Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bin zara zaran yatsunta da kallo, bayan ta zuba masa yana kallonta yace "shekarar ki nawa" Hajiya ta dago kai ta kallesa tace "Bilal....." ya juyo yana kallonta ta jijjaga masa kai alamun bataso, ta kalli Na'ima tace "je ki gama aikin dana saki" Na'ima ta juyi ta koma kitchen din Bilal na bin bayanta da kallo... Alhajin da Na'iman bata sake ganinsa ba kenan a gidan sai da tayi kwana biyar dan da sassafe yake fita sai kuma dare can yake dawowa kasancewar dan kasuwa ne babba sai ya zamto har tafiye tafiye yana yawan yi akai akai, a 'yan kwanakin nan Na'ima ta gane shayi ruwa ne a fagen aiiki gurin hajiya, zuwa sannan ma bata ganin Bilal a gidan dan inta San ya fito cin abinci ma zamanta takeyi  a kitchen ko dakinta har sai taji ya tafi, abincin dare daman can falon saman yawanci shafa take kai masa shida hajiyan.. A rana ta biyar din ne tayi sa'ar samun Alhaji a falon lokacin da taje gaishesu, Bilal na kishingide kan kujera yana danna waya ya dago ya kalleta, ganin Na'ima yasa alhajin cewa "Ayya daughter kinyi ta cigiyata ko" Na'ima tayi murmushi ta zauna nan qasa kan carpet ta gaishesu Bilal na kallonta, amsawa sukayi har da hajiyan, Alhaji yace "yau dai zanyi waya inji batun makarantar nan, nadan shafa'a wallahi" ya kalli hajiya yace "kuma baki tunamin ba" Hajiya ta dan juya kai tace "nazata kana sane toh" yace "wallahi na manta, I'll talk with sufi anjima se yazo ya kaita su mata interview" Hajiya ta gyada kai, ya sake cewa "ba'a siyo mata kaya bane, what is she wearing haka" ko ci kanka hajiya batace ba ta juya kai tana kallon tv, ganin bazata kulasa ba yasa shi dauko waya yayi transfer din kudi nan zuwa account din hajiyan yace "ki aika ko shafa ta siyo mata kayan anjima" sai sannan ta gyada kai ta juya gurin Bilal tace "Babana akawo maka shayin nan?" ya jijjaga kai tareda cewa "bazan sha ba dai hajiya" cikin lallashi tace "ayya bakaci komai ba dai har yanzu, ko ayi maka kunun madaran?" sai sannan ya gyada kansa ya maida hankalinsa kan wayarsa, kallon Na'ima hajiya tayi tace "je ki kiramin shafa" Na'ima ta amsa da "toh" sannan ta tashi ta fice tabarsu nan zaune falon..... Daren ranan Na'ima ta fito daga kitchen zata je dakinta Bilal ya shigo falon ta kallesa, sai lokacin ta qara lura ma harda qaramar chain ashe a wuyansa, kansa cike gashi me uban yawa ya tara da wani farin dan kunne qarami maqale a kunnensa guda daya, sauqe idonta qasa tayi ganin yana kallonta, cikin sanyin murya tace "Ina wuni" bai amsa ba yace "what's your name?" tace "Na'ima" yace "shekarunki nawa?" nan ma a hankali tace "Sha hudu" kallonta ya rinqa yi tun daga sama har qasa kafin ya wuce zuwa stairs, sai sannan ta sake numfashin da take ta riqewa tun dazu tayi saurin shigewa dakinta, cikin dare tana cikin bacci taji qarar mota alamun an shigo gidan, farkawa tayi adan firgice ta miqe Jin qarar motan da dan qarfi ta nufi window tana leqawa, Bilal ne ya fito daga cikin wata sport car anan parking space, hannunsa riqe da karar taba yana zuqa, saurin sauqe labulen Na'ima tayi gudun kar ya kamata tana leqensa, jefar da taban yayi sannan ya shiga gidan