Reading Gargada So By m Shakur Chapter 15 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bacci har zuwa 4 na yamma but yakasa baccin tunanin yarinyar chan kawai yake, kaman
her sick spirit na kiransa, hannunshi yadaga yakalla da Hawwa ta ciza lumshe idanu kawai yayi yabude
sannan yatashi zaune yasauka daga gadon, boxer yacire ya yar awajen yawuce abinsa naked yafada
bathroom yayi wanka yafito yawuce walk in closet dinshi dake kama dawani exquisite boutique,
shiryawa yayi yazaro Balmain monogram print flowing shirt dakeda kalan black print din kuma white
yasaka, yadauko dogon denim wando na Diesel yasaka daya zauna ajikinshi da kyau dasdas, agogonshi
yaciro from drawer na designers watch dinshi, yacire Furlan Marri yasaka dayama hannunshi kyau,
yadan juya yakalli showglass na takalmansa kaman shago yasa hannu yaciro wani suede flat takalmi na
Birkenstock Boston, sannan yadau turarukanshi yashiga fesawa yadauki brush yana taje kansa ya
shimfada dadduma yayi sallan azahar sannan yamike yabude kofa yafito yasauka kasa, chan falo yayi
yana kallon agogon hannunshi is 1:30 ba kowa afalo probably Mommy ta kwanta ko tana spa nasu ana
mata massage, kofa yawuce aka budemai yafita wajen black Mercedes Maybach S class dinshi yayi dake
kyalli tsabagen kyau da kudi, da sauri security nashi suka taho wajen yakalli Salman dake budemai motan
yace “when did you come back?” Dasauri yace “not quite long Sir everything is sorted babu wani
matsala motanta I called auto shop sunzo sun dauka har an fara gyaransa” yatsine fuska yayi kadan
baice kome ba ya shiga bayan motan ya zauna, Salman ya maida kofan yarufe yakoma gaba yashiga ya
zauna driver shima na shiga mopol dinshi ma haka, anatse yace “hospital” Dasauri driver yace “yes sir”
yatada motan suka fita yana kallon hanya chan yace “music” waka aka samai yafarabi yanadan shaking
kai yadaga wayanshi yayi selfie yasa a instagram story nashi hankalinshi kwance.



