jakan ya rufe motan shima ya zagaya ya shiga, zai kunna motan aka kirasa a waya yace da Na'ima "sorry, I have to take this" ta gyada kai, daukan kiran yayi yafara amsawa a nutse, sai bayan ya gama wayan ya juyo yace mata "akwai inda zakije ne kafin gidan" ta girgiza kanta tace "A'a" sai kuma a hankali yace "zaki rakani office inyi wani qaramin uzuri kafin in kaiki gidan" Na'ima ta kalleshi tace "akwai Uber ai" yace girgiza kai yace "No" ta sake cewa "it's okay, i understand aikine yataso maka ai" sai yayi qasa da murya yace "ban gaji da kallonki ba" sai suka tsaya kallon kallo, ta dauke idonta tace "ba gashi ka kallenin ba" ya sake cewa "bangaji ba" , tada motan yayi suka dauki hanyar office branch dinsu dake nan London, babu wanda yasake cewa komai a cikinsu, bayan sun isane Na'ima ta fito tana dan bin tall building din dake gabanta da kallo, Ahmad yafara tafiya tabi bayansa sai kuma taga ya tsaya ta qaraso suka jera atare suna tafiya suka shige cikin building din, office dinsa na 10th floor saida suka shiga elevator ya kamo jakan kafadanta yace "me kika saka a jakan, babu nauyi ne" ta gyara zaman jakan tace "babu nauyi" riqo jakan yayi ta sake masa ya sakala a kafadansa, sunzo wuce secretary dinsa daya kasance namiji ya miqe yana gaishesa, Ahmad ya amsa suka qarasa bakin office din nasa, da yatsansa ya bude door din suka shiga Na'ima nabin office din da kallon ganin komai na cikinsa black and white ne, ta tsaya bata qarasa ciki ba yatafi ya ja labulayen dake jikin glass wall din haske ya bayyana ko ina wanda kana tsaye daga inda kake kana kallon komai na city din, juyowa yayi ganinta tsaye yace "Babe kizauna mana" nan ma sunan yayi taking nata by suprise ta dago ta kallesa taga shi gurin fridge ya nufa ko a jikinsa, qarasawa tayi ta zauna a dogon kujeran dake lounge din office din, ruwa ya dauko da Apple juice me sanyi ya kawo mata, saida ya tsiyaya mata a cup ya miqa mata ta karba tareda cewa "thank you" takai bakinta, zubawa kanshi yayi shima a cup tareda zama a kujeran da take yabar gap a tsakaninsu, bayan ta ajiye cup din tana kallonsa tace "the interior looks unique and beautiful" ya dan bi office din shima da kallo yace "you like it?" Ta gyada kai tana dan murmushi, sai yace "zanje meeting room yanzu bazan dade ba zan dawo" batace komai ba kanta a qasa, yayi qasa da murya yace "Babe" ta dago kanta ta kallesa ya sake cewa "bazan dade ba, i promise" sai ta gyada kanta kawai, ya miqe ya wuce gurin executive table dinsa ya dauki wani takardu ya nufi kofan fita tana kallonsa, shima saida ya juyo ya kalleta sannan ya bude kofan ya fice..Sauqe numfashi Na'ima tayi aranta tana ayyana meyasa to bata tafi gidan bama ta biyosa, a fili tace "get a grip Na'ima" sai kuma tayi murmushi ita kadai, tajawo qaramin pillow dake kan sofan ta kwanta taciro wayanta tana kallon numbern sa, rasa da wane suna zatayi saving tayi amma tsaf ta haddace nombobin a kwakwalwarta, tananan kwance shiru bai dawo ba tafara gyangyadi a sannu kuma bacci ya kwasheta...