Bilal, samun hajiya yayi saye nan gurin stairs cikin kayan bacci tana jiran shigowarsa, marairaice murya tayi tace"Babana bazaka dinga haquri da fitan daren nan ba Fisabilillah, hankalina baya nutsuwa kasani har se ka dawo, haba Dan Allah" be kulata ba yazo ze wuce ta kusa da ita ta dan riqo hannunsa ganin alamun yau ma ya shawo abar, tace "muje ka cire kayan nan duk wari suke" ya gyada kai idonsa yayi jaaa baice komai ba suka wuce dakinsa dake nan falon saman shima, jibgewa nan kan gadon yayi bai cire kayan jikin nasa ba sai hajiya ce ta miqa hannu ta cire masa takalman kafan sa tana kallonsa, Alhaji ne ya shigo dakin ransa a dan bace yace "Bilal sit up and take off those cloth" Hajiya ta dan riqo Alhajin tace "easy mana, kansa ke masa ciwo dai" yace "bakiji kayan na wari bane" ta dan marairaice tace "yanzu ze cire ai" Bilal ya mirgina dayan side din gadon cikin magagi yace "Oh God" Hajiya ta riqo Alhajin tace "mutafi, da asuba ze cire kayan" Bilal ya sake riqo kansa bai ce komai ba, atare Hajiyan da alhajin suka duqa cikin damuwa suka fara tambayansa meya faru, ya bude idonsa da yayi jaa a hankai yace "ku barni nayi baccin" Hajiya ta gyada kai tareda lulluba masa blanket tace "toh shikenan sai da safe mayi magana" ta riqo hannun Alhaji suka fice, nan bakin qofar dakin suka tsaya bayan ta rufo kofan a hankali, Alhaji na kallonta yace "it's getting worse, we have to do something" Hajiya ta kwantar da murya tace "mubari zuwa safiya tukunna, sai mu sake masa fadan cikin lallami, har yanzu dai bai cika ashirin da biyar ba, da sauran sa a fagen hankali Alhaji" Alhaji ya gyada kai tareda cewa "banason yabi jikinsa muzo muna danasani ne" ta gyada kai itama tace "mubi komai a sannu tukunna, yaron nan kasani shi kadai ne farin cikinmu, tun yanzu in mukace zamu taqurasa sai ya shiga wata hanya daban kuma" a haka hajiya ta lallaba mijin nata suka koma makwancinsu zuciyarsu cike da tararradin hanyar da dan gudaliyan nasu dauko.... Washegari Na'ima taje falo gaishe da hajiya ta sameta zaune ita da shafa dake tsaye, gaishe da hajiyan tayi bata amsa ba ta cigaba da maganan da takeyi da shafa, bayan shafa ta gama sauraron saqon da hajiyan ke bata ta juya ta fice, jawo ledan gefenta hajiyan tayi ta wullo wa Na'ima a jiki tace "ga kayan nan, sai ki dena saka tsummokar nan kuma, ya isa haka" Na'ima ta riqo ledan tace "nagode hajiya Allah ya saka da alkhairy" gyada kai kawai tayi bata ce komai ba, ganin shirun yayi yawa yasa Na'ima miqewa ta fice daga falon riqe da ledarta, duk da kayan ba wasu na azo a gani bane hakan bai hana Na'ima yin murna sosai ba, ta fito da kayan da daddaya tana kallo, dinkin kaya kala shida,hijabai guda uku da takalma guda uku, murmushi ta rinqa yi tana gwadawa a jikin ta  nan gaban mirror, sai data gama gwadawa  sannan ta maidasu cikin wardrobe nacikin jakanta kuma ta adanasu suma bata zubar ba, da rana saiga sufi yazo kaita makaranta, sai lokacin ta gane ashe shine driver'n daya kawosu daga Adamawa lokacin da zasu zo garin kano, Sufi PA din Alhaji ne dan yawanci ba aikin waje ba har na cikin gida yana sashi yayi masa su, dazasu tafi hajiya na dakinta tana bacci