Reading Gargada So By m Shakur Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

auren yazo
za’ayi saidai su tasa yaran agaba suna kyaransu, ana gayama yara bakaken magana, ana gwanzaban su
da addabansu da aure, so yake kije titi ki kama hannu kowani d’a namiji kika gani kikawoshi gidan nan ya
aureki? Bakida samari so yake kije kijawo wani karfi da yaji yazo ya aureki? Maza nawa sukazo gidan nan
neman aurenki dazaran an tsaida magana su gudu so yake kije ki damkosu karfi da yaji suzo su aureki?
Kidnapping na maza yakeso ki fara? Besides duka duka you’re 29 why is he rushing you when bawai
kinkai 50yrs baki auren bane? Wlh banso na amsa Baba ne I know it will look disrespectful saisa kikaga
natashi najaki munbar masa wajen but I can’t take it idan yana miki irin maganganun nan, when he
should be thanking God Allah yabashi diya nutsassiya, kamila, educated and smart dake aiki da ake
biyanta da kyau ta rike masa gida tasa yaransa a school, haba, menene aure? Aure lokaci ne, kuma inaji
ajikina wani jinkirin alkhairi ne, don’t worry everything is going to be okay I’m here for you no matter
what and yarana yaranki ne so kinada yara kinji yadena cewa bakida yara you actually have Yasmeen
and Yaseer yaran Hawwa ne” tai maganan tana ciro Hawwa daga jikinta data fito ahankali idanunta sunyi
jaa kaman ba Hawwa ba tana gyadama Ni’ima kai gwanin ban tausayi tace “da Mamana na raye she
would’ve helped me nai aure, Ni’ima nima nagaji” Ni’ima ta daure cus bataso itama tai kuka takai
hannunta tana share mata hawaye, hannun Ni’ima Hawwa tarike ahankali cikin murya mai sanyi gaske
tace “Ni’ima I’m tired of everything” ahankali Ni’ima tace “I know you are” ahankali Hawwa tace “I’m
tired of yanda mahaifina, the society dana taso ciki and everyone around me suke pressuring dina into
getting married, Ni’ima nadamu I don’t know ko inada wani bakin haline maisa naki auruwa? Maisa kona
fara soyayya saurayi ke guduwa babu wani kwakkwaran dalili? They always come su bani hope and ran
yanzu bamasa zuwa kaman anyi ruwa an dauke, maisa ko an fara maganan aure saisu gudu? Anzo gaban
da ko saurayi daya banda shi yanzu, ba tsoho ba yaro ko me faskare baya shinshinata, bani bawa maza
sha’awa, my sisters kannina dasuka tazo na kula dasu, na goyasu na chanza musu pampers sunyi aure,
all my friends damukai aji daya dasu some nada 5kids ma, what is wrong with me? Ni’ima tell me the
truth maisa nakeda bakin jini? Am I not beautiful enough asoni nima a aureni? İnada wani nakasu ne”?
Ayanda take maganan kasan she’s seriously hurt maganganun su Baba da kowa ma duk sun sami waje
sun zauna a zuciyanta, hannunta Ni’ima takai ta sharemata fuska tace “Hawwa, Best kinga listen to me,
bakida bakin jini, there’s nothing wrong with you that I’m sure, it’s just time…okay, trust me it’s just
time” sake fashewa da kuka Hawwa tayi she just had enough today from Baba, zuciyanta na mata zafi
tace “time? I will be 30 in 2months time, when will the right time comes? Idan nakai 70yrs”? Sheshekan
kuka tayi sosai cikin mugun raunin murya tace “Ni’ima inaso nai aure, nima inaso naga inada miji kaman
kowace matan aure, nima akillace ni agida, I want to have my own husband someone I can call mine,
wanda I will share my soul with, wanda will make sure I eat, I sleep, I’m happy wanda will look after me,
someone I can share my happiness and sorrows with, someone that will hold hannuwana idan ina ciwo
and watch me get better, Ni’ima I’m a woman too, just because I buried damuwata doesn’t mean banda
shi, nagaji da gidan mahaifina I just want to leave naje gidan mijina, I’m so lonely Ni’ima I’m very very
and very lonely, inason aure when will that time comes eh????” Ta kankame hannun Ni’ima tana kuka
dayasa Ni’ima itama hawaye yafito daga idanunta tana kallon Hawwa bakinta na rawa irin na wanda ke
shirin kuka sai kawai ta rungumeta tafara kuka sukahau kuka babu mai lallashin wani, tana kuka Ni’ima
tace “life is not fair to you, you are the most beautiful yarinyar dana sani aduniya, the most intelligent,
your heart is as pure and ruwan dake burtsatsowa daga cikin dutse, I’m so sorry Hawwa you are going
through all this kinji, I’m so sorry don’t ever believe in maganan Baba kan kinyi kwantai bari na gayamiki
all those mazan nan da suka gudu wlh sune sukai loosing precious gem, Hawwa you’re special and Allah
ya ajiyeka for a special man ne only zaki gani, I will hold your hand, stay with you mujira the right man
for my best friend together okay”.