*

Kansu Ni’ima tayi da plastic chair data dauka dasauri Baban Yaseer yajuya yana sauke Hawwa agadon
yajuyo yasa hannu da zafi zai karbe kujeran ta zame tai gefenshi zata rafkama Hawwa dake kallon Ni’ima
completely heart broken Baban Yaseer yabude hannuwanshi ya tsaya agaban Hawwa, Ni’ima tace “kama
rungumeta idan zakayi amman saina halakata, saina halakata wlh, Allah ya kasheki ya dauki ranki sai inga
wazakaso Aliyu? Inaso naga ko zaka bita kabari kuyi soyayya, ba sumbatar juna kukeso kuyi ba kuka
ganni kuka wayance? Ka tashi agabana” hannu daya Baban Yaseer yasa ya fizge kujeran daga hannunta
yana kokarin ijiye chair a gefe tabi gefenshi zatayi kan Hawwa taji an riketa gam juyowa tayi daidai Ammi
na dauketa da mari jikake tasss! Hawwa ta zabura tana kokarin mikewa ganin yanda Ammi ta zubamata
mari but takasa tashi, Ni’ima ta dafe kuncinta tana kallon Ammi da jan idanu, Ammi tace “kika kara
maganan banza anan saina sake daukeki da wani marin shashasha” Ammi takalli Baban Yaseer dake
tsaye yana kare Hawwa cikeda fushi tace “tashi agaban yarinya na bar wajen nan, tashi nace!” ba musu
yatashi ahankali yakoma wajen kofa ya tsaya ranshi in yayi dubu yabaci sabida abinda Ni’ima keyi, Ni’ima
takalli Ammi idanunta jajir har lokacin kallon Ammi take tace “kika mareni Ammi? Ko uwata bata taba
bari naba saike”?Ammi na kallonta jin maganganun datake rai abace tace “saisa ni nake tayata bawa
diyarta tarbiya, kika karamin gara gara anan saina sake daukeki dawani marin, you’re very, very and very
stupid Ni’ima hauka kikeso kiyi sabida namiji? Eh?” Shigowa Baba yayi zuwa wajen ya tsaya kusada
Ammi babu alamun wasa akan fuskanshi yace “meke faruwa Zainab”? Ni’ima Ammi ta nuna tace
“Malam Ni’ima tana daya daga cikin dalilan dayasa Hawwa kenan wajen” azuciye Ni’ima tace “menayi?
Nakira yarku na yanke alaka da ita, naja mata layi, bansonta arayuwana dayake mayya ce, bakar mayya
mara zuciya ce ita wacce tai kwantai haka ta dinga bina tanajan gwuiwowinta akasa tana rirrikeni tana
kuka tana karna rabuda ita, nikuma na tattake hannuwan banzan nawuce nayi tafitata” sosai Baban
Yaseer ke kallonta hakama Baba da Ammi yanda take magana kaman ba Ni’ima ba, can a sweet person
turn monster over night? Sabida namiji? Ni’ima tace “mijina nawane kadai wlh, ba best friend ba ko
kanwata ce saina jamata layi wlh, kugayama yarku tafita daga harkan mijina” nuna Baban Yaseer Ammi
tayi tace “ga mijin naki nan ai shiya kawo kanshi nan, dau abinki kubar nan” cikeda rashin kunya tace “eh
zan dauki abuna amman saina gama, yar iskan yarku kokarin sumbatan mijina take, mara kamun kai da
natsuwa, Hawwa zata iyama maza fyade sabida tsabar bukat……” tsawa Ammi daka mata tace “Ni’ima!”
Rai abace sosai tace “nasan waye Y’ata! Jedai ki bincike mijin naki, munsan kalan tarbiyan da muka bata”
ganin Ni’ima zatai magana tabi Ammi da chachan baki yasa Baba yakalli Baban Yaseer strictly yace “Aliyu
dauki matarka kutafi, mungode Allah saka da alkhairi” cikeda tsantsan rashin kunya Ni’ima tace “ba dole
kace ka gode ba anci kudin mijina an koshi, yazo yabiya kudin asibiti da kudin magani, mayu kawai
kwadayayyu masu neman kai da yars……” fizgota Baban Yaseer yayi yajuyo da ita tai facing nashi ganin
abin nata yazama hauka yadaga hannu zai kwasa mata mari Baba yace “kul!”




Washegari Sunday around 11 tafito su Hamza na samata komi a booth, Baffa yace “Hawwa ayi tuki
ahankali kinjini” murmushi tayi tace “toh Baffa na” Ammi tace “Allah kiyaye hanya, dan Allah banda
gudu” Gyadamata kai Hawwa tayi su Ramla suka rungumeta tamusu sallama tafito, text tama Ni’ima
tace “gani nashiga hanya zan dawo office gobe”.



