Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
anan unguwar yake kuma tasani sai nan da nan ta isa, shiganta gidan da sallama tasamesu nan tsakar gida, Umma ta girke nan kan kujera hannunta riqe da muciya tana juya marden alala dake cikin kafulas a gabanta, yarta me suna salame zaune gefenta tana murza manja a ledojin da zasu qulla, bin Na'ima sukayi da kallo dukansu har sauran yaran, Umma sai kallon kayan dake jikin Na'ima take ganin yarinyar fes da ita ga uban ya gyara mata gashinta gwanin sha'awa, gaishe da umma Na'ima tayi, Umma bata daina kallonta ba tace "lafiya autar babanta" sai Na'ima tarasa me zata sake cewa gashi duk suna kallonta, tananan tsaye yaron umman me suna Salim ya fizge biscuit din hannunta, ta daga kai tana kallonsa batace komai ba, Salame ce tace "toh da kika tsaya mana aka din bazaki zauna bane, zo ki bude mana leda" da sauri Na'ima ta gyada kai ta zauna nan aka fara aikin alalan da ita, sai da suka gama kulla alalen nan tas da ita sai gumi take na rashin sabo, bayan sun gama ta kalli umma a hankali tace "Umma zanje gurin Anty Amarya" Salame ta sake cewa "wani ya hanaki ne" miqewa tayi tafara karkade riganta ta nufi dakin anty Amarya da ke nan gefen na umma, a kwance ta sameta kasancewar tana fama da laulayin sabon ciki, Anty Amarya na ganinta tafara murmushi tace "wace wannan kaman Na'iman abbanta?" Na'ima ta fara dariya dan tanason anty Amarya kaf gidan ita kadai take mata fara'a har ta bata abu in tazo, Anty Amarya ta sauqo daga kan gadon nata dakyar ta kama hannun Na'ima tana tambayanta ya makaranta, sai lokacin Na'ima ta sake tafara magana, data fita debo ruwa ma Anty amaryan Umma tace tazo tazauna ayi gyaran shinkafah da ita, komawa gidan goggon da bata ba kenan sai nan gidan kawu Ayuban babanta yazo ya dauke ta a kekensa suka wuce gida, da daren ranan Na'ima na zaune da mahaifin nata anan veranda na qofar dakinsu tace "Abba" ya dago kai yace "Na'am 'yar Abba" tace "dazu Salim ya kwacemin biskit dina" yayi murmushi tareda kai  hannunsa ya shafa kanta yace "sharing is caring daughter, kinga kin 'yammasa kenan" Na'ima ta jijjiga kai tace "toh zaka siyamin wani?" Ya sake gyada kai tareda cewa "gobe ma" cikin son kawar da zancen yace ta fara fado masa karatun da sukeyi a islamiya, nan tafara yana kallonta fuskarsa cike da walwala, ganinta a ko yaushe na tuna masa da Binta sosai wanda tun hakan yana sosa zuciyarsa har ya saba, sai kallonta yake tana magana aransa yana roqon Allah...yabashi tsawon rai su rayu tare da 'yarsa har girmanta. But, if wishes were horses...... Wayewar washegari Na'ima ta riga mahaifinta tashi, dama anan dakinsa take bacci shi a qasa ita akan gadon, sauqa tayi takai hannu tadan tabasa, jin kamar yana bacci yasa ta fita abunta dan dama a matse da uzurin fitsari ta tashi, har taje tayi ta dawo bai tashi ba, ta zauna tana jiran ya tashi suyi alwalan tare shiru bai tashi ba, sake taboshi tayi tace "Abba" shiru kamar me bacci gashinan idonsa a rufe, fita tayi tayo alwalan sannan tadawo tafara sallah, har gari ya waye bataga Abbanta ya tashi ba, daga qarshe ta miqe ta  fita daga gidan, gidan goggo ta nufa tana sauri, isarta gidan