[9/14, 10:07 AM] M Shakur: 💫 GARGADAN SO💫




✍🏻M SHAKUR
EPISODE
1️⃣
2️⃣ 1️⃣2️⃣




JOIN WATSAPP GROUP DINA DANAKE POSTING NOVEL DIN NAN, IDAN KINA GROUP 1,2,3,4,5,6,7
PLEASE DONT JOIN GROUP 8😫

https://chat.whatsapp.com/DvCYR6o87F40OMWr9J8HZL




Ringing da wayan Ni’ima yayi yasa ahankali Hawwa tasaketa tana share fuskanta sannan takai hannunta
tana share fuskan Ni’ima tace “tashi kije Baban Yaseer is calling you” batai musu ba ta tashi tace
“promise you will not cry again” murmushi Hawwa ta kakalo tamata tace “I won’t, wuce kije bari na
shiga wanka nima” gyadamata kai tayi tace “muje tare to daganan saina fita” tashi tayi ta sauka daga
gadon tarage kayan jikinta tadauki zani ta daura a kirji tadauki basket na sponge nata da sabulu suka fito
tare, a pampo dake compound din ta tara ruwa sannan tawuce bayin tsakar gidan tana mata bye
itakuma Ni’ima tawuce waje, sallama sukama Baba suka wuce bayan Baban Yaseer yamai kyautan
kudade sai godiya yake, suka shiga mota yaja motan suka wuce kallo daya yamata yamaida kanshi kan
tuki yace “why did you cry”? Kallonshi tayi saikuma tai shiru sake kallonta yayi ganin the way she’s
worried yasa yamika hannunshi yakama nata yarike yadan matsa yace “wat is it my Baby”? Fashewa tayi
da kuka tace “I’ve cracked my brain Sweedy countless times nakasa gane the exact reason Hawwa taki
auruwa, babu mai aurenta sai su gudu, yanzu for like 2yrs batada saurayi ko guda daya, I don’t know
mesa samarinta ke guduwa, though I know some na neman jikinta itakuma Hawwa will never settle for
that kind of love but ai naga that’s a good thing kasan kamila zaka aura, mesa suke guduwa? Just why
why whyyy?” Dan sauke ijiyan zuciya yayi yasake dan matsa hannunta ahankali yace “stop crying,
Hawwa is a smart woman, I hope next time dazata hadu damai sonta she will make smart choice, come
here” yadan karkato yana jawota kiss ya manna mata agoshi yace “stop crying banso yaranmu suganki
ahaka, I love you” murmushi tamai tace “I love you too mijina” sakinta yayi ya gyara zamanshi yacigaba
da tuki itakuma tadan juya tana kallon waje tace “I wish Hawwa tasami miji as romantic as you are
Baban Yaseer” dan kallonta yayi saikuma ya daukekai yacigaba da tuki batare dayace komi ba, chan tace
“abinda Baba yake is not nice, sai zaginta yake yana mata maganganu duk yan layi naji sai kace ba yarsa
ba, ni wlh ma kaman bayasonta dana sanin haihuwanta yake” dan ijiyan zuciya Baban Yaseer yasauke
tareda girgiza matakai hankalinshi nakan tuki yace “ku mata ne bazaku taba gane halin Baba ba” dasauri
Ni’ima tace “kana ganin haka Babe?” Gyadamata kai yayi yace “Baba na son Hawwa sosai saisa
damuwan nan tamai yawa, kullum lissafinsa da burinsa shine yanda zai aurar da ita, he feels responsible
towards Hawwa sama da duka sauran yaran daya haifa sabida yasan ita marainiya ce, batada mahaifiya
sauran yaransa na nada mahaifiya, da ace Maman su Aminu tadauki Hawwa as her own dukda abin
yazoma Baba da sauki but bata taba accepting Hawwa ba, so shi kadai Hawwa kedashi, kina ganin da
mahaifiyarta na nan da yanzu tayi wani abu akan zancen nan, uwa uwace and mothers can do
extraordinary things to help yaransu, da tana rana da sai inda karfinta ya kare wajen nemawa yarta miji,
part of abinda ke damun Baba also is fear, ya tsufa gashi baida kafa, baison yafadi yamutu bai aurar da
Hawwa ba cus yana ganin zata iya zama haka har abada batai auren ba, he looks at Hawwa as mata da
career path sukai choosing not marriage, bawai bayason aikinta bane kawai he feels aikin nata threaten
men to take her in as a wife, da ace yanada wani source of income ko yanada lafiya ko Aminu yagama
school da tuni yasa Hawwa tabar aikin nan su suyi aikin su nemo su kawo aci, so kawai babu yanda
zaiyine yana lissafi dayawa, don’t be too harsh on him, he loves Hawwa sama da yanda mu muke sonta,
he’s just an old Man so approach nashi might be wrong but look at intention nasa which is a good one”
gyadamai kai Ni’ima tayi dan tunaninta baitaba zuwa this angle da Baban Yaseer yakaita ba, hannunshi
dake nata takai bakinta ta manna ma kiss dan kallonta yayi tai murmushi tace “nataba gayamaka you are
the most amazing perfect husband a duk duniya” gira daya ya dagamata ya maida kanshi hanya yace
“gashi yanzu kin fadama Aliyu” hannunshi takai kirjinta ta rungume tace “bansan menama Allah
dayabani kai ba but you’re just the best thing in my life, we’ve been married for 6yrs bakatabamin abu
dan cusgunamin ba, like banda wani korafi akanka dazan taba iyayi cus you do everything for me, kana
sona kome nakeso u help me to love it and support it, thank you for everything, and thank you for the
money dakaba Baba, I love you Aliyu” murmushi yamata yace “I love you Ni’ima matan Aliyu” ahaka
sukakai gida.