Meeting ne na gaggawa ya riqe Ahmad gashi shine head, anayin meeting din hankalinsa na gurin Na'ima, duk ya rasa nutsuwarsa ma a dole yake zaune yana sauraron turawan dake dakin suna magana, saida sukayi spending 1 hour kafin atashi, yayi sallah ya aika personal assistant dinsa ya siyo masa lunch sannan ya koma office din, ganinta nan kan sofa tana bacci yasa shi qarasawa a hankali yana kallon fuskanta tana baccinta cikin kwanciyan hankali, komai nata burgeshi yake tun daga kan idonta har yatsun kafanta, miqewa yayi Jin zuciyarsa na rinjayarsa dayawa ya cire jacket din jikinsa ya lulluba mata , ajiye ledan takeout din yayi kan qaramin glass table din dake nan gaban sofan sannan ya wuce work station dinsa ya zauna...bude desktop din sa yayi yafara typing, jefi jefi yake kallonta da har lokacin bata tashi ba yayi murmushi yana ayyana irin baccinta a ransa..
Kwankwasa kofan akayi sau biyu sai kuma aka bude, wani baqin guy ya shigo hannunsa riqe da pappers yana cewa "Man you have to go through these papers, jason didn't...." bai qarasa maganan ba ya tsaya kallon Ahmad da yakai yatsansa baki alamun yayi shiru, dan bin office din da kallo guy din yayi idanunsa suka sauqa kan Na'ima dake kwance tana bacci, kamar hadin baki itama ta bude ido ta kallesa sai kuma ta fara miqewa zaune, guy din yana kallonta da murmushi fuskansa yace "ma Sha Allah, who is this sleeping beauty?" Ahmad ya hararesa yace "fita min daga office lamin" juyowa lamin din yayi ya taho gurinsa yana dariya ya ajiye papers din kan table yace "you have to go through these again" Ahmad ya dauki takardun yana kallo sannan lamin juya zai fita yana kallon Na'ima, tace "Ina wuni" yace "Lafiya, our beautiful princess" daga inda yake zaune Ahmad ya sake cewa "Out Lamin", yana dan dariya ya fice...
Miqewa Ahmad yayi ta qaraso gurinta yace "kin tashi" Na'ima ta gyada kai , miqa mata table water dake kan table din yayi sai ya fara bude takeouts din, ganin yana bude abinci yasa a hankali tace "zanyi sallah tukunna" yace "Okay, ga toilet nan" ta miqe ta nufi toilet din zatayi alwala, fita yayi daga office din shima, bayan tayi alwala tafito taji wayansa daya bari nan kan sofa na ringing, bata kula ba saida aka sake wani kiran ta qarasa tana kallon fuskan wayan, Sunan Laila tagani baro baro akan fuskan wayan......
Bintu Musa ce ✍️📚
https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
WhatsApp group
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
Chapter 20
Tsayawa kallon wayan Na'ima tayi tanajin yanayin zuciyarta na chanjawa, kuma batayi gigin daukan wayan ba, tananan tsaye Ahmad ya sake shigowa office din, ganinta tsaye yasa a nutse yace "sorry ban baki darduma ba ko" Na'ima ta dan gyada kai batace komai ba kuma taqi kallonsa, wucewa yayi gurin da yake ajiye spare kayansa a office din, mutum bazeyi tsammanin akwai kofa a gurin ba saida Ahmad ya saka yatsansa sai ga kofa ta bayyana ya bude ya shiga, bai dade ba ya fito hanunsa riqe da linkakkiyar darduma ya warware, nufansa Na'ima tayi ta karba kafin yace zai shimfida mata dan taga alama zai iya yin haka...daukan wayan nasa Ahmad yayi yana dubawa, Na'ima na tsaye tana kallonsa sai taga yayi saurin dagowa ya kalleta bayan yadanyi dube dubensa a