Karfe biyu dawani abu anadai neman karfe uku Hawwa ta shigo Abuja hanyan hospital din su Ni’ima
tawuce direct ta shiga tai parking ta kashe motan, wayanta tadauka tafito abayane ajikinta baki tawuce
ciki office din Ni’ima tawuce tareda knocking tana budewa wata nurse ce aciki tana ganin Hawwa tai
murmushi tace “wajen Ni’ima kikezo? Bakuyi wayaba ai batanan yau is her off” amutunce Hawwa tace
“okay okay nagode” tajuyo tafito motanta tashiga tafita daga hospital din wlh she’s so worried rabon
datai magana da Ni’ima tun Friday wani irin fushi Ni’ima keyi da ita haka, hanyar gidansu Ni’ima tayi har
zuwa layinsu mai kyau, gaban gidansu ta tsaya tai horn maidaidaicin gidane mai kyau ga babban bakin
gate nasu, lekowa mai gadin yayi Hawwa tadanmai murmushi tana jiran taga yabude gate saitaga
yabude karamin gate da fara’a kan fuskanshi yace “Hajiya barka da yamma” gyadamai kai tayi tace “ya
kuke” yace “Alhamdulillah” saikuma ya tsaya sakaka yana kallonta Hawwa tace “budemin gate ko
basanan ne”? Bazai taba iya maimaita abinda Ni’ima tacemai ma hakan yasa dasauri yace “eh basanan
tun safe suka fita” danjimm Hawwa tayi kaman daga sama sukaji muryan Yasmeen ta tsandala ihu tana
kuka wayyo kafanta dasauri maigadin yakalli gate saikuma yajuyo yasauke kanshi kasa, Hawwa dake juyo
muryan yaran tace “kace basanan ba muryan Mims naji na kuka ba” dan sosa kai yayi da hannu kanshi
na kasa yakasa kallonta yace “ahhhmm Madam tacemini duk randa nakara barinki kika shiga gidan
abakin aikina kiyakuri Hajiya” dasauri da kunya yajuya ya shiga gidan tareda maida gate din yarufe
Hawwa tai shiru tana wajen she don’t even know wat to think, her mind just went blank wlh takai minti
ashirin awajen kafin tadan fuzar da iska taja motan tabar wajen.

[9/23, 8:52 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫




✍🏻M SHAKUR




EPISODE
3️⃣
7️⃣ 3️⃣7️⃣




Kusan 5min Khaleel da Baba sukai ahaka sannan yadaga kanshi daga kafadan Baba yakalli Baba yace
“kahuta? Kadena damuwa”? Gyadamai kai Baba yayi yace “nahuta Ibrahima” sauka Khaleel yayi yadauki
crutches din yabashi Baba ya karba suka fito tare, Ammi bata wajen hanyar dakin sukayi Khaleel yaci
tura dagadan nesa Baba yajuyo yakalleshi yace “bazaka shiga ba” dan sosakai yayi saikuma ya dauke kai
ahankali yace “uhmmm kunyan nakeji” dariya Baba yayi irin na manya dinnan jin maganan dayayi yace
“kunya? Wai kunyan Ammi”? Dasauri Khaleel yajuya yana gyadamai kai yace “bye Baba sai munzo
anjima” kafin Baba yayi magana har yayi kofa su Salman dake wajen suka budemai kofa yafice suka bishi
Baba yace “jama’a wannan yaro akwai shiga rai, Ya Allah inama Hawwa na kwadayinsa sosai, Allah inhar
alkhairi ne auren nan kasa ya tabbata yau” yayi maganan a yana shiga cikin dakin da murmushi kan
fuskanshi yayi inda Hawwa take dake bacci anmata allurai da dama, Ammi na zaune ta buga tagumi
ganninshi yasa Ammi takalleshi da damuwa akan fuskanta, Baba yajuyo yaja kujeran plastic chair ya
zauna cikeda farin ciki yace “kidena damuwa Zainabu kiyi addu’a inhar Ibrahima rabon Hawwa ne kuma
mijinta ne yau za’a daura mata aure” dasauri Ammi ta kalleshi tace “waye kuma Ibrahima Malam”?
Labarin Khaleel yashiga bata all abubuwan daya sani, tai shiru Allah yasani yanda taga Khaleel yayi da
Baba taji ya burgeta, banda haka Ni’ima said some disturbing about Hawwa, ita mace ce, sannan ita
uwace, ko yara irin su Ramla sunsan sha’awa yanzu, Hawwa ba yarinya bace, babu bawa da baida
sha’awa, tanaso Hawwa tai aure ta sami natsuwa da kwanciyan hankali, ba maza Hawwa kebi ba, bata
iskanci so dole ne a irin shekarunta taji yana bukatan namiji, tabbas Hawwa na bukatan natsuwa, abun
yamata, 50/50 Ammi keji azuciyanta, one side na zuciyanta ya goyi bayan auren sabida abubuwan da
Ni’ima tafada especially bukatun Hawwa kafin yarsu tafada halaka, kota kauce hanya amata auren,
zuciya ba kashi bane tsokace duk yanda takai da karfin imani shedan zai iyacin galaba akanta wata rana
idan takasa hadiye sha’awar, another bangaren zuciyanta kuma zaiso ayi bincike akan koma waye
Ibrahiman but idan aka tsaya bincike kafin agama yaron yagudu ko yace yafasa fa? Cus abinda ke faruwa
kenan dazaran sunzo su gudu, yagudu yaushe Hawwa zata kara samin wani yafito ga Ni’ima ta tasata
agaba? Sotake tai aure tai nisa da anguwan ta huta da bakin cikin Niima, she kind of reason with Baba
sabida yanda samari ke guduwa gwara su kama Khaleel dinnan as earlier as possible, zata taya Hawwa
addu’a Allah ya albarkaci auren ya kauda fitina su sami fahimtan juna, amman dai tai auren Hawwa na
bukutan natsuwa kafin tafada wani hali, ganin tai shiru tana tunani yasa Baba yace “kin yarda Zainab?
Dan banso mukara fada yanzu komi yawuce, ni da kene iyayen Hawwa, banda mu batada kowa, ada nai
kuskure dana dinga bala’i dake, gayamin abinda ke ranki dan hukuncin nan tare zamu yankewa yarmu”
murmushi Ammi tayi jin yanda Baba ya girmamata yabata matsayi yakuma karramata, anatse tace “na
yarda Malam, nakuma aminta idan Alkhairi ne Allah yasa su dawo adaura idan ba alkhairi bane kuma
Allah ya musanya mana yabata miji da gaggawa” Baba yace “Ameen Ameen” yana murmushi suka
cigaba da hira, abinci aka kawo musu akace an riga an biya kudin abincin duk sukaci Ammi takira Ramla
tace kartai girki, tabama Baba wayan Hawwa tace “Malam kira wajen aikinta ka sanar dasu tayi hatsari”
Baba yace “nemomin number kaman DIG naji tana kiran Ogan nata duba kiciromin number” Ammi ta
karba tana ciromai.