***



GİDAN EXCELLENCY

Bude wani katafaren daki akayi aka shigo, kana ganin dakin kasan dakin yara ne, sabida yanda akai
decorating dakin with dolls teddy, kaman pink Cinderella princess room, zaune yake gaban pink princess
bed yana sanye da tun kayan jiya na jikinshi yakama hannun Noor da aka chanzama kaya aka samata
pink half gown gashinta an warware anyi parking an samata drip a hannu tana bacci yana kallo, ijiye tray
na abincin data kawomai Mommy tayi akan dan pink coffee table dake wajen tazo wajen gadon ta tsaya
daf dashi tareda dafa kafadanshi cikin whispering voice gudun karsu tada Noor tace “Khaleely” gently
yadago kanshi yasauke raunannun idanunshi kan mahaifiyarsa da tana gani tasan bacci ne acikin idanun
sosai, cikeda obsessive love for yaronta ta shafa fuskanshi tana kallon kwayan idanunshi tace “since
yesterday bakaci komi ba, you looked so malnourished, Khaleel ka chanza, ka rame kayi zuru zuru, kasan
if anything happens to you I will die ko Khaleel? Please please muje kaci abinci, I will feed you myself”
tabe fuska yayi ashagwabe zaiyi magana takai hannunta jikinshi ta dagashi tace “yakuri kadaure for me
kaji muje” takama hannunshi zuwa wajen kujeran zaunar dashi tayi ta bubbude komi na tray din chicken
soup da garlic Naan, sai Mandi rice sai coffee, baimason sight na abinci dudda he’s hungry yace “I’m
having just chicken soup” Ba musu Mommy dan lallabashi take ta dauka tace “okay” feeding nashi ta
shigayi tana kallon yanda bini bini yake kallon yarsa ko kadan baida natsuwa tace “asamo maka wasu
matan gobe?” Dan juyo da kanshi yayi yakalleta yana yatsine fuska yace “asamo guda 4 Mommy you
know my spec” dasauri tace “yes I know, Hajiya Daraja ta turomin hoton wasu bari nasa akawomin
wayana kazaba” wani agogon dake daure a writs dinta ta danna” saiga wata mata tana sanye da uniform
ta shigo dakin cikeda girmamawa ta kalli Khaleel da ake bama abinci abaki tace “good morning Sir, Good
morning Ma” ko kallo bata ishesu ba dukansu biyun balle a amsa, Mommy tace “bani wayana” bata
wayan tayi ta karba tawuce tafita itakuma Momy tashiga watsapp dinta cikeda so tace “I want you to be
fine, kadawo Khaleel dinka sak, Noor will be protected babu abinda zai kara samunta, farin cikinka shine
rayuwana, idan banga farin ciki kan fuskanka ba something bad can happen to me” dan murmushi kadan
yayi kaman wani dan yaro yadaura kanshi kan kafadanta yana kallon yanda take danna waya tace “the
audacity da Rahama kedashi na sa ayi kidnapping yarinyar nan using actual criminals shike bani mamaki,