wayan, kallon kallo suka tsaya yi, ita tafara juya kanta ta gyara gyalen abayan jikinta dayake babba ne tafara sallah, Ahmad da yasan taga miscalls din Laila yasa shi rasa me ma zaice sai ya saka wayan a aljihu ya zauna nan kan sofan yana dan juyawa ya kalleta, bayan ta idar da sallan ta linke darduman ta ajiye nan kan sofan sai ta dauki jakarta zata maqala a kafada, ganin abunda take Shirin yi yasa Ahmad kallonta a hankali kuma yace "ga abinci nakawo miki" ya qarasa magana yana bude ledan, jijjaga kai Na'ima tayi ta wani sha kunu tace "Naqoshi, gida zan tafi" ai Ahmad baisan lokacin da ya miqe ba sanin meya bata mata rai kuma, ya tsaya nan gabanta ahankali yace "Babe..." Na'ima ta juya kanta gefe bata kulasa ba sai ya miqa kansa side din take kallo, idonsa ne yafada cikin nata tayi saurin kulle idanun nata, Ahmad ya fara yar dariya still yana kallonta, ta wani turo baki cikin shagwaba tace "banaso, ni na qoshi" yana dan dariyan kuma yana kallonta, ji yake kamar ya hadiyeta ma ko zai huta da abunda yake ji akanta, ya sakeyin qasa da murya yace "Okay naji, me kikeso sai akawo miki" sai sannan ta bude idonta ta dan juyo tana kallonsa tace "gida nakeson tafiya" jitake ranta duk babu dadi a wannan moment din, gashi bata da hurumin tuhumarsa akan kiran Lailan data gani saboda itama har yanzu bata gama tantance matsayinta a gurinsa ba... Sai kuma unexpected taji yayi qasa da murya yace "zanyi blocking dinta Babe" dagowa tayi ta kalli cikin idanunsa itama a hankali tace "wa zakayi blocking, wani abu ya faru ne?" Ahmad yayi murmushi ya kai yatsa ya dunguri hancinta yace "Na'eemah", samun kanta tayi da yin murmushin itama ta miqa hannu ta dauko jacket dinda ya lullaba mata ta miqa masa, tace "thank you" karba yayi ya saka ajikinsa, ta sake cewa "I want to go home, na dade fa" Ahmad yace "Okay muje to" ..
Tare suka fita daga company din babu mai magana acikinsu suka shiga mota, ita Na'ima ba abunda ke bata mamaki irin bude mata cab din motan dayake yi aduk lokacin da zata shiga, batasan meyasa hakan yake narkar mata da zuciya ba, such a gentleman..
Saida Ahmad yayi parking gaban wani babban supermarket Na'ima ta tuna da dunut din Nafisa, ita kadai ta fara murmushi tuna irin jarabar da zata sha agurin nafisan inda ta manta, kallonta yayi yace "zaki rakani ciki babu damuwa?" Ta gyada kai tareda cewa "Toh" dan itama tanada mata uzurin.
Cart Ahmad ya turo Na'ima na gefensa, sanin bazata zabi abunda takeson ba yasashi loda duk wani junk foods da abubuwan kwadayi cikin cart din, dan ware ido tayi dan a tsammaninta nashi ne , haka ta rinqa bin bayansa yana loda kaya cikin cart sai da ya debi son ransa ya juyo ya kalleta a nutse yace "akwai wani abun da kikeso bayan wannan?" Na'ima ta ware idanu tace "all of this?" ya dan daga kafada yace "akwai su nafisa ai" tuna nafisan nason ire iren abubuwan nan din yasa Na'ima bata sake protesting ba tace "tace in siyo mata dunut" yace "Okay" gurin part na snacks suka je nan ma ya dibo masu yawa dayake acikin package suke, bayan yayi inserting card nashi anan counter aka cire kudin sai cashier'n ta hada kayan ya karba, miqa hannu Na'ima tayi zata tayasa riqewa ya kada kansa alamun ta bari but saida ta karbi wani ledan suka fice..