WAIWAYE BAYA KADAN..!




Ana fitar dasu waje har parking space aka kaisu aka tsaitsaya akansu kaman barayi, Salman yace “you
have 10secs to leave this hospital else we hand you over to police and press charges against the both of
you, we have cctv camera in every corner of this hospital starting from patient room” kallonta Baban
Yaseer yayi yanda take kallonshi tana haki, ranshi ya baci iya baci da abinda tamai, baitaba sannin this is
who Ni’ima is ba sai yau, cikin kakkausan murya yace “daganan kiwuce gidanku, namiki iyaka da gidana
zankira mai gadi na shaidamai kada ki shiga gidan nan, kije na sakeki saki daya!” Faduwa gabanta yayi
sosai zatai magana kawai yabude motan yashiga yawuce tabishi da kallo kirjinta na bugawa, Salman
yadaka mata tsawa. “Madam leave our hospital!” Jikinta har rawa yake ta wuce ta shiga tata motar ta
kunna tabar asibitin.



School nasu Yaseer yawuce direct ranshi na suya ya daukosu yace zasu danyi tafiya na 2week, sukaje
gida yahada kayansu tundaga kansu Ipad yasasu a mota kawai sukai Kano gidan iyayenshi sukaje
yakaima mahaifiyarshi yaran sunata murna yace suyi kwana biyu yasayo musu komi washe gari yabar
Kano da sassafe danso yake yaje yaga Baba he made up his mind zai auri Hawwa yanzu, he wants to
make her his wife.