bata fito bama... Wata makarantar kudi Alhajin yasa aka kai Na'ima, sai baza Ido take tana kallon yaran manyan mutane a nan cikin compound din makarantan, basu wani bata lokaci ba bayan interview din a inda sukaga kan Na'iman na ja sosai, daukanta Jss 1 sukayi akan zuwa gaba dole a mata jumping dan tayi girma a jss 1 a wannan lokacin..murna gurin na'ima ba'a cewa komai, ranar uniform dinda suka bata ma kasa sakawa tayi a wardrobe, nan ta ajiye su kan gado bini bini tana kallo... Haka rayuwan Na'ima ta kasance gidan kawunta, da shafa kadai take samun yin dogon magana dan hajiya dai qarara ta fito fili ta nuna mata bata yinta kuma, Alhaji kuma yau yana gida gobe baya qasar haka dai rayuwan take tafiya, ta fannin Bilal kuma sai tayi sati basu hadu ba dan in akace yau yashawu ma sai ya wuni a gidan yana bacci hajiya na leqashi, bayan yawan zaman falon qasa sosai saidai na sama gurin hajiya wanda nan din daman ba gurin zuwan Na'iman bane, duk dare kuma yanacan club sai daren ya tsala zai dawo yayi ta buga horn yana tada duk masu bacci a gidan, ana cikin haka Alhaji ya sake nema masa wata makarantar a qasar Europe, wata university dake nan cikin Luxembourg, dakyar suka lallabashi ya tafi hoping that a wannan karon Bilal zai maida hankalinsa yayi abunda ya kaisa batareda ya sake katse karatun nasa ba... Watarana Na'ima ta dawo daga makaranta ta samu Kawu Ayuba nan tsaye a compound din yana jiran Hajiya tayi masa iso, yakai minti talatin a wajen tsaye bata aiko ya shiga falon ba, Na'ima na ganin kawun nata tayi saurin qarasa gurinsa tana murmushi ta gaishe sa, yana kallon ta cikin fara'a yace "Na'ima haka kika koma?" tayi dariya tace "kawu yasu umma da anty Amarya?" Yace "duk sunanan lafiya sunce a gaisheki suma suna nan tafe, zasuzo ku gaisa" Na'ima ta gyada kai still tana murmushi, duk da ba wani dadin kawun nata tajiba a rayuwa ba at least taji sanyi da ta gansa, saboda har yau zuciyarta ta kasa amincewa nan din da take zaune shima kamar gidan babanta ne.. Suna nan tsaye kawu Ayuba yace ta shiga ciki, wucewa tayi ta shiga falon, hakimce ta samu hajiya tana zaune anan falon gabanta kuma wasu laces ne nan kan table tana waresu da daddaya, ganin Na'ima yasa ta cewa "je kice baban naki ya shigo" Na'ima ta juya ta samu kawu Ayuba nan tsaye ta isar masa saqon, cikin azama ya amsa da "toh" ya biyo bayan Na'ima suka shiga falon tare, bayan sun gaisa da hajiyan inda dakyar take amsawan , kawu Ayuba yace "dama inata kiran layin yaya ne baya tafiya shiyasa na zo da kafata in sanar masa Allah ya yiwa goggo rasuwa satikai biyu da suka wuce" Hajiya tace "baya qasar yanzu tukunna" Kawu Ayuba yace "Allahu Akhbar, ashe shiyasa layin baya tafiya" Hajiya tace "Allah yaji qanta, in ya dawo za'a fada masa" kawu Ayuba ya amsa da godiya, nan hajiya tayi shiru bata sake cewa komai ba, ganin yanayin atmosphere din yasa shi cewa "toh Hajiya ni zan wuce, Allah ya qara girma" ita ta fara miqewa tace "a gaida gida" sannan ta wuce stairs Ayuba ya dan bita da kallo sai shima ya miqe, fita yayi daga falon Na'ima dake jiran taji fitarsa ta fito daga dakinta cikin sauri ta bi bayansa, anan compound din tace "baba" da dan qarfi, juyowa yayi ya tsaya har ta qaraso ta miqa masa ledan  hannunta me dauke da sabbin kayanta kala biyu da kuma tsofin datazo dasu gidan  harda takalmi kala daya da hijabi guda biyu tace "Baba gashi a kaiwa salame"  karba yayi yana murmushi yace "Allah ya miki albarka Na'ima" ta gyada kai yasake cewa "ki bi mutanen nan sau da qafa kinji" ta amsa da "toh" hawaye na kawowa idonta tace "baba yaushe zanje in ga goggo" shiru yayi be ce komai ba da farko sai kuma yace "kibari sai iyayen naki sun baki iznin zuwa tukunna kinji" ta gyada kai tareda cewa "toh" da haka sukayi sallama kawu Ayuba yabar gidan ko ruwa hajiya bata bashi yasha ba balle azo batun kudin mota kuma.... Bintu Musa ce ✍️📚 ArewaPen https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c ✨ KUNCIN ZUCI ✨ Na Bintu Musa Chapter 26 A haka har Na'ima ta cika seven months a gidan kawun nata, rayuwa take cikin shiru da kunci a gidan with no one to talk to except shafa, the only place da takejin sauqi a zuciyarta daman shine in taje makaranta dan har qawa tayi a school din, watarana sun wayi gari ranar asabar bataje makaranta ba tana moping din main falon gidan, bayan ta yi Rabin aiki ta dauki bokitin zata je canjo ruwan, tanason bi ta kitchen zuwa backyard din amma tana gudun haduwa da hajiya da ke kitchen din gudun ta kyare ta akan wani laifin da batasan sa ba, a tarun lokuta Na'ima ta kanji a ranta ko Hajiyar batason ganinta ne saboda indai tana waje sai Hajiyan ta tsiro da wani abun da zata kyareta ko cikin magana ne, daukan ruwan tayi ta fita ta main entrance din falon, batakai da zagayawa baya ba maigadi ya bude kofa wata mota ta shigo gidan, tsayawa Na'ima tayi tana kallon motan, cikin sauri driver ya fito ya bude bayan motan wata babbar mace in her 70s ce ta fito riqe da sandarta na qarfe tana dan duqawa, Na'ima na nan tsaye Matar ta fara takowa gurin entrance na gidan idonta be bar kan Na'iman ba, Dan tsugunnawa tayi ta gaishe ta, ta amsa da "lafiya 'yan mata" sannan ta shige cikin gidan, sai da Na'ima ta zagaya ta debo sabon ruwa sannan ta koma falon, Nan ta samu Hajiya babba hamkince kan kujera ga Hajiya nan zaune kan carpet suna gaisawa, cikin ladabi hajiya ke gaisheta wanda Na'ima bata taba gani ba ko sanin akwai wanda Hajiya zata gani ta rusuna kamar haka ba, zata cigaba da goge gogen kenan Hajiya tayi mata tsawa "Bakiga munyi baquwa bane, fita da mopper'n nan" Hajiya babba tace "A'a barta mana tayi aikinta, ba mai aiki bace" Hajiya tace "A'a, baban Bilal ne ya dauko ta daga Adamawa wai 'yar qaninsa ce" Hajiya babba ta juya tana bin Na'ima da tayi tsuru tsuru da kallo, sai tace "toh sannu yarinya, jeki abunki" Alhaji ne ya sauqo shima ya qaraso falon cikin ladabi yafara gaishe da uwar goyon tasa, sum sum Na'ima ta bar falon bata sake komawa ba sai zuwa hantsi taji Hajiya ta kwalo mata kira daga can compound din gidan, da saurinta ta fita ta samu ashe Hajiya babban ce zata tafi su Alhajin sun rako ta, bayan Hajiya babba tayi sallama da hajiyan wadda ke ta murmushi kamar bakinta ze yanke sai Abdullahi ya bude mata backseat ta shiga shima ya shiga gaban motan da nufin ze rakata, Na'ima na