how dare she declare war for my son? Khaleel duk wanda ko wacce tanuna zatayi dakai to dani da
mahaifinka zatayi, dan before anybody yayi going through you must come true us! How dare she?
Menene babu mata ba, we changed her life dana family nata before auren, baka sonta karabu da ita wat
is there? Waya gayamata yarona will ever stay da mace da baiso, Khaleel ko yanzu ka auri wata kaji ta
isheka bakayi kuma zaka iya bata saki ta tafi, da kudinka da gatan ka why would u settle for less? Bayan
you have enough ka auri ko wacce kakeso? Tayi ciki mun dawo da ita nan menene ba’a mata ba? Still
nasa PA na na kiranta every weekend taga Noor suyi magana shine yanzu zatasa ayi kidnapping Noor?
Wat if something yasami Noor dinmu”? Iska mai zafi Khaleel ya fuzar yace “I will make her pay” dasauri
Mommy tace “you don’t have to lift ko finger she will pay tuni aka tafi da ita, kidnapping kadai yanzu
kissa ne a Nigeria, wlh idan zasu yanke mata hukuncin kissa we will not intervene let the law take it
course, ko family ta bazan attending to ba infact they’re not even allowed suzo ta premises na estate
namu, just relax and stop thinking about that babu abinda zai kara samin Noor” ta shiga chat nata da
Hajiya Daraja tabude hotunan yammata ne kusan goma, dasauri tamikamai wayan tace “gashi ka kalla
kaga” yatsine fuska yayi ashagwabe yace “just show me Mommy” dasauri tace “okay okay” ta shiga
dannawa tana nunamai, yammata ne lafiyayyu hadaddun gaske yana kallo duk yanda sukekai ga kyau
but ko irin yanuna kosawa ko wani abu ya burgeshi dasu baiyiba cus yaga wanda suka fisu ma, some of
them models ne, wasu kuma all this Abuja big girls, harta gama nunamai all the pictures bai zababa
Mommy tace “baka zaba ba? Anyi examining nasu basuda wani matsala ko tabo ajiki perfect like dinka,
matan dazaka huta dasu ne kasami natsuwa” tashi yayi daga kafadan Mommy awani gajiye yadauki glass
cup yasha ruwa ya ijiye sannan yatashi yace “Momy select 4 acikinsu you know my spec,” murmushi
Mommy tayi tabi yaron nata da kallo tanaji kaman ta hadiyeshi yawuce yahau gadon Noor ya kwanta
kusada ita yana sata ajikinshi ya kankame sosai sannan ya sauke ijiyan zuciya tareda lumshe idanu sai
bacci.



[9/15, 9:58 AM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫
✍🏻M SHAKUR




EPISODE
1️⃣
3️⃣ 1️⃣3️⃣



JUZZYFABSEVENT BUSINESS NE DAKE BAMA MUTANE SERVICES NA

Event Decoration and catering service for all types of events such as weddings, corporate events,
Naming ceremony, birthdays, etc.