****

[9/23, 8:52 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫




✍🏻M SHAKUR




EPISODE
3️⃣
6️⃣ 3️⃣6️⃣




Chak Baban Yaseer ya tsaya sabida yanda Baba yahanashi, Baba na kallonsu yace “ba’a dukan mata barta
da halinta kutafi kawai, Ni’ima karki damu babu ko biyar na mijinki a asibitin nan, kutafi Aliyu” kunya ne
yakama Baban Yaseer kaman kasa ya tsage yashiga ciki, yajata da karfi yace “let’s go” tutturjewa take
tana kallon Hawwa dake zaune abakin gadon gwanin ban tausayi tana goge hawaye dake zubomata da
sun kasa daina zubowa, Ni’ima can’t even describe yanda takejin tsanan Hawwa kawai so take ta mutu
atleast idan ta mutu zata huta, Baban Yaseer zai natsu, ina jitayi bazata iyaba a haukace ta fizge
hannunta kaman mai ciwon hauka ta taho tace “Wlh wlh saina kasheki banga dalilin da mijina zaifi sonki
akaina ba, yana kirana dakikiya sabida ke ba, he’s telling me kinfini komi” kawai Ni’ima tai kan Hawwa da
sauri Ammi ta zauna tana kama Hawwa zuwa jikinta dake sheshekan kuka ahankali dabai fita irin hurtful
cry dinnan dayake fita daga soul naka, azuciye Baba ya tare Hawwa da Ammi yakama karfenshi daya a
hammata gamgam yazare daya yarike a hannu yadaga sama, daidai Baban Yaseer na kamata tana ihu da
karfin gaske, Baba yace “Idan ban miki karatun Alam nashara da karfen nen ba ba sunana Baba ba,
hauka kikeyi ne? Nace hauka kikeyi ne? Ni’ima kin haukace ne? Kinmanta kawarki dakuke zuwa wajena
nabaku kwandala kwandala na siyan alawa? Ni’ima Hawwa fa dakike fushi dani idan na bata mata rai?
Sabida miji Ni’ima kikema kawarki fatan mutuwa? Ina amintan? Ina kauna da soyayya ina? Ina zumunta?
Duniyan nan duka duka guda nawa take? Dudda ina nemawa y’ata miji har ina bada sanarwa a masallaci
mesa bantaba mata kwadayin mijinki ba? Kin taba tunanin maisa ban ma Aliyu tayin Hawwa ba? Sabida
nasan ayanda y’ata ke sonki bazata taba so ta auri mijinki ba! Nima bazan taba kaunar ku lalata
zumuntan ku ba! Ni’ima haukacewa kikeso kiyi ne? Kunfi shekaru ishirin kuna tare meyayi zafi haka?
Auren Aliyun tayine menene haka? Bakida lafiya a kwakwalwanki ne”? Tana kallon Baba tana fizge fizge
da Baban Yaseer tace “eh hauka nakeyi Baban Hawwa! Akan Aliyu zan iyafin hakama haukacewa, yarka
ta kiyayi mijina kawai kagaya mata, ta kiyayeshi!” kallon Aliyu Baba yayi yace “Aliyu dudda bansan ko
Ni’ima ko wacece wannan ba amman dauketa kubar wajen nan kar raina yabaci” daidai lokacin some
Doctors da Nurses da security na shigowa dakin, senior consultant dinsu yace “what is going on here?
This is hospital not arena, why are you all traumatizing my patients? Everyone outside” Fizge hannunta
Ni’ima tayi kaman mahaukaciya tana kallonsu tace “sakan mini hannu” takalli likitocin tace “patient
dinku tai kwantai batai aure ba, ubanta gabaki daya yagaji da ita har tallanta yake gida gida lungu lungu,
shine yanzu suke kokarin a manna ma mijina ita” Dr yakalli Baban Yaseer dake faman riketa yace “Sir I
know you are a Muslim and bazaka so nasa security maza su dauki matarka ba, nabaka 30secs idan baka
dauketa kun fitaba zansa maza su fitar da ita this is hospital not wrestling arena, munada patients
dayawa dakuke tayarma da hankali, we can sue her for this, please kindly take her out” Aliyu da kunyan
dubiya yasa jikinshi ma yayi sanyi yakai hannu zai dauketa ta fizge tareda tureshi takalli Hawwa dake
kallonta idanunta sunyi jajur sabida kuka tanuna kanta tace “mijina zakibi Hawwa? Mijina? Wlh wlh
saidai ki mutu ko nida ke mu mutu tare daki auremin miji” tana maganan tai wajen gadon Dr yama
security guys magana sukai kan Ni’ima suna tareta suka rirrike mata hannuwa Ni’ima tafara ihu na boo 👻
mutum tace “jama’a azo aga husband snatcher, wacce bakin halinta yasa for almost 30yrs babu wanda
ya aureta, ubanta ma yagaji da ita neman kai yake da ita, infact yar iska ce, amfani take da kanta da
daddare sannan take iya bacci, nitake kira ina bata maganin rage sha’awa kullu yaumin, aure takeso
idanu rufe, da ace tanada mashinshini da tuni tabi maza sabida yanda takeda bakin jaraba, Hawwa harija
ce duk dare saitai kukan neman namiji” wani irin nishi Hawwa tafara jin yanda Ni’ima ke tona mata asiri
da karya da gaskiya zuciyanta yafara bugawa da karfi security sukai waje da Ni’ima, Ammi na ihu ganin
yanda Hawwa keyi “Dr something is wrong with Hawwa na Innalillahi” akai kan Hawwa ana sa Baba da
Ammi su fita waje.