A komawa gidan ma shiru sukayi sai Ahmad dinne yace "kinayin WhatsApp?" Ta girgiza kai tace "A'a" kallonta yayi sai kuma ahankali yace "then how am i supposed to see your face anytime" ta juya kanta tace "nidai banayi" murmushi yayi bai sake cewa komai ba har suka isa, tana shirin bude kofan motan ya tsayar da ita ta dalilin dan riqe bakin gyalenta dayayi, ta juyo ta kallesa batace komai ba, sai kallonta yake wanda haka yasa ta sauqe idonta, yayi qasa da murya yace "I'd love to wake up everday seeing those Eyes Babe" rufe idonta tayi tafara murmushi muryansa na kashe mata duk wani kuzari na jikinta, iskan cikin motan ne taji yafara mata kadan ta sake juyawa zata bude kofan yace "yaushe zaku sake fita karatun" shiru tayi kamar baza ta amsa ba, ahankali kuma tace "sai jibi Saturday" ya gyada kansa yana sakin bakin gyalen nata suka fice daga motan tare, sai da tajira shi nan tsaye ya debo kayan daga booth sannan ta qaraso garesa zata karba yace "barshi, muje ciki" ta dan ware ido tace "shiga zakayi" yace "Eh, ko da wani abun" tadan turo baki tace "in suka ganmu tare fa" murmushi yayi yace "toh ki fara shiga sai anjima can in biyo bayanki" ta gyada kai sannan ta nufi gidan yana kallonta fuskansa dauke da murmushi ya dan jijjaga kai, tana bude kofan ta shiga kenan mutanen falon suka dago kai duka suna kallonta, anty Amnah, Abban twins, Nafisa da kuma twins din, tsayawa Na'ima tayi itama tana kallonsu ganin irin kallon da suke mata, lura tayi ba itan suke kallon ba bayanta suke kallon sai itama ta juya, ganin Ahmad tayi a bayan nata tadan ware ido, yana dan murmushi ya wuce ta ya shiga falon hannunsa riqe da kayan, miqewa Nafisa tayi ta karbi kayan tana masa sannu da zuwa, anty Amnah tace "Son sannu da zuwa" samun guri yayi gefen Abban twins ya zauna, sai a sannan Na'ima ta fara takawa a hankali cikin falon ta nemi waje ta zauna tana kallonsa yana gaisawa da uncle, Anty Amnah tace "Na'ima kin dawo" ta gyada kai tareda cewa "Eh Anty" ta sake tambayanta ya karatun ta amsa da Alhamdulillah, gaishe da Abban twins tayi ya amsa shima, tadan juya tana kallon Nafisa dake mata wani irin kallo tana qunshe baki kamar me tare dariya, dauke kanta Na'ima tayi tana shafa kan jafar daya zo kusada ita, Anty Amnah ta sake cewa "son kai ka kawota kenan" yace "Eh Anty" anty Amnah tace "Ma Sha Allah" Na'ima sai jira take taji yace haduwa yayi da ita sannan ya kawota gidan amma sai taga shi ko a jikinsa ma yana barewa jabeer ledan biscuit, miqewa tayi tace "anty zanje ciki" anty Amnah ta gyada kai tace "Okay, amma inkin gama ki fito kici abinci fa" ta amsa sannan ta wuce dakinsu tabar Ahmad nan yana hira da uncle yasir..