tasamu kawu Ayuban yazo gaishe da goggon sunanan zaune a daki, ganin Na'ima ita kadai da sassafe yasa goggo tadanji hankalinta ya tashi ta fara tambayanta meya faru, fada musu tayi Abban ta yana bacci tayi tayi ya tashi kuma shiru, Ai atare goggo da Ayuba suka miqe,fita sukayi a gigice basu tsaya ko Ina ba sai gidan Yusuf suka shiga har cikin dakinsa suka samesa nan kwance kamar yanda Na'iman ta barshi, Ayuba ya jijjaga shi goggo ma ta matso tana kallonsa hankali tashe, a sannan ne suka gane rai yayi halinsa.. Yusuf ya koma ga Allah acikin baccinsa...... Bintu Musa ce ✍️📚 https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Chapter 23 Na'ima dake nan tsaye bakin kofan sai raba idanu take alamun tsoro duk ya bayyana a fuskanta bata qaraso cikin dakin ba, fara gyara masa kwanciya kawu Ayuba yayi kuma sai akayi sa'a jikinsa har lokacin da laushi, goggo sai hawaye take tana cewa "wayyo ke duniya, wayyo ke duniya, Yusuf na yafe maka, Allah na gani kai da ne me biyayya, Allah ya yafe maka Yusuf" kawu Ayuba ma da idonsa suka ciko da hawaye yafara amsawa da "Amin Amin Amin, Allah ya maka rahama dan'uwana" sai kuma ya fashe da kuka yakai yatsunsa yana danne idanunsa gwanin tausayi, sai sannan Na'ima ta fara takawa cikin dakin, goggo da ta manta tare suke da ita ne tayi sauri miqewa ta tarota kafin ta qaraso, kawai Na'ima tafara fisgewa zata kai ga gurin mahaifin nata dake kwance tafara cewa "Abba" "Abba" duk girman Na'ima haka goggo ta fara ciccibarta tayi waje da ita tana cewa "muje waje yana bacci tukunna Na'ima" bin bayansu kawu Ayuba yayi shima ya rufo dakin sannan ya fita daga gidan..kuka Na'ima tafarayi da goggon ta shiga da ita dayan dakin, itama kanta goggo zuciyarta a wannan lokacin cikin nauyi yake na rashin danta amma haka ta rugume Na'ima a jiki tafara lallashinta... Su umma ne da anty Amarya suka fara zuwa gidan suma hankali a tashe sannan mutanen unguwa suka rinqa tittilo gidan, zuwa wannan lokacin su kawu Ayuba har sunyi duk wani abunda ya kamata, Na'ima sai ido, bin kowa take da kallo babu uhm babu A'a, ganin mutanen cike a gidansu yana qara tuna mata cewa hakan akayi fa lokacin na mahaifiyarta kuma har yau gashinan bata dawo ba, sai sannan tafara ayyanawa a ranta abbanta ma haka zai faru kenan?, ai batasan lokacin da ta miqe ba ta nufi fita daga dakin tana tsallake mutane, fitan ta tsakar gidan yayi daidai da fito da mahaifin nata cikin makara, Ihu tayi da qarfi ta nufesu anty Amarya na kamota tana fisgewa, tana kukan tana cewa "wayyo abbana, wayyo kubarmin Abbana" babu wanda bata sashi hawaye a wannan lokacin ba ganin yarinyar da bata rufa shekara goma ba maraici ya mata kamu dumu dumu babu wa ko qani a duniya, Haka Na'ima tanaji tana gani aka fice da mahaifinta tana kuka kamar zata suma ta kwanta ajikin anty Amarya, rayuwa kenan, Yusuf yazama tarihi sai a bisa da addua... Da Ayuba ya kira Abdullahi ya shaida masa mutuwan dan'uwan nasu, shima yaji mutuwan sosai barin in ya tuna lokacin da yaga Yusuf din, hakuri ya bawa Ayuba ya bashi uzurin baya qasar a wannan lokacin amma da zarar yadawo zaizo nan gidan. Zaman makokin ma maidashi gidan goggo akayi, ta shiryawa Na'ima dukan