A reception Ni’ima tacigaba da ihu mutane na taruwa patients na fitowa daga daki suna lekowa aga
meke faruwa, kaman ba ita ake jaba tana nuna Baba da Ammi dasuka fito suna kallonta tace “wazai
taimakama tsohon nan ya auri yarsa datai kwantai ba miji? Bai bama yarsa tarbiya ba sabida ciyar dashi
datake yasa maza ke tsoron aurenta, itace komi nashi babu abinda yake tsinanawa sai gulman yan
anguwansu, kunsan yarsa har gayu takeci tasa janbaki kowani zai ganta yace yanaso amman shiru babu
machinchini” “get this mad woman out of this hospital!” Sukaji muryan Khaleel dayasa kowa yajuyo har
Ni’ima da Baban Yaseer daidai Khaleelna saukowa daga staircase, tundazu yana asibitin nan but yana
office dinshi asama, karasowa yayi yana tafiya daidai kaman sarki ya tsaya daidai gaban Baban Yaseer
dake kallonsa batare daya kalle kowa na wajenba sai Baban Yaseer din yace “take this mad woman and
this photo husband of hers out of my hospital and duk randa nakara ganin any of them in my hospital I
will fire tundaga gate workers to workers na reception din nan!” Yayi tsawan da saida wajen ya dauka,
kawai Baban Yaseer yaga exra security na zuwa aka rikemai hannaye both side kaman baraw idanunshi
cikin na Khaleel dake kallonshi irin kallon sworn enemies dinnan kawai aka jashi har sukakai wajen kofa
kallon Khaleel Baban Yaseer yake sannan aka fitar dashi da matar tasa….



Suna fita Baba kawai yaji jiri na dibansa yayi baya zai fadi dawani irin sauri Khaleel yazo wajen yatareshi
ahankali yace “Baba!” Kallonsa Baba yayi ahankali, ganin hawaye na tsatsowa a idanun Baba yasa da
sauri yakama hannun Baba yasa akan kafadanshi ya karbi crutches nasa daya yamikama Salman sannan
yawuce da Baba yana dinginshi zuwa wani office dake wajen Ammi tabisu da kallo tana mamakin waye
mutumin nan?.



