bacin rai yace “my wife’s house” jan
motan sukayi har zuwa unguwan su Hawwa.

Baba na kofar gida azaune da aswaki a bakinsa ya hango mota yasan Khaleel ne kawai sai yafara
murmushi kafin ma abudemai Khaleel yabude da kanshi yafito Baba ya tsareshi da idanu ganin idanunshi
adan kumbure hakama fuskanshi dasauri Baba yataso shima Khaleel yawuce wajen Baba kafin yayi
magana har Baba yakai hannunsa kan fuskanshi cikeda so yace “bakada lafiya ne Ibrahima”?Baba
Khaleel ya kalla dan ranshi abace yake yayi shiru yakasa magana sai dan huci da yasauke Baba sai kawai
hankalinsa yatashi yace “meya sameka? Tell me”? Dan ijiyan zuciya yasauke yajuyo yakalli Salman da
hannu yamai alamu yakawomai wayanshi wayan aka kawomai muryan Khaleel ba dadi yanunama Baba
wayanshi yace “Baba wasu sakonni aka turamin marasa dadi bazan iya karanta maka ba kaima, nasa
ammin tracking number” yadanyi shiru Baba da gabanshi ke faduwa yace “ina jinka gayamin menene ke
faruwa”? Cikeda jin zafi Khaleel yace “Baba matana ta batamin rai sosai, ina kyautata zaton har yanzu
tana tareda mahaukaciyan nan, so nazo na ganta ne”




Dudda Baba baiga sakon ba but ayanda yaga Khaleel yasan Ni’ima tayi wani abu ranshi inyayi dubu
yabaci tsabagen bacin rai yace “muje ka shiga gidan kacimata mutunci ba anan waje zan kiramaka itaba,
ai gidana nakane ban maka iyaka da ko’ina acikin gidannan ba, muje” Baba yayi gaba Khaleel yabishi
abaya suka shiga cikin gidan ko’ina a gyare ta buga sallama gaban dakin Hawwa, Ammi ta amsa yace “da
mijin Hawwa nazo Zainabu” Hawwa dake zaune daga ita sai dan rigan bacci tana danna wayanta dasauri
tadauki hijabi tasaka dark blue har kasa, ita dama Ammi da hijabi ajikinta Ramla kuma na kitchen tana
aiki dasauri Ammi ta tashi da fara’a tace “bismillah bismillah kushigo” shigowa Baba yayi Khaleel biyeda
shi abaya, kan Khaleel na kasa yace “ina kwana Mom” “muntashi lpy Khaleel” ahankali Baba yace “biyoni
Ammi” binshi Ammi tayi suka fice daga dakin tareda maido musu da kofan suka rufe, Khaleel yazuba
hannu a pocket nashi yana kallon Hawwa dako dagokai batayi ta kalli inda yakeba, kaman ma batasan da
mutum awajen ba, Babu wasa kan fuskanshi rai abace yace “wacece ke tareda ke jiya a office?” Batare
da Hawwa ta kalleshi ba tace “da wanda nake tare, ko wanda nai magana, ko wanda nagani a office is
none of your damn business” ran Khaleel abace ya daka mata tsawa da saida dakin ya amsa. “Nace dawa
kike tare jiya an office!”? Dagokai Hawwa tayi adan tsorace sabida yanda yayi mata tsawa ta tabbata anji
a tsakar gidan, tashi tayi daga gadon ta taho inda yake dasauri dan bataso su Ammi suji tanamai ihu
suhau mata fada akanshi, hakan yasa tace “who do you think you are kanamin ihu aka?” Ran Khaleel
abace yanunata da hannu yace “dawa kike tare an office jiya?” “My friend!” Hawwa ta amsa kai tsaye
ganin yadameta da tambayan, cikeda jin haushi tace “I was with Ni’ima me akayi? Sabida an auramin kai
saina tambayeka kafin naga kawata konai magana da kawata”? Wani irin fizgota Khaleel yayi yakai
hannunshi zuwa wuyanta ranshi abace yace “what is so special about that witch of a woman da kin kasa
hakura da ita? Are you a lesbian!? Are you really into girls?”