kayanta suka koma can gidanta aka kulle nan gidan Yusuf din, a wannan satin duk wanda yaga Na'ima sai ya zubda hawaye, magana daya biyu zatace Abbana, sai dai tayi ta bin mutane da kallo bata iya cin abinci har se anty Amarya ko goggo wani cikinsu ya tusata gaba sannan zataci kadan.. lokacin da qanwar maman Na'ima tazo, bawani saninta Na'iman tayi ba sai dai kallonta kawai data rinqa yi, ta rungumota ta fashe da kuka, tanajin har mutuwan Binta na dawo mata sabo.. Bayan anyi zaman makoki na tsawon kwana bakwai kuma ta nemi tafiya da Na'iman dukda itama bawani qarfi mijinta ke dashi ba, goggo ce ta hana, dan inta su Ayuba ne baifi ragin wani nauyin ba, goggo tace da halima yarinya ba rasa madafa tayi ba tunda ga iyayenta maza sunanan, dan haka ta barta nan cikin dangin mahaifinta za'a kula da ita. A wannan lokacin ne Na'ima ta fara daukan dangana, sai shiru kuma daya sake shiganta har hakan yana baiwa goggo dan tsoro wani sa'in, a tarin lokuta zata farka cikin dare kawai tayi ta kuka nan kan gadon goggon, sai da goggon ta fara hadawa da addu'o'i sannan Na'ima ta fara samun nutsuwa.... Bayan 'yan satikai goggo ta fara sata zuwa makaranta, Na'ima bata taba sanin nisan makarantan haka yake ba sai ranar farko da ta fara zuwa a qafa, tana tafiya hawaye cike idonta tazo tawuce ta gurin da mahaifin nata ke siya musu abinci idan ze kaita makaranta, data je makarantan ma bata gane komai ba, kawai zama tayi shiru ta rinqa kallon window, da aka tashi break ma nan kan bench dinta ta kwanta bata fita ba, da aka tashi ma haka tafito ita kadai zata tafi, gashi bawani qawaye gareta ba, daman qawarta daya ce kuma a islamiya ne, haka ta sake takawa da kafa tana gumin cikin rana ta koma gida... Ana wannan halin goggo tayi Kiran Ayuba da Nasiru wata rana da safe bayan Na'ima ta tafi makaranta, bayan sun dan taba hiransu da ya shafi rayuwa goggo ta gyara zama tace "toh, kunga dai dan'uwanku Allah ya karbi abunsa saidai mu bisa da addua da kuma fatan in tamu tazo Allah yasa mu cika da imani" suka gyada kai cikin fahimta tareda amsawa da "Amin" , goggo ta cigaba "ga jininsa nan ya bari, kuma hakki ne da ya wajaba a kanku da ku kula masa dashi, wannan yarinya yanzu gatan ta shine Allah sannan ku da nidin gaba daya" Ayuba ya sake gyada kai yace "wannan haka ne goggo" goggo tace "yauwa, acikin ku biyun nan dole dayanku ya dauki ragamar kula da rayuwan yarinya da dawainiyarta" Nasiru ne yafara magana yace "Toh goggo da kika ce mu kula da rayuwan ta, kin fa sani, ni dinnan ba iya kulawa zanyi da karatun ta ba" Ayuba yace "atoh, kar nayi magana ne ace daman na fiye subul da baka, goggo kina gani dai muma 'ya'yanmu ba makarantar nan suke ba" goggo ta dan gyara zama ta kwantar da murya tace "haquri zakuyi ai, tunda Allah ya dora mana nauyin gaba daya" Ayuba ya jijjaga kai yace "A'a goggo, wanda Allah ya dorawa nauyin yau babushi, hakuri zatayi da bokon nan, ni dai in kulawa da ita ne naji na dauka a kaina, tunda yanzu tana zama gurinki sai ta cigaba da zaman har lokacin da Allah zai kawo mijin aure, in kuma 'yar sana'ar nan zaki fara qulla mata irin nasu salame ne to duk daya" goggo tayi shiru tana kallonsu duka