Zaunar da Baba Khaleel yayi kan gadon dakin Salman yashigo yabashi crutches din ya karba ya ijiye
yawuce yafita sannan yadawo wajen Baba stethoscope dake office din yadauka ya makala a kunne
sannan yadauki abun auna BP yazo wajen gadon yadan kalli Baba in very cute and dan shagwaba voice
yace “Baba don’t pay attention to whatever she says” yashiga auna BP Baba duk Baba yana kallonshi,
chan ya saurari pulse nashi da heartbeat sannan ya ciccire komi yace “jininka yahau kadan a little sleep
da magani will help zansa akawo ma” yajuya zai fita ahankali Baba yace “Ibrahima!”Juyowa Khaleel yayi
ahankali babu wanda yataba kiran sunanshi ahaka sai Baba, tsayawa Khaleel yayi gaban gadon gently
Baba yace “kaima likita ne”? Ahankali Khaleel ya gyadamai kai yace “eh” gyadamai kai Baba yayi saikuma
ahankali yakai hannayenshi dake rawa rawa yakama duka hannayen Khaleel yarike Khaleel ya kalli yanda
yarikemai hannu yayi shiru, baki Baba yabude ahankali zaiyi magana saiya fashe da kuka irin na manya
dinnan, Khaleel yayi shiru yana kallonshi sai kawai yaji he’s feeling bad, like really bad, he can’t
remember the last time he felt this bad for anyone in his life, cikin murya mai raunin gaske dan
maganganun Ni’ima sun taba Baba dudda bai nunaba yace “yau Ni’ima ta goranta mini, ta zageni, ta zagi
y’ata duka agabana” cikeda damuwa Baba ya tsagaita kukan saiya kalli Khaleel yace “Ibrahima zuciyata
batamin dadi ko kadan banmasan mesa nake gayama ba amman har cikin jinina nake jinka wlh, Allah ya
dauramin kaunarka kaman danda na haifa” Baba yaja hanci yace “banda komi ko ada chan kaji nake
gasawa da sauransu Hawwa tana around shekara 6-7-8 haka mukai hatsari mahaifiyarta tarasu nikuma
nadawo haka saida aka guntulemin kafa daya, da kyar da wayyo Allah nasata tagama sakandire Allah
yamata baiwan iya dinki kwandala nawa babu akaratunta na jami’a ita tasa kanta hartai masters tace
zata fara aikin yan sanda, Hawwa ke kula damu da kannenta komi na gidana Hawwa ne, wata kila inda
bata daurama kanta dawainiyan mu ba ta takura kanta harta fara aikin yan sanda ba da hala by now tayi
aure nima inada laifi” ya goge hawaye yace “babu mai neman y’ata babu maison ya aureta an tsani
Hawwa na, bansan yanda zanyi ba, hawan jini yakama Hawwa sabida tunani da damuwan mesa batai
aure, kanninta hudu mata duk sunyi aure hadda yara, yaran unguwa dasuka taso tareda Hawwa wasu
yaransu hudu biyar ma, dudda bata nunawa dan tanada jarumta da taurin zuciya amman damuwa
yamata yawa, narasa yanda zanyi babu maison auren Hawwa na wayyooo Allah na kaico na amma y’ata
gorin aure” Baba kawai yacigaba da kuka da zuciya daya, shi kadai yasan kalan damuwan dake zuciyansa,
Khaleel yakai kusan 2min kallon Baba yake chan kaman mai koyan magana yace “inaso na auri Hawwa
Baba!” Dawani irin sauri Baba yadago kanshi yakalli Khaleel danjin zancen yayi kaman saukan aradu,
bakinshi har rawa yake yace “Ibrahima kace zaka auri Hawwa?” Gyadamai kai Khaleel yayi ashagwabe,
bayan hannu Baba yakai ya goge fuskansa tass da sauri yana kallon Khaleel din yasake maimaitawa.
“Ibrahima kace zaka auri Hawwa”? Gyadamai kai Khaleel yayi yace “eh” Dasauri Baba yace “kasanta ne”?
Gyadama Baba kai yayi sounding like sangartaccen yaro din nan yace “inada Baby her name is Noor
antaba kidnapping nata shine Dady na yakira wajen aikinsu ita ta tayamu nemo Noor lokacin nafara
ganinta kenan” sosai Baba ke kallon Khaleel da yanda yaron ke magana kana ganinsa kasan dan gayu ne
irin yaran masu kudin nan, yan gata he’s so adorable, washe baki Baba yayi yay kosasshiyar murmushi
saikuma ya dakatar da murmushin yace “Maza da dama sunsha zuwa suce sunason Hawwa dazaran nace
su turo magabatansu shikenan bazaka kara ganinsu ba, bazan takura maka ba Allah yasani zuciyata ta
natsu dakai idanhar da gaske kake kanason Hawwa kaje kazo da iyayenka zuwa layinmu da magriba,
kome yasamu ka kawo zan baka auren Hawwa, idan yaso bayan ta warke sai ayi maganan tarewa da
sauransu kaji, layinmu yana nan kayin gwadabe babu wanda baisan Baba gurgu ba kuzo ina jiranku”
ahankali Khaleel na kallonshi yace “okay Baba” the way yake sounding whenever he talks kaman Baby
yasa baba yace “shekarunka nawa Ibrahima?” Ahankali yace “32yrs” murmushi sosai Baba yamai sai
kawai yakai hannunshi ya shafa kanshi zuwa gefen fuskanshi yace “Allah maka albarka yarona”
murmushi Khaleel yayi kadan saikuma kawai yahau gadon yazauna kusada Baba kaman dan yaro
yadaura kanshi kan kafadan Baba, shi kawai yanason Baba without any reason.