Sai da tayi wanka ta fito daure da towel ta zauna kan stool nan gaban mirror zata shafa mai Nafisa ta shigo dakin hannun riqe da dunut tanaci, Na'ima ta wani sha kunu ita a dole kar nafisan ta kawo mata wargi, dariya Nafisa ta fara ta qarasa wajenta tana cewa "inaaa..ai ko aman wuta idonki yakeyi Na'ima sai nayi magana" Na'ima batasan lokacin da tafara dan dariyan ba itama ta jawo cream dinta tafara shafawa, tsayawa nan gefenta nafisa tayi tadan jingina da mirro'n tace "iyee Na'ima, Au anty Na'ima zance dan na fara shinshinowa kinzama anty na ma" Na'ima ta dan jijjaga kai tace "kici kanki Nafisa" nafisa bata dena dariyan ba tace "naji..yanzu dai fadamin a Ina kuka hadu harda siyayyarsa haka, chaiii Na'ima" Na'ima tace "toh dena dariyan tukunna sai in fada miki", gyada kai Nafisa tayi takai dunut baki bata daina kallonta ba fuskanta da murmushi, Na'ima tace "a Cafe dinda mukaje karatun na hadu dashi, shikenan?" Nafisa ta gyada kai tace "sai me kuma?" Na'ima tace "kamar me? ni babu komai kuma" Nafisa tace "a sannu zaki fadamin komai ma, sun tafi yin sallah shida uncle yanzu" itadai Na'ima bata sake cewa komai ba tacigaba da shafa manta, Nafisa tace "Oh yaya Ahmad, kuma nikam tayaya kuke maganganun soyayyan ne ma" Na'ima ta kalleta sannan tace "ce miki akayi maganganun soyayya yakeyi?" Nafisa ta dan daga hannu tace "A'a mu yayanmu ba daga nan ba wallahi, yanada himma a lamuransa" Na'ima tadan ware Ido tana dan dariya tace "tanan kika bullo kuma Nafisa" tace "A'a ai ni bani nan bani can ne, dangin miji ce nima kuma dangin mata" miqewa Na'ima tayi ta nufi wardrobe zata saka kaya tana dan kada kai tace "kin fi qarfina kuma" haka nafisa tayi ta janta da surutu tana amsawa har ta gama saka kayan suka fita cin abincin tare, basu samu Ahmad a falon ba ashe daga fitansu sallan bai dawo ba kuma ya wuce gidansa.....
Daren ranan Na'ima na zaune kan gado tayi shirin bacci hannunta riqe da wayanta ta maida hankali tana dannawa, Nafisa ce ta shigo dakin tace "bakiyi bacci ba" Na'ima ta gyada kai batace komai ba, nan kan gadon itama Nafisan ta zauna ta jawo laptop dinta zata bude, can dai Na'ima ta dan gyara zama tace "Nafisa kiga...uh..uh..idan na bude WhatsApp da number'n danake amfani anan qasar, in na koma gida sai nayi changing number ko?" Nafisa tace "bangane ba, WhatsApp zaki bude kaddai" Na'ima ta dan gyada kai tana kallonta, ai da sauri Nafisa ta ajiye laptop din tace "Na'ima yau din..Bobo kece kuwa?" Na'ima tayi murmushi tana dan basarwa alamun kunya, Nafisa ta sake cewa "kin gaji da Zoom app din ne" Na'ima tace "A'a, nidai ki bani amsa ta mana" karban wayan Nafisa tayi tace "Ai kawo ma in bude miki" tana danna wayan kuma tana dariya tace "Na'ima you're full of surprises these days" itadai batace komai ba tananan zaune sai murmushi takeyi...
Washegari Friday nafisa nada uzuri a school tun da sassafen ta tafi school din tabar Na'ima nan dakin tana baccin ta, jiyan saida tayi bacci Ahmad ya kirata ta dauka muryanta cike da bacci, shima jin hakan yasashi cewa tayi baccinta saida safe zai kirata
Bata tashi ba sai kusan goma na safe, sanin masu gidan sun fice yasa ta fito jikinta sanye da pyjamas ta nufi kitchen neman abunda zataci, tasamu anty Amnah ta ajiye mata nata breakfast din, zama tayi zata fara cin abincin sai kuma wayarta tafado mata a rai ta sake tashi ta koma dakin ta dauko, aikuwa miscalls dinsa tagani guda biyu duk a lokaci ma banbanta, saida ta zauna gaban abincin sannan tabi bayan kiran, Ahmad yana office a wannan lokacin kiran ya shigo wayansa ya juya yana kallon wayan, saida ya jira kiran ya katse sannan ya bi bayan atake, shiru sukayi a farko kowa da wayan a kunne sai Ahmad yace "Babe yanzu kika tashi ne?" Na'ima ta gyada kai tace "I'm sorry ka kira Ina bacci" yace "bakomai nayi