batace komai ba, haka suka karkade rigansu suka mata sallama dukansu suka fice daga gidan, aka barta nan zaune jikin duk yayi sanyi ainun.... Isar Ayuba gidan yasamu umma da anty Amarya nan tsakar gida, umma na zaune bakin murhu tana iza icce na dafin awarar da su salame zasu fita siyarwa da rana, gidan babu yara wasu sun tafi yawo wasu kuma sun fice tallan kunu, su salame da dayar qanwarta sa'ar Na'ima daman sun tafi tuyan qosan safiya can bakin titi.. Tsayawa nan tsakar gidan Ayuba yayi matan nasa suka gaishesa ya amsa sannan ya fara musu bayanin abunda suka tattauna da goggo, umma na gyara daurin dankwali tayi masa wani irin kallo tace "toh yanzu da kulawan yarinya ya dawo hannunka din, can gidan zaka rinqa binta kana kulawan da ita kenan" Ayuba yace "bangane maganar ki ba jummai" umma ta sake cewa "toh ai naga indai aka bawa mutum ragamar kula da maraya daman dauka yake a gurinsa ya riqe, wane irin kula ne kuma an baka ita kuma an riqeta, haka ake bada yaron dama" Anty Amarya dake zaune bakin kofar dakinta tana kulla kayan miyanta a leda tace "toh yanzu ina aibu anan maman salame" Umma ta daga mata hannu tana hararta tace "Kinga ni ki daina tsomamun baki in ina maganar arziqi, yarinya ba da gwal aka sassaqeta ba sai nan nan ake da ita kamar qwai" ta kalli Ayuba dake tsaye tace "akawota nan din a hadeta da sauran yaran, ai da bai fi da ba" Ayuba yace "yanzu dai duk wannan maganar bata taso ba, daman ai ni nace da goggon ta cigaba da riqeta a gurin ta ganin sun fara sabawa" a dan fusace umma tace "to wai har kun aminta da riqon kaka kenan, sai yarinya tazo ta tabarbare duniya ta rinqa zagin ku akan kun barta sakaka tun farko, to wallahi bazai sabu ba, nan za'a kawota duk ka hadeta da naka 'ya'yan ka kula dasu tare" Anty Amarya ta jijjaga kai bata ce komai, Ayuba yace "shikenan ai, dama bokon nata mun tsaidashi haka nan, zata dawo nan din da zama" Anty Amarya sai kallonsa take tanajin kamar ta makeshi, shi kenan kullum sai abunda umma tace a gidan yake amfani kamar wani qaramin yaro, Ayuba yafara murmushi sannan ya sake cewa "yanzu akwai sauran kunun da qosan ne jummai?" Umma ta juya kai tana magana dakyar  "gashi can daki ai na ajiye maka" cikin bacin rai Anty amarya ta dauki farantin kayan miyan nata ta shige daki umma na bin ta da wani kallo... Washegarin ranan da Ayuba yaje gaishe da goggo ce mata yayi ze tafi da Na'ima, goggo ta dan tsaya kallonsa da farko sai kuma ta sauke numfashi tace "kafara canja magana kenan?" yace "abun da yakamata ne goggo, in Ina ganin ta a gabana zan fi sanin halin da take ciki ai, kuma zanfi kula da ita" goggo tace "nan da can din ma ai duk dayane nagani" Ayuba ya sake cewa "goggo yarinyar nan na amsheta akan ragamar komanta yadawo wuyana, kuma inason daukanta sai ace ba haka ba" goggo ta jijjaga kai tace "ya taka ce ai Ayuba gaka ga ita, sai ka tafi da itan" tsayawa kallon goggo yayi Jin yau ta kirasa da sunansa, Na'ima ta shigo dakin hannunta riqe da kayan makarantar ta data debo daga gurin shanya, Ayuba ya kalle ta yace "Na'ima ki shirya kayanki anjima da yamma ki koma can gidan" A sanyaye Na'ima tace "toh kawu" sannan ta ajiye kayan ta sake ficewa