CONTACT THEM SUBAKI THAT YOUR DREAM EVENT HOSTING😍



*Muna abinci mai inganci da dadi both Nigerian dishes and continental dishes*

Instagram: @Juzzyfabevents



chat them up now

wa.me/+2347032644814




Ijiyan zuciya Mommy tasauke ganin yayi bacci finally, wayan ta kalla tayi selecting mata guda 4 a
hotunan sannan ta tashi tadauki tray abincin ta kashe wutan dakin sannan tabude kofan ahankali karyayi
kara tafice, tana fitowa ma’aikatan dake tsaye gaban dakin suka amsa tray sannan tawuce dakin
Excellency dayake zaune yana waya yana ganinta yace “yaci abincin” murmushi tayi tace “yaci sosai
amman saida nayi da gasken gaske” dasauri yace “Alhamdulillah Alhamdulilah wai har hankalina ya
kwanta, I think we should organize party for him ko ya kikagani Madam”? Dasauri Mommy tace “yes
idan an kawomai matan gobe I think we should organize it gobe ya yarda na zabamai 4, bari I will call
Sameer duk suzo” jinjina kai Abba yayi yace “yauwa Alhamdulillah yarona ya saki, lemme call Barrister
yayi all the paper work for the brides” hira suka shigayi abinsu suna murmushi.
Ahankali yake bude idanunshi dakin duhu tashi yayi ya zauna yana tattaba gadon, wayanshi yataba
hakan yasa yayi haske yadauka yaga this is 4PM na yamma haska gadon yayi ganin babu Noor ga drip
dinta yakare yasa yatashi da sauri yace “Noor” yayi kofa da sauri yana bude kofa masu gadi biyu dake
jikin kofan suka zube kasa. “Good evening Sir” adan birkice yace “where’s Noor?” Atare sukace “she’s
with her grand parents, Hajiya tace idan katashi kayi wanka kasamesu a garden” dan yatsine fuska yayi
tareda sauke ijiyan zuciya yawuce yana tafiya ahankali dan har yanzu akwai bacci a idanunshi yawuce
wani sashi daban still acikin flat din wanda nan ne bangarenshi, kana ganin side din kasan kaman kowa
na gidan worship him ne sabida tsabagen kyawun side din, daga nan falo akwai bene akwai lift dazai
kaishi sama, lift din direct yawuce ya shiga ya kaishi sama, bedroom nashi ya fada da zaka dauka sarki ke
zama ciki yafada bayi alwala yayi agurguje yafito yayi salla sannan yatashi ya chanza kaya zuwa shorts
baisa rigaba kirjinshi kaman zai fashe tsabagen cika yafito yabude wani daki gym ne yahau kan treadmill
yafara gudu na bala’i na kusan 30min sannan yadaga weights daban daban suma na 30min sannan
yatashi yana share zufabn dayayi da towel yafito yakoma daki wanka yayi yafito agogon bangon dakin ya
kalla he needs a woman jikinshi na gayamai hakan, shiryawa yayi cikin 3quater da bakin t-shirt sai
kamshi yake yashiga saukowa wannan karan stairs yabi yana fitowa ma’aikata biyu suka shiga dakin aka
shiga tattare tundaga bayin dan hatta boxer daya cire yana kasa cus he’s so disorganize jikinshi kadai ya
iya gyarawa garden yawuce.



Tundaga nesa ya hango Noor jikin Mommy tayi lamo dudda she’s fine but she doesn’t look happy, hango
Khaleel yasa Mommy tace “to ga Dady ki nan yafito mayyan Dadyn ta, sabida nahanaki kada ki tasan
mini d’a dabai sami bacci ba yau kwana nawa kike kumbure kumbure” dasauri ta dago kanta ganin
Babanta yasa tawani sakko daga jikin Mommy ta kwaso da gudu Khaleel yabude mata hannu yana
murmushi baiyi wata wata ba ya dauketa yace “my Princess” cikeda murna yarinyar tace “Dady who
were those bad people? I was scared Dady, I slept on the floor it was cold, I couldn’t eat anyfood, tea
kadai nake iyasha Dady, but that fine Anty saved me, ta goyani Dady, Dad she’s my superwoman ko, she
said her name is Fairy Angel Anty” tayi murmushi tana nunamai hannunta da aka cire kanula tace “Dad
zapiii” hannun ya karba ya kalla yace “sorry zai dena my princess” murmushi tayi ta manna mai kiss a
kumatu tace “Dady I love you” murmushi yayi sosai kaman bashiba yace “Noor Dady loves you too
much” tsalle tayi ta sauka daga jikinshi tana clapping hannunshi ya mikamata da sauri tasa nata aciki
yana rikeda ita suka wuce suka zazzuna atare sukaci abinci tana jikinshi.