nan tsaye gefen hajiya tana jiran sanin dalilin kiranta da hajiyan tayi sai kuma ta ji shiru, dagowa tayi da nufin ta sake cewa "gani Hajiya" sai taga Hajiyan tabi bayan motarsu hajiya babba dake fita daga gidan da wani irin mugun kallo, bayan motar ta gama fita daga gidan Hajiya ta buga wani uban tsuka me karfi sannan ta juyo ta kalli Na'ima, shan jinin jikinta tayi da kallon da Hajiyan ta bita dashi, sai kuma Hajiyan ta wulla mata ledan hannunta zuwa jikinta cikin bacin rai tace "ki kai dustbin" sannan ta juya fuu ta koma cikin gidan tabar Na'ima nan tsaye riqe da ledan a jikinta, data je zubar da kayan ledan ne taga ashe fruits ne dasu daddawa  hajiyan ta kawo gidan, tana ta mamakin zubarwan da hajiyan tace tayi, haka dai tayi abunda aka satan sannan ta koma falon saman dan gama aikinta, bata kai ga qarasawa cikin falon ba taji hajiya na waya cikin daga murya tana zubo duk zagin da yazo bakinta, Jin takun mutum yasa hajiyan juyowa kunnenta kare da wayan ta kalli Na'ima, sai tace "Ina zuwa larai zan kiraki" tace da Na'iman "Meya kuma? Bakiga Ina waya bane?" Na'ima tace "nazo wanke bandakin ne" Hajiya tayi tsuka tace "to ki je ba yanzu ba"... Tafiyar Bilal qasar Luxembourg yin karatu be dawo Nigeria ba har se da Na'iman ta shiga ss1 a makaranta, zuwa sannan Na'ima har ta hakura da zuba ido akan ko Alhaji ze barta taje qauye, amma shiru gashi har zuwa wannan lokacin Allah be bata courage dinda zata bude baki ta tambayesu iznin zuwa ba, suma duk 'yan uwan nata na qauyen aka rasa wanda yayi tunanin zuwa na musamman ya duba halin da takeci a rayuwa, abun dai kamar sun kyautar da ita ne babu me buqatar ta kuma wanda hakan ba qaramin zafi yake wa Na'ima a zuciya ba ganin qannen mahaifinta sun banzatar da rayuwarta cikin halin ko in kula...kafin zuwa wannan lokacin Hajiya da Alhajin sunje Luxembourg bila adadi dubo dan nasu amma be dawo ba, Na'ima ta kanyi mamakin sosai akan wannan qauna da suke masa, in the sense that komai na rayuwan gidan revolves around Bilal duk da baya nan, kullum sai hajiya ta sata ta gyara masa dakinsa tayi mopping, hatta plates dake kitchen din gidan da cokula an ware na Bilal daban ko Hajiya bata amfani dasu.. Ganin gatan da Na'ima zatayiwa kanta shine karatun yasa ta maida hankalinta sosai akai, a inda akayi mata jumping din daga jss2 tayi jsce dinta ta wuce ss1, saboda girman da Na'iman tayi anan ma Sufi da aka bashi ragamar kula da makarantar ta yayi magana da alhajin akan zuwa ss2 zata gwada rubuta waec da neco dinta plus jamb, Alhajin ya amince da hakan dan shima yanason Na'ima tayi karatun, kawai dai matsalar shine rashin maida hankalinsa sosai akan yarinyar da baya yi akai akai, duk wani ragamar rayuwan Na'iman ya bada shine ga Hajiya wanda ita ma Hajiya se take riqon sakaina a marainiyar Allah'n... A ranan da Bilal zai dawo har Alhajin ma be fita gurin aiki ba tare da hajiyan suka fita sufi ya kaisu airport dauko dan gudaliyan nasu, aka bar su Na'ima na kacaniyar dafe dafen abinci daban daban, zuwa sannan Na'ima ta zama me aiki a gidan da qarfi da yaji dan ayyukanta a gidan sunfi na shafa yawa, samun sararinta shine in ta je makaranta, gashi