daga dakin tabarsu nan zaune suna bin bayan ta da kallo... Da yammacin ranan goggo ta hadawa Na'ima kayanta acikin akwatinta, ta kalli Na'iman dake zaune bakin gadon karfen dakin tace "ki rinqa zuwa akai akai kinji Na'ima" dan har ga Allah kallon Na'iman na rage mata wani radadin na rashin Yusuf a tare da itan, gyada kai Na'ima tayi tana jin hawaye na zuwa mata, addua take Allah yasa ta zauna a gurin anty Amarya in taje can din, sunanan zaune Kamal yazo dan gidan umma wanda ya girmewa Salim, aikosa Ayuban yayi akan su taho da Na'iman tare, haka tayi sallama goggo na jaddada mata cewa "nan da can din duk dayane Na'ima, koyaushe kikeson zuwa kizo abinki" Na'ima na hawaye ta juya suka tafi tare da Kamal din .. A qofar gidan suka samu kawu Ayuban kasancewar bai dade da dawowa daga gurin sana'arsa ba suka shiga gidan tare da Kamal Na'ima na biye dasu a baya, dakin anty Amarya shi kawun ya nufa yafara daga labule yana leqa ciki, umma ta fito tana gyara zaninta ta tsaya nan kusa dasu, Ayuba ya kalleta sannan ya tambayeta Ina Abida dan bai ganta cikin dakin nata ba, Umma tace "gurin abidan zaka bada itan kenan" Ayuba ya gyada kai tareda amsawa da "wai hakan naga kamar yafi" Umma ta tabe baki tace "toh da cikin nata zataji ko da riqon dan wani Malam, nidin kana ganin zan mata wani mugun abune da bazaka bani riqon nata ba ko me" Ayuba yace "bana son fitina jummai, dan zan bada yarinya gurin Abida ba yana nufin zaki mata wani mugun abu bane" A dan fusace umma ta sake cewa "Malam fifiko kawai kakeson kayi anan, ace Ina babba agidan nan zaka kawo yar riqo kabawa Abida, narantse bazata sabu ba ai ba ita kafara aurowa a gidannan ba" Ayuba ya karbi akwatin hannun Kamal ya jefashi nan gaban jummai din yace "ga ki ga ita" ya juya ya fice daga gidan sanin in suka fara irin haka da umma toh ba'a qarewa qalau, Umma ta kalli Na'ima dake nan tsaye kamar ruwa ya cinyeta tace "zo ki dauki jakarki ki ki dakin su salame, can  zaki zauna" Na'ima tayi saurin gyada kai ta dauki akwatin ta wuce dakin, ranar dakyar Na'ima tayi bacci nan kan wata yolokuwar katifa, su salame duk sun matseta.. Washegari da sassafe Na'ima ta tashi, bayan tayi sallah ta fito zata debi ruwan wanka taga randa wayam, umma dake hada wutan girkin safe tace "zo ki dauki bokati ki debo ruwan acan bakin bohole din dan'iya" Na'ima ta amsa da toh ta dauki bokatin ta nufi fita daga gidan, layi ta iddasar maqil a bakin famfon, haka ta ajiye bokatinta a layin ta bi sahun 'yan jira suna nan tsaye.. Ruwa ta rinqa judowa da safiyar Allah su salame na zaune bakin murhu tareda uwarsu suna aikin kunu da hada qullin qosai, bayan Na'ima ta debo ruwan sosai tazo gurin umma a hankali tace "umma zanje inyi Shirin makaranta" Umma tace "inace makarantar ance babu ita yanzu kuma, to ki jira baban naki yazo kiji ta bakinsa" Na'ima da duk jikinta yayi sanyi ta amsa da toh ta juya zata tafi salame ta kirata tasata daukan itacen da zasuyi tuya acan wajen, tare suka tafi hannun Na'ima riqe da itacen, ranan anan gefen salame tayi wunin safiyar, babu baki sai bin kowa da Ido, in anason chanji ita ke badawa, dan miqo takarda da leda, har iza icce duk ita keyi, tun idon