tunanin hakan" gaishesa tayi ya amsa suka sakeyin shiru, can yace "do you have Zoom app?, I want to see you" shiru Na'ima tayi at first sai kuma a hankali tace "na bude wancan din" Ahmad yace "WhatsApp din?" Ta amsa da "Eh" yace "Okay let me call you" Na'ima tayi saurin kallon kayan jikinta tace "No,I'm in my..." Sai taji ta kasa fada masa kayan bacci ne a jikinta , ji tayi yace "irin wa'enda na ganki dasu a gidan Mami?" cikin jin kunya tayi shiru batace komai ba tana murmushi, ya sake cewa "Babe kinyi kyau ranan, dakyar na dauke idona" murmushi me sauti tayi shima daga can bangaren murmushin yake, sai ya kuma cewa "yanzu dai iya fuskanki kawai zan gani, I promise" tace "uhm uhm" yace "nayi alqawari fa" ta sake cewa "ni dai A'a" haka Ahmad yayita lallabinta akan fuskanta kawai yakeson gani Na'ima taqi, ganin bazata yarda ba yasa shi hakura ya sake tambayanta gobe Saturday din zata fitan tace "Eh" yace "ko nazo na kaiki" ai da sauri tace "nidai wallahi a'a, ai ban manta abunda kayimin jiya ba" yafara dariya, ta sake cewa "you broke our plan" yace "Babe I'm sorry, shikenan bazanzo ba toh"...haka suka dau lokaci suna hira wanda ta fannin Ahmad barin aikin nashi yayi duk ya lalace a jikin wayan, hira sukeyi jefi jefi cike da annushuwa wanda hakan ke sake sarqe zuciyoyinsu guri daya...sai Na'ima ce ta fara masa sallama tace zataci abinci sannan Ahmad ya kashe wayan ya koma kan aikinsa...
Da nafisa tadawo da yamma ne take fada wa Na'iman boat race din da za'ayi between Oxford university da Cambridge, Anty Amnah da fitowanta daga kitchen kenan tace "Au wai har gobe ne sport din" Nafisa tace "Eh anty, ban iya riding bane ai shiyasa babu ni, amma ni da Lauren muna cikin cheering squad" Na'ima tadan ware ido tana dariya tace "sannu nafisa" Nafisa tace "da ban karbo matching wears din dake bama ki gode Allah" Na'ima tace "bama zanje ba" Anty Amnah tace "gaskiyarki daughter yayi hayaniya gurin, akwai jama'a" Nafisa tayi dariya tace "it'll be so much fun kuwa,Allah kizo muje Na'ima" ta kalli anty tace "Anty ki fada mata ta shirya muje" ganin Anty Amnah ta Jan jijjaga kai alamun tabar maganan yasa Nafisa gane me take nufi sai tayi shiru kuma, ita harta dan manta dalilin zuwansu nan gidan anty Amnahn ma in the first place...
Ranan Saturday din da safe zarah ta kira Na'iman a waya akan su hadu at same Cafe din ranan can, bayan Na'ima ta gama shiryawa cikin farin blouse din riga mai dogon hannun wanda qarshen hannun da roba, tahada da brown jeans ba matsattse can ba, rigan a bude take sosai ta sauka har gwiwanta ta yafa brown veil, saida ta gama shirin tace da Nafisa dake nan kwance "sis ba yanzu bane game din naku" Nafisa ta qara Jan blanket tace "sai dan anjima tukunna" ta qarasa maganan tana sake lulluba blanket din har kanta..fita Na'ima tayi bataga su anty Amnah a falon gidan ba kasancewan Saturday sunacan ana bacci sai ta ciro wayanta tafara kiranta, tananan tsaye anty Amnahn ta fito daga side dinsu jikinta sanye da kayan bacci tace "harkin shirya daughter" Na'ima ta gyada kai anty Amnah ta sake cewa "bakiyi breakfast ba kuma ai" tace "zanyi acan Cafe din anty" Anty Amnah ta gyada kai tareda cewa "toh, ki kula sosai fa Na'ima" tace "toh" sai kuma ta tsaya bata tafin ba kanta adan duqe tarasa ta Ina zata fara maganan datake son yiwa anty'n, ganin hakan yasa Anty Amnah'n ta sauqar da murya tace "daughter menene? feel free with me kinji" Na'ima ta dago kanta ahankali tace "dama rancan da yaya yakawonin a Cafe din muka hadu Anty" murmushi anty Amnah tayi tace "ya fada mana bayan tashin ku daga gurin, kuma ma ai shi yayanku ne Na'ima, what's there dan ya kawoki gida?, I know who is Ahmad" Na'ima ta gyada kai sannan sukayi sallama ta fice Anty Amnah na bin bayanta da kallo still bata daina murmushin ba...