[9/23, 8:59 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫




✍🏻M SHAKUR




EPISODE
3️⃣
8️⃣ 3️⃣8️⃣




Sundanyi nisa ahanya yasa hannu yadauki wayanshi yayi dialing number Babanshi, Musbahu PA
Excellency ya dauka yace “Khaleely Babanka na kan chamber” cikeda isa yace “I don’t care kaimai waya”
cikeda lallashi Musbahu yace “Allah huci zuciyan yallabai bari na kaimai” Khaleel na kan layin kusan 5min
sannan yaji muryan Babanshi a speaker yana excuse me sai chan Excellency yayi magana cikin so da
kewa yace “Khaleely na ya akayi? Ina tsaka da meeting? Meya faru bakada lafiya ne”? Dan kishingida
yayi murya chan kasa yace “I will send you address na wani anguwa kasameni awajen by 6, kazo da trust
friends naka” dasauri Excellency yace “angama yarona zanzo, but meke faruwa lemme know wat I’m
coming there for” shiru Khaleel yayi kaman bazaice wani abuba chan yace “I want to marry someone
Pops” dasauri Excellency yace “aure? Aure Son? Ba mamanka is the one handling all of that for you ba,
an mata screening ne ita wacce kakeson auren? Why do I have to come our lawyers da Malamai can
take care of the aure for you, is my presence necessary”? Kai tsaye Khaleel yace “ai nasan dasu nace
kazo Pops” dan tausasa murya Excellency yayi yace “I know, I know, karka bata rai I didn’t mean to hurt
you, zanzo kawai nayi mamaki ne this is the first person dakake neman aure da kanka batare da Mom
naka ta zaba maka ba ta auro maka ba, wacece yarinyar?” Kai tsaye yace “that police girl” dan zaro idanu
Excellency yayi yace “you mean officer Hawwa wacce ta ceto Noor? That criminologist”? Murya chan
kasa Khaleel yace “uhmm” dan shiru Excellency yayi sai chan yace “Khaleely are you sure about this
decision? Cus naga yarinyar is hot tempered, bakaga yanda kuketa fada rannan ba, and you guys are
almost age mate fa dan ba karaman yarinya bace, banson wacce zatazo tana baka ciwon kai ba tana
wahalar da d’ana fa, I dislike stubborn girls” ahankali Khaleel yace “I can handle her Pops, I just wanna
have fun with her Pops don’t worry” dan murmushi Excellency yayi cikeda kaunar yaron nashi yace “you
know I will always give you kome kakeso ko? You have my support, see you by 6, I love you yarona
Khaleelyn Babanshi” dan smiling kadan Khaleel yayi ya katse wayan ya yar agefe yadago kanshi yakalli
Salman yace “I want every info akan mahaukaciyan nan and that photo boy of hers” gyadamai kai
Salman yayi yace “yes sir”

Please Login or Register in order to submit comment