Kusan 1hr suna zaune a katafaren hall din da aka sasu kusan mutane 20, sai kalle kalle ake awajen, bude
kofa akayi PA Mommy ne tashigo rikeda wasu files tareda wani military bodyguard biyeda ita, tsit dakin
yayi tace “good afternoon everyone” sannan ta shiga binsu set by set each set 4 people ne, Baba, Mama,
yarinya, da waliyi, tana ijiye file agaban each set sannan takoma gaba ta tsaya tace “agaban ku
agreement ne da Lawyer mu yayi drafting, already nasan Hajiya Daraja tamuku bayanin komi, wannan
aure ne da no need kuma sanar da yan uwanku cus dazaran yallabai yagaji da mata yake rabuwa da ita
but you can rest assure baza’a taba cutar da yaranku ba saima dumbin benefit da auren yake tattare
dashi dan this is life changing opportunity auren yaron richest man in Africa, and number 5 richest man
in the whole entire world, you all are here for money and zaku samesu” tai dan shiru tana kallon yanda
kowa ya natsu yana kallonta tace “some of sharrudan mu is koda wasa bamu yarda labarin auren nan
yafita ba ko bayan an rabu, yallabai bayason damuwa ko matsala kawai shi mutum ne maison hutu,
should incase yarku tayi ciki munason yara zamu amsa but yarinyar ko yaron da za’a samu batada wani
alaka da mahaifiyarta, kusan da wannan, idan kunada wata bukata ku rubuta bayan kun karanta kuyi
sigining files dana baku azo adaura auren zakuji alert immediately after” jikinsu har wani rawa yake
kawai signing suke duk ta amamsa tafita ba’a jimaba wani malamai biyu suka shigo da more bodyguards
a hall din aka daddaura aure suna biyan sadaki miliyan goma goma each aka shafa matan sukai sallama
da iyayensu PA tazo tai gaba dasu iyayensu suka fice hankalin kowa akwance iyayen na fatan yaransu su
sami juna biyu.

Clinic sukaga an wuce dasu dudda already daga ta wajen Hajiya Daraja an musu test but saida aka kara
musu har pap smear akai clearing nasu sannan akadauki kowacce akakai lafiyayyen bangare da ita.



Yana zaune tareda Noor dake saman jikinshi tana wasa da wayanshi wanda tasaba tafison wayan
Babanta kan duk wani iPad da laptop da phones nata dan babu wanda bata dashi aka shigo dakin daga
kai yayi ganin wani hadadden guy ne yashigo da kansu ke kusan daya da Khaleel, ga kitso akanshi yayi
locks da gashinsa, Noor tace “Hi Uncle Sameer, some bad people took me away but one Fairy Angel Anty
with my Dady rescue me, and Fairy Angel Anty tagoyani abayanta” Dasauri Sameer yazo wajen ta tashi
dasauri tana nunamai hannunta daya kumbura ashagwabe tace “Uncle Sameer my hand it’s hurt” cikeda
so yace “sorry Special Noor, mezan siyamiki that will take the pain away”? Murmushi tayi tadan juyo
takalli Khaleel dake kallonta kuri tace “Dady will get angry yaji, bring your ear” dasauri Sam yabata
kunnenshi tace “sugar cube” zaro idanu Sameer yayi arayuwan Noor tanason sugar cube gidan gabaki
daya an dena amfani da cubes na sugar saidai sugar powder sabida Noor cus zata iya shanye kwali daya
aka batta, dan dariya Sam yayi shima yagaya mata a kunne zaizo ya kaita su sayo, tsalle tafara tana
dariya tace “you are the best Uncle” tayi kofa da gudu Khaleel yabita da kallo tafice sannan Sam yace
“Hey Cousin” watsamai mugun kallo Khaleel yayi Sameer yakama hannunshi yace “sabida kai I just had
to leave everything nazo ko gida banje bafa, I just landed nazo nan straight Mommy da Pops suka sanar
dani meke faruwa i was angry ba’a sanar dani ba since, shine wai they’re throwing party for you nazo
and invite all our friends, please ya akwai babes”? Sharesa Khaleel yayi cus haushinsa yakeji, Sam yace
“kai nai mistake banje da Babe dina this Shanghai danaje ba kumani banson matan china wlh, na wahala
saisa nabi available flight nataho, kai you’re so lucky shege nawa kowa kakeson ci har gida za’a kawo
kubiya kudi a daura aure kaci, but why marrying her though? That’s abinda nakasa ganemaka see if I
want 100 babes yau zan samosu and do whatever I want dasu wats the point na aurensu bayan nasan
wasa kawai nake” dan yatsine fuska Khaleel yayi cikeda iskanci yace “cus marrying those desperate
creatures is fun! And I love fun!”.