islamiyan da aka saka shima sai Hajiya tana yawan hanata zuwa saboda sata aikin abincin dare da take yawan yi.. Isowar Bilal gidan suka fito daga motan bakin Hajiya kamar ya yage dan murna ta riqo hannun dan lelen nata, Bilal dake sanye cikin wata hoody riga ya saka duka hannayensa cikin aljihu sai wani qamshi yake, direct sama suka wuce suna magana da dan nasu dake amsa wa sama sama, Na'ima dake jera abincin nan kan dining table ta bisu da kallo, sai Bilal din duk ya canja mata a Ido, yazama wani cikakken saurayi dashi ga wasu Snickers da ya saka farare, kuma har zuwa wannan lokacin chain dince sanye a wuyan sa... Sai da hajiya ta tabbatar da ya sake wanka ta shirya cikin kayan da fito masa dashi sannan ta kamo kafadansa tana kallonsa tace "Babana kanacin abinci kuwa, duk ka rame" Bilal yace "inaci mana, dole na ai hajiya" sai ta sake kafadansa ta kamo hannunsa tace "muje gashican nasa ayi maka favorite dishes dinka" A falo suka tadda Alhaji ya kishingide akan kujera ya dago kai yana kallonsu, Bilal ya qarasa gurinsa zai zauna Alhaji yace "muje kaci abinci tukunna son" dan bata fuska Bilal yayi ya kalli Hajiya dake tsaye yace "Hajiya kisa akawomin nan" tace "Toh babana" ta juya ta fita da dan saurinta fuskarta cike da fara'a, su Na'ima ta samu a kitchen din tana juye pepper chicken acikin wani flask, ta dago kanta tana kallon hajiyan data shigo, sa Na'iman tayi taje ta fara daukan wa'inda takai dinning table din ta miqa sama acan Bilal zeci abincin, Haka Na'ima ta debi kayan a tray babba ta nufi sama, tunda ta shiga falon Bilal yake kallonta har ta ajiye kayan ta juya zata sake zuwa dauko wasu yabi bayanta da kallo, azuwanta ta biyu ne suka hada ido ta dauke kai tana jera abincin anan gabansa, bayan ta ajiye flask na qarshe sai ta gaishesa cikin sanyinta, ya amsa da "lafiya" bai kuma dena kallonta, miqewa tayi ta fice ganin irin kallon da yake mata, dakinta ta koma tayi wanka bayan ta fito ta shafa Vaseline dinta ta nemi wani kayan cikin 'yan qalilan dinda hajiya ta qara mata, dan sai Hajiya taga kayan jikin Na'iman ya kode yana neman yagewa sannan take qara mata kala biyu zuwa uku kuma Alhaji yasha bada kudi a mata dinkin amma Na'ima ta rasa me yasa hajiyan bata siya mata kayan... Yammacin ranar ta je falon sama gurin hajiya tambayanta me za'a girka, tasamu tana zaune kujera daya da Bilal yana nuna mata wani abu a waya tana kallo cikin murmushi, nan kan carpet Na'ima ta tsugunna tace "Hajiya me za'a dafa?" Hajiya ta kalli Bilal tace "Babana me zakaci?" Yadan sauke numfashi yace "komai ma is Okay" ta juya gun Na'ima tace "kiyi wani abu light kawai" Na'ima ta miqe Hajiyan ta sake cewa "kije can dakin shafa ki kiramin ita" ta amsa da toh zata fita Bilal yace "jeki kan gado na akwai laptop ki dauko" nan ma ta ce "toh" taje ta dauko, miqa masa tayi sai yace "ki riqe na baki" Hajiya ta wani hararesa tace "ban gane ka bata ba kuma, baka amfani dashi ne?" ya gyada kai, Hajiya ta sake cewa "toh dan baka amfani dashi se kace zakayi kyauta dashi, ita me zatayi da laptop" Na'ima dai na nan tsaye tana addu'an Allah yasa hajiya ta yarda a bata, dan yawancin yan makarantar su suna da