ta na hawayen hayaqi har ya hakura, baiwar Allah data dawo ma ba'a barta taje islamiyan ba, sai da anty Amarya tayi magana, umma ta hau masifan cewa ai yarinya dai ance tagama karatu kuma, inba Sana'a ta kama ba to bacci zatayi agidan kenan.. Daga wannan lokacin kuma rayuwan Na'ima ya chanja salo kuma tun tana binsu salame tayasau ayyuka har aka fara dora mata nata tallan, kuma babu laifi tana ciniki saidai har yau kuma babu dogon magana a lamarinta, in kaji bakinta tana magana to lissafin kudi suke da umma, sauqinta daya da ta samu shine umman tafara son ta ganin irin kawo mata kudin da takeyi, dan Na'ima komai nacin mutum bata basa bashi, gashi gurin da take kai abincin ba dogon magana take ba, sai ba kowa ke shiga harkarta ba, ana cikin wannan halin ne watarana da safe kafin Malam Ayuba ya fice aiki wani yaro ya shigo akan yana sallama dashi, bayan Ayuba ya fitan ya samu wani mutumin tsaye yana jiransa, gaisawa sukayi sai a sannan Ayuban ya gane sa abokin Yusuf ne kuma wajen aikin koyarwarsu tare, Sambo yafadawa Ayuban akan yazo ne kan batun komawan Na'ima makaranta yaga shiru bata zuwa shine yazo yaji ko lafiya, Ayuba yace "batun makarantar yarinya mun dade da ajiyeshi a gefe Sambo, sanin kanka ne duk cikin yarana babu me zuwa makaranta balle ince zan ware Na'ima ita kadai takoma karatu, toh ma da wane kudin zan kaita makarantar?" Sambo yace "toh Malam yanzu duk wannan dai bazai zama matsala ba in Sha Allah, munyi zama na amana da Yusuf wanda baici ace bayan ransa munkasa saka masa da alheri ba, Na'ima 'ya ce a wajena nima kuma in zaka amince zanyi iya kokarina na ganin na biya kudin duk wani hidimomin makarantar ta" da farko qin amincewa Ayuba yayi da batun sai da Sambo yadan bashi wani abu shima yace gashinan babu yawa yayi hidiman gidansa sannan ya yarda,bayan tafiyan Sambo ya  qirge kudin ya sake su aljihu sannan ya juya ya shiga gida, tijara umma tafara yi akan hakan bazata sabu ba, Na'ima na zaune tana taya anty amarya kullin kayan miya, ta dago kanta tana kallonsu Jin abunda da kawu ya fada, zuciyarta taji yana sanyi saboda tanason makarantar kawai anfi karfinta akai ne, Ayuba dai ya tsaya tsayin daka ranan kan jummai, akan sai Na'ima ta cigaba da makarantar ta, miqewa Na'ima tayi ta shiga dakinsu ta fara duba akwatinta, ciro kayan makarantar tayi tana murmushi zuciyarta cike da farin cikin da bazai misaltu ba.. Daga wannan ranan ne kuma Na'ima ta fara samun sauqi a lamuranta, zataje makaranta daga nan ta biya gurin goggo su gaisa dan lokacin da aka sakota gaba da tallan bata samun zuwa gurin goggon ma, islamiyan ne dai yakoma asha ruwan tsuntsaye take masa, yau taje gobe umma ta dora mata talla, haka dai rayuwan ta cigaba.. A lokacin da Na'iman takai shekaru sha uku a duniya wani dan mai unguwa dake bibiyanta akai akai ya fito gadan gadan akan yana sonta, zuwa lokacin Na'ima ta gama primary, da Sambo ya nemi ta cigaba da makarantar gaba da primary daman Ayuba cewa yayi besan wannan zancen ba kuma, yanzu kuma umma har ragamar bata nata tuyan doyon takeyi, itace me tuyan da qannenta daya zuwa biyu masu zama kusa da ita suna taimaka mata gurin saidawa, sau tari in lawan yazo