[9/15, 9:58 AM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫
✍🏻M SHAKUR




JUZZYFABSEVENT BUSINESS NE DAKE BAMA MUTANE SERVICES NA

Event Decoration and catering service for all types of events such as weddings, corporate events,
Naming ceremony, birthdays, etc.

CONTACT THEM SUBAKI THAT YOUR DREAM EVENT HOSTING😍



*Muna abinci mai inganci da dadi both Nigerian dishes and continental dishes*

Instagram: @Juzzyfabevents



chat them up now

wa.me/+2347032644814




EPISODE
1️⃣
4️⃣ 1️⃣4️⃣




Ihu Sameer yayi yace “shegen yaro like en u can have duk wacce kakeso in this world” dagamai gira daya
Khaleel yayi irin of course kana ganinsu kaga yaran masu kudi da basusan darajan komiba kawai shirye
shiryen Party suke abinsu.
Wuraren 10 nadare Party yafara, lafiyayyen exclusive party akeyi wanda sai yaron dayakai zai iya
attending, anata having fun, ga mata, ga giya ga music ga food daban daban su azul ga shisha, ga
securities na patrol suna gadin yaran.



Mommy da Excellency ne tsaye ata window dakinsu suna kallon Khaleel dake waje, the way he’s just
smiling hannunshi rike da pipe yanashan shishi yana magana da few friends idanunshi na lumshewa
yanadan dariya yasa hankalinsu ya kwanta, Excellency yakalli Momy yace “thank you Madam” yajawota
yana kama kafadanta yace “idan Khaleel naganshi yana farin ciki haka sai hankalina ya kwanta kinsan
kwana nawa yau nakasa paper work? Nakasa attending meetings dina, rayuwana tsayawa chak yake
because of Khaleel” Mommy tace “wlh nasani Husby but worry no more yariga ya soma warwarewa,
bari naje naduba Noor tayi bacci since, sainaje wajen duba gyaran da akema yarinyar da za’a kaimai
kafin yashigo” dasauri Excellency yace “okay” fita tayi Noor taduba dake bacci peacefully sannan tawuce
wani daki da aka rubuta spa ajiki kai tsaye ta shiga jiki, professional masu gyaran jiki guda biyu ne ke kan
wata yarinya dabazata wuce 25yrs ba cikin wani pool na madara suna hada kai da Momy tasauke kanta
kasa da sauri jikinta har bari yake tace “ina yini Ma” PA Momy takalla hakan yasa PA tace “ke fito daga
ruwan” adan kunyace yarinyar tafito takai hannunta tana kare kirjinta tana harde kafafunta PA tace “ki
sauke hannunki ki tsaya da kyau” kanta akasa ta sauke hannunta ahankali tana gyara tsayuwanta daga
sama zuwa kasa Momy tamata kallon wulakanci sannan tace “she’s okay” tajuya tafito itakuma aka
komar da ita ruwan, Momy tawuce tazauna afalo aka kawomata shayi tanasha takalli PA tace

Please Login or Register in order to submit comment