Nan Cafe din Na'ima tayi musu ordering sandwiches da tea itada zarahn, saida suka gama ci sannan suka fara research din nasu, yau ma dogon discussion sukayi sosai, sun dauki lokaci me tsaho suna abu daya sannan Kiran Ahmad ya shigo wayan Na'ima dake nan kan table, dauka tayi suka gaisa daga can bangaren a nutse yace "nazo at the wrong time ko?" sai Na'ima ta daga kanta tafara bin Cafe din da kallo tana nazarin mutanen cikinsa, kusada entrance ta ganshi tsaye waya kare a kunnensa yana kallonta, hannunsa daya cikin aljihu, murmushi ta masa wayan yana kare a kunnenta,cikin sanyin murya tace "sorry.. dan qaramin few minutes Dan Allah" ya dan yi murmushi tareda gyada kai sannan ya nemi table ya zauna yana kiran waiter..
Magana ta cigaba dayi ita da zarahn jefi jefi tana kai idonta gurin da yake zaune yana kallonta, aduk sanda suka hada ido zata dauke kai tacigaba da magananta da zarah, sai taji duk ta taqura kuma under his eyes, kawai tace da zarahn su bari sai wani lokaci yanzu yayanta yazo daukanta.
Zara tace "where is he?" Kallon gurinsa Na'ima ta sakeyi sai zarahn tabi gurin da kallo itama, ganin Ahmad yasa cikin fara'a ta daga hannunta alamun gaisuwa, sai ya taso ya qaraso gurin nasu ya zauna anan gefen Na'ima, qara gaisawa yayi da zarahn kafin tafara tattare kayanta zata miqe....
Bayan tafiyan zarahn ya juya yana kallon Na'ima yace "ya research din" tace "Alhamdulillah" ya sake yin qasa da murya yace "kinyi kyau Babe" ta dan yi murmushi sai kuma yau din ta amsa da "kai ma kayi kyau" dan bin jikinsa da kallo yayi yana dan murmushi yace "Really?" ta gyada kai tana kallonsa still da murmushi a fuskanta, yace "Thank you dear" sai ya sake cewa "akan me kukeyin research din, Na'ima ta juyo masa da fuskan laptop din tafara masa bayani a nutse tanayi tana dan nuna masa lines din da yatsanta, gyada kai yakeyi akai akai alamun fahimta yana dan mamakin iliminta, sai kuma idonsa yakai kan tabon hannunta ya rinqa kallon baya ko kifta ido, ganin kamar hankalinsa ya tafi wani gurin ne yasa Na'ima dan kallonsa sai taga hannunta yake kallo, saurin boye hannun tayi ajikin riganta, Ahmad yadan matso ahankali yace "Babe please ki fadamin tabon menene wannan a hannunki" ta sauqe idonta qasa tace "dagaske da wuqa naji ciwon" sai yace "a garin yaya kika yanke sosai hakan?" sai ta rasa me zatace, shidai sai kallonta yake yana jiran amsanta, tace "da ina yanka..uh..lokacin ina yankan dankali ne" sai taji shiru be ce komai ba tadan dago idonta taga kallonta yake alamun maganan bata shigeshi ba, sai kuma ya sauqe numfashi yace "Allah ya kare na gaba" tace "Amin"
Ce mata yayi ta tashi su tafi akwai gurinda zai kaita ta tambayesa ina ne, yace "it's a surprise" tace "nidai ka fadamin Dan Allah" yace "akwai boat race na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 19