gurin ta har ya gama surutunsa bata dago kai ta kallesa ma, aikin gabanta takeyi haka zai qaraci surutu ya siyi doyan ya qara gaba, da lawan yaga ba samun kanta yake ba ne yasa ya biyo ta bayan fage direct ya samu kawu Ayuba da maganan, ranan farko da yazo gurin sa daman da babbar ledarsa kasancewan yanada kantin sa na saida kayan abinci kuma ba laifi yana samun rufin asiri da sana'ar, da lawan ya gama fadawa kawu Ayuba buqatarsa sai ya hada da miqo ledan hannun wadda ke cike da kayan abinci da kuma dan abubuwan amfani na yau da kullum, ba kunya Ayuba ya miqa hannu ya karba yana godiya yace masa zai turo masa Na'iman in ya shiga kuma ya kwantar da hankalin sa yarinya babu goron kowa akanta daman, murya gurin lawan ba'a cewa komai.. Da Ayuba ya shiga gidan umma ya fara fadawa wannan abun arziqi, zuwa wannan lokacin duk wani zafin umma akan Na'ima daman ta sauqe shi tunda yarinya na kawo mata riban Sana'a isasshe ga babu qiwiya a lamuranta, washe baki tayi tace "Na'ima dai yarinya da qashin arziqinta take yawo" Ayuba yace "yaro kam da arziqinsa, kantinsa na nan babba a bakin kasuwa" Umma tace "gashi ance har buhunhunan shinkafah yake sarowa daga legas" salame dake zaune bakin kofan umma tace "kuma wallahi umma duk Thailand, babu 'yar tsinta" itadai Na'ima na zaune kan kujera tana dinke hijabin ta da zare da allura batace komai ba, Amma zuciyarta se zafi take jin wai lawan dinda bataso suke qoqarin qaqaba mata, sauqar da kanta tayi gudun kar su ga hawayen da ya taru a idonta, Anty Amarya tace "Amma Malam baka nemi amincewar yarinya ba har da karban abun hannun yaron Fisabilillah" Umma na gyara daurin zaninta tafara nuna anty Amarya da yatsa tace "ke fa dadi na dake indai aka fara magana ta arziki sai kin san yanda kika yi kika lalata ta, abun naki zai fara komawa hassada kuma" Anty Amarya tace "meyasa zanyi hassada a Na'ima tana matsayin yar cikina, gaskiya ce dai bakwa so" Ayuba ya dubi Na'ima yace "ke, ajiye abunda da kikeyi kije yaron na waje yana jiranki" Na'ima ta zare alluran sannan ta miqe tazo ta wuce ta gaban su suna tsaye ta shiga dakinsu kanta a duqe, umma tace "ahtoh, yaro da rufin asirinsa kuma me za'a jira, ai duk gidan da akace akwai abinci, toh lafiya lafiya" Anty Amarya ta jijjaga kai tace "shine kawai damuwanki" umma tace "shine damuwar kowa ma, shi kawun nata kinga yana kawowa akai akai aci a qoshi ne, ba kowa tasa ce take fisshesa ba watarana a gidan nan" ganin abun ze dawo kansa ne yasa kawun cewa "ya isa hakan nan banason wata fitina kuma"...duk yanda lawan yaso shawo kan Na'ima ta masa magana taqi, wani daskarewa tayi nan tsaye idanunta na kallon gefe dan ko fuskarsa batason gani, yace "kiyi hakuri bansan ta yanda zan bullo ki aminta dani bane, wallahi Ina sonki Na'ima" duk qananan shekarun Na'ima a wannan lokacin ta san me kalman so din ke nufi, tace "ni banaso kasake zuwa gidanmu, makaranta nakeson inyi" lawan ya marairaice yace "indai makaranta ne zan barki kiyi har ta gaba da sakandiri Na'ima, nidai ki amince kawai muyi aure" bata amsa masa ba ranta a bace ta juya ta shige gidan ta barsa nan tsaye..hakaa lawan ya maida kofar gidan kawu Ayuba

Chapter 12 of 19