Ja idanun Hawwa suka soma yi tafara dukan hannunshi hakan yasa yasaki wuyanta tadanyi tari kadan
sannan ta kalleshi tace “da aurenka gwara zama da Ni’ima! At least ita bata living wayward life irin
naka!”Radadi zuciyan Khaleel yafara sai kawai yakara fizgo Hawwa yakama kafadunta ya matse yana
kallon cikin idanunta zuciya yakaimai wuya da kishi kai da komi ma ganin yanda Hawwa ke son Ni’ima
yace “idan nakara ganin ki da yarinyar nan i will killl her! I will ruin her life! I will make her life a living hell
you know me so well to know duk abinda nakeso nayi sainayi, stay away from that witch evil vile woman
inba hakaba saina kasheta!”

[10/6,
7️⃣ 10:39 AM] +234 706 565 5343: EPISODE 5️⃣7️⃣
5️⃣




Ayanda yau taga idanun Khaleel saida Hawwa ta tsorata wlh, bata taba ganinshi haka ba, yanda ranshi
yakai ga baci yasa kawai ya turata yajuya yabude kofa yafito Baba da Ammi na tsakar gidan sunyi charko
charko a tsaye, yama kasa kallonsu sabida baison suga kwayan idanunshi yawuce zaure da sauri Ammi
tabiyoshi daidai ya shiga zaure tace “Ibrahim!” Chak Khaleel ya tsaya batare daya juyoba, dasauri Ammi
ta taho tazagayo ta gabanshi sai kawai Ammi tasa hannu takamashi ta zaunar dashi kan bench dake
zauren ahankali yazauna sai kawai yakai hannayensa biyu yarufe fuskansa yafuzar da iska masu zafi
kaman zai kama da wuta sakonnin nan nacimai rai, ahankali Ammi tace “it’s okay ya isa Khaleel ya isa”
sauke hannunshi yayi ya gyadamata kai ahankali yace “thank you Mom” anatse Ammi cikin hikima tace
“can you show me sakonnin da aka turamaka game da Hawwa”? Araunane ya girgiza kai yace “Mom
banso kowa yagani, sirrin matana ne I can’t show you banso kumata wani kallo” kirji Ammi tanuna tace
“nine mahaifiyar Hawwa, show me Ibrahim idan akwai abinda yakamata namaka bayani zan maka,
banso ku fara aure da zargi ko kokonto aranka, ayanda abin ke tafiya nan gaba hala za’a iya maka
sakonnin dayafi wayan nan daci ma da tada hankali ma, so show me” Allah yasani sabida nauyin Ammi
dayakeji ne yasa gently yamikama Ammi wayanshi daya bude mata message yace “5 numbers suka turo
sakkonni, nasa anmin tracking akace lambobin wasu beggars ne, jiya danai magana da ita suna tare a
office dinta, I believe somehow she took my number from wayan Matana batare datasan anyi ba” duka
sakon nin Ammi tabi takaranta ran Ammi yama Ammi badadi sai kuma takaraji ta natsu da Khaleel tama
aminta dashi gabaki daya, dawani ne da yasaketa yace yafasa aure but shi yazo kawai yayi warning nata
kan zama da Ni’ima ne, ahankali tace “Khaleel wlh karyane kazafi akeso ama Hawwa! Babu wani abu na
Hawwa daban sani ba, Ni’ima so take takashe auren ku, wlh Hawwa bata taba soyayya da Oganta ba,
Hawwa maza tsofaffi ma basa burgeta, sheri ne diyata ba haka takeba, sai kuma abokin aikinta Abraham
tabbas ta sanar dani yaron na bibiyanta shima bawai ya iya yafurta da bakinsa yana sonta ba, ai bata
bashi fuska,

Please Login or Register in order to submit comment