laptop, Bilal yace "common Hajiya, in inaso ai bazan bata ba" Hajiya tace "Toh sai ita kadai kagani da zaka yiwa kyautan, bani laptop dinnan Na'ima" Na'ima tayi saurin miqa mata, ta sake cewa "yaushe tayi girman riqe laptop itadin, ni banason irin haka" Bilal ya miqe zai fita tace "Ina kuma zakaje, fushi kayi?" bai kulata ba ya nufi hanyar fita sai ta wullawa Na'ima laptop din tace "gashi ai na bata kuma" shidai bai kulata ba ya fice, ai da sauri Na'ima ta bi bayanshi gudun hajiya ta kuma kwace laptop din, A matattalan stairs din ta iddasa tace "Nagode yaya" ya juyo yana kallonta yace "kina aji nawa yanzu?" Tace "ss1" ya bita da kallo sannan yace "you've grown up Na'ima" sai tayi murmushi tazo zata wuce sa kawai ya kamo hannunta, saurin yin baya tayi ta janye hannun nata, sai yace "kwaro nagani a hannun naki fa" tayi saurin dago hannun nata tana dubawa sai yayi murmushi yadan jijjaga yace "silly" sannan ya juya ya fice daga falon ya barta nan tsaye tana kallon bayansa, da murnanta ta kai laptop din daki tana murmushi, rabonta da tayi murna haka harta manta, dayake makarantar kudi Na'iman takeyi sai ya zamto ita kadai ce batada laptop din, kuma malamin computer dinsu yasha mata magana akan hakan, kawai batasan wa zata fadawa bane, dan tasan ko giyar wake tasha bazata fara fadawa Alhaji a gaban Hajiya ba.... Bata sake haduwa da Bilal ba dan ya dawo da wani irin yawo na masifa, sai ya jera kwana biyar sai dare ya raba yake dawowa gida.. Ranan Na'ima na kitchen tana tace shayi da dare aka bude kitchen din Bilal ya shigo, kulle kofar yayi yana kallonta yace "Na'ima aiki kike" ta gyada tana gyada dan gyara dankwalinta dan jikinta babu hijabi, ya qaraso nan inda take tsaye yace "kwana biyu baki ganni ba bakya cigiyata ne" Na'ima duk ta taqura da irin kallon da yake mata tace "A'a yaya" sai yace "nima zansha tea din kinji" ta gyada kai ta juya zata dauko cup yabi bayanta da kallo kamar idanusa zasu fado, bayan ta zuba shayin sai ta miqo masa, madadin ya karba sai ya hada da hannunta ya riqe, da sauri Na'ima tayi nufin kwace hannun nata sai ya damqota hannun da dayan hannunsa yana kallon idonta, kiciniyar kwace wa ta fara tace "yaya kabari" yayi qasa da murya yace "babu abunda zan miki, kawai riqeki zanyi kinji" tayi saurin jijjaga kai tace "banaso yaya" sai ya bata rai ya sake hannun nata tayi saurin yin baya ta fice daga kitchen din ta kofan baya jikinta na rawa, zagayawa Na'ima tayi ta shiga falon ta gaban compound din gidan, hajiya ta gani nan gurin stairs tana sauqowa sai tayi stiff anan tsaye tana raba idanu, Hajiya tace "Ina shayin dana sa ki kawomin" Na'ima ta kasa cewa komai, Hajiya ta sake cewa "daga ina kike daga wajen" jikin Na'ima na dan kyarma tace "naje..uh..uh.." Bilal ne ya fito daga kitchen din fuskarsa a dinke, hannunsa riqe da cup din tea yakai baki yana kurba anan tsaye yana kallon Na'iman, ganinsa yasa hajiyan cewa "Babana yanzu fa nace ta zubo maka shayin ta kawo, ashe ka gaji da jira ka debo abunka" ya daga kafada baice komai ba, Hajiya ta kalli Na'ima dake nan tsaye tace "wato anfara zuwa gandun da zan saki aiki ki ajiye nawan kiyi wani

Chapter 14 of 19